Join Our WhatsApp Group

YAYA DA DUKIYA BA'A KETARSU Complete Hausa Novel Document by YAYA DA DUKIYA BA'A KETARSU


YAYA DA DUKIYA BA'A KETARSU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 20100



YAYA DA DUKIYA BA'A KETARSU

Reading Time: 1 Hours

Added On: 11, Nov 2023

Author: Rasheeda A Kardam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 111.51 kb

File Type: txt

Views: 402+

Download: 141+

Last download: 2 days ago

Description/Story: YAYA DA DUKIYA BA A KETAR SU

Na Rasheedah A kardam

Ebook creat by Shuraih Usman

Ebook publish by www.hausaebooks.cf

Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf

Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai



Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com

YAYA DA DUKIYA BA’A

K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. ﻦﻤﺣ ﺮﻟﺍ ﻟﻠﻪﺍ ﻢﺴﺒﻟﺍ

ﻩﺮﺳﻭ ﻪﺘﻴﻧﻼﻋﻭ ﻩﺮﺧﺁﻭ ﻪﻟﻭﺃﻭ ،ﻪﻠﺟﻭ ﻪﻗﺩ ،ﻪﻠﻛ ﻲﺒﻧﺫ ﻲﻟ ﺮﻔﻏﺍ ﻢﻬﻠﻟﺍ . ﻢﻴﺣ ﺮﻟﺍ.

ﻢﻴﻫﺮﺑﺇ ﻝﺁ ﻰﻠﻋ ﺖﻴﻠﺻ ﺎﻤﻛ ﻪﺘﻳﺭﺫﻭ ﻪﺟﻭﺯﺃ ﻰﻠﻋ ﻭ ﺪﻤﺤﻣ ﻰﻠﻋ ﻞﺻ ﻢﻬﻠﻟﺍ .

ﻚﻧﺇ ،ﻢﻫﺮﺑﺇ ﻝﺁ ﻰﻠﻋ ﺖﻛﺮﺑ ﺎﻤﻛ ﻪﺘﻳﺭﺯﻭ ﻪﺟﺍﻭﺯﺃ ﻰﻠﻋﻭ ﺪﻤﺤﻣ ﻰﻠﻋ ﺖﻛﺭﺎﺑﻭ

ﺪﻴﺠﻣ ﺪﻴﻤﺣ . GATARWA Dukkan yabo ya tabbata ga Allah.

Ina godiya a gare sh’i, ina neman taimakonsa, ina neman

gafaransa, kuma ina neman tsarinsa daga sharrace-

sharracen rayukanmu da mitagyn ayyuka. Wanda Allah

ya sh’irye sh’i babu mai b’atar da sh’i, wanda kuma ya

b’atar ba mai sh’iryar da sh’i. Ina shaidawa babu abin

bautawa da gsky sai Allah, shi kad’ai, babu abokin

tarayya gare sh’i. Ina shaidawa cewa Muhammadu

bawansa ne kuma manzonsa ne. Ya Allah kayi tsira ga

wad’anda suka bish’i da ky’aky’awan kw’aikw’ayo har

zuwa ranar kiyama. Kuma ka musu aminci, aminci mai

yawa Ameen. SADAUKARWA Na sa daukar da wannan

littafi mai sun YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU, ga

Mummy’s d’ina Khadija’s. GODIYA godiya mai d’imbin

yawa gareku, da bazarku nake taka rawa a duniyar

Rubutu, Allah ya barmu tare. Maryam .S. Bello Maryam

Alkali Mamu(Mrs Jabo). Page-1~5. Tari wanki ne a

gabanta, sai faman wanke su takeyi, kalo d’aya zaka mata

ga gane ta gala baita sosai, har k’arfin har bata jin karfin

jikinta. Gwaggo ne ta taho da wasu kayan wankin ta kara

mata, tace “Khadi maza- maza kiyi sauri ki wanke ma

Beeba kaya, zata gidan Innarku. A wahale na d’ago nace

“Inna ga wasu sabbin kayanta can na wanke su, sun

bushe tasa su, kuma suna da ky’au, gash’i nayi wankin da

yawa na gaji. Gwaggo wani uwar ashar ta narko, wanda

ni Rash bansan lokacin da nayi baya da sauri ba. Shako

ta Inna tayi tace”dan jakar ubanki ni zaki fad’a ma kin

wanke wasu, kuma har kina iya cewa kin gaji. Eh!

Lallekam yau zaki gwadan ke yar Zamani ce, ban isa dake

ba ko?. Khadi cikin muryan kuka tasoma cewa”dan Allah!

Gwaggo kiyi hak’uri wlh ba da wara manufa na fad’i

hakan ba. Gwaggo kara shaketa tayi tace”ko uwar ki ma

bazata mayar min da martani ba. Kafin Khadi tayi

magana ji kake tass tass tass ta wanke ta da mari har sau

uku, dukanta tafarayi ta kota ina. Wayyo ni kaina Rash na

tausaya ma Khadi, don ga alama fuskan gwaggo nan bata

da tausayi ko kad’an Taku a kullum mai k’aunar ku ﺪﻴﺷﺍﺭ

9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA

DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-6~10. Gwaggo sai da tayi likis ma Khadi kafin ta

ky’aleta, tace”wlh sai kin gama wankin nan yau ko na

miki dan banza duka, sha-sha kawai, mts tayi tsaki ta nufi

cikin d’akinta. Khadi kam kuka tasha ga wani yunwan da

ke murd’amata ciki. Kama cikin tayi ta tamke da d’an

kwali abunka da Khadija maganin Maza cikin dakiyar

zuciya ta fara wankin , da ikon Allah kafin akira Sallah

la’asar ta gama. Gwaggo ta fito da abinci a d’an k’aramin

kwano wanda ko d’an yaro bazai ish’esh’i ba. Ta turo

mata kwanon ta juya tayi d’akinta ko tausayin Yarinyan

nan bata ji ba. Ga uban aikin da ta mata a cikin gidan

kamar jaka. Malam Ahmadu ne ya sh’igo da Sallamansa,

in donsa ne ya sauk’a kan Khadi dake kwance tamkar

wanda aka d’aura ma dutsin dala da gauron dutsi aka. Da

sauri ya k’arasa gurinta cike da tausaya wa, ya tallabo ta

yace “Mama na ya dai? Mai ya same ki na ganki haka? .

Gwaggo ta fito cike da masifa tace”komai ne ya same ta

ko zaka karb’a mata ne, sai in sani. Cike da b’acin rai

Malam Ahmad ya nufo ta, yace”kee Hauwa wlh ki kiyaye

ni zan sas-saba miki akan Khadija sam ba kya tausayin

yarinyan nan. Gwaggo tace “ina ko zan tausaya mata ba

sanin zafinta nayi ba bare na san miye tausayi. Malam

yace”duk aikin da take yi a gidan baky’a gani ko?. Kuma

ba ky’a sanya yar cikinki. Wannan yarinya Yata ke a gun

mu, duk irin rikon da muka mata Allah zai tambaye mu,

Hauwa kiji tsoron Allah. Gwaggo tace”ehehe wa’azi

zakamin ai tsoron Allah kulum cikinta muke, yar wani ba

yata bace nawa kawai na san, fuuu tayi d’aki in ka gama

sai ka sanar min. Taku a kulum mai k’aunar ku ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺪﻴﺷﺍﺭ

9:12] ﻡﺩﺮﻛ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA

DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-11~15. Cikin ta kaici yazo ya tallabi Khadi ya d’agata

sai a lokacin ya kalli d’an abinci da gwaggo ta bata.

Taburma ya d’auko a d’akinsa ya sh’in fid’a mata, ya

zaunar da ita. Kular abincinsa ya kawo mata tare da juye

ruwa mai zafi ya had’a mata Lipton ya bata da kyar ta iya

sha. Abicinsa ya kara mata, sai da ya tabbatar ta kosh’i

kafin ya ci sh’ima. Khadi ta mik’e jiki ba kwari ta nufi

rijiya ta d’ebo ruwa ta nufi bayi, wanka tayi ta fito, ta sha

fa mai kayanta masu d’an kyau ta saka ta dawo waje gun

Malam don gudun bala’in Gwaggo. Malam yace”Mama

nah bazan fasa miki nasiha ba, inaso ko kasance mai

yawan hak’uri kinga halin Gwaggon ku kullum Addu’a

nake mata Allah yasa ta gane gsky. Khadiya duk halin da

kika samu kanki, ki kasance mai hak’uri zakici riban

rayuwanki. Kai ta d’aga masa alamae Eh!. Heeba ce ta

sh’igo da Sallaman ta, cikin fara’a ta k’araso gun su,

sannu da gida ta musu kafin tace”Addah ina ta sauri inzo

in tayaki aiki, da aka tash’i a makaranta, ban samu abun

hawa ba, Gash’i har kin gama. Khadi tayi murmushi

tace”ba komai k’anwata, ya makaranta?. Alhamdulilah! Ki

d’auko abinciki kici to Adda. Malam yana jin dad’in

yanda yaransa suka had’a kai, baran Beeba da sam bata

gado halin uwarta ba, heeba ya rinya ce mai hankali

kamar Khadi. Sabanin Rabi da ke ji da taken rash’in

kunya, halinta sak na uwarta hatta kama da Gwaggo take

kama. Gwaggo tafito tsawa ta daka ma Beeba kee mai

kikeyi a gunsu, kin dawo ko sanar ni bazakiyi ba, ni bana

son kina taraya da mai fiska kaman na muciya. Oh! Ni

Rash nace”wannan Gwaggon wata irin macece ta fiye

son kanta, anya ma idonta na gani kuwa?. Duk irin kyan

Khadi tana zaginta. Ko beeba ma bazata gwada mata

kyau ba don ta d’aran mata nesa ba kusa ba. Taku a

kullum mai k’aumarku . 9:12] ﻡﺩﺔﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺪﻴﺷﺍﺭ PM,

9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A

K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-16~20. Jiki

ba kwari Beeba ta nufi d’akin, don sam ita bata son irin

yadda mahaifiyarta ke nuna tsana ma Khadi. Gash’i ko

kad’an Khadi bata nuna damuwarta kuma hakan ba sh’i

zai hanata biyayya ba.Allah yasa Gwaggo ta gane. Ya

sh’irya mana ita Ameen. ‘Dakin su tash’iga Gwaggo ta

balbaleta da masifa, Gwaggo tace”Beeba bana son ganin

ki da wancan mai fuskan mujiyan, kema kuma sai niman

kai kike da su. Ni har Malam da ke biye mata ba kyalesh’i

zanyi ba, ko kad’an bana k’aunar in bud’e ido imganta a

gidan nan. Beeba tace”haba Gwaggo ba kyau fad’an haka

fa, kuma ae Addah tana iya k’ok’arinta gurin kyautata

miki. Ita ne kulum cikin aiki bata hutawa ko ni bana miki

aikin da take, nikam ina son Addah na tana da halaye

mai… Bakinta Gwaggo ta make tare da wata harara

tace”kee a kul d’inki kar na kara jin cewa kina had’a kanki

da wannan yarinya, Ko kema ta shanye miki Zuciyan ne?,

kama yanda ta shanye na Malam baya ganin laifita baya

son amata fad’a. Beeba tace”ko d’aya Gwaggo gsky kenan

Khadi tana da halaye mai kyau. Mts Gwaggo ta ja tsaki ga

abinki can maza ki ci don zaki gidan Innan ku, zaki anso

min aika a gunta. Beeba ta d’auko abinci zatafita gunsu

Malam Gwaggo ta dakatar da ita, ba yanda ta iya dole

yasa taci a d’aki badan taso ba, don ta fi jin dad’in

kasancewa da yar’uwanta. Gwaggo tace”Beeba yi sauri ki

sh’irya kije min gidan Inna ku. To ta amsa ta kammala

cin abinci tayi wanka ta d’auko kayanta masu kyau ta

sanya su, ra fes da ita. Gwaggo “nagama sh’irin ke nake

jira kizo fad’an sakon, don inje kar dare ta min a hanya.

Sai da Gwaggo ta d’auko sakon da zata kai ma Inna kafin

ta bata kud’in mash’in tace”kice ta had’a miki duka aikan

harda kayan da na saya d’in, to ta amsa ta fito sai da tayi

sallama wasu Malam kafin ta tafi. Taku a kullum mai

k’aunarku 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺪﻴﺷﺍﺭ PM, 9/14/2016] Rash

Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM. Notice Masu karatu na zansa

sunan littafina daga KHADEEJATUL-KUBRAH zuwa YA’YA

DA DUKIYA BA’A K’ETARSU, cos Daman YAR’RIKO ne suna

Da na fara sawa, sai aka samu wacce tayi. So yanzu

namar dashi YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU. Yafi

ma’ana kuma sakon littafin akan haka zai tafi. Pg-26~30.

Ana kiran sallah tayi d’akin su ta kwanta, kasanewan

garin da sanyi lokacin hunturu ne. Addu’a tayi ta kwanta

ga yunwar da ke addabarta. Haka har bacci b’arawo yayi

awon gaba da ita. Dukun-kune take a yar ta barmata gefe

kuma katifar Beeba ne yar k’arama wanda mutum d’aya

zai d’auka. Bacci take amma sanyi ya dameta. Kiran

Sallah asuba ya farkar da ita da kyar ta mik’e ta d’ibo

ruwa a randa sai d’ari take yi. Alwala tayi ta koma d’aki

tayi sallah bayan ta idar ta fara azkar d’in safiya wani

bacci ne ya d’auketa kamar daga sama taji an shek’a

mata ruwa mai sanyi nan take ta fara d’ari-d’ari, duk da

haka Gwaggo bata kyaleta ba wani ruwan ta k’ara kwara

mata. Barin da takeyi ya tsananta, Gwaggo tace”ke har

kimsami daman da zaki kwanta bacin safe, uban wa ya

baki dama?. Malam yana karatun Al-qur’ani mai girma

sai yaji kamar ana hayaniya jin maganan yayi yawa ya

fito, yaji d’akin su Khadi ne da sauri ya sa kai cikin d’akin

ganin Khadi ta fi luuuu zata fad’i yaje da sauri yana”Salati

ya tare ta fad’a a hannunsa cikin k’unan rai ya d’ago ya

kalli Gwaggo yace” in kin kasheta ae kin huta, kin san

yarinya tana fama da Pneumonia kuma yayi mata yawa

zaki kwara mata ruwan sanyi, haba hauwa anya kina

tsoron Allah kuwa ae d’a ko ba kai ka haifeshi ba, bai

kamata kina wula kanta ta ba.( Yan uwa mata kira

gareku, kune jigon gida duk lokacin da gida yayi kyau

kune, kusani Ya’ya da Dukiya, da Dabba ba’a mugun tar

su. A rauwa ba kasan wanda zai taimake ba, sai kaga d’an

da ka haifa da cikin ka wani lokacin bai jik’anka ba,

wanda baka san zafin sa ba ya taimake ka kuma Ya’ya

Rahmane dan Allah kuna kyautata ma yara ba sai naka

ba ku d’auka duk d’aya suke a gunku). Gwaggo ko a

jikinta tayi waje tana cewa”ni dai dole ta fito ta min aiki

yau ko ta ji a jikinta. Malam ya kali Khadi ta idanunta

suka kafe a sama da sauri ya d’auketa ya fita waje da ita.

Beba da ta fito daga d’aki ganin halinda Adda ta ke ciki

yasa tayi gun Malam da hanzari suka fita dake garin da

sanyi da kyar suka samu mai Napep yace”Yaro Asibitin

Murtala zaka kai mu, Malam da Beeba suka shigar da ita

ciki suka d’au hanyar Asibitñ, sun d’anyi tafiya kafin suka

iso asibitin, kud’in mai napep ya basa kafin ya d’auki

Khadi suka shiga cikin Asibitin nurse suna hango su, suka

tahoda sauri suka karb’eta. Emergency aka nufa da ita,

Dr Abdul ke bakin aiki, da sauri “nurse suka sanar masa

an kawo patient. Yace “ok! I’m coming now”. Bata dad’e

da isa gun su Malam sai ga Dr Abdul nan ya iso. Dubata

ya soma yi yaga tana wani yanayi numfashinta na shirin

d’aukewa, tai makon gaggawa aka bata cikin ikon Allah

suka samu numfashinta ya dai-daita. Magunguna ya

rubuta ya mika wa Malam yace”Baba gashi kaje

Pharmacy ka sayo, in ka dawo ka bawa nurse sai ka

same ni a office d’ina. Malam ya amsa da rawar jiki ya

nufi pharmacy. Taku a kulum mai k’aunar ku . ﺓﺪﻴﺷﺍﺭ

9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA

DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-21~25. Malam suna hira da Khadi Gwaggo ta fito

wani sak’on kalon da Gwaggo ta aika ma Khadi, yasa ta

mike ba sh’iri ta nufi kitchen ta d’aura girkin dare, sai da

ta magama aiki Gwaggo tazo ta d’auke tukunyan d’akinta

ta sh’iga dash’i duk abun da suke Malam na kalon su bai

ce mata komai ba. A zuciyansa ya na mai jin-jina bak’in

hali irin na Gwaggo, Malam ya mike ya fita waje zuwa

gurin da suke d’aukan karatu. Rabi ce ta sh’igo tayi

d’akinsu ta nufa ta dau naira goman Gwaggo tasa a

wando ta fita waje, alawa ta siya sai da ta shanye kafin ta

dawo gida. Gwaggo tazo d’aukan raina gomanta don a

siyo mata sikari ta saka a surki, taga babu kud’i cike da

masifa tazo ta danki Khadi tace”ke barauniya bani kud’i

na da kika d’aukar min wato satan ma gadonsa kikayi a

gun uwar ki. Khadi tace”Gwaggo ko d’akin ma ban sh’iga

ba ina zaune a nan gurin fa. Gwaggo tace”oh! Sharri zan

miki ko?. Ni a ya’ya na babu b’arawo ba mu gaji sata ba

sai dai ko gun uwarki ne zuri’an barayi. Nan take Khadi ta

soma hawaye jin takaicin yanda ake kiran iyayenta da

suke kasa. Eyeh lalle kin samu gu dan ban dakaki ba

shine kike kuka ko?. Gwaggo ta d’auko dorina tazane

Khadi sai da taji hannu ta ya gaji tace”naira goman da

kika d’auka a madadin abinciki na yau da kuma karin

safiya. Gwaggo ta juya zata tafi sai ta dawo ta rike kunne

Khadi tace”saura in Malam ya baki abunci ki karb’a ki

gani ni dake yau a gidan nan. Ina son ana kiran Sallah ki

sh’iga d’aki ban yarda ki leko waje ba, ina ga munanan

kafarki a guri kin san sauran ta nufi d’aki. Taku a kullum

mai k’aunar ku 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016] Rash

Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-31~35. Malam ya sayi

maganin dubu buyu da d’ari biyar ya nufo k’ofan

Emergency ya mika ma nurse “Malam ya tambayi office

d’in Dr Abdul nurse ce ta gwada masa, godiya ya mata

nufi office d’in, da Sallaman sa ya tura k’ofar aka bashi

izinin shigowa, Dr ya nuna masa gun zama Malam ya

zauna. Sai da Dr ya gama yan rubuce-rubucen sa tukun

ya d’ago da fuskansa tare da zare yar faran glass d’in da

ke manne a kyakyawan fuskansa. Malam ya msa sannu

da aiki,Cikin girmamawa ya amsa, kali Malam yace”Baba

jikin Khadeeja yayi tsanani sosai, mai yasa kuke barinta

tana aiki da ruwan sanyi?, kuma tana zama a inda ke da

sanyi, mai ya kawo hakan bacin na sha fad’a muku illar

hakan amma kun kasa koyayewa. Malam da jikinsa yayi

sanyi yace”Dr in Allah ya yarda wanan karon zamu

kiyaye fatan mu kawai yanzu ta samu lfy. Dr Abdul ya

kallesa sosai tabbas ya gano damuwa a cikin idonsa ga

alamar magana a bakinsa, amma tunda bai fad’a ba “ni

dai zanyi iya kokarina ganin na taimaka mata, ya Allah

kabata lfy ameen. Ya kalli Malam yace”shikenan zaka iya

tafiya amma akula mata da shan magani. Kai Malam ya

d’aga masa alamar eh!. ‘Dakin da aka kwantar ta ya

yashiga Beeba ya gani a bakin gadon ta zuba mata ido ga

alamar tayi kuka sosai. Da Sallama ya shigo Beeba ta

masa sannu ya amsa tare da zama a d’aya daga cikin

plastic chairs d’in dake d’akin. Yace”Beeba ya jikin Addah

ki?. tace” da sauki amma har yanzu bata tashi ba, bacci

take ya kalli Khadi yace”Allah ya baki lfy,...


Read / Download YAYA DA DUKIYA BA'A KETARSU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album