Join Our WhatsApp Group

CIKI DA GASKIYA Part 2 Complete Hausa Novel Document by CIKI DA GASKIYA Part 2


CIKI DA GASKIYA Part 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 124918



CIKI DA GASKIYA Part 2

Reading Time: 10 Hours

Added On: 03, Oct 2023

Author: Bilyn Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : HASKE WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 847.02 kb

File Type: txt

Views: 1222+

Download: 1826+

Last download: 15 hours ago

Description/Story: *_Typing📲_*[9/6, 6:54am]Aysha Galadima:



🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_


*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭



*_part 2_*
(littafi na biyu📕)

*_Ina mai farin cikin sake had'uwa daku a CIKI DA GASKIYA.....kashi na biyu, ALLAH ya amfanar damu abinda ke cikinsa, kuskurena kuwa ku watsar dashi gefe, dannima mutumce kamar kowa ajiza, ALLAH ya mana jagora, yajikan mahaifanmu dadukkan musulmai baki d'aya._*
Ina godiya agareku sosai😘😘😘.


➡1⃣

Fadeela dake bayan Aysha tace, "gwaggo! Dama kece babu lafiya?, ina mama taganoki?.
Duk atare tajero tambayar.
Da k'yar Gwaggo bintu take fidda numfashi, da yak'en dole wa Fadeelah, Aysha kam takasa cewa komai, jitake tamkar takashe gwaggo bintu kawai kowa yahuta.
Wani mugun plashing yashigo wayarta, saikuma sak'o yashigo, samun kanta tayi da ciro wayar daga post d'in hannunta taduba.

_karki yarda kiyi wani abunda zai nuna gwaggonki tayi wani mugun Abu akanki, hakan tamkar wargaza aikinmune, ki kiyaye, so kisan yanda zaki nuna komai normal tsakaninki da ita saboda sister d'inki, karki 6atamin aiki._

Abinda aka rubuta kenan kuma an 6oye number, Aysha takuma maimaita sak'on a karo Na biyu, cikin mamaki tace wanene wannan?......
Muryar gwaggo bintu ta tsinkayo tana fad'in Aysha da gaske kece? Kece kika dawo garemu? Tayi maganar tana rushewa da kuka.
Da sauri Aysha taje ta rungumeta, ta fakaici idanun su fadeelah tafad'a ma gwaggo bintu magana a kunne, _gwaggo kada kiyarda ki nuna wata alamar dazata gane kin saka rayuwata agarari, wlhy inba hakaba sai an kasheki, kinuna murnar dawowata daga karatu, Dan ALLAH ya juya zalincinku agareni yazama alkairi nayi karatun._.
Su fadeelah dabasu San abinda ke faruwaba suka Shiga lallashinsu, fadeelah ta janye Aysha daga jikin gwaggo bintu tana bata hak'uri.
Bak'aramin mutuwa jikin gwaggo bintu yayiba, tabbas maganar Aysha ta shigeta, _(nace karan bana aishi ke maganin zomon bana gwaggo bintu😂)._
Aysha takoma kusada gwaggo bintu ta zauna, bishirah jitake tamkar cinye Aysha dan murna, suna rik'eda hannun juna, kai Aysha wlhy kin canja, ilimi dad'ine dashi, kamar bakeba wlhy😁.
Dariya Aysha tayi, wlhy nima duk kin canja mini bishirah, kinzama babbar budurwa, halan kinkusa aure ma?.
Hhh saura wata 2 ma.
Eyeee Ashe zamusha biki, ALLAH yasanya alkairi.
Ameen fadeelah ta amsa.
Sund'an dad'e a sibitin, amma gwaggo bintu takasa sakin jikinta, sai yanzu nadama da Dana Sani ke k'ara yawa a zuciyarta, taci amanar d'iyar zumunta, gashi wadda tasata aikata hakan y'arta ta azabtar da ita, tunda ta kwanta asibitinnan babu jinin hajia babba ko d'aya daya lek'o dubata, bare ita hajia babban, lallai tayi kuskuren dabatasan tushen gyarashiba, afakaice taketa share hawaye, Wanda Aysha Ce kawai talura dasu.
Aysha taja bishirah gefe suka zauna.
Bishirah nikam bayan barina gidannan miya farune?.
Humm abubuwa dayawa sun faru Aysha, ciki harda Auren da alhaji ya k'ara, tas bishirah takwashe komai tafad'ama Aysha, har zuwan gwaggo bintu Lagos da dawowarta, harda sanadin kwanciyarta a asibitin.
Aysha tace ALLAH ya kyauta.
Itama bata 6oyema bishirah komaiba, tabata labarin komai akan abinda yafaru da'ita, kuka sosai bishirah takeyi harda majina, tad'ora mata bayani akan amaryar alhaji mahaifiyartace.
Bishirah kinsan miyasa na baki labarin sirrina kuwa?.
A'a saikin fad'a Aysha.
Saboda ki taimakeni, kuma Dan ALLAH ki rik'emin sirrina, zan d'auki fansa akan hajia babba da sauran mutanen k'ungiyarsu, amma hakan bazai faruwa saina samu wasu sirrika atareda ita.
To Aysha wane taimaki kikson namikine?.
Kawo kunnenki.
Aysha tagama fad'ama bishirah abinda nikam banjiba🤷🏽‍♀.
Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan al'amuran rayuwa dakuma yanda zasu 6ullowa komai kafin auren bishirah.
Hango fadeelah dake nufosune yasakasu mik'ewa suna dariya.
Aysha tace yi hak'uri yaya fadeela munbarki ke kad'ai, kinsan andad'e ba'a had'u baneba.
Batace komaiba sai juyawa tayi sukabi bayanta.
Koda suka koma basu dad'eba sukamusu sallama, Dan itama gwaggo bintu suna saran sallama yau da daddare.


_____________________________

K'arar dasukajine tasakasu farga da abinda ke faruwa, da sauri babban yaron Barau modibbo yalek'o, ganin jami'an tsaro yasakashi rikicewa, yunk'urawa yayi danufin guduwa amma sai hakan ya gagareshi, sakamakon harbinsa da Joseph yayi a k'afa.
Da sauri ya khaleel dake la6e kusadasu yafito shima, saukar harbi yaji a hannunsa Na haggu.
Da sauri yadafe wajen tareda kallon saitin da'akayo Harbin, barau modibbone, yakuma Harbin ya khaleel a ciki, amma bata shigaba, saboda rigar dake jikinsa mai kare shigar bullet.
Ganin haka barau modibbo yajuya da sauri zuwa wani d'aki.
Cikin sassarfa ya khaleel dawasu ma'aikata suka take masa baya, dukda d'an Karen azabar da hannunsa ke masa, ga jini tuni yafara jik'a yellow d'in rigarsa.
Neman duniya sunrasa inda barau modibbo yake, babu binciken dabasuyiba agidan, amma babu ko alamarsa.
Basusan ya silale tawata k'ofaba yabar gidan tabaya, dama antanaji k'ofarne saboda irin wannan ranar.
Saidaga baya ya khaleel yafarga da k'ofar, cikin cije le6ensa yatura Waldrop dake wajen gefe, cikin nazarin k'ofar yace, Taheer inaga yagudu ta Nan.....
Awahalce yake magana saboda jiri daya fara gani, sakamakon jinin dake zuba a hannunsa.
Suduka suka k'araso wajen da sauri, wasu fita sukayi, inda k'ofar ta kaisu harcan baya, alamar tashin motarsa suka gani, wannan ya tabbatar musu cewa yagudu.
Dawowa sukayi inda ya khaleel yake dafeda hannunsa, sai faman lumshe idanu yakeyi.
Da sauri Adams yak'araso wajensa, sunma manta boss yasamu harbi, youseef ne ya yago bedsheet d'in gadon da hanzari Adams yakar6a ya d'aure hannun ya khaleel Dan tsaida zubar jinin.
Basu wani 6ata lokaciba sukabar gidan da gawar wad'anda ya khaleel ya kashe, saikuma yaraonsa dasuka kama.
Dr Abraham sukakira, yace yana General hospital, suyi hak'uri su sameshi a can, Dan sun fad'a masa boss ne yasami harbi.
Da sari Adams ya amsa da to, Emmanuel muje general hospital.

motar Ramadan na niyyar fita daga Asibitin tasu ya khaleel tashigo, Ramadan yace ai wannan motar ya khaleel ce, yay maganar yana taka birki.
Wani irin fad'uwar gaba Aysha taji, tuna a yanayin daya fita d'azun, fitowa sukayi sudukansu. Ramadan yanufi motar da Sauri.
Da kansa yafito, saida kana ganinsa kasan babu lfy, Dan dak'yar yake d'aga ido ya kalli hanya, wannane ya haddasama tafiyarsa d'an rangaji.
Da sauri Ramadan yak'arasa ya rik'eshi yana fad'in ya khaleel lfy?.
Cikin jarunta irin tasa yace, shiga dani ciki, mubi ta baya. Banason su tada hankalinsu, harbine kawai.

Ta baya sukabi, Aysha da Fadeela suka nufi cikin asibitin hankalinsu a tashe.
Kai tsaye office d'in sa suka nufa, Bahama a ciki.
Babu dad'ewa Saiga Dr Abraham, tareda Adams suka shigo suma.
Duk fita sukayi, suka bashi damar aikinsa, ya khaleel nazaune akan kujera yajingina da bayansa idonsa a lumshe.
Cikin hanzari Dr Abraham yake gudanar da aikinsa.
Ya khaleel akwai jarunta, inbanda matse ido dad'an cije baki babu abinda yakeyi, har Dr Abraham yagama cire bullet d'in, sai zufa ya khaleel keyi saikace ana kwara masa ruwa, dukda kuma ac dake aiki a office d'in, duk wani abinda yadace anmasa, harda allurar barci, dak'yar Dr Abraham ya lalla6ashi ya kwanta a gadon dayake duba marasa lfy, amma da yadage akan gida zaije, Dr Abraham yace yayi hak'uri allurar da akayi masa ta sakesa first, saiya tafi.

Su Aysha Na waje sai safa da marwa sukeyi, ahaka baffah da Ramadan yakira yak'araso.
Cikin tashin hankali yake tambayarsu miya faruda Mu'azzam d'in?.
Adams ne yamasa bayanin harbine, baikai k'arshen zancenba Dr Abraham yafito.
Ya tabbatar musu ancire, kuma ya khaleel yana barci, zaid'an huta danya saka masa k'arin ruwane.
Damuwar tad'an ragu agaresu yanzu.
Amma banda Aysha, daketa share hawaye tun d'azun, idon baffah na kanta, duk abinda takeyi yana kallonta, ganin kukan datakeyi yak'i ya karene yasaka baffah matsawa kusada ita yana lallashinta, da nuna mata tamasa addu'a ba kukaba.

*_hours ago_*

Bayan awoyi kusan 5 ya khaleel ya farka, dama tuni ruwan ya k'are, saboda tashin hankalin da 'yan gida suka shiga yasakasu tafiya gida, lokacin anata sallar isha'i.
Su Aysha tuni baffah yasaka ya Ramadan ya maidasu gida dama.

Duk suna falo kowa jigum-jigim, hajia babba ce kawai babu da y'ay'anta, itama tana 6angarenta jigum, Dan labari yazo mata akan abinda yafaru da ya khaleel d'in.
Shigiwarsu tasaka kowa mik'ewa, kowa yayo Kansu, Dan dukkan mazan gidan suna asibitin, a babban falo yazauna sunata masa sannu.
Ganin yanda suke arud'e yasakashi sakin murmushi, yace kufa kwantar da hankalinku, ni Na warke.
Jiki a sanyaye suketa d'aga kai.
Anty Mamie takawo masa tea, kar6a yayi yana fad'in thanks you Mamie na.
Murmushi tamasa tana jinjina kai.
Ahankali yake sha idonsa Na kallon familien nasa, daduk suke zaune afalon, harsu hajia babba dasuka fito, saidai yanayinta yabama kowa mamaki yau, Dan babu masifa, saidai tanata kaffa-kaffa da ya khaleel d'in.
Ahankali yad'ago idonsa ya sauke akanta, tanacan raku6e bayan Umme amarya, daka ganta kasan a hargitse take.
Guntun murmushi yayi, aransa yace, trouble marker d'ina yau kuma miya maidata haka?.
Aysha dabatasan ita yake kallonba tad'ago ido danufin satar kallonsa, amma sai karaf suka had'a ido, da sauri ta janye nata tana d'an tura baki gaba.
Shima ya kauda kai gefe, ahankali yace anan da hali.
Hajia babba dake gefensa duk hankalinta atashe tace mikace?.
No momy bance komaiba, baradai naje nad'an watsa ruwa, Na rama sallolin dake kaina.
Ok.
Mik'ewa yayi sunata masa sannu.
Hajia babba tabi bayansa, dakanta tahad'a masa ruwan wankan, sai wani dama-dama takeyi dashi, danso take taji idan sun kama barau modibbo.
Abin Na momy mamaki yake bama ya khaleel, Dan bayaune karon farko da'aka ta6a harbinsa ba, amma momy bata masa irin wad'annan abubuwan, hasalima saidai Anty Mamie tamasa.
Baikawo komai aransaba yashiga wankan, itakuma tafita tabashi waje.



*bayan 2days*
Ya khaleel yaji sauk'i sosai, ga kulawa ta musamman dayake samu daga momy da Anty mamie, harma da mama dadukkan sauran 'yan uwansa.
Aysha bata ta6a zuwa gaidashiba a kwana biyunnan.
Daga wajen aikinsa kam lamarin ba'a cewa komai, manyansa dayawa sunzo, hakama wad'anda suke k'asa dashi.

Gwaggo bintu ma an sallamota jiya.
Mama da kanta tayima baffah bayanin dangan takarta da gwaggo bintu.
Baffah yasha mamaki, danbai ta6a zaton hakaba.
Yacema mama to yakamata gwaggo bintu takoma hannunta, baikamata tacigaba da zama mai aikiba, ya y'antata.
Mama taji dad'in haka sosai, Dan dama haka take so.
Wani sepia d'aki aka gyara mata a 6angaren mama.
🤣saidai abinda nalura dashi, gwaggo bintu bata murna da hakan, idan San samune ita kawai ta fece Kano abinta. Amma tana nuna hakan mama zata gane wani Abu, shiyyasa tayi gum da bakinta😂.

Hajia babba duk batasan hidimar da'akeba sai ayau.
Wannan lamari yatada hankalinta, da gaggawa ta aika aka kira mata gwaggo bintu kuwa.

Bintu! Wane labari nikeji agidanan? Kina nufin k! Y'ar uwar fad'ima ce? Idan hakane ina yarinyar damuka tura karatu?.
Ganin yanda tarikice sai abin yabama gwaggo bintu dariya, amma batayiba, mamaki takeyi dama akwai abinda zai tsorata hajia babba haka?.
Bintu dake nakefa, kikamin shiru.
Gwaggo bintu tanisa, tareda fad'in hajia ni k'anwar mijin fad'ima ce uban Aysha dakika kai karatu, amma ki kwantar da hankalinki batasan komaiba, har anzu azatonta d'iyarta tana makarantane, kuma ni bazan ta6a fad'a mata komaiba kinji.
Ajiyar zuciya hajia babba ta sauke, tadafa kafad'ar gwaggo bintu tana fad'in yauwa bintu ngd sosai, shiyyasa kike birgeni, ga wannan kud'in dubu100 ne, kiyi amfani dashi.
Sosai gwaggo bintu ta nuna murnarta, hajia babba ta sallameta tana zabga mata godia.
Fitowa tayi tana mai daria a zuciyarta, tace hajia laurah kenan, aii bazaki ta6a fitaba daga wannan tarkon, Shiga ukuma yanzu kika fara Shiga cikinta wlhy, masu iya magana kance *CIKI DA GASKIYA...* wuk'a bata hudashi aii🤷🏽‍♀ aii.

Nace na hajia babba kam babu *GASKIYAR NAN* nasan 6us!!!!! zamu hudashi🔪🤰🏻aradu😆😆😆🤣.


________________

Da daddare baffah yatara dukkan families d'in nasa, harda Ammah data dawo aranar saga Jigawa............✍





Komi baffah zai fad'a??🤔.
Kumuje zuwa my...


Read / Download CIKI DA GASKIYA Part 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album