Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

*Book 1*
*Page 15*





Tunda ta fito daga d'aki yaga tana cika tana batsewa yasan akwai tashin hankalin da take nema dashi hakan ya saka ya cigaba da kallon tv yayi kamar bai ganta ba dan baya son tashin hankali. Zama tayi a gefen sa tana shan khamshi kamar gimbiya kana tace, "wai yaushe Amir zai dawo ne? Nifa na gaji da zaman gidan nan baya nan." Ko kallo ta baiyi ba yayi mata banza sai daga baya ya juyo ya kalle ta yace, "Bazai dawo ba."

Baki ta tab'e tace, "Kaima kasan wasa kake."
"In nace na barwa Hajiya shi akwai abinda zaki iya ne?."
"Akwai mana domin nice na haife shi dole a bani shi ko kotu ta karb'ar min." Kallon ta yake yi dan ya lura raga mata da yake yi shine ya saka take sake raina masa hankali dan kawai yana hakuri.

"Ga hanya nan jeki" ya fad'a yana nuna mata k'ofa. Kai ta girgiza tayi k'wafa tana girgiza kanta ta k'arfi so take ta jawo masifar da zai sake ta. Tsaki yaja ya tashi ya fita bai sake kallon inda take ba itama ta mayar masa da martanin tsakin sa. Sarai ya jita baice komai ba ya fita daga gidan gabad'aya.

Da harara tabi hanyar da yabi tace, "Aikin banza, wallahi ko ta wanne hali sai na bar gidan nan ko baya so." Wayar tace tayi k'ara ganin sunan Zakiyya ya saka ta d'auka kafin tayi magana daga can b'angaren tace, "Kee Wai ya ake ciki ne? Har yanzu bai yi sakin ba?." Fiddausi tace, "Gashi nan sai kace dan mayya."
"Kuma kina masa rashin mutunci kuwa? Nasan halin ki fa wani lokacin kina da tsoro."
"Na rasa tsoron wa zanji sai na Ibrahim? Mtswww kema dai wasa kike wallahi. Jiya baki ga yadda yazo a matuk'ar buqace dani ba amma nak'i bashi had'in kai na gaggaya masa magana mai d'aci amma yau ko gezau baiyi ba sai ma wani sabon salon da ya fito dashi."

Zakiyya tace, "Ya kamata mu san abin yi domin kuwa wallahi Alhaji ya kagu, bana son mu rasa wannan damar ne Fiddau". Fiddausi tace, "Babu batun rasa dama Kiyya, wallahi sai ya sake ni koda baya so. Kafin nan cikin k'udin nan Ina son a had'a min solar yau a gidan nan."

"Mtsww, Keda kike shirin barin gidan solar uban me za'ayi miki?."
"Ai hakan zai sake tunzura shine, koda na bar gidan ya dandali arzuki shima." Zakiyya tayi dariya tace, "Zan aiko da masu had'a miki da komai da komai nan da anjima kad'an. Amma Ina da shawara." Fiddausi tace, "Ina jin ki."
"Ke kin san yadda yake girmama hajiyan sa, me zai hana baza kije kiyi rashin mutunci a gidan su ba kinga in ta fad'a masa ai dole ya sake ki ko?."

Fiddausi tayi shiru tana juya maganar kafin tace, "Hajiyan sa tana da kirki sosai fa Kiyya, bana son sako ta cikin wannan maganar Allah ya sani."
"Ai shikenan sai ki tayi ai, ki bari kirki ya rufe miki ido Alhaji ya sub'uce miki ki shiga uku."
"Bazai sub'uce min ba Kiyya, nasan abinda zanyi kawai ki kyale ni."
"Haka kike cewa amma kin kasa aikata komai sai shegen cika bakin tsiya". Kafin Fiddausi ta kuma magana zakiyya tace, "Alhaji ya takura min yana so ya ganki fa, ya za'ayi ne?."

Fiddausi tace, "Hak'uri zaiyi komai ya lafa tukunna."
"Kawai ki kunna datar ki zai kira ki video call ta WhatsApp Tunda yanzu shegen ya fita ko?."
"eh ya fita, amma kar wani ya shigo ya tarar dani fa."
"Dallah malama a gidan ki kike fa, ki tashi kije ki kulle waccan langa-langar k'ofar gidan naki kizo kiyi kwalliya ki saka rigar da ta d'an miki yawa yadda wuyan zai dinga yin k'asa a haka zamu sake kamo wuyan Alhaji."

Fiddausi ta tashi waya na Kunen ta ta kulle kofar kamar yadda Zakiyya tace ta dawo har lokacin wayar na kunnen ta kafin tace, "Ke ni bazan saka wata Riga ba zanyi a haka bana son iskanci."
"Banza doluwa kawai, ai ganin wani abu daga cikin surar ki shine zai saka koda ya yi niyar fasawa ya haqura ya jira ki sai kin fito dan shima ya mora. Wallahi Fiddausi kika tsaya wasa wannan girmama yayar taki da ake a gidan ku ke baza'a yi miki ba har abada, in fa kika aure shi wallahi ko meena da muke ganin ta kere mu albarka. Amma kar kiyi nifa Ina cikin daula ke nake ji amma naga kamar bakya so" ta fad'a Tana niyar kashe wayar.

Da sauri Fiddausi tace, "Sarkin masifa kar ki kashe dan Allah zan saka, in na saka kiran sa zanyi?." Zakiyya tace, "Gani nayi ai kamar bakya so sai na kyale ki tunda bani bace ba."
"Nace ai zanyi ko?".
"Kar ma kiyi kanki zaki cuta wallahi bani ba."
"Yi hakuri, yanzu ya za'ayi?."
"Ki saka rigar zan ce masa ya kira ki, kiyi masa shagwab'a ai kin gane dai."


Dariya Fiddausi tayi kawai ta kashe wayar zuciyar ta na nuna mata abinda take niyar yi fa sam-sam ba daidai bane. Numfashi ta fesar jin tunanin yana neman yin galaba a kanta tace, "burina auren mai kud'i n samu jin dad'i naje duk inda nake so na hau duk motar da nake so, to meyasa zanyi wasa da damar Dana samu ne wai?". Kai tsaye d'aki ga wuce ta canja kaya zuwa doguwar riga ta atamfa wacce wuyan ta yake sauka akan kallon kirjin ta ta sama sosai.

Kallon kanta tayi a madubi tace, "kai Anya zan iya bari ya ganni haka?." _Sai me dan ya ganki haka ai ba tab'awa yayi ba, babu wani abu kiyi kawai mafita kike nema._ shawarar zuciyar ta tabi ta dauki wayar ta kunna data ta zauna a gefen gado.

Kamar ana jira ta d'auka kiran ya shigo gaban ta ya fad'i amma haka ta kawar da ko me take ji ta d'auki wayar nan take fuskar sa ta bayyana yana kwance k'ayataccen daki shi kad'ai. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yayi tozali da fuskar ta yace, "Fid kin wahalar dani yau kwana biyu ban ganki ba duk na damu, wallahi zuciyata ciwo take min Akan hakan amma ke naga ko a jikin ki."

Shagwab'e fuska tayi ta turo baki gaba tana girgiza kafad'arta tace, "Ina kewar ka mana kasan babu abinda zan iya ne ai ko?."
"Ya Allah!" Ya furta lokacin da rigar tayi k'asa saman fararen kirjin ta ya bayyana a kan wayar zuciyar sa ta harba jijiyoyin jikin sa suka harda a tare. Kare mata kallo yake yi yana sauke numfashi hakan ya saka taji wani iri itama ta saka hannu zata ja rigar sama yace, "Dan Allah Fid kar ki rufe, ki barni na gani ko zanji saukin kewar ki da nake a zuciyata. Kin ganni Ina Abuja amma kewar ki ta saka ko office na kasa zuwa, dan Allah ki bari na gansu ko zanji dadi na samu karfin guiwa. Ina sonkiiiii Fiddddd!" Ya fad'a da wani irin salo da sai da taji tsirgawar abu a jikin ta nan take ta fara jin abu nayi mata yawo a dukkan ilahirin jikin ta, jikin ta yayi sanyi ta kasa motsi sai kallon sa take yi kamar yadda yake kallon ta.

"Zan iya neman alfarma?." Yadda muryar sa ta fita nan ma sai da taji wani abu a jikin ta ta kalli Idon sa taga ya canja launi yanayin jikin sa ya canja tace, "Inaa jinka".
"Ko me nace zaki min Fidd?."
"Uhum!" Ta furta kawai bata ce komai ba dan bata so ya gano yanayin ta.
"Dan Allah zaki iya yi min k'asa da rigar na gansu sosai?, wallahi Ina cikin wani hali in na gansu zan iya jin daidai. Sau d'aya kawai Fid dan Allah".

Ta cikin wayar ta kalle shi tace, "Me kake nufi?."
"babu komai Fid, Ina so naga kirjin ki ne kawai ba wani abun ba, dan Allah ki taimake ni" ya fad'a yana jann numfashi. Kawar da fuska tayi tana sauke nata numfashin kafin ta juyo tace, "bazan iya ba" tana fad'a ta yanke kiran da sauri tayi baya ta kwanta a kan gadon tana sauke numfashi zuciyar ta na bala'in harbawa.

Bata san adadin lokacin da ta kwashe a haka ba sai 'karar wayar ta taji, kamar bazata d'auka ba sai kuma ta duba ganin mai kiran ya saka ta dauka daga can Zakiyya tace, "Me Alhaji yayi miki ne? Ya kirani yace na bak hak'uri wai kinyi fushi wallahi ya kasa rik'e kansa ne, duk ya rud'e kamar Wanda ya yiwa uwar sa laifi." Fiddausi tace, Iskanci yazo min dashi, wai na zame rigata dan Allah yaga kirjina, shine na kashe wayar kawai dan ya bani haushi, ai ba y'ar iska sunana ba."

Zakiyya tace, "Eh gaskiya bai kyauta ba, amma dai kiyi hak'uri hakan da kika yi ma wani sake kama shi kika yi. Yanzu dai ki d'aga wayar sa yace min yana kira baki d'auka." Bata ce komai ba Zakiyya ta kashe wayar a lokacin kiran sa ya shigo ta d'auka ta saka a kunne kafin tayi magana yace, "I'm sorry my queen banyi dan na bata miki rai ba, Kiyi hak'uri sonki ne yayi min yawa har na kasa controlling kaina. Ki yafe min dan Allah bai kamata nace miki haka ba koda baki da aure balle kina da aure, Kiyi hak'uri kinji Baby?."

Kamar bazata amsa ba hakan a saka ya kuma cewa, "Kiyi hak'uri dan Allah." Sai a sannan tace, "Kar a sake." Numfashi ya sauke yace, "Baza'a kuma ba in sha Allah Baby, Ina sonki." Murmushi tayi tace, "Nima Ina sonka Babyna."
"ba wani babyn ki bayan kin hana babyn naki ganin abincin sa, koda yake nace ayi hak'uri."
"Ka sake wani laifi dai".
Dariya yayi yace, "Tuba nake."

Hıra sukayi mai cike da soyayya kafin su kashe wayar ta tashi tsaye a lokacin take jin ana buga gidan nata ga kiran sallar azahar da ake yi dole ta fita zuwa tsakar gida dan ga bud'e.

Tana bud'e gidan taga Rukayya kafin tayi magana ta bangaje ta ta wuce tana fadin, "Fitsari nake ji." Dariya tayi tace, "Rukky sarkin fıtsari, ke ayi tafiya mai nisa dake ko wahala." Bata kula ba sai da ta fito daga band'akin ta sauke numfashi ta kalle ta tana tsaye inda ta barta tace, "Ke fitsari rahama ne wallahi, kinji yadda nake jina sakayau?."

Fiddausi tace, "Haka dai kika iya, Sam bakya iya rik'e fitsari."
"Akan me zan rik'e ya zamar min cuta? Ku da kika ga zaku iya sai kuyi, ke nifa Yunwa nake ji wallahi." Gaba Fiddausi tayi Rukky tabi bayan ta sai kuma ta dawo tace, "Alwala zanyi fa na manta na biki" ta fad'a tana zuba ruwa a buta Tana alwala.

Lokacin da ta shiga bata ga Fiddausi a falon ba da yake gidan ba bak'on ta bane tasan Ina ne alqibla ta tayar da sallah. Bayan ta idar ne Fiddausin ta shigo falon ta zauna tana cewa, "Na d'ora miki indomie sai kije ki k'arasa kin san ba yi miki zan ba." Rukky ta mik'e tana fadin, "Abinda Ina da k'afa ba gurguwa bace ba ni" ta fad'a tana fita Fiddausi tayi dariya kawai.

Nan da nan ta gama dafa indomie harda kwai da ta gani a ajjiye ta soya ta fito da plate din a hannun ta zata wuce akayi sallama ta amsa ta shiga falon ta fad'awa Fiddausi. Fita tayi bata jima ba ta shigo Tana cewa, "Masu had'a solar ne, yanzu zasu fara aikin su ma huta muma da wannan rashin wutar da ake fama."
Rukky ta haddiye abincin bakin ta kafin tace, "Wallahi Mrs ibrahim kina sha'anin ki, yanzu ke ana fama da abinci ke ta solar ma kike, lallai ibrahim ya tsaya miki Allah ya bar soyayya."

'Karamin tsaki yayi tayi ta tab'e baki tace, "ke a ganin ki ibrahim yana da kud'in yin solar ne? Ko fa keke bashi dashi da k'afa yake yawo har gobe, Ina yaga wannan arzuk'in?." Rukky ta kalle ta tace, "Ke dai Fiddausi baza ki canja ba, ban tab'a ji kin yabi mijin ki ba Kullum cikin aibata shi kike duk tarin kulawar da yake miki, wallahi ki canja hali wannan ba daidai bane."
"Rukky karya nayi? Ke kanki kin san ibrahim talaka ne, a cikin mu nida ke da Zakiyya da Ameena waye yake auren talaka kamar ni? Duk da ma ke ba auren ne dake ba amma nasan baza ki auri wanda bashi da komai kamar sa ba."

Rukky ta ajjiye abincin tace, "Wallahi zan aura Fid indai zai rik'e ni hannu biyu zai kula da dukkan hakkina da Allah ya d'ora masa wallahi zan zauna dashi, ni ba kud'i nake hange ba kwanciyar hankali kawai Fid. Kinga Zakiyya da Meena da kike hange; wallahil azim sai ta yu kin fisu kwanciyar hankali, domin kud'i ba shine kwanciyar hankali ba musamman a bangaren zamtakewar aure."
"A ganin ki ba, amma wallahi a wajena kudi sune kwanciyar hankali, ke baki ga yadda Ameena take fantamawa ba komai mijin ta ya zube mata sai k'iba take tana haske kamar tana wanka da madara; kice min kud'i ba shine jin dadi ba....? Wallahi a wajena shine kuma in sha Allah sai na dandale shi nima."

Rukky tace, "Hmm Fidy baza ki tab'a canjawa ba." Fiddausi tace, "Indai Akan kud'i ne wallahi bazan canja ba, daman Keda Amina ai halin ku d'aya tun Muna makaranta, duk rashin son auren mai kud'in da Amina take cewa sai Gashi ta aura ta barki kina neman miji irin Ibrahim." Rukky tace, "Allah ya riga ya rubuta shine mijin ta, kuma daman mu ba mai kudi muke gudu ba, waye yak'i kud'i Fidyy...? kawai in talakan shine zai rik'e mu Allah ya kawo shi ya bar mai kud'in, meye amfanin kud'i in babu kwanciyar hankali...? Kuma wallahi ni ko wanda bai kai ibrahim rufin asiri bane indai zai rik'e ni zan zauna wallahi. Auren fa nake so babu mijin, Akan me zan tsaya zab'e?."

"Kan bala'i, ke a ganin ki wai Akwai Wanda bai kai Ibrahim rufin asiri ba? Kenan shi me za'a Kira shi?, faqiri amma dai ko....? dan ya wuce talaka shi. Wannan fa indomie da kike gani ni na siya da kudina bashi ba, wannan solar da kike gani ni zan had'a bashi ba. Ina rufin asiri a nan?. Wallahi ki yiwa kanki fad'a mu kanmu da muke cikin talaucin so muke mu fita ke kuma kina so ki shiga." Rukky tayi ajiyar zuciya Tana girgiza kai tace, "Wallahi banga talaucin mijin ki ba domin ya tsare miki komai daidai gwargwado, kawai rashin godiyar Allah ce irin taki."

Fiddausi tayi dariya tace, "Baza ki gane ba ai Tunda ba kece a matsayina ba shiyasa."
"To yanzu ke waye ya baki kud'in had'a solar? Dan iya wannan kayan da naga suna shigo dasu zasu yi miliyan, an ina kika samu?."
"Hanyar Allah da yawa take, zan baki labari sai komai ya fad'a."
"Allah yasa dai ba wani abun kike ba" ta fad'a tana cigaba da cin abincin ta.

Fiddausi dariya kawai tayi suka cigaba da hirar makaranta tun lokacin da suna bording school suna ta dariya suna rayuwar da sukayi a can.

Gab da magriba Ibrahim ya dawo lokaci an kammala saka solar ko Ina haske ya d'auka fanka sai wulwulawa take kamar ba gidan ba. Lokacin da ya shigo falon Rukky na zaune Tana danna waya ita kad'ai jin sallamar sa sai ta kalle shi tace, "Sannu da zuwa." Murmushi yayi yace, "Rukayya yau kece a gidan namu? Lallai munyi Babbar bak'uwa." Dariya tayi tace, "ina zuwa bama had'uwa ne kawai, Ina wuni." Ya amsa tare da fad'in, "ya su Maman naki kowa Lafiya?."
"Alhamdulillah."
"Ki gaishe su dakyau" ya fad'a yana kallon fanka ganin ta sabuwa dal ba kamar wacce ta fita ya bari ba.

Fiddausi ce ta fito yana ganin ta sai ya juya ya fita zuwa dak'in sa tabi bayan sa ta samu yana kallon fanka tana shigowa yan kalle ta yace, "fankokin nan wanke su kikayi ne? Sannan naga waje babu wuta ya akayi gidan nan muke da wuta?." Fiddausi tace, "Ba wanke su nayi ba ba kuma wuta bace, sababbi ne ba'a jima da gama saka su ba, wutar solar ce bata nepa ba d'azu na saka aka had'a mana duka gidan. Kaga yanzu ka huta da kwana da mafici a hannu."

Sak yayi yana kallon ta cikin mamakin da ya saka gaban sa fad'uwa yace, "Ban gane me kike nufi ba Fiddausi, yi min bayani yadda zan fahimta."
"Bafa wani abun nake nufi ba, Ina nufin na saka an had'a mana solar kasan kuma dole a canja fankoki a saka na solar shine aka saka."

"Kin saka an had'a solar fa kika ce?."
"Ashe Kaji me nace, na gaji da zama a zafi ne shiyasa." Kama k'ugu yayi yana kallon ta ya sake kallon fankar ya sake kallon ta yace, "A Ina kika samu kudin da zaki wannan aikin? Fiddausi ban gane miki ba kwanakin nan an ina kike samun w haka?."
"Wai Ina nake samun kudi bayan kasan wa yayata take aure, kasan kuma mijin ta yana fitar da zakka duk shekara."

Cikin b'acin rai da fusata yace, "Tun da meyasa bai tab'a baki zakkar ba sai yanzu?, kar ki raina min hankali ki mayar dani yaro k'arami. A Ina kike samun kud'in da kike kashewa kwanakin!?." Itama cikin d'aga murya tace, "Ba Gashi na fad'a maka ba in ba a nan ba a ina nake samun kudin? Kaga Ibrahim bana son zargi in kana ganin hasken bai maka ba sai ka cire na wannan dakin ba lallai ba dole."

A fusace yayo kanta kamar zai mare ta tayi baya da sauri tana kallon sa yace, "Fiddausi zaki fad'a min indai kike samun kudi ko na nuna miki asalin kalar ibrahim a yanzun nan? Ni zaki mayar shashasha?, mijin yayar taki auren ki yake da zai dauki kudi masu yawa ya baki ki dinga wannan facakar?. Wallahi ko ki fad'a min ko ma fasa miki baki."

Waje tayi a guje tace, "Wallahi sai dai ka dake ni amma bazan cire solar ba dan ba kai ka saka ba ba kuma da kud'in ka aka saka ba, Ina ruwan ka da inda nake samun kud'i ai kasan ba sata nake ba ba kuma bin maza nake ba, Baka isa hanani yin abinda naga dama ba wallahi." A fusace ya biyo ta yayo kanta ta fad'a falo a guje yabi bayan ta sam ya manta Rukky tana nan ya nuna ta yace, "wallahi baki isa ba Fiddausi a wannan Karon bazan raga miki ba sai kin fad'a min a inda kike samun kud'i, kin siyo kayan girki da kayan abinci kince min yayar kice ta baki na yarda, naga kudi masu yawa a hannun ki kince na Mama ne na yarda, naga waya a hannun ki kince ta aro na yarda. Yanzu kuma nazo naga anyi solar an kashe kudi sama da dubu d'ari biyar shima kice min wai Yayar ki ko mijin Yayar kine ya baki. Wallahi ko ki fad'a min ko ranki ya 'baci."

"Me kake so nace maka to? Na fad'a maka inda nake samun kud'i ai, kawai dan kai Baka da dalilin su shikenan nima bazan yi ba?. In Baka gaji da zama a duhu ba ni na gaji kuma wallahi dole ka bar solar nan in ba haka ba sai dai mu rabu, na gaji da zama a rayuwar talauci wallahi ni ba kalar matar talaka bace, nayi hakuri iya yina yanzu kuma bazan iya ba!" Ta fad'a cikin ihu tana kallon sa shima ita yake kallo.

Fusata yayi tare da yin kwafa ya juya ya fita kai tsaye inda aka ajjiye battery solar ya nufa ya tsinke duk wayar da take jiki jikin sa har rawa yake sabida b'acin ran da yake ciki, babban tashin hankalin sa bai wuce a ina Fiddausi take samun kudi ba, zuciyar sa sai abubuwa take kawo masa masu muni game da Hakan.




#Comments
#Share
#Vote

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu.
https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

*Book 1*
*Page 16*




Hankalin Rukayya duk ya tashi bata tab'a ganin mata da miji suna fad'a gaban ta ba jikin ta har rawa yake yi hankalin ta ya kai k'arshe wajan tashi sai bin su take da kallo tana dana sanin ma zuwa gidan , a zabure tabi bayan Fiddausi zuwa d'aki ta same ta a tsaye tana mita cikin masifa kamar a gaban sa take.
"Haba Fiddausi!, Haba Fiddausi, mijin ki kike yiwa wannan rashin kunyar har haka? Kuma ko kunya bakya ji a gaban idanuna?."

Fiddausi ta kalle ta tace, "Ke din bak'uwa ta ce? Ko kuma akwai abinda zan b'oye miki ne?. Kinga na gaji da zama da mutumin nan wallahi saki na nake so yayi ko yana so ko baya so, zaman shekara biyar d'in da nayi dashi Allah ya amfana nayi k'okari iyakar iyawata, tura takai bango a wannan lokacin bazan iya ba wallahi." Rukayya mamakin ta kawai take dan bata san rashin hankalin Fiddausi har ya kai haka ba tace, "Wai kina cikin hankalin ki kuwa? Kin samu miji mai sonki da qaunar ki da burin kyautata miki shine kike neman yiwa kanki salalan tsiya?, ne ya shiga kanki ne? Ina ilimin addinin da na sanki dashi?. Kowa a unguwa kwatance yake da mijin ki yana fatan y'arsa ta samu kamar sa amma shine kike fad'ar haka?."

Fiddausi tace, "kee har ilimi in talauci yayi yawa fecewa yake, ki adana wa'azin ki wallahi bazan raga masa ba daman kiris nake jira, bai isa yayi min na kyale ba, solar kuma dole na saka tunda kudina ne."
"A Ina kika samu kudin ke?."
"Wannan kuma sırrı ne bai dame ku ba, Kun San dai ba sata zanyi ba." Girgiza kai Rukayya tayi tace, "Wallahi kin bani mamaki, kin bani kunya, ban tab'a zaton hakan daga gare ki ba. Mijin ki na aure, mijin ki na sunna kike yiwa wannan tijarar a gaban idon b'akuwar ki kuma hakan bai dame ki ba. Mijin ki uban d'anki wanda kika haifa Keda shi kike yiwa wannan wulaqancin kawai sabida wani abun ya rufe miki ido. Kiyi gaggawar neman yafiyar sa in ba haka ba zaki kuskuren da baki tab'a yi ba a rayuwar ki."

Dariya Fiddausi tayi ta tafa tace, "Ai kuskuren nake so nayi Rukayya, indai wannan fak'irin zan bawa hakuri kice za'a tashi kiyama kenan, kuma wallahi bai isa ya hanani abinda nayi niya ba Tunda shi bashi da kud'in da zaiyi min. D'ana kuma dole a dawo min dashi gabana na gaji da zaman gidan nan baya kusa dani." Rukayya da take kallon ta mamaki sai ya hana ta sake cewa komai sai kallo kawai kafin ta bud'e baki tace, "in ma wani yake zuga ki, in ma aljanu ne a akanki Ina baki shawarar kiyi gaggawar neman mafita dan zasu kai ki su baro kine, suna so ki aikata kuskuren da har abada baza ki goge shi ba. Mijin ki ba talaka bane domin ya tsare miki dukkan haqiin ki da yake wuyan sa, ke kinfi matar wani mai kudin Kyan gani sabida kulawar da yake baki. Talaka shine wanda bashi da cin yau bare na gobe ke kuwa kin fin k'arfin abinci" ta sassauta murya kana ta cigaba da cewa,

"Kin samu miji Allah ya rufa miki asiri meyasa kike son tonawa kanki asiri kina d'aga murya maqota suna jinki? Mu da bamu da mijin nema muke meyasa kike wulaqanta naki Fiddausi?. Ina ilimin da ake baki kyauta a kansa lokacin da

Please Login or Register in order to submit comment