Join Our WhatsApp Group

ABU MALEEK Complete Hausa Novel Document by ABU MALEEK


ABU  MALEEK

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 173587



ABU MALEEK

Reading Time: 14 Hours

Added On: 18, Oct 2023

Author: NimcyLuv Sarauta ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +2348119237616

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 935.24 kb

File Type: txt

Views: 1026+

Download: 1902+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: 🌈🌈🌈🌈
*ABU_MALEEK*
🌈🌈🌈🌈
*NA*
NA'IMA SULAIMAN SARAUTA
Nimcyluv

20/11/2021
21/7/1443AH



*DEDICATED TO* ALL _ONLINE WTITERS, AL'KAIRIN ALLAH YA KAI MU, ALLAH YAY MAKU LIƊIFI DA KUMA JAGORA UBANGIJI YA KYAUTATA ƘARSHENKU YA YI RIƘO DA HANNAYENKU_


BOOK 1
PAGE 1-2


Edo/ Benin City state

Iska mai daɗi ce take Kaɗawa a garin, yayinda da samaniya tai wani kalar gwanin sha'awa, duk da cewa dare ne,Amma hakan bai hana ƙwantaccen hadarin dake ƙasan gajimare baiyana ba.
Yayinda gajimaran ke haske yana bada wani ƙara mai nuni da cewa hadarin gab yake da tashi.
Musamman yadda garin yay jajir baka jin sautin komai sai na tsuntsaye da kuma sassanyar iskar dake Kaɗawa a garin.
Yadda hadarin ke ƙara haɗi da wani bada kalar sauti mai rugugi yana ƙara shaidawa mutanan garin cewa Tabbas ruwan gab yake da sauka, sbd yadda gajimaran yake ta gudu yana haɗa kansa hakan ya data hankalin tsuntsayen dake saman bishiyoy da Flowers damar tashi domin samun mafaka.
Yayinda da a gefe guda ƙaramin Yaron wanda bai zai gaza shekara 15 yake tafe cikin sassarfa sbd samun damar shigewa makwancinsa,
Gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake sbd ruwan da yake jin ya fara sauka, sosai Allah ya ɗarsa masa tsoran saukar ruwan sama.
Fararan kayan baccin sa dake manne a farar fatar jikinsa suka ƙara mannewa.
Kasancewar su masu tsantsi da kuma sulɓi.
Tsayawa yay cak sbd sautin tafiyar da yaji a bayansa, gaba ɗaya a tsorace yeke, domin wannan shine karansa na farko daya fito cikin dare.
Juyawa yay yaci gaba da tafiya har ya samu damar cimma shashin nasa yana gab da buɗe ƙofa.
Aka sakar masa wani doka a tsakiyar kansa.
Ƙara ya saki yana mai dafe da kansa nan da nan kuma jini ya fara gudana ta ƙasan kansa ya shiga sauka saman wuyansa zuwa kafaɗarsa,
yayinda idanunsa suke lumshewa, sabida tsananin azaba haɗi da zugi wanda yake ƙara hargitsa masa dukkan tunaninsa, Tabbas da gaske dokan ya shigesa har baya iya gane inda yake.
Maimakon ya shige part ɗin nasa sai kawai ya juya ya nufi wani sashin.
Gefe guda kuma, wani ƙyakƙyawan Yaro ne Shima wanda bazai wuce 15yrs ɗin ba.
Ƙyakƙyawa ne ajin farko, ɗan leƙawa yay yaga da gaske babu kowa duk da cewa bashi da tsoro amma shi ɗin Mutum ne mai son kare martabar sa, ga isa da kuma ikon gaske baya shayin kowa..
Da sauri yabar wajan sabida foot sounds da yaji.
Yana mai dafe da kansa dake ɗan zubar da jini ya ƙarasa inda take tsaye,
Ganinta a wajan ne kuma yasa gaba ɗaya ya nufi inda take gadan-gadan, ihu tasa amma duk da hakan bai hana shi rapping ɗin ta ba, sabida shi ɗin stubborn ne very stubborn bai ji sam, duk da cewa yana da tsoro.
Ganin abinda ya aikata
ne kuma yasa cikin sauri ya tashi yana mai naɗe wandonsa yabar wajan yana sakin tattausan Murmushi.

*SAHEL*
Wani yanki da cikin garin Sahel, San sanin Fulani ne wanda ya daɗe da kafuwa duk da kasancewar duk Fulanin wajan Makiyaya ne,
Masu tashi su sauya sheƙa a duk sanda suka so,
Gaba ɗaya cikin rugar bukkoki ne da ko wanne waje ga tarin garken shanu da ragona haɗi da raƙoma,
Amma gaba ɗaya shanun wajan sunfi ko wacce dabba yawa a cikin garken,
Dare ne mai cike da tsoro haɗi da tsantsar fargaba, gaba ɗaya Fulanin rugar sun hana idaniyar su bacci sabida tunanin abinda zai je ya dawo,
Gaba ɗaya basu da wata kwanciyar hankali kullum suna rayuwa cikin tsoro da tarin fargaba gaba ɗaya an hanasu kwanciyar hankali da farin ciki,
Basu da wata walwala ko kaɗan,
Misalin ƙarfe 2:30 ma daran yanar juma'ar kamar a mafarki Fulanin cikin rugar suka fara jiyo saukar bindiga da ƙarar fashewar abu kamar bom,
Cikin sauri ko wanne magidanci da kuma samarin rugar suka fara fitowa ɗauke da makamai yawanci kuma bawai makaman arziƙi bane,
Duk da yawanci jama'ar Duniya bawai gari ba sunawa Fulani kallan mugwayen mutane marasa tsoran ALLAH,
Amma a zahiri kuma ba haka bane, Fulani sam basu ƙaunar tashin hankali sabida sam basu sama da shi ba,
Kasancewar gaba ɗaya rayuwar daji suke rayuwa mara ƴanci,
Sosai hankalin Fulanin rugar ya tashi sabida kafin su yi wani tunani,
Tuni mugwayen mutanan sun ƙaraso cikin rugar suna harbin dukkan wanda suka yi katari da shi,
A can gefe guda kuma Wani magidanci ne ya fito daga cikin bukkar sa yana riƙe da hannun matarsa,
Wacce take dafe da cikinta wanda ya cika wata 9 a duniya,
Cikin sauri yake mata magana suna tsaka da tafiya taji mijin nata ya saki ihu,
Da sauri ta juya taga ashe harbinsa akai baki ta buɗe zatai ihu,
Yay saurin sanya tafin hannunsa ya toshe mata baki dashi,
Cikin fitar rai ya cire wani (GURI) nasa ya damƙawa matar tasa,
Yana shirin yin mgn sai Numfashin sa ya ɗauke alamar dai rai yay halinsa,
Cikin sauri ta miƙe Idanunta na zubar da waye, a ranta take addu'ar tsira da abinda yake cikinta,
A haka ta kawo gaɓar wani kogi,
Sabida tashin hankali da yay mata yawa yasa naƙuda ta kamata, nan kuma take ta samu nasarar haifar farar jaririyar ta,
Wacce dunda tazo dubiya ta cilla yatsarta a baki, alamar haƙuri ya bayyana a tare da jaririyar, wacce aka haifa cikin tashin hankali,
Kuka ta fara hakan ya jawo hankalin mutanan da suke ta kaɗa shanun rugar suna gaba dasu cike da mugunta da kuma son zuciya,
Zanin Jikinta ta cire ta naɗe jaririyar da shi,
Kamar daga sama taji wani yace.
"Kawo ta nan"
Bata tsaya jiran abinda zaice ba tai saurin sauyawa yarinyar (GURI) wanda mijinta ya bata,
Da sauri kuma ta faki idanun mutanan wanda suke rufe da fuskokin su, kana tai azabar cillah jaririyar cijin ƙaton kogin dake gudana wanda babu wanda yasan inda ya tsaya,
Tana cillah Yarinyar suna sakar mata harbi.

(MAFARIN buɗewar ƙaddarar kenan)

*BAYAN SHEKARU ASHIRIN*

ALAAFIN OF EDO/BENIN *(MASARAUTAR KANZAF)*

Babbar Masarauta tace ta Yarabawa, Masarautar ta samu a sali tun iyaye da kuma kakanni,
Kowa yasan Yarabawa da riƙe Al'ada, basu wasa da dukkan abinda zai shafi kima da kuma matarta barsu,
Tun a ginin masarautar zaka tabbatar da ƙarfin iko na masarautar,
An ƙawata Masarautar da ginin jar ƙasa,
Mai ratsin fari da kuma Maroon,
A Ƙofar farko akwai Fadawa masu tsaron ƙofa sama da mutum Ashirin,
Babban cikinsu shi ne OBA LEKUN (SARKIN ƘOFA).
harabar wajan kuma sauran Fadawa ne cikin yadin uniform ɗin su,
Daga wannan babbar ƙofa,
Sai wata ƙofa wacce aka gina ta ɗan yar Azurfa, banda sheƙi babu abinda take, ga kuma tambarin masarautar (Alaafin means Masarauta) a jikin ƙofa,
Nan ma Fadawa ne da kuma tarin barori da kuyangi kowa yana aikin gabansa,
Sosai masarautaru take da tsari mai kyau gwanin sha'awa ga baƙon da mai taɓa saninta ba.

Da sauri bisa sassarfa yake taka ƙafafuwansa a ƙasa, kansa a sunkuyar duk inda ya ratsa mutane zubewa suke suna gai dashi,
Hannayensa cikin Alƙyabbar lokacin zuwa lokacin yakan kawo gefe da gefen Alƙyabbar ya ƙara rufe jikinsa da ita,
Fari ne tass dashi amma fuskarsa babu walwala ko kaɗan,
Kana kallonsa kasan yana cikin matsanancin damuwa da kuma tarin fargaba domin duk yadda yakai
Da ɓoye abinda yake zucyarsa tuni fuskarsa ta riga ta fallasa asirin zuciyarsa,
Yana gab da shikewa wani babban sashe yaji anyi gyaran Muryar daga gefensa,
A hankali yakai dubansa ga wajan ɗan Murmushin sa na gefen baki ya sauke mata yana mai ƙara gyara tsaiwarsa sabida ya fuskanci akwai tarin magana a cikin bakin nata,
Kamar bazai magana ba sai kuma yace.
"Shirwa kike baki jewar banza, mene a ƙasa?"
Murmushin jin daɗi IYALODE (Jakadiya) tayi kafin ta rusuna tana ƙara ɗaga hannunta sama tace.
"Kifi na ganin ka mai jar koma, Wahainiya kake mai wahalar fahimtar launi bare kuma a fahimci naka launin, gaisuwa nake uban gidana, ɗan sarki jikar sarki wanda ya gaji Sarautar a nono,
Kaga sarkin Masarautar Kanzaf na gobe"
Murmushi yana mai ɗan janye fararan idanunsa daga gare ta,
Sosai ya ke jin daɗin yadda Iyalode take ƙara karfafa masa quiwwa bisa ganin muradinsa ya cika,
Muradin da aka haifesa da shi wanda a yanzu yake ganin tarin nasara da kuma haske na cikar muradin,
Fuskarsa ya shafa yana gyara zaman Alƙyabbar jikinsa yace.
"Aku sarkin labari, ai ni damusa ne mai farautar fukkan wanda yace zai ga baya na, shiyasa King (Oba, Sarki, Mai martaba) yake min kirari da SAHUN GIWA ƁADDANA RAƘUMI"
Jinjina kai Iyalode tayi zuciyarta fal farin ciki tace..
"Kaya ya sauka da zafinsa"
Ajjiyar zuciya Aremo Shakiru (Prince, Yarima, Shakiru) Ya yi yana mai juyawa kaɗan ganin babu kowa yace.
"Ya launin kayan suke?"
Kai tsaye Iyalode (Jakadiya) tace.
"Kayan suna da nauyi da kuma wahalar fahimtar launin su, Amma ga Damusa Aremo Shakiru Tunde Muhammad Jalal abin mai sauƙi ne"
Haɗe fuska Aremo Shakiru yay yace.
"Fasaltamin kayan, tun kafin ki tunzura zuciyata ki sanya mutanan cikin Kanzaf su shiga uku"
Da sauri tace.
"MALEEK ya mutu, Amma Mai Babban ɗaki da Oumuu-Ayman sun toshe ko wacce hanya da zata tabbar da mutuwar MALEEK ɗin"
Wani mahaukacin sauke ajjiyar zuciya Aremo Shakiru yay tare dayin baya cikin farin ciki da kuma jin daɗi yace.
"MALEEK!? Mutuwar MALEEK ta ƙara tabbatar min Eh lallai tabbas Muradina na gab da cika maza jeki kuma ki tabbatar da cewa babu wanda ya san wannan Maganar idan kika sake wani yasan maganar to tabbatas kin kawa iyalanki masifa"
Yana faɗin haka ya nufi Shashen damansa yana mai ɗaure fuskarsa.
Bayansa Iyalode tabi da kallo kafin ta saki dariya yana tafa hannu tace.
"Da Iyalode kake Magana, sai na tabbatar ka kusa cika muradin naka ni kuma zan kaika ƙasa, domin Kimata tafi wannan muradin naka"
Tana faɗin haka ta juya kamar walƙiya tabar wajan.
Kai tsaye Aremo ɓangaren OBA TUNDE MUHAMMAD JALAL ya nufa.
A bakin ƙofar shiga tirakar tasa ya tsaya kasancewar yau ko waje King Tunde Muhammad Jalal bai leƙa ba,
Haka kuma ya hana kowa zuwa
Inda yake shima yanzu zai amfani da Soyayyar da King Tunde yake masa,
Yasa zai shiga tirakar tasa yaga meke faruwa, tsayawa yay yana ƙarewa masu tsaran Kofar kallo,
Cikin isa da gadara haɗi da ƙarfin iko yace.
"Yimin iso wajan King"
Ya faɗa yana kallon ɗaya daga cikin hadiman King Tunde ɗin,
Jininta na rawa sabida tsoran Aremo Shakiru Tunde Muhammad Jalal ɗin tace.
"Afuwa Uban ɗaki na, Tuba nake kayi min rai kada kasa na karya dokar King Tunde"
Gajeran tsaki Aremo Shakiru yay yana cillawa Hadimar kallo yace.
"Meye dokar?"
Cikin bashi girmansa na kasancewarsa ƊA a wajan King Tunde,
Ƙara ƙasa tayi da kanta tace.
"Umarni ne daga Oumuu-Ayman cewa kada wanda aka bari ya shiga cikin tirakar ta King Tunde, kuma Umarnin itama daga sama ya sameta wajan Mai Babban ɗaki"
Shu'umin Murmushi Aremo Shakiru yay ba tare da yace komai ba ya juya kai tsaye zuwa shashin OLORI AYOOLA (Queen, matar sarki, Olori Ayoola).
A can ɓangaren Oumuu-Ayman kowa tana zaune a saman Sallaya idar da sallar ta kenan,
Tayi Shiru tana tunanin sabon al'amarin daya kunnu masu kai ba tare da sanin hakan zai faru ba,
Sai yaushe ne komai zai dai-dai-ta? Sai yaushe gaskiya zata bayyana ne? Sai yaushe Allah zai kawo lokacin da za'a warware wannan cukurkuɗaɗɗan wannan Lamari?
Ubangijin Jallah wa'azam! Ne kawai yasan abinda yake ɓoye, amma a kullum tana addu'ar Allah ya kawo ranar da gaskiya zatai halinta,
Abubuwa suna ta faruwa wanda ba'a san ta inda abin ya kunnu kai ba,
Numfasawa tayi a hankali sabida jin maganar Hadima Akin a gefenta,
Kallonta tayi tana sakin ƙyakkyawar fuskarta mai cike da kamala haɗi da zallar haƙuri tace.
"AKIN ya akai?"
ƙasa Hadima Akin tayi da kanta tana mai jan numfashi tace.
"ina fatan uwar ɗaki na Oumuu-Ayman zata fahimci wannan sabun lamarin da yazo ma?"
Jinjina kai Oumuu-Ayman tayi tana mai ɗan sakin murmushi tace.
"Mene ya faru kuma Akin?"
Juyawa Akin tayi kamar mai tsoron faɗin abinda yake bakinta, ganin hakan kuma yasa Oumuu-Ayman tace.
"Kada ki samu babu kowa ni ɗaya ce"
Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Hadima Akin tayi tace.
"Queen Ayoola ta matsa dole tana son sanin inda MALEEK yake"
Lumshe idanu Oumuu-Ayman tayi tana jin wani irin yanayi mai kama da ruɗani yana shiga zuciyarta kafin ta numfasa tace.
"Wacce Amsa kika bata?"
Kai tsaye Hadima Akin tace.
"Haba Uwar ɗaki na, bayan ni kaina bansan Inda MALEEK yake ba, tayaya zan bata amsa"
Hamdala Oumuu-Ayman tayi a ranta tana mai jin daɗi da farin cikin Babu wanda yasan abinda yake faruwa,
Kamar ba zatai magana sai kuma tace.
"Ya Rabb! MALEEK na shashin Mai Babban ɗaki ai, tashi maza jeki wajan aikin ki"
Fita Hadima Akin tayi ba tare data fahimci komai a fuskar Oumuu-Ayman ba hasali ma sai tarin gaskiya da kuma kamewar dake saman fuskarta.
Tana fita Oumuu-Ayman tabi bayanta da kallo zuciyarta fal wasi wasi.
A hankali kuma ta miƙe tana ɗan gyara murya tare daci gaba da tasbihi ga Ubangijjn sammai da ƙassai.
Aremo Shakiru na shiga sashin Queen Ayoola ya sameta zaune,
Saman wata lallausar ladduma irin tasu ta masu mulki,
Ga Hadimanta sun yi mata ƙawanya, Wasu na firfita,
Wasu nayi mata tausa a ƙafarta kege guda kuma wasu na mata massaging a kanta wanda ta ɗan sutale hular Alƙyabbar jikinta,
Hannunta riƙe da Apple tana sha a hankali tana ɗan ɓata fuska,
Ganin Aremo Shakiru kuma ɗan nata ne yasa ta saki Murmushi tare da bawa Hadiman nata damar tafiya zuwa anjima,
Zama yay ƙasan ƙafafuwan ta, yana mai gaisar da ita yace.
"Queen Ayoola Mumyna, ina fatan wannan yanayin da muka riski kanmu yana maki daɗi?"
Murmushi tayi a hankali ta miƙewa tsaye tana mai ɗaukan Inibi takai bakinta tace.
"Uhm, Akwai abinda yake faruwa da King Tunde wanda ba'a so jama'ar Kanzaf su sani, amma menene shi? Ta ina zan sani wannan shi ne abinda nake tunani tun safe, tunda na nemi izinin wajan waccar funafukar Oumuu-Ayman akan tayi min iso wajan King Tunde tace na tara wani lokacin banda wannan satin nasan Tabbas akwai matsala"
Murmushi Aremo Shakiru Tunde Muhammad Jalal yay domin ya daɗe da fahimtar mene ya faru,
Tunda Iyalode ta faɗa masa komai,
Amma sai yay kamar bai sani ba yace,
"Ina Mamaki sosai ainun ace mutum da mijinsa sai wata tana da dama Matarsa zata ganshi,
Ko kuma duk adalilin ba'a so a san Meke faruwa a cikin Alaafin (Masarautar)?"
Murmushi Queen Ayool tayi tace.
"Wannan ba Shine damuwa ta ba, yaushe ne burina zai cika yaushe ne zai dawo?"
Aremo Shakiru yace.
"Queen Ayoola wakike magana akai?"
Daga bakin ƙofar shigowa tirakar ta akace.
"Mahaukacin a koda yaushe zaki iya samun labarin ya dawo, idan har Oumuu-Ayman da Otun (Galadima) basu ɓoye zuwan nasa ba"
Matashin saurayin ya faɗa yana shigowa ciki tare da tsayawa a gaban Mahaifiyarta sa"
Cikin farin ciki Queen Ayoola tace.
"Da gaske JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL ya kusa dawowa?"
Jinjina kai SHAREFUDDEEN yayi yace.
"Bana kuskure a abinda na faɗa kuma za Kice na faɗa maki"
Yana faɗin hakan ya juya ya fice daga cikin tirakar Aremo Shakiru yabi bayan Sharefddeen da kallo yana mai kissima abu a ransa.
A can shashin Mai Babban ɗaki kowa Adams ne zaune a gabanta yana jin abinda take faɗa amma sam baya shiga kunansa,
Cikin gajiyawa kuma da maganar ta yace.
"Zan wuce"
Kallonsa kawai Mai...


Read / Download ABU MALEEK

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album