Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata tab’a sanarwa da kowa ba.

Aure su babu jimawa ya fara canjawa ashe a lokacin ya fara neman aure ita bata sani ba Ammah ce ta sani sai yake ganin kamar da saka hannun ta, Yaya Adam duk sanda yazo kano sai yaje gidan Ameena zai ganta tas babu damuwa hankalin sai ya kwanta Dan bata tab’a fada masa komai ba. Ameena bata da abokin shawara dan k’awayen nata ma basu San Matsalar ta ta gidan Yusuf ba kallon biri suke mata tana musu kallon ayaba, yan uwan ta da suke uba d’aya bata tab’a gangancin fadawa kowa ba sabida kowa a cikin su buri yake yaga wanda ba d’an dakin su ba cikin masifa a nan zaiyi farin ciki.

Kowa da kowa yana kallon ta matsayin Mara damuwa a gidan mijin ta sabida kudi, da gida da kuma mota amma ita sam basu take so ba kulawar mijin ta take so amma ta nema ta rasa, wannan dalilin take sha’awar auren Fiddausi sabida son da mijin ta yake mata yake kuma kula da ita take jin Ina ma itace, yayın da Fidy take kallon Ameena tana cewa Ina ma itace.

Ameena na hakuri da halin Yusuf abu kad’an tayi fad’a ko ya kai mata duka ta fuskanci halayyar sace tun farkon auren su, a hakan kuma yana kiran yana sonta itama kuma har lokacin tana jin son sa a ranta sai dai in ya mata wani abun tayi kuka ta gode Allah.

Maganar auren sa bata damun ta sosai akan canja mata d’in da yayi, farkon auren su ba haka yake ba sai daga baya ya fara canjawa halayyar sa ta asali tana bayyana da maganar auren sa ta ratso kuma sai komai ya sake lalacewa har ta kai ta kawo ya d’auki k’afa ya bar kasar sabida Ammah tace bazai yi aure ba ya manta da Ameena da kuma y’ar sa na tsahon wasu kwanki.

Ameena baiwar Allah mace mai hak’uri da kawaici har lokacin babu Wanda yasan Yusuf yana dukan ta ba balle yasan yana Shan giya, ga kulle sirrin a zuciyar ta tana kuma yi masa addu’a a ko yaushe akan Allah ya shirya shi yasa ya daina abinda yake yi. In yayi kamar ya shiryu ya daina sai kuma ya sake karkarcewa bata gajiya ba tana sake kula dashi tana kuma fad’awa Allah.



Yusuf yaga Asiya yana sonta amma ba da niyar aure ba ganin ta na farko a store din sa ya sakko ya shiga cikin store ya ganta tazo siyayya, bai mata magana a lokacin ba sai da ya sake ganin ta a nan sukayi exchanging number suka fara gaisawa kafin ya fara zuwa gidan su. Ya fara zuwa gidan da niyar nan da wasu kwanaki kawai a neme shi a rasa, bai je da niyar yin wani abu da ita ba kawai yaje wajan ta da niyar budurwa a waye mata a gida amma shi sam bada aure ya fara neman ta ba. Tunda suka bincika aka tabbatar yana da kud’i sosai suka hana shi koda d'aga k'afar sa, aka rikita masa lissafi akan Asiya har ta kai ga ya yi yaji ya bar gidan sa akan ance bazai aure ta ba. Lokaci d’aya yaji yana son auren ta Kai tsaye mahaifin sa ya samu ya fad’a masa shi kuma ya fadawa Amma a nan tace sam bai isa ba bazai kuma isa ba.

Wannan dalilin ya saka ya sake canjawa Ameena a ganin sa ita take zuga Ammah abin da yake mata sai ya ninka na baya, yayi amfani da rashin wayo na Ameena da kuma soyayyar da take masa dan cikar burin sa na auren Asiya abar son sa.

Asiya yarinya ce mai kyau daidai ita mai duhun fata y’a wajan Hajiya Atika wacce Unguwa suke mata laqabi da itace mijin, gidan nasu mata maza biyun ne dasu kuma k’anana matan sune manya. Maimuna, Fauziyya, Asiya, Momi, sai Sudes da Aminu. Mahaifiyar su itace miji a gidan su baban su bashi da k’arfi akan komai domin bata wani d’auke shi da mahimmaci ba.

Gabadayan su tarbiyayar Umma ce basa girmama kowa sai sun ga dama, dangin mahaifin su basa ganin girman su dan Sunce basa son su basa son mahaifiyar su suma baza su so su ba. Tunda Allah ya yiwa mahaifin su karayar arzuki ya zama hajiya Atika itace take d’aukar d’awainiyar yaran ta shikenan ta raina mijin ta, dan suyi fad’a a gaban yaran ta ba komai bane suma tun suna jin babu dad’i har ya zama sun saba.

Burin Umma ta aurar dasu matan guda hudu da suke gaban ta har Maimuna da ta kasance bazawara, hakan ya saka tunda Yusuf ya kawo kai gidan suka kamo shi bai isa ya gudu ba duk abinda suka San zasu yi dan kar ya gudu sunyi da taimakon k’awar Umma mai suna Umma Sakina.
Wannan Hali na mahaifiyar ta ya saka Ammah bata son auren Asiya da Yusuf ko kusa, hakan ya saka take ce masa in zai auro kowa ya aura amma banda Asiya shi kuma duk duniya ita yake so ya aura.


Anya burin sa zai cika….?



Cigaban labari…..!


#Comments
#Vote
#Share
#F5

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 7*

Ammah suna gama waya ta fita zuwa b'angaren mijinta ta same shi a zaune yana breakfast ta zauna batayi magana ba har ya kammala cin abincin sannan tace, "Matar Yusuf ce tazo min tana neman alfarmar wai na barshi yayi auren tunda yana so, wato dana hana shi sai yaje yasan yadda ya lallab'ota ita da yake bata da wayo sai ta amince tazo ta same ni” ta fad’a tana kallon sa.

Yayi murmushi yana kallon ta yace, "To ai daman tun farko kece kika matsa akan maganar nan banga dalilin da zaki hana shi aure ba tunda Allah ya hore masa babu abinda ya nema ya rasa akan me zaki hana shi tunda yana so?.” Ammah ta kalle shi tace, "Haba Abbah, kwata-kwata kwanan sa nawa da auren da yake tunanin wani? In akayi haka ba'a yiwa matar sa adalci ba sam, inda Humaira ce a wannan yanayin ai banza so hakan ba, kafi kowa sanin Ina d’aukar yarinyar nan kamar ni na haife ta.”

"To akwai wanda zai ja da ikon Allah ne? In Allah ya rubuta ita wacce yake burin auren matar sace ke da kika matsa sai ya d'auki ranki bayan bakya duniya kuma ayi. Tsananin rabo yana kisa musamman rabo irin na aure nasan kin San da hakan sake tuna miki nake yi, Tabbas bai kyauta mata ba amma ya za'ayi da abinda Allah ya k'addara akwai wanda zai canja ne?.”

Ammah tayi shiru bata ce komai ba tana kallon wani wajan daban yace, "Kuma tunda ya fara maganar nan kika hana shi yake ganin kamar itace ta hana sanin kanki ne baza taji dad'in auren ba gabad'aya domin shi namiji in yana son abu musamman ma k’arin aure idanun sa rufewa yake yi indai baiyi auren nan ba hankalin kowa bazai kwanta ba ciki kuma harda ke. Ki barshi yayi auren hankalin matar ya kwanta namu hankalin ma ya kwanta dan Allah."

Ammah tace, "A jikina nake jin auren nasa ba alkhairi bane." Ya katse ta da fad'in, "Allah yana canja k'addara komai girman ta sai dai in baka addu'a."
"Yarinyar nan da yake so bata da tarbiyya ko kad'an, y'ay'an mata ne basa girmama mahaifin su, kowa ya shaida basu d’auki mahaifin su a bakin komai ba taya zamu bari ta shigo ahlin mu?.”

Abbah ace, "Ke ya akayi kika sani?." Ammah tace, "Na saka anyi min bincike a kanta tun farko, mahaifiyar su itace kamar mijin a gidan mahaifin su shine matar. Dan Allah taya zamu d'auko irin wannan yarinyar mu kawota ahlin mu sai ta gurb’ata mana suna?.”

Abbah yace, "Duk abinda Allah ya tsara babu wanda zai canja shi, tunda kika ga ana zuwa a dawo akan maganar nan kawai ki kawar da kai daga kai baki san me Allah ya b'oye ba, duk abinda kika ga yana tafiya yana dawowa dakyar in bai faru ba gwara ki saka hak’uri a zuciyar ki. Zan saka ayi binciken da kaina domin tabbatarwa zan kuma saka aje a nema masa auren ta hankalin kowa ya kwanta” ya fad’a yana kallon ta itama tana kallon sa.

Ammah tace, “baka ganin yayi wuri?.”
“Baiyi wuri ba, dan Allah ki bar maganar nan haka. Indai da gaske kina son matar sa kamar y’arki to kiso kwanciyar hankalin ta, kina nan tana can baki san me yake mata akan hakan ba tunda ba fad’a miki zata yi ba.”
Ammah ta sauke numfashi kawai tayi shiru badan taso ba sai dan babu yarda zatayi ne amma zuciyar ta gabad'aya tak'i karb'ar auren Yusuf koda wasa.


*☆☆*

"Abban Amir ina so zanje asibiti a duba ni yau na tashi bana jin dad'i gabad'aya" ta fad'a tana zaune ba tare da ta kalle shi ba.
Kallon ta yayi ya cigaba da cin abincin sa yace, "A dawo lafiya, Allah ya kara lafiya.”

Kallon sa tayi tace, "kud’in mota dana magani." Bai ce komai ba ya gama cin abincin ya tashi ya d'auki dari biyar a aljihun sa ya ajjiye yace, "Gashi nan Kiyi na mota na maganin in kin dawo wanda aka rubuto sai na siyo." Ta kalle shi ta kalli kud'in tace, "Wannan kud'in ai bazai kaini asibiti ba balle kuma ya siya min magani. Kuma ni bafa murtala zan tafi ba ko wani k'aramin asibiti ba, asibitin kud'i zanje can sunfi kula da mutane na daina zuwa k’aramin asibiti. Kawai ka bani dubu biyar na gwada na gani."

K'are mata kallo yake tana magana kafin yace, "baki ji me nace ba? Nace in aka rubuto maganin zan siyo ko?.”
“Ni so nake na siyo gabad’aya gaskiya, kuma ko iya zuwa asibitin ai naira dari biyar tayi kad’an.”
“Itace dani in bakya so na d'auki kayata." Hannu ta saka ta d'auka tana b'ata baki tace, "Amma dai Allah ya sani na gaji da wannan rayuwar, wallahi na gaji." Bai tanka ba ya fita ya barta tana mita yayi k'okarin rufe kunnen sa dan kar ma ya jiyo ta dan bazai tanka ba.

Yana fita ta tashi tana fad'in, "Haka kawai a dinga mayar dani baya cikin y'an uwa da abokan arzuk'i, wallahi bazan je asibitin gwamnati ba na kud'i zanje kuma dole ka biya ni kud'in da zan kashe dan a wajan ka zan fashe komai" ta fad'a tana shiga d'aki dan ta shirya ta tafi.

Tsaf ta shirya cikiin riga da siket na lace da yayi mata kyau yadda kayan suka karb’e ta in ka kalle ta baza kace matar Ibrahim mai d’aukar bulo bace domin tayi kyau matuk'a kamar ba ita ba.
Gidan ta kulle ta fita zuwa bakin titi ta hau adadaita sahu kai tsaye asibitin kud'in da ake bata labarin kyaun sa ta nufa. A can baya aka sauke ta dan kar aga ta sauka daga adaidata sahu a raina ta tana takun isa kamar matar gwamna ta shiga asibitin.

A zaune ta tarar da mutane ta zauna itama tana basarwa kamar matar wani alhajin sai kuma ta tashi ta nufi wajan wata kanta da taga wata mata a tsaye tace, "Sannu fa."
Matar tace, "Welcome Madam."
"Nazo ganin Dr."
"Sabuwar zuwa nan ce?."
"Eh, yau na fara zuwa ina driving ne naji kaina yana ciwo shine na shigo naga Dr."
"Okay Madam zaki buɗe file" ta fad'a tana juyawa ta d'auko file sabo ta mik'a mata had’e da abin rubutu.

Da iyayi Fiddausi ta cike file ta bata ita kuma ta fara shigar da sunan ta a computer kafin ta gama ta kalle ta ta nuna mata d'akin da zata je wajan likitan. Shiga tayi jim kad'an ta fito aka nuna mata lab taje tayi gwajin da yace ta koma ta kai masa.

Yanayin yadda ta fito zai tabbatar maka da abinda aka fad'a mata ba abu bane mai dad’in ji ba gabad'aya ta diririce yanayin ta ya canja daga farin ciki zuwa akasin sa , tana fitowa wani ma'aikaci ya tare ta yace, "Madam ga bill na abubuwan da kika kashe, zamu je kiyi payment."

Kai ta d'aga kawai ba tare da ta karb'a ba yayi gaba tabi bayan sa suka tsaya a inda zata biya kud'in tace, "Nawa ne total d'in?." Wanda yake gaban computer d'in yana dubawa yace, "Kud'in file, kud'in ganin dr, kud'in test, dana magani gabad'aya dubu talatin da uku da naira d'ari uku."

"Mee!?" Ta fad'a da k'arfin gaske tana kallon sa shima ita yake kallo idanun ta a waje k'irjin ta yana mugun bugawa cikin zallar tashin hankali da tsoro mai yawa, shikenan tasan a cell zata kwana dan bata da wannan kud’in bata da kuma dalilin su.

Ya kalle ta yace, "Eh haka kud'in suke." Nan take ta fara had'a gumi dan ita harga Allah ta d'auka baifi dubu biyar ba shiyasa tayi burga take yin komai a gadarance bata d'auka kud'in sunje haka ba da bazata fara zuwa ba dan kudin sunfi k’arfin ta sosai.

"Cash ne ko atm?." Abinda ya fad'a shine ya katse ta ta dawo da kallon ta gare shi sai tayi k'okarin dawowa hankalin ta tace, "Atm ne."
"Okay" ya fad'a yana d'auko p.o.s yana jira ta mik'a masa.
Hannun ta ta duba kamar gaske sai tace, "Subahanallah badai na yar da Atm d'in ba?" Ta fad'a tana waigawa kamar da gaske akwai abinda take nema d'in.

"Cire mata a nawa." Aka fad'a daga gefe hkan ya saka tayi saurin juyowa taga wanda yayi maganar suka had'a ido dashi yayi murmushi yace, "Kar ki damu ki kira customer care suyi blocking bank d'in kar a kwashe miki kud'i kin san masu irin wannan d’abi’ar sunyi yawa.”

Sak tayi kawai tana kallon sa ganin babban mutum ne mai shekaru kai da ka ganshi kasan kud'i ya zauna dan fatar sa ma d'aukar idon da take yi sai khamshi yake mai sanyi ga wayar hannun sa da makullin mota kai daga gani kasan ba k’aramin mutum bane. Da yake y'ar gari kuma wayayyiya ce sai tayi murmushi tace, "Na gode. Let me call" ta fad'a tana d'an komawa gefe ta d'auko k'aramar android d'in wayar ta kamar da gaske d'in wayar take.

Ganin ya nufo wajan ta da leda ya saka ta sauke wayar tayi murmushi ta karb'i ledar da yake mik'o mata tace, "Na gode sosai."
"Meye abin godiya dan na taimakawa kyakykyawar surar nan?." Murmushi tayi taji dad'i har zuciyar ta tayi far da idanu tana kallon sa tana ji kanta ya k’ara girma babban mutum kamar sa ya kira ta da kyakykyawa.

"In babu damuwa ko zamu iya tafiya?." Ta kalle shi tace, "No kar ka damu yanzu driver na zaizo ya d'auke ni." Shima yayi murmushin yace, "Nima drivern kine ai mai kyau, dan Allah muje na sauke ki bazan so kita zaman jira haka ba."

Kafad'a ta d'aga tace, "Okay." Yayi gaba ta bishi a baya sai kuma gaban ta yake fad'uwa sosai dan karo na farko kenan da ta kula wani tun bayan da tayi aure, tsoro ya mamaye mata zuciya zuciyar ta shiga harbawa da sauri, . Motar da taga ya buɗe sai da ta kusa suma sabida bata tab'a ganin ta a kusa ba sai dai a nesa ta basar ya buɗe mata gaba yace, "Bismillah."

Murmushi tayi ta shiga ya kulle ya zaga ya shiga shima ya kunna motar suka fita daga harabar asibitin. Kallon ta yayi yace, "Ina zan kai gimbiyar?."
"Kabuga zanje.”
"An gama gimbiya" ya fad'a yana d'aukar hanyar Kabuga kamar yadda tace.

"Gashi ban san sunan gimbiyar tawa ba?." Tayi murmushi tace, "Fiddausi." Ya wara idanu yace, "Wow! Suna mai dad'i.”
"Thanks" ta fad'a cike da iyayi tana kallon kan titi.
“Yadda masu irin sunan ki basu da yawa a duniya haka masu suffar ki ma basu da yawa.” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba yace,

"Da kamar bazan fito ba ashe rabon na had'u da sarauniya Fidy shiyasa nazo hospital d'in nan, gaskiya I'm very lucky today." Murmushi tayi kawai bata ce komai ba suna tafiya yana janta da hira kad'an-kad'an har suka shiga unguwar.

Ita ta dinga nuna masa kasancewar ba wahala gidan suka tsaya bakin wani k'aton gida mai kyau ta kalle shi tace, "To nazo gida, na gode sosai." Ya bita da kallo yace, "Bana so naji kina kin gode d'in nan kin wuce haka. Baki tambayi nawa sunan ba."
"Ayi haƙuri, a sanar dani."
"Sunana Alhaji Bello Sagagi." Wara idanu tayi tana kallon sa dan indai kana jin radio kasan wannan sunan sabida yadda yayi fice a fannin kasuwanci.

Tace, "Haba shiyasa nake ta tunanin nasan fuskar nan ashe a TV nake ganin ta, gaskiya nice nayi sa'a ba kai ba." Yayi murmushi yace, "yadda kika amince dani har kika biyo ni nine zan gode bake ba. In babu damuwa ki bani number wayar ki akwai maganar da nake so mu tattauna in kin huta."

Shiru tayi kamar baza tayi magana ba tana tunanin yin abinda yace wata zuciyar tana cewa ta bayar wata tana hanata ganin hakan ya saka yace, "Dan Allah kar kice A'a." Murmushi tayi ta kalli wayar da yake mik'o mata alamun ta saka masa ta karb'a zuciyar ta na bugawa sosai ta fara dannawa. Allah ya taimake ta ma tana danna wayar su Ameena da Zakiyya da taya zata iya amfani da wayar sa.

"Ki taimaki bawan Allah dan Allah kar a bani wrong number." Jin abinda yace sai ya dakatar da ita daga bashi wrong d'in ta saka masa number ta ya karb'a ya kira yaji tana vibrating a jikin ta yayi murmushi yace, "Na gode Gimbiya Fidy."

Murmushi tayi ya d'auko kud'i masu waya ya mik'a mata yace, "Ga wannan asha ice cream." Batayi musu ba ta karb'a tace, "Na gode sosai."
"U deserve anythings." Murmushi tayi shima haka sukayi sallaam ta fita sai da yaga ta shiga gidan sannan yaja mota ya tafi.

A guje Fiddausi ta shiga gidan k'awar ta Zakiyya tana shiga kai tsaye inda fridge yake ta nufa ta buɗe ta d'auki ruwa tana sha kafin ta dawo daidai ta kalli inda Zakiyyar take da itama kallon ta take yi ta k’araso wajan.

"Lafiya kike kuwa Fid? Wannan shigowa a firgice kamar wacce aka biyo?" Zakiyya ta fad'a tana kallon ta, k'arasowa tayi ta zauna tana sauke numfashi sai a sannan Zakiyya ta kula da kud'in hannunta tace, "Shegiya wannan dukiyar fa?" Ta fad'a tana karb'ar kud'in tana kalla.

Fiddausi tace, "Bari kawai Kiyya, tsautsayi ne yau ya fito dani na aikata abinda ban tab'a ba."
"Me kika aikata haka? Wani ne ya kai ki hotel?." Hararar ta tayi tace, "Haba Kiyya, wanne irin hotel kuma ana zaune lafiya?."
"To gashi nan na ganki kinci uwar gayu sai khamshi kike ga uban kud'i a hannun ki ba dole na d'auka wani ne ya baki ba, kinga fad’a min gaskiya.”

Fiddausi ta sauke numfashi tace, "kin san waye ya kawo ni gidan nan?." Ta girgiza kai alamun a'a Fiddausi tace, "Bello Sagagi."
"Wanne Bello Sagagi?."
"Wanda dai kika sani mai company Sagagi investment da sauran su.”

Zakiyya ta kyalkyale da dariya mai k'ara mai cike da kin ma raina min hankali ta kalle ta tace, "Haba Fid rage mana." Fiddausi tace, "Wallahil azim ba k'arya nake ba, da gaske nake shine ya kawo ni har k'ofar gidan nan, ke kin San ban tab’a yi miki irin wannan k’aryar ba ko?.”

Zakiyya ta gyara zama tace, "Kuma da gaske kike wai?." Fiddausi tace, "Wallahi da gaske nake." Duka ta kai mata a kafad'a tace, "Shegiya Fiddausi akwai farin ciki kawai Allah yayi rabon Ibrahim ce ke. A ina kuka had'u?."

Labari ta bata har k'arshe kafin tace, "Wallahi Kiyya dana san abinda zai faru kenan da banje ba, gabad'aya nayi nadamar abinda faru domin Allah kad'ai yasan yau zunubin dana kwasa. Nidai zanyi blocking number sa na goge na huta kawai” ta fad’a tana kokarın yin hakan.

Kwace wayar Zakiyya tayi tace, "Baki da hankali ashe Fiddausi, yanzu ke sai ki goge number sa ko kiyi blocking?, ke kin San manyan mutanen da suke neman lambar sa ke kin samu zaki wulakanta?.”
"To Kiyya so kike na dinga waya dashi? Naji ma da zunubin dana kwasa a iya yau ma mana, in na cigaba da waya dashi me kenan?.”
"Baza ki daina kula shi ba ai ba wani abun zaki yi dashi ba da Allah zai rubuta miki zunubi, kawai ki zage Hajiya kici arzuk'i ki barshi."

Fiddausi ta girgiza kai tace, "Nidai bazan iya ba Zakiyya, ina jin tsoron Allah nasan akwai aure a kaina fa.” Zakiyya tace, "To sai me dan da aure a kanki?, naga ba wata mummunan abu kika aikata ba ko?. Kuma dan kina sauraron sa arzuk'i ne, ke kin san adadin dukiyar da yake da ita kuwa?."

Fiddausi tace, "nidai bazan iya ba." Zakiyya tace, "Zaki iya ai ba wani abun bane mai wahala kawai waya ce fa ya kike ya kika tashi kenan.”
"Ni ba wannan ba, Zakiyya wai ashe rashin lafiyar da nake ji ina yi sama sama wai ashe ciki ne dani har na sati hud’u?."

Zakiyya ta wara idanu kamar wacce tayi cikin Shege tace, "Ci me? Ciki fa kika ce?, cikin ma kuma na Ibrahim. Ke ya akayi kika bari akayi hakan?."
"Tsautsayi Zakiyya, dan zan iya cewa ma tun ranar da akayi cikin bana tunanin na sake sauraron sa. Ashe a ranar ya cuce ni ban sani ba."
"Sai ki d'auki mataki tun kafin ya sani dan ina ke ina haihuwa yanzu ana cikin wannan matsalar rayuwar? Shi kansa Amir d'in ba wata sutturar arzuk'i ne da ita ba ina ga kin haifo wani?. Wallahi ki san abinda zakiyi kafin lokaci ya k’ure miki.”

Fiddausi ta sauke numfashi tace, "To ya kike ganin za'ayi?." Zakiyya ta kalle ta tace, "Kawai ki zubar tunda k’arami ne!.”

#Comments
#Vote
#Share
#F5
#Book1
#Nana Halema

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 8*


Kallon ta Fiddausi take da mamakin abinda tace kafin ta girgiza kai cikin sanyin jiki tace, "Na zubar fa kika ce Kiyya?." Ta wara hannayen ta tace, "To meye amfanin sa?, na gida ma ya aka cika dashi da za'a fara k'ok'arin samun wani?. Ni wallahi na raina wayon ki ma ban d'auka zaki sake bari kiyi ciki a wannan gidan da kike ciki mai kama da kejin kaji. Kinga Kefa nake yiwa gata ba kaina ba.”

Fiddausi tace, "Koma dai meye bana tunanin zan fitar da cikin nan."
"Akan me? In fa kin zubar bai sani ba."
"Yayi zaman chemist a da yasan maganin masu ciki yana gani zai gane, ni bazan iya ba."
"Ai sai ki ta zama dashi har Alhaji Bello ya gano matar aure ce ke ya rabu dake y’an kudaden da nake miki hangen zaki samu ki rasa."

"Nifa daman bance zan saurare shi ba, ina fa da aure Zakiyya."
"To wannan auren naki ai dashi gwara babu, aure babu jin dad'in rayuwa kullum kina zaune cikin duhu kina fama da gawayi wani lokacin nama ma gararar ki yake yi meye amfanin sa?. Ki duba gidan nan ki kuma duba gidan Ameena, ko Ruky da bata yi aure ba gwara ita a kanki sabida ita tun da iyayen ta kin san ya suke. Dukkan mu k'awaye nehar mukayi candy ko wacce tana cikin daula kece kawai kike zaune da matsiyaci duk da nasan rabon Amir ne ya saka aka kai yanzu.”

Fiddausi tace, "Kin manta Rukayya gwara ni da auren ita kuma ai babu." Zakiyya tayi dariya tace, "To banda abin ki Fid ba gwara ma Rukky tasan bata da auren ba a kanki? Bata da aure kuma babu abinda ta rasa. Kefa gabad'aya kece kika k’askanta a cikin mu ni kuma bana son ganin hakan Allah ya sani. Dakyaun ki, da saurar ki ace kina zaune a gidan da dubu goma zata gagare ki."

"Bari kawai, kudin ma fa da naje nayi burga dasu Meena ce taje gidan ta bani tace na Amir ne in badan

Please Login or Register in order to submit comment