Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zauna kamar wacce take jiran wani kafin ta kuma tashi ta nufi saman nasa. A tsaye ta ganshi ya idar da sallah Zaytun na zaune a kan gadon shi kuma yana saka hula cikin manyan kayan da sukayi masa kyau fiye da wanda ya cire sai khamshi yake yi.

Kallon ta yayi suka had'a ido ya d'auke ido ya gama saka hular yana kallon kansa ta tsaya a bayan sa yana ganinta ta jikin mirror d’in itama tana kallon sa tace, "Na gama abinci." D'an jimm yayi domin kuwa baya son ci, dan sunyi da Asiya tayi masa girki in yaci wani abun bazata ji dad'i ba hakan ya saka yace, "Ki barshi kawai zanje taro yanzu a can zanci."

"Amma ai na riga na girka maka" ta fad'a tana kallon sa. Kallon ta yayi yace, "Nace kuma bazan ci ba, wai meyasa kike haka ne?."
"Allah ya baka haƙuri."
"Mtswww" yaja tsaki yana cigaba da shiryawa.

Lins d'insa ya tuna ya barsu a toilet da zaiyi alwala hakan ya saka shi ya koma a wannan lokacin kiran waya ya shigo wayar sa, kallon wayar tayi taga my love ta k'arasa ta d'auki wayar a hannunta tana kallon sunan kawai sai ta amsa kiran ta saka a speaker, "My love kai nake jira fa, na gama yi maka girkin kazo ina kewar......" caraf taji anyi sama da wayar ya danna kashewa ya kalle ta suka had'a ido sai ya basar ya d'auki key d'in mota yayi hanyar fita ba tare da yace komai ba.

"Daman taron da zaka je kenan shiyasa ka k’i cin abincina?, ina laifin kaci nawan in kaje itama kaci natan ko yaya kaga kayi adalci a tsakanin mu, tun kafin ta shigo har ka fara nuna min ta fini a wajan ka?." Kalaman ta suka shi ya tsaya cak tare da juyowa ya kalle ta kamar zai magana sai kawai ya fasa ya juya ya fita da sauri bai ma sake kallon ta ba.

Hawaye taji suna neman sakko mata sai tayi haƙuri ta danne su ta d'auki Zaitun suka sauka daga saman nasa jikin ta har rawa yake yi sabida tsabar tashin hankalin da zuciyar ta take ciki. Ajjiye Zaitun tayi ta jingina da bango hawayen da bata so su zubo suka sakko mata ta fara kuka kamar k'aramar yarinya.

Nan da nan zazzaɓi ya rufe ta ta dawo gefen gado ta zauna ta dafe kai dan ji take kamar kan zai cire, dafa ta Zaitun tayi ta baya ta mik’e tsaye tana wasan ta hakan bai saka ta juya ba. Bata da kowa wanda zasuyi shawara ta fad'a masa damuwar ta ya share mata hawaye, ita ba irin wacce take fad'awa k'awaye damuwar ta bane duk da sun saba kowa yasan sirrin kowa amma ba komai take son fad'a musu ba, da ace tana da uwa da babu abinda zai hana bata tafi ta fad'i akan cinyar ta tana kuka ba dan ita kad'ai ce maganin damuwar ta.

"Allah ya jiqan ki Mamana, Allah ya gafarta miki yasa kina aljanna. Abbana Allah ya yafe maka yasa ka huta. Yusuf ya kasa rik’e amanar da ka bashi Abba....bazai iya ba ya gaza bani kulawar da kake yi min mafarki Abba....." ta k'arasa fad'a cikin kuka mai ban tausayi zuciyar ta na bugawa da sauri.


K'arar wayar ta taji kamar bazata duba ba sai ta duba taga sunan Yayata yana yawo a kai ta jawo ta d'auka ta saka a kunne, kafin tayi magana taji tana kuka hankalin Yaya ya tashi cikin kidima tace, "Amina lafiya kike kuka? Meya faru haka?." Bata yi magana ba kuka take yi sosai hakan ya sake tayar mata da hankali tace, "Dan girman Allah kiyi hak'uri ki daina wannan kukan ki fad'a min damuwar ki, meya faru?."

Bata daina kukan ba kuma batayi magana ba sai daga baya tace, "Yayata Kaina ciwo yake min, zuciyata zafi take yi, ke kad'ai nake da ita kuma kinyi min nisa Yayata. Dan Allah kizo kafin azo a fitar da gawata dan Allah."
"Subahanallah! Meena meya faru haka? Dan Allah ki fad'a min wani abun ne ya same ki?."
"Yayata Yusuf aure zaiyi, na rasa inda zan saka raina, komai baya min dad’i zaman gidan ya ishe ni" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da kuka.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Aure kuma Meena? Yusuf d'in ne zai aure yayi miki kishiya?." Bata iya magana ba sai kuka tace, "Ki nutsu ki fad'a min wannan kukan ba magani bane ba, Yusuf d’in ne zaiyi aure Amina?."
"Eh Yaya, aure zaiyi yanzu haka ya tafi wajan wacce zai aura ma. Na rasa abinda yake min dad'i ji nake kamar na fad'o daga sama na mutu ya huta da ganina."

"Hasbunallahu wani'imal wakil! Ki nutsu Amina kiyi haƙuri in sha Allah gobe zan shigo Kano, ki daina wannan kukan dan Allah ba magani bane kita karanta Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ki daina zubar da hawayen ki domin ba magani bane ba. Addu’a itace magani kin ji ko?.” Kuka take yi Yaya tana kwantar mata da hankali cikin kalamai masu dad'i har ta samu ta tsayar da kukan ta tabbatar mata da tana hanya gobe kafin suyi sallama ta kashe wayar Amina tana jin dad'i a ranta dan sai take ji kamar tayi magana da mahaifiyarta ne.

Yusuf kuwa koda ya fita sai da yayi sallar i'sha sannan ya tafi gidan su Asiya kai tsaye kamar ko yaushe. A inda ta saba tarbar sa a nan ta ajjiye shi ta kawo masa abinci da ruwa ta zauna tace, "Ina Zaitun d'in bayan kace min zaka zo min da ita?."

Murmushi yayi yace, "tayi bacci ne, amma next time zaki ganni da ita. Ina so fa naje na gaida Umma yau mun kwana biyu bamu gaisa ba."
"Ka gama cin abincin in yaso sai mu shiga" ta fad'a tana kallon sa da murmushi. Shima haka ya kalli abincin yace, "To ayi serving d'in mana Madam."

Y'ar dariya tayi ta taso ta zuba masa ya karb'a abincin sai khamshi yake yace, "sabida wannan abincin kona madam banci ba." Tayi farrr da ido tace, "Ashe ina da babban matsayi haka a wajan ka, har a tsallake abincin uwar gida ran gida azo aci nawa." Murmushi yayi kawai ya fara cin abincin dan khamshin yana d'aukar hankalin sa sosai.

Da taga ya fara ci sai tayi shiru a haka yaci ya rage kamar yadda ya saba ya ajjiye yace, "Alhamdulillah. Abinci yayi dad'i sosai, Allah yasa dai ke kikayi." Tayi dariya tace, "In ma bani din bace zaka tabbatar nan gaba.” Yayi murmushi itama tayi tace, "Ka nuna min hoton Yayata na ganta kar wata rana a had'u a hanya azo aji kunya.”

Wayar sa ya d'auka yana dubawa yana fad'in, "Anya ina da hoton ta? Ni dake bana ajjiye hotuna a waya indai ba naki ba, Allah yasa a samu."
"Ka jika, ka ajjiye nawa ma balle nata?. Bana son dad’in baki.”
"Sai na ajjiye nakin ai ban ajjiye nata ba, ita ina ganin ta kullum ke kuwa in kewar ki ta motsa in banga hoton ba bana samun nutsuwa."

Tayi dariya kad'an tace, "Allah yasa dai na samu rabin rabin matsayin da take dashi a wajan ka." Ya sake murmusawa yace, "matsayin ki daban ai nata daban, kowa da fadar da aka ajjiye shi” ya fad'a yana hasko mata screen d'in wayar ta karb'a tana k’arewa Amina kallo.

Tayi kyau sosai a hoton t nan take taji wani abu ya soke ta a zuciya domin ta tabbatar komai Amina ta fita gata fara tasss kamar ba bahaushiya b, ga kyau yadda taga gaban kanta hakan ya bata tabbacin bazata rasa gashi ba dan ga gashi nan kwance a goshin ta. Dak'yar ta iya b'oye yanayinta tace, "ma sha Allah. Yayar tawa ta ko ina ta wuce ni."

Karb'ar wayar yayi yace, "kece kike ganin haka amma banda ni." Tayi dariya kawai suka cigaba da hira kafin ta raka shi cikin gida su gaisa da Umma da Baba ya ajjiye musu kud'i daga nan ta rako shi sukayi sallama ya tafi zuciyar sa na sake nitso cikin Kogan soyayyar ta.

Tunda ya saka k'afa yana hawa saman yake jiyo kukan Zaytun da sauri ya k'arasa dan in akwai abinda ya tsana bai wuce kukan yaro ba ya nufi dak’i ta kai tsaye yana zuwa ya samu Zaitun d'in ta fad'o daga kan gado tana ta kuka ita kuma tana kwance a kan gadon bata motsa ba.

Da sauri ya k'arasa ya d'auke ya sakata a kafad'arsa yana jijjiga ta ya kalli Amina yace, "Wannan wanne irin wulaƙanci ne kina ji tana kuka baza ki tashi ki d'auke ta ba kina zaune kina tunanin banza da wofi." Maganar sa take ji a sama ta buɗe ido ta tashi zaune yaja tskai yace, "karb’e ta" ya fad'a yana mik'a mata ita wajan Karb'ar nata hannun su ya had'u da nata.

Zazzafan zafi yaji a fatar hannun nata hakan ya firgita shi ya tab'a wuyan ta yaji zazzaɓi kamar wuta ya kama k’ugu yace, "ban san me yake damun ki ba, na fad’a miki muje asibiti kin k’i haka kike so ki zauna da ciwo?." Bata iya magana ba ta fara shayar da Zaitun d'in ya bita da kallo kafin ya sake cewa, “Ban San yaushe kika koma haka b wallahi” ya fad’a tana fita daga d’akin.

Bai jima ba ya dawo da magani ya zauna ya bata maganin da kansa tasha ya tashi ya fita ba tare da yace mata komai ba. Bata sake ganin sa ba hakan ya saka ta kwanciya dan bata da kuzarin tashi tayi wanka a haka bacci ya d'auke ta dan taji dad'in ciwon kan sosai zazzaɓin ma ya sauka.

*☆☆*

Fiddausi da mai adaidaita sahu ta koma guda cike da kaya domin siyayya tayi sosai son ranta, ta kashe kud’i yadda take so tana sauka aka shigar mata da kayan cikin gida ta fara tattara kayan tana saka su a inda zata ajjiye kafin ta shiga band'aki tayi wanka ta fito ta saka kaya masu kauri sabida sanyin da ake yi.

Girki tayi kafin ta koma d'aki tayi kwanciyar ta tana shafa sabuwar wayar ta cikin farin ciki da tsantsar nishad’i zuciyar ta ji take fari tas. Sallah ce kawai ta tashe ta tana sallar magriba ya shigo ganin tana sallah sai ya fita zuwa d'akin nata.

Bai dawo ba har akayi i'sha tana zaune tana cin abinci ya shigo da sallama bata kalle shi ba ya zauna yace, "Naga kaya a tsakar gida da kitchen."
"Uhum siya nayi."
"Siya kika yi? Da wanne kud'in kikayi wannan siyayyar?" Ya fad'a yana kallon wayar ta da take dannawa.

"Kud’ina mana dasu nayi siyayyar" ta fad'a tana kallon sa. Abincin da take ci ya kalla yaga abincin dai bai saba shigowa irin gidan sa sosai ba ba yace, "Fiddausi ban fahimta ba an ina kika samu?." Cikin k’osawa tace, "bafa wasu kud'i masu yawa bane yan kad'an ne na kashe, kuma daman ai na fad'a maka Yaya ta bani kud'i to meye na damuwa da lamarin?."

Jin yadda take d'aga murya tana magana ya saka shi zuba mata ido yana kallon ta da mamaki ganin yadda ta canja daga fitar ta zuwa dawowar ta yace, "da kud’in kikayi wannan siyayyar?."
"Haba dan Allah, na fad'a maka kud'in kad'an ne fa dan Allah ka daina damuna in baza kaci ba ka barshi."

"Ita kuma wayar fa?." Ta kalli wayar ta kalle shi tace, "tawa ce itama siya nayi, dan girman Allah ka daina takura min bana son magana kai ka sani, abinci nake ci duk kabi ka dame ni da magana."
"Ke bana son rashin mutunci, ina miki magana kina d'aga min murya kamar wani sa'an ki?."
"Sa'ana ne mana, waye kai in ba sa'an nawa ba?."

"Ki shiga hankalin ki Fiddausi bana son rashin kunya ki gane da wanda kike magana kafin ranki ya b’aci.”
"Rashin kunya ka siye ta da kud'in ka domin na gaji da zaman gidan nan ko da yaushe zaman gida a cikin duhu babu haske kamar kabari, solar zan saka a had'a a gidan nan gobe goben nan domin bazan iya zama haka ba, zaman da na kwashe ma a baya Allah ya bada lada” tana fad'a ta tashi ta bashi waje ya bita da kallo zuciyar sa nayi masa zafi sai kawai ya zabura yabi bayan ta dan bazai k’yale ta ba.

Unexpected taga shigowar sa dan bata yi zato ba ta zabura hannunta yana rawa shi kuma yana bin hannun nata da kallo ganin kud'i masu yawan da bai tab'a rik'e su ba hakan ya saka ta rud'e duk ta dirirce ta rasa yadda zatayi tunda ya riga ya sani…..



#Nana Haleema
#Book 1
#Fitattu biyar
#rikicin gidan aure

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

Masu nema daga farko ku duba Whatsapp channel zaku samu
https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*


*Book 1*
*Page 13*



Yadda ta firgice tana zare idanu shine ya kai hankalin sa ga hannunta da kud'in da suka zube a k'asa sun watse ya bisu da kallo yana kallon ta cikin mamaki mai yawa kafin yaga ta daidaita nutsuwar ta ta sunkuya ta tattara kud'in ta nufi inda kayan ta suke ta buɗe ta saka ta juyo suka had'a ido ta sake d'aure fuska ta wuce ta zauna a gefen gado tace, "Haka kawai a dinga shigowa mutane babu sallama."

Shigowa d'akin yayi jikin sa yayi sanyi zuciyar sa na bugawa a guje tsoro ya gama mamaye jikin sa k'araso yana kallon ta yace, "Fiddausi wannan kud'in masu yawa a na waye?." K'aramin tsaki tayi ta murguda baki tace, "Bafa kud'ina bane kud'in Mama ne ta bani na ajjiye mata, kasan dai ba wannan kudin ne dakai ba balle kace sata na fara yi maka dan bana tunanin ka tab'a rike kud'i kamar su."

Share abinda tace yayi dan so yake yaji yace, "Amma yadda kika firgita hakan ya nuna min kamar baki da gaskiya" idon sa ya kai kan iPhone 11 d'in da take hannun ta a d'azu ya k'arasa wajan wayar zai d'auka tayi zaraf ta d'auka tace, "Wai yaushe ka koma mai bincike ban sani ba?, kawai dan kaga waya baka san ta wacece ba sai ka dauka?. Na fad'a ai tawa ce ko? Zakiyya ce ta aramin nayi amfani da ita."

"Me zakiyi da ita da kika ara? Ke meyasa bakya gudun abun magana ne Fiddausi?."
"Meye abin magana a nan?, naga dai kawata ce kai ka san da hakan ko?."
"Kawar ki ai ba y'ar uwar ki bace ba."
"Kaga Abban Amir dan Allah ka kyale ni kaje ka kwanta ni na gaji bana son magana" ta kalli d'akin taja tsaki tace, "Ni wallahi na gaji da zama a duhu, tun ban shiga kabari ba na saba da zaman duhu wallahi bazai yu ba."

Numfashi ya sauke yana girgiza kai zuciyar sa tana so ta jefa masa alamar tambaya akan Fiddausi domin abubuwan da take yi ya fara k'in amincewa da lamarin taya cize bakin sa ya fita domin kuwa dole yasan abinda zaiyi. Yana fita tayi tsaki tace, "Aikin banza, ko ta tsiya kota arzuk'i sai na bar gidan nan wallahi. Ni a dawo min da d'ana ma hutun ya isa haka na gaji da zaman gidan nan babu shi."

*Washe gari.*

Tunda Yayar Bauchi ta sanar da Amina ta taso ta daure take dan yi mata abinda zata ci dan zuciyar ta cike take da zumudin ganin yayar tata dan sun jima basu had'u ba tun wani taro da akayi suka had'u basu sake ganin juna ba. Sai a lokacin Yusuf ya sakko ya same ta a tsaye a falon tana magana da masu aikin ta ganin sa suka gaishe shi suka bar falon.

Juyowa tayi ta kalle shi suka had'a ido sai tace, "Barka da safiya." Gira ya d'age duka biyun yana kallon ta kafin ya furzar da iska daga bakin sa yace, "Barka" yana fad'a ya fita daga falon bai sake ko kallon ta ba ta bishi da kallo tayi saurin kawar da abinda yazo ranta ta koma ta cigaba da aikin ta.

Sai azahar Yayar ta ta shigo cikin gidan a lokacin ta gama yi mata komai ta shirya tana zaman jiran zuwan ta. Shigowar ta ya saka Amina tashi a guje ta fad'a jikin ta sai kawai ta fashe da kuka.

Rungume ta tayi itama tana shafa bayanta tana fadin, "Haba Amina yanzu irin tarbar da zan samu daga wajan ki kenan?." D'agowa tayi ta goge idanun ta tace, "Kiyi haƙuri Yayata, Sannu da zuwa, muje sama kiyi wanka ki huta." Hannunta ta riƙe zasu hau saman sai a sannan ta lura da babar yar Yayar tata mai sunan Maman su wacce suke kira da Amira tace, "Amira ai ban ganki ba."

Tayi dariya tace, "Taya zaki ganni Anty Amina kina murnar ganin Mama?." Dariya tayi tace, "Bari kedai kawai, Yaya nake gani kuma Mama nake gani a fuska guda d'aya." Dariya Amira tayi kawai suka hau saman gabad'aya tana jin kewar mahaifiyarta na sake zagawa jikin ta.

Dak'i suka shiga wanda yake kusa dana Amina ta kalli Yayar tace, "Yaya kiyi wanka bara na kawo muku abinci" ta fad'a tana niyar fita. Hannun ta Yaya ta rik'o tace, "Ba wanka ko hutawa ne ya kawo ni ba Amina, nazo ne akan abinda yake damun ki har kikayi wannan ramar." Kallon Yayan tayi jin yadda take magana da rauni tana kallon ta alamun abin na damun ta sai tayi murmushi tace, "Ku fara hutawa tukkuna Yaya, Amira shiga kiyi wanka zaki ji dadi. Ina zuwa" ta fad'a tana fita duk suka bita da kallo ganin yanayin tafiyar tama kana kallo kasan bata da cikakkiyar lafiya.

Sai da ta tabbatar sunyi wankan sannan ta dawo saman da manyan flakas masu kyau ta ajjiye a falon sannan ta shiga d'akin ta same su har sun canja kaya tace, "Yaya ga abinci a falo kuzo muci" bata jira amsa ba ta juya ta fita dan bata son su fara maganar sai Yayan ta huta. A tare suka fito suka zauna suka fara cin abincin sai babu wanda yake magana a cikin su burin Yaya bai wuce taji damuwar tilon kanwar tata b shiyasa ta kasa sukuni tayi shiru dan kar ma wata hirar tazo.

Ameena tace, "Ina aka baro Hidaya da Abban mu?." Yaya tace, "Suna gidan kakar su daman sun je Hutu."
"Aka musu wayo aka tawo babu su."

Bata ce komai ba Yayan bata ci sosai ba ta ajjiye ta kalle ta tace, "Amina ba cin abinci ne ya kawo ni abinda yake damun ki nake so naji. Me yake faruwa a cikin gidan nan haka?." Shiru tayi ganin hakan ya saka Yaya ta kalli Amira tace, "Amira dauki abincin kije daki kici." Ba musu ta tashi ta dauki plate din abincin ta shiga d'aki ita kuma ta fuskance ta tace, "Ke nake saurare."

Ameena ta sauke numfashi tace, "Yaya aure Yusuf zaiyi."
"Nasan wannan kin fad'a min tun a waya, dalilin zai k'ara aure ne kika koma haka Ameena?." Kai ta girgiza alamun A'a hawaye ya sakko daga idon ta ta share tace, "Ba aure ne yake d'aga min hankali ba Yaya, canjawar da yayi shine abinda yake bani tsoro. Yaya yanzu Yusuf bai San damuwata ba ko kallo ban ishe shi ba, zaman gidan nan gabadaya ya gama gundura ta, barin sa kawai nake fata."

Yaya ta dawo kusa da ita ta dafa kafadarta tace, "Auren sa kar ya dame ki Ameena tun farkon auren ku nasan babu lallai ya rayu dake ke kad'ai a gidan nan, canjawar sa kuma zan iya cewa a cikin kaso d'ari na mazan hausawa in zasu k'ara aure kashi tamanin sai sun canjawa matan su. Kar wannan ya dame ki kalli yadda kika koma dan Allah kamar ba ke ba, na tabbata babu lallai ya samu macen da ta fiki Ameena, ki kwantar da hankalin ki. Yanzu da kika saka damuwa kika rame akwai abinda ya fasa daga hidimar gaban sa?" Ta tambaya tana kallon ta.


Girgiza kai tayi alamu A'a Yaya ta kuma cewa, "to meye na saka damuwar? Kinga tabbacin duk abinda ya same ki wannan ke kika jawowa kanki koda mutuwa kika yi bazai fasa auren sa ba. Nasan da ciwo amma ki daure ki kawar daga zuciyar ki wata rana sai labari." Idanun ta sun jiqe sa hawaye tace, "Amma Yaya ban dauk'a zai min kishiya da sauri haka ba, kwata-kwata kwanan mu nawa da auren har zai kawo mata?. Na tambaye shi ko akwai inda na gaza har yake k'ok'arin d'auko wata yak'i ya fada min. Yaya ya canja fiye da tunanin ki dan yayi kwana biyu bai waiwaye ni ba abu mai sauki ne a wajan sa Yaya, dole na damu kin San ina son sa tun ba yanzu ba zuciyata ji nake kamar zata fashe".

A kafadarta ta kwantar da ita tana shafa kanta cikin rarrashi tace, "Nasan kina son Yusuf Ameena nafii kowa sanin hakan, shima yana sonki wannan canjin na d'an lokaci ne duk zai zo ya wuce ya zama labari."
"Allah Yaya asiri yarinyar tayi masa dan baki ga yadda ya gigice ya daina kula ni kawai yana tunanin nice nake zuga Amma tak'i ya aure ta".
Yaya tayi karamar dariya tace, "Hmmm ba wani asiri Amina, kawai in namiji yaso k'arin aure hankalin sa kamar barin jikin sa yake sai yayi yake dawowa daidai, kar ki damu komai zai wuce In sha Allah."

Shiru sukayi dukkan su babu wanda yayi magana kafin Amina ta dago daga jikin Yayan ta goge idanun ta Yaya tace, "Kiyi hakuri ki daina saka damuwa a zuciyar ki ke hakan zai cutar ba wani ba. Ni banga abinda zai saka ki rama haka a cikin abinda kika fad'a ba, Anya iya abinda yake damun ki kenan?." Ameena tace, "Shikenan Yaya bayan wannan babu komai."
"To aure akan ki aka fara da zaki tayar da hankalin ki haka? Nasan babu dad'i amma ai komai zai wuce, ki jira yayi auren ki gani zai koma yadda kika san shi a baya, kawai ki ta addu'a Allah ya had'a ki da abokiyar zaman ta garı." Kai ta girgiza alamun gamsuwa tana Jin nutsuwa na shiga zuciyarta ko babu komai ta samu rarrashin data jima bata samu ba.

Sallar la'asar ce ta tashe su daga wajan sukayi sallah Yaya ta tilasta mata taci abinci nan da

Please Login or Register in order to submit comment