Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Muna islamiyya? Ina duk suka tafi?, ya akayi kika bari shaid......" saurin dakatar da Rukayya tayi tace, "Ke bani da wani aljan ko shad'ai ko zuwan bil adama kamar ni da zaiyi tasiri a kaina, duk wannan soki burutsun da kike ba tasiri zaiyi a kaina ba. Zancen miji da nake dashi baki dashi me zai hana bazaki auri ibrahim d'in ba? Daman ai naga ke talaka kike nema ko? To Gashi kin samu ki aura ki shigo ki zauna ni kuma na fita domin banga abin kishi a wajan sa ba. Ke ko ina gidan nan ma ki shigo, banga abinda zanyi kishi a wajan sa balle ni ficewa zanyi wallahi bazan zauna ba."

Mamaki ya saka Rukayya ta kasa magana sai kawai ta fara hawaye ta toshe bakin ta tana girgiza kai dan bata d'auka son duniyar Fiddausi ya kai haka ba tace, "kiji tsoron Allah Fiddausi, kiyi ta'awizi ki kori shaid'an in ba haka ba wallahi yana gab da komawa gefe yayi miki dariya. Shawara nake baki matsayina na k'awar ki mai son cigaban ki, wallahi Fiddausi ki tuba kije ki bawa mijin ki hak'uri."
"Wallahi baza ni ba, ina kuma tabbatar miki da baza ki sake dawowa ki tarar dani a gidan nan ba sai dai wani amma ba nan ba, ke ki aure shi kinga kin samu abinda kike so."
"Allah yana kallon ki duk abinda kike yi Fiddausi" abinda ta iya fad'a kenan ta juya ta fita daga d'akin da sauri. A zaune taga Ibrahim yayi tagumi fuskar sa ta nuna alamun b'acin rai da alama duk yaji abinda suka tattauna bata iya yi masa magana ba ta fita a guje tana kuka zuciyar ta na sake tabbatar mata tabbas akwai abinda yake damun Fiddausi.

^^^^^^^

A haka Rukayya ta shiga gidan su tayi d'aki a guje kai tsaye band'aki ta shiga tayi alwala ta fito ta daure tayi sallar magriba ta zauna jugum abinda ya faru yana yi mata yawo a kanta gani take kamar a mafarki shiyasa take mamakin abun sosai. Bata tab'a ganin fad'a ba mata da miji a zahiri ba sai da a film ko a littafi, mata da mijin ma kuma wai k'awar ta Fiddausi.

"ke Rukayya!" Aka fad'a Ana shigowa ta juya ta kalli Umman ta da ta shigo tace, "Na'am Umma."
"Sai yanzu kika ga damar dawowa daga gidan Fiddausin? Bayan kin San na fad'a miki zakiyi bak'o?."
Ajiyar zuciya tayi tace, "Kiyi hak'uri Umma na manta ne wallahi." Umma ta Harare ta tace, "Ai dole ki manta tunda daman ba so kike ba, tashi kije gashi can a d'akin Baban ku saura ki dawo naji wata magana daban." Da to ta amsa ta tashi jikin ta a sanyaye ta fita zuwa falon Abban nasu da hijjabin da tayi sallah a jikin ta.

Tunda ta doshi shiga d'akin take jin warin sigari; da ta sake kusantar falon ta tabbatar a ciki take jin warin, kai ta saka ta shiga ta hango wanda akace zai zo hannun sa rik'e da sigari yana sha yana busa ta sama ganin ta shigo sai yayi saurin cillar da ita akan tiles ya saka k'afa ya take ya mik'e tsaye yana dariya da yaga shigowar ta.

Fuska ta d'aure dan bata son sakar masa fuska ma ya samu wata dama ta saka gefen Hijjabin ta ta toshe hanci tana kallon sa shima haka kafin yace, "Barka da zuwa hajiya Rukayya." Bata cire hijjabin a bakin ta ba tace, "kaine bak'on nawa?." Ya gyara tsayuwa yace, "Kwarai nine, na jima Ina sonki wallahi."
"Ni kuma bana sonka kar ka sake ka sake zuwa gidan mu, bazan aure ka" ta fad'a tana niyar barın falon taji yace, "ji mana y'an mata, ai daman ba sai kin soni ba taimaka miki nazo yi sanin kin jima a gida babu mai zuwa yace yana sonki, kizo na taimaka na aure ki na rufa miki asiri kafin a fara kad'a miki ganga ana yawo da hoton ki a masallaci."

Takaici bai bari ta bashi amsa ba ta fita da sauri ta bar masa falon zuciyar ta na k'una hawaye sun ciko idanun ta. Shikenan da ka samu jinkirin aure ko wanne banza yazo sai a bashi dama ya ganka, Tsautsayi ya saka ka amince kuma ayi auren wani abun ya faru azo ana dana sani.

Tana shiga falon Umma zata wuce Umma ta dakatar da ita tace, "Ya kuka yi dashi naga har kin dawo?." Ta kalli Umma a lokacin hawaye suka zubo mata tace, "Umma dan na kai wannan lokacin banyi aure ba ba hakan yana nufin zan auri dan shaye-shaye ba ko mai kama da haka, Umma taba fa yake sha a gaban idanuna ko kunya baya ji kuma sunan yazo gidan mu neman aure."

Tsaki Umma tayi tace, "Dan yana shan taba sai me? Baban ki ma da yasha taba kafin ya girma ya daina. Kina so kice min kawai kin kore shi ko?." Ta goge idanun ta tace, "Gwara na mutu babu auren Umma da dai na amince na auri irin su, bazan iya auren sa ba dan Allah ki fahimce ni. Duk sanda na gari yazo zan amince amma banda wannan."

Umma tace, "Yaushe zai zo? Mun jima Muna jira har yanzu bai zo ba meyasa baza ki amince da wanda yake hannu yanzu ba?."
"Bazan iya ba wallahi Umma, kiyi hak'uri."

Umma zatayi magana aka dakatar da ita cikin taushin murya mahaifinta yace, Rukayya kina da wanda kike so ne?." Jin muryar Baba ta ya saka ta d'ago ta girgiza kai alamun babu yace, "To haka kike so mu saka ki a gaba muna kallo babu aure Rukayya?, duk wanda yazo kice bakya so?."
"Baba duk wanda ake kawo min bana gari bane, in na amince nice zan shiga cikin wahala, nasan inda Kaga abinda wannan da naje yake yi da kanka zaka ce bazan aure shi ba" ta fad'a murya ta rawa sabida kukan da yaci karfin ta.

Baba ya sauke numfashi yace, "Allah ya kawo na garin, tashi kije." Kamar jira take ta tashi ta shiga dak'i k'anwar Zuhra ta tabi bayan ta, Umma ta kalli Baba tace, "Na gaji da halin Rukayya wallahi, kowa yazo tace bata so to wa take so?." Abba ya kalle ta yace, "Ki cigaba da yi mata addu'a kawai, Allah ya yanke mata da gaggawa" yana fad'a ya tashi ya fita zuciyar sa duk babu dadi, inda abinda yake so bai wuce yaga Rukayya tayi aure ba kanwar ta har haihuwa tayi ga wata an kusa biki itama.

Kuka Rukky take yi sosai tunda ta shiga d'aki dan bata san me zatayi ba, Zuhra taji tausayin ta sosai tace, "Kiyi hakuri Anty komai zai wuce." Kai kawai ta girgiza tana kin kuna a zuciyar, tabbas da tasan inda zata nemo aure da taje ta nemo shi tayi kodan ta huta da abinda ake mata a cikin gidan su.

^^^^^^

"Ai ya fad'a min wallahi da ni ya samu bazai k'ara aure ba, matar na tasa fa yace kawai hakuri yake da ita ba wani jin dadin ta yake ba" Asiya ta fad'a tana kallon kawar ta Safina cikin murmushi wanda yake nuni da farin cikin abinda yake furtawa.

Safina ta bata hannu suka tafa tace, "kice zaki walwala a gidan ita kuma zata zama yar kallo." Dariya tayi tace, "Bari kawai, shiyasa tun yanzu nake cika nake batsewa dan bana son ya samu wani nak'asu a jikina da uwar gidan sa zata zarce ni."
"Kin yi min daidai tawan, Gashi an cafarko wuyan dan banza" ta fad'a tana kama tsintsinyar hannun ta suka sake kwashewa da dariya.

Anty Fauziyya ce ta shigo tana fad'in, "ke in kuma tare da Safina bakya ji bakya gani, to iyayen Yusuf sunzo har sun koma." Ido ta zaro ta dafe kirji tace, "Dan girman Allah da gaske Anty?." Ta Harare ta tace, "Da gaske mana."
"Ya akayi to? An tsayar da lokacin?." Anty tayi dariya tace, "Ga Baban can yana neman kwafsa miki wai yace suje zai neme su."

Tsaye ta mik'e tace,"Kamar ya kenan?."
"Kamar yadda kika ji, Gashi can suna maganar da Umma" ta fad'a Tana fita sai kuwa Asiya tabi bayan ta a guje.

A kofar d'akin Umma ta tsaya taji muryar Umma na cewa, "Ban gane kace zaka neme su ba, akan me ba'a tsayar da ranar auren ba?." Baba yace, "Ina so nayi bincike a kan yaron ne sosai bana so a sake maimaita abinda akayi a lokacin auren Maimuna." Umma tace, "binciken me za'ayi to? Waye bai San iyayen yaron ba?."

Baba yace, "Maganar yaron ake bata iyayen sa ba, shi muke so mu san waye shi ba iyayen sa ba. An kawo min wani labari duk da ban tabbatar ba ance min yaron yana...." Umma tyi saurin dakatar dashi tace, "Yana me? Me akace yana yi, neman mata ko?. Kai Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ban San me na yiwa dangin ka ba da inda suka ga alkhairi ya tunkaro ni sai sun saka k'afa sun hamb'arar dashi. Daga ji yaron zai auri Asiya har an fara lallab'owa ana fad'a maka magana Mara dadi a Kansa kawai dan a raba su ko?."

Baba ya girgiza kai yace, "Wanda ya fad'a min bashi da alaqa da dangina, kuma bazai min 'karya dan son ransa ba."
"To wallahi tallahi ko yankan kai akace Yusuf yana yi babu abinda zai hana Asiya auren sa sai dai d'an bakin ciki ya mutu wallahi, babu damar aga arzuki yana kallona sai an samu wanda zai nuna min bak'in cikin sa k'arara dan kawai an tsane ni an tsani y'ay'ana?. Ka toshe kunen ka kome za'a zo a fad'a maka auren nan babu fashi wallahi."

Kallon ta kawai Baba yake har ta kai k'arshe sannan yace, "Baki ma tsaya kinji me akace min din a Kansa ba kina ta wannan kunfar bakin."
"Bana so naji, bana so wallahi. Kuma ba wani bincike da za'a tsaya yi yadda suka zo da kud'in aure da saka rana nan da sati takwas kayi musu waya kawai kace ka amince, akan wanne dalili zaka ce sai anyi wani bincike bayan kasan komai akan yaron. Bana son haka wallahi gwara ayi a gama a wuce wajan."

Baba yace, "In kuma abinda aka fad'a ya tabbata fa?." Umma tace, "Bazai ma tabbata ba, Kaga malam in baza ka Shege gaba akan auren nan ba wallahi sai naje na samu y'an uwana suyi komai a gama. Sai kece kana yiwa y'arka bak'in ciki....?, bayan in ta shiga gidan arzuki kaine ka shiga yawo da k'afar nan da kake watarana sai ka ganka da mota amma ka dinga fad'ar wannan maganar." Baba ya sauke numfashi yace, "Kwanciyar hankali nake so ta samu ba kud'i ba."
"To akwai kwanciyar hankalin da ya wuce kudi? Kai kanka da kana da kud'in ai baza ka tsaya ja in ja ba."
"To naji, amma wata biyu yayi kusa a barshi wata biyar kafin nan an samu abubuwan da za'a yi na kai mata d'aki."

Wata harara tayi masa tace, "Kai kake musu daman?, Ina ga ko pad baka tab'a bata ta siya ba komai ni nake mata ko?, to na shirya zan iya yi mata kayan gado koda guda goma ne, babu ruwan ka kawai a tsayar da ranar." Zuciyar Baba sam babu dad'i ,d'aci yake ji a zuciyar sa hakan ya saka shi yayi shiru baice komai ba. Umma ta kuma cewa, "Ka kira mahaifin nasa ka fada masa magana kayi jugum, 'karya na fad'a ne ko me?."

Baba yace, "Zan kira sai da safe yanzu dare ya riga yayi. Amma kafin nan inaso ki san duk abinda ya biyo baya a auren Asiya babu ruwana, Allah ya sani nayi abinda zan iya matsayina na mahaifinta." Umma tace, "babu abinda zai biyo baya ma sai alkhairi, a daina mana fata in sha allah sai dai y'an bak'in ciki su mutu."

Baba bai iya cewa komai ba ya tashi ya fita yana fita Asiya da Fauziyya suka shigo Asiya tace, "Umma me baban yace?."
"Ke rabu dashi, munafukai har sun fara zuga shi wai ayi bincike, babu abinda za'a bincika waye bai San uban yusuf ba?." Fauziyya tace, "Kinga Kawu D'anlami..?; Sam baya so yaga min cigaba a gidan nan, Kullum cikin tsine mana suke mune y'an duniya nasa kuma masu tarbiyya."

Umma tace, "Barni dasu ai nafi k'arfin su wallahi, daidai nake da k'ugun kowa a cikin su." Asiya tace, "Yanzu Umma an gama komai?." Umma tace, "Gobe zai kıra su ya sanar dasu nan da sati takwas za'ayi auren daman da haka suka zo. Sai ki fara shiri dan ko kwana daya bana so a k'ara." Fauziyya tace, "Umma babar Yusuf na samu labarin tana son uwar gidan sa fa sosai, kar ta bamu matsala nan gaba."

Umma taja tsaki tace, "dukkan su a tafin hannuna suke, dashi Yusuf din, da matar sa, da uwar sa, da kowa nasa sai nayi maganin su akan Asiya. Asiya bazata tab'a zama bora a gidan ba wallahi sai dai mowa, in muka ga uwar gidan zata kawo mana matsala cillata waje zamuyi. Ke bazan d'auki rainin da aka yi wa Maimuna bafa, wannan Karon shiri zanyi Asiya badai ta bar gidan Yusuf ba sai dai ita matar tasa ta bari."

Dariya sukayi dükkan su Fauziyya tace, "Allah ya bar mana Hajiiya Umma. Daman kuma ba wani son matar tasa yake sosai ba, kinga sai muyi amfani da wannan damar mu dama."
"Sakina tace yana son matar sa amma hakan bazai hana mu nasara a kan su ba, kudai ku zuba ido ai sai Asiya ta zamar musu ciwon ido, badai babar sa bata son auren nan.....hmm muje zuwa" ta fad'a tana tashi ta fita Asiya dad'i yayi mata yawa ta fita da sauri zuwa d'akin su dan tayi waya da habibin ta.




#Share
#vote
#Nana haleema
#F5

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

Masu nema daga farko ku danna wannan link din zaku samu.
https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36


*Book 1*
*Page 17*



Ameenatu kuwa tana zaune a falon ta k'asa Zaytun na cinyar ta tana wasa ita kuma rik'e take da waya tana dubawa sun gama waya da Yaya kenan tana sanar da ita sun jima da isa gida ita kuma tana saka mata godiya. Falon shiru sai sautin cartoon ake kallo akan tv da yake tashi kad'an-kad'an.

"Ina abincina?." A sama taji maganar hakan ya saka ta zabura ta juya tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta yana tsaye a bayan ta tace, "ban dafa ba sai dai in na dafa maka yanzu." Ido ya wara yace, "Baki dafa ba?." Tace, "Eh, In na dafa baka ci shiyasa ban dafa ba asarar sa ake."
"Ke kika kawo abincin?."
"Bani bace amma nice mai dafawar, in na dafa ya lalace na zubar nice nayi almazazzaranci."

"Hmmm kin kyauta” ya furta kawai ya bar wajan zai koma sama. Bata tashi ba balle tayi niyar dafawa ta d’auki Zaytu suka hau sama ta shiga d'akin ta dan bazata dafa ba sai dai duk abinda zaiyi yayi ta gaji itama da wulak’ancin da yake mata dan yaga tana yin hak’uri.

Yusuf yana shiga d'aki wayar sa ta fara k'ara ganin sunan My love ya saka shi katse kiran ya samu waje ya zauna sannan ya kira ta tana d'auka tace, "Shine Ina kiran ka baka d'auka ba ko?." Murmushi yayi yace, "na sauka k'asa yanzu na shigo."
"Kodai kana wajan Antyna ne?."
"Mtsww! Ki daina min maganar ta kar ki sake b'ata min rai."

Dad'i ya mamaye zuciyar Asiya ta sake kashe murya tace, "Kayi hakuri my love. Naji muryar ka wani iri baka da Lafiya ne?." Yusuf ya shafa kansa yace, "Yunwa nake ji kuma abincin ki kawai nake so naci" ya kalli agogon hannun da yace, "Gashi dare yayi har takwas ta kusa da nazo naci." Kamar yana gaban ta Asiya tayi farii da ido tace, "Dare baiyi ba my love zan girka maka, me kake so kaci?." Ya girgiza kai yace, "no bana so na wahalar dake."

"Babu wata wahala my love, zan girka maka yanzu me kake so?." Yayi murmushi yace, "Duk abinda kike so shi nake so, gani nan zan zo but take away zanyi."
"Ba matsala."
"Kinga sai mu tattauna yadda bikin mu zai kasance, ki fad'a min abubuwan da kike so ko?." Tayi dariya tace, "Sai kazo kawai." Shima murmushin yayi ya kashe wayar ya tashi ya d’auki key din mota ya sakko daga saman.

Yana sakkowa falon Ameena na saman ya ganta a tsaye a jikin fridge din falon tana shan ruwa ta saka rigar bacci gajeriya mai kyau sai khamshi take gabad'aya khamshin turaren ta ya cika falon, ga khamshin mai sanyi kana ji kasan night perfume ne. Rigar tabi jikin ta sosai halittar jikin ta ta bayyana komai ya fito rasss tana shan ruwa dan bata San ma ya sakko ba. Ido ya zuba mata kawai yana kallon ta yana jin wani abu na shiga jikin sa hakan ya saka shi kasa d'auke ido daga kanta.

A sannan ta juyo suka had'a ido sai ta d'auke kai kamar bata ganshi ba ta sake bud'e fridge d'in ta d'auki madara a jarka ta wuce shi zuwa d'akin ta. Numfashi ya sauke lokacin da ya daina ganin ta kamar yabi bayan ta sai kuma ya fasa ya sauka ya hau mota ya fita.

A bangaren Asiya tana sanar da Umma batun girkin nan da nan aka fara had'a masa farar taliya da miyar kwai, nan da nan aka gama tana kwashe miyar tana zubawa a pack na roba irin wanda in anci za'a yar ta shigo tace, "Mayar da miyar nan cikin tukunyar ki zuba wannan rubutun ki ya sake tafasa sai ki kwashe." Karb'a tayi ta kuma yi abinda tace sannan ta kwashe ta shiga dak'i tana shafe jikinta da turaren da Umma Sakina ta bata.

Tana gamawa yayi mata waya gashi ya k'araso ta d'auka ta fita ta hangi motar sa ta k'arasa ta bud’e bayan motar ta saka masa abincin sannan ta shiga gaban motar ta zauna tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta. Turaren ya shak'a ya lumshe ido Allah ya sani turaren ta yana bala'in kashe masa jiki kawai dauriya yake yi duk sanda suke tare.

"Barka da zuwa my love." Sai da yayi Ajiyar zuciya sannan yace, "Barkan ki dai my love, na baki aiki ko?." Ta rausayar da kai tace, "Haba wanne irin aiki kuma? Dan mata ta yiwa mijin ta abinda yake so shine aiki?." Murmushi yayi yana kallon ta itama haka yace, "Bana so Baba ya d'aga bikin nan my love." Ta jingina da kujera tace, "Bazai k'ara ba naji suna maganar da Umma."
"Har naji dad'i. Me kike so to?."
"Duk abinda yayi maka Ina so." Nan ma murmushi yayi yace, "Mayi maganar daga baya to, gobe za'a cigaba da aikin bangaren ki so nake nan da four weeks ayi a gama."

Farrr tayi da ido ta d'an zame mayafin t daga sama tace, "Allah ya Muna mana wannan ranar da rai da Lafiya my love. Baka zo min da Zaytun ba?" Ta fad'a tana sakin wayar ta da gangan ta fad'i wajan k’afar ta ta sunkuya dan rigar jikin ta ta zazzago ta d’auki wayar ta dago sai kuwa ta kama shi yana kallon kirjin ta. Suna had'a ido tayi kamar bata gane ba shi kuma ya lumshe ido ya bud'e yace, “Tayi bacci." Yadda yayi maganar sai da ta kalle shi domin kamar mai bacci haka ya furta maganar tace, "kaima da alama baccin kake ji, bara na k’yale ka kaje kaci abincin ka Kaji da madam."

Hannun ta ya riko yace, "karki tafi dan Allah, ke nake so kiji dani." Kamar bata fahimci yanayin sa ba tace, "Kamar ya kake nufi?." Murza yatsun ta yayi tare da yin shiru baice komai ba. Dariya take masa a zuciyarta dan tasan ta gama kama Yusuf ta ko Ina, mai kwace shi a hannun ta zai sha wahala.
"My love dare yanayi zan koma gida" ta fad'a a sanyaye tana kai hannunta fuskar sa.

A lokacin ya bud'e ido ya kalle ta ta d’auke hannun ta tace, "Zan tafi." Idon sa cikin nata yace, "Baza ki zauna dani ba?."
"Me zai hanani zama da kai my love?."
"Gashi kina guduna bayan kece silar komai." Iska ta wura masa tace, "Zanyi maganin komai sai nan da sati takwas" ta fad'a tana fita da sauri tana dariya ya bita da kallo har ta shiga gida.

Dakyar ya iya jawo motar sa ya dawo gıda ya d’auki abincin ya hau saman sa yaci badan ya masa dad'i sosai ba sai dan kawai yana ji a ransa in bai ci ba ranta zai b'aci. Bai cinye ba ya ajjiye ya jingina da kujera yana sauke numfashi, tuno Ameena yayi a yanayin d'azu tsigar jikin sa ta tashi sai kawai ya mik'e ya sakko zuwa dakin ta.

Ameena daman tunda taga kallon da yake mata tasan za'ayi haka bata shirya ba ita kuma hakan ya saka ta kulle k'ofar ta kuma yi alwashin koda ya buga bazata bud'e ba. Buga kofar taji yana yi yana fadin, "Ameena zo ki bud'e." Jin maganar sa sai tayi banza kamar bata jj shi ba ya sake kiran sunan ta ta sake yi masa banza amma zuciyar ta harbawa take yi karo na farko kenan da ya neme ta bata bashi had'in kai ba.

"Nasan kina jina baki bacci ba ki tashi ki bud'e" ya fad'a a fusace dan yasan idanun ta biyu raina masa hankali kawai take yi. Bata motsa ba balle ta tashi ya fusata sosai yaja tsaki ya bar k'ofar d'akin. Tana jin takun barin sa wajan ta sauke numfashi ta tashi zaune tana zare ido kamar Mara gaskiya, "Anya na kyauta kuwa?" Ta fad'a a bayyane tana jin babu dad’i a ranta dan Allah ya sani itama tana buk'atar mijin ta kawai wulakancin da yake mata ne bata so.

_ke sau nawa yana wulaqanta ki akan hakan, shi baiji bai kyauta ba sai ke._ zuciyarta ta fad'a mata sai tayi k'aramin tsaki ta tashi ta saka takalmin yawo a falon ta fita zuwa saman sa. Gaban ta har fad'uwa yake ta tura k'ofar ta hange shi a zaune ya saka abinda ta tsana a gaba yana cika kofi yana sha idanun sa har sun canja kala sunyi ja. Dummm taji wani abu ya mamaye mata zuciya nan take zuciyar ta take fad'a mata kece sila da kin amince dashi da ba'a yi haka ba. Da sauri ta k'arasa ta dauke kwalbar giyar tace, "Meyasa kake son shan wannan abun ne? A ganin ka Itace zata kawar maka da b'acin ranka?."

Cikin muryar mai kaushi yace, "Bani kayata ki fita ki bani waje." ‘Kin bashi tayi tace, "Bazan bayar ba wallahi, na gaji da ganin kana sab'awa Allah, Ammah zan fad’awa ko ita in ta maka fad'a zaka ji. Da ba halin ka bane ya akayi ka koyo wannan banzar dabi’ar?.” Tasowa yayi yana kallon ta da idanun sa da suka yi ja yana nuna kansa yace, "Ni kika wulaqanta ko?." Baya tayi yana binta ya juya ya kalli belt din da take kan gado wacce ya cire kayan jikin sa ya d'auka ya nannad'e ta da hannun sa tana baya yana binta tana girgiza kai dan bata shirya shan dukan da ya sba yi mata ba a duk lokacin da yake wannan yanayin.

Zata gudu kenan ya kamo ta kwalbar ta fad'i da yake tana da kwari bata fashe ba ya fara sauke mata belt din nan a gadon bayan ta kamar Allah ya aiko shi cikin fitar hankali. Kuka take tana ja baya a zaune yana sake binta yana duka yana fad'in,

Please Login or Register in order to submit comment