Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar.

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad @Nana_haleema
ArewaBooks @nanahaleema11


_Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah subahanahu wata'ala da ya bani dama da ikon sake d'aukar alqalami a wannan lokaci, ya Allah yadda ka bani damar fara labarin nan lafiya Allah ka bani ikon gamawa Lafiya. Ya Allah ka bani ikon aikata alkhairi a ciki sa kasa na kaucewa akasin hakan, Allah ka iya min ka dafa min muje karshen sa cikin aminci da kwanciyar hankali, Ameen._

_Wannan labarin na k'irk'ire shi ne banyi da wata ko wani ba, in kin karanta yayi kama da naki ayi hak'uri rashin sani ne._

_Ban yarda wani ko wata su canja min labari zuwa wata siga daban ba tare da izinina ba._

https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

*Book 1*
*Page 1*

Babban gida ne mai hawa uku sama da tsakiya da kuma can k'arshe, yana da tsayi sosai dan sai ka mik’a wuya sosai zaka iya hango k’arshen sa, tun daga gate d'in gidan zaka san ba k'aramin gida bane zaka tabbatar da mamallakin gidan ba k'aramin dukiya yake da ita ba, duba da yanayin tsaruwar gidan da kyale-kyalen da aka yi masa kana gani kasan na matashin mai kud'i ne. In ka shiga compound d'in gidan girman sa sai ya baka mamaki dan motoci sama da hamsin zasu yi parking a gidan sabida girman sa ga shuke-shuke na fulayoyi karaye ko ina da haske a tare dasu.

Daga cikin gidan a can sama na biyu a tsaye take a bakin k'ofa tana tunanin ta shiga ko kar ta shiga, gaban ta fad'uwa yake sabida bata san tashin hankalin da zata tarar da cikin ba in ta shiga hakan ya saka firgici ya bayyana a tare da ita sai zare idanu take sabida tsoro da tashin hankali. Iya fad’an da zai mata ma tayar mata da hankali yake yi balle kuma in yayi mata tsawar da take haukata mata tunani.

Dak’yar ta daure a hankali ta tura k'ofar falon ta shiga da sallama ta hange shi a zaune ya d'ora k'afa kan d'aya da sauri tace, "Amma ce tazo, gata can ak'asa tana jiran ka." Banzan kallon da yayi mata sai da hantar cikin ta ta juya ya taso yazo kusa da ita yace, "Munafurcina kika kai mata kice sai yau na dawo ko?." Kai ta girgiza tace, "A'a, kawai tazo ne amma ba muyi waya ba." Kwafa yayi ya sauka zuwa falon ta biyo bayan sa.

Babban falo ne iya ganin ka girman sa na ban mamaki an saka masa kujeru a tsakiya da carpet mai laushi sanyin a.c yana tashi ga kuma t.v na aiki a kunne. Babbar mace ce a zaune akan kujera ta d'ora k'afa kan d'aya tana bin su da kallo shi da ita musamman ma da yake zaune a kusa da ita da kallo fuskar ta babu alamun annuri ko kad'an kana kallon ta kaga b'acin rai a tare da ita.

"Yusuf yaushe ka dawo?." Jin yadda tayi maganar babu wasa ya saka shi yin shiru ya kasa magana hakan ya saka ta sake cewa,

"Yusuf baka ji me nake ce maka bane?." Wanda ta kira da Yusuf ya gyara zaman sa baice komai ba kansa yana k'asa kana kallon sa kasan bashi da gaskiya. Kallon wacce take gefen ta tayi suka had'a ido ta sake kallon wacce take zaune kusa da Yusuf d'in tace, "Ameenatou kika ce min tun kwana uku da ya wuce ya dawo gida, kenan daman k'arya kika yi min da ki kare shi?."

Wacce aka kira da Ameenatou ta shafa kanta ta sake sunkuyar da kai bata ce komai ba kafin tace, "Kiyi hak'uri Amma." Ammata kalli wacce take gefen ta tace, "Yaushe Ameena zatayi hankali ne akan Yusuf? Har ta kai ta kawo tana b'oye min laifin sa dan kawai kar nayi masa fad'a?." Wacce ta kalla batayi magana ba sai sauke ajiyar zuciya da tayi ta sake kallon sa tace, "Yusuf baza ka fad'a min matsalar ka akan rashin dawowar ka k'asar nan ba bayan kasan kana da mata?."

Sai a sannan ya d'ago ya kalli mahaifiyar tasa kafin yace, "Kiyi hak'uri Amma."
"Tambayar ka nayi ba hak'uri nace ka bani ba."
"Babu komai." Amma ta gyara zama tace, "Kenan kawai iskanci ne da rashin mutunci? Ko kuma dan na hana ka auren waccen y'ar macen wacce bata da tarbiyya balle ilimi shiyasa kake wucewa akan Ameena dan kaga tana da hak'uri ko?."

"A'a Amma, ba haka bane." Cikin fad'a tace, "To yane?." Jin yadda tayi maganar da fad'a sai ya sake sasauta murya yace, "Allah ya wuci zuciyar ki. Aiki ne yayi min yawa a can shiyasa ban shigo ba." Amma ta sake cewa, "Aikin yafi matarka da y'arka?, da zaka yi min zancen aiki aikin uban me kake yi a can? Naga duk wani kasuwancin ka a nan kake yin da ko?. kai ma'aikaci ne da aiki zaiyi maka yawa a wata k'asar?."

shiru yayi bai amsa ba Amma ta girgiza kai tace, "in ma akan waccan yarinyar ne da ka d'auko zaka kawo mana ita cikin dangi kake wannan fizge-fizgen wallahi gwara ka dawo hankalin ka domin babu kai babu ita. Aure ka da matar ka ko shekara uku bai ba amma dan tsabar had'ama kake hangen wata?, watan ma kuma rainon mace wacce uban ta bashi da wani katab'os a kansu bata da tarbiyya. Ahir d'inka wallahi Yusuf ka shiga hankalin ka kar na sake ji kar na sake gani, sannan babu inda zaka koma in ma kasuwacin ne Usman yaji da komai."

Yusuf shi dai kansa yana k'asa yana jin me take cewa kafin yace, "Kiyi hak'uri, hakan bazai sake faruwa ba in sha Allah." Amma ta mik'e tsaye duk suka mik'e ta rik'e hannun Ameena tace, "kwantar da hankalin ki Ameena, yadda Yusuf yake d'ana na cikina haka nake kallon ki matsayin y'ar dana haifa, bazan tab'a bari naga ana cutar dake nayi shiru ba. Batun auren sa babu koda zai k'ara sai nan gaba amma yanzu lokacin ki ne babu wanda ya isa ya shigo miki gidan ki. Kiyi haƙuri kar hakan ya dame ki kinji?."

Ameena tayi murmushi kamar babu abinda yake damun ta tace, "Babu komai Amma. Allah ya saka da alkhairi ya skaa da gidan aljanna." Amma tayi murmushi tace, "Amin daughter. Zamu wuce." Ameena tace, "Ina zuwa Amma" ta fad'a tana shiga ciki Amma ta bita da kallon murmushi Allah ya d'ora mata qaunar sirikar ta da zuciya d'aya domin ta cancanci a sota sabida biyayyar ta da kuma nutsuwa.

Ba jimawa ta dawo da pack babba ta mik'awa Babar yayar su Yusuf tace, "Yayan Abuja a rik'ewa Amma dambun kaza ne." Yayan Abuja ta karb'a tana murmushi tace, "Amma y'ar gatan Ameena, to an gode Allah ya saka da alkhairi" ta fad'a suna yin gaba suka biyo bayan su har suka shiga mota suka fita.

A sannan ta kalli Yusuf taga ya d'aure fuska matuk'a yaja dogon tsaki ya koma ta bi bayan sa jikin ta a sanyaye dan tasan daman za'ayi hakan. Kulle k'ofar falon tayi kamar yadda ta saba bayan tayi karatu ta wuce zuwa d'aya falon da yake da stairs a jiki ta kalla dan tasan ya hau sama ta sauke numfashi tana murmushin da ita kadai tasan dalilin sa.

Kitchen ta wuce ta samu juicer ta yanki kankana ta cilla a ciki ta kunna ta markada ta juye a kofi, ta buɗe fridge ta d'auki madara pick ta fasa ta juye a ciki ta kafa kai ta shanye tass ta ajjiye kofin ta k'arasa wajan wankewa ta wanke ta ajjiye sannan ta koma wajan fridge ta d'auki zuma tasha da yawa dan tana so ta burge mijin ta.

Tana gama sha taji yana kwala mata kira ta fito da sauri ta ganshi ta sama a tsaye daga shi sai k'aramin wando ko riga babu a jikin sa yana fad'in, "Tsabar shirme kina jin Zaytun tana kuka baza kizo ki d'auke ta ba kina can kina haukan banza wanda bazai amfane ki da komai ba." Bata ce komai ba ta fara hawa saman suka had'a ido yaja dogon tsaki ta wuce shi ta d'auki yarinyar ta wacce take bata wuce shekara d'aya ba zuwa da rabi ta zauna tana shayar da ita a falon saman shi kuma ya wuce sama na biyu wanda a nan d'akin sa yake.


Sai da Zaytun tayi bacci ta kaita d'akin ta ta kwantar da ita akan gadon ta sannan ta hau saman da niyar tambayar sa akwai abinda zai ci, a tsaye ta same shi ya fito daga wanka yana shiryawa ta shiga da sallama ya amsa a ciki ts k'araso tana tace, "Akwai abinda zaka ci?."

Shiru bai amsa ba kamar bai ji ba sai ma juyowa da yayi suka had'a ido ya sake d’auka kai ba tare da ya amsa din ba tace, "Magana nake fa." K'aramin tsaki yayi yace, "Bana ci kuma bazan ci ba." Jin yadda yayi maganar sai tace, "Allah ya baka hak'uri." Banzar harara ya sakar mata ya sake jan tsaki yana magana k'asa-kasa.

"Meyasa kake min haka ne?, me nayi maka ka canja min daga mijina mai qaunata wanda na sani a baya?. Auren mu kwata-kwata bai wuce shekara biyu da rabi ba zuwa uku, yarinyar mu ko yayeta ba'a yi ba, dame na rage ka kake zancen aure tun ban rufe watanni a gidan ka ba?, akwai abinda na gaza baka ne kake tunanin nemo wacce zata baka?" Ta fad'a murya na rawa tana kallon sa cikin karayar zuciya.


Kallon da yake mata bai saka ta daina fad'ar abinda take fad'a ba sai da ya jira ta gama maganar ta kana yace, "Babu abinda kika rage ni, aure ne kawai ina so nayi kuma sai nayi baki isa ki hanani ba wallahi. In baki je kin samu Amma kince mata kin amince da maganar auren nan ba wallahi keda zaman lafiya har abada. Haba! Sai kace kece y'ar gold akan ki mahaifiyata tana neman yi min baki, kin koma kamar itace ta haife ki bani ta Haifa ba, komai nayi fad’a take min sam bata ganin laifin ki sai nawa”ya fad'a yana wurga mata harara cikin b'acin rai.

Hawaye ya sakko daga idanunta tace, "ban tab'a cewa Amma kar ta barka kayi aure ba hasali ma ni ina cewa ta k'yale ka ne, ra'ayin tane ba ni nake saka ta ba, dan haka babu inda zani in ta amince shikenan in bata amince ba sai ka hak'ura."


"Bazan hak'ura ba!, in ma tunanin ki kenan gwara ki ajjiye shi a gefe, aure tamkar nayi na gama. sai na auro wacce nake so tazo
gidan nan koda ke bakya so." Ta sassauta murya cikin rauni tace, "Ni baka sona kenan?." Yadda tayi maganar ya saka shi ya kalle ta yace, "wannan kuma ke kika sani in Ina son ki ma in bana sonki bai shafe ki ba, amma matuk'ar baki je kin samu amma ta janye kalaman ta akan aurena ba baza ki tab'a ganin daidai a gidan nan ba, aure ne Tunda nace zanyi sai nayi koda bakya so. Domin kece kike zugata dan Ammana tana son duk abinda nake so shigowar ki rayuwata kika raba mu."

Ta fusata itama tace, "Sai na tattara na bar maka gidan ka k’arata kai da amaryar sai me?." Yayi murmushi na rainin hankali ya kalle ta sama da k’asa yace, "indai zaki bar gidan nan da yanzu kin tafi, ni na tabbatar babu inda zaki iya zuwa, ni na tabbatar baza ki tab'a yiwa tafiya ki barni ba, domin son da kike min bazai barki ki aikata haka ba. Kar ki manta tun kafin na aure ki son da kike min ya ninka wanda nake miki sau babu adadi. Tafiya ki barni tamkar rabuwa da numfashin kine ba iyawa zaki ba ki daina fad’ar abinda baza ki iya aikatawa ba kinji?.” Fad'ar hakan da yayi sai ta lumshe ido sabbin hawaye suna sake sakko mata tana Jin kamar ta goge abinda ya wuce, a lokacin baya da ake fad’a mata ta sassauta soyayyar da take masa gani take kamar dan basu San abinda take ji bane ashe wannan lokacin ake guje mata.


Ganin tana hawaye ya saka shi sake jan tsaki yace, "Ki tattara hawayen ki ki barmin d'aki zan kwanta, kuma na rantse da Allah in kika sake bar min yarinya tana kuka sabida haukan banzan ki sai ranki yayi mugun b'aci. Shashasha k'azama!" Ya fad'a yana zama a gefen gadon. Hawaye ta share tana kallon sa zuciyar ta cike take sosai da buk'atar mijin ta amma bazata samu abinda take so ba tasan da hakan. Cikin muryar kuka ta sake cewa, "Yau watan ka biyu zuwa uku baka gidan nan, a cikin wata biyu sau biyu kawai kayi min waya. Baka tunanin ina da damuwa da nake so na fad'a maka?."

"Damuwar me? Me kika nema kika rasa a gidan nan?. Kud'i?, abincin?, jin dad'i?, suttura?, fad'a min me kika rasa balle ki samu wata damuwa?" Ya fad'a yana kallon ta.
"Kulawar ka na rasa, ita na rasa itace kuma damuwata. Kud'i ko wani abu ba shine abinda nake so ba domin baza suyi min maganin damuwata ba.”
"Mtswww! Kyaji dashi kuma wannan. Kinga malama zan iya rik'e kaina na tsahon shekara ba tare dana neme ki ba, kema kiyi k'ok'arin koyawa kanki hakan dan nasan abinda yake zuciyar ki kenan kuma ba samu zaki ba. Kin dame ni malama ki wuce ki bani waje" ta fad'a yana kwanciya tare da d'aukar wayar sa.

Ajiyar zuciya tayi ta girgiza kai ta juya ta fita kamar yadda yace ta sauka zuwa saman tsakiya wanda yake nata ta shiga d'akin ta. Tsayawa tayi a jikin wardrobe kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya domin bata da abinda ya wuce yin kukan shine kawai magani a wajan ta. Wayar ta taji tana k'ara ta kalli agogo taga k'arfe goma ta tabbata babu mai kiran ta yanzu sai y'an uwanta ta k'arasa inda wayar take ta d'auka ta saka a kunne daga can b'angaren akace, "Amarya a wajan Yusuf kuma uwar gidan Yusuf, ya dare?."

Ameena ta daure ta had'd'iye abinda take ji tace, "Alhamdulillah Yaya. Ya Bauchin?." Wacce ta kira da Yaya tace, "A'a ya naji maganar ki kamar mai kuka, Lafiya?." Ameena ta girgiza kai tace, "Babu komai Yaya. Kaina ne yake min ciwo kawai nasha magani kuma."
"To Allah ya k'ara lafiya. Ya Zaitun tana lafiya?."

"Lafiya lau Yaya, gata tana bacci." Yaya tace, "To haka ake so. Akwai bikin y'ar wajan Kawu da za'ayi mun had'a kudi zamu bada gudunmawa shine nace bara na tabo ki ko zaki bayar tunda nasan babu lallai kije qauyen." Ameena tace, "Gaskiya dai zuwan dak'yar ne. Kamar nawa zan bayar?." Yaya tace, "Yadda kika yi niya, nidai dubu biyar na bayar."

Ameena tace, "Zan tura miki dubu talatin yanzu a basu dubu ashirin dubu goman ki riƙe." Yaya tayi shewa cikin murna tace, "kaji manya! Allah ya saka da alkhairi ya barki da Yusuf. Mai yafi wannan dad'i ace yar uwar ka tana cikin kwanciyar hankali da jin dad'in rayuwa?, yanzu in badan ke d'in bace waye zai bani?. Na gode wallahi sosai kamar kin san dak'yar aka had'a dubu biyar d'in, Allah ya biya ki."

Tayi murmushi yake tace, "Amin Yaya. Zan tura miki da safe."
"Allah ya kaimu goben. Ke kam kin huta Ameena baki da wata damuwa komai Allah ya baki, kije k'asar da kike so ki hau motar da kike so ki kwana a a.c. shiyasa fa su Amira suke cemin in ayi hutu gidan ki zasu tawo hutu."Ameena tayi murmushi tace, "Allah ya kawo su Yaya, kaina na ciwo sosai Sai da safe" daga nan sukayi sallama ta kashe wayar ta ajjiye.

Baki da damuwa, kina zaune cikin k'aton gida kina hawa mota kina zuwa ko wacce k'asa. Kalaman mutane kenan a kanta a koda yaushe kallon wacce bata da damuwa suke yi mata, basu San damuwar da take ciki tafi duk wannan abubuwan da suke lissafawa ba. Ita kudi b shine a gaban ta ba kula da tattali take so amma ta rasa tun bayan wasu kwanaki da auren ta. Tayi murmushi yake mai ciwo a bayyane tace, "Ko waye ya fad'a musu rayuwar aure a gidan mai kud'i itace jin dad'i ban sani ba" ta fad'a tana lumshe idanunta ta sake cewa, "Nikam jin dad'in aure na wata biyar kacal nayi daga nan komai na canja, tabbas akwai kud'i da k'aton gidan amma babu kwanciyar hankal, yau duka gobe zagi jibi cin mutunci” Tayi murmushi tace, “in kuwa yasha giyar sa ya bugu ranar nida ball bamu da maraba wajan dakuwa.”

Numfashi ta sauke ta mik'e a sanyaye kanta na ciwo sosai ta shiga band'aki tayi wanka ta fito ta saka kayan bacci ta kwanta a kan gadon ta marar ta nayi mata ciwo. Tashi tayi ta k'arasa inda take ajjiye magunguna ta sha p.c.m ta dawo ta kwanta ko zata ji dad'in ciwon da marar take mata. Dak'yar ta samu bacci ya d'auke ta zuciyar ta cike da tunani kala-kala.


*☆☆☆*

Madaidaicin gida ne kai tsaye baza ka ce masa na talakawa ba haka baza kace masa na masu kud'i ba amma zaka iya kiran sa na mai rufin asiri dan yasha fenti tun daga waje duk da bashi da girma. Tun daga soron gidan yake kaca-kaca duk bak'in gawayi har tsakar gidan wanda yake da fasassun tiles an saka a ko ina amma sam Baka ganin tiles d'in sai bak'in gawayi a ko Ina.

A tsaye yana bayan ya fito daga d'aki yana kallon tsakar gidan cikin mamaki kafin ya buɗe murya yace, "Fiddausi!." Daga cikin d'akin ta amsa ta fito ta kalle shi tace, "Gani." Ya kalli gawayin ya kalle ta yace, "Yaushe buhun gawayin nan ya k'are har aka fitar da buhun ya b'ata wajan nan haka?."

Ta yatsine fuska tace, "Ba k'arewa yayi ba, nan baya gidan Maman Zainab itace ta aiko na sammata sai kawai nace yaron ya d'auka gabad'aya ya kai mata. Shiyasa wajan ya lalace." Kallon ta yake yi ganin ko a jikin ta maganar ta take kai tsaye kamar ita t siya yace, "Fiddausi ya d'auka gabad'aya fa kika ce? Kenan ke bakya buk'ata?."

"Haba dan Allah Abban Amir, kalli fatata tsabar kunna gawayi duk ta zama bak'a kai kasan ai ba haka ka d'auko ni ba. Wallahi ni ba kalar aiki da gawayi bace na daure nayi na wasu kwanaki yanzu kam bazan iya ba. In baza ka iya cigaba da siyo mana kalanzir ba kawai ka siya mana gas."

Kallon ta yake yi da zallar mamaki kafin yace, "Yanzu tsakani da Allah Fiddausi buhun gawayi naira dubu hud'u baki san taya na samu kud'in na siya ba dan kawai bana son siyan abu kad'an-kad'an sai ki d'auka kiyi kyauta ba tare dana sani ba?."
"To Abban Amir dan na bayar ai ba laifi bane, naga da ka kawo cewa kayi nayi aiki dashi kenan nawa ne dan nayi kyautar sa ai ba wani abun bane. Kuma da kasan yadda matar take min kallon matar alhaji da baka ce haka ba wallahi, gani take Nafi karfin komai dan nayi wannan ai ba wani abun bane."

Kai ya girgiza zuciyar sa cike da d'aci yace, "Ai kin kyauta" ya fad'a yana wuce ya buɗe rijiya ya d'ebo ruwa ya shiga band'akin tsakar gidan. Tsaki tayi kad'an bayan ya shiga tace, "Wallahi sai ka siya min gas bazan je gidan k'awaye da y'an uwa na gani ni babu a naaa gidan ba, haka kawai salon ayi min dariya daman duk cikin y'an uwa ni ake kallo a tsiyace, wallahi bazai yu ba. Ko a gidan mu ni ake kallo koma baya Yaya da take aure mai kudi hatta su Umma sunfi sonta dani.”

D'aki ta koma bai jima ba ya fito ya shiga d'aya d'akin da yake kusa da wanda ta shiga ya shirya ya fito tsaf dashi ya shiga d'akin da take ya same ta akan kujera yace, "Ina abincina?." Ta d'an sosa kai tace, "Daman jira nake ka shigo nace ka siyo mana madara da milo da kuma biredi, na dafa mana shayi." Kugu ya rik'e yana kallon ta yace, "Amma kamar akwai ragowar gasarar kunu ko? Kuma jiya na shigo da awara d'anya nace ki soya mana da safe ko?."

Ta kalle shi tace, "banyi bane kawqi bana son karyawa da kunu da awara ne wallahi, kawai ka siyo mana biredi musha shayi yau d'aya dai."
"Fiddausi meyasa kike min haka ne wai?." Ta mik'e tsaye tace, "Me nayi maka? Dan kawai na fad'i ra'ayina sai kawai abun ya zama laifi?."

"Yanzu haka zan tafi kenan ban karya ba?." Tace, "Na fad’a maka akwai ruwan zafi ka aika a siyo mana kayan kaga aiki da cikawa yanzu." Yace, "Bashi nake so naci ba, kije ki dama min kunun yanzu ki kawo min" ya fad'a yana zama. Badan taso ba ta fita tana magana ita kad'ai ta dama kunun ta kawo masa a kofi ta mik'a masa tace, "Na riga na bayar da gawayin babu wanda zan soya awarar dashi."

Baice komai ba ya karb'a yasha kunun ya

Please Login or Register in order to submit comment