Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MAI DAKI book 1 Complete Hausa Novel Document by MAI DAKI book 1


MAI DAKI book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 68948



MAI DAKI book 1

Reading Time: 5 Hours

Added On: 24, Feb 2025

Author: Nana Haleema ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Fitattubiyar

Author Phone : 09030398006

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 354.81 kb

File Type: txt

Views: 5+

Download: 17+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: *MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar.

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad @Nana_haleema
ArewaBooks @nanahaleema11


_Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah subahanahu wata'ala da ya bani dama da ikon sake d'aukar alqalami a wannan lokaci, ya Allah yadda ka bani damar fara labarin nan lafiya Allah ka bani ikon gamawa Lafiya. Ya Allah ka bani ikon aikata alkhairi a ciki sa kasa na kaucewa akasin hakan, Allah ka iya min ka dafa min muje karshen sa cikin aminci da kwanciyar hankali, Ameen._

_Wannan labarin na k'irk'ire shi ne banyi da wata ko wani ba, in kin karanta yayi kama da naki ayi hak'uri rashin sani ne._

_Ban yarda wani ko wata su canja min labari zuwa wata siga daban ba tare da izinina ba._

https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

*Book 1*
*Page 1*

Babban gida ne mai hawa uku sama da tsakiya da kuma can k'arshe, yana da tsayi sosai dan sai ka mik’a wuya sosai zaka iya hango k’arshen sa, tun daga gate d'in gidan zaka san ba k'aramin gida bane zaka tabbatar da mamallakin gidan ba k'aramin dukiya yake da ita ba, duba da yanayin tsaruwar gidan da kyale-kyalen da aka yi masa kana gani kasan na matashin mai kud'i ne. In ka shiga compound d'in gidan girman sa sai ya baka mamaki dan motoci sama da hamsin zasu yi parking a gidan sabida girman sa ga shuke-shuke na fulayoyi karaye ko ina da haske a tare dasu.

Daga cikin gidan a can sama na biyu a tsaye take a bakin k'ofa tana tunanin ta shiga ko kar ta shiga, gaban ta fad'uwa yake sabida bata san tashin hankalin da zata tarar da cikin ba in ta shiga hakan ya saka firgici ya bayyana a tare da ita sai zare idanu take sabida tsoro da tashin hankali. Iya fad’an da zai mata ma tayar mata da hankali yake yi balle kuma in yayi mata tsawar da take haukata mata tunani.

Dak’yar ta daure a hankali ta tura k'ofar falon ta shiga da sallama ta hange shi a zaune ya d'ora k'afa kan d'aya da sauri tace, "Amma ce tazo, gata can ak'asa tana jiran ka." Banzan kallon da yayi mata sai da hantar cikin ta ta juya ya taso yazo kusa da ita yace, "Munafurcina kika kai mata kice sai yau na dawo ko?." Kai ta girgiza tace, "A'a, kawai tazo ne amma ba muyi waya ba." Kwafa yayi ya sauka zuwa falon ta biyo bayan sa.

Babban falo ne iya ganin ka girman sa na ban mamaki an saka masa kujeru a tsakiya da carpet mai laushi sanyin a.c yana tashi ga kuma t.v na aiki a kunne. Babbar mace ce a zaune akan kujera ta d'ora k'afa kan d'aya tana bin su da kallo shi da ita musamman ma da yake zaune a kusa da ita da kallo fuskar ta babu alamun annuri ko kad'an kana kallon ta kaga b'acin rai a tare da ita.

"Yusuf yaushe ka dawo?." Jin yadda tayi maganar babu wasa ya saka shi yin shiru ya kasa magana hakan ya saka ta sake cewa,

"Yusuf baka ji me nake ce maka bane?." Wanda ta kira da Yusuf ya gyara zaman sa baice komai ba kansa yana k'asa kana kallon sa kasan bashi da gaskiya. Kallon wacce take gefen ta tayi suka had'a ido ta sake kallon wacce take zaune kusa da Yusuf d'in tace, "Ameenatou kika ce min tun kwana uku da ya wuce ya dawo gida, kenan daman k'arya kika yi min da ki kare shi?."

Wacce aka kira da Ameenatou ta shafa kanta ta sake sunkuyar da kai bata ce komai ba kafin tace, "Kiyi hak'uri Amma." Ammata kalli wacce take gefen ta tace, "Yaushe Ameena zatayi hankali ne akan Yusuf? Har ta kai ta kawo tana b'oye min laifin sa dan kawai kar nayi masa fad'a?." Wacce ta kalla batayi magana ba sai sauke ajiyar zuciya da tayi ta sake kallon sa tace, "Yusuf baza ka fad'a min matsalar ka akan rashin dawowar ka k'asar nan ba bayan kasan kana da mata?."

Sai a sannan ya d'ago ya kalli mahaifiyar tasa kafin yace, "Kiyi hak'uri Amma."
"Tambayar ka nayi ba hak'uri nace ka bani ba."
"Babu komai." Amma ta gyara zama tace, "Kenan kawai iskanci ne da rashin mutunci? Ko kuma dan na hana ka auren waccen y'ar macen wacce bata da tarbiyya balle ilimi shiyasa kake wucewa akan Ameena dan kaga tana da hak'uri ko?."

"A'a Amma, ba haka bane." Cikin fad'a tace, "To yane?." Jin yadda tayi maganar da fad'a sai ya sake sasauta murya yace, "Allah ya wuci zuciyar ki. Aiki ne yayi min yawa a can shiyasa ban shigo ba." Amma ta sake cewa, "Aikin yafi matarka da y'arka?, da zaka yi min zancen aiki aikin uban me kake yi a can? Naga duk wani kasuwancin ka a nan kake yin da ko?. kai ma'aikaci ne da aiki zaiyi maka yawa a wata k'asar?."

shiru yayi bai amsa ba Amma ta girgiza kai tace, "in ma akan waccan yarinyar ne da ka d'auko zaka kawo mana ita cikin dangi kake wannan fizge-fizgen wallahi gwara ka dawo hankalin ka domin babu kai babu ita. Aure ka da matar ka ko shekara uku bai ba amma dan tsabar had'ama kake hangen wata?, watan ma kuma rainon mace wacce uban ta bashi da wani katab'os a kansu bata da tarbiyya. Ahir d'inka wallahi Yusuf ka shiga hankalin ka kar na sake ji kar na sake gani, sannan babu inda zaka koma in ma kasuwacin ne Usman yaji da komai."

Yusuf shi dai kansa yana k'asa yana jin me take cewa kafin yace, "Kiyi hak'uri, hakan bazai sake faruwa ba in sha Allah." Amma ta mik'e tsaye duk suka mik'e ta rik'e hannun Ameena tace, "kwantar da hankalin ki Ameena, yadda Yusuf yake d'ana na cikina haka nake kallon ki matsayin y'ar dana haifa, bazan tab'a bari naga ana cutar dake nayi shiru ba. Batun auren sa babu koda zai k'ara sai nan gaba amma yanzu lokacin ki ne babu wanda ya isa ya shigo miki gidan ki. Kiyi haƙuri kar hakan ya dame ki kinji?."

Ameena tayi murmushi kamar babu abinda yake damun ta tace, "Babu komai Amma. Allah ya saka da alkhairi ya skaa da gidan aljanna." Amma tayi murmushi tace, "Amin daughter. Zamu wuce." Ameena tace, "Ina zuwa Amma" ta fad'a tana shiga ciki Amma ta bita da kallon murmushi Allah ya d'ora mata qaunar sirikar ta da zuciya d'aya domin ta cancanci a sota sabida biyayyar ta da kuma nutsuwa.

Ba jimawa ta dawo da pack babba ta mik'awa Babar yayar su Yusuf tace, "Yayan Abuja a rik'ewa Amma dambun kaza ne." Yayan Abuja ta karb'a tana murmushi tace, "Amma y'ar gatan Ameena, to an gode Allah ya saka da alkhairi" ta fad'a suna yin gaba suka biyo bayan su har suka shiga mota suka fita.

A sannan ta kalli Yusuf taga ya d'aure fuska matuk'a yaja dogon tsaki ya koma ta bi bayan sa jikin ta a sanyaye dan tasan daman za'ayi hakan. Kulle k'ofar falon tayi kamar yadda ta saba bayan tayi karatu ta wuce zuwa d'aya falon da yake da stairs a jiki ta kalla dan tasan ya hau sama ta sauke numfashi tana murmushin da ita kadai tasan dalilin sa.

Kitchen ta wuce ta samu juicer ta yanki kankana ta cilla a ciki ta kunna ta markada ta juye a kofi, ta buɗe fridge ta d'auki madara pick ta fasa ta juye a ciki ta kafa kai ta shanye tass ta ajjiye kofin ta k'arasa wajan wankewa ta wanke ta ajjiye sannan ta koma wajan fridge ta d'auki zuma tasha da yawa dan tana so ta burge mijin ta.

Tana gama sha taji yana kwala mata kira ta fito da sauri ta ganshi ta sama a tsaye daga shi sai k'aramin wando ko riga babu a jikin sa yana fad'in, "Tsabar shirme kina jin Zaytun tana kuka baza kizo ki d'auke ta ba kina can kina haukan banza wanda bazai amfane ki da komai ba." Bata ce komai ba ta fara hawa saman suka had'a ido yaja dogon tsaki ta wuce shi ta d'auki yarinyar ta wacce take bata wuce shekara d'aya ba zuwa da rabi ta zauna tana shayar da ita a falon saman shi kuma ya wuce sama na biyu wanda a nan d'akin sa yake.


Sai da Zaytun tayi bacci ta kaita d'akin ta ta kwantar da ita akan gadon ta sannan ta hau saman da niyar tambayar sa akwai abinda zai ci, a tsaye ta same shi ya fito
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MAI DAKI book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album