Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda zata ji wannan daga baya ne.

Yace, "Me kike so ki fad'a min ko meye." Sai ta fashe da kuka tace, "Kar ka sake nisa dani, ka cigaba da zama a my choice din dana sani tun a baya. Kar ka koma min Yusuf dan Allah,sam bana jin dad'in hakan ina cutawa sosai. Kar kuma ka aure ta ka wulaƙanta....." Bata k'arasa ba ya toshe mata baki da hannun sa yana girgiza kai yace, "Har abada hakan bazata faru ba My choice, kece farko kece k'arshe babu wata bayan ki. Ina sonki" ya fad'a yana kallon idanin ta itama haka.

Kwanciya sukayi zuciyar sa tamkar audiga sabida haske farin ciki yake ji sosai yana kuma gode Allah da ya bashi mata mai k'aramin wayo kamar Ameena wacce soyayyar sa tayi mata yawa zata ita komai sabida shi, Burin sa kawai gari ya waye dan yasan da anje an samu Amma zancen ya k'are sai dai tayi fad'an ta gama amma zata amince tunda Ameena din ce zata fad’a da kanta.

Bata iya komawa bacci ba shima haka ta b'angaren ta zallar damuwa ce da dana sanin amincewa shi kuma farin ciki yayi masa yawa har taso ta fahimci hakan duk da yana b'oyewa amma taso ganewa dan labarin zuciya a tambayi fuska, yanayin fuskar ta saki sosai sai sun had’a ido sai ta d’an yi murmushi.

Yana fita sallar asuba itama ta d'auki Zaitun ta bar d'akin nasa gabad'aya bata jin dad'in zuciyar ta haka ta koma nata d'akin ta kwanta bayan ta idar da sallah ba tare da tasan abinda yake damun ta, jin zuciyar ta take kamar an d’ora mata dutse sabida nauyin da tayi mata ga zafi da take ji a duk jikin ta. Da ya dawo yaga bata nan d'akin nata ya nufo ya same ta a kwance.

"My choice" ya fad'a yana shigowa ta d'ago ta kalle shi ya k'araso yace, "ya naga kin sakko?." Tace, "Babu komai."
"Akwai my choice, kalli fuskar ki fa duk ta canja alamun Kinyi kuka. Ko maganar jiya ce dai?."

Ta girgiza kai tace, "A'a, kawai bana jin dad'i ne shiyasa." Ya sake kallon ta yace, "To me ya same ki haka?."
"Nima ban sani ba."
"My Choice na fad'a miki in akwai damuwa a bar maganar nan farin cikin ki yafi min komai a duniyar nan."

Ta girgiza kai tace, "ba wannan ne a raina ba kawai ina tunanin Mamana da Abbana ne."
"To ai addu'a zaki musu ba tunani ba ko?." Ta d'aga kai alamun eh yace, "Jiya an fara karatu a islamiyyar da aka Gina domin su, yanzu zancen da nake miki sun fara samun ladan karatun alkur'anin da ake a ciki domin makarantar gabad'aya sadaukarwar su ce."

Sai taji sanyi a zuciyar ta tayi murmushi tace, "Allah yasa hakan, Allah yasa suna aljanna." Yayi murmushi yace, "Amin ya rabbil alamin. Yanzu dai taso mu koma sama ina son a sake bani irin farin cikin jiya." Ta langwabar da kai tace, "Allah kaina ciwo yake min bana son tashi.”

Ya mik'e tsaye ya zaga gefen ta ya d'auke Zaitun ya kwantar ya dawo ya kwanta a kusa da ita yace, "to mu kwanta a nan" ya fad'a yana jawota jikin sa. Murmushi kawai tayi bata ce komai ba gabad'aya sai take ji a jikinta kamar canjawar nan tasa akwai dalilin yinta zuciyar ta sai take fad’a mata duk abinda ya fad’a ba gaskiya bane kawai yayi dan cikkon burin sa, tunda yayi mata waccan maganar ta kasa sukuni a haka bacci ya d'auke su ita dashi.

Ya rigata tashi ya bar d'akin bai jima da fita ba itama ta tashi ta yiwa Zaitun wanka itama tayi ta bata abincin ta ta gyara d'akin kamar kullum ta hau saman da niyar gyara nasa d'akin. Abin mamaki ya gyara d'akin tass tamkar itace ta gyara tabi d'akin da kallo tana kallon sa tace, "Morning my Choice." Bai amsa ba ya matso ya mata kiss a goshi yace, "Morning my beautiful wifey" ya fad'a yana karb'ar Zaitun.

"Da kanka kayi aikin nan?." Ya kalle ta yace, "naji kince baki da lafiya shiyasa nayi dan kar ki wahala." Tayi murmushi tace, "amma ni nasan bana son yin shara, ya akayi kayi haka yayi kyau?.” Ya kalle ta yace, “ai dakin yana samun kula a wajan ki wata ran sai kiga kamar ba’a kwanta ba.” Tayi murmushi tace, “kayi k'ok'ari." Shima murmushin yayi tace, "Bara na d'ora breakfast" ta fad'a tana fita taja tsaki shifa duk ba wannan yake so ba kawai ya gansu a gidan Amma shine burin sa shiyasa yayi mata aikin dan kar ma a jima basu tafi ba.

In badan kar ta fahimci wani abun ba ai bazai barta ma tayi wani abinci ba to baya so tayi sauri d'agowa shiyasa ya share ya k'yale ta. Nan da nan kuwa ta had'a musu breakfast ya sakko suka ci tare ya kalle ta yace, "zan tafi office ni." Ta kalle shi tace, "da wuri haka?."

"Eh, ai zan biya na gaida Ammah” ya fad'a dan ya tuno mata maganar jiya ya lura tana sharewa kamar ta manta kuma yasan tana sane.
"Bara na d'auko mayafi muje." Yayi murmushin jin dad'i yace, "okay." Ta hau sama ta sakko da mayafi ya d'auki Zaitun suka fita bayan sun kulle falon suka hau mota kai tsaye suka wuce gidan Amma gaban ta yana fad'uwa.

Lokacin da suka faka a babbar harabar gidan su Yusuf ya kalle ta yaga tana kallon wani wajan daban ya kamo hannun ta yace, "My choice!." Ta kalle shi yace, "Ni naga fa duk kin canja." Tayi murmushi tace, "Babu komai, muje" ta fad'a tana fita daga motar ta shiga ciki shima ya biyo bayan ta.

Amma ce kad'ai a zaune sai k'anwar su Humaira suka yi sallama suka shigo ta amsa da murmushi tana fad’in, "Ga daughter, ga Takwara ta" ta fad'a tana karb’ar Zaitun a hannun Ameena.
A kan carpet suka zauna gabad'ayan su Yusuf yace, "Barka da safiya Amma." A ciki ta amsa Ameena tace, "Barka da Safiya Amma."
"Barka dai Ameena, ya gidan?."
"Alhamdulillah" ta amsa da murmushi kamar yadda Ammah take murmushi.

Tashi yayi ya shiga cikin wajan Abbah Ammah ta kalle ta tace, "Lafiya dai ko na ganku da safiya?." Tayi y'ar dariya tace, "Lafiya lau Ammah. Humaira ina school?." Tayi dariya tana karb'ar Zaitun daga hannun Mama tace, "Munyi hutu, yanzu ma zancen zuwa gidan ki nake yiwa Ammah dan na gaji da zaman nan."

Amina tace, "Ai kuwa da naji dad'i." A lokacin Yusuf ya fito ya kalle ta yace, "My choice har na dawo kina nan ko zaki wuce?." Ta kalle shi tace, "Har ka dawo d'in." Ya girgiza kai ya kalli Ammah yace, "Ammah sai anjima" ya fad'a yana fita ta bishi da kallo ta kalli Ameena tace, "Ni dai ban amince da yanayin ki ba, inda matsala ki fad’a min."

Ameena tace, "Wajan ki nazo daman Ammah." Ammah tace, "Taahi muje d'aki." Ta tashi suka shiga d'aki aka bar Zaitun a hannun Humira Ammah ta zauna a kan gado ita kuma ta zauna a kan carpet Ammah tace, "me yake damun ki?."

Ameena tace, "Ammah alfarma nazo nema a wajan ki nasan kuma zaki min." Ammah da mamaki tace, "Wacce irin alfarma kuma?."
"Ammah dan Allah ki amincewa Daddyn Zaitun ya k'ara aure kamar yadda yake so. Wallahi Ammah in baiyi auren ba hankalina da naki bazai tab'a kwanciya ba tunda yana so gwada kawai yayi a wuce wajan, hankalin sa zai fi kwanciya nima nawa zai fi kwanciya.”

Ammah tayi shiru tana jin abinda take cewa cike da mamaki tana girgiza kai da jinjina tsananin wayo irin na Yusuf tace, "Ameena taso ki dawo kusa dani ki zauna." Ba musu ta tashi ta zauna kusa da ita Ammah ta rik'e hannunta tace, "Ke da kanki kike cewa na amincewa mijin ki ya k'aro miki kishiya? Kin san wacece kishiya kuwa?." Ameena tayi shiru Ammah tace, "Fad'a min shine ya saka ki kizo ki same ni?. Ni tunda naji ana kiran my choice a gabana nasan akwai wata tsiyar daya shirya, fad’a min shine ya turo ki?.”

Ta girgiza kai alamun a'a tace, "Ammah baiyi min ma wannan maganar ba na lura in baiyi auren ba komai sake lalacewa zaiyi. Yana son yi Ammah kuma Allah ya wore masa gwara kawai yayi tunda shi ya saka a gaba koda yanzu ya hak'ura nan gaba sai yayi gwara kawai ayi na huta shima ya huta kema ki huta Ammah. Dan Allah ki amince, amincewar ki kawai yake jira shiyasa nazo na nema masa alfarma da kaina a wajan ki. Ki amince yayi auren sai hankalina yafi kwanciya nima kinga in yayi na huta da tunanin auren” ta fad'a tana zamewa daga kan gadon tana kallon Ammah tana hawaye.

Ammah ta sauke numfashi ta d'ago Ameena itama ta mik'e tsaye tana kallon ta tace, "Amina y’arki ko yaye ta baki yi ba amma ki dinga zancen na amince mijin ki ya k'aro aure? Har yanzu kika gama sanin sa da zaki so ya kawo miki wata?. Kin san meye kishiya kuwa? Kin san yarinyar da yake niyar kawo miki?.”

Amina tace, "Ammah yana so wallahi in baiyi ba bazai tab'a komawa yadda na sanshi a baya ba. Dan Allah ki amince badan shi ba danni zaki amince Ammah."
Ammah ta sauke ajiyar zuciya tace, "Soyayyar sa har tayi miki yawan da zaki Zab’i farin cikin sa akan naki? Namiji ne fa nan gaba kar kizo kina dana sani akan abinda kika aikata Ameena. Ni ke nake ji in badan ke ba ya auro d'ari bai dame ni ba. Yusuf d’ana ne amma sabida ni na haife shi bazan fasa fad’ar gaskiya a akansa ba, wallahi in ma shi ya saka ki dad’in baki yayi miki cutar ki kuma zaiyi yana yin auren ya gama dake, ke kin san namiji kuwa…..?.”

Ameena tace, "Babu komai Ammah, in sha Allah babu abinda zai faru ni nace na amince taki amincewar kawai nake so." Ammah tayi shiru kafin ta kuma kallon ta tace, "Baki san meye kishiya bane shiyasa kike fad'ar haka."
"Naji na gani Ammah."
"Ameena da k’uruciya a lamarin ki.”
“A’a Ammah, kawai ayi a wuce wajan yafi sauki.”
“Shikenan zanyi shawara." Ameena tace, "To Ammah na gode Allah ya k'ara girma. Dan Allah Ammah ki amince kar ki yanke akasin haka."

Kai ta girgiza tana kallon ta Ameena ta fita daga d'akin jikinta a sanyaye Ammah ta bita da kallo tana jinjina yawo irin na namiji in yana son abu yasan yadda zaiyi ya samu koda ran wani zai b’aci.

Waya Ammah ta d'auka ta kira babar yarta mace da take Abuja ta d'auka suka gaisa Ammah tace, "Kin san dalilin da ya saka na kira ki?." Daga can b'angaren tace, "A'a Ammah."
"Ya kike gani akan maganar auren Yusuf, na amince masa ko kuwa?."
"Ammah amince masan shine yafi, namiji ne fa tunda ya saka auren a ransa in baiyi ba Ameena bazata tab'a jin dad'i ba, in kuwa yayi shikenan an wuce wajan hankalin kowa zai kwanta. A ganina barin sa d'in shine yafi Ammah sabida gani yake yi Ameena ita take hana ki amincewa.”

Ammah ta girgiza kai cikin gamsuwa tace, "Amma an cutar da Amina."
"To ya za'ayi? Barin sa baiyi auren ma cutarwa ne dan bazata tab’a jin dad’in sa ba kuma ita ba fad’a miki take yi ba, gata marainiya babu wanda zata kaiwa kukan ta kinga zata dinga cutuwa ne, in kuwa akayi shikenan an wuce wajan."
Ammah tace, "Shikenan" ta fad'a tana kashe wayar tana ji a ranta barin nasa shine ya dace amma sai tayi shawara.


#Vote
#Share
#comments

*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar

©️ *Nana Haleema.*


https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36


*Book 1*
*Page 6*

Ameena y'ar kano ce mazauna unguwar Yakasai, tun tana k’arama mahaifiyar ta t rasu ta barta a hannun Yayar ta Samira da kuma kishiyoyin ta guda biyu. Mahaifin su Malam Tijjani yana da mata guda uku, mahaifiyar su wacce ake kira da Mama sai Umma da Aunty, tun zaman su basu da had'in kai kowa d'an sa ya sani hakan ya saka yaran suka taso gabadaya kowa d'an d'akin su ya sani ba wani zumunci suke yi da wanda suke uba d'aya ba. Duka y’ay’an sa mata ne guda daya ne kawai namiji wanda yazo daga bangaren Uwar gidan sa shi kuma bashi da halayya irin tasu dukkan su yana son su musamman ma Ameena da ta kasance bata da uwa tana yarinya.

Cikin hikima ta Allah duk matan sai da suka riga shi barın duniya aka barshi da yara a lokacin Ameena ce ta kasance k'arama manyan duk an musu aure, lokacin da aka yiwa Yaya Samira aure za'a kai ta Bauchi ta dage akan da Ameena zata tafi mahaifinta yace sa ta barta a hannu sa zai kula da ita. Tasha kuka sosai haka itama Ameena sabida ita yake yiwa kallon uwa bata tamkar Mama haka take kallon ta.

Basu da wasu dangin mahaifiya domin mahaifiyar tasu ita kadai iyayen ta suka Haifa kuma iyayen sun rasu wanda suka sani kad’an ne kuma ba wani zumunci suke dasu ba sabida sun kasance talakawa. Bangaren dangin mahaifin ma suna qauye gabad’aya ko ziyara suka je basa wani karb’ar su hannu biyu tun mahaifin nasu yana raye hakan ya saka basu saba dasu ba gabad’aya.

Da taimakon Abba da kuma taimakon babban d'an sa wanda ya kasance shi kadai ne namiji a gidan wanda suke kira Yaya Adam aka cigaba da kula da Ameena, duk da Kasancewar su ba masu kud’i ba amma suna kokari wajan kula da ita musamman shi Yaya yana son Ameena baya nuna y’an ubanci a tsakanin su dan in yana waje Baka isa ka tab'a Ameena ba sai ya d'auki mataki. A haka Ameena ta taso cikin gata na Yaya da kuma na Abba ta fara zuwa makaranta kafin a mayar da ita boarding school.

Fiddausi, Zakiyya da kuma Rukayya duka y'an Unguwa d'aya ne da basa wata magana sosai amma tunda zaman makaranta ya had'a su suka zama tamkar y’an uwan juna, shakuwar su ya saka suke kiran kansu da four stars Wato Ameena, Fiddausi, Rukayya da kuma Zakiyya, inda suka canjawa kansu suna Ameena suke kiran ta da Meena, Fiddausi suce Fidy ko suce Fid, Rukayya suce Rukky, Zakiyya suce mata Kiyya. Dukkan su suna da k’ok’ari babu kamar Fiddausi wacce duk ta fisu saurin ganewa daga ita sai Ameena sai sauran su biyo baya, ganin yadda suke k'ok'ari sosai gasu da tarbiyya hakan ya saka iyayen su dukkan su suke jin dad’i har ya zama iyayen kowa yasan na ko wacce a cikin su ana gaisawa ana kuma zumunci. Har ta kai ta kawo in iyayen daya zasu je visiting musamman iyayen Rukayya da suka fi dukkan iyayen su karfi duk abinda suka siyarwa Rukayya sai sun siyawa sauran ukun.

Tun a boarding halin Ameena dana Rukayya yafi zuwa daidai, babu tsadaddiyar rayuwa a lamarin su komai suka samu zasu yi kuma ko zancen aure ake yi su biyun fatan miji na gari kawai suke yi babu ruwan su da miji mai kudi. Fiddausi da Zakiyya sune masu sha'awar luxury life ko a cikin malamai masu cewa suna son su basa kula talaka sai masu kud’i wanda zai kawo musu kayan dad’i ba kwaki ba. Sun shak’u sosai basa b’oyewa juna komai tare zasu had’a a zauna a tattauna a kawo mafita.

A haka suka kammala secondary school suka dawo gida a shekarar suka shiga makarantar hadda alkur'ani da kuma sanin littafan addini dan na boarding school ba wani sosai ake yi ba, cikin shekara d'aya da rabi suka gama ko wacce cikin su taci suka yi bikin sauka cikin farin ciki.

Dukkan su farare ne tas kyawawa babu kamar Ameena da ta fisu manyan ido sai aka fi ganin kyaunta a kansu amma ko wacce ba baya ba hakan ya saka a unguwar ake ce musu fararen taurari hud'u. Fiddausi ta fisu farin jinin samari amma kuma duk ba masu kudi ba hakan ya saka take bak'in ciki dan bata ga amfanin auren talaka ba, Ameena da Rukayya su tayi mata fad’a akan hakan yayin da Zakiyya take zuga ta.

Mahaifin Fiddausi dadtijo ne yasan mutunci ba kuma ya d’aukar shirme hakan ya saka Fiddausi bata tab'a bari saurayi yaje gidan su ba sabida Abba ma kar yaji labari ya aura mata shi. Kwatsam Allah ya kawo Ibrahim wanda ya ganta a lokacin da suka gama hadda ya yaba da ilimin ta kowa ya tambaya a kanta sai kaji ana kawai ka neme ta yarinyar ta gama had'a komai, kai tsaye Abba ya samu mahaifin ta yaji dad’i sosai ya saka aka bincika masa Ibrahim aka tabbatar da mutumin kirki ne kuma yana da Sana'a daidai gwargado nan ya bashi damar ganin Fiddausi.

Ibrahim akwai kalamai na hikima akan harshen sa dasu yayi amfani ya siye Fiddausi lokaci d'aya taji a ranta zata iya zama dashi ta amince masa aka saka ranar biki.K’awayen ta aka dinga murna dan itace zata fara aure a cikin su a lokacin su sun cigaba da karatu, suna ta shirin biki ana tsare-tsare a taara wannan a tsara wancan sai gashi abun yazo musu ba wani shagali Kasancewar yanayin mijin nata.

Akayi bikin Fiddausi aka gama wanda ya kasance ita kad’ai ce a gidan su take auren miji mai k'aramin k’arfi sai take fuskantar canji daga mahaifiyarta a fahimtar ta dan sai ta basu yayyen ta mata wanda suke auren masu kudi abu ita ba'a bata ba, sai ayi abu su a fad’a musu ita ba'a fad’a mata ba in tayi magana ace tausaya mata ake sabida kud'in mota duk da babu wani nisa tsakanin su. Wannan abun yana tsayawa Fiddausi a zuciyar ta dan gani take anfi son y’an uwan ta da suke auren masu kud’i a kanta.

Ana haka Zakiyya ma tayi aure ta samu mai kud’i kuma dan mai kudi dan ko siyan bakin ta kudi dubu hamsin aka basu sai hankalin Fiddausi ya sake tashi ta fara jin auren Ibrahim yana fita a ranta itama tana hangen Ina ma itama mai kud’i ta aura, Ina ma bata yi gaggawar auren Ibrahim ba ta jira mai kud’i yazo.

A bikin Zakiyya Ameena ta had’u da Yusuf ya kai kansa gaban Abban ta shima da maganar auren Abban ta ya amince masa aka bincika masa komai akan Yusuf nan da nan aka fara shirye-shirye. Ameena na son Yusuf sosai son da ya ninka wanda yake mata sau babu adadi, shima yana son ta ba baya so ba amma wanda take masa ya disashe nasa, sau da dama in suna waya da Yaya takan ce mata ki rage wannan soyayyar nan gaba kar ta cutar dake amma Ina bazata iya ba domin shine wanda ta fara so a rayuwar ta. Shima yana sonta sosai amma soyayyar da take masa ta danne wacce yake yi mata.

Tun farkon zuwan Yusuf bai yiwa Yaya Adam ba gabad’aya kawai ya amince ne sabida ita tana so kuma yaga Abba ma yana so amma shi sam bai masa ba.
Gab da bikin su Abban ta ya fara rashin lafiya ga gidan nasu babu kowa ko wacce tayi aure sai Yaya Adam aka kai Abba asibiti lokacin da Yusuf yazo duba shi ya rik’e hannun da yana bashi amanar Ameena shi kuma yayi alqawarin bazai tab'a saka ta kuka ba wannan kalamai na Abba shine na karshe ya bar duniya.

Ameena taga tashin hankali sosai tayi kuka kamar ranta zai fita kafin komai ya wuce ta cigaba da yi masa addu'a. Wannan rasuwa da mahaifin ta yayi ya k’ara soyayyar Ameena a zuciyar Ammah da y'an gidan su, tunda suka ji labarin ta kowa yayi Na’am da ita barın Ammah da take jin ta tamkar ita ta haife ta badan komai ba sai dai haka Allah ya saka mata son ta a zuciyar ta. Bayan sadakar arba'in aka fara shirin biki a lokacin Yaya Adam ya zama cikakken soja aikin sa ya fara kai shi gari gari na Nigeria a lokacin zai tafi Lagos ya kira Yusuf ya dinga jajjaba masa amanar Ameena dan daman shi ba wani son sa yake yi ba.

Aka gama bikin Ameena aka kai amarya gidan ta sai ya danne na Zakiyya domin Yusuf ya fi mijin Zakiyya kud'i, babu wanda ya tayar da hankalin sai Fidy abinda take dannewa a ranta yana tasowa tana ji a ranta ita ba kalar Ibrahim bace kota wanne hali sai ta san abinda zata yi. Tun daga wannan lokacin ko meye Ibrahim zai mata bata gani sai dai kawai tayi shiru bata nunawa kawai hangen kawayen ta take yi.

A haka Fiddausi ta haifi Amir ba jimawa sosai Zakiyya ta haifi Fahad ita kuma Ameena tayi b'ari a kasar England. Wayo k'asa-k'asa da Ameena take yi zuciyar Fiddausi kamar me ba bak'in ciki take mata ba kawai itama hange take yi na Allah ya kaita wajan da suke itama dan in ta shiga cikin su ki take ta fita daban duk da babu wacce ta canja amincin su yana nan babu abinda ya ragu a ciki amma Fiddausi bata ganin haka.
Rukayya ce a cikin su shiru babu saurayi balle mai neman miji, bata tab’a yin saurayi ba tun hankalin ta baya tashi har ya zama ta fara damuwa akan lamarin duk da suna kwantar mata da hankali dan dukkan su abokan kuka ne basa barın d'ayar su a cikin damuwa.

Aka yi bikin k'anwar Rukayya hakan ya saka magana ta sake yin yawa a kanta musamman lokacin da kanwar ta haihu Ameena ma ta haifi Zaytun. Gabad’aya sai zaman gidan su ya fara isar ta sabida zaman babu dad’i duk da kasance gidan basu da y’an uba amma bata jin dad’in zaman gidan dan abun tun ana yi mata gori a waje har ya zama ana yi mata a cikin gidan su k'anwar ta wacce take ganin kansu d'aya tayi bala'in raina Rukayya dan gani take komai daidai suke yi.

Abin bai cigaba da damun Rukayya ba sai da mahaifiyar ta ta fara canja mata akan batun auren, ta fara kawo mata duk namijin da ya nuna yaso duk rashin nagartarsa sai tace ta aura ita kuma tak'i hakan shine ya saka koda yaushe a cikin fad'a take mata tana ganin itace tak’i yin auren tunda ana kawo mata miji sai tace bata so.

Rukayya kuwa ta barshi a aure lokaci ne zai zo indai tana da rabo, Gashi gidan su suna da rufin asiri sosai dan har Umrah Baba yana zuwa amma ta b’angaren rashin auren Rukayya Allah ya jarrabe shi kuma ya k'arbi kaddara Umma ce dai ta kasa karb'a sabida maganar mutane musamman y'an uwatan ta da kawayen ta kowa zancen sa har yanzu Rukayya batayi aure ba gaskiya ta girma ya kamata ace tayi aure.

Damuwar ta yiwa Ruky yawa Kullum cikin kuka take da k'unar rai, Gashi ta gama makaranta Baba ya hanata aiki ya kuma hanata cigaba da karatun Kullum tana gida in zaman gidan ya ishe ta sai taje gidan d'aya a cikin k'awayen ta musamman gidan Ameena dan tasu tafi zuwa d'aya ko taje gidan Fiddausi ma zancen guda d'aya ne shiyasa bata fiya zuwa ba.

Ameena ta fara shan wahalar zaman gidan Yusuf ne lokacin da ta gano yana Shan giya, hankalin ta ya tashi ta kasa nutsuwa tana ta kuka in ya dawo hankalin sa tayi masa magana sai yace tayi hakuri bazai sake ba. Maganar kenan Kullum amma sai ya sake in tana kusa yasha ya bugu babu abinda zai hana bai mata duka ba ta silar dukan da yake mata cikin ta na farko ya zube amma bata fad’awa kowa dalilin ba. A ko yaushe Yaya tana fad’a mata na ko wanne sirri ake fad’awa duniya kowa yana da damuwa a gidan sa amma hak’uri yake yi hakan ya saka

Please Login or Register in order to submit comment