Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"ni kika kullewa k'ofa, kina ji Ina magana kika min banza, ni kika raina, dan kinga Ina miki wasa, dan Ina raga miki, dan kinga Ina sonki" kana jin yadda yake maganar kasan ya fara fita daga hankalin sa, Allah ya taimake ta tazo bakin ‘kofa haka ta fita a guje tana kuka sosai.

Tana shiga d'aki ta fad'a kan gado ta fashe da kuka mai ciwo, tashi tayi zaune ta dafe kanta ta dafe kai tana kuka mai tsuma zuciya kanta har harbawa yake sabida kuka jijiyoyin goshin ta sun mik’e sosai.
Sai da tayi kukan iya kuka ta tashi tana kallon kanta a madubi musamman fuskar da kuma wuyan ta da sukayi ja alamun ta daku, dan wuyan ta har jini ne ya fita, hawaye y sakko daga idanun ta ta goge t shiga band'aki. Ta jima a ciki ta fito ta zauna a gefen gado ta dafe kanta kirjin ta na d'agawa ga zafin da yake mata ga zafin jikin ta da take ji.

Da baya ta kwanta tana kallon sama babu abinda yake mata yawo a idanun ta sai lokacin da suka fara soyayya ita da Yusuf da kuma rayuwar da suka yi a farkon auren su. Juyi tayi jikin ta duk ciwo yake mata sabida dukan da ta sha ta lumshe ido tana kallon Zaitun da take bacci ta sake lumshe Idon ta zafi yana sake game gangar jikin ta.

A haka ta farka da asuba tayi sallah dakyar dan jikin ta ciwo yake bayan ta idar Zaitun ta tashi ta shayar da ita ta koma bacci ta zauna tana lazimi a haka har gari yayi haske. Jikin ta ta tab'a taji zafi ta sauke numfashi ta tashi ta shiga band'aki tayi wanka ta fito ta tsaya a gaban mudubi tana kallon wuyan ta da shatin dukan Jiya yake kwance a wajan yayi yaja sosai ya kuma yi alamun ciwo. Ajiyar zuciya tayi ta bar wajan ta shirya ta saka abaya mai mayafi bak'a a lokacin Zaitun ta tashi tayi mata wanka a gaggauce ta shirya ta cikin riga da wando y’an kanti masu kyau ta taje mata kai duk da bata ciki walwala gashi bata da lafiya amma a haka t daure.

Tana gamawa ta dauke ta ta fita tayi sa'a Sani driver yana nan duk da safiya ce sosai bazata iya tuk’a mota ba ta shiga ya kaita asibiti. Bata jima sosai ba ta dawo bayan ta siyo magani tana zuwa ta koma sama dan masu aiki sun gyara k’asan ko ina tsaf ta wuce d’akin ta.

Gyaran kan da ta yiwa Zaitun taga ya lalace ta zauna a gefen gadon tana gyara mata zuciyar ta na tuna mata maganar likita, _Amina na fad'a miki ki daina saka damuwa a ranki, bana son d'ora ki akan magangunan hawan jini da k'arancin shekarun ki, in baki daina saka damuwa ba zaki iya kamuwa da ciwon zuciya ki cuci kanki ki cuci yar ki. Lokacin saka damuwa akan namiji ya wuce ki kawar da komai kiyi facing rayuwar ki in ba haka ba wallahi kina ji kina gani zaiyi aure ya barkı da lalura._

Numfashi ta sauke tana cigaba da gyara mata kanta zuciyar ta a raunane sosai, tana son Yusuf har gobe duk abinda yake mata in taji haushin sa na wani lokaci ne da ya wuce sai taji son sa yana nan a zuciyar ta. Har kuka take a kan hakan duk da wani abun ya ragu tun daga sanda ya fara Shan giya. tana gama gyara mata kan kenan aka bud'e k'ofar aka shigo ta juya ta kalle shi suka had'a ido ta d’auke kanta a lokacin Zaytun ta fara dariya tana mik'a masa hannu. Daukar ta yayi yana bin Ameena da kallo jikin sa a sanyaye sosai ya zauna a bakin gado yana yiwa Zaitun wasa da take ta k'ananun magana tana kiran Daddy.

Bata kalle shi ba dan tasan abinda ya kawo shi a koda yaushe sai ya gama dukan ta cikin maye sai yazo yace zai bata hakuri dan ya raina mata hankali, shiru d'akin yayi sai wasan da Zaitun take yi shi ya kasa magana gabadaya. Ganin hakan Ameena tace, "in baka da abin fad'a zan fita" ta fad'a tana mik’ewa tsaye ya kalle ta cikin sanyi yace, "Ina zaki je?."

Numfashi ta sauke ta runtse ido bata kula shi ba yace, "Kiyi hak'uri dan Allah ba'a son raina hakan ta faru ba kema kin sani, bana cikin hankalina ne in badan hakan ba bazan iya dukan ki. Kiyi hakuri." Baki ta tab'e bata ce komai ba ta mikawa Zaitun hannu tak’i tawowa wajan ta sai ma sake rike shi da tayi sai ta bar masa ita ta juya zata fita yace, "Wannan shine na ‘karshe, dan Allah kiyi hakuri."

Juyowa tayi ta kalle shi tace, "Sau babu adadi kenan kana cemin wannan shine na karshe, bazan ce maka ka daina ba tunda a baya na fad'a kak'i ji. Wallahi bazan zauna kana dukana ba zan tattara na bar maka gidan domin ba jaka bace ba, duk abubuwan da kake min ina jurewa amma bazan jure duka ba wallahi. Zama da kai ya fita daga raina wallahi, na gaji baza ka kashe ni da karancin shekaruna ba."

Ganin tana hawaye jikin sa ya sake yin sanyi sosai ya ajjiye Zaitun a gefe ya taso yazo kusa da ita yace, "Ban tab’a tunanin zan tsinci kaina a wannan hali ba wallahi, ko a mafarki ba d’auka zan sha taba bama balle giya. Haka kawai na tsinci kaina a wannan halin kin San da ba haka nake ba zaki bawa kowa labari, ina so na daina na kasa ki taya ni da addu'a. Ki daina kuka dan Allah nasan nayi ba daidai ba amma bazan sake ba.”

Baya tayi bata ce komai ya sake matsowa kusa da ita yace, "Nasan matata tana da hak'uri tana kuma hak'uri dani, a wannan Karon ma ayi min wannan alfarmar a karo na karshe bazan sake aikawa ba da yardar Allah. Bana son ganin hawayen ki My choice." Sunan da ya kira ya saka ta kalle shi suka had'a ido ya daga mata kai yana murmushi da sauri ta sauke kai k'asa zuciyar ta na bugawa sosai.

Kasa murmushin tayi ya rik’e hannun ta yace, “Zan je office na dawo yanzun nan anyi min kiran gaggawa ne. Amma ki sha magani naji jikin ki akwai zafi.” Kai ta d’aga kawai ya saki hannun ta ya fita tabi bayan sa da kallo. Sai ta daina ganin sa ta koma kusa da Zaitun ta zauna tayi shiru tana kallon wani wajan daban gabadaya komai baya yi mata dad’i tana daurewa ne kawai sabida bata da wanda zata kaiwa kukan ta.

Shigowar mota take ji cikin gidan ta tashi ta yaye labulen ta bud’e tana kallon masu shigo tana motar aiki ce da siminti, tiles harda kofofi da taga. Inda suke shiga ta kalla ta girgiza kai tana kallon wajan a bayyane tace, “daman inda yake cemin yana gida apartment din sa ashe na amarya ne?. Allah sarki ni yanzu so nake ma tazo itama taji abinda nake ji a cikin gidan.”

Wata motar ce ta kuma shigowa taga ta Yusuf ne tana tsaye ya fito fuskar sa a washe da annuri yana amsa waya kana kallon yanayin da yake maganar kasan da wacce zai aura yake yi. Daina kallon sa tayi ta koma d’akin ta zauna ta hana kanta tunanin ta d’auki wayar ta ta shiga group din su na four sisters taga babu wanda yayi magana a ciki, rubutu tayi ta tura cikin group din ta ajjiye wayar ta dafe kanta da hannayen ta duka biyun zuciyar ta na mugun harbawa.

“Assalamu alaikum, my Ameena maza saka mayafin ki Ammah tace tana neman ki yanzu yanzu shiyasa na dawo dan na kaiki” ya fad’a yana shigowa ya dauki Zaitun yana kallon ta. Kallon sa tayi itama tace, “Meyasa ka dawo? Naga ai zan iya zuwa da kaina ko?.”
“Yeah I know, kawai ina so muje tare ne.” Kallon sa take kafin ta kawar da kai ta dauki mayafin da ta kwance ta d’aura yayi gaba tabi bayan sa bayan ta dauki wayar.

Babu Wanda yake magana har suka shiga motar suka fita kallon titi yake Zaytun na cinyar sa itama tana kallon gefe d’aya. Kallon ta yayi yaga hankalin ta baya wajan sa yace, “Ki cigaba da rufa min asiri Ameena, in sha Allah zan daina duk abinda nake yi. Wani lokacin kamar wanda aka yiwa asiri haka nake jina bana sanin na aikata wasu abubuwan sai daga baya, kiyi hakuri dani.”

Numfashi ta sauke tayi murmushi jin abinda yace daman tasan batun da zai rok’e t kenan shiyasa yake ta shige mata in ba dan hakan ba da ita da banza duka d’aya, sabida kar ta fad’awa Ammah yake wannan abubuwan. Ganin tayi murmushi sai ya tsargu yace, “Duk da bakya cikin walwala amma murmushin ya miki kyau.” Bata tanka masa ba suka cigaba da tafiya har suka zo gidan Amma.

Tare suka shiga har dakin Ammah tana zaune kamar ko yaushe tana waya suka shiga suka zauna suma jiran ta k’arasa . Tana gamawa ta kalli Ameena fuskar ta ta washe tace, “Daughter zo mu gaisa.” Ameena ta matsa kusa da ita sosai Ammah ta dafa kafadarta tace, “Duk lokacin da zan ganki sai naga canji a fuskar ki, meye ya same ki fuskar ki ta canja haka?.” Ameena tayi dariyar dole tace, “Babu komai Amma na tashi yau da zazzabi ne sai da naje asibiti aka bani magani.”

Ta kalli Yusuf tace, “Amma baka ce min bata da Lafiya ba ai da bazan ce tazo ba.” Yace, “Ganin ta samu sauki kuma naga kina son ganin ta shiyasa ban fad’a miki ba.” Amma ta sake kallon sa tace, “Kaine ka kaita asibitin?.” Ya d’an zare ido ya rasa me zaice hakan ya saka Aminatou tace, “Bashi bane ba Amma, Sani ne ya kaini lokacin ina so naje a bani magani ban jira ya farka ba.”

Amma ta sake kallon ta tace, “Me suka ce yana damun ki?.” Ameena tace, “Malaria ce, sun bani magani sunce na dinga shan ruwa sosai.” Amma tace, “ Allah ya kara lafiya. Cire wannan mayfin naga kina gumi maganin ya shiga jikin ki sosai, ga a.c a kashe.” Bata tab’a yiwa Amma musu amma tana jin tsoron cire wa da sai Amma taga wannan shatin dukan gashi bata shiryawa tambayoyin ta ba.

A hankali ta ware mayafin ta bud’e shi Ammah tace, “Ke kefa, zaki fi jin dadi” ta fad’a tana daukar waya tana dannawa kafin ta saka a kunna tace, “a kawowa Ameena tea ta sha.” Abinda tace kenan ta yanke wayar ta kalli Zaytun da take kwance a kirjin Yusuf tana kallon ta tace, “Indai baban ki yana waje ke bakya zuwa wajan kowa ko?.” Kamar taji mai Amman tace sai tayi dariya itama tayi tace, “Ja’ira irin baban ta.”

Humaira ce ta shigo da shayin tana cewa, “Sis shine zaki shigo ko a neme ni.” Kallon ta Ameena tayi tace, “ni na Isa, na dauka ma kina school.” Karb’ar tea d’in tayi Humaira ta zauna a gefen ta tace, “Banje ba sai anjima. Yaya Yusuf ina kwana?.”
“Lafiya” ya amsa a takaice burin da Amma ta sallame shi ya bar wajan.

Humaira ta kalli Aminatou tace, “Kai sis abayar nan ta miki kyau wallahi, amma ni sai naga kin rame ko Amma?.” Amma tace, “Maganar da nake mata kenan ashe bata jin dadi.” Humaira tace, “Ayya sannu. Kodai kodai” ta fad’a tana kallon ta tana dariya. Ameena ta mintsine ta Humaira tayi dariya.

Murmushi itama tayi ta kai coffee d’in bakin ta tasha daman babu abinda taci, kallon gefen wuyan ta Humaira take yi kafin tace, “Kai Sis! Meye wannan yayi shati haka a wuyan ki kamar duka?.” Amma da take gefe ta kalli inda Humaran ta kalla tace, “Wanne irin duka kuma?!.”




#Vote
#Share
#Comments
#F5


*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*


Masu nem daga farko ku shiga channel zaku samu.
https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36


*Book 1*
*Page 18*



A tare dukkan su suka kalli juna gaban Yusuf yayi mugun fad'uwa ya fara zare idanu ya sunkuyar da kai yana shafa kansa hankalin sa ya tashi sosai, yasan Ameena baza ta ya dake ta ba maganar Ammah ce baya so. Amma ta sake kallo Ameena da ita kanta fuskar ta ta nuna alamun rashin gaskiya tace, "Amina me nake gani a wuyan ki haka? Da gaske duka ne?." Bata iya amsa mata ba dan bata san me zata ce ba Ammah ta sake cewa, "Kalli yadda wuyan ki yayi Ja fa, Yusuf ne ya dake ki?."

Yadda gaban Yusuf yake fad'uwa haka ita kanta Ameena din dan bata san abinda zata ce ta kare kanta ba, a tare gaban su yake faduwa shi tsoron kar ta tona masa asiri shine rashin hankalin sa ita kuma rasa abinda zata cewa Ammah shine yake d'aga mata hankali ita kanta Ammah burin ta kar taji ance Yusuf ne yayi dukan. "Kai Meya same ta haka?". Ta fad'a Tana kallon Yusuf ya dago kai ya kalli Ameena kafin yayi murmushi yana tattaro abinda zai fad'a yace, "Mayafi ne, ta nad'a jiya a wuyan ta da tazo cirewa sai taja shi da karfi shine yayi haka."
"Da yake mafayin qusoshi ne a jikin sa?" Ta tambaya tana kallon sa.

Kafin yayi magana Ameena tace, "Haka ne Amma, kin San wani lokacin baka yi tsammanin abu ba sai ya faru. Ni kaina ban San wajan yayi ja haka ba zai d'azu dana gani."

Da mamaki Ammah take kallon su duka biyun kafin tace, "amma wannan baiyi kama da abinda kika ce ba da zanen abin duka yayi kama." Murmushi tayi tace, "Amma waye zai dake ni?." Ta kalli Yusuf da yake kallon Amina Ammah tace, "ka fada mata zancen tsayar da ranar bikin naka?." A firgice ya kalli Amma ya kalli Amina da take kallon sa ya sake kallon Amma yace, "Ban sanar da ita ba Amma."
"Meyasa?."
Tashi tsaye yayi yace, "rashin Lafiyar da take fama da ita ya saka ban fad'a mata ba, ban San ta inda zan fara fad'a mata ba shiyasa na bari sai ta samu Lafiya. Ammah ana kira a store Sai na dawo" yana gama fad'a ya fita daga d'akin da sauri.

Amma ta kalle ta tace, "An tsayar da lokacin bikin sa sati takwas mai zuwa." Amina ta girgiza kai tace, "Allah ya nuna mana lokacin."
"Amin Amina. Kar ki saka komai a ranki kar komai y dame ki kinji ko?." Murmushi tayi tace, "To Amma in sha Allah." Humairah da take gefe har lokacin bata ce komai ba tausayin Amina take ji sosai a zuciyar ta tana kuma tabbatar da ba wani mayafi dukan ta kawai aka yi.

Kalamai masu dadi Amma ta dinga amfani dasu tana kwantar mata da hankali har sai da taga ta saki jiki suna hıra da Humaira sannan ta basu waje Amina zuciyar ta cike take da tsoro wani b'angren kuma cike take da Jin dadin uwa da ta samu bayan rasa wacce ta haife ta da tayi, badan Amma da take kwantar mata da hankali ba tabbas da zuciyar ta zata iya bugawa ko wanne lokaci.


Tunda ya zauna ya dafe kai baiyi magana ba itama kuma bata ce masa komai ba dan Tunda taga yanayin da ya shigo tasan akwai babban abinda yake damun sa sosai. Musamman da yayi tattaki yazo gidan ta duk da mutum ne mai zumunci amma bai cika zuwa ba sai da dalili. Shirun taji yayi yawa ya saka tace, "İbrahim Lafiya wai?."

Sai sannan ya d'ago ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "Ina zan kai damuwar Fiddausi ne?." Murmushi tayi tana kallon sa tace, "Ikon Allah yau kuma da kanka kake tambayata inda zaka kai damuwar Fiddausi masoyiyar ka?." Kai ya girgiza ya lumshe ido zuciyar sa na bugawa sosai dan Allah ya sani yana son Fiddausi so mai tsanani abubuwan da take masa bai saka son ya ragu da yawa ba, damuwar daren jiya ce ya kasa jurewa sai da ya garzayo gidan Yayar tasa abokiyar shawarar sa ya furta mata abinda yake zuciyar sa ko zai ji dadi.

Ganin ya sake yin shiru ya saka tace, "Me Fiddausi tayi maka?."
"Meye ma bata yi ba?, sam Fiddausi ta canja akwai Wanda yake zuga ta ko kuma aljanu sun shafe ta."
"Ba wata zuga ko aljanu wallahi, ita kad'anta itace aljanar kanta. Tun yaushe nake fad'a maka yarınyar kanta yana rawa nan gaba bazata zauna da kai ba kace min kai ba haka ba?. Tana da hange ne İbrahim Tana kai kanta inda Allah bai kaita ba, gasa take da k'awayen ta wanda suka fita auren masu kudi. Ita kuma gasa duk wanda yace zaiyi wallahi yana tare da wahala."

Sake kallon ta yayi yace, "Nasan da wannan halin nata tun ba yau ba, amma na yanzu yayi yawa abubuwa take yi kamar wacce bata cikin hankalin ta. Ni wallahi zargi nake anya ba aljanu ne suka shafe ta ba?." Wacce take amsa sunan Yayar tasa wacce yake bi ta kalle tare da tab'e baki tace, "Hmmm! To me tayi maka a wannan karon?." Bud'e Baki yayi zai yi magana sai kuma ya fasa ya kawar da kansa gefe yace, "Ki cigaba da taya ni addu'a kawai Allah ya daidai ta tsakanin mu."

"To amin, addu'a kayi ai babu abinda yafi k'arfin Allah. Amma matar nan taka sai dai kayi hak'uri dan kai kasan bazan 'boye maka ba na fad'a a bayan idanun ka ba, in da tana sonka yanzu bata sonka hangen wani wajan take yi. Kaga ban san me tayi maka ba ko? Amma a jikina nake Jin babban abu ne tunda gashi har ka kasa jurewa kazo ka same ni da batun ta, Allah ya shirya ta in tana da rabo in kuma babu Allah ya kawo karshen auren naku kawai."

Kallon ta yayi fuskar sa dauke da firgici yace, "Haba Mariya wannan wacce irin magana kike yi haka?." Hannu ta wara tace, "To akwai wacce ta fita ne?."
"Taya zaki fatan mu rabu bayan mun fara tara zuri'a nida ita? Kodan Amir bai kamata kice haka ba gaskiya."
"Ko babu ita Amir zai taso cikin gata da kuma tarbiyya, ko babu Hajiya akwai ni ga yayyen mu babu wands bazai rike Amir ba."

Numfashi ya sauke a sanyaye yace, "Duk da hakan dai bai kamata kice haka ba." Ta girgiza kai tace, "To naji, Allah ya daidaita ku." Ya
amsa da amin suka fara hira dai sama-sama kafin ya tashi ya tafi ko babu komai ya samu saukin abinda yake ji a zuciyar sa.

Fiddausi kuwa tun da abin ya faru take cika tana batsewa ita k'adai koda taji fitar sa tsaki tayi ta koma ta kwanta a fili tace, "Tun kafin kasan akwai ciki a jikina ya kamata na zubar dashi dan bazan sake haihuwa da kai ba, talakan banza da wofi kawai." Wayar tace tayi k'ara ta fara kallon agogon wayar taga karfe goma na safe sannan ta kalli mai kiran ganin Zakiyya ya saka ta dauka daga can bangaren tace, "Ke Lafiya babu wani feedback ne?."

Fiddausi taja tsaki tace, "Ban San ya zanyi masa ba Kiyya, nayi duk abinda ya kamata amma mutumin nan kamar mata zuciya. Jiya Ruky na gidan nan a gaban ta nayi masa rashin mutunci amma bawan Allah nan kalmar saki ya kasa furtawa sai huci da yake kamar wani zaki."

Zakiyya tayi dariya tace, "Kice kin sha wa'azi a wajnan Rukayya."
"Kamar kin sani, ta saka ni a gaba tana fad'ar wannan ta k'arasa da wancan, dan munafurci harda kuka wai ita da take neman mijin nida na samu ina wulakantawa nace in ya sake ni ya aure ki kinga shikenan kin samu miji a sama."
"Banza ce ai yarinyar nan zata iya auren nasa fa, ita bata gudu abinda ake gudu." Fiddausi tace, "Ai ba cikakken hankali ne da ita ba, Ana gudu wahala tana so ta saka kanta a ciki."

Zakiyya tayi dariya tace, "Ya batun cikin?."
"Ban zubar ba har yanzu kuma bai sani ba, kamar yadda kika ce na fison saki da zubewar sa kinga shikenan na huta da idda." Zakiyya ta sake yin dariya tace, "Shegiyar kaya kice kin matsu dai ki ganki an America ana honey moon ko?." Itama dariyar tayi tace, "Waye yak'i dad'i?."
"Ke ina so na fad'a miki wani abu."
"Ina Jin ki."
"wai ashe Yusuf din Ameena aure zaiyi bata fad'a mana ba?."

Daga kwance Fiddausi ta mik'e zaune ta wara ido tace, "Kece wallahi?." Zakiyya tace, "Wallahi da gaske wai aure zaiyi, har an saka rana ma nan da sati takwas bikin."
"Innalillahi wa'inna ilahiri raji'un, y'ar uwa kinji yadda k'irjina yake bugawa kuwa?. Daman Yusuf zai iya yiwa Ameena kishiya?, duk wannan soyayyar da yake yi mata zai iya had'a ta da wata macen a duniya?. Kai lamarin rijalu sai Allah, duk soyayyar da Amina take masa yanzu wata zai kawo mata?."

Zakiyya tace, "Bari kawai kedai, wallahi ni kaina naji abin a zuciyata fiye da tunanin ki, in a tuna waye Yusuf a wajan Ameena sai naji kamar nayi kuka. Yaushe ma akayi bikin nasu da zai yi wani aure dan Allah?."
"Abinda na gani nima kenan ai Kiyya, an ina kika ji labarin?."
"K'awar wacce zai aura ce take fad'a min, da farko ban gane ma Yusuf take nufi ba sai da ta ce min ke mijin k'awar ku fa Ameena. Ashe shi da irin yaudarar nan yaje neman auren ai kuwa suka kamo shi caraf ya haukace akan amaryar. Gashi tace min basu da tarbiyya yaran ko kad'an basa girmama kowa, sai dai muyi addu'ar Allah ya zaunar dasu Lafiya."

Fiddausi tace, "Allah sarki Ameena, ya kamata muje gidan nata muyi mata jaje."
"Banza wai jaje kamar wacce aka yiwa sata? Kawai zamu je ne matsayin mu na k'awayen ta kuma y'an uwan ta mu kwantar mata da hankali. Nasan halin ta yana nan a tashe ko Baka son miji yace zai k'aro aure sai kaji a jikin ka balle kana son sa, ko da yake sai nake ganin kamar ma bai dame ta ba harkar ta kawai take." Fiddausi tayi dariya tace, "To indai da kud'i meye wani abin kishi Kiyya? Ai in kika ji ana d'aga murya akan miji wallahi talauci ne." A tare sukayi dariya kafin Zakiyya tace, "Kedai kudi kawai matar Alhaji." Dariya itama tayi kafin suyi sallama ta kashe wayar.

^^^^^^

Rukayya kuwa haka ta tashi babu kuzari a jikin ta gabadaya, abinda ya faru a gidan Fiddausi ne yake dawo mata sai kuma d'an shaye-Shayen da yazo da sunan wai yana neman auren ta har cikin gidan su, komai yin sa take a sanyaye har ta kammala ta koma d'aki tayi wanka ta fito ta ci abinci har lokaci Umma tak'i yi mata magana tun jiya take fushi da ita akan tace bata son wanda yazo jiya.

Kasa jure hakan Rukky tayi bayan Umma ta shiga d'aki tabi bayan ta ta dur'kusa a kusa da ita tace, "kiyi hak'uri Umma da b'ata miki da nayi jiya, ki yafe min." Umma kamar jira take tace, "Ai in kinga na yafe miki kawai kin amince anyi auren nan, ke haka kike so ki ta zama kowa yana aure yana barın ki?. A haka kike so ki tsufa a gida? Ki duba tun da kyaun ki sai ya disashe sannan kika so ki tashi?."

Rukky ta sauke numfashi tace, "Umma aure ai lokaci ne in nawa lokacin yazo zanyi."
"Sai na buge miki baki keda lokacin, ni zaki fad'awa aure lokaci ne? Nifa na sani kika yi ko me?."
"Kiyi hak'uri."
"K'anwar ki tayi aure

Please Login or Register in order to submit comment