Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

*Book 1*
*Page 11*


Da sanyin jiki ta tashi a haka tayi wanka ta gyara gidan kamar kullum ta d'ora ruwan tea kafin almajirin ta mai mata aike yazo ta d'auko kudi ta bashi ya siyo indomie da kwai ta dafa indomie ta soya kwan zuciyar ta na bugawa sosai bata san dalilin hakan ba, gabadaya in ta tuna inda take niyar zuwa sai taji gaban ta ya fad'i.

Tana gamawa tayi wanka dan da wuri take son fita ta shirya tana fitowa falon ta ya shigo ya bita da kallo kamar ba ita ba yace, "Khamshin me nake ji haka?." A sanyaye tace, "Kwai ne, ka zauna" ta fad'a tana nuna masa wajan zama. Bai musa ba ya zauna yana kallon ta yace, "A ina aka samu kwai a gidan nawa?."

Zama itama tayi tace, "Jiya daga asibiti ai na biya gida, shine Yaya ta bani kudi tace na hau mota shine da ragowar na siya." Yayi murmushi yace, "Allah Sarki! An gode sosai." Murmushi itama Fiddausin tayi kafin tace, "Kaci abincin." Kallon abincin yayi indomie d'in tayi kyau sai tiriri take sabida zafi ga kwai a kai sai ya girgiza kai yace, "Bana jin zan iya cin wani abu a yanzu gaskiya, kici kawai."
"Meyasa?." Yadda tayi maganar ya saka shi ya kalle ta yace, "Bana jin yunwa ne."

Ledar hannun sa ya mik'a mata ta karb'a tana kallon sa yace, "Atamfar da kike so ce ita na siya miki jiya. Nayi ciniki jiya Alhamdulillah, mai gidan mu yazo yayi mata kyautar dubu ashirin ashirin duk wanda ya tarar a wajan sai na cire kud'in atamfar na siyo miki naga kina so" ya fad'a yana kallon ta da murmushi a kan fuskar sa.

Buɗe ledar tayi ta tab'a atamfar taji jikin ta yayi laushi sosai alamun babbar atamfa ce ba k'arama ba, kallon sa tayi da murmushi tace, "Na gode, tayi kyau ka iya zab'ar kala." Murmushi shima yayi ya matso kusa da ita yace, "Koda zan rasa farin cikina a duniya zan iya jurewa indai zan samar miki da naki farin cikin, burina naga kina farin ciki a koda yaushe bana so naga kina b'ata rai akan komai, zan iya rasa komai sabida ke. Ki cigaba da daurewa akwai ranar da zakiji dad'i dukkan burin ki zai cika, babban gida, babar mota, kayan more rayuwa da komai in sha Allah zan samar miki dashi matuk'ar Ina da rai. Wannan gidan da muke da kanki zaki kyautar sa ga wanda kike zuwa lokacin kin fi k'arfin sa. Sai anyi haƙuri ake cin riba, arzuk'i lokaci ne Fiddausi" ya fad'a yana rik'o hannunta yana kallon idanun ta cikin taushin murya yayi maganar.

Kallon sa take yi zuciyar ta na mugun harbawa domin indai iya kalamai masu kwantar da hankali Ibrahim ya iya su yanzu zai karya maka zuciya ka fasa abinda kayi niya. Shiru tayi tana kallon sa kafin tace, "Ina so zanje gidan Zakiyya d'anta Fahad bashi da lafiya." Numfashi ya sauke ya kalle ta yace, "Sai kin dawo, amma kar ki kai dare" ya fad'a yana tashi tace, "In sha Allah." Kallon ta yayi dan shi mamaki yake yi ganin daga jiya da daddare zuwa safiyar nan ta canja gabad'aya kamar wacce aka yiwa wani abun.

Fita yayi tana jin fitar sa ta sauke numfashi ta kalli abincin itama sai taji yana neman fita daga ranta haka kawai a bayyane tace, "Bazan yi asarar kud'i ba sai naci." Ta fad'a tana jawo abincin ta fara ci sai ta kalli atamfar ta tab'e baki ta cigaba da cin abincin.

Bayan ta kammala ta kwashe kayan ta kai kitchen ta sake gyara wajan, sai sha d'aya da rabi na safe ta kulle gidan kai tsaye gidan Zakiyya ta wuce.
Lokacin da ta shiga mijin Zakiyya yana fita a mota tana tsaye a kusa dashi suna sallama suka gaisa ta shiga ciki, bata jima da zama ba ta shigo tana fad'in, "Hajiya Fidyn Alhaji Bello, wallahi yarinyar nan farin jini gare ki kinga yadda ya tayar min da hankali jiya? Ga Sweet yana nan hankalina ya tashi kar yaji ina waya dashi" ta fad'a tana zama kusa da ita.

Fiddausi ta d'aga kai ta kalle ta tace, "Daman ya sanki ne?."
"Ina ya sanni, ai a cikin wannan awannin ya saka anyi bincike a kanki da nima har number ta aka samo masa ya kira ni shifa wallahi da gaske yake ya za'ayi, nace masa to yau mu had'u a nan dan Abban Fahad jirgin sa a America zai sauka yau."
"Zakiyya ni wallahi tsoro nake ji fa."
"Tsoron me? Dalla kar ki bada ni. Tun muna makaranta burin ki auren wanda zai d'auke ki ku tafi America ne, yanzu kuma kin samu shine zaki dinga jin tsoro?."

Fiddausi ta karyar da kai tace, "Kiyya Ibrahim fa?." Zakiyya taja tsaki tace, "Uwar sa, ke nifa kin san tun farko bai min ba kawai rabon Ameer ne ya saka na saduba, yanzu kuwa lokaci yayi da zaki nuna masa kefa ba sa'ar sa bace daman ya kamata ya fahimci hakan ai."

Fiddausi ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru bata ce komai ba Zakiyya ta kuma cewa, "in kuma kina ganin baza ki iya ba ai ba wani abun bane ba Fiddausi, sai kita zama a gidan da dubu goma zata gagare ki kece a wahala ai ba wani ba. Kuma wallahi ko a gidan ku in kana da kud'i anfi sonka, ke kanki a gidan ku anfi son y'an uwan ki dan sune masu zuwa Saudia da mazajen su ke kuwa ko zaria baku tab'a zuwa ba Keda shi ba. A haka kuma zaki zauna dashi?."

Fiddausi tace, "Ina son rayuwar jin dad'i Kiyya kuma ina burin shigar ta zan kuma yin komai dan ganin na shiga. Amma ta wacce hanya Alhaji Bello zai aure ni bayan ina d aure?. Wannan shine kawai tunanina amma bawan dan bana son rayuwar bane."
"Kashe auren zamuyi ai, ta dole zamu saka ya sake ki."
"Amma me zance a gida?."
"Ai baza mu rasa abin fad'a ba, daman gashi kina da ciki yana sakin ki sai mu zubar da cikin shikenan kinga kin gama idda a lokacin zaki iya aure."

Ta sauke numfashi tace, "Hakan kuma babu matsala?." Zakiya tayi tsaki tace, "Wacce matsala ce? Sai dai in ke zaki bamu matsalar ban sani ba ko soyayyar sa tayi miki yawan da baza ki iya rabuwa dashi ba."
"So kuma Kiyya? Hmmm ai daga ranar dana tabbatar bazan samu mafarkina ba a tare da Ibrahim ba shikenan nake jin yana fita daga raina. Amir nake ji dan shi d'ana ne kuma Ina son sa."

"kina da uwa da y'an uwa koni zan iya rik'e miki Amir balle su. Ke in fa zaka duba y'ay'a a wannan zamanin wallahi babu abinda zaka cimma a rayuwar ka, dan haka ki saki jiki kawai Hajiya meye a cikin ido banda ruwa...? Alhajin nan bada iskanci yake neman ki ba aure yake so kuyi sabida kin masa daga jiya zuwa yau, kina auren sa wallahi kaf din mu kin kere mu sai dai mu biyo bayan ki, har ita Meena d'in da kike hange sai dai ta biyo bayan ki."

Fiddausi tayi shiru tana tunani kafin tayi murmushi su tafa tace, "Wallahi sai nake ji kamar kina cire min fargabar da tashin hankali. Yanzu k'arfe nawa yace zai zo?."
"Yace min ko wanne lokaci zai iya zuwa bai bani time ba, amma nasan bazai wuce zuwa la'asar ba dai haka."

Wayarta taji tana k'ara ta kalla tace, "Kinga ma shine, wataƙila ko yanzu zai shigo" ta fad'a tana d'aukar wayar ta saka a speaker tace, "Barka da safiya Alhajin Allah."
"Barka malama Zakiyya, ina fatan mutuniyar zata amsa gayyatar mu dan wallahi banyi bacci ba tunanin ta kawai nake yi."

Ta kalli Fiddausi tayi murmushi tace, "Ai Alhaji ta amsa gayyata gata a zaune a kusa dani, sai dai nasha fama kafin ta amince kasan ta akwai jan aji." Murmushi taji yayi mai sauti yace, "Ai girman tane, tunda ta iso bazan bar madam tana jirana ba zanzo yanzun nan. Kuma sakamakon saka ta tazo da kika ki tura min account number ki akwai kyauta."

Zakiyya ta buɗe idanu tayi farii tace, "Ina matukar godiya, Allah ya barku tare." Ya amsa da amin yace, "Yanzun nan zan k'araso, a bawa Fid haƙuri na ajjiye ta jira."
"Ai babu komai sai ka k'araso" ta fad'a tana yanke wayar ta kallli Fiddausi tayi dariya itama haka tace, "ke ba'a nema da sanyin jiki bara nayi maza na tura masa kar ya manta" ta fad'a tana tura masa account number d'in.

Ta kalli Fiddausi tace, "Tashi maza muje ki canja kaya akwai wasu da aka kawo min daga d'inki bayan tafiyar ki jiya muje ki saka zasu fi miki kyau" tare suka tashi zuwa saman Zakiyya ta nuna mata kayan riga da siket ne ta karb'a ta saka ai kam sun mata kyau sosai sun kamata musmaman daga sama wajan k'irjin ta komai ya fito ras kamar kayan ta.

Window Zakiyya taje kalla tace, "Gashi can fa ya iso, maza saka turare ki sakko irin baki san yazo din nan ba kar ki saka mayafi in kika sakko kika ganshi sai ki dawo ki saka mayafin kinga yaga komai ai, bara na kira mai gadi ya buɗe masa" ta fad'a tana fita ita kuma ta saka turaren kamar yadda tace.

Wajan tagar taje tana kallon sa har ya shigo cikin falon tayi dariya tare da yin fari da ido tana jin farin ciki a ranta wai kamar wannan Alhajin ne ya haukace haka a kanta, ta fito daga d'akin ta sakko k'asa, "Wai ina Fahad ne tunda nazo fa ban ganshi ba, ban san meyasa kike son bawa y'an aiki rik'on sa ba wallahi ke gabad'aya bakya son raino bayan kuma...." ta fad'a tana sakkowa irin bata san yazo d'in ba suka had'a ido dashi hakan ya saka ta dakata da maganar.

Binta yake yi da mugun kallo domin kuwa tayi masa bala'in kyau cikin kayan komai ya fito a jikin ta duk yadda ta motsa ko ina na jikinta motsawa yake yi hakan ba k'aramin d'aukar hankalin sa yayi ba ya kasa daina kallon ta, kallon ta yake bai san ya saki baki ba yana had'd'iye yawu tare da lasar lab'ba ba sai da Zakiyya ta d'aga mata gira sai ta basar tace, "meyasa kika yi haka?" Ta fad'a tana juyawa da sauri ta hau sama jikin ta na sake yin shaking har ya daina ganin ta bai d'auke ido daga wajan ba.

Sai a sannan ya kalli Zakiyya yace, "Ina son k'awar nan taki Zakiyya, na rasata basan abinda zai same ni ba. Daga naira million d'aya zuwa d'ari zan baki indai zaki shawo min kanta ta amince dani." Murmushi Zakiyya tayi zatayi magana suka ga ta sakko da mayafi ta k'araso ta zauna ya sake binta da kallo yana shak'ar khamshin turaren ta yace, "Ranki ya dad'e, barka da fitowa."

"Barka da rana" ta fad'a fuskar ta ba yabo babu fallasa.
"Barka dai Gimbiyata, ina fatan na same ki lafiya."
"Lafiya" ta fad'a a tak'aice kafin yayi magana tace, "Meyasa kake nemana?."

Ya gyara zama yace, "Alkhairi ne ya saka nake neman ki Fid, tunda na ganki jiya Allah ya saka min soyayyar ki a zuciyata, ina sonki kuma auren ki zanyi." Ta kalle shi tace, "Amma na fad'a maka ina da aure ko? Kiyya da wanne yare zan fad'a masa ina da aure ya fahimta?" Ta fad'a yana kallon Zakiyya.
Zakiyya tace, "Ya fahimta ai Fidy, dama yake so ki bashi domin gina tasa rayuwar auren."
"Ana aure akan aure ne daman?."
"A'a, kawai dai yana so ya rabaki da wanda bai dace dake ba. Fidy tun farko kin san dai wancan talakan ba ajin ki bane irin su Alhajin nan sune tsarin ki. Rabo ne kawai ya kai ki gidan ibrahim rabon Amir kenan, yanzu kuma lokacin barın ki gidan yayi."

Ta sauke numfashi tana kallon sa ganin ya zuba mata ido ko d'auke kai bayayi ta tab'e baki ta jingina da kujera yace, "Indai zaki kashe auren ki wallahi zan aure ki, ni sai na samu mijin naki ma na biya shi indai zai bar min ke, ko nawa yake so zan bashi wallahi. Daga naira million d'ari zuwa sama zan iya bashi a kanki domin kin fimin kud'in mahimmaci. Fid dan Allah ki taimaki dattijon nan domin in bai same ki ba akwai matslaa."

Kamar zatayi kuka tace, "Taya kuke ganin zan iya kashe aurena?." Yadda tayi maganar sai da tsigar jikin sa ta tashi ya kalle ta yace, "Ko meye za'ayi Fid a kanki." Duk sukayi shiru basuyi magana ba yace, "Ina da uku biyu yara tara, bakwai sunyi aure biyu ne kawai suka rage. Baza ma ki zauna cikin su ba zan d'auke ki na kai ki America kiyi zaman ki a can kiyi duk abinda kike so domin kalar ki ta zaman turai ce."

"Salon na aure ka ka karo min ta hud'un ko?." Da sauri yace, "Har Abada Fid, wanda yake da kamar ki ina shi ina auren wata?." Ya kalli Zakiyya yace, "Kawar mu ki saka baki mana, bana son rasa wannan halittar Allah ya sani." Zakiyya tace, "Kar ka damu Alhaji, in sha Allah kamar ka same ta ka gama." Ya yi ajiyar zuciya yace, "Indai hakan ta tabbata zan miki gagarumar kyautar da sai kinji kamar ba'a duniya kike ba."


"Zakuwa ayi min kyauta domin hakan zata faru in sha Allah" ta fad'a tana murmushi tana kallon sa. Yace, "Da wuri nake so hakan ta kasance, inda hali auren ya mutu a yau tayi idda ta wata uku ayi auren nan a wuce wajan muyi azumin Ramadan a saudia" ya fad'a yana kallon Fiddausi har lokacin fuskar ta bazaka fassara abinda yake ranta ba.

Zakiyya tace, "In sha Allah. Na fad'a mata Amir koni zan rik'e mata shi karta damu."
"Sai na rik'e Amir din nima ai, abinda ta haifa ai nawa ne nima" ya fad'a yana kallon ta. Agogo ya kalla yaga lokacin azahar yayi yace, "Badan na gaji da kallon ta ba zan tafi sai dan ayyukan da suke gabana, dan Allah Zakiyya ayi min k'ok'ari cikin satin nan komai ya k'are wallahi ni kad'ai nasan halin da nake ciki daga jiya zuwa yau."

Zakiyya tace, "Kar ka damu fa Alhaji, wannan kamar an gama ne." Ya mik'e tsaye ya d'auki ledar hannun sa ya ajjiye a kusa da Fid yace, "Gimbiya zan tafi bazan samu wata kalma mai dad'i ba?." Murmushi tayi mai kyau tace, "Ka gaida gida."
"Kin biya ni, da ace kin zama mallakina dana bada tukwuicin wannan murmushin, amma Allah ya kaimu gaba" ya fad'a yana yin gaba yana murmushi.

Da hannu Zakiyya tayi mata alama da tana zuwa tabi bayan sa suna fita ta d'auki ledar nan tayi karo da zunzurutun kud'i y'an dubu dubu kamar zasu yi magana. Jim kad'an Zakiyya ta dawo tana ihu tana fad'in, "K'awata kin dace wallahi, burin ki ya gama cika a duniya Saura na lahira kawai zaki jira." ta fad'a tana rungume ta cikin farin ciki kamar yadda itama Fiddausin yake cikin farin ciki.

D'agowa tayi daga jikinta tace, "Kin san naira million biyu ya tura min sabida kawai na saka kinzo? Ke kiyi tunanin in na saka kika aure shi nawa zai bani?, ai wallahi dole ma ki aure shi" ta fad'a tana dariya kafin ta kalli ledar tace, "Nawa ne a ciki?" Ta fad'a tana bude ledar ganin kud'in ya saka ta sake yin ihu suka sake rungume juna Zakiya tace, "Ashe kin iya acting ban sani ba?, wanna shagwaɓa ba dole ki saka ya sake susucewa ba. Gabadaya ya fita daga hankalin sa Ina Lura dashi duk inda kika motsa kallon ki yake, ke Allah ya isa wallahi shekarun da kika kwashe da wancan banzan."

Suka yi dariya a tare tafa Fiddausi ta d'auki rafar kudin guda d'aya tana girgiza ta tace, "Ban tab'a jin son auren nasa a zuciya ba sai yanzu Kiyya, ya zamuyi da Ibrahim? Dan ya zama dole n rabu dashi ko baya so."


#Book1
#Nana Haleema
#F5
#Share saboda Allah.

*MAI ƊAKI...!*
FitattuBiyar

©️ *Nana Haleema.*


*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

*Book 1*
*Page 12*

Jan hannunta tayi ta zauna akan kajure ta kalle ta tace, "Ta dole ai zamu saka ya sake ki ba wani abun ba, yanzu dai kafin wannan yasan da cikin jikin ki?." Fiddausi ta girgiza kai tace, "Bai sani ba kuma bazan fad'a masa ba."
"Yauwa kar kiyi gaggawar fad'a masa, ki buɗe shafin rashin mutunci daga yau kinga yana sakin ki sai mu zubar da cikin shikenan kin gama iddah."

A tare suka tafa cikin zallar nishad'i Fiddausi tace, "haka za'ayi. Amma bana tunanin akwai abinda zan yiwa Ibrahim da zaiyi saurin sakina domin kin san shi yana da haƙuri kamar bashi da zuciya, kome nayi masa wallahi zai iya jurewa. Ki duba wulaƙancin da nayi masa akan had'a shinfid'a dani amma wallahi baiyi fushi ba shine ya sake nemana, kuma atamfar da nake d’aga murya a kai yau ya siyo min."

Tsaki Zakiyya tayi tace, "Indai zaki tuna wannan to wallahi bazaki tab'a samun abinda kike so ba. Ki ajjiye batun haƙuri ko wani abu malama kiyi abinda yake gabaki in kika yi sake wallahi garin neman gira zaki zo ki rasa idanu."
Ajiyar zuciya tayi tace, "Zanyi fa Kiyya ke kin san zanyi, kawai ina jin zuciyata wani iri ne wallahi."
"Yauwa, in kika yi mana asarar Alhaji Bello ai kin cuce mu wallahi. Ayi auren nan a wuce wajan ku wuce Saudia."

Farrr tayi da idanu ta buɗe kudin ta fito dasu tace, "wanda ya bani jiya mafa suna nan Kiyya badan kin bani jaka ba haka zan tafi dasu a hannu, ga wasu wanda suka fi wad'annan yawa ina zan kaisu?." Kiyya tace, "ki kashe."
"Bazan iya ba ai, kinga zan d'auki wani abun dan ina so nayi siyayya a hanya" ta mik'a mata wasu tace, "Ajjiye min wannan sabida tsaro."

Karb'a Zakiyya tayi tace, "Ki saka a account mana."
"Tuni ya jima da zama domant ai account d'in, ina naga kud'in da nake sakawa ba dole su kulle ba?." Zakiyya tayi dariya tace, "Kawo wayar ki na buɗe miki Opay yanzu sai na saka miki na karb'i cash d'in daman Sweet yana nema.” Ba musu ta bata wayar ta kalli wayar ta kalle ta taja tsaki tace, "Wallahi yanzu za'a canja wayar nan, kin gama amfani da ita daga Yanzun nan" ta fad'a tana tashi ta fita.

Jim kad'an ta dawo tace, "yauwa yanzu za'a kawo waya ki zab'a ki darje wannan karakani toilet d'in mai aikina zan bawa." Ita dai bata ce komai ba sai akayi sallama aka shigo Zakiyya tace, "Yauwa kawo muga." Ya k'araso yana fadin, “Hajjjaju kamar nasan zan amsa kiran ki yau ban fita kasuwa ba.” Karbar wayoyin leda ya bata tana dubawa tace, "Wannan za'a d'auka. Nawa?." Mai wayar yace, "Hajajju IPhone 11 ce. Naira dubu dari biyu da hamsin ce kacal babu tsada.”

Zakiyya ta d'auki kud'in ta bashi tace, "Gashi nan, na siya." Karb'ar kud'in yayi ya bata shaidar biya yana fad’in, “Ai wallahi nasan harka dake babu Wa’alaiki a fad’a a cika kenan.” Karb’ar shaidar tayi ya tafi Fiddausi tace, "haba Kiyya, waya harta wannan kud'in?." Hararar ta tayi tace, "ta hannuna miliyan d'aya ce da wani abun, yanzu kike cewa baki san me zakiyi da kud'in ba dan an siyi wayar dubu dari biyu wani abun ne?. Mtswww kina bada ni wallahi, kamar ba Fidyn dana sani ba" ta fad'a tana ‘bare kwalin wayar.

Tashi tayi ta saka chajin wayar ta dawo suka cigaba da hirar yadda abin zai tafi cikin tsari yadda babu wanda zai kawo suna sa hannu a abun kafin su tashi suyi sallar azhar a d'auki sabuwar waya ana saita ta.

*☆☆☆*

Tun bayan tafiyar Rukky Ameena take zaune daman zaman su tare da Rukky ne yake d'auke mata wata damuwar amma tunda ta tafi sai take jinta kamar marainiya komai baya yi mata dad'i gidan gabad’aya yana sake fita daga ranta. Tana zaune shiru daga ita sai Zaitun da take wasa a jikinta gabad'aya hankalin ta baya jikinta.

Har ya shigo bata sani ba sai girgiza kafad'arta taji anyi ta kalli wajan da take jin motsin suka had'a ido dashi yace, "Tunanin me kike?." Yanayin fuskar sa sai ya hanata magana domin kuwa a d'aure take kamar yadda ya saba yi mata a kwanakin baya ba kamar yadda ya sake a kwanakin nan ba.

"Magana nake miki" ya sake fad'a yana d'aukar Zaytun da take mik'a masa hannu ya zauna yana kallon Ameena. Kai ta girgiza tace, "Babu komai, bana jin dad'i ne kuma kasan hakan."
"Allah ya k'ara lafiya" ya fad'a a tak'aice yana tashi rik'e da Zaytun ya hau sama bai sake kallon inda take ba a ganin sa Matsalar tace tunda tak’i fad’a masa.

Hawan sa saman ba wahala aka kira sallar magriba ta tashi da niyar yin alwala sai ta tuna bata cikin tsarki ma sai ta canja akalar ta zuwa hawa sama. D'akin ta ta shiga

Please Login or Register in order to submit comment