Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan ta sake tana hira da Yayarta kamar ba ita ba. Bayan sun idar ne Yaya tace, "Badan na gaji ba dana lek'a gidajen su Sumayya wallahi." Ameena tace, "Sai kije gobe."
"Kai da wuri nake so na wuce gobe gaskiya, da dai Yaya Adam yana Kano a can ai zan kwana bazan yi abin kunyar kwana a gidan k'anwa ba."

Ameena tayi dariya tace, "ai tafiya ce mai nisa kika yi ba wani abun bane ba." Yaya tace, "Kedai kawai baki san yadda nake jina a d'aure ba wallahi." Dariya kawai tayi suka cigaba da hira. Kamar yadda ta saba bayan sallar magriba tayi girki tayi wanka ta shirya duk da batayi kwalliya ba amma dai tayi kyau tana zaune wajan su Yaya suna ta hira har Yusuf ya dawo bata sani ba. Fitowa tayi da niyar dauk'ar lemo a fridge nan tayi karo da leda a kan stool har zata wuce sai ta k'arasa ta bud'e taga cake ne k'anana masu kyau a ciki ta kalli saman sa dan dai tasan ita ba ma'abociyar yin cake bace Tunda mai gidan baya ci sai dai ya siyo taci ta bayar dan yasan tana so.

"Ya dawo kenan?" Ta tambayi kanta tana sake kallon sama kafin ta k'arasa wajan varanda ta bud'e nan ta hangi motar sa a ajjiye alamun ya dawo, baya ta dawo ta kulle varandar ta d'auki d'aya a cikin cake din ta fara ci dan a tunanin ta ita ya tawowa dashi kamar lokacin baya. A daidai nan ya sakko ya bita da kallo itama shi yake kallo a fusace ya k'araso ya kwace ledar hannun ta yace, "waye ya baki damar tab'a min cake? Dan kawai kinga abu sai ki d'auka kici naki ne ko kuma ajiya kika bani ko aike na kikayi?."

Ganin yadda yake fad'a sosai sai ta zuba masa idanu tana kallon sa ganin hannun sa da takardar cake din da alama yaci kenan, mamaki take yi dan baya ci Tana kuma mamakin abinda ya saka shi fad'a haka. ganin tayi shiru sai binsa sa da take da kallo ya saka shi yin tsaki ya kwace ledar daga hannun ta yace, "karki sake kuskuren tab'a min abu indai bani na baki ba, bana son bincike."

Gabad'aya daina Jin taste din cake din tayi hakan ya saka ta had'd'iyewa dakyar tace, "Kayi hakuri na saba d'auka ne in kazo dashi sanin ni din kake kawowa kai ba ci kake ba." A sanyaye tayi magana hakan ya saka shi sakar mata harara yace, "to yanzu Ina ci, kar ki sake wannan gangancin na fada miki, in naki ne in na shigo zan baki." Kai ta girgiza kai ya saka yin tsaki ya juya zai hau sama tace, "ina zan kawo maka abincin?."
"Ki barshi bana ci kar kuma ki dame ni bana son takura" ya fad'a yana hawa sama ya barta a tsaye Tana kallon sa har ta daina ganin sa sai sautin kulle k'ofa da taji.

K'asa ta sauka ta shiga kitchen ta kulle kanta ta fashe da kukan da ya zamar mata abokin hira, sai da tayi mai isar ta sannan ta fito bayan ta wanke fuskar ta ta koma saman d'akin dasu Yayan Kaduna take. Hira ta samu sunayi da Amira sama-sama ta shiga da sallama ta zauna Yaya ta bita da kallo tace, "Na dauk'a kin tafi wajan mijin ki sai da safe kuma?." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ganin hakan sai Yaya tace, "Ba nisanta kanki zakiyi dashi ba a wannan lokacin samu zakiyi ki kusanta kanki dashi fiye da baya, wannan baya-bayan da kike dashi bazai haifar miki d'a mai ido ba."

Numfashi ta sauke sannan tace, "To Yaya zanje yanzu, ban sanar dashi zuwan ki bama da yazo kun gaisa."
"Ma gaisa da safe in Allah ya Muna mana, yanzu tashi kije ga Zaitun nan har tayi bacci."
Amira tace, "Anty ki bar min zaitun din a nan in baza tayi kuka ba." Amina ta kalli Zaitun tace, "Baza tayi kuka ba, bara na kawo miki maganin tarin ta ki tashe ta ki bata tasha."

Yaya tace, "Ya kamata kuwa dan naji tun d'azu take tari." Amina bata ce komai ba ta tashi ta fita zuwa dakin ta. Bata ga maganin ba hakan ga bata tabbacin yana saman Yusuf ta kama k'ugu tana kallon sama tare da furzar da iska dan bata son zuwa inda yake. Bata da mafitar da ta wuce dole ta fita zuwa saman nasa duk jikin ta a sanyaye.
Hannu ta d'ora da niyar murd'a handle d'in d'akin sa sai ta fasa ganin ta a bud'e ma zata tura taji yana fad'in, "Ke yayi dad'i my love ban tab'a cin sa ba sai wannan da kika bani."

Dariya taji yayi yace, "Bari kawai kedai burina bai wuce na ganki a cikin gidan nan matsayin matata ba, gabad'aya bana jin sha'awar ko wacce mace sai ke kawai." Shiru yayi alamun Ana bashi amsa kafin taji ya sake cewa, "Hmmm! Bari kedai kawai waye yake ta waccan Kullum abu ba canji? Ke nifa da ke na samu bazan sake yin aure a rayuwata ba, ta ko ina kin had'u baki da abin kushewa ko kad'an, ni na tabbatar zan samu abinda nake so a wajan ki shiyasa bani da fargabar komai. Kya had'a data gidan nan da ko......." Sai kuma taji yace, "Hmmm a dai yi shiru kawai."

K'irjin tane yake duka sosai bata san ta bud'e dakin ba sai had'a ido da sukayi dashi ta haddiye abinda yazo mata wuya tayi k'ok'arin mayar da hawayen idanunta ta shiga ciki kai tsaye inda ta hango maganin tayi ta d'auka ta fita ba tare da ta sake kallon sa ba.
Jikin sa ne yayi sanyi dan ya tabbatar taji me yace yasan kuma k'arya yake yi abinda yake fad'a ba gaskiya bane kawai dan waccan taji dad'in kalaman sa ne, ya d'an cize bakin sa kamar ya tashi ya biyo ta sai kuma ya fasa ya cigaba da waya da masoyiyar sa.

A guje ta fad'a kan gado tana kuka kalaman da ya fad'a suna mata amsa kuwa a kunnen ta ta saka hannu ta toshe kunnen ta zuciyarta na bugawa sosai, bata d'auka abin nasa ya kai haka ba shiyasa jin kalamin sa ya tayar mata da hankali. tashi tayi zaune Tana goge idanun ta amma wani hawayen ne yake sake sauka ta tashi da son kawar da tunanin ta shiga wanka. A haka ta shirya ta fita ta kaiwa Amira maganin ta dawo dak'in ta kwanta badan tana jin bacci ba sai dan kawai bata so Yaya tasan tana dakin ta ba dakin sa ba.




#Share
#Vote
#Comments
#Book1
#Nana Haleema

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

Masu nema daga farko ku shiga WhatsApp channel zaku samu.
https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*


*Book 1*
*Page 14*




Ta jima tana bacci, sallar asuba ma dakyar ta iya tashi tayi Tunda ta koma ta kwanta take bacci sosai, sai da rana ta fito ta farka tunawa dasu Yaya suna nan ta tashi da sauri ta shiga band’aki ta wanke bakin ta ko wanka batayi ba ta fito zuwa d’akin dasu yayan suke.

Da sallama ta shiga Yaya ta amsa tana zuba kaya a jaka ta juyo tana kallon ta itama ita take kallo kafin ta dauke Kai tace, "Yaya barka da Safiya." Kallon ta tayi tare da yin murmushi tace, "Barka dai! Maza d’auki Zaytun sai kuka take tun d'azu." Ba musu ta d’auke ta ta d’ora a cinyar ta ta fara shayar da ita.
"Ina kwana Anty Amina?" Amira ta fad’a tana kallon ta ta amsa tana fad’in, "Amira amma dai kin had’a muku breakfast ko?". Tayi dariya tace, "Tun yaushe ma, Taya Mama zata kai yanzu bata karya ba kin San ai bazai yu ba."


Amina tayi dariya tace, “Wallahi bacci nayi ne sosai shiyasa.” Yaya tace, "To Ameena mufa Mun shirya tsaf daga nan zamu dan zaga dangi zamu wuce Bauchi." Da mamaki Ameena tace, "Kai Yaya wai tafiya zakuyi?".
"Ga zahiri Amina" ta fada tana zuge zip d’in k’aramar jakar. Amina ta marairaice fuska tace, "Amma Yaya baki fada min ba, na d’auka sai gobe wallahi zaku tafi. Dan Allah ku bari sai gobe sai ku tafi bana so ku tafi yau wallahi" ta fad’a kamar zatayi kuka tana kallon su.

"A'a wallahi bazamu Kai gobe ba, ke kin san da yadda na iya kwana a gidan nan naki kuwa? Matsayin uwa nake a wajan ki kuma nazo gidan y'ata na kwana, baki ji yadda nake jin nauyi ba kamar an daure ni wallahi. Yau zan tafi minti talatin bazan k’ara a gidan nan ba." Hawaye suka sakko daga idanun Ameena ta janye Zaitun daga jikin ta ta kalli Yayan tace, "Matsayin uwa kike a wajena Yaya shiyasa nayi tunanin zaki zauna dani na kwana biyu kodan zuciyata tayi sanyi, in kika barni a nan ciwo zai iya kamani. Zaman ki daga jiya zuwa yau kina ganin bacci nayi mai nauyi Yaya, Yaya zaman ki a gidan nan kamar magani ne a wajena wallahi, bana so Kiyi nisa dani.”

Jikin Yaya yayi sanyi amma bata nuna mata ba sabida kar hankalin Ameena din ya tashi ta zauna a gefen ta tace, "Hakuri zakiyi Ameena, zamana a nan bazai canja abinda Allah ya riga ya rubuta ba. Kiyi hak’uri ki daure komai zai wuce kamar bai faru ba, in kika rik’e abubuwan dana fad’a miki tabbas baza kiyi dana sani ba." Ido Ameena ta goge ta kalli Amira tace, "Daughter ki taya ni bawa Yaya hak'uri dan Allah ta bari sai gobe."

Amira ta kalli Yaya bata ce komai ba ita tace, "Bazan zauna bafa Ameena, tafiya zamuyi ko meye zai faru ma yi magana a waya.”
"To ki bar min Amira dan Allah."
"Bana yanke hukunci mahaifinta bai sani ba, ki bari mu koma sai na tambayar miki shi in ya barta sai ta dawo tayi miki wata guda ta koma tunda bata fara makaranta ba yanzu."

Ameena ta girgiza kai jikin ta duk ya mutu ta sake goge idanun ta, zuwan Yayar tata ya saka tana ji tamkar mahaifiyar su ce tare da ita, hakan ya k'ara mata nutsuwa a zuciyarta shiyasa bata son rabuwa da ita gabad'aya. Yaya ta kalle ta tayi dariya tace, "Kiyi hakuri Ameeantun Yaya Adam ki saki jikin ki komai lokaci ne dashi, auren da an d’aura shikenan komai zai wuce kiyi fatan Allah ya baki ta gari kawai. Nasan kina da kyakykyawar zuciya baza kiyi wani abun da zaki cutar da ita ba, nasan baza ki biyewa rud’in zuciya ba kice zaki bi malam ko boka dan hana auren ba, kiyi addu'ar Allah yasa haka itama take kamar ki kuyi zaman ku Lafiya. Shifa namiji da kike gani in ya d’auko aure sai kin jure dan zaki ta ganin abubuwan da baki kawo su ranki ba, haka nayi fama da Abban su Amira lokacin da ya auro matar sa ta biyu, wallahil azim kud’in abinci baya bamu gabad'aya kudin sa na aure ne. Ki gode Allah ke akwai ci da sha ni da akayi min tawa babu abincin kirki a gidan amma haka zai kwashe kudin sa ya Kai mata."

Ta dafa kafad'arta tace, "Ga Amira nan ki tambaye ta wahalar da muka sha ban fad'a miki bane sabida bana son yawan rok’on ke kin sani balle ma kina iya bakin kokarin ki a kaina. To Kiyi hak’uri nima da nayi hak’uri yanzu gashi komai ya wuce ta shigo taga bazata iya zaman gidan ba ta fita ta barni dashi d’in. Daman in kika ji ana kayi hak’uri an maka wani abun ne Ameena; amma zaki ga ribar sa wallahi. Sai kin daure dan a wannan zamanin da muke ciki babu macen da zata samu miji kamar Yusuf ta bari ya kubce mata, duk hanyar da zata bi zata bi domin ganin ta sake rik'e shi bai je ko Ina ba. Kishiya akwai ciwo na sani sai Kinyi hak'uri kin kawar da kanki komai mai wucewa ne."

Kai ta girgiza dan kalamam sun shiga jikin ta sosai tace, “in sha Allah zanyi Yaya. Ki dinga min addu'a kin fi kowa sanin ya Yusuf yake a zuciyata ji nake kamar nayi hauka wallahi, Daughter dan Allah ki taya ni da addu'a kema" ta fad'a hawaye na sake sakkowa daga idanun ta tana kallon Amira. Dakyar Yaya ta danne kukan ta dan zuciyar ta ta kare tafi kowa sanin irin son da Ameenatu take yiwa Yusuf sarrafa kishin ta akan sa abu ne mai wahala dan ma Tana da juriya ne da kawar da kai ne.

Amira ta kalla da take kuka tace, "Ya isa Malama, kema Ameenatu ki bar wannan kukan kiyi abinda nace miki kawai, shine maganin damuwar ki wannan kukan ba magani bane.” Sai da tayi kukan ta sosai sannan ta share hawayen ta ta tashi tsaye ta d’auki Zaitun ta fita daga dakin. Yaya ta kalli Amira tace, "Tashi ki d’auki kayan mu sauka bana so rana tayi mana sosai, in munje in ya barki sai ki dawo zuwa jibi." Kai kawai ta daga dan tausayin Ameena take ji a ranta ta d’auki kayan suka fito.

Sakkowar sa daga sama kenan yake jiyo kukan Zaytun a tsakiyar falo, da sauri ya k’arasa ganin ta a kwance akan carpert da alamaa daga kan kujera ta fad'o, d’aukar ta yayi har lokacin kuka take nan da nan yaji ransa yayi mugun b'aci yana kallon falon yana so yaga ta inda zata b'ullo.

Da leda a hannun ta ta dawo falon ya k’arasa kusa da ita yana aika mata da harara yace, "Wai kwana biyun nan me yake damun ki ne? Dan tsabar shirme da wulak'anci Zaitun ce tayi miki wani abun da kike barin ta tana kuka irin haka?. Kika d’ora ta akan kujera kika yi tafiyar ki kika barta ta fad'o in taji ciwo ko a jikin ki ko?, meyasa baki da hankali wani lokacin?."

Jin yadda yake fad’a sosai sai ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa ya sake fusata kamar zai dake ta yace, "Kina ji ina miki magana kika yi min banza? Wato ga mahaukaci ko?."
"Allah ya Baka hak’uri" ta furta ba tare da ta kalle shi ba yaja dogon tsaki yace, "Baza ki karb’e ta ba kenan ko?." Hannu ta saka ta mik’a zata karb’e Zaitun ta kwanta a jikin sa alamun bazata zo ba.

"Tsabar shirme da rashin hankali har kin dasawa yarinya tsoron ki gashi tana gudun zuwa wajan ki, kina azabtar da ita kina barinta ki tafiyar ki kina abinda bashi da amfani kamar ba ke kika haife ta ba. Dallah Malama ki karb’e ta ki bata nono tasha ko zata daina kuka!." Bata ce masa komai ba ta karb’e ta yaja tsaki ya juya zai bar wajan yaji ance, "Yusuf barka da safiya."

Cak ya tsaya gaban sa ya fad’i ya juyo a hankali suka had’a ido ya wara idanu waje cikin mamaki yace, "Kai Kai! Yaya saukar yaushe?." Murmushi mai kama da yaqe tayi masa tace, "Saukar jiya gashi har zamu koma."

Kana kallon sa zaka fahimci yanayin sa sanyin jikin sa ya bayyana amma bai bari hakan yayi tasiri ba yace, "Innalillahi! Wai hakan yana nufin a nan kika kwana Yaya?" Ya kalli Ameena yace, "Meyasa baki sanar dani dan Allah?" Ya fad'a kamar zaiyi kuka yana kallon ta cikin rashin jin dad’in hakan.

Ganin yadda Ameena ta kasa magana sai Yaya tace, "Kar ka damu Yusuf ni nace ta kyale ka ma had’u yau, daman ziyara ta kawo ni naso ma tafiya gidan y’an uwa itace ta dage sai na zauna a nan."
"Amma banji dadi ba Yaya" ya furta a sanyaye yana kallon Ameena har lokacin bata ce komai ba.

Y’ar dariya Yaya tayi tace, "Babu komai wallahi, kar ka damu kanka." Sai a sannan ya kalli Amira yace, Amiran Mama ya makaranta?." Mugun haushin sa Amira take ji hakan ya saka a ciki ta amsa masa ta kawar da kai. Yaya tace, "To Aminene mu zamu wuce, Rana tana sake yi gwara muyi mu wuce kar muyi yamma.”

Da sauri yace, "Yaya baza'a yi haka ba, bara na saka a kaiki Ina zuwa" ya fad'a yana hawa sama ya juyo ya kalli Ameena ya cigaba da hawa saman. Numfashi ta sauke ta kalli Yaya da take kallon ta itama tace, "Ina zuwa Yaya" ta fad'a tana mik'awa Amira Zaitun tana hawa saman jikin ta a sanyaye.
Yaya ta kalli Amira tace, "meyasa bakya jin magana ne? Dan kinji sirrina da y'ar uwata shikenan sai ki canjawa mijinta?, naga da wasa kuke da dariya meyasa yau kika amsa masa a ciki?."

Tace, "Wallahi Mama mugun haushin sa nake ji maganar ma kawai dan ta zama dole ne."
"Kar ki sake aikata abinda kika yi, ko meye mijin tane har yanzu ya zama dole ki cigaba da girmama shi kamar yadda kike yi a baya. In kina taya ta jin haushi ne ke zata zo tana jin haushi ba gwaninta zaki mata ba, ki shiga hankalin ki dan ba’a shiga tsakanin miji da mata.” Amira tayi shiru bata ce komai ba Tana wasa da Zaitun da take yi mata dariya.


Ameena kuwa Tunda ta shiga falon sa taga ya juya baya ya kama k'ugu gaban ta ya fad'i tayi sallama ta k'arasa inda yake tsaye, juyowa yayi ya kalle ta yace, "Wulak'ancin naki ya kai har Yaya tazo gidan nan ta kwana ban sani ba?, ke a komai in baki b'ata min rai ba bakya jin dad'i ko Amina?." Kallon sa take cikin mamakin abinda yake cewa kamar ba shi bane yace kar tazo inda yake tace, "Kai fa kace kar nazo inda kake, banzo inda kake ba ta yaya zan.....!" A fusace ya dakatar da ita yace, "Zan tsinka miki Mari kika sake kika k'arasa maganar nan, da nace kar kizo inda nake babu wayar da zaki fada min zuwan ta?, ko text baza Kiyi min ba?, lallai sai kin saka an tafi dani a baki ana cewa Yayar matata wacce take matsayin uwa a gare ta tazo gidana har ta kwana ban sani ba ko?."

Shiru tayi bata amsa ba ya girgiza kansa cikin fusata yace, "kin kyauta ai hakan da kika yi daidai ne kinji ko? Ki cigaba da abinda kike yi kanki kike cuta wallahi. Bani account number ta na saka mata kudin mota.”
"Bani dashi" ta fad'a a taqaice bata kalle shi ba. Tsaki yaja mai tsaho ya dauk’i wayar sa yana dannawa yana fad'in, "Dan tsabar an raina ni har a kwana a tashi ban sani ba kawai sabida wulaqanci da son a jawo min magana, amma zanyi maganin komai wallahi in ma ana yin hakan ne dan zanyi aure anyi a banza domin aure babu fashi."

Kallon sa tayi jin yana ta mita shi kad'ai tana so taga anya giyar da yasha ta sake shi kuwa domin sai yana maye yake mata irin wannan d'abi'ar. Ido suka had'a bata janye nata ba shi ne ya d’auke nasa Idon yana girgiza kai kafin yace, "na tura miki dubu d'ari da hamsin, ki bata d'ari ki bawa Amira hamsin. Sannan zanyi magana da Sani zai kaita yanzu" yana gama fad'a ya zagaya ta baya ya wuce ta ya barta tsaye cikin mamakin sa da kuma al'ajabi da sanyin jiki.

Bata bari komai yayi tasiri a ranta ba ta sakko ta samu baya wajan da alama har sunyi sallama ta kalli Yaya tace, "Yaya ga dubu d'ari yace a baki, Amira kuma dubu hamsin yana account d'ina zan tura miki." Maimakon Yaya ta nuna farın ciki sai ta dafa kafad'arta tace, "Mun gode Ameena, Allah ya saka da alkhairi. Amma......" katse maganar tayi ta kalli Amira tace, "Keji bakin gate ki jira ni." Ameena tace, "zaki ga motar Sani da yake kaini Bauchi shine zai kai ku." Kai Amira ta d'aga kawai ta fita hannun ta rik'e da zaitun.

Yaya ta kalle ta tace, "Bayan wannan canjnawar da Yusuf yayi Anya babu wani abun da yake miki Ameena?." Ameena tayi murmushi tace, "Babu komai Yaya, kin San Ina da kishi ne kinfi kowa sanin son da nake yi masa."
"Bayan wannan akwai wani abun Ameena dan sai nake ganin son kamar ba irin na baya kike masa ba, ki fad'a min ni tamkar Mama nake a wajan ki, baki da wacce ta fini mu biyu Maman mu ta haifa, ki fad'a min damuwar ki Ameetau."

D'ago Idon ta tayi ta kalli Yayan zuciyar ta na fad'a mata kawai ta sanar da ita halayyar da Yusuf ya shigo da ita ko zata samu Sauk'in abinda take ji amma wata zuciyar na hana ta yin hakan, numfashi ta sauke tace, "Babu komai Mama ki taya ni da addu'a kawai." Yaya tace, "Addu'a kullum cikin yin ta ake Ameena, Allah ya yaye miki koma meye yake damun ki. Ki rik'e addu'a kar kiyi sake dan Allah itace kawai maganin ki.” Kai kawai ta d'aga suka fito tare har bakin motar ta karb'i Zaytun Yaya ta shiga motar sukayi sallama suka tafi bayan ta cika musu boot da kayan abinci da kayan tab’a ka lashe.




#Vote
#Share
#Comments
#Book1
#Nana Haleema
#F5.

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar


©️ *Nana Haleema.*


Masu nema daga farko ku shiga WhatsApp channel zaku samu.
https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36


*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin

Please Login or Register in order to submit comment