Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta barki kina yawo da hijjabi a titi da lunguna. Duka k'awayen ki uku yara ne dasu amma ke kina nan sai dai kici kiyi bacci ko samarin nan irin na waya baki dasu. Wallahi ni na gaji da ganin ki a gabana jinina hawa zaiyi, kamar a kanki aka kawo bak'in jini duniya? Kanwar ki ta biyu gata nan aure zatayi amma ke kowa yazo kice bakya so kashe ni kike so kiyi Rukayya?".

Yadda Umma ta k'arasa maganar kamar zatayi kuka y saka Rukayya ta girgiza kai tace, "A'a Umma Kiyi hak'uri dan Allah, in lokacin yayi zanyi auren." Umma tace, "Na gaji da ganin ki haka aure nake so naga kinyi shine hankalina zai kwanta."
"To Umma zanyi."
"Yaushe?."
"Nima ban sani ba Umma."
"In kika fita samari basa tare ki?."
"Babu wanda yake min magana har naje na dawo."

Umma tace, "Taya kike so hankalina ya kwanta ama irin haka?." Rukayya ta fashe da kuka mara sauti Ummw tace, "Ba kuka zaki ba amsar duk wanda yazo yana sonki zakiyi ayi auren nan kema ki huta. Kin wuce lokacin da za'a ce sai kin zab'a ai Rukayya, lokacin zab'en miji a wajan ki ya wuce." Kai ta girgiza alamun to kafin Umma ta sake cewa, "Ki dai yiwa kanki fad'a ki daina tsayawa zab'e, ai tunda kika wuce shekara ashirin da biyar zab'e ai ba naki bane kawai da anzo ki amince bana son wani wasa da hankali. Ki bar yara suce zasu yi zab'e amma bake ba."

Nan ma kai ta d'aga kawai sabida kuka bazata iya magana ba Umman tace, "in ma dan shaye-shaye ne kuna tare albarkar aure sai kiga ya daina, balle ke mai ilimi da wuri zaki nusar dashi ya daina yin abinda yake yi. Amma da yake ke ga kareena kapoor gaki benu sarkin yarinta kice sai kinyi zab'e ana rok'o Allah ya kawo ya kawo kuma ke kina cewa bakya so." Murmushi takaici Rukayya tayi tana cigaba da hawaye Umma ta kalle ta tace, "Tashi kije ki d'ora girkin rana amfanin ki kenan daman ai." Jiki a sanyaye ta mik'e ta fita zuciyar ta kamar zata buga sabida bakin ciki da takaici, har tana ji a ranta zata amince da duk wanda aka sake kawo mata matsayin miji ko wanne irin hali ne dashi zata karb'a kodan Umma.




#Comments
#vote
#Share

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu.
https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36


*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake, amma kayan nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅


*Book 1*
*Page 19*



A guje ta shiga d'aki ta tsaya a jikin k'ofa ta fashe da kuka mai sauti da tsayawa a zuciya. Zuciyar ta zafi take mata da rad'ad'i kanta har sarawa yake sabida 'kuna da bak'in cikin da take ji a zuciyar ta. Tabbas da itace mai iko da kanta da yanzu ta jima da barın gidan su, da duk inda mijin ta yake taje ta Nemo shi kodan ta huta da gorin da Umma take yi mata.

"Umma ya zanyi da raina ne? Ina zan saka zuciyata naji dadi?. Kullum cikin hantara kike kamar ba kece kika haife ni ba, aure nufi ne na Allah, sai lokacina yayi sannan zanyi, Umma ya akayi kika mantaaaaaa!"ta fad'a cikin kuka mai sauti tana zamewa a k'asa ta zauna tare da kifa kanta a guiwoyin ta tana kuka sosai.

"Umma kina gani 'kannena duk sun raina ni sabida suna ganin kan mu daya dasu, ya ake so nayi ni zanje na nemo mijin nace yazo ya aure ni?" Muryar ta har rawa take yi sabida kukan da yake addabar zuciyar ta. Kuka tayi mai yawa zuciyar ta na sake fad'a mata Anya Umma ce ta haife ta? Abban tane kawai yake rarrashin ta amma Umma ko a jikin ta duk rashin nagartar namiji in yazo bata dubawa kawai so take tayi aure ta daina ganin ta a gaban ta.

Sai da tayi kuka son ranta sannan ta tashi daga inda take a daidai lokacin wayar ta ta fara 'kara ta d'auka ganin sunan mai kiran ta saka a kunne kafin tayi magana akace, "ke banza ya kike?." Murmushi tayi tace, "normal Kiyya, Ina Fahad?."
"Yana nan, bakya neman mutane ko ziyara."
"Kaina ne ya dauki chaji wallahi."
"Ai naga alama, naji maganar ki wani iri mura kike?."
"Eh."
"Gobe zamu je gidan Meena kin San mijin ta aure zai 'kara, matsayin mu na kawayen ta yana da kyau muje mu taya ta jaje."

Idanu Rukayya ta zaro waje tace, "Yusuf zai yiwa Amina kishiya?." Kiyya tayi dariya tace, "Abin mamaki ko? Wallahi nima da naji sai da gabana ya fad'i, yanzu da muka gama magana da Fidy ma itama abinda tace kenan." Ruky tace, "Kuma wai da gaske ne ba k'arya ba?."
"Wallahi da gaske ne, ki shirya muje goben." Rukky ta sauke numfashi tace, "Allah ya kaimu ma had'u a can." Kiyya ta amsa kafin ta yanke wayar Rukky tabi wayar da kallo zuciyar ta na mugun bugawa ta zauna a gefen gado a bayyane tace, "Yusuf zai yiwa Amina kishiya? Wai aure zai k'ara fa, wai Yusuf din Amina." Mamaki lamarin yake bata sosai domin kuwa ko a mafarki bata tab'a kawo hakan ba duba da son da suke yiwa junan su.


Ibrahim bai koma gıda ba sai lokacin da ya saba ya tarar da gidan ko Ina da haske da alama ta kira an mayar da wayar da tsinke ya tsaya a tsakar gidan yana kallon gidan zuciyar sa na harbawa sosai, dakyar ya iya k'arasawa cikin d'akin sa ya zauna a gefen katifar sa ya dafe kansa zuciyar sa na sake harbawa da sauri.

D'akin ya kalla yana nan yarda ya barshi da alama ko shigowa dakin ma bata yi ba balle ma ya samu arzukin gyarawa. numfashi ya sake yi a lokacin aka fara kiran magriba ya tashi ya fita zuwa tsakar gidan yayi alwala ya fita masallaci.

Tana Jin motsin sa kiran sallah ne ya saka ta katse wayar da suke da Alhaji ta fito itama tayi alwala ta koma daki tayi sallah tana zaune taji motsin dawowar sa taja tsaki tare da hararar k'ofar ta d'auke kai. Tashi tayi ta fito tsakar gidan a daidai lokacin shima ya fito bai kalle ta ba ya wuce itama ta shiga kitchen tana tsaye ta dafa indomie ta zuba a faranti ta fito ta shiga d'aki taci ta k'oshi ta fito ta ajjiye kwanon ta koma d'akin tayi sallah i'sha tar da shafa'i da wutir tayi kwanciyar ta tana Danna waya.

A bangaren Ibrahim koda ta bashi abinci daman baiyi niyar ci ba zuciyar sa har lokacin zafi take yi abubuwa Kala-kala zuciyar sa take saqa masa, babban abinda yafi komai tsaya masa a rai a ina Fiddausi take samun kudi?. Shaidan sai kawo masa abubuwa Mara kyau yake yi game da hakan. Tashi tsaye yayi yana sake kallon fankar da take wulwulawa a sama ya lumshe idanun sa ransa na suya.

"A Ina take samun kudi haka? Waye yake bata?." Ya fad'a a bayyane duk da yasan babu mai bashi amsa. _Ka sani ko ta fara neman maza ne._ abinda zuciyar sa ta fad'a masa kenan yayi sauri tsayawa cak tare da furta, "Innalillahi wa'inna ilahiri raji'un, a'uzubillahi minal shaidanir rajim." Duf duf duf zuciyar sa take bugawa hankalin sa yaji yayi mugun tashi shaidan yana sake saqa masa abinda bai tab'a zuwa zuciyar sa ba.

Da sauri ya fito daga d'akin yana kallon wayar da ta bawa d'akin sa haske da fanka ya shiga kitchen ya d'auki wuk'a ya datse wayar ya sake kallon wacce ya haska gidan ya sake yankewa, tsaki yayi a fusace ya saka wuk'a ya yanke duk waya da ta zaga ko Ina a gidan nan take gidan yayi duhu gabad'aya.

"Me yake faruwa naga gidan yayi duhu haka?" Ta fad'a Tana fitowa tana kallon tsakar gidan. Ko kallon ta baiyi ba ya wuce ta zuwa d'aki tabi wayar da kallo tana kallon sa nan take ranta ya b'aci sosai tace, "Wai Ina ruwan ka da abinda nayi da kudina ne? Tunda kai baza ka iya yi min ba dan nayi da kud'ina Meya shafe ka?." Yana Jin ta yayi mata banza baya son sauraren ta dan yadda yake Jin zuciyar sa tsaf zai mata dukan da zata kasa tashi.

"Kuma wallahi sai na gyara ai ba kud'in ka bane, kud'i na ne; in baka so ka yanke ta d'akin ka amma wallahi ni sai na gyara ai ba kai ka siya min ba. Aikin banza aikin wofi ace wai mijin ka shine zai maka bak'in ciki dan kayi arzuqi " ta fad'a tare da jan dogon tsaki ya shiga d'aki. Duk yana Jin ta bazai tanka bane ya kuma yi alwashin ko sau dubu zata gyara shi kuma sai ya yanke sau dubu sai dai wani ya gaji ya hakura.

Amina sai bayan sallar Isha suka koma gıda tun bayan da ya sauke ta ya sake fita ko bai fad'a ba tasan wajan amaryar sa ya tafi haka ta zauna ta dinga kuka har kanta ya far ciwo, bacci da Zaitun tayi ne ya saka ta tashi taje ta kwantar da ita a sama ta zauna a falon ta na sama tayi tagumi.

K'arar wayar ta ya saka ta duba inda take ta dauk'a ganin sunan Yayan Bauchi ya saka ta d'auka tace, "Tun dazu nake kiran ki amma baki d'auka ba." Shiru tayi alamun Ana bata amsa kafin tace, "Eh wallahi, an saka wata biyu. Abin haushin ma Yaya bai fada min ba sai tashi nayi naga Ana aiki a filin da aka shigo dashi gidan mu, d'azu da naje wajan Amma take fada min..." ta fad'a muryar ta na rawa hawaye na cigaba da zubo mata.

Shiru tayi alamun magana take yi mata kafin ta goge ido tace, "To Yaya in sha Allah, ki cigaba da yi min addu'a Allah ya bani sassauci akan abinda nake ji. Wallahi yanzu kishiyar bata gabana Yaya......!." Rarrashin ta ta cigaba da yi a wayar kafin su yi sallama a lokacin kiran Zakiyya ya shigo.

Amina ta dauka tare da fadin, "Kiyya bakya neman kowa ke kam." Dariya tayi kadan tace, "ke ai naga kina nemana, ya kike ya Zaitun?."
"Alhamdulillah, ya fahad?."
"Yana nan Lafiya, gobe kina gida ne?."
"Ina nan, Allah yasa zuwa zakiyi." Dariya Zakiyya ta sake yi tace, "Bama ni kad'ai ba har su Fidy, sai a yi mana abinci mai dadi dan wallahi baza muci na masu aiki ba."

Murmushi tayi zuciyar ta ta d'an yi sanyi kad'an tace, "Kar ki damu Allah ya kaimu goben kawai." Ta amsa da amin suka dan yi hira kad'an kafin su kashe wayar ta ajjiye. Motsi taji a bayan ta tasan shine hakan ya saka bata juya ba ya zauna a kujerar kusa da ita yayi shiru kamar bazai yi magana ba. Waya yake dannawa itama haka bata ce komai ba shima bai ce komai, kallon ta yayi yace, "Ki fad'a min abinda kike so na baki, kud'i kike so ko kuma kaya kike so?."

D'agowa tayi ta kalle shi suka had'a ido ta d'auke kai tayi shiru bata ce komai ba ya sake kallon ta yace, "Baki ji abinda nace bane?." Ta sake kallon sa shima ita yake kallo fuskar sa a d'aure sosai tace, "Naji, bana son magana ne kaina ciwo yake min sosai." Idanu ya wara yace, "Kina ji kika yi min banza, ga d'an iska ko?." Ta janye idanu daga kallon sa tace, "Kaina ciwo yake min na fad'a maka, in nayi magana kamar zai cire."

"Kanki yana ciwo bakin kine yake ciwo?. Wai Ameena waye yake zuga ki kike wannan banzayen halayen?." Numfashi ta sauke zuciyar ta nayi mata zafi sosai bata ce komai ba ya girgiza kai yace, "in ma zuga ki ake yi akan zanyi aure kika fara wannan d'abi'un wallahi an cuce ki, dan ke kanki kin San aure babu fashi. Kaya kuma ko kud'i in kinga zaki karb'a kanki in baza ki karb'a ba wannan duk ke ta shafa; bani zasu yiwa amfani ba kece, rashin karb'ar ki bazai hana ni abinda nayi niya ba" ya mik'e tsaye ya zaro wani cream a aljanun sa ya cilla mata yace, "Ki shafa a ciwon nan bana son k'ananun maganganu" yana fad'a ya bar wajan a fusace ta bishi da kallo.

Sai da ya b'ace ta daina kallon sa ta kalli maganin tayi murmushin takaici a bayyane tace, "Ina ma Ina da uwa, Ina ma Mama tana raye, Ina ma Mamana bata koma ga Allah ba, Ina ma Mama na kusa dani. Da jikin ta zanje na fad'i nayi kuka ko babu komai d'umin jikin ta zai kawo kin sassauci a zuciyata. Sai dai Kash....." sai tayi murmushi tace, "Mama bata nan, tayi min nisan da har abada bazata dawo ba, Allah ya gafarta miki." Bata san adadin lokacin da ta kwashe a wajan ba ta mik'e ko ta kan cream din bata bi ba ta shiga d'aki tayi alwala ta tayar da sallah tana yi tana hawayen da yak'i tsayawa a zuciyar ta da idanun ta.


Asiya kuwa lokacin da Yusuf ya bar wajan ta gıda ta koma ta shiga d'akin Umma ta same ta ita da Yaya Maimuna suna magana tace, "Umma Akwai matsala fa wallahi." Umma ta kalle ta tace, "Har kin saka gabana ya fadi, wacce matsala ce?." Asiya tace, "Wannan matar Yusuf din mana, wani magani na gani a hannun sa yanzu nace masa na meye wai ciwo matar sa taji a wuya ya siyo mata ta shafa. Har yanzu yana bata kulawar da dan taji ciwo a wuya sai ya bata magani Umma? A wuya fa ciwon yake kana ji kasan ba ciwon kirki bane."

Yaya Maimuna taja tsaki tace, "Banza har kin saka naji tsoro wallahi, zuciyata har bugawa take na d'auka wani abun ya fada." Umma tace, "Bari kawai Yayar su, ni kaina zuciyar tawa bugawa take."
"Akan wannan abun zaki wani damu kanki? Ki jira ayi auren mana ki gani, ke a tunanin ki zamu bari ki zama bora a gidan Yusuf ne? Ai wallahil azim ko kwan lantarki bazai kai ki haskawa a gidan ba. Ita kuma uwar gidan sai ta gudu da kafar ta."

Asiya tace, "Nifa bana so naga yana nuna yana sonta ko kad'an wallahi, yadda yake fad'a min yafi sona da ita bana son wani abun ya canja gaskiya Yaya." Umma tayi tsaki tare da dariya tace, "Ke baki ji sunan da ake fad'a min bane? Murucin kan dutse ce ni ban fito ba sai da na shirya yarinya. Ki saka a ranki wannan ba komai bane Allah dai ya ki damo ga hawara." Sai a sannan tayi murmushi Umma tace, "Ya kuka yi dashi? Nawa zai baki na hidimar biki?." Asiya tace, "Cewa yayi na lissafa masa da wuri, sannan wai lefe kudin nake so ko kayan nidai nafi son kayan Umma."

Umma tace, "Ya baki kud'in kawai kaya kina dasu in ya bayar sai ki sake k'arawa ." Asiya tace, "Umma ni nafi so a kawo lefen yadda mutane zasu ga kayana su san ba talaka zan aura ba." Yaya Maimuna tace, "Ke dallah can ki karb'i kudin a samu ayi miki gyaran jiki na fitina a kuma had'a miki d'aki sauran sai Kiyi dinkin ko Umma?."

Umma tace, "Tsaya, yanzu bayan anyi lefen zai baki wani kudin na hidimar biki?." Asiya ta d'aga kai Umma tace, "Kyale shi yayi lefen, sannan kudi kice masa kinyi lissafi abinda za'a kashe miliyan uku." Asiya ta wara ido waje tace, "Umma miliyan uku fa kika ce?, kuma banda kayan lefe?."
"Eh haka nace, hakan kuma zaki ce masa nasan kuma zai bayar."
Asiya tace, "Anya Umma baiyi yawa ba? Kar yaga haukana fa."

Yaya Maimuna tace, "Lokacin aure na mijina da bai kai Yusuf kud'i ba miliyan d'aya muka kwak'ulo balle kuma Yusuf, ai wallahi na dauka biyar ma za'a nema Umma." Umma tace, "Kyale shashasha, in baki karb'a yanzu da yake rawar k'afa a kanki ba yaushe zaki karb'a ?. Ke baki san a wajan saurayi yanzu ake kab'ar kudin kayan d'aki bane?, duk wani Abu da zamu siya kamar bashi ne sai ya biya mu." Yaya Maimuna tace, "Yanzu ne lokacin ki, duk abinda kike so zai baki bazai ji komai a ransa ba. In wannan lokacin ya wuce bayarwa baya zatayi."

Asiya ta kalle su tace, "To zan ce masa miliyan ukun in ya bayar to in ya rage kuma shikenan" ta fad'a tana shigewa d'aki ita gabadaya haushin Ameena ne a zuciyar ta ba wani abun ba, tana jiyo muryar Umma na magana bata koma ba ta shiga d'aki ta kwanta tana tsara plan din farko in ta shiga gidan sa wanda zata gabatar.




#Comments
#Share
#Vote
#F5
#Book1

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu.
https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan Kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake, amma kayan nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅


*Book 1*
*Page 20*



Washe gari Ibrahim bai bi ta kan Fiddausi ba fita yayi tun safe kai tsaye gidan su ya nufa duk da suna da nisa amma a k’asa yaje sabida zuciyar sa gabadaya babu dad’i a haka ya kwana ya tashi komai ya tsaya masa baya Jin dad’in komai. Har baya so ayi masa magana sabida abinda yake ji a zuciyar sa baya son bud’e bakin sa. Da sallama ya shiga gidan su ya tarar da Hajiya a zaune a kan kujera a tsakar gida Jin maganar sa ya saka ta dago kai ta amsa tace, “A’a ibrahim kaine yau da safe?.” Murmushi yayi ya k’araso ya zauna a kan tabarmar da take kusa da Hajiyan yace, “Barka da safiya Hajiya.”

“Barka dai, ka tashi lafiya? ya wajan su Fiddausin?.”
“Lafiya lau.”
“Baka tafi wajan aikin ba?.”
“Bana Jin dad’i sai zuwa anjima.” Hajiya ta kalle shi tace, “naga ka fad’a kuwa fuskar ka ta nuna alamun rashin Jin dadi. Amma ka sanar da mai gidan naku baza ka samu damar zuwa ba?.”

Ibrahim yace, “zan fad’a masa.” Hajiya tace, “Ya kamata dai ka fad’a masa.” Ya kalli tsakar gidan ganin baiga giftawar kannen sa ba yace, “Ina Fadima da Sadik naji gidan shiru?.” Hajiya tace, “Fadima na aike ta gidan ka ta mayar da Amir ya koma gaban Babar sa tayi kara da yawa ai kar ya zama an cutar da ita, shi kuma Sadik ya tafi siyo min gawayi.”

Ibrahim yace, “Meyasa aka mayar da Amir din yanzu?.” Hajiya tace, “Haba kai kuwa kwanan sa nawa a nan din? Ai gwara a kai mata shi itama ko babu komai in baka nan zata dinga jin mostin sa a kusa da ita.” K’arar bude kofar band’aki ya saka ya kalli wajan yaga Mariya ta fito yace, “Ke kuwa zuwa da safe?.”

Ta ajjiye butar hannun ta tace, “Kaima kazo balle ni?.” Murmushi yayi kawai Hajiya tana ta bin sa da kallo ganin yayi shiru sai tace, “Ko zaka sha kunu? Dazu na dama.” Ya daga kai Hajiya ta kalli Mariya tace, “Taimaka ki kawo masa yana madafa a kwanon sha, sai dai yayi sanyi.” Mariya ta tashi ta d’auko ta kawo masa had’e d a kofi ya bud’e yana zuba yana sha.

“Salama alaikum” Fadima ta fad’a tana shigowa ita da Amir. A guje Amir yayo wajan Ibrahim yana fad’in, “Abba oyoyo” ya fad’a jikin sa shima ya rik’e shi yana murmushi yace, “Dan gidan Hajiya.” Mariya tace, “Ya kuka dawo da Amir din?.” Fadima ta zauna tace, “Mun je gidan muna ta bugawa ba’a bud’e ba sai Maman Zainab din nan makociyar ta tace ai ta fita yanzun nan aka d’auka ta a mota.”

Daidai lokacin Ibrahim ya kai kofin kunun bakin sa bai san lokacin da kofin ya kusa sub’ucewa ba kunun ya dan zuba a gaban rigar sa ya kalli Fadima kafin yayi magana Mariya tace, “Daman bata gıda da ka fito? Ta fad’a Tana kallon sa.

Dakyar ya daidaita nutsuwar sa yace, “jiya tace min zata je unguwa daman yau, na manta shaf sai yanzu.” Zuba masa ido Hajiya tayi Tana kallon sa kafin ta d’auke kai tace, “Anjima da daddare a kawo shi to.” Da sauri yace, “A’a Hajiya a kyale shi kawai, yana jin dad’in zama a nan d’in ya koma nan gaba.” Hajiya bata tanka ba dan ta hango matsala a zamantakewar auren d’an nata ko a yanayin sa ya gwada haka.

Fadima ya kalla yace, “Bani ruwa da tsumma a goge kunun nan da ya zube min.” Ta tashi ta kawo ya goge Amir na kusa dashi ya tashi tsaye ya saka hannu aljihu ya dauko dubu biyu ya ajjiye gaban Hajiya yace, “Hajiya a k’ara a siyi wani abun, na wuce wajan aiki.” Hajiya tace, “Kace baka jin dadi kuma.”
“Zan lallab’a naje kawai.”
“To Allah ya kiyaye, Allah yayi maka albarka ya k’ara arzuki” ya amsa da amin ya fita jiki a sanyaye.

Yana fita Mariya tace, “kin tabbatar da abinda nake fada miki ko Hajiya? Yarinyar nan ta jima tana fita bata fad’a masa ba, sau da dama zamu yi magana dashi nace zanje yace tana gıda babu inda zata je in naje naga bata nan, yau gashi a gaban ki kin tabbatar.” Hajiya ta kalli Amir da yake gefe sai ta fasa magana ta tashi ta shiga d’aki sai kuwa Amir ya mik’e yabi bayan ta.

Fadima tace, “Wallahi Aunty Mariya Yaya yana cikin damuwa sosai, matar nan tasa ta canja wallahi ni gabadaya yanzu haushi take bani.” Mariya ta tab’e Baki tace, “Yar iska ce wallahi, shi kuma baya son laifin ta. Amma zamu yi maganin ta nan kusa.” Kawar da maganar sukayi suka fara tattauna wani abun daban.

Da Zazzabi Ameena ta tashi ko gyaran saman kasawa tayi tana yiwa Zaytun wanka ta shirya ta ta kwanta ba tare da tasha magani ba. Tana kin tashin motar sa daga inda take kwance alamun ya fita ta rufe ido kawai abubuwa suna gilmawa a idanun ta.

_”Nifa bance baza ka yi min kishiya ba My choice in na fad’i hakan nasan k’arya nake yi, kawai bana so in hakan ya taso kar ka wulakanta ni ne. Yusuf da yake kallon ta yayi murmushi yace, “nida nake da kamar ki wacce mace zan sake aurowa? Wallahi Ameenatou kin fiye min mata dubu a duniyar nan, duk ranar da akace na wulakanta ki to ki d’auka bani da hankali, ke ko bani da hankalin mai aikin ki bazan iya wulakantawa ba. K’uda bana so naga ya hau jikin ki balle ki zubar da hawaye.”_

Tunawa da kalaman Yusuf na baya ya saka Ameenatu yin murmushi ta share

Please Login or Register in order to submit comment