Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayi dana sanin dukana dan wallahi sai na d’auki mataki a kanka, sai ka gwammace baka San wata Fiddausi a duniya ba.” Tana gama fad’a ta shige d’aki a guje. Ibrahim ya kalli Maman Zainab tace, “Babu komai Maman Zainab ki koma Mun gode.” Maman zainab tace, “A cigaba da hakuri, sai da safe” ta fita shi kuma ya shiga daki ransa yafi na baya b’aci ganin abinda bai tab’a faruwa ba ya faru shine maqota su shigo gidan sa sabida ihu ko wani abun Mara dad’i.


Bai sake sauraron fa ba dan in ya biye mata zai iya b’allata, ga ciki a jikin ta ko ya ya aka tab’a ta wani abun zai iya faruwa. Bai tab’a kawo zai iya dukan ta ba Tunda suke amma sai gashi shine harda mari sabida halayyar da take nuna masa. Ranar dukkan su kwanan b’acin rai sukayi hakan ya saka koda safe bai waiwaye ta ba ya fice daga gidan kai tsaye gidan su ya nufa san yana son had’uwa da mahaifin sa akan lamarin Fiddausi ya gaji gwara manya su shiga, ya gaji da ajjiye maganar matsayin sirri gwara a Kira ta aji meye yake damun ta.

Mahaifin nasa kuwa yana nan da yayyen sa maza guda biyu harda yayar Hadiza Mariya ce babu a wajan da Fadima ya shiga da sallama duk suka juyo suka kalle shi suka amsa ya k’arasa ya zauna suka gaisa gabadayan su, Hajiya ce ta shigo tana fadin, “A’a, Ibrahim yau ma da safe ka fito?.” Fuskar sa babu walwala ko kad’an kamar yadda ya saba yace, “Eh hajiya, barka da safiya.” Ta amsa tana zama kafin Mahaifin sa yace, “Ibrahim me yake damun ka haka ka rame?, ga fuskar ka ta nuna alamun damuwa sosai, lafiya kake?.”

Ibrahim ya gyara zama yace, “Alhaji daman abinda ya kawo ni kenan wajan ka.”
Alhaji yace, “to ina Jin ka, Allah yasa lafiya.”
“Akan matsalar Fiddausi ne, Ina so na kai ‘karar ta wajan iyayen ta, bana so nayi hakan babu sanin ka shiyasa na fara sanar da kai.” Hajiya ta kalli Alhajin su shima ya kalle ta dan abin ya bawa kowa mamaki karo na farko kenan da yazo gida ya fad’i damuwar sa akan Fiddausi.

Alhaji yace, “Wacce matsala ce har ka kasa jurewa kazo ka sanar damu Ibrahim?. A sanina babu wata damuwar da ka tab’a zuwa ka fad’a mana a kanta balle muce a sake maimaitawa, me yake faruwa?.”

Ibrahim ya kulle ido ya bud’e Allah ya sani baya daga cikin masu son fad’ar damuwar iyalan sa, sabida shi zai iya mantawa ya cigaba da zama da matar sa iyayen sa kuma baza su manta ba har abada, shiyasa ya zab’i yin shiru Akan duk wata magana ta iyali.

Zaiyi magana kenan aka ji sallamar Fiddausi a k’ofar d’akin aka amsa kowa ya bita da kallo ganin fuskar ta ta tasa ga bakin ta ya kunbura ta zauna ta gaishe dasu tace, “Alhaji na kawo k’arar Ibrahim ne, jiya da daddare yayi min duka bayan yasan Ina da ‘karamin ciki, ya dake ni akan gaskiyata dan kawai na fad’a masa laifin sa shikenan ya rufe ni da duka. Bazan zauna ya dinga dukana kamar wata jaka ba gaskiya, ba jiya aka fara ba ko yaushe da nay laifi zai ce zai dake ni. Maganar gaskiya na gaji da halayyar Ibrahim ni kawai ya sake ni, bana son sa, bana qaunar sa, bana qaunar zama dashi ko kusa, in aka tilastamin zama dashi komai zai iya faruwa gaskiya, dan zan iya kashe shi!” ta fad’a kai a sunkuye kamar munafuka kafin ta mik’e tsaye ta kalli kowa na d’akin bata sake magana ba ta juya ta fita.

Baki sake kowa yake kallon ta aka rasa wanda zai fara cewa komai, Ibrahim kamar ya zubar da hawaye haka yake ji a wannan lokacin Hajiya tace, “Ibrahim ka saki yarinyar nan indai nice na haife ka! Babu amfanin zama da ita ka sake a yanzun nan!.”




#Nana Haleema ce.

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*
*Page 22*



Gaban Ibrahim yayi mugun fad’uwa ya runtse idanun sa zuciyar sa nayi masa zafi da rawa sosai jin abinda Hajiya tace ya bud’e ya sauke numfashin da yake ji ya tsaya masa a k’irji a hankali ya kalli Hajiyar da take kallon sa kafin yayi magana Alhaji yace, "ya zaki yi saurin yanke hukunci haka? Ai sai ki jira muji abinda yake faruwa har aka zo wannan gab’ar.”

Hajiya tace, "Baka ji me tazo ta fad’a bane? A gaban idona a gaban ka da y’an uwan sa, tazo har cikin gidan su tace wai ya sake ta bata qaunar sa in ba haka ba zata kashe shi, kuma sai ayi shiru a barshi ya cigaba da zama da ita akan me?. Ai ko a akan wanne dalili ne babu wannan maganar Alhaji.”
"B'acin rai ne yaja ta fad’a haka amma in komai ya daidaita sai kiga komai ya wuce, baki San me yayi mata har tazo tace hakan ba, kamata yayi a tsaya a bincika tukunna.”
"Zancen komai ya wuce ai bai tashi ba, yarinyar da tazo har gaban mu ta furta wannan kalmar meye zai wuce kuma?. Ai babu abinda zaiyi saura, in ma laifin nasa ne haka zai sake ta tunda abinda take nema din kenan.”

Alhaji ya kalli ibrahim yace, "Kai me ya kai ka dukan matar ka? Matar taka ma mai ciki?, ga shaida nan kuma Mun gani dan ga fuskar ta nan a kunbure haka ma bakin ta. Haba Ibrahim kamar ba kai ba." Shiru yayi baice komai ba dan bai san me zaice ba dan Fiddausi ta shayar dashi ruwan mamaki gabad’aya bakin sa ya d’aure ya kasa furta komai.

Babban Yayan su wanda suke kira da Yaya Sulaiman yace, "Alhaji ba na shiga maganar ku baku sako ni ba, amma tunda yarinyar nan ta kai ga furta wannan kalaman a gaban ku zama da ita bafa alkhairi bane, macen da zata furta kisa akan sab’ani na miji da mata ai ba wacce za'a saki jiki da ita bace." Wanda yake biye masa wanda suke kira Yaya Yaqub yace, "nima dai hakan zance gaskiya, babu amfanin zama da ita gaskiya abu mai sauki ya sake ta."

Alhaji yayi murmushi yace, "Duk da haka zamu zauna da ita ai ba'a san dalilin da ya saka ta furta hakan ba, zan kira mahaifinta ya kira ta aji a inda matsalar take. Waye yake son rabuwar aure banda dole? Ga d'an su Amir so kuke ya tashi babu mahaifiya a kusa dashi?. Kuma in kuka tuna shida ita babu wanda ya tab’a zuwa yace mana kallon banza wani a cikin su ya yiwa wani, Tunda har aka zo nan sai a tsaya a nutsu kuma a gano inda damuwar take ba a yanke hukunci nan take ba.” Hajiya tace, "ni banga amfanin wani magana ba wallahi Alhaji, Tunda sakin take so ba sai ayi ba."

Alhaji bai bata amsa ba ya kalli Ibrahim yace, "Meye ya had'a ku?, baka tab’a kawo k’arar ta ba muna alfahari da hakan nida mahaifiyar ka, mahaifin ta ma yana alfahari da kai dan yana fad’a min in muka had’u. Yau ka kawo k’arar ta na tabbata ba Abu bane mai sauki sai wanda yafi k’arfin tunanin ka, kafin kayi magana itama tazo kaga kenan matsalar ba k’arama bace, Meya had’a ku?.” Numfashi ya fesar ya sunkuyar da kansa k'asa yace, "Alhaji in rabuwar ce alkhairi gwara kawai mu rabun." Hajiya tayi karaf tace, "Tunda kaji ya furta hakan gwara kawai a san abinda za'a yi gaskiya, bana goyan bayan ace wai za’a daidaita su Allah ya sani.”

Alhaji ya mik’e tsaye yace, "zan kira iyayen ta yanzu in yaso sai a had’a su da Ibrahim din aji abinda yake faruwa, ai ba'a shari’ar aure b’angare d'aya, ku kwantar da hankalin ku in sha Allah babu wata damuwa. Kai Ibrahim muje" ya fad'a yana fita duk mazan suka bi bayan mahaifin nasu.

Bayan fitar su Yaya ta kalli Hajiya tace, "Wallahi Hajiya ba k’aramar wahalar Fiddausi yake sha ba, kawai yana sonta ne kuma Allah ya d’ora masa hak’uri da zurfin ciki shiyasa baya fad’a, kin san Mariya ce k’awar shawarar sa yaje har gida da matsalar Fiddausi shekaran jiya, kowa a unguwar yasan ta canja daga wacce aka sani a baya.”

Hajiya tace, "ki ture duk abubuwan da take masa a bayan idanun mu ne ya faru, amma wannan har gabana tazo tace bana son sa bana qaunar sa, yanzu ko daidaita auren nasu akayi har abada zan ga farin tane?." Hajiya ta girgiza kai tace, "Har abada bazan ga farin ta ba wallahi, ta fita daga raina gabad’aya in sha Allah kuma k’arshen auren nasu ne yazo dan ni kalamam ta sun bani tsoro."
“In sha Allah auren ya kare, babu amfanin zama da mace irin ta.”
“To koma meye har gıda Kizo gaban iyayen mutum kice bakya son sa?.” Yaya Hadiza tayi shiru kawai dan taga alama kalaman t sun yiwa Hajiya zafi sosai.


Fiddausi tana barin gidan su Ibrahim kai tsaye gidan Zakiyya ta wuce bata jima ba driver yazo ya d’auke ta suka tafi passport office, da yake abu ne na kud’i babu b’ata lokaci aka yi mata komai aka tabbatar komai yayi sannan suka dawo.

Daga nan ma gidan Zakiyya ta wuce ta zauna bayan ta sha ruwa mai sanyi ta jingina da kujera tayi shiru tana tunani abinda ya faru, Zakiyya ta fito ta kalle ta sai ta kunshe dariya tace, "Wallahi bakin ki sam babu kyaun gani, ya kunbura sosai.” K’wafa tayi tace, "bari kawai, wallahi Allah sai na saka an hukunta min shi da zarar na auri Alhaji, sai na saka ya kwana a cell dan ya tabbatar ba ‘karamar mace ya daka ba. Marin da yayi min kuma sai na rama.”

Ta zauna kusa da ita tace, "Shine daidai ki nuna masa kema yanzu ba sa'ar sa bace, in banda hauka ma kamar ki zai daka?". Bata amsa ba dan taksicin hakan take ji a zuciyar ta sosai Zakiyya tace, "har yanzu ba wani cigaba akan zancen sakin?." Fiddausi tace, "Hmmmm! Shiru dai, amma na tabbatar da zamana dashi yazo k’arshe . Babban abinda yake d’aga min hankali akaimaganar nan wajan Abba, kar a gano laifina ne kin san halin sa wani lokacin yana da fad'a, in ya saka ni a gaba sai na gwammace ban aikata ba wallahi.”

Zakiyya tace, "Tashi zaki yi yanzu ki tafi can gidan in maganar ta riske su kafin zuwan ki sai kisan k’aryar dai da zaki yi ki wanke kanki, in kuma bata riske su ba ki shirya taki k'aryar kafin suzo ki hasala zuciyar kowa yadda zasu amince da sakin a lokacin Ta girgiza kai tace, "Bana Jin yanzu basu samu labari ba gaskiya, amma dai" ta fad'a tana mikewa tsaye ta saka mayafin ta ta fita daga gidan ba tare da ta sake magana ba.

Gida ta wuce kai tsaye kafin ta k’arasa ta tabbatar idanun ta sun yi ja sosai yadda ana gani za’a san tayi kuka ta shiga da sallama, gifta d’akin mahaifin su tazo yi a nan taga takalma ta jiyo tashin muryar mahaifin Ibrahim da alama sun jima da zuwa. Gaban ta ya fad’i sosai har zata wuce mahaifinta ya hango ta yace, "Fiddausi!." Sai da ta rantse ido sannan ta amsa ta d'aga labulen ta shiga da sallama kanta yana k’asa tsoron ta d’aya Allah yasa kar Abba ya goyi bayan Ibrahim.

"Samu waje ki zauna" taji muryar mahaifinta ya fad’a ba musu ta zauna a inda take tsaye tana raba idanu. Mahaifinta yace, "Daga ina kike yanzu?.” Fiddausi t kulle ido ta bud’e tace, “Naje asibiti ne.” Abba ya sake cewa, “me ya had'a ki da mijin ki?." Shiru tayi kamar gaske ta fara kuka bata ce komai ba sai kuka da take yi. Alhajin su Ibrahim yace, "Magana zakiyi ai babu wands zai tauye ki gwara kawai ki fad'a a samo mafita."

Muryar ta na rawa tace, "Ibrahim baya sona, Kullum cikin dukana yake komai nayi banyi daidai ba, ya zage ni yaci mutuncin iyayena. Ban tab’a fadawa kowa ba tun zaman mu dashi hak’uri nake yi. Ni na gaji da zama dashi wallahi bazan iya komawa gidan sa ba, in aka tilasta ni komai zai iya faruwa."

Alhaji yace, "Kai Ibrahim meyasa kake dukan ta?." Shi kam mamaki ma ya hana cewa komai sai kallon ta da yake yi jin yadda take kuka tana fad’ar abinda ba shi ne yake faruwa ba. ita kuma bata san yana wajan ba sai gaban ta ya fad’i jin an ambace shi ta d’ago ta kalle shi suka had’a ido sai ya d’auke kai ya sunkuyar da kansa kasa yace, "Ban tab’a saka hannu na dake ta ba sai jiya."
Abban ta yace, "Kika ce yana dukan ki?."
"Yana dukana wallahi, a tambayi maman Zainab makociyata tana Jin kukana Kullum indai yana dukana, itace take zuwa ta bani hak’uri tace na rike sirrin kar na fad’a gida kowa ba’a son abinda yake ciki ba. Abba Tunda kuka ga nace na gaji da zama dashi ku amince akwai abinda nake b’oyewa.”

Abba yace, “meye shi abinda kike boyewa din?.” Shiru tayi bata amsa ba Abba ya sake cewa, “indai akwai abinda kike boyewa yau ranar da zaki fad’a ce, in kuma karya kike sai Kiyi shiru, dan ni har yanzu banji dalilin da zai saka kice zaki kashe shi ba.” Fiddausi ta fara girgiza kai tana hawaye tace, “kuma sannan.... Kuma...." Sai tayi shiru bata ‘karasa ba.

"Kuma me? Muna Jin ki" Alaji ya fad’a yana kallon ta. Ta sake yin ‘kasa da kai tace, "Baya kula ni sai lokacin da yaga dama, in nayi magana yace yaje wajan aiki ya gaji na kyale shi haka zan kwana Ina kuka, Ina Jin tsoron fad’awa halaka dan Kullum lamarin sa gaba yake. Ya gaji da zama dani nima haka wallahi, na gaji da rufa masa asiri ni kawai ya sake ni" ta fad'a da kuka sosai ta tashi a guje ta shiga cikin gida.

Tana zuwa jikin Maman ta ta fad’a tana kuka tana cew, "Mama kar ki bari a ce na koma na gaji ni saki na nake so yayi, Kullum duka da cin mutunci ga babu abincin kirki sai dai na nema zanci wani lokacin, na gaji dan Allah kar a mayar dani". Mama ta rungume ta tace, "Kar ki damu komai zai daidaita in Allah ya amince." Dago fuskar ta tayi ta kalli bakin ta da ya kunbura tace, "Ga shaidar duka nan a bakin ki, duka ai ba d'abi'ar miji na gari bace ba gaskiya.”

Mama ta sake cewa, “ni tunda akace Kun samu matsala dashi jikina ya bani babba ce duba da baki tab’a kawo k’arar sa.”
Kuka take tayi sosai Umma na bata baki kafin ta tashi ta shiga daki zuciyar ta na bugawa so take kawai taji an kawo k’arshen maganar.

Bata san ya aka k'are ba taji Abba na kiran ta ta fito ta tsuguna tace, "Gani Abba." Ya zauna yace, "Zauna kema." Ta zauna ya kalle ta yace, "Shi zaman aure hak’uri ake ba ko yaushe ake neman saki ba, duba da yanayin zaman ki da mijin ko kowa sha’awar ki yake yi sabida babu abinda kika rasa ga hankali ki a kwance bai kawo k’arar ki ba kema haka. Dan haka Fiddausi dan an samu matsala sau d’aya baza’a ce za’a rabu ba, wannan maganar sakin da kike ta fita daga bakin ki Fiddausi zaman gida bashi da dad’i, duk lalacewar gidan mijin ki yafi gidan ku dad’in zama, Kiyi hak’uri ni nasan mijin ki yana sonki kuma yana k’okari a kan ki sosai komai hakuri ake nan gaba komai zai wuce."

Sai ta saka fashewa da kuka bata ce komai ba sai kukan da take yi na bak’in cikin rashin samun nasara Mama tace, "nifa tunda naga yarinyar nan na kuka akan Ibrahim naji auren ta dashi ya fita daga raina, ba'a san me yake faruwa bafa, kar muzo ana da an sani.”
"Babu abinda yake faruwa kiyi mata fatan alkhairi,ke kin san waye mijin ta ai nida ke Muna zama mu tattauna a kansa, Muna kuma jin dad’in yadda ya rik’e ta hannu biyu bai bartata nemi wani abun ta rasa ba. Akan matsala d’aya da tazo wajan mu shikenan sai muce ya sake ta?. Ai ba’a yin haka a dinga yin sara ana duban bakin gatari mana” ya dawo da kallon sa ga Fiddausi yace, “in Allah ya kaimu anjima da daddare ki koma gidan mijin ki da zama, ki cigaba d hakuri kamar yadda kike yi zaki ga ribar a nan gaba. Sannan koda nan gaba kar ki sake ambaton kisa komai yawan b’acin ran da zaki shiga.”

Mama da ta gamsu da bayanan sa tace, "to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi". Daga haka Abba ya tashi ita kuma tana saune zuciyar ta kamar dutse ji take kamar tayi hauka.


Mama ta kalle ta tace, "Kiyi hakuri komai ai zai wuce, duk abinda mahaifin ki ya fad’a akan mijin ki gaskiya ne, Kiyi hakuri ki cigaba da zama Allah ya baki mijin da bai bawa wasu matan ba.” Kai kawai ta d'aga ta tashi ta shiga d’aki komai yana neman lalace mata ita ba haka take so ba, ya zama dole ta samo mafita kafin komai ya tashi a banza.

A bangaren Ibrahim koda suka koma gıda mahaifin sa nasiha ya dinga yi masa yace, "Kayi hakuri komai da kake gani zai wuce ba'a son rabuwar aure ka daure ka cigaba da zama da ita, tana sonka kana sonta bai kamata wannan damuwar tayi tasiri a wajan ku ba.” Kai ya girgiza ya kalli Alhaji yace, "Bazan iya ba Alhaji, a da zan iya cigaba da zama da ita amma a yanzu bazan iya ba. Kayi hakuri."

Alhaji yace, "Meyasa baza ka iya ba yanzu?."
"Alhaji duk abinda ta fad’a a kaina wallahi ‘karya take, sakin kawai take so na tabbata koda Mun cigaba da zama da ita zaman bazai tab’a yin dadi ba,
Tunda aka fara haka hakan za’a cigaba, gwara a rabu din zai fi."
"Baza'a rabu ba Ibrahim, kun fara tara zuri'a fa akan me zaka sake ta? Kayi hakuri komai zai wuce zatayi nadamar abinda tayi maka da kanta. In ma laifin naku ne kai da ita duk zaku yi nadama amma batun rabuwa babu.”

Shiru yayi yana Jin nasihar mahaifin sa zuciyar sa na sake yin sanyi a hankali yake Jin nutsuwa na shigar sa ya sauke numfashi yace, "To Alhaji za'a cigaba da hakurin." Alhaji yace, "Ko kai fa, Allah yayi maka albarka." Ya amsa da amin ya kalli Hajiya da alama abin bai mata dadi ba ya tashi ya fita.

Hajiya ta kalli Alhaji tace, "Wai kana nufin ya cigaba da zama da ita ta kashe shi ta kashe banza kenan?." Alhaji yayi murmushi yace, "Bazata kashe shi ba, ta fada ne kawai itama amma bazata iya aikatawa ba bacin rai ne." Hajiya tace, "ni wallahi gani nake zata iya." Alhaji yayi dariya kawai ya fita bai ce komai ba.

Bayan sallar magriba Abban su Fiddausi ya yiwa Alhaji waya yake sanar dashi Fiddausi ta koma gidan ta yayi godiya ya shiga gidan ya tarar da Ibrahim da Yaya suna cin abinci ya kalli Ibrahim yace, "Matar ka ta koma gidan ta İbrahim , in Yayan naku zai wuce ya tafi da kai ya sauke ka ya shiga ma ya sake muku nasiha gabadaya kai da ita.”

Ya amsa da to ya shiga d’aki Hajiya dai bata ce komai ba har suka gama cin abincin ya tashi zasu tafi Amir ma ya tashi yace, "Abba zan bika." Ibrahim ya kalle shi ya kalli Hajiya ko zata ce wani Abu amma bata ce ba yace, "Kayi zaman ka a wajan Hajiya gobe sai nazo mu tafi."
Ya nok'e kafad’a yace, "Nidai zan bika." Hajiya tace, "saka takalmin ka ka bishi." Ya saka takalmi ya rik’e hannun sa suka fita daga gidan Hajiya bata ce uffan ba.

A k’ofar gidan suka tsaya suka shiga ciki Ibrahim yana gaba Yaya na bayan sa suka shiga da sallama. Ai tana jin sallamar Ibrahim sai ta zabura kamar an cillo ta ya ganta a gaban da hannun ta rik’e da wuk’a tace, "Ibrahim ko ka sake ni ko na kashe ka Yanzun nan.”

Da mamaki yake kallon ta ya kalli Yaya Sulaiman da shima yake kallon abin mamaki yace, "ki kashe ni?."
"Eh na kashe ka, ai na fad’a maka daman wallahi muka cigaba da zmaa da kai sai na kashe ka. Na gaji da zama da talaka irin ka, duk abinda nayi maka bai saka kayi zuciya ka sake ni ba to wallahi ko ka rabu dani ko naga bayan ka."

Shi gabad’aya ma ya rasa abinda zai ce yadda yaga tana magana da alama bata kula da Amir da Yaya da suke tare ba hankalin ta ya karkata akan abinda take yi idanun ya ya rufe saki kawai take nema, “Ka sake ni!" Ta fada da k’arfi tare da yankar sa a hannun sa nan take jini ya fara zuba daga hannun yayi baya yana rik’e da hannun yana kallon ta cikin mamaki da tsoro da tashin hankali.

Yaya ne ya k’araso wajan da sauri ganin da gaske fa zata iya yin kusan in ya tsaya yana kallon ta zai iya ganin yawa ya a rik’e hannun da yake jini yana kallon ta yace, "Mahaukaciya ce ke?."
Cikin fitar hankali tace, "Eh itace, indai kuma bai sake ni ba zai ga yadda ake asalin hauka wallahi” ta dawo da kallon ta ga Ibrahim tace, “Ibrahim in ka cika cikin uwar ka da uban ka Ibrahim ka sake ni, na gaji da zama da kai Ina son fara sabuwar rayuwa ka sake ni!."

Ibrahim da yake cikin azabar ciwon da hannun sa yake masa ga jini na zuba ga zuciyar sa na zubar da jini wanda shi kad’ai yake Jin hakan ya sake kallon ta kafin yayi magana Yaya ya kalle shi a fusace yace, "Matsayin uba nake a wajan ka Ibrahim nine babban Yayan ka, dan haka Ina baka umarının ka saki yarinyar nan Yanzun nan.”

Ibrahim ya kalle shi da jajayen idanun sa shima shi yake kallo yace, "Ka sake ta Ibrahim yanzu, in ka b’ata lokaci zata iya yi maka illa.” Ya juya ya kalli Fiddausi yay shiru kamar bazai yi magana ba, ya kulle ido ya bude zuciyar da na bugawa sosai yace, "na sake ki saki d'aya!." A daidai wannan lokacin marar ta ta d’aure alamun maganin da tasha zai fara aiki kenan.

Duk da abinda take ji hakan bai hana ta fad’uwa ta kalli gaban tayi sujjada ta mik’e ta yi dariya tana tafa hannayen ta kalle shi tace, "Alhamdulillah! Ko yau kasuwa ta tashi dan koli yaci riba, ko yau aka busa k’aho burina ya cika na rabu da talakan miji Mara abin mora kamar ka. Naji dad’i zan bar zaman gidan talaka wanda bashi da komai, naji dad’i na fita daga rayuwar k’unci da cin manja da yaji, naji dad’i na fita daga rayuwar zama a duhu, naji dad’i na fita daga rayuwar wanka a bandakin tsakar gida. Ashe kana da zuciya a kirjin ka na d’auk ai da ka yar ne kare ya d’auka. Na fita daga gidsn ka ina yi maka albishir da nan gaba kad’an zan fara sabuwar rayuwa irin wacce nake so" tana fad’a taja mayafin ta da yake gefe tazo wuce shi tayi tsaki tare da tofar da yawu tace, "Kaje ka samu daidai kai ni kam nafi k’arfin ajin ka, kaf dangin ku a yanzu na wuce ajin su balle kai” tana

Please Login or Register in order to submit comment