Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su ba da yanzu ina murtala ina kan layin ganin likita.”

Zakiyya tace, "A haka kuma kike cewa zaki kuma haihuwa dashi." Fiddausi ta kalle ta tace, "Bazan yi saurin yanke hukunci ba sai naga abinda hali yayi. Yunwa nake ji fa." Zakiyya tace, "Kedai kika sani kece a gidan bani ba" ta fad'a tana kwalawa mai aikinta kira ta bada umarnin a kawowa Fiddausi abinci nan da nan aka cika mata kan table da abinci ta fara ci.

Ta jima a gidan Zakiyya sai bayan azahar ta tafi kai tsaye gidan su ta nufa da niyar gaida mahaifiyarta.
Y'an gidan su mata duk suna nan k'annen ta da kuma yayen ta ta shiga cikin falon Maman su tana fad'in, "Yau babban taro ake shine ko a sanar dani?."

D'aya daga cikin su ta kalle ta tace, “Kaga matar Ibrahim irin wannan kyau haka kamar ba ke ba, lallai Ibrahim ya tsaya miki kina abinda kike so. Fiddausi ta karaso ta zauna jin ta take wani iri kamar magana suke fad’a mata.

Maman su da take zaune tana shan rake irin wanda aka yanka k’anana tace, "Ai sai dai ku fi Fiddausi manyan gida da motoci amma zaman lafiya da biyan buk'ata baza ku fita ba. Mijin ta yana k'ok'ari da ita sosai duk da bashi da k'arfi amma burin sa ya samu abinda zai kyautata mata shiyasa kullum kya ganta fess kamar Hajiya."

Duk sukayi dariya wata a cikin su ta kuma cewa, "Ai haka shine fata daman ba ka auri mai kudin ba kaje can kasha wahala, ita kam ai ta dace sosai, Allah ya cigaba da baku zaman lafiya.” A tare suka amsa babbar su ta kuma cewa, "Kwanciyar hankali yafi zama a cikin daula wallahi. Allah ya k'ara muku zaman lafiya k'anwata ya kawo mana kani ko k'anwar Amir."

Yak’e tayi ta zauna tana fad'in, "Ni ko gaisawa bamuyi ba ana ta magana." Gaisawa sukayi gabad'ayan su kafin Maman su tace, "Daga ina haka da rana?."
"Naje asibiti ne sai na biya gidan Zakiyya."

"Too ko dai an samu k'anin Amir?" Yayar ta ta fad'a tana kallon ta. Fiddausi tayi dariya tace, "Wanne ciki ana zaune lafiya? Ciwon kaine sai suka ce jini na ne yayi k'asa na dinga shan ruwa sosai." A tare suka had'a baki sukayi mata sannu kafin Mama tace, "Har yanzu Amir d'in yana gidan kakar sa kenan?." Ta d'aga kai tace, "yana can, amma nasan dak'yar in bai dawo dashi yau ba" ta kalli y'an uwan nata tace,

"badan nazo ba kenan baza'a fad’a min kuna nan ba ko?.” Babar yayar su wacce suke kira Yaya Zubaida tace, "Sallama nazo yiwa Mama zamu wuce Saudia ashe dukkan su suna nan ban sani ba."
"Har yaushe kika dawo daga Dubai zaki sake komawa Saudia?."

Tayi dariya tace, "To ya za'ayi haka mai gidan yace, sam bai cika son zaman nan ba shiyasa nifa jin dadin Zaman kasar wajan wallahi.” Fiddausi tayi murmushi tace, "Allah sarki, Allah ya kawo namu lokacin da zamu taka Saudia din nan mu ma.” Aka amsa da amin ana hira duk sai taji zaman gidan yana neman fita daga ranta gabad’aya zuciyar ta na juya mata maganar y’an uwan ta.

K'aramar cikin su k’anwar Fiddausi su Hafsa tace, "Kee wai sai naji matar Aminu mak'ocin mu ta kuma haihuwa, kai matar nan akwai haihuwa tana fama da kanta abincin da zasu ci ma gagarar su yake amma duk shekara sai ta haifo wani ko wahala ma bata ji.

"Bari kedai kawai, kaji dana gaban ka ma ka samar musu ilimi da abinci da suttura kafin ka haifo wani. Talaka akwai son haihuwa, talakawan ma kuma wanda babu ci babu sha sun fi haihuwa. ni kuma Allah da wata ce a k’asar nan sai na hana talakan da bashi da cin yau da gobe haihuwa sai ya samu abin yi, in ba haka ba kuma na kama shi.”

Mamma ta kalle ta tace, "Akan me?." Ta kalli Mama tace, "Wallahi Mama irin sune yaran suke fara bara ko su fara sace-sace sabida an haife su an zube su babu kula balle tarbiyya, yaro shi zai nemo abincin da zai ci ba dole su lalace ba. Da anyi magana suce annabi ne yace ku hayayyafa dan ranar tashin alqiyama nayi alfahari daku, Allah ya jiqan malam Albani Zaria yace annabi zaiyi alfahari da ‘barawo ne ko zaiyi alfahari da d'an daba?."

Wacce take binta suke kira Anty Balaraba tace, "Ina fa. Kuma masu kud'in sune suke gudun haihuwa amma talaka kamar daman sabida haihuwa yazo duniya. Ni wallahi banga abinda zai sake saka ni na haihu ba yanzu, na gabana ma na gama basu tarbiyya da ilimi kafin na bar duniya” ta fad'a tana girgiza kanta.

Fiddausi tana jin su bata tanka ba ji take gabad'aya maganar su da ita suke shiyasa gabad'aya zaman gidan bai mata dad'i ba duk ta takura zuciyar ta tana karb'ar shawarar Zakiyya akan zubar da cikin jikin ta kota wanne hali, Gasu da suke auren masu kudi suna cewa baza su haihu ba Wacece ita da zata sake haihuwa itama? Ina bazai yu ba dole cikin yabi rariya ko ta wanne hali. Sai bayan sallar la'asar tayi musu sallama ta tafi dan tasan su sai dare tunda zuwa za’a yi a d’auke su ita kuwa adaidaita zasu ne.



Duk yadda Ameena taso tsayar da hawayen ta kasawa tayi ta shiga band’akin d’akin Humaira tayi kuka kamar ranta zai fita sai da ta gaji dan kanta ta wanke fuskar ta ta fito ta zauna a d'akin ta jima sosai har akayi la'asar sannan ta fito zuwa falon.
Bata samu Ammah ba daman tasan ta hau sama bazata sakko ba suka cigaba da hira da Humairah sama-sama dan ba fahimta take sosai ba a haka har akayi sallar magriba a lokacin ne Yusuf ya dawo gidan.

Bayan sunyi sallah suka shigo harda yayen sa maza guda biyu da k'anin sa namiji mai kama dashi suka samu Ammah da Abbah a zaune a falon da suka saba zama duk suka zauna ana sake gaisawa.

Kallon da Ammah take yi masa ne ya saka shi fad'uwar gaba amma da yake namiji ne sai ya jure kamar ba shi ba sai ma sakewa da ya sake yi ana hira da shi. Abbah ya kalle su yace, "Yauwa dalilin da yasa nace in kun tashi daga wajan aiki duk kuzo magana ce a kan k'anin ku Yusuf gashi nan, aure yake so ya k'ara nasan kun san maganar tun da babar kuce take hanawa."

Babban yayan su a kaf gidan da suke kira da Abie mai sunan mahaifin Abbah ya kalli Abbah yace, "Eh mun san da maganar tun farko Ammah ce taka dakatar da ita, kuma tana da gaskiya har yaushe yayi auren da zai fara neman wata? Kuma suna zaune lafiya da matar sa akan me zai tayar da hankalin akan k’ara aure.”

K'anin sa wanda yake bin babban Yaya Jamil yace, "Ni a ganina Abbah tunda dai yana so kuma Allah ya wore masa me zai saka baza'a barshi yayi ba?." Abbah yace, "Abinda nace kenan nima, duk yadda akayi akwai rabo tsakanin sa da yarinyar shiyasa maganar take ta yawo har yanzu, ana ta zuwa ana dawowa akan maganar nan gwara a tsayar da matsaya in yi ayi, in baza’a yi ba a hak’ura. Dan haka kaine babba me kake gani?" Ya fad'a yana kallon Abie.”

Abie yace, "Abbah duk abinda kace daidai ne, hukunci yana hannun ka namu goyan baya ne kawai." Abbah yace, "to nidai na amince mahaifiyar sa ma itama ta amince yanzu” ya fad’a yana kallon Ammah da ba shi take kallon ba ya sake cewa, “Dan haka zan saka a nemo min iyayen yarinyar nayi bincike a kan su da ita kanta kafin aje a nema masa auren ta, in sha Allah a cikin satin nan za'ayi komai a gama tunda haka Allah ya k'addara babu wanda ya isa ya canja Hakan.”

Abie yace, "Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Ammah an fad’awa Zahra’u maganar?." Ammah da ta fahimci Yayar Abuja yake nufi tace, "Eh ta sani."
"Shikenan Allah ya shige mana gaba." Aka amsa da amin kafin suyi sallama su tafi Abbah ma ya hau sama aka bar wajan daga Yusuf sai Ammah.

Ammah ta kira Ameena ta fito ta nuna mata waje ta zauna ta kalle shi tace, "Shine kaje ka samu Amina kace tazo ta same ni tace na barka kayi aure ko?." Da sauri ya d'ago ya kalli Ammah sai ya kasa cewa komai ya sunkuyar da kai dan bai San ya sukayi da Ameena ba bazai yi saurin magana Ameena tace, "Ammah ba shine ya turo ni ba, nayi ne kawai dan naga yana son hakan kuma shine kwanciyar hankalin mu baki d’aya.”

Ammah tace, "Ameena bake na tambaya ba dashi nake, jin abinda nake cewa ai ko?.” Yusuf yace, “Ba haka bane Ammah.” Ta kalli Ameena tace, “Yarinya ce ke Amina, amma babu komai akwai Allah. Na amince da auren kamar yadda kake so shikenan hankalin ka ya kwanta ko?." Kasa d'ago kai yayi amma a zuciyar sa ba k’aramin farin ciki yake yi ba kawai yana b'oyewa ne sabida Ammah kar ta gano shi.

Ammah ta tashi tace, "Amma duk abinda ya biyo baya a bayan auren ka da yarinyar kar ka zargi kowa ka zargi kanka, sannan kar kayi kuka da kowa kayi kuka da kanka. Zan maimaita maka ka kuka da kanka kar ka saka kowa cikin damuwar ka" tana fad'a ta wuce ta barshi Ameena ta tashi tabi bayan ta da niyar yi mata sallama ta kuma d'auko Zaytun su wuce gida.

Farin cikin sa ya bayyana sosai akan fuskar sa har Amina ta dawo bai sani ba ya d'auki waya yana rubutawa Asiya message tana tsaye sai da ya gama ya d'ago sai ya wayance yace, "My choice mu tafi?."
Yadda yayi mata maganar sai da gaban ta ya fad'i ta d'aga kai alamun eh ya karb'i Zaitun a hannun ta suka fita zuciyar sa fari tasss kamar ana wanke masa ita haka yake ji.

Tun a mota yake ta murmushi tana lura dashi gashi baice mata kanzil ba tuk'i kawwi yake har suka shiga gida yana fakawa ta fita ta shiga gidan ta samu kayan da ta bari kan dining yana wajan ta kwantar da Zaitun akan kujera ta kwashe kayan ta kai kitchen ta fito a daidai lokacin ya shigo falon yana murmushi.

Zuwa tayi da niyar d'aukar Zaitun ya riga ta ya d'auke ta yace, "muje saman." Yadda yake murmushi tsoro hakan yake bata ta bishi da kallo yayi gaba tabi bayan sa zuciyar ta sai bugawa take bata san dalili ba amma tasan murmushin nan nasa yana saka ta bugun zuciya.

Saman sa taga ya wuce da Zaitun ita kuma kawai sai t a shiga d'akin ta ta shiga band'aki tana wanka tana kuka a haka ta fito shi kuma ya shigo d'akin. Ganin tana kuka sai ya matso kusa da ita da sauri yana kallon fuskar ta yace, "Haba My Choice meya faru kike zubar da hawayen ki haka?."

Bata bashi amsa ba ta zauna a gefen gado ya tsuguna a gaban ta yace, "Tun farko sai da na fad'a miki in bakya son abin nan a barshi amma kika ce zaki samu Ammah da maganar yanzu kuma dan ta amince shine kike kuka?."

Kallon sa take jin yama raina mata hankali nufin sa duk farin cikin da yake yi bata gani kome?. Ganin tayi shiru sai ya dafa hannayen ta da har lokacin suke da ruwa a jiki yace, "My choice dan Allah ki daina kuka, nifa bawai zanyi auren nan dan son raina bane na fad'a miki dalilina.”

"Hmmm" shine abinda tace can k'asan mak’oshi kafin ta zame hananyen ta ta mik'e tsaye ta k'arasa wajan kayan ta ta buɗe tana d'auko wanda zata saka ta ajjiye ta mayar da murfin ta rufe. Biyo bayan ta yayi ya rik'e hannun ta ya juyo da ita yana kallon ta yace, "In kina wannan kukan sai naji kamar ban kyauta miki bane bayan da amincewar ki akayi komai. Dan Allah ki nutsu ki daina wannan kukan dan Allah, Ina son ki har abada a haka zamu cigaba da zama” ya fad'a yana janta jikin sa ya rungume ta.

Sakin ta yayi ya saka hannu ya goge mata idanun ta ya kalle ta yace, "Kizo muje sama kinga na bar Zaitun a can kar ta tashi."
"A'a zan kwanta a nan, ka mik'o min ita kawai."
"My choice why?."
"Kawai ina so na kwana a nan d'in ne kaje kawai, burin ka ya cika kuma meye kake rarrashina?."

"My choice na fad'a miki fa duk abinda ya faru kika amince to yanzu meye laifina a nan?." Ta kalle shi irin kallon da ya kasa fassara na meye tace, "Babu." Ta bar inda yake tsaye ta koma ta d'auko kayan ta ya sake dawowa kusa da ita yace, "Nifa wannan damuwar da zaki shiga ita na gujewa shiyasa nace a barshi kika ce A'a my Choice."

Ta kalle shi tace, "Kaji nace wani abun ne kuma?." Ya girgiza kai alamun aa tace, "To ka k'yale ni kawai." Ya sauke numfashi yace, "Shikenan my choice kiyi haƙuri" ya fad'a yana fita ta bishi da kallo kawai ta fashe da kuka da kukan da ta rasa na meye, na haushin kanta ne ko kuma na rainin hankalin da yake mata ne bata sani ba.

_Kishiya ni My Choice? Hahaha to akan me zan miki kishiya bayan Allah ya baki dukkan abubuwan da ko wanne namiji yake so a wajan mace?. Son da nake miki my choice bazai bari na k'aro wata bayan ki ba, bazan iya kallo wata mace da fuskar soyayya ba in bake ba, ke kawai nake so kece zab'ina._

Kalaman sa suka fad'o mata lokacin basu jima da tarewa ba ta share idanun ta tare da lumshe idanu zuciyar ta na bugawa. _Aure nake so zanyi ban damu da kwanan mu nawa da aure ba kawai zanyi aure ne, badan na gaji dake ba kawai zanyi aure ne babu abinda zai dakatar dani._ kalaman sa suka sake fad'o mata a lokacin bata jima da haihuwar Zaitun ba ta lumshe idanu tana jan numfashi tunawa da kwanakin da ya kwashe baya nan dan kawai Ammah tace bazai aure ta ba.


Motsin sa taji ya saka ta kalle shi ya k'araso ya kwantar mata da Zaitun akan gadon da take bacci ya kalle ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fita tare da ja mata k'ofar. Murmushi yayi bayan ya fita daga d’akin yaja tsaki yace, "Tunda dai Ammah ta amince burina ya cika Meena koma me zakiyi duk daga baya ne, nayi amfani da soyayyar da kike min na samu cikon burina, wannan b’ata ran da kike ba wani amfani zaiyi min ba. Asiya ta kusa zama mallakina in sha Allah" ya fad'a yana barin wajan da sauri dan so yake ya k'arasa d’aki ya kira Asiya su sha soyayya.



#Comment
#Vote
#Share
#Book1
#F5

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 9*

Tunda Fiddausi ta koma gida ta shiga d'aki bata fito ba tana jin motsin dawowar Ibrahim tayi burus kamar bata ji ba tana zaune tana tunanin maganar Zakiyya da kuma maganar y'an uwan ta akan abinda yake cikin ta, tabbas ya zama dole ta d'auki mataki kafin wankin hula ya kaita dare, bazata bar cikin ba gwara kawai ta zubar tun lokaci bai k'ure mata ba.

Tasan sai yaje yayi sallah ya dawo sannan zai shigo tana zaune aka kawo wutar nepa haske ya gauraye d'akin gabad'aya, tayi ajiyar zuciya ta tashi tayi itama tayi sallar tana nan zaune tana sak'awa da kwacewa har ya shigo d'akin da sallama.

Da kallo ya bita ya zauna kafin yace, "Ya jikin naki? Na kira ki naji yanayin ki baki d'auka ba kuma baki kira ni ba. Me suka ce a asibitin?." Ta kalle shi tace, "ka bani kud'in katin ne?." Kawar da maganar yayi bai tanka ba kafin yace, "Yanzu dai me yake damun ki?."

"Jinina ne yayi k'asa sunce na dinga shan ruwa sannan inda hali a dinga siyo min hanta kullum ina ci."
"Subahanallah, abun har ya kai haka kenan?."
"Uhum!" Ta bashi amsa a tak'aice ba tare da ta kalle shi ba dan wani irin k'unci take ji a zuciyar ta in ta Tuna tana da ciki.

"Bara na fita na samo miki hantar kici sai ki kwanta" ya fad'a yana tashi ya fita ta bishi da kallo ta tab'e baki tare da jan k'aramin tsaki. Tana ji ya buɗe kofa ya fita tace, "Dole ne na rabu da wannan cikin tun kafin ya farga, maganar Zakiyya gaskiya ce ya akaji dana gidan ma balle a samu wani? Ai komai sai ya sake lalacewa."

Wayar ta taji tana k'ara ta jawo tana kalla taga bak'uwar lamba bata kawo komai a ranta ba ta d'auka ta saka a kunne, "Amincin Allah ya tabbata a gare ki kyakykyawar sura fara mai farar aniya, ina fatan gimbiya Fidy ta koma gida lfiya?."
Gaban ta yayi mugun fad'uwa ta wara idanu waje jin muryar mutumin da batayi tunani ba ta had'd'iye yawu ta kasa magana tayi shiru kirjin ta na bugawa cikin tsoron da ya bayyana a kan fuskar ta. "Gimbiyata kinyi shiru, baki gane mai magana bane?."

Muryar ta rawa take yi ta kasa furta komai yayi murmushi yace, "Kar ki damu na samu komai a labarin ki, kina da aure kina kuma da yaron mu Amir. Gidan wacce muka je d'azu gidan k'awar kine Zakiyya wacce kuka taso har kuka yi makaranta tare da ita, haka ne abinda nace?."

Wara ido waje tayi kamar yana gabanta murya na rawa tace, "kasan ina da aure meyasa ka kira ni?."
"Sabida ina sonki tsakani da Allah badan wani abun ba, ina so na aure ki ne in kin amince. Ban kira ki da niyar b'ata miki aure ba, ga gaske auren ki zanyi."
"Kamar ya ka aure ni bayan yanzu kake shaida min kasan ina da aure?."

Ya sake yin murmushi yace, "Gidan da kike Fiddausi bai dace dake ba, matar manyan mutane ce ke sam baki cancanci zama da wannan mijin naki da kuke tare ba. Ke matar manya ce kowa ya kalle ki a kallon farko zai gane hakan, matar irin mu ce ke kawai ki bani dama." Fiddausi tace, "me kake nufi?."
"Kinga maganar waya bazata yu ba, yaushe zamu had'u?. Bani nufin cutar dake ko d'aya, ni auren ki nake so nayi."

Shiru tayi bata amsa ba ya sake cewa, "Taya kike tunanin zaki zauna a irin gidan da kike zaune Fidy? Ke kalar hawa manyan motoci ce da hawa jirgi ki bar k'asar meyasa kike zaune da wanda ba ajin ki ba?. Kalli k'awar ki Zakiyya mana bakya sha'awar irin tata rayuwar?. Ina tabbatar miki da matukar na aure ki rayuwar ki zata ninka ta ta rayuwar sau babu adadi." Shiru tayi bata amsa ba tana shawarwarin ta kashe ko kuma ta cigaba da jin abinda yake cewa kafin ya kuma cewa, "A shirye nake da na aure ki in kika kashe auren ki, baki da wata fargaba domin Allah yasa min sonki lokaci d'aya ba tare dana shiryawa hakan ba. Yaushe zamu had'u mu tattauna?."

Fiddausi duk tsoro ya cika mata zuciya ga tsoron kar Ibrahim ya dawo tace, "ni bazan iya had'uwa dakai ba, kayi haƙuri." Jin zata kashe wayar yayi saurin dakatar da ita yace, "Kar ki kashe dan Allah, ki taimake ni ki kuma taimaki kanki ki amince mu had'u, wallahi ni ba irin wanda kike tunani bane da zuciya d'aya nazo wajan ki. Ki amince gobe mu had'u a gidan k'awar ki domin mu samarwa da kanmu mafita. Da gaske nake ina sonki kuma wallahi auren ki zanyi."

Numfashi ta sauke tana kallon d'akin ji take kamar Ibrahim zai iya shigowa a lokacin ta sauke numfashi tace, "Shikenan zanzo goben, amma dan Allah kar ka sake kirana." Sautin murmushin sa taji yace, "Bazan kira ki ba gimbiyata sai na tabbatar mijin ki baya nan, yanzu ma an tabbatar min da fitar sane shiyasa na Kira ki. ina sonki ina k'aunar kasancewa dake, kiyi kwanan farin ciki" yana fad'a ya yanke wayar tabi wayar da kallo har lokacin kirjin ta bai daina bugawa ba, babban tashin hankalin ta bai wuce waye ya fada masa tarihin ta? Waye ya fad'a masa İbrahim ya fita?.

"Fiddausi!." A firgice ta juya jin muryar Ibrahim ya k'araso da leda a hannun sa ya zauna yana kallon ta yace, "ya na ganki a firgice akwai damuwa ne?." Kai ta girgiza alamun a'a ya mik'a mata yace, "Gashi kici." Hannunta har rawa yake ta karb'a ganin hakan sai ya rik'e hannun ta yace, "Lafiya kike kuwa?."

Kai ta girgiza alamun babu komai ya bita da kallo ya rik'e fuskar ta yace, "In akwai damuwa ki fada min."
"Babu komai" ta furta a sanyaye ya buɗe mata ledar da kansa khamshin hantar ya daki hancin ta ta fara ci duk da nata tare da nutsuwar ta.

K'are mata kallo yake dan ya tabbatar ba haka ya fita ya barta ba ta koma wani iri kamar mara gaskiya sai zare idanu take yi, "Fiddausi ba lafiya kike ba." Ya sake fad'a yana kallon ta ta girgiza kai alamun babu komai sai ya girgiza kai kawai ya tashi ya fita.

Gabad'aya hantar ta fita daga ranta ta ture gefe ta tashi ta fita daga d'akin ta wanke hannunta tare da dawowa ta kwanta a gefen gado kalaman Alhaji Bello na sake yi mata yawo a cikin kanta. Hasken d'akin taga an kashe sai k'arar fanka da take tashi tasan shine ta lumshe idanunta tana ji ya kwanta a bayan ta amma ta kasa motsin kirki dan bata san me zatayi ba. Tunanin ta gabad'aya yana wajan Alhaji Bello lamarin sa ya bata tsoro sosai gaban ta sai fad'uwa yake yi.

Yadda bata da kwarin jiki zuciyar ta ma babu k'arfi da wannan damar yayi anfani ya samu abinda yake so a wajanta ita kuma tana can duniyar tunani tana sakawa da kwancewa domin samarwa kanta da goben ya mafita mai kyau.

Washe gari.

Matashiya ce wacce bazata wuce shekara ashirin da bakwai zuwa da takwas ba doguwa mai kyaun jiki duk da bata da kib'a amma tana da kyau daidai gargwado. Tsaye take a bakin fanfo a tsakar gida tana zuba ruwa a bokiti kafin ta kashe fanfon ta d'auki bokitin ta wuce zuwa d'aki.


A falon Umma ta tarar da ita a zaune ita da k'annen ta biyu Zuhra da Sajida ta kalli Sajidan tace, "yaushe kika shigo?." Sajida da take zaune tace, "Ban jima da zuwa ba." Zuhra ta kalle su tace, "Yaya Ruky ki gaishe ta mana." Ta wata idanu waje tace, "Sajidan zan gaisar?."
"Eh mana, in kin girme ta a shekarun yanzu ai yayar kice" ta fad'a tana k'unshe dariya.

Rukayya ta kalli Mama dan taga ki zata tsawatar sai taga shiru kawai sai ta dauki bokitin ta tazata wuce tace, "Rukayya me zakiyi da ruwan zafi naga kin kuma dafawa bayan d'azu kinyi wanka?."
"Wankan janaba mana Umma, in ba shi ba me zatayi?" Zuhra ta fad'a Tana kallon ta

Umma ta kalli yarinyar tace, "Ke bana son shirme wacce irin magana ce wannan?." Shiru tayi tana kallon Rukayya kafin Rukayya ta wuce d'aki zuciyar ta na zafi sosai amma bata nuna ba haka ta shiga band'akin tayi wanka tana fitowa Mama ta shigo ta bita da kallo ganin kanta a jike tace, "Da gasken da maganar Zuhra ta fito wankan janaba kika yi ga kanki nan yasha ruwa."

Rukayya kamar zatayi kuka tace, "Umma me zai had'a ni da wankan janaba?." Umma tayi murmushi tace, "Rukayya kenan, yadda kika jima babu auren nan duk sa'anin ki daga mai yara biyu sai mai guda d'aya ai dole wanka ya kama ki wani lokacin. Shekara ashirin da bakwai ai ba wasa ba."

Hawayen da take b'oyewa suka sakko ta share Umma ta sake kallonta tace, "Ba kuka nace kiyi min ba malama, tashi zaki ki shirya na

Please Login or Register in order to submit comment