Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

GIDAN NAGOGGO Complete Hausa Novel Document by GIDAN NAGOGGO


GIDAN NAGOGGO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 23842



GIDAN NAGOGGO

Reading Time: 1 Hours

Added On: 20, Jun 2024

Author: Fateezah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : HIKIMA WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 130.67 kb

File Type: txt

Views: 564+

Download: 400+

Last download: 32 minutes ago

Description/Story: *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO* 🏨


This is my first novel.




*A true life story*

*Written by fateeyzah 🥰🥰*

Bismillahir rahmanir rahim.


Page0⃣1⃣




Tsawar da naji shi ya dakatar dani da bude dakin Ammy na.
"wallahi Bahijja in kika shiga dakin nan sai na bata miki rai,Uban mai kika zo yi mini a gida,ki tashi ki koma inda kika fito,tunda baki daukeni a bakina komai ba "cewar Alhaji kenan.
Take naji wata wata fargaba ta ziyarceni,wai yaushe zan fara samun kwanciyar hankali da maslaha tsakanina da Mahaifina,maganar Ammy tace ta tsinke min dan gajeran tunanin da na shiga wacce take tambaya abunda ke faruwa.
Alhaji ne ya fara magana cikin fushi "Amina ki juya ki koma ciki, in ba so kike fushin wannan mara kunyar ya shafeki ba,in kuma ba haka ba wallahi zanyi mummunar saba miki".
Da sauri na juya domin fita daga gidan don ganin Ammy na ta juya tana hawaye,ji nayi na tsani kaina,don tun ina Yarinya har girmana ta dalilina Ammyna ke zubar da hawaye.
Daga gefen gidan na tsaya ina kokarin tsaida hawayena da tunanin mafita.
Yanke hukunci nayi kawai akan na tunkari gidan Yaya Baffa wanda shine Babba a mazan gidan,don ina tunanin duk da 'Yan Uba nake dashi zai iya taimakona ya rokan mun Alhaji duk da wannan karan bansan laifin da nayiba.

Achaba na tare na hau tare da fada mai Anguwan dazai kaini,cikin 10minutes muka isa gidan saboda bamu da nisa,kasancewa Alhaji yana Banzazzau shikuma Yaya Baffa yana filin Mallawa,sallamar dan Achaba nayi na karasa nayI knocking din gidan,after some seconds Gateman yazo ya budemin tare da mun sannu da zuwa na kutsa kai harabar gidan.
Gida ne wanda ya amsa sunansa wanda kallo daya kayi ma gidan kasan mai gidan ya jiku da naira,hanyar da zata sa dani da main door din gidan na nufa,zuciyata na bugawa kamar zata tsago ta fito saboda shima bansan irin karban da zaya min ba.



More comment,more typing.

Yaya zata kaya tsakanin Bahijja da Yaya Baffa.





*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO* 🏨


*A true life story*

*Written by* *fateeyzah** 🥰🥰


Bismillahir rahmanir rahim .




Page0⃣2⃣


....Knocking din main door din nayi ,sai da nayi some seconds tukunna aka bude min kofar,Murmushi tamin tare da cewa "Bahijjah ce,sannu da zuwa,yaushe a Garin" dukka ta min wannan tambayar a lokaci daya.
Nima na maida mata da martanin murmushi tare da cewa"Nice Aunty Hanna,yau nazo".
"Karaso ciki mana"cewar Aunty Hanna.
Shiga cikin parlour nayi tare da kulle kofar,nan danan ta cika mini gaba da Snack da Drinks,tukunna ta zauna muka kuma gaisawa tare da tambayarta ina Yara.
Tace "Sun tafi school.
sannan tace "kici Snacks din mana"
Nace "Aunty Hanna bazan iya cin komai ba,don Allah Yaya nanan"?
Ta amsa min da"Yana nan bari inyi masa magana amma don Allah Bahijjah ki daure ki danci Snack din ko kadan ne".
Na amsa da "to Aunty"
Tashi tayi ta nufi ciki,ni kuma nasa Hannu na dauki Samosa daya na fara ci,ji nayi kamar ina cin magani.

Sun dau lokaci Basu fito ba,don har na fara gundura da zaman,sai gashi Sun fito dukkansu fuska ba yabo ba fallasa,nan da nan nasha jinin jikina,na zamo daga one sitter da nake zaune na gaisheshi,Ya amsa fuska a hade kamar hadari,sannan na koma na zauna,suma suka zauna a 2sitter dake facing din inda nake zaune.
Gyaran murya Yayi tare da tambaya ta"me ke tafe dake"?
Muryata a sanyaye nace "Yaya nazo ne don Allah ka taimake ka rokan min afuwa a gurin Alhaji Don naje ya koreni,kuma ni bansan mai nayi mai ba wannan lokacin "na kara she tare da kokarin maida kwallar dake barazanar saukomin.
Ya tambayeni "Bahijjah kikace baki son mai kikayi ma Alhaji ba"?
Na amsa da gyada kana sama.
Yace" alhaji Yace tunda kika koma Sokoto baki taba kiranshi kin gaishe shiba har maganar auren nan naki da ya taso,baki kira kin sanar dashi ba sai da Yaya Arsala ya kira shi ya fada mai,kuma Tace yana ji kuna waya da Ammy,amma shi kin maida shi Makiyinki,yanxu watan ki nawa da komawar ki Sokoto amma ko so daya baki taba kiranshi ba,yanxu tsakaninki da
Allah Bahijjah kin
kyauta?,yanda fa Ammy keda hakki a kanki haka Alhaji shima yana da hakki a kanki".

Kaina a duke nace"Yaya nasan nayi laifi amma wallahi Yaya ko na kirashi baya dauka,so uku ina kiranshi bai daukaba,shi yasa ni kuma ban kuma kiransa
ba,saboda na dauka bai bukatar gaisuwar tawa".

Kara gyaran murya yayi tare da cewa"look Bahijja ni kwata kwata ban ganin laifinku,na Ammy nake gani,amma zan sami Alhaji muyi magana,yanxu dai mai ya kawo ki garinnan,ina zaton yau saura 3weeks bikinki?"ya karashe da tambayata.
Nace"Kaduna zan wuce,in gyara kayan bed dina"
Yace"to da kike maganar gyaran kayan bed
kina da kudi ne?"
"eh,angon ya ban 10k saboda in gyaran kayan"
Anan Aunty Hanna ta saka baki tare da cewa«Honey,ni a ganina da Bahijja tabar maganar gyaran gadonnan kawai ka canza mata sababbin gado,tunda wancan auren nata shekara 10,kaga sun tsufa da yawa"
Yace"A,ah Sweety kibarta taje ta gyara kayanta,tunda tazo da niyyar gyarawa"sannan ya juyo gareni tare da cewa"Bahijja kije ki gyara kayanki,zan sami sauran 'yan uwa muyi maganar gudunmawar da za a hada miki ".ya karashe tare da mikewa yana kallon Aunty Hanna sannan yace Sweety ni na dita,in zata tafi ki duba drawerta ki bata 2k tayi transport"
Bai jira cewarmu ba yasa kai ya fita,sai da mukaji fitar motor dinshi sannan Aunty Hanna ta juyo tare da cewa"Bahijjah kiyi hakuri da rayuwa wata rana sai labari".



Fateeyzah



*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


*GIDAN NAGOGGO* 🏨


*A true life story*

*Written by fateeyzah* 🥰🥰


Bismillahir rahmanir rahim


Page0⃣3⃣







Nace "to Aunty nagode,kuma muna nan muna kai kukanmu wurin Allah,Allah ya kawo mana dauki a wannan rayuwar ta gidanmu,wallahi Aunty Hanna ban damuwa da kaina akan yanda nake damuwa da mutum biyu wato Ammyna da Aunty Zubaida,kina gani yanxu Aunty Zubaida abin nata kamar hauka amma duk da haka Alhaji yaki dena fushi da ita,kuma yace idan Baban Fadila ya maida ita gidanshi,wai bashi ba Baban Fadila".
"aini Bahijja ban ganin laifin Alhaji sai na Ummeey da yaranta Mata,wallahi wadannan ba Allah a ransu,shi yasa nake fadin ma Honey ya bar yadda da kananan maganganunsu amma yaki,kiri_kiri sun tsare ko inna acikin gidan suna gidan aurensu amma kunnansu na gidan Alhaji,duk su suke hada fitina,shiyasa ranar da muka yi da Mamy na wanke ta tsab wai naje gidan Alhaji ta fara min hayagaga wai in fita daga gidan tunda ba gidan Ubana bane,ni kuwa nace mata ai tasan nawa gidan Uban yafi nasu,don baza ma a hada gidanmu da nasu ba,wai fa duk abinda ya kawo fitinar sunce wai Alhaji ya karbi dukiyarshi a wurin Honey saboda wai da kudin yake Almubazaranci wai yana kashemun".
Nace"ai mu Aunty 'Yan dakinmu duk abinda yake faruwa a gidannan bama sani,kina ganin Asma'u da take kusa da gidan ma Alhaji ya hana ta zuwa wai sai bayan 3month saboda wai 'yan dakinmu muke hada fitina a gidan,tsakani da Allah ga Mamy nan da kullin tana gidan da ita da Mijinta da 'Yarta amma su ba a hanasu zuwaba sai mu".
Aunty tayi gyaran murya tare da fadin"kedai Bahijja mubar maganar nan Allah ya shiryesu,don ni ina fada ma Honey abun kunya ne a wurinsu ace kamar gidan Alhaji Nagoggo,ana Samun wannan matsalar.yanxu wai a ina za ayi bikin tunda Alhaji yace badai gidanshi ba kuma kinga Dokoto tayi nisa".
Nace"Mun yanke shawara zamuyi biki ne a Kano gidan Aunty Aisha tunda kin ga nan zan zauna".
"Ok,yanxu abunda za ayi in kinje Kaduna kin dawo ki biyo tanan ki karbi bedsheets a matsayin gudunmawa ta don
nasan ba bari za a yi inje bikin ba".
"shi kenan Aunty na gode,Allah ya kara budi".
Tace "amin,ina zuwa".
Tashi tayi ta Shiga daki,sai da tayi like 3minute tukunna ta fito ta mika min kudi tare da cewa "Ga 12k nan,2k kudin da Honey yace in baki na transport,10k kuma ki kara a kudin gyaran bed".
Take naji kuka ya tawo min na mike tsaye tare da rungumeta ina kuka tare da mata godiya.
Itama kukan ne yazo mata tare da cewa"Allah ya tona asirin wanda ya raba Bahijja da Alhaji,yanxu Bahijja akan 12k kike kuka,sai kace wadda aka bata millions".
Nace"Aunty ba komai ya sani kuka ba,sai alamarin Ubangiji dana tuna,wai yau nice na ke murna akan 12k,abunda lokacin da nake auren Tasi'u nafi karfinsa,sai dai ni in
bada,lallai na yadda duniya juyi juyi wanda ya dauketa da fadi yana tattare da wahala,Allah dai yasa mu dace".
Tace Amin Bahijjah.
Mikewa nayi tare da saba jakata Nace Aunty ni xan wuce dai na dawo a gaishemin dasu Baby,ta amsa da za su ji,Rakiya ta yimini har main door tukunna muka kuma sallama ta juya,ni kuma na fice gidan,Achaba na hau wanda zaikaini Agoro Motor Park don in shiga Motar Kaduna.





Wacece bahijja?

Pls manage

🖊fateeyzah


*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download GIDAN NAGOGGO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album