Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aike ki gidan Anty Salamatu" ta fad'a tana zama a kusa da ita ta kuma cewa, "mun yanke shawara zamu had'a ki da Lawan na wajan ta ayi auren nan a rufawa juna asiri, ke kina zaune ba miji babu wanda yake zuwa yana cewa ana sallama ballantana mu saka rai gwara ayi auren nan kowa ya huta kema ki huta."

Hawaye ya sakko mata sharrr ta share tana kallon gefe tace, "Umma yanzu kin amince na auri Lawal? Matan sa uku fa, kuma kin san mata uku ya saki."
"Dan matan sa uku sai me? Har ke ba hud'u ba kenan, ko haram ne dan ya k'ara ta hud'u?. Shi kuma saki ba zuwa yake ba?."
"Amma Umma da kanki kike cewa bai tsarewa gidan sa komai ba sabida bashi da sana'ar kirki amma kike cewa na aure shi?."
"Nufin ki kinfi k'arfin sa kenan?."

Yadda Umman take kallon ta ya saka ta sauke idanu k'asa tace, "Ba haka bane Umma, amma bana fatan irin wannan auren Allah ya sani." Umma tayi tsaki tace, "Ya zama dole ki amince da auren Lawal domin na gaji da ganin ki a gabana muna had'a kafad'a nida ke da k'anwar ki, in kina zaune ita kanwar ki waye zai kula sta har tayi auren?, ko so kike yadda kike zauna kika dankare a gida itama ta zauna?."

Rukayya tace, "Umma ai aure nufi ne na Allah" ta fad'a tana fashewa da kuka. Umma tace, "na fiki sanin nufi ne na Allah amma akwai niya, sai kin saka a zuciyar ki kin kuma amshi wanda yazo miki sannan zai nufa ki tashi. Ke Rukayya! Bana son wannan ranin hankalin, kowa yazo kice bai miki ba wa kike so yazo inda kike? A gida kike so ki gama tsofewa?."

Rukayya bata ce komai ba sai kuka da take yi Umma ta nuna ta da yatsa tace, "Ko bakya so sai kin amince da auren Lawal domin na gaji da ganin ki a gaban idanuna, naji da k'annen ki ma da suke tasowa ke zaman gida ba naki bane. Duka k'awayen naki su wacece bata da miji? Dukkan su yara ne dasu amma ke an samu Lawal din ma ya amince kice wai ke ga zance ga magana. Ga kanwar ki Sajida haihuwa ta biyu take niyar ki ke kina gida. To wallahi na gaji kinji na fad'a miki" tana fad'a ta fita ta barta sai mita yake yi.

Rukayya tabi Umma da kallo tana kuka zuciyar ta nayi mata mugun zafi, k'anwar ta Zuhra ce ta shigo ta k'araso kusa da ita tace, "nikam da zaki ji shawara ta da kin amince da auren Lawal d'in tunda dai babu wani bayan shi."
Rukayya ta kalli Zuhra tace, "Zuhra meyasa kika raina ni ne kwana biyu?." Ta tab'e baki tace, "Gaskiya nake fad'a miki fa, babu wanda yake zuwa inda kike meyasa baza ki....."

Saukar marin da taji ya hanata k'arasawa zuhra ta zaro ido tana kallon Rukayya cikin mamaki itama kuma kallon ta take cikin zallar b'acin rai da k'unar zuciya tace, "Kar ki sake saka min baki a cikin lamarina, ni ba sa'ar ki bace bana son rashin kunya."
"Dan na fad'i gaskiya kawai sai ki mare ni!? Karya nayi, naga ai babu wanda yake zuwa inda kike d'in baki tab'a yin saurayi ba. Wallahi kar ki sake marina dan in aka sake bazan k'yale ba!" Ta fad'a cikin ihuu tana kallon ta.

Rukayya kallon take yi cikin k'unar zuciya tace, "Zuhra dake ni."
"Bazan dake ki ba amma wallahi karki sake marina."
"Malamai lafiya nake jin ihun ku da safiyar nan?" Umma ta fad'a tana shigowa tana kallon su.

Rukayya tace, "Umma ki mata magana babu ruwanta da lamarina, bana son rashin kunya dan taga ina kyale ta." Umma ta kalli Zuhra tace, "Malama bata haƙuri." Zuhra kamar zatayi kuka ta bata haƙuri tana fita daga d'akin.

Umma ta kalle ta tace, "Tana ganin ku kai d'aya ku kwana waje d'aya ku tashi waje d'aya, ki saka braziya itama ta saka, ki saka pad itama ta saka to me zaki nuna mata?. Aure ne zai banbanta ku amma kin ki har kina da bakin cemin Lawal bai dace dake ba sai kace in an Baki dama ki kawo wanda ya dace dake d'in zaki samo, samarin da baki yi ba tun kina y'ar sha takwas zuwa ashirin yanzu da kika tafi talatin ai baza kiyi su ba. Dole ki amince da duk wanda yazo wallahi na gaji da ganin ki a gidan nan" ta fad'a tana fita daga d'akin ta bar Rukayya a tsaye tana kuka.

A fusace ta k'arasa wajan kaya ta saka tana kuka ta saka dogon hijjabi ta d'auki kud'in ta da suke cikin kayan ta ta fita daga gidan da ji take zuciyar ta na mugun tafasa in ta zauna a gidan zata iya fashewa gwara ta fita kawai daga gidan.


#Vote
#Share
#Comments
#F5
#Book1
#Nana Haleema

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 10

Da ciwon kai ta farka mai zafi hakan ya saka tunda tayi wanka take zaune Zaitun tana ta wasan ta ta d’auko wannan ta d’aiko wancan yana ta magana ita kad’ai, ko gyaran d'akin ta kasa sabida yadda take jin kanta na ciwo sosai kamar zai rabe biyu. Buɗe k'ofar d'akin taji anyi hakan ya saka ta juyo ta kalle shi ya k'araso yana kallon ta tare da fad'in, "My choice lafiya kike?" Ya fad'a yana tab'a wuyan ta yaji zafi ya kalle ta ya kuma cewa, "Jikin ki akwai zafi my choice, me yake damun ki haka?."

"Kaina ne yake min ciwo" ta furta a sanyaye hannunta dafe da kanta.
"Tun yaushe kan yake ciwo?."
"Safe" ta bashi amsa a tak'aice tana sake dafe kanta.
"Kin sha magani kuma?."

Zatayi magana wayar sa ta fara k'ara ya juya screen d'in my love ya bayyana a jiki ya kalle ta yaga ta gani sai ya danna power d'in wayar screen d'in ya d'auke ya basar kamar bashi ba yace, "Bara na kawo miki magani kisha bakya zauna da ciwo ba" ya fad'a yana tashi ya k'arasa inda drawer take ya d'auko magani ya buɗe k'aramin fridge d'in d'akin ya d'auko ruwa ya kawo mata.

Karb'ar tablet din tayi ta damke a hannunta amma bata sha ba ya kalle ta yace, "Kisha mana." Shiru tayi bata ce komai ba sannan bata sha ba ya sauke numfashi ya tsuguna a gabanta yace, "Tun farko na fad'a miki in maganar nan zata haifar miki da damuwa a barshi amma kika k’i gashi yanzu hakan yana jawo miki matsala."

Ruwan da ya bata tasha amma bata ce komai ba ta kalle shi sai tayi murmushin takaici ta cize bakin ta ganin hakan sai yasha jinin jikin sa dan ya kasa fahimtar me murmushi yake nufi ya kuma tabbatar da wata manufa tayi ya kalli agogon hannun sa yace, "Kisha maganin mana my choice."
"Basai nasha ba." Mik'ewa tsaye yayi yana kallon agogo yace, "Ana jirana an office ina da bak'i na gaggawa, Kisha magani pls" ya fad'a yana dafa kanta kafin ya d’auke hannun sa ya fit.

Da kallo ta bishi har ya b'ace ta sauke numfashi ta koma da baya ta kwanta tana jan numfashi kanta na harbawa sosai kirjin ta na duka kamar ana buga ganga. Hawaye taji suna sakko mata daga idanunta tuna sunan da ta gani akan wayar sa yana yawo ta lumshe ido zuciyarta na cigaba da bugawa kamar zata fito, zuciyar ta n sake tabbatar mata da wautar da ta aikata na goyan bayan auren sa.

Damuwa tayi mata yawa dalilin da ya haifar da ciwon kan kenan zuciyar ta zafi take sosai ji take kamar zata fashe, ta tabbata aka auna bp din ta ya hau a lokacin sabida damuwar ba k’arama bace. Tashi tayi zaune ta saka maganin a baki ta d'auki ruwan tasha ta koma ta kwanta tana jan numfashin ta zuciyar na nayi mata d'aci.

Rufe ido tayi abubuwan da suka faru suna dawowa mata cikin kanta, tarin soyayyar da yake nuna mata tana cigaba da bayyana a idanunta kamar a lokacin da hakan yake faruwa. A hankali ciwon kan yake sauka tana jin dad'in kan har lokacin idanunta yana kulle amma yadda jijiyoyin kan suke harbawa yana raguwa sosai.

"Meena lafiya kike dai?." Jin muryar wacce batayi zato ba ya saka ta buɗe ido ta kalli bakin k'ofar ganin Rukky ya saka ta tashi zaune ita kuma tayi saurin k'arasowa ta rik'e ta tana fad'in, "Meena yadai?." A kafad'arta ta kwantar da kanta kawai sai ta fashe da kuka mai ciwo dan bata da wanda zata kwanta a kafadar sa tayi kika a kusa da ita.

Hankalin Rukky ya tashi jin yadda jikinta yayi zafi sosai tace, "Subahanallah! Meena jikin ki yayi zafi sosai, kodai muje asibiti?." Kai take girgiza mata alamun a'a tayi shiru tana sauraron kukan nata tana ta bata hakuri kafin ta sassauta kukan ta mik’e tana goge idanunta.

Rukky tace, "Meena me yake damun ki haka?." Kai ta girgiza kafin ta kalli Rukky taga itama fuskar ta tayi ja ga alamun damuwa ya bayyana a tare da ita tace, "Rukky lafiya kike?."
"Ke zaki fara fad'a min abinda yake damun ki Meena, kin rame sosai fa sai haske da kika sake yi. Ko dai ciki ne dake?."

Murmushin takaici tayi tana jin kanta na harbawa sabida kukan da tayi ta kalli Rukayya tace, “ki fara sanar dani damuwar ki, dan ni babu abinda yake damuna Ruky kawai ki fad’a ke meye yake damun ki?." Rukyya ta sauke ajiyar zuciya tana kallon ta tace, "Ban yarda babu komai ba kawai baza ki fad'a min bane, ko meye Allah ya kawo miki sauk'i, in kuma ciki ne Allah ya raba ku lafiya."

Shiru tayi batayi magana ba Rukky tace, "Meena na gaji." Jin yadda muryar ta tayi rawa wajan furta ta gajin ya saka Ameena sake fuskantar ta duk da ciwon da take ji a kanta amma haka ta daure ta tattara hankalin ta ga Rukkyn murya a dashe irin ta wacce tyi kuka tace, "Me ya faru?."

"Umma dasu Zuhra suna neman saka min hawan jini Meena, shin wai nice ban bawa kaina mijin aure ba?” Ta fad'a idanunta na taruwa da hawaye. Ameena ta girgiza kai alamun a'a kafin Rukky tace, "Har abin ya kai Umma tace nac na auri dan yayar ta Lawal bayan ta shaida yana shaye-shaye ga auri saki gashi babu wata Sana’a mai k’arfi, nayi magana Umma tace in bashi ba waye zai aure ni....?. Meena yau Zuhra ni ta kalla ta cewa wai wankan janaba nayi....Take kallon idona wai na gishe da Sajida Wai in na girme ta a shekaru ai yanzu Yayata ce tunda tayi aure ta haihu ni banyi ba, a gaban Umma kuma take fad’a fa. Meena zuciyata zata iya fashewa, bak'in cikin da nake shak'a a gidan mu ya ishe ni...wallahi ya ishe ni Ameena!" ta fad'a tana fahewa da sabon kuka.

Ameena ta sauke ajiyar zuciya tana gigira kai zuciyar ta na fad'a mata wato kowa ka gani ka sake kallon sa kawai kar kace komai akan lamuran sa domin baka san abinda yake zuciyar sa ba domin mai d'aki ne kawai yasan inda yake zuba, "Rukky ki daina kuka dan Allah, zubar hawayen ki ba shine zai kawo mijin ba ai ko?." Fuskar ta tayi kaca-kaca da hawaye ta d'ago tace, "Ya zanyi Meena? Baba ya hanani cigaba da a karatu tun bayan na kammala diploma, ya hanani aiki yace sai nayi aure bayan na samu aikin amma ya hana. Gashi ba auren ba karatun kuma babu aikin, dame ake so naji....? Zuhra ni take kallo tana cewa zata daka in na sake dukan ta, Zuhra fa Meena k’anwata ta biyu, a shekaru na bata shekaru kusan biyar amma ni take fad’awa wannan maganar Ameena!” ta fad'a tana sake fashewa da kuka sosai.

Tausayin ta Ameena take ji sosai a zuciyar ta ta rik’e, ita da tayi auren ba jin dad’i take ba ga wacce bata yi yi auren bama ga halin da take ciki, hannun ta ta rike tace, "Komai lokaci ne Rukky, aure da mutuwa wa da k'ani ne, yadda baza ka mutu lokacin ka baiyi ba haka baza kayi aure lokacin ka baiyi ba. Wannan zubar da hawayen da dukkan abubuwan da kika ce suna faruwa wallahil azim in lokacin auren ki baiyi ba bazaki ba, haka Allah ya tsara miki rayuwar ki kiyi addu'a Allah yasa hakan alkhairi ne a tare dake."

Rukky tace, "Meena da gaske na damu gani nake kamar Allah baya amsa addu'ar da nake yi ba dare babu rana."
"Haba Rukky! wannan wacce irin magana kike yi?."
"To Meena kullum sai na rik'i Allah amma abin shiru, da bana jin wani abun yana damuna amma yanzu ina jin sha'awar kasancewa da namiji Meena, bana so wannan yanayin ya saka na fad'a halaka.”

Ameena ta dafa kafad’arta tace, "Babu abinda zai faru in sha Allah. Ki ta addu'a kina neman tsari daga shaid'an kina kuma fatan Allah ya rabaki daga sharrin zuciya. Wallahi indai kina da rai Allah ya rubuta zaki aure mijin ki yana nan yana bulayin neman ki, akwai k'addarar da zata gifta ku had'u dake dashi kiga anyi komai an gama kamar komai bai faru ba. Ko wacce mace da mijin ta a duniya, babu wacce zata auri mijin da bashi Allah ya bata ba, yana nan zuwa a gare ki wallahi ki kwantar da hankalin ki ki kuma mayar da lamarin ki a gare shi komai zai wuce wallahi. In kina fadar wannan kalaman ashe baki k’arbi k’adarar ba, ai jurewa zaki yi ki ta maimaita addu’ar baki Allah yana son mai naci wanda baya gajiya da rok’on sa.”

Rukky ta share hawaye tace, "Haka ne Ameena. Amma da an barni karatun ko aikin da hakan zai rage min wata damuwar ko?." Ameena tace, "Haka ne, amma dai kiyi haƙuri da abinda Allah ya tsara miki, ki kuma karb'i maganar Baba tunda haka yake so ki kwantar da hankalin ki domin kuwa Allah ne yasan shirin da yayi miki. Allah yasa jinkirin alkhairi ne a gare ki yasa kiga ribar haƙuri, yasa kice gwara da Allah ya jinkirta min.”

Ta amsa da amin tana share hawayen ta dan sosai Meena ta kwantar mata da hankali kafin Meena ta kuma cewa, "Wata ran haka zamu tuna wannan ranar dake muyi dariya mu tafa wataƙila lokacin ma da d'anki ko y'arki." Murmushi tayi tace, "Allah ya tabbatar Meena. Amma nima ina son auren Allah ya sani, ina fad'awa Allah nasan yana ji kuma yana gani zai min magani.”

"Kina kai kukan ki ga mai bayarwa da hanawa kin kama dahir a raywuar ki tunda kika rik'e Allah." Murmushi Rukky tayi kafin tace, "Nifa ko Umman bata san ma na fito ba tsabar b'acin rai, amma yanzu sai nake ji kin rage kaso mai tsoka daga cikin abinda yake damuna. Ina sonki Meenatuwan Yusuf." A tare sukayi k'aramar dariya Ameena tace, "Kema dai dan Allah ki daina shiga shirgin su Zuhra, ki dinga kawar da kai daga lamarin su in ba haka ba wallahi wata ran zakuyi fito na fito dasu. Bafa wai dan sun raina ki bane kawai zmaan tare ne ya kawo hakan, amma in kika tafi d'akin mijin ki har marmarin zuwa ma inda kike zasuyi."

Rukky ta girgiza kai cikin gamsuwa tace, "In sha Allah. Amma d'azu naji haushi gaskiya, ga Umma ma da ta shigo taga na sake yin wankan na wanke kaina shikenan sai tace wai maganar zuhra gaskiya ce. Kuma fa period d'ina ne ya d'auke shine dalilin wankan amma suka fassara ni da wani abun daban."
"Kiyi hak'uri dai wata rana sai labari, Umma da take miki haka ba dan bata sonki bane soyayyar ce ta jawo haka” Ameena ta fad'a tana kallon ta da murmushi itama tayi murmushin ta rik'e hannunta tace, "Allah ya barki da mijin ki k'awata. Ki fad'a min me yake damun ki dan Allah."


Ameena tayi murmushi tace, "ki taya ni da addu'a kawai Rukky, amma ina cikin damuwa sosai."
"Shikenan k'awata Allah ya yaye miki duk abinda yake damun ki, duk da dai nasan Yusuf baya barin ki da damuwa tun kafin aure ina kuma ga bayan aure..?." Murmushi tayi kawai bata ce komai ba kafin kuma ta tashi tsaye tana dafe kai tace, "yau fa ko k'asa ban sauka ba balle nayi breakfast, zo muje ki samu abinda zamu ci."

Rukky ta tashi tana fad'in, "Shiyasa naga masu aikin ki a k'asa suka ce baki sakko ba kina nan shine kawai na tawo nan d'in. Amma jikin ki fa da zafi ya kamata yayi kisha magani ki kuma huta." Tayi dariya tace, "To k'aramar nurse naji zanyi" ta fad'a tana fita daga d'akin itama tabi bayan ta tana dariya.


*☆☆☆*

"Umma! Umma!! Umma!!!" Ta fad'a da k'arfi tana fitowa daga d'aki jikin ta na rawa fuskar ta a washe sabida farin ciki sai tsuma take tana k’aramin tsalle. Umma da take zaune ita da Umma Sakina suna tattaunawa ta kalle ta tace, "Malama lafiya wannan kira kamar kina bina bashi?."

Ta zauna kusa da Umman tace, "Umma tun jiya fa Yusuf ya kirani yake cemin Iyayen sa sun amince da auren mu, na dauka wasa yake sai yau ya sake tabbatar min da nan kusa za'a zo nema masa ni" ta fad'a tana rufe idanunta da hannayen ta.

Umma ta kalli Umma Sakina da take zaune sukayi dariya a tare suka tafa Umma sakina tace, "Daina rufe fuska Asiya bud’e fuska ai bamu fara komai ba." Ba musu ta buɗe fuskar ta tana kallon ta itama haka tace, "Wanne irin farin ciki kike ji a ranki?."
"Wallahi Umma Sakinah ban san adadin sa ba."
"To in kace yau an kawo kud'i ko an saka rana wanne iri zaki ji kenan?."

Asiya tayi farr da ido tana sauke ajiyar zuciya alamun bata san ma adadin sa ba Umma Sakina tace, "Nasan baki san ya zaki ji ba, dan haka sai mun sake dagewa domin na saka an nemo min komai a kan matar sa an tabbatar min da tabbas yana sonta, kuma babu abinda kika fita domin fara ce irin tass d'in nan gata yarinya duk da zata girme ki. Dole mu dage mu disashe wnanan soyayyar da yake mata mu haskaka taki domin mu a dangin mu bama zama bora ko ya kika ce k'awata?" Ta fad'a tana kallon Umma.

Umma tace, "Wannan haka yake, da naga ranar da y'ata zata zama bora ai gwara na mutu." Umma Sakina tace, "To sai mun sake zage dantse wajan sake kamo shi a hannun mu, kinga abinda mukayi an samu nasara har iyayen nasa ma sun amince, to ba iya shi ba har iyayen nasa sai sun dawo hannun mu dan bama so a samu matsala ne ko kad'an."

Umma tace, "Kamar kin shiga raina, kinga y'an unguwar nan munafukai ne, na tabbata kuma za'a zo bincike akan Asiya da gidan nan tsaf zasu iya kore su dan ba k'aunata suke yi ba nida y'ay'ana."
Umma Sakina tace, "Zamuyi maganin wannan ma ai, tunda Yusuf ya shigo hannu ai wallahi bazai fita ba sai ya aure ta tunda ya riga ya furta bai isa ya guje ba" ta fad'a tana d'aukar jakar ta ta d'auko katon jan goro da ruwan rubutu a jarka ta mik'awa Asiya tace, "Saka goron a bakin ki gabad'aya ki tauna shi ki tara a bakin ki kar ki cinye sai ki kora da wnanan ruwan maganin ki had'd'iye."

Karb'a Asiya tayi tana kallon Goron ganin yarda rubutu a jiki Umma sakina tace, "Me kika fahimta an rubutu a jiki?." Asiya ta kalla sosai tace, "ajami ne bana gane shi sosai, amma dai naga an saka Yusuf."
"Kedai tauna, yadda zaki taune goron ki had'd'iye haka zaki taune zuciyar sa ki had'd'iye ta kece kawai zaki sarrafa ta."

Ba musu Asiya ta saka goron a baki tayi yadda tace duk da bata jin dad'in sa amma tunda akace zata mallake Yusuf take taune shi ta sha ruwan ta had'd'iye. Umma da take gefe tace, "Kenan yana son matar sa ko Sakina?."
Umma Sakina ta kalli Umma tace, "Wai tunanin ki kema irin na yaran ne dan yazo neman aure dan bai jima da yi ba hakan yana nufin baya son matar sane?." Umma tace, "A'a, kawai dai na d'auka akwai wani abun ne da ya saka shi hakan tunda naga bai jima da aure ba yaga Asiyan."
"Kin manta ranar mai na bawa Asiyan ta saka a idanunta? Kwallin farin jini ne da dak'yar ka shafa shi ka fita ka dawo ba'a ce ana sonka ba, a ranar suka had'u dashi kuma sanin kanki ne koda ace da wasa yazo tunda ya riga ya kawo kansa bai isa ya koma ba."

Umma tace, "Haka ne kuma." Asiya tace, "Amma Umma Sakina yace min da ni ya fara samu bazai kara aure ba, matar sa wai sam bata iya abubuwan da yake so ba." Umma Sakina tayi dariya tace, "K'arya yake munafuki ne, namiji ne fa, hmmm....ke baki san in namiji yana son ya mallaki abu ba duk yadda zaiyi sai yayi wajan ganin ya samu ba?, musamman ma ace mace ce zai ta amfani da kalaman da zai saka kiji kece ta farko a zuciyar sa amma wallahi k'arya yake matar sa itace gaba domin abu na farko akwai tsayawa a zuciya. Yana fad'a miki haka ne dan kiji dad'i amma maganar gaskiya matar sa babu ta inda kika fita sai dai ta fiki, auren ki da zaiyi dan bai jima d aure ba ba hakan yana nufin wai ta gaza bane, kawai mun riga min kama shi ne bai isa ya gudu ba kuma yana son naki da gaske ba wasa ba, batun wai bata iya kaza ba k'arya yake yi kedai kawai ki jira ayi auren."

Asiya sai jikin ta yayi sanyi gabad’aya ba haka take so ba so take ace yafi sonta akan matar tasa dan wallahi in akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce matar Yusuf ba, burin ta kawai ace ta fita daga gidan ba ta bar mata shi ita kad’ai. ganin yadda jikin ta yayi sanyi sai Umma Sakina tace, "Kar ki damu fa wallahi sai munyi maganin sa shida matar tasa, ki bari ki shiga gidan wallahi in batayi wasa ba sai ta gudu da k'afarta ta bar miki gidan. Ta fiki kyau da haske ke kuma ki fita a zuciyar mijin, kina dani fa kar ki damu Asiya Ina tabbatar miki da sai Mun fitar da Ameena da zarar kin auri Yusuf.”

Sai a sannan tayi dariya tace, "Har anji dad'i Umma Sakina. Wallahi na tsani matar nan tasa ki kusa bana son ta.” Uamma Sakina ta sake saka hannu a jaka ta d'auko leda bak'a ta mik'a mata tace, "Ki saka a fridge kar ta lalace. Zuciyar akuya ce aka jika ta da ruwan magani duk ranar da zai zo kiyi masa y'ar Miya mai kyau da dad'i ki kai masa, amma fa ko a gidan nan kar wanda ya sake ya saka miyar a bakin sa dan ta mallaka ce duk wanda yaci shi ya jiyo" ta k'arasa fad'a tana dariya.

Umma tace, "waye ya isa yaci? Maza jeki ki ajjiye bana so a shigo kin san mutane da magana." Ba musu ta tashi ta saka a cikin fridge d'in tana ji a zuciyar ta dole ma tafi Amina a wajan sa domin bata son zama a k'asan uwar gida tafi so uwar gida ta kasance a k'asan ta, yadda Umman ta take juya Baba haka take so itama ta juya mijin ta dan hakan yana burge ta matuk'a yana sakata farin ciki ta kuma yi d'anmarar sakawa Yusuf ya dawo haka kota wanne hali.


#Book1
#Nana Haleema

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*


*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki

Please Login or Register in order to submit comment