Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

TSAKA MAI WUYA Complete Hausa Novel Document by TSAKA MAI WUYA


TSAKA MAI WUYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 6358



TSAKA MAI WUYA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 11, Oct 2023

Author: Yusuf Abdullahi A Jibaga ,Bukar Mada ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 37.65 kb

File Type: txt

Views: 1047+

Download: 214+

Last download: 1 day ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

TSAKA MAI WUYA...!!!
KOTU! KOTU!! KOTU!!!
21 April

"Hajiya Rahama munaso ki tabbatarwa da KOTU hujjojinki akan zargin da kikeyiwa direban gidanki YUSUF na kashe miki tilon 'yarki har lahira, Shin ya al'amarin yafaru ne? Kamashi kikayi dumu - dumu ko kuwa ya abin yake ne Hajiya?"

kotun cike take makil ba masaka tsinke sbd sauraron wannan shari'ah mai razanar da tunanin duk wanda yaji taken karar, hajiya rahama wadda ke tsaye a inda aka tana a kotun dan amsa tambayoyi ta gyara tsayuwarta sannan ta dubi lauyanta wanda yayimata wannan tambayar,
"Wato al'amrin yafaru ne da maraicen wata ranar juma'a dai - dai lokacin da SAFARA'U tadawo daga makaranta, tana shigowa gida kamar yadda tasaba sai ta nufi firji domin samun Maltina mai sanyi kamar yadda tasaba, to awannan ranar sai akayi rashin sa'a domin kuwa maltinan dake gidan gabadaya ta kare, gashi kuma ta saba shanta kusan koda yaushe, dan inhar batasha ba to ba kasafai take xama cikin walwala ba, dan hakane sai ta kira yusf direba ta aikeshi dayaje yasiyo mata maltina mai sanyi,

bayan dan takin lokaci sai yakawomata ta koma dakinta domin tasha, tundaga nan najita shiru har wajen magriba dan hakane sai na leka dakinta domin atunanina barci takeyi, to anan ne na tarar da ita ta mutu adakinta kuma kumfa cike abakinta wanda likitana ya tabbatarmin da cewa 'yata safara'u tasha GUBA ne wanda adalilin hakan tarasa ranta..."

Hajiya Rahama ta karashe ragowar zancen da kuka mai tsuma xuciya, Lauyan nata ya dubeta kana yace "yanzu likitan naki yana tare damu awannan kotun dan tabbatarwa da kotu cewa guba silar mutuwar 'yarki safara'u?" hajiya rahama ta amsa da 'Eh' Lauyan yakoma xuwa ga Alkali domin neman ixininsa dan gabatar da likitan Hajiyar"

Dakta kotu tanaso ka gabatar da kanka da kuma hujjoji irin naku na likitoci wanda ya tabbatar da cewa safara'u GUBA ce ta xama silar shekawarta lahira" Likitan dan baki mai kira irin ta mutane kudu wato Dan Tittirna yafito yaxo yatsaya kana ya gabatarwa da kotu duk hujjoji da kuma bayanai a rubuce wanda ya tabbatar da cewa safara'u ta mutu ne sanadiyar guba da tasha.

Lauyan ya maida dubansa xuwa ga wanda ake xargin yacemasa "Malam yusuf wacca hikima ce ko riba agareka da har kaxamo sila na mutuwar 'yar uwar gijiyarka? Shin menene yakaika ga aiwatar da wannan cin AMANAR haka?"
Tuni idanun kowa dake cikin kotun yakoma xuwa kan Dan Matashin saurayin wanda ake kira da yusuf Direba, jabir yadago kai yai duba ixuwa cikin kotun wanda kamar an umarceshi daya mayar da kansa kasa sai ya mayar da dubansa xuwa kasa, hawayene ke fita daga fuskarsa, hannayensa hagu da dama daure suke cikin sasari.

"Inna Lillahi wa'inna ilaihir raju'un Na rantse da sarkin dake busamin numfashina ban aiwatar da wani abu ba wanda yaxamo sanadiyar mutuwar safara'u ba, aikena kawai tayi kuma nasiyo nakawomata nafita sai kawai naga rundunar 'yan sanda taxo gidan hajiya kuma akarshe suka cakumeni suka tafi dani da sunan nine na kashe safara'u, wlh bani bane... Kutaimakawa rayuwata... Mahaifiyata bata da lfy nine gatanta wlh... Batasan halin danake ciki ba yanxu... Banaso taji sbd xai iya xama silar rasa ranta idan har taji ankamani da xargin kisan kai kuma a gidan danake aiki... Gidan danake bata lbrn irin karamcin da akemin a gidan...

Innalillahi Wa'inna Ilaihir rajun... Kutaimakawa rayuwata wlh ko bera bantaba kashewa ba balle mutum guda..."
"Ya mai girma mai shari'a abisa kwararan hujjoji da muka gabatar daga wajen bayanan Hajiya Rahama da kuma likitan ta to tabbas hakan ya isa ya gamsar da kotu cewa yusuf Direba shine sanadiyar mutuwar 'yar Hajiya Rahama, kuma ga duk kan alamu yusuf yanuna kansa tunda yagaza bada dalilai masu karfi wanda karshe yabige da koke - koke wanda kuma wannan ba hujja bace da kotu xata dauka ko yarda da ita, Allah yataimaki mai shari'ah"

Lauya AIA kenan yagabatarwa da alkalin kotun jawabinsa na karshe wanda kuma daga nan ne ake dakon abinda alkalin xai xartar.
"kotu taji duk kan bayanai daga kowanne bangare, kuma kotu xata dage xaman wannan kara har nan da 28 ga wannan watan, wato nan da mako daya kenan, wanda ake xargi yana da damar daukar lauya wanda xai kareshi idan kuma har babu har xuwa wannan lokacin to kotu xata yanke hukunci akan abinda yake shine dai - dai kuma bisa hujjoji, sannan kotu tana umartar 'yan sanda akan sucigaba da tsare wanda ake xargin batare dayin beli ba"

Alkalin kotun kenan ya gabatar da jawabinsa wanda da hakane aka kawo karshen xaman wannan shari'ar ta yau.

ZAN CI GABA....

Daga Yusuf Æbdullâhi Æ JibagâTSAKA MAI MUYA 2...!

"Ai ina fadamaka wlh xai iya aikatawa, barganinsa wani sumi - sumi haka yanxu duniyar nan dakake gani da irin wannan sumi - sumin ake fakewa ana tafka ta'asa, kawai ya kashe 'yar mutane, kuma ni abin haushin ma kwastoma tace sosai dan kusan kullum sai ta fito taxo tasiyi tarin alawowi kala - kala, ko banxa ai yamin asarar ciniki, Allah ya isa na ma wlh, dan banza mai kirar 'yan daudu ashe shi karin kunama ne daga antabashi sai harbi" wanda ake fadawar yadan muskuta kadan daga kan dan bencin dake bakin 'yar karamar Tiredar, "wato kai musty bama ta rashin ranta kake ba kai ta asarar daina siyan kayanka kake ko? Wato kai ba ruwanka da jin kai da tausayi na 'yan uwantakar musulunci kenan?" wanda yafara maganar wanda kuma abokin hirar yakira da musty yadubi na biyun cikin alamun mamaki "to in banda abinda Habu sokake na kwanta xaxxabin Maleria sbd direban gidan masu hannu da shuni ya kashe 'yar gidan? Ko kuwa sokake naje kotun nace asakeshi a.......

kamani? Kawai yakashe musu 'ya dan haka sumatse dan banxa sai yatona asirin suwaye suka sashi." na biyun wanda musty mai tiredan yakira da Habu yadubi mustyn cikin alamun takaici "Ni kam wlh xuciyata tana bani tabbacin cewa wannan salihin bawan Allahn baxai iya aikata wannan mugun abin ba, wai dan inaneshi? Dan naga kamar dan kusa da unguwar nan ne" musty mai tireda yadubi Habu din yace "Dan layin CENTRAL MARKET can kasa xakaga wani gida mai kama da bukka to nan ne gidansu, kasan shi talaka dama bashi da kashin arziki inbanda haka kana aiki gida irin wannan amma katashi ka make 'yar gidan har lahira, haba!!!!

Ai wlh su jibgi dan banxa kawai, ni dama baya birgeni sbd yadda kullum nake ganinsa sumi - sumi baya kula mutane dan banzan" "kai musty kaji tsoron Allah, wlh Allah xaikamaka akan irin wannan kagen dakakeyiwa bawan Allahn nan, kai bakasan komai ba dangane da lamuran kasar nan, nan - nan sauro sai yakashe mutum axo ace wanine"

"hahahaha amma lallai habu agaisheka, sauro yabawa mutum guba har yasha ya mutu? Amma wannan sauron girmansa yakai girma kam" habu ya kurawa musty mai tireda idanu kana cikin takaici yamike tsaye wanda da alamu yaji xafin yadda yaga mustyn ya zake wajen kara aibata dan uwansa musulmi abisa abinda bashi da tabbacin hakan, " ni xan tafi, kuma Insha'allahu xanyi kokarin xuwa gidansu bawan Allahn dan bincikar ko iyayensa sunsan halin dayake ciki, dan yanda na lura kamar ita hajiya mai gidan baxa ta fadawa iyayen nasaba" musty mai tireda yadubi habu din bayan da habun haryafara tafiya da xummar barin wajen, "kace dai tsohuwarsa kawai, dan ni bantaba ganin ubansa ba, nasan dai tsohuwar gyatumarsa..."

****************************
Dogon layi ne mai matsakaicin fadi wanda hakan bayarasa nasaba da yawan dakalin da mutanen layin kowa ya malala wanda hakan yaxamo sanadiyar yiwa layin kamshin mutuwa ta yanda ya xamto bashi da fadi gabadaya, daga can kuryar yamma na layin yadanfi fadi sakamakon wasu gidaje guda biyu da basuyi dakalin ba, layin yalwace yake da wadatuwar yara ta ko ina wanda hakan yake nuni da cewa layin na 'ya 'yan malam SHEHU ne (talaka).

Dai - dai kusan wannan lokacin ne HABU ya shigo cikin layin, tafe yake yana ta rarraba idanu dan dai ganin ko xai iya gane gidan da musty mai tireda ya kira da MAI KAMAR BUKKA din, can idanunsa suka kai ga kuryar yamma na layin inda wasu gidaje guda biyu suke a ware waje daya, can daga gefe wasu tarin yarane axaune suna wasa dan haka kai tsaye habu yawuce xuwa ga yaran domin samun agajinsu wajen fadamasa inane ainihin gidansu YUsuf din.

"kai sannunku, inane gidansu yusuf dan Allah? wanda yake aiki a gidan hajia rahama dake layin G.R.A " wani yaro daga cikin ragowar yaran yai saurin bada amsar ta hanyar yin nuni da dan yatsansa xuwa ga daya daga cikin gidajen nan guda biyu dake ware waje daya, "gashi can wancan na farkon ne mai kofa abuden can" shine gidan su...


Read / Download TSAKA MAI WUYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album