Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau yayi domin har hugging d'ina yayi" ta fad'a tana kulle fuska da hannun ta. Dariya ta sake yi ta dake ta a bayan ta tace, "Kin rikita shi ne, ina tabbatar miki da ko babar tasa ce da gaske bata so ko matar tasa a wannan karon bazai tsallake tarkon mu ba, zai iya barin kowa saboda ya mallake ki. Ai ba iya wannan aikin zamu tsaya ba akwai na karkashin k'asa."

Umma da take ta kallon su tana murmushin farin ciki Asiya ta mik'awa Umma Sakina kudin tace, "kinga abinda ya bani." Ta karb'a ta juya kud'in tace, "Dubu d'ari ce gata nan ko tab'a ta ba’ayi ba. To muna ganin irin wannan arzuk'i taya zamu bari ya kubce mana? Ai wallahi sai mun sark'afo shi ya kasa guduwa ko ina."

Umma tace, "ai wallahi ko k'afar sa bai isa ya d'aga daga gidan nan ba tunda har ya furta ya shiga uku, ko meye zamuyi dan ya auri Asiya bai isa ya gudu muna kallo ba."
"Barshi kawai k'awata. Yanzu kinga wannan kud'in zan d'auki dubu d’aya ta sama data k'asa dan nasan tabbas akwai wacce yatsun sa suka tab'a, to daman haka muke so da ita zamu kuma amfani wajan kamo shi hannu biyu. Dan so muke fa ko ta shiga gidan kar uwar gidan ta rufe ta, ta zama itace gaba uwar gidan na baya, dan yadda muka kasance na gaba a gidan mu haka muke so ta zama itama.”

Umma tace, "Gaskiya ne wannan." Umma Sakina ta kalle ta tace, "Ya rage abincin da kika bashi?." Asiya tace, "ya rage yana plate ma."
"To maza jeki ki d'auka ki zaga baya wajan shukar baban ku ki hak’a rami ki binne, ki binne sosai fa kar a tono ta nan kusa. Yadda kika binne ta daidai yake da kin binne zuciyar ki a cikin tasa.” Ta amsa da to ta mik'e ta fita cikin zumud’i.

Umma Sakina ta kalli Umma tace, "Ki kwantar da hankalin ki cikin shekarar nan in sha Allah sai mun rage y'an matan nan da suke gaban mu, Asiya sai ta shiga gidan aure ko ta tsiya kota dad'i." Umma tace, "Allah yasa. Burina kenan Sakina ko bacci nayi mafarkin hakan nake."
"Kar ki damu zai tabbata, komai ai yazo k'arshe." Kiran sallar magriba ya saka suka tashi daga hirar da suke yi.

*☆☆☆*


"Assalamu alaikum." Kallon sa tayi ta amsa a ciki ta d'auke kanta ya k'araso ya ajjiye ledar hannun sa yana kallon ta yace, "Fiddausi lafiya kike naga duk kin canja?, akwai abinda ya faru da bana nan ne?” Ya fad'a yana zama yana kallon ta cikin tsantsar kulawa.

Banza tayi masa bata amsa ba ya sake cewa, "Fiddausi magana nake miki fa, meya same ki?." A kufule tace, "Nifa babu abinda ya same ni kawai na gaji da zaman gidan nan ne." Kai ya girgiza kawai baice komai ba daman yayi tunanin hakan zata ce.

Ledar hannun da ya ajjiye ya mik'a mata yace, "Yau nayi ciniki a wajan aiki ga wata atamfa na gani na siyo miki na sanki kina son kala ja" ya fad'a da murmushi yana mik'a mata. Karb'a tayi ta buɗe ledar tana kallon atampar tare da tab’a cikin ta takalle shi tace, "Kuma nawa kud'in ta?."

"Dubu shida" ya fad'a yana kallon ta. Dogon tsaki taja ta cillar da atamfar kan kujera tace, "Ni ai ba irin wannan nake so ba na fad’a maka ta dubu goma nace ba wannan raka ni gidan mutuwar ba. Banda abinka dan Allah me zanyi da wannan atamfar mai kama da ta y'an qauye?, kana jin jikin ya kasan mix ce.”

Kallon ta yake yi ransa yaji ya b'aci matuk'a gabad'aya Fiddausi bata da hankali bata tab'a ganin duk wani abun da yake mata duk k'okarin da yake a kanta gabad'aya bata gani kullum cikin kushewa take tana hangen na k'awayen ta wanda suka fita, bata tab’a kode masa akan duk abinda yake mata sai kushewa.

Daurewa yayi baice komai ba ya mik'e ya fita daga fallon nata zuwa d'akin sa. Tsaki taja ta sake kallon atamfar ta sake yin tsaki ta jingina da kujera tana kada k'afar ta ita sam ba irin haka take so ba, so take ta dinga saka kaya manya masu tsada kamar kawayen ta da yayyen ta na gidan su.

Bai jira ta ba ya shiga kitchen ya zuba abincin sa yaci yasha ruwa ya fita masallaci sallar i'sha. Yana dawowa ya kulle gidan dan lokacin sanyi ne mutane duk sun shiga gida. Tsakar gida nasa duhu sosai a bayyane yace, "Zan saka a saka mana fitila koda ta solar ce wannan duhun yayi yawa" ya fad'a yana shiga d'aki.

Ya jima sosai sannan ya fito ya shiga falon nata bata nan ya shiga d'aki nan ya same ta zaune a gefen gadon ta ya zauna shima yace, "Ameer bai dawo ba kenan?."
"Uhum." Bata kalle shi ba tana zaune da littafin hausa a hannun ta tana karantawa cikin hasken fitilar ta mai haske wacce ta haske d'akin.

"Fiddausi kizo muje d'akina" ya fad'a a tausashe yana kallon ta. Kallon sa itama tayi tace, "nayi me a can?."
"Ko ban fad'a ba kin san me zakiyi ai."
"Ban sani ba sai ka fad'a."
"Fiddausi yau kwana nawa rabon da mu had'a shinfid'a dake? Hakan baya damun ki?."

Ta ajjjye littafin tace, "Akan me zai dame ni? Baka san ita kanta sha'awar sai da kwanciyar hankali da kayan lashe-lashe take zuwa ba?" Ta fad'a tana kallon sa. Kallon ta yake yi kafin yace, "kin rasa kwanciyar hankali ne ke?.” Tayi shiru bata amsa ba yace, “Ni hakan yana damuna, kuma ina buk'atar ki a yanzun nan Fiddausi."

Ta tab’e baki ta kawar da kai tace, "Gaskiya kayi haƙuri bazan iya yin wani abu a yanzu ba. Sai dai gobe wataƙila." Bai iya cewa komai ba kallon ta yake yi cikin mamakin ta duk da ba yau aka saba ba amma kullum lamarin ta sake gaba yake yi yace, "nayi hak'uri fa kika ce? Kenan abinda nake nema bazan samu ba?."

"Kusan hakan" ta amsa a tak'aice.
"Akan wanne dalili?."
"Ni bazan iya yin komai a duhu da zafi ba gaskiya, ka jira in sun kawo wuta to in basu kawo ba kuma sai ayi haƙuri."
"Lokacin baya daman sai an jira masu nepa sun kawo wuta?."
"Dah fa daban yanzu ma haka, ni kawai na gaji da wahalar da kaina ne a cikin zafi in kuwa akwai wuta ko babu komai ai za'a sha iskar fanka tunda bamu da arzuk'i a.c. kawai kayi haƙuri nasan zaka iya jurewa ai” ta fad’a tana cigaba da karanta littafin.

Numfashi ya sauke yana kallon ta sai yaga ta zame ta ajjiye littafin ta kwanta ta juya masa baya alamun abinda fa yake so bazai samu ba ita bacci zatayi. Mik'ewa yayi ya fita ya bar mata d'akin ta bishi da kallo tace, "Ai na rantse da Allah indai baka siya min atamfar da nake so da gas ba baza ka sake samuna ba, haka kawai na dinga wahalar da kaina kullum a abu guda d'aya? Lokacin wannan ya wuce ga talauci ga gajiya ai abun sai ya maka yawa” ta fad’a tana komawa ta kwanta.

Shi kuwa d'aki ya koma ya zauna a gefen kafitar sa yayi shiru yana tunani sabbin halayen da Fiddausi take zuwar masa dasu a ko yaushe. Wato in a da aka ce masa Fiddausi zata aikata abubuwan da take yi yanzu sam bazai amince ba sabida ilimin da tara na addini. A wajen taron bikin haddar alkur'ani mai girma ya had'u da Fiddausi an gayyaci makarantar su shi kuma shine ya wakilci islamiyyar da yake koyarwa har ta kaisu ga aure kowa murnar samun ta yake masa sabida ilimin ta da ake sha'awar sa.

Ga ibada sallar dare, azumin nafila duk basa wuce ta, ana yin kira zata tashi sallah amma gabad'aya bata amfani da ilimin nata tunda hangen wanda suka fita take yi tana ganin gazawar sa akan duk irin kyautatawar da yake mata. Yana sonta yana kuma da haƙuri shi kansa yasan da hakan shiyasa take yin abinda taga dama amma tara ta yake yi duk sanda ya fashe bazata ji dad'i ba.

Numfashi ya sake yi ya kwanta a gefen gadon yana ji a ransa dole ma gobe yaje wajan mahaifiyar sa ya dawo da Amir shi kad'ai ne yake d'auke masa kewa in tana wannan rashin mutuncin nata.

*☆☆☆*

Yusuf kuwa tunda ya bar gidan su Asiya tunanin ta yak'i barin zuciyar sa a haka yayi sallar magariba sannan ya shiga cikin gidan sa ya same ta a tsaye a falo ta dafa hannunta akan dining table.

K'are mata kallo yake ta baya ta saka riga da siket y'an kanti sun mata matuk'ar kyau musaman daga k'asan ta hips d'in ta ya buɗe haka boobs d'in ta daga baya sun tashi a cikin siket d'in shape dinta ya fita sosai. Lumshe ido yayi dan shi kasan yana alfahari da Meena dan Allah yayi mata baiwar kyaun sura duk inda ka kai ga kushiyar ka in ka ganta sai ka yaba.

Motsin sa taji daga baya ta ta juyo tana kallon sa shima ita yake kallo musamman k'irjin ta sai kuma ya kalli fuskar ta yaga ta rame sosai sai haske da ta sake yi daman taga fara sosai idanun ta sunyi ja alamun tayi kuka.

Wani abu mai kama da tausayin ta yaji ya tsirga masa yaga ta sauke idanun ta kasa yaji tace, "Shikenan ma k'arasa maganar gobe" ta fad'a tana sauke wayar daga kunnen ta tace, "Sannu da zuwa." Abinda ta jima bata ga yayi mata ba shi taga yayi murmushin da ya saka zuciyar ta bugawa ya tako zuwa kusa da ita yana kallon fuskar ta yace, "Me ya samu fuskar Princess?."

Yarr taji a jikinta jin sunan da ta jima bata ji a bakin sa ba ta kasa sarrafa nutsuwar ta dan nan da nan yake kamo lagon ta duk rashin mutuncin da yayi mata kuwa, ganin hakan ya saka shi rik'e k'ugun ta yace, "My choice kinyi kyau." Jikinta yaga yana rawa sosai hawaye suna k'okarin sakko mata sai ya sake ta yayi hanyar da zata kaishi sama yace, "Ina zuwa yau sai an fad’a min kukan nan na meye."

Daskarewa tayi lokacin da taji takun sa zuwa sama ta bishi da kallo taga har ya hau ta fara kuka da murmushi jikin ta yana rawa kawai ta zube ta kalli gabas tayi sujjada tana kuka ta d'ago tace, "Alhamdulillah. Allah na gode maka, Allah ka cigaba da daidaita min lamarina. Da kai kad'ai na dogara kayi min maganin damuwata ya rabbil alamin. Allah kasa wannan chanjin ya kasance har abada” Sai kuma ta mik'e tana kallon kanta a mudubin da akayi ado daahi a falon tana ji kamar a mafarki abin ya faru, dan rabon da ya rike hannun ta ma ta manta.

Tana nan tsaye ya sakko da jallabiya taji saukar lab’b’an sa a kumatun ta suka had'a ido yace, "Naje sallah." Ido ya kashe mata sai taga yayi murmushi ya fita sai ta zabura tayi sama a guje cikin farin ciki da zallar murna a zuciyar ta.

Sallah tayi itama farin ciki gabad'aya ya mamaye mata zuciyar ta, tana idawar Zaytun ta tashi ta dama mata custard ta fara bata amma gabad'aya tunanin ta yana ga Yusuf d'in ta da ya koma mata wanda ta sani a da mai sonta da nuna mata kulawa a ko yaushe a kuma ko wanne lokaci.

Tana cikin bata ya shigo d'akin ta manta rabon da ta ga k'afar sa a d'akin ta ya k'araso ya d'auki Zaitun daga cinyar ta yana mata wasa sai dariya take alamun na tasan mahaifinta tana kiran sunan Daddy. Kallon sa take yi ji take kamar ta had'd'iye shi sbaida son da take masa sai ta sunkuyar da kanta k'asa ya kalle ta yace, "Madam baza'a ce min komai bane?."

Sai yaga ta diririce yayi murmushi yace, "Nutsu mana." Ta kalle shi suka had'a ido yace, "Ba abinda za'a bani?." Tace, "Banyi abinci ba in nayi baka ci asara ake shiyasa ban dafa ba, amma in kana so sai naje na dafa maka yanzu."
"Nooo! Naci abinci nida Usman a office. Ba abinci ai nake so ba wani abu nake so ki bani na musamman."

Ta d'ago idanun ta wanda suka tara ruwa suka sake kyau ta sake kallon sa tace, "Kamar me kenan?." Ya wara idanu yace, "baki sani ba?, zo muje sama na nuna miki. Amma kafin nan me zaki yiwa y'ar nan taki tayi bacci?."
"Yanzu ta tashi bana tunanin zata koma yanzu" ta fad'a a sanyaye tana kallon sa.

Yace, "Aikam dole ta koma, zo muje" ya fad'a yana mik'a mata hannun sa ta rik'e ya d'aga ta suka fita Zaitun na kafad'ar sa. Saman sa suka hau lokacin Zaitun tayi luf a kafad'arsa alamun bacci zai kuma d'aukar ta a haka suka shiga d'akin.

A hankali yace, "Kar kiyi magana, bara na samu tayi bacci" ya fad'a yana zagawa a d'akin a hankali yana jijiga ta ita dai kallon sa take gani take kamar an canja shi daga fitar sa zuwa dawowar sa dan rabon da ta ganshi hakan ta jima da mantawa.
Lokaci kad'an tayi bacci d'an k'aramin gadon ta da yake d'akin ya ajjiye ta ya shafa fuskar ta yace, "Ayi bacci lafiya My love" ya fad'a yana mata kiss ya bar wajan ya dawo yana kallon Ameenatu.

A kusa da ita ya zauna yaga tana ta wasa da hannun ta ya rik'e hannun yace, "Sai wani d’ar-d’ar kike kin kasa sakin jikin ki kamar wata amarya ko nace kamar ni bak’on kine.” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba sai ya sassauta murya tace, “Nasan nayi miki ba daidai ba my choice amma kiyi haƙuri ki yafe min kinji?." Kallon sa tayi ya lumshe ido ya buɗe alamun abinda taji haka ne ba mafarki take yi ba abinda yace kenan tayi murmushin jin dad'i amma bata ce komai ba.

Ya sake cewa, “kin yi shiru Baki amsa ba, Baki yafe min din bane?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, "Babu komai ya wuce. Amma dan Allah ka daina nesa dani har na wasu watanni abinda kake tunani a kaina ba haka bane."

Ya rungume ta yace, "na sani kiyi haƙuri, nasan ai ke kina son dukkan abinda nake so. Sharrin shaid'an ne bazan sake ba." Jinta a jikin sai kwnaciyar hankalin ta ya sake k'aruwa yana shafa bayan ta a hankali yana murmushi domin kuwa ya kamo lagon ta daman kuma wajan yake so azo.

"Nayi kewar ki da yawa My choice, me zan zamu?."
"Komai da kake so zaka samu."
"Really?" Ya fad'a a kunnen ta ta d'aga masa kai ya cizi kunnen ta yace, "Okay, we shall see" ya fad'a yana shafa bayan ta a hankali cikin salon sake d'auke hankalin ta kamar yadda y sani.

Nan da nan ya rikita ta daman an jima ba'a had'u ba lokaci d'aya ya saka ta fara manta duk wata damuwar ta ta baya ta fara tunanin mijinta na baya ya dawo kamar yadda yake da, zallar soyayya ya nuna mata a wannan lokacin itama haka tayi k'okarin ta wajan nuna masa tata bajintar dukkan su babu wanda bai ji dad'in wannan lokacin ba dan sunyi kewar junan su sosai ba kad'an ba.

Bayan lafawar komai tare suka fito daga band'aki cikin so da qauna ta saka riga a cikin kayan ta da suka d'akin shima ya shirya suka kwanta tana jikin sa. Shiru ne ya ratsa tsakanin su yana wasa da gashin kanta taji yana cewa, "Ya zanyi da alk'awarin dana d'auka? Gashi bana son sake ‘batawa my choice rai, bana so na ganta cikin damuwa, ina sonta bana son duk abinda zai saka zuciyarta a rud'ani. Ya zanyi?."

Kallon sa tayi ganin kamar zancen zuci yake tace, "My choice meya faru?." Firgita yayi irin bai san taji d'in nan ba yace, "Wani abun kika ji?." Ta kalle shi tace, "Magana naji kana yi fa, wanne alk'awari ne?."
"Oh wai a fili nake magana?" Ya dafe kai yace, "Ban san meya same ni ba, manta kawai My choice babu komai."
"Akan me zan manta? Dan Allah ka fad'a min naji kamar a kaina ka kasa cikawa.”

Ya kalli idanunta yace, "in na fad'a miki zai saka zuciyar ki a damuwa ne babu lallai kuma ki amince da abinda zan zo miki dashi."
"Damuwar ka damuwata ce, zan iya yin komai sabida kai. Ka fad'a min ko meye dan Allah."

Ya sauke numfashi yace, "My choice yarinyar da na nemi auren tane kwanaki to yanzu na fasa sabida bana son saka ki a rud’ani da tashin hankali, abinda ya faru ma a baya bana so na tuna sabida ina tsanar kaina ne sabida abubuwan da nayi miki shiyasa na haƙura na tabbatar kece kawai farin cikina abinda kike so shi zanyi. To yarinyar ce aka min waya wai tasha guba sabida nace bazan aure ta ba, dana je naga halin da take ciki ta bani tausayi tana sanar dani indai bana aure ta ba sai ta kashe kanta..." ya k'arasa fad'a a raunane cikin kalar tausayi kamar da gaske.

Gabanta ya fad'i amma bata nuna ba ya cigaba da cewa, "mahaifiyarta kuka take min tana cemin na taimaka mata kar ta rasa y'arta amma ni nace bazan iya ba sabida ke bana son d'aga miki hankali a halin yanzu. Gashi a kwanaki nayi mata alk'awarin aure duk ta kori masu sonta yanzu ban san ya zanyi ba tana can in ta mutu nine sıla my choice, Allah ya sani kuma bana so na b’ata miki rai" ya fad'a yana goge idanun sa alamun kuka.

Ta kalle shi zuciyar ta a karye duk da dukan da k'irjin ta yake yi haka ta daure tace, "Shine kake kuka?."
"Ba kukan sonta nake yi ba My choice Allah ya sani ke kawai nake so, duk wacce zan so a bayan ki take. Kwanaki ma ban san me ya shiga kaina nake neman aure bayan ina da kamar ki a gidana ba. Ina kukan tausayin tane nasan kin san meye so a zuciya nima na sani ta dalilin sonki, guba fa tasha My Choice ya zanyi in ta mutu?, ta sila ta fa kenan ta mutu kuma har a wajan Allah Ina da laifi.”

Ameena tayi shiru gabad'aya ya kashe mata jiki ta rasa ma abinda zata ce ganin yanayin ta sai ya sake cewa, "Da nace zan aure ta kawai duk da yanzu bana sonta to nasan in nayi hakan ban kyauta miki ba ga Ammah kuma bazata bari ba. In na bar yarinyar can a halin da take ciki my Choice sai Allah ya saka mata."

Shiru ta sake yi ya kalle ta yace, "ki bani shawara my choice." Ta sauke numfashi tana kallon sa tace, "To ban san me zance bane ba ai my choice, kaga Ammah tace baza ka aure ta ba daman."
"Noo My choice na Ammah mai sauk'i ne indai zaki taimaka min na ceto ranta, bawai ina sonta bane kawai ina so na taimake ta, ni ke kawai nake so duk duniya nasan kin san da wannan. Inda zaki amince min na aure ta d'in kece kawai zaki samu Ammah da maganar ta amince, to nasan it's very difficult ba amincewa zaki ba nasan kina sona kina kuma kishina abu ne mai wahala a wajan ki.”

Shiru yaga ta kuma yi ta tashi zaune daga jikin sa shima ya tashi yana kallon ta ta k'aramin hasken d'akin ganin tana hawaye ya saka yace, "Sabida bana son ganin hawayen ki ya saka nace na haƙura bazan fada miki ba kika ce na fad'a. Kiyi haƙuri bazan sake miki maganar ba dan Allah ki daina kuka."

"Dan Allah my choice kana sona?." Ya rik'e hannayen ta yace, "Wallahil azim babu macen da nake so kamar ki My Choice, kece farko kece k'arshe. Ita kanta yarinyar da nake fad'a miki babu sonta a raina gabad'aya da dai akwai amma yanzu ya fita sabida ganin ki cikin damuwa ya kori gabad'aya soyayyar ta sai tausayi kawai. Ni auren ta nake so kawai nayi dan na fitar da ita daga halin da take ciki na kuma sauke alqawarin da yake kaina, nasan kin san mahimmacin alqawari bazaki so na sab'a ba. Amma kiyi haƙuri tunda naga ranki ya b'aci bazan sake maganar ba. Auren ma na hakura ai Allah ya gani zan dinga neman yafiyar sa tunda a baya na cutar da ita, in ta mutu ne kawai ban san ya zanyi ba.”

Ta goge idanunta tace, "Da gaske zaka aure tane badan na gare ka da komai ba?." Ya sake matsowa sosai kusa da ita yace, "Haba my choice dame kika rage ni? Ai ni komai ina samu daga wajan ki babu abinda na rasa. Nifa basan sha'awa ko wani abun zanyi aure ba sai dan abinda na fad'a miki, na aureta d'in shine nake so amma dan na ajjiye ta ban shiga inda take bama har k'arshen rayuwata abu ne mai sauk'i tunda ina dake nasan zan samu dukkan farin ciki a wajan ki. My choice kece wacce nake so sanin kina son abinda nake so y saka na fad’a miki, kin sani kece abokiyar shawarata bani da wata kamar ki.”

Ta gyaɗa kai cikin zallar wauta da karayar zuciya, kalaman sa sunyi tasiri sosai a jikin ta musamman kalmar da yake furtawa da yasan tana son abinda yake so tace, "Shikenan zan samu Ammah da maganar in sha Allah bazata mutu ta dalilin ka ba" ta kalle shi tace, "Zaka aureta tunda baka sonta kuma ban rage ka da komai ba, zan samu Ammah nayi mata maganar Allah yasa dai ta amince."


#F5
#Book1

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*


https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

*Book 1*
*Page 5*

Sassanyan dad'i yaji yana shiga ilahirin jikin sa, farin ciki yana mamaye ko wanne gurbi na zuciyar sa kamar ana soka masa allurar farin ciki haka yake ji dan tunda yaji ta amsa yasan shikenan kuma amma bai nuna mata ba ya rausayar da kai ya kalli idanun ta yace, "My choice kar fa na takura ki kiyi abinda ba shi kike so ba, na fad'a miki zan iya hak'ura."

Hawayen da suka sakko mata ta goge tace, "babu takura my Choice ayi hakan kawai, in ta mutu ta dalilin ka kamar ta dalilina ta rasa ranta, ga alk'awarin da ka d'auka gwara kawai ayi a wuce wajan." Tsam tsam ya rungume ta yana jera mata kisses a fuska da bayan ta son da take masa bai tab’a yi masa rana ba sai lokacin yace, "Na gode My Choice, na gode Allah ya biya ki da gidan Aljanna. Ke din mai qaunar cigaban rayuwata ce Allah a barmu tare dani dake har abada.”

Ya d'ago ta daga jikin sa yana kallon ta yaga tana murmushi tace, "yaushe zamu samu Ammah da maganar?." Fuskar sa baza ka fassara yanayin sa ba yace, "Sai muje da safe kafin na wuce office. Amma dan Allah my choice ban cutar dake ba?."

"Duk abinda kake so shi nake so koda zai cutar dani" ta fad'a a sanyaye tana kallon sa ya sauke numfashi yana binta da kallo yace, "Duk yadda akayi Allah ya k'addara ita d'in matata ce, kin san k'addara tun tana ciki Allah ya rubuta sunana a matsayin mijinta tun bamu zo duniya ba. In badan haka ba banga dalilin da zai saka na auro wata bayan ke ba, ke kawqi nake so dake kawai naso rayuwa amma k'addarar aure ta kan iya d'aukar rai."

Numfashin itama ta sauke bata ce komai ba yace, "Allah zai baki ladan taimakona da kika yi itama kuma kin taimake ta. Har abada bazan manta da wannan taimakon naki ba My choice, Allah yayi miki albarka ya baki duk abinda kike so." Ta amsa da amin a ciki ya bita da kallo yasan akwai abinda take ji a zuciyar ta amam shi dai tunda ta amsa shine burin sa duk

Please Login or Register in order to submit comment