Join Our WhatsApp Group

HEEDAYA Complete Hausa Novel Document by HEEDAYA


HEEDAYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 78899



HEEDAYA

Reading Time: 6 Hours

Added On: 18, Oct 2023

Author: Husba'ahfama ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 496.53 kb

File Type: txt

Views: 836+

Download: 548+

Last download: 6 days ago

Description/Story: 馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃拕馃拝 *HEEDAYA* 馃拝馃拕
( I Kirari)
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼



Writing by *husba'ahfama*


*IG officiall_ husba'ahfama*
Facebook *Real husba'ahfama*


Bismillahir Rahamanir Rahim



Barka da salla masoyana *am back with another new novel* da fatan ze samu karbuwa kamar yanda wayan can suka amsu ameen




1-2

wani ran tsatsen mota ne ya faka a wani kofar gida dake bakin hanya sai da suka jima sannan wata budurwa ta bude mota ta fito

Farace tas mai madai daicin tsawo Mai masa kaicin jiki hidaya kenan batafi shekara 20 ba

"Nagode Rabi'u sai mun hadu gobe a school

Fitowa Rabi'u yayi

"Bakomai hidaya yiwa kaine kishirya da wuri zanzo mu tafi tare

"Ok to sai kazo

Rabi'u y shiga mota ya tafi tana daga mishi hannu harya bace hidaya ta nufi hanyar gida gaban wani dake zaune akan tabarma da radio a gefen sa taje ta sunkuya har kasa

" Assalamu'alaikum Abba inawuni

malam Nazifi kenan mahaifin hidaya

Kallo ya mata me cike da tuhuma dan sa rai yaga wanda ya kawo ta gida lpy klau yace tare da dauke kansa daga ganin ta

A sabule ta tashi ta shiga gida

"Assalama'alaikum

"Wa'alaikumus salam hidaya andawo

"eh mami inawuni

"Lpy kalau y karatu

"Alhamdulillah momi gobe zamu fara jara bawa

"Dafatan dai kina karatu sosai duk da nasan dai kedin ba bayaba wajan karutu kuma kina fitowa da saka mako mai kyau

Murmushi tayi "hakane mami ina nan yanda nake ban canza ba

Guda suka jiyo daga daya dakin dake fuskantar su "awai ayi mu gani idan tusa zata hura wuta karima kinji wai jara bawa kuma harda saka mako me kyau

umma rabi dasu karyar banzane kawai bawani karatu da jara bawa muna nan dake zakiji Kuma kiga karatun da takeyi

"Allah karima

"Wlh umma mun fasan komai shiru kawai nakeyi itace wancan gida wancan hotel taka meme bata da

Matsuguni kowana jaki kare binta yake mudai ayi a hankali kar a ciyo leda a kawo Mana gida ehhhe

"Allah ya nuna mana wannan Rana zamusha kallo kinko kula da yanda take ta dashewa tana danyan cewa

mami ta maida kallon ta ga hidaya hidaya ma kallon kanta takeyi

"hmm umma kinsan me ina matukar son karin maganar malan ba haushe wanda beji bari ba yaji hohu nidai nasan ba

makarantar da take zuwa kudin makarantar idan an bata hotel take kamawa waye be sani ba

karima ta fada tana hararar hidaya

hidaya ta yunkura zatayi magana mami ta riketa ta girgiza mata kai alamar karta kula

su hidaya da Shiga daki rai a bace mami tabiyo bayan ta hidaya tayi jifa da mayafi da jakar dake hannun ta

Karima da uwarta kofar dakinsu hidaya sukazo suka labe suna jin abinda zasu ce

"Hidaya kiyi hakuri mana sunyine dansu kunna ki nidai ina rokonki kome zasu miki karki kula su

kizama me hakuri shikuma me hakuri shike dafa dutse haryasha romon sa ninasan tarbiyar dana miki bazaki

taba aikata abinda suke dangan taki da shiba Allah ya kara sarkake miki zuciyarki ya haneki da saba masa Allah ya miki Albarka Ameen

"Ameen hidaya tace

umma tace bawani kinsan gaskiya kina dai rufe wane dan yarkice kar sunanta ya baci

Bace na nawa kuma ai ya gama baci har sunan gidan muma ya baci waye besan abinda take yiba Allah ya mana tsari da ita kawai

kinga karima zomu shiga daki dan tsayu warmu anan ma wani abune karsu goga mana bakin hali da aka gada a gurin uwa da uba

Hakane kuma umma suna tafe suna kananan magan ganu harsuka karasa

hidaya da mami najinsu har suka tafi

"Kisaki fuskar ki ki cigaba da walwala kamar yanda kika saba jekiyi wanka bari na kawo miki abinci kici kiyi dariya mana hidaya

hidayi tayi murmushi

"yauwa koke fa jekiyi wanka ina zuwa

toh tace tashiga ban daki tayi wanka ta fito ta shirya tazo inda mami ta ajiye mata abinci ta zauna tabude Tana ci harta gama mami na mata nasiha tafito ajiye kwano taji ana kiran sunan ta juyawa tayi dan ganin waye

murmusawa tayi "yaya mansir sannu da zuwa

yauwa hidaya y karatu

ajiye kwanon tayi ta anshi ledar hannun shi

"Alhamdulillah yaya y aiki

"Aiki sai godiya gobe zaku fara jara bawa ko

eh yaya amma ya akai Kasani koda yake ba abin mamaki bane hala kun hadu da junaidu ko

eh hargurin aiki na yazo y fada min

Karima ta fito taimausu kallo banza ta zubar ta taho da sauri hartana bige hidaya ledar hannunta ta fisge

Tinda ba na yayanki bane muna fika Allah ya fiku daga ke har uwarki shima manla kemana shi zakiyi

mansir y daka mata tsawa karima bakida hankali idan da kara mahaifiyarta ai takice

A hankali karima tace uwa uwa tace tata tatace

Bakinta mansir ya gani yana Mitsubishi "mekikace

Bance komai ba kinji dadi kinshiga tsaka nina da yayana ba abin mamaki bani idan muna fiki ya rikaka shiga dakin uwarka ko ruwa bazaka shaba taja tsaki ta tanufi hanyar dakin su

Karima bani ledar nan ke kika aike ni ko nace Nakune ba ta mika mishi tana gunguni daki ta

shiga da sauri ta taso umma data fara bacci umma umma tashi tanayi tana kallon kofa

Cikin muryar magagi tace karima mekuma ya faru

yaya mansir ya dawo da ledoji2 shake da kaya na ansa zan shigo dashi ya zageni ya anshi ledar zebawa waccan makirar hidaya

Da Raina da lpy ta haka zefaru matsa kiga da sauri ta fita tana cewa menake gani haka mansir ina daya ledar take Ke Tsaya inda kike idan kika bari na karaso saina karya kafafun nan naki hidaya hartasa kafarta a daki sai ta ciro waje

"Kawo min ledar

Mansir yace hidaya shiga daki

"nace ki bani

hidaya ta shiga daki ta turo kofa

nanfa ta fara salati ta dora hannu akai tana kuka "mansir kaida kanka kabawa yarcikina dama ta raina ni duniya ta lalace mansir da kanka

Umma mushiga daki makiya na farin ciki bakiji sunyi shiru suna jin abinda ke faruwa ba kiyi hakuri mu shiga daki

daki suka shiga suka tafa


Umma kinga yanda jikin yaya mansir yayi sanyi kuwa

"nagani ina sane nayi haka gobe baze sake ba meya kawo ne karima duba mana

umma kayan marmarine a ciki sai kaza gashaishe

"Shine ya takai Cemu yabawa wayan can daya ledar

"su insha Allah a wuya ze tsaye musu umma ki kwantar da hankalin ki

Ameen y Allah

Suka baje kayan suna ci saida mansir yayi wanka ya canza kaya sannan y shigo sallama yayi umma da karima suka ammasa

Yasamu guri ya tsugunna "umma inawu

Daban wuniba Zaka ganni kamarni mansir Zaka Bari makiya su shiga tsaka ninmu

Umma kiyi hakuri yawuce haka baze sake faruwa ba

Eh umma kiyi hakuri baze sake ba

shikenan ya wuce Y kasuwa


Alhamdulillah ya zauna sukayi yar hira sannan y fito yaje masallaci a tare suka dawo gida da malam Nazifi mahaifinsu

******

*gidan malam nazifi* nada mata 2 Hafsat da hauwa'u malam nazifi nada rufin asiri dai-dai gwargwado ba

abinda babu a gidan shi karamin gidane me dakuma 5 dakunan na kallon juna 2 ciki da falo ne inda huwa'u uwar

gida keda 1 Hafsat keda 1 1 kuma hidaya da karima ne suke kwana sai dai karima ta kwashe kayanta ta koma

dakin umma da kwana dakin yanzu ya zama na hidaya 1 kuma na malam nazifi NE daya daki yana daga waje

babbane sosai mazane suke kwana a ciki Hafsat mami suke ce Mata tanada yara 3 maza 2 usman NE babba

yana abuja yana aiki Ali na s1 Mace 1 hajara ana ce mata hidaya tana Jami'a level 200 Tana karan ta nursing


hauwa'u umma suke ce Mata uwar gida itace matar malam nazifi ta farko tanada yara 5 2 maza mansir ne

babba sai Adam na ss2 mata 3 hadiza Asma'u sunyi aure karima taki karatu kotaje gudowa take yi mansir da kanshi

yake Mai data data gane saita dena dawo wa gida ta koma zuwa gurin kawarta lubabatu
Wananan kenan

Washe gari hidaya ta shirya tsaf zata tafi makaranta tafito zata tafi karima ta tsai da ita

"ke hidaya tsaya kijirani na shirya mu tafi tare

"Eh banjiba

"bana maimaita magana abinda kunan ki ya jiye miki daidai ne

hedaya ta bushe da dariya ran karima ya baci

"Dahalla malama meye abin dariya anan da kike dariya ko kinga nayi kama dame bada lbrin barkwanci

"Ba daya bare dangin biyu kekanki kinsan me nake yiwa dariya yaushe rabonki da makaranta rana tsaka kice zaki koma anbarki a baya fa

umma ta fito Harar hidaya toyar iyayi kinfita sanine koko kinfita damuwa da karatun kanwa uwar gami harda

wani daga murya kin dauka mahaifinku nanan yaji ya yi mata fada kike so kome toh ya fita shikenan wannan
beyiba ki sake wani


nidai kinga tafiyata idan kin shirya kitaho dama ba tare muke zuwa ba Allah Kadai yasa dalilin ki nacewa na jiraki


Bata jira taji abinda zasu ce ba tayi tafiyar ta

Ah Lallai yarin ya ba karya baki dauka a kasaba ta tsotsa a nono damu kike ma gana gaba daya yarin ya ta iya ko ince takoyi bakin hali irin na uwarta Allah dai ya kyauta













New writer's



Hakan Take
*husba'ahfama*馃槏鉂ゐ煠�

*'Yar kwalliya* 鉂ゐ煉�


馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃拕馃拝 *HEEDAYA* 馃拝馃拕
*(I KIRARI)*
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼




Writing by *husba'ahfama*





*IG Officiall_husba'ahfama*
facebook *Real husba'ahfama*







3-4


Umma ta kama hannun karima suka shiga daki

"karima dake meyasa kika ce ta jiraki gashi a banza Tana gaya miki magana

"ki bari kawai umma harzuciyata ina jin haushin hidaya niya nayi idan ta zauna jirana sai na shigo nai kwanciyata nai bacci ita kuma ta rasa jarabawa

Dariya umma tayi "yaro Man kaza inbanda ke da abinki kema kinsan wannan bazeyi aiki ba kibarni da hidaya Ninasan tuggun da nake shirya mata kodan ban fada miki bane

"umma fada min dan Allah me kike shirya wa

"dadai bazan fada miki ba amma kawo kunnanki ki

nanfa umma ta shiga gayawa karima akunne nidai banji komai ba nasan dai komeye ze fashe a gaba

tana gama fada mata karima tayi salle tarungume umma sai gasu a kasa

"Karima karyani zaki

"Umma ina cikin farin ciki Allah ya kara miki tsawan rai indan na karyaki ina zansa kaina

"ni madai abinda na gani kenan dan haka karima kizuba ido ki gani

"toh umma ina nan ina jira bari nayi sauri na je gidan hajiya naja'atu na anso miki sakon

"Yauwa kiyi sauri kije Allah yasa ki samu yaran ta nanan basu fita ba kinsan meyasa nakeso ki zuba

sammako inaso a cikin yaran ta maza su ganki wani ya yaba ayi dashi kinga munhuta daga ke harni yaushe zamu

zauna anan kullum suna kan fita kuma ta jirgi suke zuwa inda zasu kinsani

karima tayi murmushi "hakon mu ya kusa cimma ruwa dan naga danta na 2 najib na kallona

"Kingani maza jeki caba ado kizo ki tafi

"toh umma

Karima ta caba ado ta fito sai kanshin tirare take yi

"umma ya kika gani

"kinfito fes dake karima jeki sekin dawo Allah ya bada sa'a

Ameen tace dan sahu ta hau ya kaita har gidan hajiya naja'atu tabashi kudinshi tanufi gidan megadin yasan ta yana ganin itace ya bude mata ta shiga

babban gidane da yasha ado tin daga waje har ciki filawoyi zagaye a gidan kai tsaye tanufi cikin gidan

Ashe kallo be kare ba cikin gidan ba a magana kujerune kosassu gidan sai kanshin tirare yakeyi labilen

kujerun da komai dake wajan Kalar pink ma aikata Nata Kai kawo a kujera karima ta zauna sai gyara mayafin

jikinta takeyi hajiya naja'atu tafito tana takama ta zauna karima ta zube kasa

"hajiya barka da fitowa Antashi lpy

Saida ta jima sannan tace lpy

"umma tace nazo zaki bani sako nakai mata

bata amsaba tace habiba

Na'am hajiya da gudu habiba ta fito Tana niyar faduwa ta zube a gaban hajiya naja'atu

"gani hajiya

"kawo min kayan nan dana ware

Karima sai murmushi takeyi tana wasa da maya Finta kanta a kasa hajiya naja'atu sai kallon wula kanci

take mata tana yatsine fuska kamar taga kashi habiba bata dade ba tafito hannunta biyu rike da jaka dakyar take janyo su

"hajiya gasu nan


Saki taja wanda ya razana karima da habiba jikin habiba ya kama rawa

"kewai yaushe zakiyi hankali habiba kullum karatu daya zan dinga biya miki a gidan nan idan

bazakiya aiki a gidan nan ba ki fada min ina da kudin da Zan dauko wasu duk yawansu kema kin sani kullum ina

fada miki idan nace ki dauko abu ki kawo min idan kin ganni da wani shi zaki ba inda ni zanyi amfani dashi

bazance kikawo min yanzuba datin dazu Zan ce kikawo min katazo ki kula dan nagaji aikinki na rawa a gidan nan na fada miki

Habiba zata haifi hajiya naja'atu amma bata duba haka idan zata cimata mutun ci

hajiya kiyi hakuri bazan sake ba zankiya ye nan gaba

"kallon banza ta mata ta watsar

Ganin yanda take jan jakan dakyar yasa karima ta taso zata tayata

hajiya naja'atu ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu cikin jan aji "karki tayata aikin tane inko kika tayata saina cire a cikin kudinta

Karima ta zuba mata ido cike da birgewa "kina birgeni Allah kasa na shigo dau lar nan a dama dani ajiya abinda kikeyi akadan ne akan wanda zanyi karima ta fada a zuciyar ta

Har habiba ta ajiye kayan a gabanta bata sani ba


Hajiyace ta kira sunan ta da karfi karima kallon nan na meye

"Babu komai hajiya kawai kina birge ninne

hajiya tayi murmushi me kama da yake "gashi nan ki kai mata ga wannan ki bata kudi ta ciro ta mika mata

"hajiya angode Allah yasaka da Alkhairi

"Nizan koma

Batace mata komai ba sai bimta da kallo da tayi tana kici niyar daukar jakar taji fitowar mutane da alama

yaran hajiya ne dasauri ta Saki jakar tafara gyara jikin ta da murmushi a fuskanta tabi inda sautin tafiyar

kezuwa da kallo gaba dayan sune suka fito maza 3 basiru ne babba sai najib sai Amjad mace daya yasmeen

Mommy barka da hutawa

"yauwa harkun fito

Yasmeen tace eh

hajiya naja'atu ta maida hanka linta ga kareema dake tsaye ta zuba musu ido su basu sanma tanayiba

Kareema hajiya ta fada da karfi batafiya zakiyi ba me kike jira

"eh jakar da nauyi na...


Read / Download HEEDAYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album