Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

KOFAR AJALI Book 2 Complete Hausa Novel Document by KOFAR AJALI Book 2


KOFAR AJALI Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 27515



KOFAR AJALI Book 2

Reading Time: 2 Hours

Added On: 14, Nov 2023

Author: Abdul Alhaji Musa 10k ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION

Author Phone : +2349077974042

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 154.01 kb

File Type: txt

Views: 779+

Download: 512+

Last download: 1 day ago

Description/Story: πŸ’€πŸ’€πŸ’€
*KOFAR AJALI*
_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
πŸ’€πŸ’€πŸ’€

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*πŸ’―βœ…
* EPISODE 0️⃣1️⃣*

*_NEW BEGGING_*

*Amrita!* *Amrita!*
Haka ake Kiran wannan suna cikin sauri kamar ana son dakatar da Mai wannan sunan aikata wata gagarumar abar...

Aiko wacce nake kyautata zaton itace Mai wannan sunan ta kasance tana tafe cikin zafin nama yayinda fuskar ta Babu annashuwa ko kadan,Shigar ta ofishin ta jibge wasu decoment dake rike hannun ta hade da cewa.

"What the heck,Mai kuke nufi da Kun sauke wannan binciken?."

Aiko fadar hakan keda wuya sai ga Mai Kiran sunan nata a baya ya shigo ofishin.

"Amritah Ya kamata ki dakatar da wannan shiriritar."

"Shiririta fa ka Kira abinda nake yi,Hm shin kasan Rayuka nawane a cen cikin had'ari?".

Haka Amritah da wannan santalele saurayi suka fara cacan baki kamar zasu doki junan but at the end juyawa tayi ta kyale sa Hadi da dawowa kan Jami'in dake zaune gaban ta.

"Ka iyya bude baki kace an sauke bincike Amma baka iyya d'aga katon tumbin Nan naka kaje binciken ba..."
Fadar hakan da tayi sai Wannan santalelen saurayin da suka shiko tare ya Kirawo sunan ta *Amritah* alamar ta tsayar da abinda take kokarin yi but sai hassalata Kiran sunan keyi haka tayi ta jifan sa da bakaken maganganu Hadi da cewar Babu ankin da suka iyya illa karban cin hanci,Kuma tayi takaici da gomnati tasa ragamar binciken a hannun su.

Wannan Dan sanda dai Yana da Damar daure ta but yayi shirune Dan mutuncin mahaifin ta da yake gani...
Amma dayaga abin ta soma wuce gona da iri sai ya Mike yayinda suka fara kaiwa junan su.... Kowa na fadar abinda tazo Masa a bakin,kamar Shirin film Yau dai ga rikici a ofishin Y'an sanda.

Wannan santalelen saurayin Hadi da Tarun ma'aikar gurin bude baki sukayi suna kallon su domin kuwa abin yafi karfin su.

"Amritah 2years fa ba kwanaki kadan bane."
Abinda ya fito daga bakin Wannan santalelen saurayin kenan yayinda sukayi shiru inda Amritah ta juyo ganinta izuwa kansa.

"bance Yayanki baya Raye ba,but Y'an sandan Suma suna iyyakan kokarin su wajen ganin sun shawon kan Komi da sunsan idan suke da tuni sun naimo su but they don't, that's why zasu sauke binciken domin duniyar da akawai matsaloli da Dama bazasu iyya tsayawa akan Abu daya har su kare ba."

Jiyo hakan yasa tayi sanyi,sauke kanta kasa tayi cen sai ta yunkura ta fice a fusace,Aiko fitar ta taja mota ta wuce...

Wannan santalelen saurayin ko ya fito cikin sauri inda ya tarar taja mota ta wuce...

"What's wrong with her?."
Abinda ya fito daga bakinsa kenan...

#Sunan ta Amrita,And Dalilinta na fada da wacen Dan sandar ko shine sun sauke bincike akan Yayanta Wanda suka 'bata shekaru biyu da suka wuce tare da abokan aikin sa....Duk da cewar wannan batan nasu ta dauki lokaci Mai tsawo but sai take ji ajikinta har Yanzu Yana a Raye...
Haka tayi driving babu inda ta tsaya sai Tsakar gidan su,inda ta sauka cikin sauri ta karasa ciki da shigarta ta tarar da Wannan santalele saurayin data Baro a police station zaune zaman jiranta..

Hada fuska tayi Ranta abace yayinda take kallon cikin Idanu sa..

"Aunt,Ni Bari in wuce gida."
Haka saurayin Nan ya furta inda ya Mike bayan sunyi sallama da matar dake zaune gefen sa..

Takawa yayi har ya wuce yayinda Amrita ke tsaye sai famar harararsa take...
Bayan ya fice daga falon ta Soma taku tadau hanyar dakinta na wannan mata ta kirawo sunan ta...

"Amrita!."

Cek ta take biriki yayinda matar ta mike tsaye ta tako izuwa gurinta ba tare da ta juya ba...

"Ya'u kinyi matukar bani kunya."

Cikin sauri ta juyo inda ta furta cewa...

"Aunt meye Kuma *Adam* din ya sanar dake Yau?*

_sunansa *Adam* kowace mace a duniya tana Tara kawaye da Dama yayinda itako Amrita aboki daya Tak gare ta wato Adam's..._
_Sun kasance tamkar y'an uwan juna sa'annan kuma sun kasance makobtar juna, sun tashi tare sunyi yaranta tare har izuwa manyantar su suna a tare and they're doing great, *best friends forever*_

*Let's get back to the business*

"Aunt meye Kuma *Adam* din ya sanar dake Yau?*

"Meye Kuma zai sanar Dani bayan anyi Komi akan Ido na."
Haka ta Bata ansa inda ta zura idanu auntyn nata ko ta karasa wajen ta Hadi da riko Mata hannaye ta Soma cewa.

"Amrita bawai bamu Son Yayanki *#Atif* bane, A'a we do love him and Muna hoping mu same sa ko yanzu, but what you're doing it's not right kwata kwata abinda kikeyi bai dace ba..."

Sauke Kai Amrita tayi inda Auntie nata ta jata izuwa bakin kofar dakin da Mahaifiyarta ke kwance tasa hannu ta bude Hadi da cewa

"Amrita dubi Halinda ummar ku ke ciki bayan 'batar Atif."
Ajiyar zuci tayi gami da cewa..
"Komi nata ya dawo baya,kullum itace kamar Babu Komi but hakan na cimata rai, lokacinda kuka kasance kuna cikin farin ciki tare da Mahaifiyar ku ba haka take ba Amma yanzu ta sauya kullum tunanin Atif,Kuma har Yanzu kimanin shekaru biyu Bata daina Kiran sunan sa a mafarki ba."

Ije maganar tayi yayinda kwalla ta ciko idanunta Amrita ma haka Nan sai ta rungume Amrita Hadi da sake cewa...

"Idan y'an sanda suka daure ki bansan halin da Yar uwata zata shigaba Dan Allah karki sake irin wannan abin domin Allah kadai yasan halin da zata shiga idan ta rasaki."

Haka ta cika Mata hannu ta wuce ta kyale Amrita tsaye bakin kofar,sukum tayi tana kallon Mahaifiyar tata cen sai tayi furucin cewa..

"Ina sonki Mummy."
Bayan Nan ta wuce dakinta inda da shigarta agogo ya buga 06:00pm Shep Nan sai ta bude window ta leka motar data Bari a bakin get bayan ta duba lafiyar motar ta dawo da ganin ta Hadi da wucewa ta shige toilet....

Anwala tayi sa'annan Bayan ta fito tayi sallah bayan ta idar ta sauka suka ci abinci sai tayi sallama da aunt, Mummy ta hade da Daddy sai ta dawo dakin ta...

Nan ta Ciro wata farar pepa tayi rubutu akai ta aje a center table,cikin kankanin lokaci tayi shiga ta kananun kaya baki wuluk.

Ko minti guda Bata sake ba ta ficce daga dakin ta window...batare da kowa ya ganta ba Aiko fitar nata keda wuya wannan fefar datayi rubutu akai iska ya fureta ta fado cikin motar nata wacce kirar *Highlander ce* ,Jan motar tayi ta wuce...

Faka motar tayi gaban wani tsohon gini inda tayi fito...
Shiru kake ji Babu motsi ko kadan a gurin cen sai taji an dire a saman motar ta inda tayi matukar firgita,Aiko datayi yunkurin lekawa wajen sai tayi arba da wasu karti hudu Suna karasowa wajenta Nan tayi saurin kulle motar ta d'aga gilashin Motan cikin tsoro ta Marne jikin kujeran but then da tayi arba da wacce ta dire mata a saman motar sai tayi tsaki Hadi da bude motar suka shigo ciki.

"Amrita irin wannan tsoro haka."

Haka wannan yarinyar ta fada inda Amrita tayi saurin cewa da ita...

"Aiko ba haka muka tsara ba,mundai tsara anan Zan dauke ku bawai anan zaku tsoratar dani ba."

Fashewa sukayi da dariya inda Amrita taja motar suka wucce.

Wannan karti hudu dai sun kasance cikin shiga ta bakaken Kaya wacce tayi musu kyau sosai yarinyar cikinsu ko tata Shigar tayi matukar karbar ta Danko kab Babu Wanda ya kaita kwalisa,ta wani bangaren ko tayi kama ganstar wato Y'ar ta'adda.

Karamar bayani game da wannan tawagar......Sun kasance sojojine Wanda sukayi murabus Babu dalili Dan kuwa ko ritsa su kayi ka tilasta musu susanar da Kai dalilin su na barin aiki Bazasu iyya baka ansa ba .

Sun kasance suna karbar kowace irin aiki Mai kasada idan har sukasan akwai samu a ciki wacce hakan ne ta hadasu da Amrita suka Kuma shirya shiga wannan Daji da yayanta Atif ya Bata a ciki shekaru biyu da suka wuce.....domin naimo su ko Kuma samo bayani akansu.

Haka sukayi ta tafiya Mai nisa yayinda suke ta fira hade da Raha...

"Amrita shin kin Sami taswirar guri kamar yadda muka bukata?."
Haka shugabar tawagar ta tambayi Amrita inda ta sanar da ita...


Read / Download KOFAR AJALI Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album