Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hawayen da ya zubo mata a fuskar ta. A bayyane tace, “Ko da gaske bashi da hankalin?.” Sai kuma ta girgiza kai tace, “yana sane duk abinda yake yi.” K’ofar falon ta taji ana bugawa ta tashi dakyar ta fita ta bud’e, Zakiyya ta gani da Fiddausi a tsaye ta saki fara’a nan take fuskar ta ta canja zuwa farin ciki suma haka ta rungume Zakiyya da take a gaba tace, “Kamar Kun San ku nake jira kawai.” Sakin ta Zakiyya tayi ta rungume Fiddausi ta sake ta Fiddausi tace, “amma jikin ki da zafi fa Meena, Lafiya kike?.”

Ta sauke numfashi tace, “ku Bari kawai, da Zazzabi yau na tashi wallahi. Ku shigo mana” ya fad’a tana komawa baya suka shigo suka zauna itama ta zauna Zakiyya tace, “Ko dai an samarwa da Zaytun k’ani ne?” Ta fad’a tana kashe mata ido cikin shaqiyanci. Murmushi tayi tace, “Ni y’ar gidan ciki, jaririyar y’ata nayi yaya da ita?. Gasu Fiddausin nan ma sun k’i balle ni.”

Dariya sukayi a tare Meena tace, “Ina Rukky kuma?.” Zakiyya tace, “Daman Mun yi da ita zata same mu a nan.”
“To Ina kuka baro Fahad da Amir din?.”
Fiddausi tace, “Amir yana gidan Hajiyan Ibrahim, Fahad kuma ta barshi a gidan Maman su.” Amina tace, “Kuna abinda kuke so wallahi.”

Zakiyya tace, “Kema haka ai, amma kin rame fa Meena.” Ameena tace, “Haka ake cewa ni kuma bana gani wallahi” ta fad’a tana tashi ta d’auko ruwa da lemo a fridge ta ajjiye musu ya kuma cewa, “Me zamu girka ne?.”

Fiddausi tace, “Kaji zaki girka mana wallahi, daman an jima ba’a had’u ba.” Tayi dariya tace, “Fidyn Ibrahim wallahi baza ki canja ba.” Zakiyya da taje shan ruwa tace, “to mu koma falo k’asan mana sabida yafi mana sauk’in shiga kitchen din.”Ameena ta mik’e tace, “Bara na d’auko Zaytun.”

Da sauri Fiddausi ta riga ta yin hanyar d’akin tace, “Keda baki da Lafiya, zauna na dauko ta” ta fad’a Tana shiga dakin. Zaytun din ta d’auko ta tsaya tana k’arewa dakin kallo tana girgiza kai had’i da murmushi tace, “Nima na kusa shigowa wannan level din”. Tare suka sauka bayan ta fito suna zama a falon Rukayya na shigowa.

Tare suka zauna aka fara hira kafin Ameena ta dafe kai tana yatsine fuska alamun kanta na ciwo ta mik’e tace, “Bamu d’ora komai bafa.” Fiddausi tace, “yi zaman ki bara na dafa mana.” Amina ta koma ta zauna tace, “Da kin taimaka.” Kitchen din Fiddausi ta shiga ta barsu a zaune.

Nan da nan ta had’a musu girki lafiyaye yaji nama dan ganin arha ma kaji da nama ta had’a waje d’aya ta zubo musu gabadaya a tray suka zauna Suna ci duk da ba ci Ameena take yi ba. Bayan sun gama ne aka d’auke kwanon aka kai kitche suka dawo suka zauna aka cigaba da hira. Zakiyya tace, “Ameena sai muka samu labarin aure, wai da gaske ne Yusuf aure zai yi?.”Ameena tayi murmushi nan da nan hawaye ya cika idanun ta suka sakko ta share tace, “Eh da gaske ne Zakiyya, an tsayar da rana saura sati takwa. Baku ga sabon gini ake bama?.”

Rukayya tace, “Innalillahi wa’inna ilahiri raji’un, dama Yusuf zai iya yi miki kishiya?.”Kai take girgizawa kafin tace, “Gashi kina gani ma Rukky, kad’an daga aikin namiji kenan.” Zakiyya tace, “Amma meyasa baki fad’a mana ba?.”
“Ban San ta inda zan fara bane ba Kiyya shiyasa kawai nayi shiru.”

“Shirun shine yake cutar dake kike ramewa haka” Fiddausi ta fad’a tana kallon ta. Ta kalli Fiddausi tace, “Kin San wannan dole ne kawai ku taya ni da addu’a itace kawai mafita a wajena.” Kafin wata ta kuma magana aka bud’e k’ofar falon aka shigo duk suka kalli mai shigowar. Yusuf ne ya shigo cikin manyan kaya yayi kyau sosai yana amsa waya, ganin su sai ya ja burki ya tsaya ya sauke wayar daga kunnen sa yayi murmushi yace, “lallai yau akwai manyan b’aki a gidan nan.”

Zakiyya ta kalle shi tace,” Dole kace manyan bak’i mana zaka daukowa y’ar uwar mu kishiya, wallahi ni da naji labarin ma na d’auka mafarki nake yi, wai Yusuf din Ameena dana sani.” Murmushi ya sake yi yace, “Kina taya ta kishi kenan?.” Fiddausi ta amshe tace, “Kaima kasan ai dole ne wannan.” Fuska a sake ya sake cewa, “Ya za’ayi da abinda Allah ya tsara babu Wanda zai canja ai ko?.” Rukayya tace, “Haka ne, amma kasan akwai ciwo ko? Kuma da niyar hakan .”

Kawar da maganar yayi bayan yayi y’ar dariya daman yasan in suka had’u wata sai tayi masa ciwon baki akan lamarin yace, “Na jima ban ganku gabadayan ku haka ba. Gwara ma da kuka zo ku taya ni tambayar ta gabadaya tak’i bani amsa.” Kafin suyi magana ya sake cewa, “Batu ne akan kud’in da zan bata ko kaya kodai duk abinda take so tace ita wai bata so, ni kuma bazan amince da hakan ba amma ta dage akan wai ita bata so. Ku taya ta zab’a ko nawa tace tana so ko me tace tana so zan mata.”

Fiddausi ta gyara zama dan dadi take ji tana hira da mai kud’i tace, “Kasan duk abinda zaka bata bazai siyi kishin ka da take ji a zuciyar ta ba.” Kai ya d’aga yace, “Na san da wannan Fiddausi, amma in bata karb’a ba kamar ban mata adalci ba.” Rukky tace, “Haka ne. Kar ka damu zamu rarrashe ta amma sai a hankali gaskiya wallahi, dan ni Allah ya sani ma haushin ka nake ji a raina.”

‘Yar karamar dariya yayi yace, “Allah ko Rukayya? To ayi hakuri, tuba nake. In kina cewa haka sai ki saka yau a hana ni shigowa” ya fad’a yana kallon Ameena. Ameenatu dai kallon sa take yi kawai tana mamaki dan yanzu tsoro ma yake bata yadda yake canjawa da zarar yaga bak’i sai ya koma mata Yusuf din da ta sani a baya da zarar bak’i sun tafi kuma sai duka da tsawa da cin mutunci.

Ganin kallon da take masa ya saka shi kallon ta shima duk da haka bata d’auke ido ba ya tab’a wuyan ya yaji zafi yace, “Har yanzu zazzabin bai sauka ba?.” Nan ma bata daina kallon ba ba kuma tace komai ba yace, “Dan Allah ki kwantar da hankali damuwar nan taki na saka naji kamar nayi kuka wallahi.” Bata san lokacin da murmshin mamaki ya bayyana akan fuskar ta ba ta girgiza kai ta d’auke kai daga kallon sa, lallai Yusuf tsaf zai iya acting dan ya iya salo Kala-kala.
Barın wajan yayi ya hau sama Rukayya tayi ‘karamin tsaki tace, “Kulawar banza da wofi ana neman kawo maka wata.”

Zakiyya tace, “Namiji kenan, yanzu Tsakani da Allah waye zai ce Yusuf zai iya yiwa Ameena kishiya?. Ko da yake ita da sauk’i ma fa da yana kula da ita duk da aure zai k’ara, wallahi k’anwar Mama in kinga yadda mijin ta ya dinga wulak’anta ta akan zai yi aure sai Kun yi mamaki.” Takun sakkowar sa suka ji hakan ya saka suka yi shiru ya k’araso da leda a hannun sa ya ajjiye kusa da ita yace, “Ki basu a siyawa yara alewa” ya sake ajjiye mata magani yace, “Ki sha dan Allah in bai sauka ba sai ki kira ni na dawo mu je asibiti.” Kallon su yayi yace, “Mun gode 4stars; naji dad’in ziyarar nan sosai, dan Allah a bata baki kafin na dawo naga ta kuma canjawa. Ku gaida gida” ya fad’a yana fita yana ji suna cewa sun gode.

Yana fita Fiddausi ta d’auki abinda ya ajjiye ta bud’e taga rafar sabbin dari biyar ne guda uku alamun kowa d’aya ta d’auka tana kallon Ameena tace, “Wallahi in nice Ameena ko; ko guda uku zai k’aro bayana bazan damu ba Tunda dai zai bani abinda nake so kuma zai kula sani, ai kud’i zan yanka masa kawai ya bayar in yana so ma na ‘kara masa kwana bakwai ya biya in amarya tazo.”

Rukayya tace, “Ai ita ba ke bace ba Fidy” ta fad’atana kallon ta dan haushin ta take ji. Murmushi Fiddausi tayi tasan abinda yake ran Rukayya tacee, “Kishin banza da wofi, kee kud’i sune gaba da komai wallahi. Ni yanzu da ibrahim zai k’aro aure Ina ruwana? Mtsww!.”

Rukayya tace, “Daman Ina so nayi muku magana akan a yiwa Fiddausi fad’a, da dai bazan fad’a ba tunda sirrin gidan tane amma abin nata yana buk’atar ku shiga maganar, naje gidan ta na tarar da abu mara dad’i ita da mijin ta. Gaskiya ya kamata mu nusar da ita abinda take yi ba daidai bane miji ai ba abin wasa bane. Kud’in banza da wofi, ai miji yafi dukiya.”

Fiddausi tayi dariya tace, “A wajan ki b Hajiya Rukayya, ni a wajena gwara naira dubu goma akan Ibrahim wallahi. Nasan kina yin hakan ne dan kar ya sake ni ko? Nasan damuwa kika yi dani yasa kike fad’ar hakan, to ki kwantar da hankalin ki Rukayya abinda nake so kenan wallahi.” Rukayya ta kalle ta tace, “Amma Ibrahim bai cancanci haka daga wajan ki ba wallahi.” Fiddausi tace, “baza ki gane bane Rukayya, amma fa kina da damar sa in ya sake ni, ke ko a yanzu zaki aure shi ko a jikina a nan zaki tabbatar da abinda nake fad’a.”

Ameena tace, “kai! Wai Fiddausi da hankalin ki kuwa?.” Tayi dariya tace, “Rass nake wallahi Amina, kawai dai akwai target d’ina ne zaku ji shi nan gaba in da lokaci. Koda nan gaba za’a sake maimaitawa indai Ruky batayi aure ba taga zata iya auren Ibrahim ko a yanzu da nake matar sa ta shigo wallahi, banga abin kishi a wajan sa ba” ta fad’a tana dariya sosai suna tafawa da Kiyya.


Zakiyya tace, “Rukayya bafa dan wani abun tace haka ba, kawai taga ke kamar kin kasa gane Ibrahim jinin talakawa ne shiyasa, kin damu da lamarin sai magana kike a akai kamar shine na farko. Duk da damuwa da ita ne ya jawo Hakan, amma kar ki damu wannan ba matsala bace.”


Amina ta kalli Rukky tayi mata alama da kar ta sake magana tayi shiru kawai, ai kuwa shiru sukayi basu amsa ba sai suka canja hira zuwa ta rayuwar islamiyya aka cigaba da hira a kai Ana dariya, har la’asar suna gidan kan Ameena ta sake sosai dariya da ita kafin suyi mata sallama su fita gabad’ayan su.




#Comments
#Vote
#Share
#F5
#Book1
#NanaHaleema

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

Masu nema daga farko ku shiga wannan link din.
https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake, amma kayan nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅



*Book 1*
*Page 21*



A mota suna tafiya Fiddausi a gaba kusa da Zakiyya tana tuk’awa Rukayya tana baya tana danna wayar ta abinda yake damun ta daban da abinda yake damun su, Zakiyya tace, “Wato ke Rukky wai d’auka kike mijin da bashi da ko sisi yana da wata daraja ne?.” Rukayya ta d’ago ta kalle ta tace, “da Allah ya tashi bayani akan miji ai bai ware mai kudi yace yafi daraja ba ko?.”

Fiddausi tayi dariya tace, “Kiyya wannan fa bazata fahimci komai ba sai Allah ya had’a ta aure da irin su İbrahim sannan zata gane me nake nufi.” Rukayya bata ce komai ba tayi shiru suka cigaba da tattaunawa ita da Zakiyya kafin Zakiyya ta kuma cewa, “Rukky an ina zan sauke ki ba gida Fiddausi tayi ba.” Rukayya tace, “Sauke ni a nan ma kawai na k’arasa.”
“A’a mu k’arasa gaba sai ki sauka.”
“A’a sauke ni kawai daman Ina so na biya gidan Sajida.”
“Okay to, ki gaishe ta” ta fad’a tana samun wajan parking sukayi sallama Ruky ta sauka su kuma suka yi gaba.

Fiddausi tace, “Ni wallahi tausayin Rukayya nake ji, Gashi ta jima babu aure sannan ga zuciyar son talaka.” Zakiyya tace, “Nima haka wallahi, Ina mata addu’ar samun mijin da zai rik’e ta haka ni kaina bana jin dadi wallahi musamman in Muna tare haka.”
“Dukkan mu da aure da yara ita kadai ce babu, ko saurayin ma bata dashi abin sam babu dadi.”
“Allah ya kawo mata da gaggawa. Ke muyi abinda yake gaban mu, mu k’arasa gıdana ku had’u a can?.”

“Mijin ki baya nan?.”
“Yana lagos sai gobe zai dawo.”
“Muje to.” Hanyar gidan Zakiyya suka nufa kai tsaye dan Alhaji yayi mata waya zai shigo bayan magriba.

Suna zuwa ba jimawa akayi sallah Fiddausi ta sake wanka tayi sallah Zakiyya ta bata kaya ta saka tayi kyau sai khamshi take a wannan lokacin Alhaji yazo yana jiran ta. A hankali take fitowa yana zaune a kujerar da take kallon inda take fitowa ganin ta fito tana tafiya da rausaya ga khamshin da take yi bai San ya mik’e tsaye ba sai da ta ‘karaso yayi murmushi tace, “Barka da zuwa Alhajina, ka zauna mana” ta fad’a tana zama kamar wacce ta bashi Umarni ya zauna yana sake bin t da kallo.

Fiddausi ta had’a dukkan abinda yake so a jikin mace, gata fara, gata mai murjajjen jiki, gata da sura mai kyau. Hakan yana daga cikin abinda ya saka hankalin sa yake tashi, in yana tare da ita dakyar yake iya daidaita kansa a gaban ta dan in badan hakan ba komai zai iya faruwa. Ya kasa daina kallon ta har sai da ta sake yin murmushi tace, “Barka da dare.” Lumshe idanun sa yayi ya sauke Ajiyar zuciya Maimakon ya amsa mata sai yace, “Fiddausi ki tausayawa bawan Allah ki san yadda zakayi dani, wallahil azim bana so na rasa ki” ya fad’a kamar zai mata kuka yana kallon ta.

Fiddausi tayi dariya tace, “Waye yace zaka rasa ni?.”
“Gashi kina neman saka min hawan jini, kin kasa kashe auren ki nace miki zan biya mijin naki ya sake ki kince A’a, kaina ya kulle ban san ya zan miki ba Fiddausiiiiiii!” Ya ‘karasa fada da wani irin salon da ya saka ta jingina da kujera tana kallon sa.

Tace, “Bawai nak’i bane kawai dai….” Ya katse ta ta hanyar fad’in, “Kawai me? Dan girman Allah kar ki min haka in ba so kike na rasa raina tun lokacina baiyi ba.” Fiddausi tayi shiru bata ce komai ba tana kallon sa hakan ya saka ya sake cewa, “Soyayyar ki tayi min mugun kamu Fiddausi, wallahi waya ake min tafiya zuwa America ta kama ni amma na kasa tafiya sabida bana son tafiya ba tare da magana mai k’arfi tsakanin mu ba.”

Fiddausi tace, “Ina bin komai a sannu ne bana son nayi abinda za’a gano nice na kashe auren da kaina, kodan sabida iyayena bana son yin abinda zai jawo musu magana.” Ya girgiza kai yace, “Kina da gaskiya, amma ni kuma takura min hakan yake yi wallahi bana iya yin komai gashi ko waya ban cika samun ki ba, inda ina jin muryar ki da sauk’i to sai lokaci zuwa lokaci. hankalina yana neman bari jikina ko aiki bana yi yi gabadaya.”

Fiddausi tace, “Lokaci ya kusa kar ka damu ni kaina Ina son kasancewa dakai.” Ya sauke numfashi yayi shiru kafin yace, “Kina da international passport?.” Ta girgiza kai alamun A’a yace, “gobe Monday in kina da lokaci zan aiko a d’auke ki a kaiki passport office za’a yi miki emergency passport, ki d’auki national I.d card din ki da hotuna guda biyu. Ana d’aurin auren mu zu wuce America bana son wani tsaiko gwara ayi komai a kan lokaci, kinga sai Kiyi zaman ki a can kiyi karatu.”

Wani irin dad’i ya mamaye zuciyar Fiddausi nan take ta sake jin in bata kashe auren ta ba ai zata iya mutuwa tayi farrr da idanu tace, “shikenan in akwai lokacin zan kira ka sai ka turo nan sai ya d’suke ni mu tafi.”
“Dan Allah kiyi kokari kar wani abun ya hana ki zuwa goben sabida lokaci baya jira.”
“Kar ka damu Baby.”

Murmushi yayi yana kallon ta kafin ya mik’e tsaye yace, “Zan wuce sauri nake yi ki gaida Zakiyya a mik’a min gaisuwa, zaki ji alert.” Itama tashi tayi ta raka shi har bakin mota ya shiga suka yi sallama ya tafi.

A guje Fiddausi ta shiga falon Zakiyya ta tarar da ita a tsaye ta rungume ta tana ihu tace, “Na kusa zama babbar yarinya.” Zakiyya ta cika ta tace, “Ba ke kin tsaya hauka da shirme ba, cikin jikin ki sai k’ara girma yake in baki zubar dashi ba ke a ganin ki zai tsaya har ki haihu ki yaye ne?.”

“Ai wallahi yau d’in nan za’a zubar da cikin nan, zancen yi min passport yake yi gobe fa ana auren mu sai America!” Ta fada da wani irin salo tana juyawa da falon. Zakiyya tayi dariya tace, “kiyi da gaske wallahi in ba haka ba alkhairi kina gani zai wuce ki.”
Fiddausi ta zauna tace, “Bari kedai y’ar uwa, abinda zan yiwa Ibrahim ya sake ni cikin satin nan nake so nayi masa.”

Zakiyya tace, “Ki dai yi tunanin abinda zai yi saurin tunzura shi.” Fiddausi tayi shiru tace, “ na farko akwai cikin nan, na biyu kuma sai dai ko iyayen sa….” Sai tayi shiru alamun tunani ta sake cewa, “zan dai san abinda zanyi.”
“Shikenan, kije ki same su kice ke kina so ya sake ki in ba haka ba zaki kashe shi.” Fiddausi ta kalle ta tace, “Anya hakan yayi? Hajiyar sa tana so na sosai ke kin sani.”
“Shikenan to zauna kallon ruwa kwad’o yayi miki k’afa.”

Fiddausi ta tashi zuwa d’aki tana fad’in, “Bari kedai kawai zan san abin yi.” Nan da nan ta canja kayan ta zuwa na d’azu ta fito Zakiyya ta saka driver ya kai ta gida zuciyar Fiddausi cike da tunanin mafita dan dole tasan abin yi kafin lokaci ya k’ure mata.

Tana sauka a motar Ibrahim yana kallon ta yana tsaye a k’ofar gida ta kalle shi itama ta wuce shi ta shiga gidan ta same shi da duhu ta dafe kai sam ta manta za’a yi mata gyaran solar wallahi, kafin ta kai ga shiga d’akki taji muryar sa yana cewa, “Ina kika je?.” Banza tayi masa kamar bata ji ba ya sake cewa, “Fiddausi daga gidan ubanwa kike!?.” Juyowa tayi ta kalle shi tace, “Daga Unguwa nake, Ina ruwan ka da inda naje?.”

Bai San lokacin da tsinke ta da mari ba abinda bai tab’a yi ba cikin fusata yace, “Uban waye ya ajjiye ki a mota? Waye ya d’auke ki d’azu? Wa kika tambaya da zaki fita?.” Hannun ta yana kan fuskar ta cikin mamaki tace, “Ni ka Mara?.”
“Na mare ki, Fiddausi zaki rama ne?.”
“Baka wuce na rama d’in ba ai, amma bazan rama a yanzu ba sai lokacin yayi zaka tuna da kanka, amma ka sani wallahi bazan fad’a maka ba” tana fad’a ta wuce ciki shi kuma yayi kwafa ya fita daga gidan dan yin sallar i’sha duk da baya nutsuwar sa.

Tana shiga d’aki kiran Zakiyya ya shigo ta d’auka a fusace tace, “Wai ni Ibrahim zai saka hannu ya mara Zakiyya?.” Zakiyya tace, “Mari? Akan me?.” Fiddausi ta girgiza kai tace, “Yana ganin gangar jikina a banza ne shiyasa yake ganin ni ba komai bace, amma wallahi zan koya masa hankali.”
“Daman na Kira ki ne akan na turo a kawo miki maganin abortion din yanzu, zai zo zai kira ki sai ki karb’a .” Da to akwai ta amsa ta kashe wayar tana wuci.

Dakyar ta iya yin sallah i’sha tana idarwa aka Kira ta a waya har lokacin bai dawo ba ta fita taje ta karb’o tana shirin dawowa suka kuma had’uwa lokacin motar ta tafi. Ko kallon sa batayi ba ta wuce d’aki ta kunna fitilar wayar ta ta ajjiye maganin akan mudubi a lokacin ya shigo d’akin ya kalle ta yace, “me kike ji dashi ne?.”
“Abinda kake ji dashi Ibrahim, wallahi sai kayi dana sanin marina da kayi, sai na tabbatar maka ni ba wacce zaka saka hannu ka daka bace.”
“Waye wannan d ya kuma zuwa wajan ki?.”
“Saurayina ne akwai wani abun kuma!?” Ta fad’a cikin ihu tana kallon sa.

Kan madubin ya kalla yaga maganin da yake ajjiye duk da shi ba likita bane amma yayi zaman chemist yasan magani kala-kala, ya kalle ta yace, “Me zakiyi da wannan maganin?.” Sai da gaban ta ya fad’i dan ta manta dashi a wajan da zata d’auke da ya shigo amma sai ta jure ta kalle shi kamar zatayi magana sai kuma ta bud’e jakar ta da take ajjiye ta d’auko result din cikin ta nuna masa tace, “Ciki ne dani kuma zubar dashi zanyi wallahi bazan kuma haihuwa dakai ba, na gaji da tara iyali tare da talaka.”

Kafin ya d’auki maganin ta d’auke jikin sa ya soma yin rawa b’acin ransa ya ninka na baya yana takowa tana yin baya jikin ta yana rawa yace, “Zaki zubar da ciki kika ce?.” Kafin tayi magana ya cafko ta ya murd’e mata hannu ta saki ihu ya kwace maganin hannun nata yana nuna ta da yatsa yace, “Na gaji da d’aukar iskancin ki Fiddausi, na gaji da jure duk abinda kike yi kina ganin kamar tsoron ki nake ji.”

“Daman so nake ka gaji ai, daman haka nake so ka gaji d’in ka sake ni kowa ya kama gaban sa. Na gaji da zama dakai wallahi ka sake ni ko kuma nayi maka abinda baka tab’a tunani ba.” Juyawa yayi ya fita ta biyo shi a guje zuwa tsakar gida cikin murya mai sauti tace, “in ka cika d’an halak ka sake ni Ibrahim, indai akwai zuciya a kirjin ka ka sake ni yanzu ba anjima ba. Kuma wallahi sai na zubar da cikin nan dan ka kwace magani a banza a wofi ai ba na duka duniya ka kwace ba, wallahi bazan sake haihuwa da talaka ba.”

Bai San lokacin da ya saka k’afa ya fyalli ‘kafar ta ta ba ta fad’i k’asa ta saki kuka sabida yadda bayan ta ya bugu sabida bata shirya hakan ba, Tunawa da cikin jikin ta ya saka shi sauke numfashi da dana sanin hakan yace, “Ki kiyaye ni Fiddausi kar ki kaini bango.” Sai kuwa ta mik’e tsaye duk da yadda take ji ta chakume shi tace, “So nake na kaika bangon daman ai, ka sake ni nace in ka isa kai dan halak ne, indai da gaske kake wannan maganar kawai ka sake ni domin bazan tab’a kiyayar ka ba. Aikin banza talaka shashasha mara mammora!.”

Sau uku ya wanke ta da maruka zafafa har ya fasa mata baki ta sake yin ihu tana kuka yace, “Na fiki iya rashin mutunci, duk abinda kike ji dashi na fiki Fiddausi.”
“To ka nuna min iskancin naka mana, indai da gaske mai shi din ne ka sake ni mana. Wallahi ciki kuma sai na zubar dashi.”

Sake zuwa tayi ta chakume shi ta yaga masa rigar da take jikin sa duk da kuka take amma haka take yin abu hauka-hauka tace, “ka sake ni nace!.” Ya kalle ta yace, “Bazan sake ki ba, kuma wallahi kika sake kika zubar da cikin nan a bakin auren ki!.”

“Subahanallahi! Ibrahim Lafiya?” Maman Zainab mak’ociyar su ta fad’a Jin ihun Fiddausi yayi yawa ya saka ta shigo. Fiddausi bata ji shigowar ta bama tace, “daman ai sakin nake nema kuma sai na zubar kaga kenan daga lokacin babu auren ka a kaina, kuma wallahi sai

Please Login or Register in order to submit comment