Join Our WhatsApp Group

DAN MAJALISA Complete Hausa Novel Document by DAN MAJALISA


DAN MAJALISA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 86238



DAN MAJALISA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 24, Sep 2023

Author: Autar Manya ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : HOME OF QUALITIES WRITTER'S ASS

Author Phone : 08142105218

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 482.03 kb

File Type: txt

Views: 1057+

Download: 1147+

Last download: 3 days ago

Description/Story: 🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*Mallakar*
_AUTAR MANYA_🌹


~~~~~~~
📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER'S ASS*
~~~~~~~

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_


🅿️ *1*


Daƙarfin gaske ya bugi ƙaton table ɗin dake gabansa wanda yake shaqe da tarin takardu, sannan ya ɗago rinannun idanunshi waɗanda suka cika da zallan ɓacin rai marar misaltuwa ya zubasu akan p.a wanda yake gurfane agabansa cike da ɓarin jiki dana zuci.

"Me kake son kacemin _P.A_ kana nufin aikin da mukai ya lalace"!! yafaɗi maganar fuskarsa cike da tarin bakin ciki marar misaltuwa.

Wanda aka kira da p.a ne ya qara rissinar da kansa a qasa tare da kallon uban gidan nasu cikin rawar jiki.

"Wallahi tallahi nima ɗazu habu wakili yake sanar dani cewar aikin da mukai a Ɗawisu l.g ya lalace sannan kuma ansamu wasu ɓata garin samari sun haura cikin makarantar ƴammatah ta ɗawisun har sunyiwa guda uku fyaɗe" yakai maganar yana sadda kansa a qasa batare daya kalli uban gidan nashiba.

Rintse idanunshi yay harna wajan mintuna biyar kafin ya warasu yana bin _p.a_ dasu cike da tarin ɓacin rai ya ɗaga masa hannun alamun yabar masa office.

Cike da sassarfa _p.a_ ya miqe ya nufi hanyar barin office ɗin.

Tare da qara rissinawa yace. ALLAH ya taimaki _Megirma *MAS*!_ yakuma huci zuciyar ka mutumin qwarai fari mai farar zuciya sukari bakai farin banza ba yaro mai jini ajika wanda duniya take yayi ALLAH yacigaba da dafa maka adukkan lamuranka yasa maqiyanka suzama fadawanka!!

Yana kaiwa nan yaja masa qofar office ɗin ya fita sanin halin _mai girma *MAS* mutum marar son yawan kirari ko fadanci.


Da sauri ya koma da baya ya faɗa saman kujerar office ɗin nasa ya ɗaga kansa sama yana kallon rufin p.o.p office ɗin cike da bakin ciki yana ayyana yadda zewa ma'aikatan daya baiwa wannan contract ɗin rashin mutunci danshi mutum ne tsayayye sam baya son, son zuciya shiyasa baya zama da duk wani mutum marar amana.

Cike da qwarin gwiwa ya ɗauki wayarsa wadda take yashe a saman table ɗin yafara neman layi.....

Ringing biyu aka ɗaga daga can ɓangaren tare da cewa."ALLAH ya taimaki _Maigirma *MAS*........"

Bai tsaya jiran cigaba da maganar na cikin wayan tashiba yafara magana cike da ɓacin rai "Haba sardauna yaya zakuyi mana haka mu baku aiki amman kuyi mana almun dahana kasan dai halina kuma kasan waye ni natsani rashin gaskiya arayuwata wannan dalilin yasa waccan tafiyar ban baku aiki ko ɗaya ba" yakai maganar yana komawa ya lafe a saman kujerar daya ke kai.

Cike da bakin ciki wanda aka kira da sardauna ya mayar da abinda ya taso masa zuciyarsa tare da qaqalo murmushin qarya sannan ya soma bawa _Maigirma MAS_ hakuri tare da cewa shima bai san haka yaransa sukai aikinba amman gobe monday zeje yagani,


Batare daya tanka masa ba ya katse kiran cikin rashin jin dadi.

Kiran sakataren sa yay a waya ya sanar masa. ya cewa _p.a_ ya kai masa jaka mota ya tashi. Cikin muntuna biyar ya haɗa tarkacan sa yabar office ɗin ransa duk ajagule.

Dagudu gourd's ɗinshi suka rufa masa baya tare da saurin bude masa marufin wata shegiyar mota ya faɗa cikin gajiya yana gyara links ɗin hannun rigarsa.

Acikin mintunan da basu wuce goma ba motarsa tabi hanyar babban titin cikin garin ƊAWISU.


Gabaki ɗaya kowa yaga yadda manyan motocin bayan motar daya ke ciki, suke gudu yasan babu lafiya dan haka jama,a sukaita matsawa suna bawa motocin hanya waɗanda aqalla zasuyi guda goma.


Bai sanar da ƴan jarida ko wani cewar ze fita ba dagashi sesu habu p.a da sauran gourds ɗinshi haka suka nufi cikin garin ɗawisu.

Wanda zuwa lokaci kaɗan zancan zuwan bazatan da *ƊAN MAJALISA MAI GIRMA SANATA MUHAMMAD ANWARR SAMEER ( MAS )* yay cikin garin ɗawisu ya gama cika gari wanda yasa ma'aikatan sardauna constuructions suka shiga ɗimuwa

Abakin tafkeken qaton gate ɗin makarantar *ƊAWISU BORDING SCHOOL* ya dakatar da drivern sa da kansa ya buɗe marufin motar tare da ziro da santala santalan fararen qafafunshi waje.

Cikin azama duk wasu masu bashi tsaro sukayo caa! akansa tare da rufa masa baya wanda ya taka da qafafunshi har cikin makarantar.

Da gudu - gudu principal ɗin makarantar tayo wajansa wadda zancan zuwansa ya kaɗa mata ciki zubewa tai agabansa tana kwasar gaisuwa sannn ta miqe tai masa jagora har wajan aikin daya bayar na kwangilar sola.

Zagaye yay sosai acikin makarantar sannan ya koma can wajan office ɗin principal inda aka miko masa farar kujera ya zauna akanta.

Da rikitattun idanunsa waɗanda suke kama dana maijin bacci ya dubi. p.c yana jefa mata tambayoyinsa masu kama dana ɗan jarida akan yadda akai har garada suka hauro cikin makarantar batare da malamai ko ita sun luraba wanda alhakin kula da students ɗin akansu yake.

Gumine ya tsurgo mata sannan ta soma basa haquri akan wannan lamari tare da shaida masa qaddara ce babu yadda zasuyi.

Taune qasan laɓansa yay yana jin tsigar jikinsa tana miqewa babu abinda yafi tsana a duniya kamar zina babban abinda yake ɗaga masa hankali yaji anyiwa ƴammata ko yara fyaɗe wallahi jiyake inda zega waɗannan garadan da babu abinda ze hana ya kashe tsinannu.

Ɗago idonsa yay ya kalli p.c sannan ya nemi data turo masa dukkan wasu masu ɗankwali na cikin makarantar da kuma mamomin ɗakuna dan yana son sanin asalin yadda lamarin ya faru.

Cike da sauri p.c ta baxa sakonsa sannan ta koma ta tsugunna agabansa tana jimanta abun aranta.


Hostel!

Dagudu wata baqar budurwa mai ɗan tsaho ta, taho wajan wata farar yarinya mai ɗan tsaho kaɗan marar jiki wadda take ɗaure da ɗaurin kirji ajikinta tana wanke hause ware masu kalar blue.

Cikin haki ta karaso gabanta.
Ɗaka mata duka tai tare da cewa.
"F.K kizo kece shugabar makaranta wallahi *ƊAN MAJALISARMU* yazo akan zancan haurowar da yaya gardi yayi kuma ya nemi da akira duk wasu masu ɗan kwalin cikin makarantar nan yanxu haka p.c tana can tana nemanki ashe kekina nan kina wanki.

Wadda aka kira da f.k ita ta ɗago da sauri tana kallon wadda take mata maganar cike da sanyin hali "kai lebour ni wallahi harkin bani tsoro wallahi canake wani gardin ne ai wannan murya haka"

Dariya lebour tai sannan ta kalli F.K malama nasanki da sanyin jiki sefa kinyi da gaske sabida kiran gaggawane dan ALLAH kada ki tsaya wannan yangar taki.

Tsaki F.K tai sannan ta tsame hannunta ta wanke ta nufi hanyar ɗakinsu.

Kwanarsu taje ta dauki qaton hijabi har qasa sannan ta dubi walida wadda suke kwana ɗaya da ita cikin nutsuwa "walida zanje kiran p.c dan ALLAH ki tsaman idomie ta kada ta jiqe takai maganar a nutse" wadda ke zaune daga gefe tana karatu ta ɗago ido ta kalli f.k.

"Waidaman feenah baki ci abincin nan ba tun ɗazu nifa narasa kanki tunda muka dawo daga wannan hutun naga kin sauya sanyin jikinki ya qaru kodai su baffa ne suka kuma...." kallon walidan tai cikin basarwa "nidai idan naxo mayi magana dan ALLAH ki tsaman" takai maganar tana futa daga cikin kwanar tasu.

Hanyar area class tai cikin sanyin jiki wai ahakama tana sauri.

Adai dai bakin office ɗin p.c taji sautin bugun zuciyarta yana qaruwa fiye da nada wanda qaddara tasa ta gamu dashi batare data shirya ba.

Addu,a tacigaba dayi hartaja qafafunta zuwa bakin office ɗin.

Seda ta kutsa kanta sabida yawan jama,a ga security's kota ina ga malamansu haka ta samu ta qarasa wajan da aka ce musu su taru ta tsugunna tana saukar da kanta a qasa.

Yawan bugun zuciyarta da rawar jikinta dasuka tsananta sune suka saka babu shiri ta haɗe jikinta waje ɗaya tana tsukewa kamar maijin shigar sanyi.

Kafin taji wani daddaɗan mayen kamshin turare ya cika mata hancinta wanda take tunanin ina ta sanshi?

Ɗago kanta sama tai wanda adai dai wannan lokacin shima yake neman waje akan kujerar da aka ware masa dan ya zauna.

Cike da tsoro ta ware idanunta duka waje meya kawosa nan?".......



*ƊAN MAJALISA*

_Na kuɗine akan farashin naira 200 ta asusun wannan banki 0078174806 starling bank shedar biyan kuɗinki ta nan 08142105218 masu buqata ana baku ta p.c base kun shiga group ba kuma zaku biya 1k ta wannan asusun na sama kuturo sheda ta number sama_



_Idan kina buqatar littattafaina na kuɗi dana kammala complt *KOBA SO* Dakuma *H A S K E* Zaki turo naira 500 ta asusun bankin 0078174806 starling bank shedar biyanki ta 08142105218 inda zan baki complt ɗinsu da yardar ALLAH_
🌹 *ƊAN MAJALISA* 🌹
( Love story )



*Mallakar*
_AUTAR MANYA_🌹


~~~~~~~
📚 *HOME OF QUALITIES WRITTER'S ASS*
~~~~~~~

_Dasunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Ƙai_


🅿️ *2*


Lumshe manyan idanunta tayi tare da sake warasu akansa tana jin wata iriyar nutsuwa ta shigeta kafin taji sautin bugun zuciyarta yafi nada qaruwa sosai ta shagala da kallonsa wanda takejin kamar ta dawwama a haka tana kallonsa batare data gajiyaba.
Cikin zuciyarta kuma matsanancin mamakine fall tayaya yazo cikin makarantarsu? ita data gansa a ƊAWISU GENERAL HOSPITAL har takai masa files ɗin kaka, anya kuwa shine kodai aljanine tayaya yazo a ƊAN MAJALISAR SU? Kuma ta gansa a matsayin likita wannan lamari ya cuɗa mata kanta ya hanata sukuni tabbas tana da tarin tambayoyi aranta amman babu mai bata amsarsu dan haka ta kuma jan jikinta ta tsuke tana ayyana koma dai waye shi ita taji ta gani!!
Ta cikin wutsiyar idanunta take kallon yadda yake motsa ɗan madai daicin bakinsa yanawa ɗaya daga cikin masu tsaronsa magana wadda ba lallai na nesa dashi yaji miyake cewaba.
Mintuna kusan goma suna tsugunne kafin taga p.c ta miqe tsaye tanawa baba vise magana wanda kafin hankalinta ya dawo kanta taji yana kiran sunanta.
"Nafeesa Kabeer" taji baba vise ya kira sunanta yana kuma umartarta data matso gaba ana son ganinta.
Cikin rawar jiki f.k ta miqe daman can ita bamai yawan magana bace ba sannan kuma batada sakewa acikin mutane tun fill azal balle yanzu dataga taron maza damasu ɗammara wannan dalili yasa tafara karanto addu,oi cikin bakinta harta samu ta qarasa gaban p.c ta sake tsugunnawa.

P.c ce ta umarceta akan ta matsa gabansa wanda faɗin hakan da p.c tai yakusan sakata ta ɗimauce bada ban qarfin addu,aba da tabbas seta faɗi a wajan.
Cike da sanyin jiki dana zuciya ta qarasa gabansa wanda yake zaune akan kujera ya ɗora qafa ɗaya kan ɗaya gefensa masu tsaronsa ne duk sun riqe bindigogi se wasu mutane daban dake bayansa suma a tsaye.

Agabansa ta tsugunna tare da mayar da kanta a qasa tana zana qasar gabanta da yatsun hannunta tana jin wani sanyi yana ratsata ga wata iriyar faɗuwar gaba data qaru acikin kirjinta.
Wata qwalla ta matso mai zafi tare da saka gefen hijabinta ta share a fakaice tana kallonsa yadda yay kamar bai san da ɗan adam a wajanba seda taga wani mutum ya risina yay masa raɗa a kunnensa sannan ya ɗago ya jefeta da wani shu'umin kallo mai kama dana raini da qasqanci.

"Ke"! yafaɗa muryarsa a daqile kamar wani basarake cike da saurin jiki p.c ta daka mata tsawa "ke nafisa ba magana ake maki ba" cikin sanyinta ta ɗago idanunta waɗanda suka soma yin jaa! sabida damuwar data taso mata ta diresu akansa tana kallonsa batare data tanka masa ba kuma batare data ɗauke idanunta daga kan nasa ba.

Cike da mamaki _mai girma MAS_ Yake kallon yarinyar gaban nasa wanda take yaji wani ɓacin rai ya ziyarcesa jiyana mata magana ta mayar dashi kamar wani wawa tsaki yaja kaɗan tare da lumshe idanunsa waɗanda yake jifanta da kallonsa na rainin hankali dasu kafin ya furzar da iska mai zafin gaske ganin tana son ta ɓata masa lokaci.
"Ke wace irin wawiya ce ana maki magana kinyiwa mutane banza hala bebiyace"! ya faɗi maganar muryarsa adake!!
F.k wadda ta shagala a kallonsa lumshe idanunta tai cikin muryarta mai dadin sauraro mai kama data mai jin sanyi ta fara magana "ALLAH ya baka haquri banji kaba" tana faɗin maganar taja bakinta tai gum jikinta duk ya dauki rawa sakama kon wani wawan kallon wulaqanci daya mako mata.

Ɗan tsaki kaɗan yaja cike da halin ko in kula yafara yi mata bayani akan yadda zasuna kula da ɗakunansu suna tsare kansu batare da sun jira malamai sunzo ba a yayin da garada suka hauro masu.
Cikin tattausan lafazi yake mata bayanin wanda idan ka kallesu seka rantse wata magana suke ta soyayya.
Abinda yafi bata mamaki yadda taga duk magana ɗaya seya lumshe idanunsa sannan yake faɗinta dalla dalla kuma yake mata maganar yadda zata fahimta sedai kuma ta lura kamar yanada ɗan saurin magana kaɗan.
Har yay yagama bayanin nasa bata fuskanci komaiba illa wata karin damuwar daya kuma jefata aciki tare da shiga ruɗun rashin makama akansa haka ta miqe jiki na rawa tai masa godiya tabar wajan.
Kafin ta qarasa wajan da aka tsaidasu taji maganganu sun karade wajan akan yay masu kyautar maqudan kuɗi.
Sallamarsu akai akan su tafi se an nemusu, inda shikuma ya miqe aka rufa masa baya ya nufi wajan ganin aikin daya zuba ai acikin makarantar.

HOSTEL

Tana tafe tana haɗe hanya kamar wata zararriya haka ta qarasa cikin ɗakinsu akwanar su ta yada zango tare da tube hijabin jikinta, da gudu walida tazo ta rungumeta "wayyo shugabar makaranta naji abin alkairi _mai girma MAS_ yabamu kyautar kuɗi masu yawa sannan yasa a dauke waɗanda akaiwa fyaɗe a fitar dasu waje aga lafiyansu mudai ALLAH yasa a rarrabamana kuɗinnan kinsan halin malaman nan kowa kansa yake gyarawa"
Ganin kamar f.k bata hayyacinta yasa walida taɓata "F.k lafiyanki kuwa?" ɗago kanta tai ta kalli walida da idanunta waɗanda sukai jawur! sannan ta mayar...


Read / Download DAN MAJALISA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album