Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son rayuwar kud'i amma abin nata yanzu yayi yawa tace, "Fiddausi wai meyasa kike yiwa Ibrahim haka ne? Yana sonki yana kula dake amma sakayyar da zaki masa kenan?."

"Allah ya sani na tsani rayuwar talauci Ameena."
"Kece kike a rayuwar talauncin? Kina da ci da sha da suttura da wajan kwnaciya ki dinga kiran kanki da mai rayuwar talauci?. Mijin ki na kula da duk wata damuwar ki yana sonki to me kike so yayi miki?."

Fiddausi tace, "Kedai ayi shiru kawai. Karb'i ki shanye dan ni in aka barmin ma wallahi bazan sha ba." Aminatou tace, "Nima bazan sha ba domin danke akayi in baza ki sha ba sai ki zubar. Wallahi ki dinga gode Allah domin yayi miki ni'imar da bai iyawa sauran matan duniya ba."
"Hmmm! A hakan wai? A wannan gidan kuma?, Kuma cikin sauran matan har ke?."
"Har ni mana, kin fini da abubuwa da yawa domin mai d'aki ai shi yasan inda yake yo-yo."

Fiddausi tace, "Kar kiyi sab'o mana Ameenatou, me kika nema kika rasa a cikin gidan ki?. Ga kud'i, ga gida mai kyau aljannar duniya, ga mota ki hau wacce kike so, duk k'asar da kike so za'a buga miki visa ki tafi, ga miji mai son ki. Me kike nema bayan wannan?." Aminatou tace, "Wannan abubuwan da kika lissafa a tunanin ki sune farin ciki?."

Fiddausi ta girgiza kai cikin tabbatarwa tace, "Sune farin ciki Aminatou domin kudi ko ba naka bane in kana kallon su dadi kake ji balle ace naka ne, wannan abinda na fad'a su kuma ni na rasa a cikin gidan nawa auren, wata kulawar sa duk ta banza ce tunda buk'atar dubu goma sai ta gagare ni a hakan kuma kice wai ina da abinda sauran mata basu dashi?."

Ameenatou ta bita da kallon baki san komai ba tace, "Wannan abinda kike rainawa shine abinda wata ta nema ta rasa a nata gidan auren, wallahi Fiddausi kud'i ba shine farin ciki ba; soyayyar da mijin ki yake miki itace tsantsar farin ciki a zamantakewar aure. Ki daina hange ki tsaya iya inda Allah ya ajjiye ki, ki dinga kallon wanda suke k'asa dake kar ki kalli na sama in ba haka ba baza ki gode masa ba."

Baki ta tab'e Baki dan ba yarda tayi ba tace, "Hajiya Ameenatou kenan dan bake bace a cikin gidan nan ba shiyasa kike fad'ar haka. Ke babu abinda kika sani sai farin ciki, ga miji bai sonki ga komai Allah ya baki shiyasa kike tunanin yadda kike cikin farin ciki haka kowa ma yake." Aminatou ta yafa mayafinta ta Fiddausi ta d'aukar mata Zaitun ta d'auki Jakarta ta buɗe ta d'auki kudi ta ajjiye mata tace, "Amir na bawa bake ba."

Fiddausi tayi dariyar nishad'i tace, "Ai kinga irin abinda nake fad'a miki, inda nice a irin rayuwar da kike ciki wallahi bazan yi k'orafi akan komai ba koda kuwa mijin nawa Kullum zai Zane ni ne." Ita dai bata sake ce mata komai ba dan ta gaji da bata amsa ta raka ta har bakin mota ta shiga taja motar ta tafi ita kuma ta koma gida zuciyar ta cike da son rayuwa irin ta Ameenatou, ji take a ranta duk tsanani duk wahala itama sai ta zama kamar Ameenatou hakan shine burin ta kuma sai ta cika shi.


#Vote
#Share
#Comments
#F5
#Book1
#Nana Haleema.

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*


https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36


*Book 1*
*Page 3*


Yusuf kai tsaye katafaran store d'in sa mai hawa uku da yake kan titin zoo road ya nufa, store ne babba wanda babu abinda ba’a siyarwa, tun daga kan kayan abinci, kayan wuta, kayan sakawa da sauran su. tunda aka hango motar sa aka buɗe gate ya shiga mutane suka zo suka zagaye shi ana kawo gaisuwa ya sallame su ya wuce can k'arshe saman ya shiga office d'insa.

Kulle k'ofar yayi ya k'arasa wajan taga ya d'aga labule yana hango mutanen da suke shige da fice a cikin store d'in duk wanda ka gani ka ganshi da k’atuwar Leda a hannun sa yayi siyayya wasu kuma da karama. ya saki labulen ya zauna a akan kujara maganar Ammah tana sake dawo masa cikin zuciyar sa. "Meena" ya furta a bayyane yana jin jikin sa yana sake yin sanyi sosai tausayin ta yana sake shiga jikin sa musamman in ya tuna alqawarin da ya yiwa mahaifin ta.

Waya ya d'auko a aljihu da niyar kiran ta sai kira ya shigo wayar, sunan My love shine yake yawo akan screen d'in wayar ya furzar da iska kamar bazai d'auka ba sai kuma ya d'auka ya saka a kunne kafin yace, "Zan kira ki." Datse kiran yayi ya kirata ta d'auka kawai sai ta fashe masa da kukan da baya son ji.

Lumshe ido yayi ya buɗe yana jin sautin kukanta har cikin zuciyar sa yace, "Kukan na meye?." Bata daina ba sannan bata bashi amsa ba sai sake k'ara d'aga murya take yi hakan ya saka shi yin shiru yana sauraren ta kusan mintina biyu a haka sannan ta sassauta kukan tace, "My love kana sona kuwa?."

Yadda muryar ta take rawa ya tabbatar masa da kukan gaske take yi kuma daga zuciyar ta yake sai ya sauke numfashi yace, "Ina sonki mana My love, kinfi kowa sanin ina sonki."
"Amma me ya hanaka turowa gidan mu har yanzu? Kasan da cewa su Baba suna niyar yi min auren dole?."
"Wanne irin auren dole kuma My love?" Ya fad'a da mamaki da kuma tsoro.

"Nidai kawai kazo gida kafin zuciyata ta buga, kai nake so kuma kai nake qauna in suka rabani dakai ban san inda zan saka raina ba. Dan Allah kazo."
"Shinenan my love kwantar da hankalin ki, in akayi sallar la'asar zanzo amma ki daina wannan kukan dan Allah kin san bana so ko?."
"Taya zan daina kuka bayan ana so a raba mu?."
"Babu wanda zai raba mu My love, ni mallakin kine in sha Allah. Ki daina wannan kukan yana tab'a min zuciyata.”

Asiya tace, "Shikenan my love, na daina sabida kace baka so amma kazo gida anjima." Yusuf yace, "in sha Allah zanzo, kar ki damu."
"Me zan dafa maka?."
"Abinda nafi so" ya fad'a yana murmushi itama tayi murmushin tace, "Tohm sai kazo. Ina sonka."
"Nima ina sonki My love." Murmushi sukayi a tare ya yanke wayar yana sauke numfashi har lokacin murmushin yake yi dan yana matukar jin dadin hira da Asiya.

Knocking d'in k'ofar akayi ya bada umarnin shigowa aka shigo kai tsaye inda yake zaune wanda ya shigo yayi ya zauna kusa dashi yace, "Yusuf yane? Na d’auka ma bazaka shigo ba." Yusuf ya kalle shi yace, "Kasan na dawo ne?." Usman yayi murmushi yace, "Nasan ka dawo mana tunda gashi har nazo nan kai tsaye. Gwara da ka dawo ai akwai abubuwa da yawa wanda ake jira kayi approving, akwai wanda suka kawo kaya suna so a karb’a a fara siyarwa cikin shopping store.”

Yayi k'aramin tsaki yace, "Dole sai ni? Wai meye amfanin kane Usman?." Shima ya kalle shi yace, "Akwai abinda bani da amfani dole kai ake nema bani ba. Akwai wata mata da tazo min da buk'atar tana son kawo irin kayan zak’i kamar su alawar madara haka da sauran su, amma ban karba ba dan nasan baza’a saka kaya a cikin store babu nafdac ba kuma a yanayin ta kamar bazata iya aikin nafdac ba.”
"To yanzu meye amfanin fad'a min?" Ya fad'a yana kallon sa cikin jin haushi.”

Usman yayi dariya yace, "Sabida gabad'aya Store d'in mallakin kane ba nawa ba, aikina sai Baka nan yanzu kuma kana nana.” K'aramin tsaki ya kuma yi ya zubawa waje d'aya idanu alamun tunani Usman da yake kallon sa yace, “Me yake damun ka ne?.” Ya kalli Usman d’in yace, "Ammaa fa ta matsa min akan bazan auri Asiya ba Usman, ban san meyasa Ammah bata son na auri Asiya ba."

Usman yace, "bawai bata sonta bane ba Yusuf tana guje maka fad'awa matsala ne, kwata-kwata kwanan ka nawa da auren Ameena har da zaka fara tunanin wani auren dan Allah?. Y’ar ku fa har yanzu goya ta ake ko makaranta bata shiga ba ai dole Ammah ta hanaka, ban ga amfanin ma yin auren ka a yanzu ba wallahi, gabadaya ka canja ka koma kamar ba kai ba.”

Ya kalli Usman yace, "Amma bakwa tunanin dole ce ta saka zanyi auren?."
"Fad’a min wacce irin dole ce wannan Yusuf? Kai da kanka ka fada min babu abinda ka rasa wajan matar ka to meye dolen?."
"Ka sani ko akwai ya kasance sirri shiyasa ban fad'a ba?."
"Maybe hakan ne, amma a shawarce ka jinginar da batun nan tunda bata so, ka jira zuwan lokacin in Allah yayi matar kace zaka aure ta. Akan Asiya ka canja gabad'aya Yusuf matar ka gabad'aya bata jin dad'in zama dakai, har kana iya daukar k'afa ka bar ‘kasa ka kwashe wata da watanni kawai dan kana tunanin ita take zuga Ammah baka tunanin halin da zata shiga dan kawai tana da haƙuri kuma bata da iyaye.”

Yusuf ya kalle shi kamar zai magana sai ya share Usman yace, "Dole ka kasa magana ai Yusuf, yadda kake son Ameena take sonka wallahi ban d’auka zaka iya yi mata kishiya bama balle ka d'auko auren a wannan lokacin da baku jima tare ba. Ga abubuwa kala kala da kake mata kawai dan ka gama yayin ta kana hangen wata. Duk abinda ya faru Ammah tana sanar dani amma ni na rasa daga inda kake samo wannan halayen.”

Ya kalli Usman yace, "Ni nace maka na gama yayin Meena? Ina son matata har gobe babu abinda ya ragu a son da nake mata."
"K’arya ne wallahi, inda kana sonta da baka yi abinda kake mata ba, da da kake sonta ai ko saurayi Baka so ka gani a k’ofar gidan su, kafin ma ka aure ta kenan amma yanzu daka aure ta sai komai ya canja.”
"Hmmm!." Jin abinda Yusuf d'in yace ya saka Usman mik'ewa yace, "Kowa dai ya aikata daidai ya sani, in ya aikata ba daidai bama ya sani. In ka cuci yarinya kamar ta mai hakuri da maraici Wallahi Allah bazai barka ba, Kaga tafiyata" ya fad'a yana fita ya barshi zaune ba tare da ya motsa ba.

Sai da yaji k’arar rufe k’ofa sannan ya motsa daga yadda ya zauna ya sauke numfashi yace, “Ban San abinda zanyi ba, komai ya tsaya min cak” ya fad’a yana dafe kansa cikin rashin sanin abinda ma zaiyi.

*☆☆☆☆*

"Umma munyi waya ya tabbatar min zai zo bayan la'asar" Asiya ta fad'a tana kallom Umma da take zaune ita da k'awar ta. K'awar ta wacce suke kira Umma Sakina tace, "ai kina yi masa girki yaci ko?."
"Eh Anty, dan yanzu ma yace na dafa masa abinda yake so."
"Yauwa yar gari. Karb’i wannan ledar" ta fad'a tana mik'a mata leda ta karb'a kafin tace, "Ruwan rubutu ne, duk abinda zaki dafa masa ki zuba shi a ciki da zarar yaci shikenan mun sake kamo wuyan sa, ba matar sa ba ko babar sace matsalar wallahi sai ya aure ki na tabbatar miki da wannan."

Asiya tayi dariyar farin ciki tace, "To Umma Sakina na gode." Itama murmushi tayi tace, "jeki ki fara shirya masa abincin kizo akwai turarukan da zan baki ki shafa kafin yazo." Da zumud'i ta juya ta tafi Umma Sakina ta kalli Umma tace, "Sai munyi maganin Yusuf, in ma matar tasa take hana shi zata gane kuren ta, ai tunda ya kawo k’afar sa ahlin mu wallahi bai isa ya kubce ba.” Umma ta bata hannu suka tafa cikin farin ciki tace, "Haba ai gwara, abu yak’i ci yak’i cinyewa kusan shekara ana abu d'aya babu cigaba. Ta auri Yusuf ai mun warke wallahi."

Umma Sakina tace, "Ai wallahi hatta kud'in kayan gadon da zamuyi mata a hannun sa zamu karb'a, haka in ta shiga cikin gidan nasa ma a hannun sa zamu b'anb'aro na auren y'an uwanta. Taya muna ji muna gani zamu bari wannan daula ta wuce mu?." Suka sake yin dariya tare da tafawa Umma tace, "Shiyasa nake mugun yinki aminiya, Allah dai ya bamu sa'a." Ta amsa da amin suka cigaba da hira.

Cikin lokaci kad'an Asiya ta dafa masa farar shinkafa da wake kamar yadda tasan yana so ta yanka salad da kayan had'in sa ta daka masa lafiyayyen yajin tafarnuwa harda nama ta had'a a ciki ta soya man gyad’a da albas sai khmashi yake ta had'a su waje d'aya.

Wanka taje tayi bayan ta fito tayi sallar la'asar dan tasan baya African time tunda yace mata zai zo bayan la'asar a lokacin zata ganshi. Cikin sauri ta shirya cikin doguwar riga ta atampa ta d'aura d'ankwali tayi kyau sosai ta fito zwau wajan Umma da Umma Sakina da suke hira. Umma Sakina ta bita da kallo tana murmushi tace, "kinyi kyau amaryar Yusuf, amma hausawa sunce in kana da kyau ka k'ara da wanka. Karb'i turaren nan ki shafa shi yadda zai dinga tashi a jikin ki sosai" ta fad'a tana bata k'aramar kwalbar ba musu ta karb'a ta shafa d'in lokaci d'aya d'akin ya garwaye da khamshin sa mai sanyi da kwantar da hankalin mai jin sa.

Umma tace, "Sakina wannan turaren akwai khamshi sosai ni kaina ya burge ni." Ta kalli Umma tace, "Sannan kuma akwai aiki, zaki ga abinda zai biyo baya" ta sake kallon Asiya tace, "A ina kuke zancen?."
"A d’akin Baba na waje."
"To had'a garwashi yanzun nan ki kona wannan turaren a falon " ta fad'a tana sake bata wani turaren ta karb'a Umma Sakina tace, “in ma babu garwashi ki samu wannan gawayin da ake saka masa ashana ya kama kije Kiyi da sauri kafin yazo.” Da to ta amsa ta fita.

Ba jimawa ta dawo suna ta hira da Umma ta wuce ta shiga d'aki lokacin taga wayar tana haske alamun Kira yana shigowa. Mayafi ta yafa ta fito ta kalli su Umma tace, "Umma yazo." Umma sakina tace, "Kar ki nuna masa kina cikim yanayi mai dad'i ki marairaice kita kuka yadda zai kasa gane kanki, ki fad'a masa kefa indai bai turo a wannan lokacin ba kawai zaki gudu ki bar garin nan. Kiyi masa abinda zai karya masa zuciya kar ki barshi da wani gurbi na sukuni a wannan lokacin."

Asiya tace, "zanyi hakan Umma Sakina."
"Yauwa. D'auki abincin da ruwa da lemo ki fitar masa dashi ki kuma tabbatar yaci." Nan ma ta amsa ta d'auki tray d'in da ta had'a komai ta fita ta fara ajjiye tray d'in a falon sannan ta fita suka shigo tare dashi har cikin falon.

Khamshin dakin ya fara dukan hancin sa ya kulle ido ya buɗe jin kamar an tsira masa allura a zuciyar sa lokaci d’aya yaja numfashi dan khamshin ya masa dad'i ya kalle ta yaga fuskar babu walwala ya matso kusa da ita yace, "My love yane?."

Tana sane tayi wani irin juyi khamshin jikinta ya tashi ya sake dukan hancin sa bai san lokacin da ya lumshe idanun sa ba ya buɗe ya furta, "Wow!” Ya furta a hankali a kuma sanyaye dan khamshin yayi mata dad’i sosai. Ganin yanayin da ya shiga sai farin ciki ya kama zuciyar ta tace, "to ka zauna."

Idanu ya buɗe yana kallonta gani yake kamar an sake k'ara mata kyau k'aunar ta na sake shiga ransa ya zauna d'in ta tsuguna kusa dashi tana zuba masa abincin ta mik'a masa tare da sunkuyawa saman k'irjin ta ya bayyana ta gaban rigar.

Da bak'in lalle ta zana kalmar Y da babban bak'i a kan fatar k'irjin ta hakan da tayi ya bashi damar ganin abinda yake zane a kai daman tana sane tayi hakan dan ta sake jawo hankalin sa tayi kuma da alama hak’ar ta ta cimma ruwa. Motsawa tayi tana sane k'irjin ta ya motsa ya taune lab’b’an sa yaja numfashi amma ya kasa d'auke idanun sa daga kai.

Komawa tayi da baya ta zauna a k'asa shi kuma yana kan kujera tace, "To kaci sai muyi magana, kasan bana so kana zama da yunwa." Kamar soko haka ya fara cin abincin kamar daman umarnin ta yake jira, ganin yaci farin cikin ta ya sake ninka na baya tana nan zaune amma bata nuna ba har yaci rabin wanda ta bashi yasha ruwa.

Ganin ya gama sai kawai ta fashe masa da kukan shagwab’a yanayin fuskar sa ta canja hankalin sa ya tashi ya sakko ‘kasa kusa da ita yana kallon ta yace, "My love kina so na mutu ne?." Ta d'ago idanunta cike da hawaye haka fuskar ta tace, "Nima kana so na mutu ne My Love? Kana kallo ana so a raba mu da kai amma ka kasa yin komai. Shekarar mu kusan biyu tare amma har yanzu babu wata magana mai k'arfi a tsakanin mu, ni na fara tunanin anya ma ba yaudarata kake ba?” ta sake fashewa da kukan da tasan dole ya shiga zuciyar sa.

"Ba yaudarar ki nake ba My love ina sonki Allah ya sani, kuma ina burin auren ki. Dan Allah ki daina kuka."
"Taya zan daina kuka bayan baka mayar da hankali akan auren nawa ba? Taya kake so na amince da zaka aure ni da gaske?. Ni wallahi guduwa zanyi na bar garin nan kawai tunda baka sona bazan iya auren wani in ba kai ba."

Hankalin sa ya tashi gabadaya baya so yaji tana kuka ko kad’an ya gigice yace, "Haba My love, dan Allah ki daina fad'ar haka ni mallakin kine har abada. Kin san ina sonki ina kuma qaunar ki fiye da komai a duniya, ni da ace ke na fara samu tun farko banga wata macen da zan kalla a duniya ba balle nayi niyar auren ta, sai yanzu Allah yayi zan same ki dan haka ki kwantar da hankalin ki. Ki daina kuka ki nutsu ki fad'a min me kike so ayi."

Bata daina kukan ba ya sake cewa, "in kina so nayi kukan Nima sai ki cigaba."Share hawayen ta tayi ta kalle shi yace, "me kike so?."
Cikin muryar kuka tace, "Kawai ka turo cikin satin nan ayi maganar auren nan a wuce wajan."
"Bama iya maganar aure ba har auren za'ayi my love, ni kaina na k'agu ki zama mallakina a yau d'in nan inda ke mallakina ce Allah kad'ai yasan irin soyayyar da zan nuna miki My love. Ina tabbatar miki aurena dake bazai wuce nan da wasu kwanaki kad'an ba, ko meye zanyi indai zan mallake ki, zan iya rabuwa da komai a kanki.”

Yadda yake maganar ya tabbatar mata da gaske yake har zuciyar sa yake maganar tace, "Da gaske kake?." Ya d'aga kai yana murmushi yace, "Da gasken gaske nake My love. Ina tabbatar miki da zuwa gobe zaki ji an kira Baba an sanar dashi za'a zo neman auren ki, ina sonki ina so na rayu dake nima."

Kawar da kai tayi ya kalle ta yace, "To kiyi murmushi mana." Murmushin tayi shima yayi tare da sauke ajiyar zuciya yace, "Har naji dad'i da naga kina murmushi my love" wayar sa ta katse shi ya juya ya kalli mai kiran sai ya kashe k'arar ya dawo da kallon sa a gare ta yace, "Shikenan abinda kike so?."

Tace, "Daman ai duk abinda nake so a bayan ka yake My love."
"Nima haka My love, ina ji ina ma na zama mallakin ki a yanzu dana hango wani abu." Kallon sa tayi kamar bata san me yake nufi ba tace, "Me ka hango?."
Ya d'aga gira sama yace, "wani abu ne na gani kamar farkon sunana aka zana a wani waje mai mahimmaci.”

Rufe fuskar ta tayi alamun kunya yayi dariya yana kallonta Allah ya sani shidai yana sonta musmaman a yau ji yake kamar ana k'ara masa qaunar ta a zuciyar sa ji yake koma meye zaiyi a kanta. Hira suka cigaba da yi ta soyayya kafin ya tashi zai tafi itama ta tashi tana kallon sa yana kallonta yace, "My love zan iya yin wani abu?." Ta kalle shi tace, "me kenan?."
"Kamar haka...." ya fad'a yana jawo hannunta ya had'a jikin sa da nata ya rungume ta sosai a jikin sa dan ji yake in bai had'a jikin sa da nata ba a wannan lokacin zai iya shiga wani yanayin khamshin turaren ta ya tayar masa da hankali sosai badan ya daure ba bai San abinda zai iya ba.

Luf tayi a k'irjin sa tana shak'ar nasa khamshin mai dad’i tana Jin wani irin farin ciki jin ta a jikin sa, sai kuma ta fara kwacewa tana fad'in, "My love kasan bana son irin haka ko?." Sakin ta yayi yace, "I'm sorry, na kasa sarrafa kaina ne yau, ni nake kamar ana zuba min sonki a raina My love. Kiyi haƙuri banyi da niya ba."

"To kar a sake" ta fad'a tana d'aure fuska kamar gaske. Yayi murmushi yace, "Baza'a sake ba har sai kin zama tawa." Murmushi tayi shima haka ya d'auko kud'i a aljihun sa masu yawa ya mik'a mata yace, "A cigaba da siyan turare mai khamshi ana sakawa in zanzo kawai ba in za’a fita ba.”

Ba musu ta karb'a tace, "An gode." Baice komai ba ya kalle ta yace, "Bance a raka ni waje ba ki shiga ciki bana so wani ya ganki." Dariya tayi tace, "My love sarkin kishi, shikenan a gaishe min da Daughter Zaitun. Har Antyna ace ina gaishe ta." Kai kawai ya d'aga mata ya fita daga gidan zuciyar sa tana fad'a masa ko ana muzuru ana shawo sai ya auri Asiya a cikin wannan lokacin.


Ya jima zaune a mota yana tunanin hanyar da zaibi waja shawo kan Ammah ta amince akan maganar nan dan itace kawai Matsalar sa tana amincewa zance ya k’are, kai yake girgizawa dan yadda yake jin zuciyar sa indai bai aureta ba akwai matsala shiyasa yake son nemo hanyar da zai aure ta da gaggawa.
"Ameena itace kawai maganin matsalar nan" ya fad'a a bayyane yana shafa goshin sa kafin ya kuma cewa, "Tabbas itace kawai zata samu Ammah da maganar ta amince.” Sai kuma ya d’aga kai sama ya sauke numfashi yace, “Anya Ameena zata amince da hakan? Tana sona sosai tana kishina zata iya samun Ammah da maganar aurena?.”

Shiru yayi na wani lokaci kafin yace, “tabbas itace zata yi min wannan aikin domin tana son dukkan abinda nake so, Ameena tana da k’arancin wayo dana tsarata na nuna mata soyayya shikenan komai ya wuce, tana sona da wannan soyayyar zanyi amfani tayi min amfani” ya fad'a yana kunna motar ya bar unguwar a guje.

#Vote
#Share
#Comments
#F5
#Book1
#Nana Haleema.

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36


*Book 1*
*Page 4*


A guje Asiya ta shiga gida tana shiga falon ta fad'a jikin Umma Sakina tana ihun murna da farin ciki, Umma Sakina ta rik'e ta tana dariya tace, "Buk'ata ta fara biya ko?." Asiya ta d'ago daga jikinta tana dariya farin ciki ya cika fuskar ta tace, "Wallahi Umma Sakina bai tab'a nuna min soyayya kamar yau ba, bai tab'a min magana ta hankali wacce zata tabbatar min da gaske zai aure ni ba sai yau. Kinga yadda jikin sa yake rawa da ina kuka? Sai fa da ya sakko daga kan kujera ya tsuguna yana rarrashina. Umma Sakina Allah ya bar mana ke" ta fad'a tana sake rungume ta cikin farin ciki.

Umma Sakina tayi dariya mai sauti ta d'ago ta d’aga jikinta tace, "Ai na fad'a miki abinda yaci da abinda ya shak'a ba abubuwa bane masu sauk'i, zasu ta tasiri a jikin sa har sai yaga ya aure ki hankalin sa zai kwnata. Yau yana nan yana fama da muguwar qaunar ki da kuma sha'awar ki bashi da burin da ya wuce a yanzu yaga ya mallake ki. Shin baiyi yunƙurin tab'a ki ba?."

Asiya tace, "Abinda bai tab'a min ba

Please Login or Register in order to submit comment