Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

RAINA KAMA Complete Hausa Novel Document by RAINA KAMA


RAINA KAMA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 304723



RAINA KAMA

Reading Time: 25 Hours

Added On: 14, Aug 2023

Author: Billyn Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 1.86 mb

File Type: txt

Views: 11111+

Download: 16800+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story:  *_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._*
👉🏻1⃣





assa
https://2gnblog.blogspot.com/
*Matsanan cigar* hayaniyar dake tashi agidan ce taja hankalina, cikeda bak'in ciki natashi daga barcin safen dana koma, fitinar gidanmu dabance data kowane family House dana Sani kona ta6a jin labarinsa a rayuwata, haka gidan namu yake kullum tamkar kasuwar 'yan danbe, daga matan gidan zuwa 'yan mata da yara tamkar muna ganin hanjin juna, saika rantse badaga tsatso d'aya muka fitoba.
Kururuwar danaji maman Safara'u ta kurma yasani kuma jan dogon tsaki, sai kuma najiyo muryar gwaggon haleema Na fad'in “kai amma wannan lamari baiyi dad'iba, kekuwa maman biyu ya kamata ki canja wannan halin naki, dan tabbas inba wani abu kikayiba babu yanda za'ayi yaronan Sadeequ yadage shi cikinsu *MUNAYA* yakeso, duka yaushe aka gama maganar nan akan shafi'u amma shine zaki koma kan Sadeequ kuma yanzu?”.
gaba nane ya fad'i, cikin zaro idanu waje nace, “ashema mu akanmu fitinar take yau?”. yink'urin sakko nake daga gadon Munubiya tashigo tana share kwalla, binta nayi da kallo harta fad'a saman gadon ta kwanta rufda ciki tareda fashewa da kuka mai ban tausayi. Hakan Yakuma tabbatar min lallai mud'inne dai ake hargowar akanmu. a fusace Na dirgo daga gadon na nufi k'ofar fita, (ko kad'an banida hak'uri, musamman akan cin zarafin mahaifiyarmu da akeyi agidan lokuta da dama idan irin hakan ta taso), taku biyu nayi naji an damk'oni, najiyo cikin masifa dan nasan Munubiya ce.
“wlhy ki sakeni kafin nafara huce haushina akanki munu! yau saina gyarama kowacce 'yar iskar mata zama agidannan dan kutu.....
Bankai ga k'arasawa ba Munubiya tai saurin rufe bakina da tafin hannunta.
Kici-kicin kwacewa nafarayi amma nakasa, dan bak'aramin ruk'o taminba, raina yak'ara 6aci ainun danjin irin rashin kunyar da Safara'u ke zubama innarmu a tsakar gida, bansan na wancakalar da Munubiya gefe ba nafice da gudu.
Babu Wanda yaga fitowata sai dai saukar sautin marin dana zubama Safara'u a farar fuskarta sukaji.
Hakan yaja gidan yay tsit na wucin gadi, sai kuma hayaniya takuma 6allewa, Safara'u da mamarsu sukayo kaina danufin duka....
Tsawar da baba k'arami ya bugace tasaka kowa dakatawa tsakanin ni dasu, hakama matan gidan sai suka fara jan k'afafu danufin barin wajen.
A tsawace yace, “kar wadda tabar wajen!!”.
Tsitt kakeji gidan yayi, tamkar bashi bane d'azun ya cakud'e da hayaniya tamkar ana biki ko suna.
Jarabar gidanmu ba bak'on Abu bane a anguwarmu, danta rigada tazama tamkar ajininmu take (yo ajininmu mana zance) tunda kullumne babu fashi sai anyi hayaniya, kodai matan gidan kokuma mu 'ya'yan gidan. Babu mai d'agama wani k'afa koda na second d'ayane kuwa, yanzun zakaji gidan shiru, anjima k'ad'an kaji an doka gangar shaid'an, musamman ma fad'an yara dayafi komai saurin had'a fad'an matan gidan da a kulum, a rana sai ayi fad'a biyar akan yara kawai, innarmu ce kawai da Maman Fauziyya keda k'ok'arin K'aucewa irin wannan fitintunun dasuka zama tamkar shan ruwa acikin gidanmu.
Baba k'arami yafara fad'a tamkar zai ari baki, inda yake shiga bata nan yake fitaba, kowa yayi tsit yana saurarensa, (saboda kasancewar masifaffe shima) sai da yayi mai isarsa sannan yajuya yafita yana fad'in nida Safara'u mu sameshi falonsa. harda iyayenmu mata.

Duk abinnan da akeyi innarmu na kicin tana had'a Karin kumallon safe, kuma kalma d'aya bata tofaba a zancen nasu, datasan ma zan fito bazata barniba nima.

A falon baba jafaru yanemi jin ba'asin tushen fitinar, cikin d'aga muryar da hargowa maman Safara'u tafara fad'in “Alhaji wlhy kashiga tsakanina da maman biyu a gidannan, idanfa tanama sauran matan gidannan Yanda taske so, suna barinta nibazan bartaba, tasanni tasan waye ubana ehe, kum.......
Hannu yay saurin d'aga mata, “kinga Suwaiba nifa ba wannan ne yasani kiranku ba, sonake naji minene ya kawo hayaniyar?”.
Cikin jin haushin an tareta tace, “Alhaji akan yaronnan Sadeequ ne, kowa yasan wajen Safara'u yake zuwa a unguwarnan, amma jiya da yamma sai ya aiko kiran Munaya, dayake ALLAH yatashi tonon asirinsu sabida bayaune na farko ba sai d'an Aiken ya kwatsa maganar a tsakar gida, babu dai Wanda yace komai, dan azatonmu ba Sadeeq d'in Safara'u baneba, goshin magriba saiga Safara'u tashigo tana kuka. Na tsareta da tambaya da k'yar tacemin cikinsu 'yan biyu tagani da Sadeeq a zauren gidan Malam halilu suna hira da dariya, kuma hardama mata gwalo akayi. Saboda na gaskata zancenta na sake aiken Rahma taganomin da idonta, harma taji Sadeeq d'in nafad'in ai koma miza'ayi bazai auri Safara'u ba, cikin wad'an nan munafukan yaran daba ganesu akeba zai aura, saboda darene yasani d'inne maganar a raina har safiyar yau d'inan, amma wlhy Alhaji da k'yar na iya barci nida Safara'u jiya.

“hummm” kawai nafad'a ina dafe kaina, saboda jin Yanda aka canja maganar.

Babak'arami ya kalleni yace, “Munubiya ce ko Munaya?” (dan basa ganemu saboda tsananin kamata da hassana ta).
Zuciyata cikeda bak'in ciki nace, “Baba Munaya ce”.
“yauwa Munaya, ina 'yar uwarki?”.
“Tana ciki baba”.
Baba ya kalli Safara'u daketa matse kwallan munafurci tun d'azun yace, “k! Safara'u tashi kiramin Munubiya ”.
Batareda ta amsaba tatashi tafita, mintuna kad'an saigata sun dawo tareda Munubiya datasha kuka idanu sukayi luhu-luhu. tsaki naja a raina ina hararta ta gefen ido, rashin jarumtar ta na bani haushi, ta cika hak'uri da sanyin hali tamkar innarmu.......
Maganar baba ce tadawo dani daga tunanin dana tafi. nad'ago ina kallonsa saboda kiran sunana dayayi, muryar a dake na amsa da “na'am baba”. kallonsa ya maida kan Safara'u yana fad'in “wacece acikinsu kika gani tareda Saddik'un?”.
Binmu da kallo Safara'u tayi, cikin matse kwalla tace, “baba niba ganesu nakeba, sai sun banbanta min Kansu sannan”.
Baice komaiba dan shima yasan da hakan, (ta hallaya ne kawai kowa ke banbantamu agidan, hatta da innarmu kuwa). Baba yabimu da kallo alamar son sanin wacece acikinmu.
Da sauri Munubiya tace, “baba nice”.
Nima na kar6e da fad'in “baba k'arya takeyi nice jiya Sadeeq ya aiko kira, kuma babu wata alak'a dake tsakaninmu, hasalima ya kirani ne akan Safara'un, sune dai suka maida zancen haka”.
Daga Safara'u har mamanta harara suka ballamin, babu ragi nima na rama kuwa.
Baba ne yakatsemu da fad'in “miya faru to Munaya?”.
Janye idona nayi daga Kansu na maida gareshi, kaina ak'asa Nace,
“baba ya kirani ne yana tambayata minene abinda Safara'u tafiso a rayuwarta, dan yanason yabata gift na birthday d'inta, kuma soyake yayi mata bazata. shinefa nake lissafa masa muna dariya saboda ina cewa ya had'o mata da gyad'a soyayya dan ita mayyarta ce, a dai-dai lokacinne kuma na hangota zata shigo gida, nifa dama tsokana namata gwalon, Ashe ita ta d'aukeshi wani Abu. Kuma wlhy Rahma k'arya takeyi, lokacin data fito tareda yaa Hameed ta ganni yana bani kayansa nakai masa ciki shi zai shiga masallaci salla. Wannan shinefa abinda yafaru, shine suke cewa nakwace mata Sadeeq, har ana cin zarafin innarmu da farar safiyar nan”.

Ajiyar zuciya innarmu ta sauke a hankali, taji dad'i daba abinda suke zargin baneba.
Wata uwar harara baba jafaru ya watsama maman Safara'u, “kai Suwaiba kedai ALLAH ya gyaraki, dan ALLAH kuringa bincike akan Abu idan yara sun fad'a muku, tokinji dai abinda yafaru, kekuma Safara'u dayake bakida tarbiyya har bakinki yana iyama Ai'sha rashin kunya ko, ki tabbatar saina saka Abdulhameed yacimin ubanku keda Rahama yau a gidannan. Ai'sha kiyi hak'uri dan ALLAH ”.
Innarmu ta yink'ura zata mik'e tana fad'in babu komai babansu, ALLAH ya kauda fitinar gaba”.
“Amin” muka fad'a muma muna mik'ewa mukabi innarmu a baya.

Koda muka fito, sai matan gidan suka zubo mana ido suna kallo tamkar yau suka fara ganinmu, a raina nace munafukai, haka zaku k'are.

Ran innarmu ya6aci matuk'a a wannan karon, amma kasancewarta mutum mai hak'uri da shanye damuwa sai...


Read / Download RAINA KAMA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album