Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shanye ya ajjiye kofin ya mik'e tsaye tace, "ka bada kud'in kayan miya." Ya kalle ta ita sam bata damuwa da yana dashi ko babu akwai a bata shine burin ta a ko da yaushe ya girgiza kai yace, "bani dasu, akwai manja ina da wake ina kuma da yaji ayi shinkafa da wake, zan tawo da kifi in hakan ya samu."
"Kifi kamar wasu maguna, haba dan Allah ina laifin tsire ma?. Mtsww" ta fad'a k'asa-kasa tana kallon sa.

Kamar bai jita ba ya share ta tace, "Kud'in kalanzir din da za'a dafa waken." Ya bita da kallo dan ta fara fusata shi kafin yace, "wallahi bazan siya ba, naga ragowar gawayin a kitchen yanzu ki dafa dashi in baza ki iya ba ki barshi."
"Nifa wallahi ba kalar aiki da gawayi bace."
"Sai Allah ya kawo ki gidan wanda yayi kala da aiki da gawayi dan haka sai Kiyi hak’uri. Kullum magana d’aya babu canji?.”

Ta tab'e baki tace, "K'addarar aure ce amma in ba haka ba ina ni ina gidan nan?" ta fada a ciki bata san ya jita ba ya sake yi mata banza ta kalle shi tace, "Yauwa ankon bikin k'awar mu na fad'a maka dubu goma ce atamfar ana ta bayarwa nice ban bayar ba." Bai kulata ba ya d'auki hular sa ya skaa ta sake cewa, "kaji fa mai nace. Kawayena duk sun siya kasan su masu kud'i suke aure kaima ba kaso ace nice na fita daban a cikin su ba."

Ya kalle ta yace, "Fiddausi hangen masu kud'in da kike yi kina ganin Sune masu jin dad'i kina Raina taki ni'imar da Allah yayi miki wataƙila a cikin su akwai wacce take sha'awar taki rayuwar, har take je ina ma itace a matsayin ki. Ki gode Allah a duk inda kika samu kanki ba ki dinga hangen wanda ya fiki ba. Indai zaka kalli na sama da kai baza ka gode Allah ba, in kin tashi ki dinga kallon k'asa."

Dariya tayi ta rainin hankali tace, "Amma Ibrahim ka bani dariya wallahi, yanzu waye zaiyi sha'awar rayuwa a wannan gidan? Gida mai d'aki uku da band'aki d'aya a tsakar gida da fallan kitchen?. Gidan da ake aiki da gawayi wata rana ma abincin gagarar mai gidan yake, har yaushe muka fara cin abinci sau uku a rana Abban Amir? Ka manta wai da wannan?, a haka za'a so rayuwata?. Kaima dai fad'a kake kaf kawayena babu wacce zata so wannan rayuwar. Ameena babu abinda ta rasa in taga dama sai tayi shekara goma bata Nigeria me irin su zasu so a tawa rayuwar?. Rayuwar k’unci da rayuwar talauci” ta fad’a tana sake kallon falon da suke tsaye.

_Ameena dai._ ya furta a ransa dan babu ranar da zata fito ta koma batayi misali da Ameena ba, a cikin kawayen nata ma tafi sha'awar ta sabida mijin ta yafi kud'i da yarinta, ko yaushe cikin hangen rayuwar Ameena take bata tab’a godewa duk abinda ya kawo mata. Baice komai ba ya juya kawai ya fita ta bishi da kallo tana k'arewa gidan kallo tace, "Ina ma nice a gida irin na Ameena?. Ga kud'i, ga komai sai ka barshi, baka da damuwar komai domin kud'i sune maganin damuwa a wannan zamanin, in kana dasu kallon su kawai ya isa ya saka ka farin ciki balle ace naka ne. a haka wai yace akwai mai sha'awar rayuwata, Mtswww sai dai in almajira" ta fad'a tana shigewa d'aki zuciyar ta na sake tabbatar mata da duk inda kud’i yake shine farin ciki.



#Nana Haleema
#FitattuBiyar
#May2024
#Book1
#Wattpad and ArewaBooks.

*MAI ƊAKI...!*
FitattuBiyar

©️ *Nana Haleema.*

https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36


*Book 1*
*Page 2*


Yadda take kallon sa idanun ta kyam a cikin nasa tana tab'e baki zaka d'auka d'anta ne ko kuma k'anin ta wanda suke sa'anni ita dashi, kana kallon irin kallon da yake masa zaka tabbatar babu girmamawa a lamarin, duk abinda yake fad'a girgiza kai kawai take yi alamun maganar ba shigar ta yake yi ba kawai dai tana jira ya kai k'arshe ta d'ora da abinda yake bakin ta itama.

Duk da yana lura da kallon da take masa bai fasa fad'ar abinda yake fad'a ba yace, "Kina ji Atika?; Y'an mata uku ne a gaban mu ga babbar yayar su bazawara kinga guda hud'u kenan dukkan su babu manema, shekaru kullum ja suke gaba suke yi ba baya ba, yau in muna raye bamu da tabbacin zamu kai gobe a raye. Wannan dalilin ya saka na yanke hukunci ko nace muka yanke hukuncin zamu had'a su aure da y'an uwan su domin rufawa juna asiri."

Wacce ya kira da Atika ta gyara zama tace, "Ina jinka." Ya sake cewa, "D'an wajan Yayata Saifu kenan kinga yana da hankali da sa'ana kuma yana da aure da yara ya rik'e su da mutunci na tabbata muka bashi Maimuna zai rik'eta hannu biyu daga ita har yaran ta, shi kuma Kalamu ya nuna yana son Fauziyya me zai hana bazata amince ba tunda ta kammala karatun nata? In muka rage biyun kinga saura biyu ko babu komai za'a daina wayo damu a baki a cikin unguwar nan ana cewa sunk'i aure Muna jiran mai kud'i."

Ta tab'e baki tace, "To banda abin Alhaji sai me dan anyi yawo damu a baki? Ai ni da y'ay'ana bakin mutane babu abinda zai mana, inda baki yana fitowa a jiki da yanzu kaf jikina zagi ne da bakin mutane ne, musamman en uwanka da y'an unguwar nan meye basa cewa a kaina?.

"A'a Atika, in kasan bakin wani baka san na wani ba. Abinda ya kamata ayi shi na fad'a miki, kullum addu'ar mu Allah ya kawo musu mazajen aure kuma....." ta dakatar dashi ta hanyar fad'in, "Dakata Alhaji! Tun bayan da karayar arzuk'i ta same ka akwai wanda ya tab'a bani sabulu a cikin y'an uwan ka yace na kula da yarana?, nice nake fad'i tashin neman abinda zan rufa mana asiri har muka kawo wannan mataki. Yanzu kuma kwatsam sai azo da wani batun auren dole akan y'ay'ana? Auren ma kuma da y'ay'an y'an uwan ka?."

"Atika waye yace miki auren dole ne? Duka yaran nan su suka ce suna son su ba had'a su akayi ba ai baza ki kira shi da auren dole ba."
"Kaga Alhaji, ko auren had'i ne kona soyayya ban amince dashi ba wallahi. Babu wanda ya isa ya yiwa y'ay'ana auren dole ko auren cushe sai wanda ya gansu yace yana so suna so suma. Kafi kowa sanin harka da y'an uwan ka ba so nake ba domin tun farko ba k'auna ta suke ba dan haka kowa ya kama gaban sa shida yaran sa."

Kallon ta kawai yake yi yana jin duk abinda take cewa domin kuwa daman yasan ta gama raina shi gabad'aya bata ganin girman sa kamar ba mijin ta ba in tana yi masa magana, tunda ta fara d'aukar d'awainiyar da shi ya kamata ya d'auka a gidan shikenan dan ta kalle shi ta fad'a masa magana ba wani abun bane, wani lokacin tana mantawa mijin tane sai ta gama fad'ar maganar son ranta take tunawa, In tana yi masa fad'a kamar d'an da ta Haifa haka take yi. Ya sauke numfashi yace, "Yanzu so kike mu saka su a gaba muna kallo kenan?."

"Allah zai kawo musu har inda suke amma ban amince da auren dangin nan ba, daman ana musu kallon marasa tarbiyya in suka auri ahlin ka nan gaba shiga dangin sai ya gagare su ko kuma ace musu kafurai,. Bazan lamunta ba wallahi kowa yaje ya aura a waje har gida Allah zai kawo musu, duk wata mace da mijin ta a duniya sai dai in Allah bai rubuta zatayi auren ba."

Kai yake girgizawa kafin yace, "Ina da iko da y'ay'an nan kamar ke, ina da ikon aurar dasu na nemi shawarar kine dan kin kasancewa uwa a wajan su amma da zan iya yanke hukunci sai dai kiji labari." Tayi shewa tare da tafa hannu tana yi masa wani kallo na raini tace, "Allah Alhaji? A hakan yanzu akwai iko a tare dakai? Har kana da bakin ma fadar haka?. ai tun ranar da na d'aukewa y'ay'ana ci da sha, suttura da kud'in makaranta daga ranar na koma mijin ka koma matar. Me kake mana a gidan nan da zaka kalle ni kace min wai kana da iko dasu? Ai wallahi da kayi gangancin had'a auren nan da kayi gagarumar dana sani wacca Baka tab'a yi ba. Nice nake da iko da y'ay'ana bayan ni babu wani domin nice nasan wahalar su tsahon shekara goma sha, banga wani mai iko dasu bayan ni ba, kuma wallahi baza'a ayi auren nan ba."

Ransa yaji ya b'aci sosai ya kasa furta ko wacce kalma sai kallon ta da yake yi, ya rasa meyasa duk abinda mace tayi maka a rayuwa akwai ranar da zata yi maka gori akan abun musmaman in wani abun ya had'a ku da itaa, balle kuma ace itace take d'aukar nauyin gidan ka daga ranar kai da banza duk d'aya. Baice komai ba ya tashi ya fita daga falon ta bishi da kallo tana fadin, "Ina dalili, nida wahala wani k'ato da aurar mu da yara? Wallahi bazata sabu ba wai bindiga a ruwa. Fauziyya!" Ta fad'a da k'arfi tana kallon wata k'ofa da take falon aka amsa daga ciki suka fito.

Mata ne guda hud'u duk suka fito dukkan su kansu d'aya sai dai d'aya tafi d'aya kiba da haske da kuma shekaru. Suka zauna babbar cikin su Maimuna tace, "Umma lafiya?." Umma tace, "Baban kune yazo min da wani zance, wai sun yanke hukuncin zaki auri Saifu ita kuma Fauziyya Kamalu yana sonta." A tare suka kalli juna suka kalli Umman kafin Fauziyya tace, "Amma dai Umma baki amince ba?."

"Har abada wannan abun ai ba mai yuwa bane ba, akan wanne dalili ana so a rabu da talauci suna k'okarin sauke mayar damu cikin sa. Ke Asiya wai ya maganar Yusuf ne? Kwana biyu bana ji ko waya kuna yi?." Wacce aka kira da Asiya ta tab'e baki tace, "Umma matar sa fa so take ta raba mu, tak'i bada ko wacce irin dama da zai aure ni, banda had'a shi da babar sa babu abinda take yi ya rasa yadda zaiyi. Jiya ya dawo mukayi waya kamar zai min kuka yake sanar dani irin fad'an da ta saka aka yi masa, amma anjima yace min zai zo."

Anty Maimuna tace, "Umma maganin uwar gidan ya kamata muyi tun yanzu, bazai yu muna ganin arzuk'i yana hararo mu tana k'ok'ari b'arar mana dashi ba. In ma fitar da ita ne a fitar da ita daga gidan ta k'arfi da yaji domin daga ranar da Asiya ta shiga gidan Yusuf shikenan kakar mu ta yanke sak'a wallahi. Duk wannan wahalar kin daina Umma sai dai ta aiko a kawo mana, haka kawai bata isa ba wallahi, ai yadda Yusuf yazo gidan nan da niyar yaudara ya gudu muka kamo shi ya kasa tafiya ai Uwar gidan sa ba komai bace."

Wacce tunda ake maganar bata ce komai ba mai suna Momy tace, "Gaskiyar kine Anty Maimoon, maganin ta za'ayi ko bata so. Wannan k'aton gidan ga mota kullum matar bata k'asar nan, wallahi can zan koma da zama ko k'asar zaki bari muje tare."

Umma tayi dariya tace, "Kwantar da hankalin ki uwata aure kamar anyi an gama ko matar tasa bata so, ita ba'a auren aka aure ta?, ai Tunda yazo gidan nan wallahi yazo wuya" Ta d'auki waya tana fad'in, "Bara na nemo Umman Ku Sakina a waya yanzun nan mu san abin yi, bana bin malamai amma akan wannan auren zan fara. Ku hud'u a gabana d'aya ta samu miji ana neman ayi min sagegeduwa wallahi bazai yu ba" ta fad'a tana saka wayar a kunne.

"Hajiya Sakina ya gida?." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tayi dariya tace, "Bari kedai kawai, labari sai kin shigo ma."
"Au zaki zo anjima?." Ta sake yin shiru tace, "Allah ya kawo ki ina jiran ki" daga nan ta kashe wayar ta kalli y'ay'an nata tace, "Kuje a d'ora mana abinci rana tana yi, kuyi mana taliya jellop a saka ragowar naman jiya a ciki. Ina zuwa" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki Momy ta tashi ta nufi kitchen su kuma kowa ya fara aikin danna waya.

*☆☆☆*

Tunda ta farka take aikin gyara inda take gyarawa, ta yiwa yarta wanka ta shirya ta cikin kaya masu kyau sai khamshi take ta gyara d'akin da falon tas sai tashin khamshi yake yi. Ita tayi wanka ta saka doguwar riga mai kyau ta saka hula a kanta sannan ta sauka k'asa.

Masu aikin ta yarinya da kuma mai shekaru ta samu suna ta aikin gyara k'asan duk da baiyi wani dauda ba amma kullum sai sun gyara. Da murmushi ta k'araso tana fad'in, "Barkan ku da aiki." Tare suka juyo ko wacce tace, "Barka da safiya Hajiya."
"Barka, da fatan an tashi lafiya."duk suka amsa suna yiwa Zaitun wasa ta bar musu ita ta shiga kitchen.

Bata jima sosai ba ta fito lokacin Zaitun na kuka ta d'auke ta ta koma sama su kuma suka fita zuwa mazaunin su. Tana shiga falon yana sakkowa yayi wanka ya shirya da alama fita zaiyi suka had'a ido ya janye idanun sa daga kanta ya mik'a hannu ya karb'i Zaytun da take hannun ta yana mata wasa sai dariya take tana kiran Dady.

"Barka da safiya" ta fad'a tana kallon sa muryar ta a sanyaye. Kai kawai ya d'aga mata kafin ya ajjiye Zaitun akan kujera ya kama hanya zai sauka tace, "Na gama abinci." Kai ya girgiza baiyi magana ba ya sauka ya barta a wajan.

Numfashi ta sauke ta zauna a gefen kujera tayi tagumi nan ta jiyo tashin motar sa alamun ya fita ta cize bakin ta zuciyar ta cike da k'unci, ta manta rabon ma da yaci abincin ta ko yaushe tyi masa tayi sai yace baya ci. Mijin ta mai sonta da qaunar ta amma ya canja lokaci d'aya akan kuma laifin da ba nata ba ko tace akan abinda bata san tayi masa ba.

Irin soyayyar da suka shinfida ta tuno tayi murmushin takaici tunawa da baya tab'a fita ba tare da yaci abincin ta ba, ba kuma ya fita sai yaji ya ta tashi ko akwai abinda yake damun ta. Kukan Zaytun ya saka ta dawo hankalin ta ta tashi ta k'arasa inda take ta d'auke ta suka hau saman sa dan ta gyara masa d'akin sa.

Shi kuwa Yusuf lokacin da ya fita gidan su ya wuce kai tsaye ya faka motar suka gaisa da ma'aikatan gidan ya shiga ciki zuciyar sa cike da fargabar had'uwa da Ammah sa. A babban falon ya same su ita da yayen sa maza shigar sa su kuma duk sun mik'e zasu tafi suka gaisa dasu gabad'aya suka fita shi kuma ya zauna.

"Barka da Safiya Ammah." A ciki tace, "Barka." Jin yadda ta amsa sai yaji babu dad'i ya kalle ta yace, "An tashi lafiya."
"Lafiya."
"Abbah ya fita ne?."
"Yaje jana'iza" ta bashi amsa tana d'aukar waya a gefen ta.

Shiru ya ratsa wajan ya kalle ta yaga fuskar ta a d'aure ya sauke numfashi yace, "Dan Allah Ammah kiyi hak'uri ki daina fushi dani." Ammah ta kalle shi tace, "Fushin kake so ne Yusuf shiyasa na fara daga yanzu." Shiru yayi bai amsa ba tace, "fad'a min tsakanin ka da Allah akwai abinda matar ka ta rage ka dashi ne kake son k'ara aure?."

Shiru yayi baice komai ba tace, "Magana nake maka, ka amsa min." Kai ya girgiza alamun babu tace, "Kenan kawai dan kaga tana da hak'uri kuma tana sonka shiyasa kake mata wulaƙancin da kaga dama?. Auren ku gabad'aya kwanan sa nawa amma hangen wata kake yi tun matar ka tana amarya, yayen ka da suka fita yanzu daga mai shekara takwas da aure sai me sama da haka duk basu k'ara aure ba sai kai?."

Nan ma yayi shiru baiyi magana ba ta sake kallon sa tace, "Dan kuma na hanaka shine sai kayi tafiyar ka wata k'asar ka kashe wata da watanni baka nan wato taci kanta koma meye ya sameta kai baka damu ba tunda ba k'anwar ka bace, na tabbata inda k'anwar ka Humaira ce bazaka so ayi mata irin abinda kayi mata ba. Baka damu da ya take ba kawai kai burin ka kake so ka cimma. Kana tunanin watannin da kayi baka nan Allah bazai karb'ar mata hakkin ta da ka d'auka ba?."

Kansa yana k'asa yana jin abinda take cewa baice komai ba dan bai San abinda zai ce bata kuma cewa, "Kai da kanka kace min mahaifinta yana numfashin k'arshe yake damk'a maka amanar ta a hannun ka, kar ka manta tun asali mahaifiyarta ta jima da rasuwa kai kad'ai ne da ita a nan yayar ta a bauchi take aure kuma kasan yayar tata ita kad'ai gare ta. Ka d'aukarwa mahaifinta alk'awarin kula da ita har abada ka auro ta dan kana sonta ka ka d'auko ta daga gidan da aka haife ta ka kawo ta nan. Kana tunanin sab'a alk'awarin da ka d'auka da kake yi Allah zai k'yale ka?. Cutar da marainiya wacce ta rasa iyayen ta?."

Jikin sa taga yayi sanyi da alama ya tuna lokacin da ya d'auki alk'awarin hakan ya saka ta sake cewa, "Ban hanaka aure ba Yusuf, ban isa na hana abinda Allah ya k'addara ba wataƙila itama matar kace akwai rabo a tsakanin ku, amma meye laifin Aminatou da ka d'auki laifin ka d'ora mata? In zaka kauracewa wacce ta hanaka aure ni zaka kauracewa ba ita ba domin ita sam bata da laifin komai."

"Ka nutsu ka dawo hankalin ka ka koma Yusuf d'in dana sani mai son matar sa ka ajjiye wannan banzar dabi'ar da ka d'aukowa kanka. Ita kuma yarinyar da kake hange ban amince da tarbiyyar gidan su ba kasan mahaifin ka ma bazai amince da ita ba, baza ka d'auko ta ka kawo ta cikin mu ka gurb'ata mana ahli ba."

Sai a lokacin yace, "kiyi hak'uri, in sha Allah zan gyara."
"Karma ka gyara mana Yusuf, kar ka gyara kai tayi kai da Allah dan sai ya saka mata duk abinda kake yi mata." Shiru ya sake yi zuciyar sa duk babu dad'i jikin sa yayi sanyi abubuwan da suka gabata kawai yake tunawa wani bangare na zuciyar sa na sake jaddada soyayyar da Amma take yiwa Ameena.

"Tashi ka bani waje" ya tsinci muryar Ammah babu yadda zaiyi haka ya mik'e ya fita gabad'aya komai ya tsaya masa tausayin Aminatou yake ji yana tsirga masa zuciyar sa cike da dana sanin abinda yake aikata mata. Jikin sa ya sake yin sanyi lokacin da ya tuna kalaman mahaifinta ya sauke numfashi yana jin zuciyar sa tana bugawa da sauri a haka ya shiga mota ya bar cikin gidan.

K'arar shigowar sak'o yaji a wayar sa ya duba yaga sunan matar sa ya bud'e message d'in yaga ta rubuta, _In ka min izini ina so zanje gidan Fiddausi._ titi ya kalla ya saita tuk'in kafin ya rubuta mata a dawo lafiya ya ajjiye wayar ya cigaba da tuk'i zuciyar sa duk babu dad'i. Shi Kansa bai San abinda tayi masa ba kawai wani lokacin sai yaji haushi take bashi gabad'aya.


Lokacin da ta ga sak'on sa ba k'aramin dad'i taji ba duk da zuciyar ta babu dad'i amma tayi farin ciki ko babu komai zatayi hira a gidan k'awar ta, mayafi kawai ta yafa ta d'auki key din motar ta da Zaitun ta d'auki jaka ta fita ta shiga mota ta fita zuwa gidan Fiddausi dake unguwar soron d'inki.

A k'ofar gidan ta faka motar ta fito rik'e da Zaitun a hannunta ta shiga cikin gidan da sallama. Daga cikin falon taji ta amsa sallamar ta shiga falon tana fad'in, "Sarkin zaman d'aki nasan kina ciki ai daman." Ganin wacce batayi tsammani ba ya saka Fiddausi yin tsalle ta taso ta rugume ta tana fad'in, "oyoyo k'awar arzuk'i." Karb'ar Zaitun tayi ta zauna itama ta zauna tace, "Kin sannkuma ban d'auki muryar ki ba."

"Ta ina zaki d'auka kina zaune a d'aki ko yaushe kamar munafuka." Fiddausi tayi dariya tace, "Sai dai zaman d'akin ai. Hajiya Meena barka da zuwa." Ameenatou tayi dariya kawai bata ce komai ba kafin Fiddausi tace, "gashi ban san abinda zan kawo miki ba."
"Kawai baki niyar bani din bane" ta fad'a tana kallonta.

"To ai babu abinda zaki iyaci a gidan namu, bara dai na dubo ko ruwa na kawo miki" ta fad'a tana tashi ta k'arasa inda k'aramin fridge d'inta yake ta d'auko ruwa ta kawo mata ga mamakin ta sai taga ta fasa ledar pure water d'in tana sha.

Kallon burgewa take binta da shi kafin tace, "Aminatou matar Yusuf had'in Allah, kinga yadda kike kyau duk da naga kin rame amma sai kika k'ara haske." Kafin Ameenatou tayi magana wayar Fiddausi ta d'auki k'ara ta duba taga sunan mijin tace ta saka a kunne kafin tace, "Baizo ba har yanzu" tana fad'a ta yanke wayar Ameen tayi dariya tace, "Fiddausi ta Ibrahim had'in Allah."

Tab'e baki tayi tace, "Bari kedai kawai k'awata na gaji da rayuwar gidan nan wallahi." Ameena tayi k'aramin tsaki tace, "Kedai kullum magana guda d'aya kinki kiyi hankali."
"Dan bake bace a cikin gidan nan shiyasa kike cewa haka."
"Kawai dai ke kin cika 'korafi." Fiddausi tace, "Bara kiga na d'ora mana abinci kar na barki da yunwa" ta fad'a tana tashi sai kuma tace, "gashi kalanzir d'in nawa ya k'are wallahi, ban iya kunna gawayin can sosai ba"ta fad'a cikin yanga ita a lallai bata saba amfani dashi ba.

Sai kuma ta fita ta d'an jima kafin ta dawo tana fad'in, "Na barki ke kad'ai, aikin gawayi akwai wahala wallahi. Nayi-nayi ya siya min gas yak'i na tsani aikin gawayin nan." Ameenatou tayi murmushi ta ajjiye wayar ta tace, "banda abinki ai gwara gawayin akan itace."
Zatayi magana akayi sallama ta amsa yaron ya shigo yace, "Wai gashi inji mai gidan nan yace in akwai abinda kike so a siyo" ya fad'a yana mik'a mata ledar.

Karb'a tayi ta buɗe taga kifin da yace zai siyo ne da kuma salad da kayan had'in sa ta kalli yaron tace, "babu abinda za'a siyo." Tafiya yaron yayi ta ajjiye ledar Amina tace, "Wallahi Ibrahim yana ji dake, har aikowa yake akwai abinda kike so yana can yana kasuwanci hankalin sa yana kanki, kin huta fa Fidy."

Tabe baki tayi tace, "Bari kawai, kifi ne fa ba wata tsiya ba." Ameenatou tace, "Nawa ne suke neman sa?."
"Hmmm!." Itama shiru tayi jin abinda tace d'in ta mik'e ta sake fita ta bar Ameenatou a zaune.

Sake dawowa tayi kafin ta zauna suna hirar makaranta lokaci kad'an ta gama abincin ta zubo musu tare suka ci sosai Ameenatou taci dan taji dad'in abincin sosai ba kad'an ba. Sai da ta k'oshi tace, "Bara na tashi nayi sallah na wuce gida" ta fad'a tana tashi zaune ta kalli Zaitun da take bacci ta fita tayi alwala ta dawo ta tayar da sallah.

Bayan ta idar ne Fiddausi ta shiga d'aki sai gata da jarka doguwa ta fito ta mik'awa Aminatou tace, "Kune amare ko nace kune abin zai muku dad'i, had'in kwakwa ne akayi jiya daga gida aka aiko min Allah yayi rabon kine." Aminatou ta kalle ta tace, "Ke bakya so kenan?." Ta tabe baki tare da yin tsaki tace, "ke rabani da wannan sabgar, ku take yiwa dad'i bamu ba. Kalli kiga inda muke fa ina wani abun zai tafi yadda ya kamata a nan?. Nifa badan yana takura ni ba wallahi dan na kwashe kwanaki ban waiwaye shi ba lafiya lau zan zauna, to matsalar daga shi ne duk abi a takura maka, mtsww."

Da mamaki Aminatou take kallon ta duk da tasan halin ta tun suna makarantar kwana mace ce mai

Please Login or Register in order to submit comment