Join Our WhatsApp Group

ACI BULUS Complete Hausa Novel Document by ACI BULUS


ACI BULUS

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 25632



ACI BULUS

Reading Time: 2 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 136.05 kb

File Type: txt

Views: 582+

Download: 197+

Last download: 1 day ago

Description/Story: ACI BULUS - 01
.
(c) Nazir Adam Salih
.
.
"Ni ban ce da ke mummuna ne
ba. Yana da kyau daidai
gwargwado. Abin dai kawai da
nake so da ke shi ne ki
bambance tsakanin karya da
gaskiya."
yan matan biyu suka dubi juna
na dan lokaci. Sannan wankan
tarwadar ta dubi farar ta ce.
"Me kike nufi ne Asma'u? Ni fa na
kasa gane wannan soki burutsun
naki. Ban san abinda imran yayi
miki ba bakya son sa". "ba wani
haka bane Rabi'atu. bawai bana
son sa bane. Abinda nake so ki
gane shine duk son da nake
masa bai kai wanda nake yi miki
ba. Ke kawata ce tun muna yara.
Dole ne na shawarce ki ga bin
duk abinda nake ganin ya dace ki
bi domin amfanin kanki haka ma
na hane ki ga barin duk abinda
nake ganin zai cutar da ke".
Asma'u ta yi shiru tana maida
numfashin ta san nan ta dubi
Rabi'atu ta ce.
"Yanzu ke kina tsammanin imran
zai iya auren ki kuwa? Dan
makaranta ne fa, karambani ne
kawai irin na yaran samarin nan
mayaudara, yanzu ke in banda
lalacewa ina ke ina kula wani
imran, wanda ba shi da wani
(hope) a rayuwa, ba fa dole bane
in ya gama makarantar ma ba ya
sami aikin da zai iya rike ki, kuma
kina nufin yanzu jiransa za ki yi
har sai ya gama karatun kuwa
me kike nufi?".
Asma'u ta dubi Rabi'atu, sannan
Rabi'atu ta dubi Asma'u ta
girgiza kanta cikin damuwa.
"Asma'u, ina son ki sani cewa
idan har babu wata mafita, to
dole ne na yi jiran nasa har sai ya
gama domin Allah ne mai komai,
bana jin zan iya zama da wani da
namiji in ba shi ba, domin shi na
ke so kuma na tabbata shima
yana kaunata tsakani da Allah."
"Kin dai bani kunya wallahi".
Asma'u ta ci gaba da cewa.
"Amma kina da aiki, sai ki yi ta
jiran nasa gani ki ka yi za ki iya
idan kikayi wasa kuma, wallahi
sai ya gama makarantar ya sauya
wata budurwar kinga daga nan
sai ki hakawa kan ki kabari, ki
shiga a binne ki tunda kuwa kin
ce baki iya zama da kowa sai shi,
to idan ya mutu fa yaya za ki yi...".
"Ba zai mutu ba Asma'u, kinga ya
ishe ki, wane irin fata ne kuma
haka na mutuwa."
Ama'u ta fashe da dariya, har da
kyakyatawa.
*
"Iye!! Harma wani kare shi kike
yi, ke dai wallahi har yanzu
bagidajiya ce, sau da yawa ki kan
bani mamakin abinda kika gani a
jikin Imran kika like masa haka
kamar cingam, ga wani can
kullum yana fama da ke amma ko
gaisuwa kin ki tsayawa ku yi".
"Kina nufin Abdul?". Rabi'atu ta
tambaya.
"Ashe kina iya ma rike sunan sa
daman da gangan ki ke
walakanta shi saboda Imran...".
"Kin ga ni ba wulakanta shi nayi
ba, ke wallahi Asma'u kin cika
sharri."
"Ah! To sharri ne, in gaskiya ne
to idan ya zo yau a kula shi mana
kamar kowa."
Asma'u ta yi shiru, gami da yar
boyayyiyar atishawa, sannan ta
dada da cewa. "Rabia'tu ya
kamata ki yi wa kan ki fada ya
kamata ki daidai ta tsakananin
Imran da Abdul, na sha fada miki
Abdul din nan so yake ya aure ki,
duk da yake dai shima ba wani
hali yake da shi sosai ba, amma
shi yana da (hope) domin ina
tabbata miki da cewa nan da
wata hudu zai shi go gari. Amma
ke kin nace wa Salula, tsammanin
warabbuka wai malam ya ki
noma don zakka.
Wallahi Rabi'atu duk cikin
samarinki babu wanda ya ke
sonki da aure kamarsa, ke ce dai
ba ki sani ba, kuma kin ki ma ki
saurare shi ballantana ki gane
manufarsa. To kanki, ni dai
shawara na ke baki ba wai don
Abdul dan'uwana ba ne, ni dai
kawai ina ganin kamar shi ya
dace da ke."
Asma'u ta mike tsaye ta gyara
daurin zaninta sanan Asma'u ta
mike tsaye ta gyara daurin
zaninta sanan ta ce.
"Ni zan tafi, amma don Allah
Rabi'atu idan Abdul ya zo gobe ki
saurare shi, bai dace ba a ce kina
share shi a gaban Imran, ke baki
san halin samari ba ne, wallahi in
kika sake Imran ya gane kina
kaunar shi kin gama yawo. Ke ko
irin gwajin nan ma kin ki ki yi
masa irin wanda ake yi dan ki
gane ko yana kaunar ki ko baya
yi. Share shi za ki yi na kwanaki
biyu sai ki gani, idan ya share ki
ya ki ya lallabe ki to wallahi ba
kaunar ki ya ke ba."
*
"Kai Asma'u ke kuwa kamar
shedaniya. Ai ni wallahi da kyar
zan iya yiwa Imran haka, domin
tsoro nake kada ransa ya baci
kuma ina kaunarsa kinsan....".
"To shike nan daman shawara
ce, tunda kuwa kin ki sai ki je ki
yi ta zubar da mutuncin naki
gabansa." Asma'u ta ce cikin
fushi. Rabi'atu ta dubeta ta ce.
"Ke kuwa abina da ke kenan
wallahi saurin fushi ni ban ce ba
zan dauki shawarar ki ba, ai
ciwon ya mace na ya mace ne."
"Ashe dai kin gane yar gari. To
tunda dai kin fara gane abinda
nake nufi daga yau sai Abdul ba
Imran ba kayansa."
"A'a... Shima zan ke kula shi ai
ba...".
"Ba cewa nayi ki daina kula shi
ba, amma abin da za ki yi masa
shine kafin ki kula shi sau daya ki
kula Abdul sau bakwai, kin gane ai
.
"Na gane." Rabi'at ta ce, zuciyarta
na wasuwasi, anya kuwa za ta
iya yiwa masoyinta Imran haka,
sun dade da shi kuma ta san
yana matukar kaunarta kamar ya
hadiyeta, a kullum ba shi da wani
zance sai na ya aure ta, to amma
ta kance da shi da sauran lokaci,
to kuma sai gashi katsam wani
yana shirin faruwa anya kuwa za
ta iya. "Ni zan tafi, sai jibi zan
dawo na ji yadda kuka yi da shi
Abdul din." Sannan ta dubi
Rabi'atu ta yi murmushi lokacin
da ta nufo kofar dakin Rabi'atu,
na biye da ita a baya. "Ko ke fa
Rabi'atu, amma a ce kyakkyawa
kamarki ta rasa wanda za ta kula
wai sai wani marar mamora, wai
Imran, ni wallahi har kunya nake
ji naga ya zo gunki zance a
tsohon keken nan mai kamar
dokin kara." Yam matan biyu
suka fashe da dariya. Rabi'atu ta
kaiwa Asma'u duka a baya. ***
*
Abdul ya shafi gashin bakinsa
sannan ya sake kallon fuskarsa a
cikin madubi, a kalla dai
shekarunsa basu nuna ba karara
a fuskarsa, in ka dauke jajayen
idauwansa kiri-kiri da su babu
wanda zai iya zata ya kai shekara
talatin da bakwai a duniya. Abdul
gajere ne wankan tarwada, zai yi
wuya ka iya karanta abin da ke
kunshe a zuciyarsa ta hanyar
duba fuskarsa. Domin in har da
fuskarsa za ka yi amfani to kana
iya zabarsa a matsayin babban
limamin masallacin unguwarku,
amma a zuci, zai baka mamaki,
domin an dade a duk fadin
unguwar ba a sami cikakken dan
bariki ba kamarsa, kwararre ne
wajan kora ruwan bagaja,
sannan kuma kartagi ne gurin
caca, sai dai yanzu ana iya cewa
sambarka ya dan shiryu, tunda
dai ya daina caca da shan giya,
abu daya ne kawai bariki ta
barshi da shi, shi ne neman mata,
wanda abin ya zame masa kamar
jaraba, hakan shi ya sa shi
shantake kafafu, ya ci gaba da
tafka aikin masha'a. To kuma
katsam, sai abin hangen mata, ya
hango masa Rabi'atu. Tun sa'ad
da ya dora idonsa a kan ta ya
dauki aniyar ko ta yaya sai ya
mallake ta, kai ko da auren ta
nema yana iya yi. Shi kansa abin
yana bashi mamaki ba don
komai ba kuwa sai don tun da
yake a rayuwarsa bai taba
tunanin aure ba, kai shi a
tunaninsa ma mata irin na aure
ba su san mene ne rayuwa ba.
Katsam rana guda Rabi'atu ta
sauya tunaninsa, tun da ya ganta
ya ke fatan mallakarta, bai damu
ba da cewa Rabi'atu tana da
wanda ta ke kauna tun kusan
shekaru hudu da suka wuce, ya
san cewa ko da na ci da bin
malaman tsibbu sai ya yi nasarar
mallakarta. Ba karamin girgiza ya
yi ba, lokacin da ya ga ya gama
nacin duk a banza, Rabi'atu ko
kallo bai isheta ba, gashi kuma
kullum sai masifar kaunarta ce ke
shiga zuciyarsa, hakan shi ya sa
shi yanke shawarar da bai taba
tsammanin a da zai yi ba. Lokacin
da Abdul ya fuskanci ya gama
duk abin da zai iya yi, ya kuma
gama kaskantar da kansa gare ta
amma sam abin ya ci tura, kuma
abin bakin ciki ma shi ne kusan
duk sa'ad da ya je gurin Rabi'atu,
ba za ta tashi wulakanta shi ba
sai a gaban Imran wannan abu
ya kona masa rai matuka. "Sai na
rama, wallahi sai ta san ni ta ke
yiwa haka". Abdul ya yi wa kansa
alkawarin hakan. Kusan malaman
tsibbu goma sha biyar ya baiwa
kwangilar Rabi'atu, yau ne kuma
ranar da aikin ya kammalu, dan
haka lokacin da Asma'u ta zo ta
ce da shi ai yau mutuniyar sa
wato Rabi'atu ta ce ya je, sai farin
ciki ya lullube shi domin ya san
malamansa sun cimma nasara.
Sai kuma ta je gidan za ta gani.
Ya ce da kansa sai na gana mata
irin azabar da ta gana min. Abdul
ya mike tsaye ya janyo farin
kambas dinsa daga karkashin
gado ya sa, sannan ya gyara
shimfidar gadonsa ya matsa
gaban madubi ya sake gyara
gashin bakinsa, sannan ya gyara
shimfidar gadonsa, ya sake
matsawa gaban madubi a karo
na biyu ya gyara gashin bakinsa,
sannan ya yi wa kansa
murmushi, a daidai lokacin da
aka turo kofar dakin babu
sallama, a ka shigo kai tsaye.
"Some body got to die!!" Mai
shigowar ne ke fadi cikin
shakakkiyar muryar da kan iya
tsorata yara a tunaninsa, wai
waka yake yi. Abdul ya juya cikin
sauri suka yi ido biyu da Nasiru
jackal. Nasiru jakal shine babban
abokin Abdul tare suke sheke
ayarsu a doron kasa. "Ina kuma
za ka na ga kana wani shirye
shirye, ba dai wajan mara kunyar
yarinyar nan za ka koma ba?".
Abdul ya yi murmushi sannan ya
ci gaba da goge takalminsa da
wani farin tsumma. "kai ma ai ka
sani". "Na san me, kana nufin
gurin nata za ka koma kai fa
wallahi kamar kare ka ke baka da
zuciya, Haka kawai za ka bar
wata yar cilikowar yarinya
karama tana juya ka yadda ta so
kamar wata waina, idan ba ka sa
ni ba Abdul bari yau na fada
maka, duk abokanmu sun tsane
ka saboda wannan yarinya, kai
ba aurenta za ka yi ba, to mene
ne na nace mata, sanin kanka ne
ba irin matan mu bace to kuma
mene ne na bata lokacinka." "wa
yace maka ba aurenta zan yi ba."
Abdul ya katse shi. Nasiru Jakal ya
dube shi sororo sannan ya ce.
"Amma kuwa ka hadu da wahala,
kuma ka bani kunya, kana nufin
kenan ka jefar da kambunka,
yanzu a kan wannan yar
cilakowar zaka wani...ACI BULUS - 02
.
Kana nufin kenan ka jefar da kambunka,
yanzu a kan wannan yar
cilakowar za ka yi wani abu wai shi aure?" Abudul ya yi
murmushi sannan ya dubi jakal
ya ce "Dan haka ko yaushe nake
son ka rika girmamani, a
matsayina na Malaminka a harkar
bariki, Abinda na ke son ka gane
shi ne a duk sa'adda ka nemi
mace iya kokarinka, amma taki
ka, ta kuma nuna maka
matsayinka a gaban wani
karamin kwaro, to kada ka ce za
ka yi fushi domin idan ka yi fushi
ka rabu da ita, ta gama da kai
domin ta bata (record)". Abdul ya
dan yi shiru yana mai da
numfashi sannan ya ciji fatar
baki ya ce da jakal. "Abin da ake
yi musu shi ne, sai ka lallaba su
su zo hannunka, kada ka yi fushi
duk irin wulakancin da za ta yi
maka sai ka daure ka nace kota
halin kaka sai ta zo gurinka. Da
zarar ta zo sai ka nuna mata kai
ka fita iskanci! Sai ka ribanya
abin da ta yi maka sau biyu."
Abdul ya dubi Jakal yana
murmushi sannan ya ce. "Wallahi,
idan Rabi'atu ta zo hannuna sai
na ribanya wulakancin da ta yi
min sau babu iyaka...". "To kai da
kake ta wannan shirmen ta zo
hannun naka ne? jakal ya
tambaye shi. Abdul ya fashe da
dariya. "Shi ya sa Jakal akullum
nake yi ma ka kallon dabaibayi
duk da yake kai kana yi min
kallon turke. To bari in fada maka
Rabi'atu kamar ta zo hannuna
ne." "Ta yaya bayan ko kula ka
bata yi?". Nasir Jakal ya bukata
"Yanzu kuwa za ka gani". Abdul
ya amsa, sannan ya durkusa
karkashin gadonsa ya janyo wata
tsohuwar jaka ya bude ta, daga
cikinta ya fiddo da wata kwalba
fara mai dauke da garin wani
magani bakinkirin, sannan ya
dan bubbuga gindin kwalbar a
gefen katakon gadonsa.
Wani farin hayaki ya yi tsiri sama
daga cikin kwalbar, ya hada wani
dan karamin gajimare a sararin
samaniyar dakin. Nasir Jakal ya yi
tsalle gefe guda cikin fargaba.
"Kada ka ji tsoro Jakal wannan
gwaji ne kawai na yi maka
yanzun nan zan bunne kwalbar,
daga nan kuma sai gurin
Rabi'atu, ina tabbatar ma ka da
cewa binne kwalbar nan, kamar
binne soyayyar Rabi'atu da Imran
ne, soyayyar su kuma daga yau
sai dai tarihi." Abdul ya sake
murmushi a karo na biyu, lokacin
da ya dubi fuskar Jakal ya yi
sharkaf da gumi, kamar ya yi ido
biyu da fatalwa. Za ku gani jakal,
ba ku na yi min dariya ba ku da
(Friends) abokai, wai har ma kin
rakani kuke yi gurinta wai kada
ku wulakanta to ai shike nan,
wannan shi ne bambancina da
ku a harkar bariki, ku ci gaba da
dariyar ku ku na ji kuna gani
ZAN CI BULUS
ku na shirme." Ya fashe
da dariya, sannan ya nufo kofar
dakin kwalbar, har yanzu farin
hayakin bai daina fita daga cikin
kwalbar ba. Nasir Jackal ya bi shi
da kallo. Tabbas ya yi gamo da
aljannu ya ce cikin zuciyarsa.
*
PART (2) PAGE (17)
________________
Imran ya daga kansa sama yana
duba izuwa ga wani dan
kankanin tsuntsu mai doguwar
jela, launin rawaya da shudi. Tun
sa'ad da suka zauna gindin
bishiyar tsuntsun ke ta rera
wakoki cikin wani irin yare da
Imran bai iya ganewa. Imran ya
so ya tashi tsaye daga kan
kujerar da yake zaune domin
kawai ya karewa tsuntsun kallo,
to amma irin Halayyar da Rabi'at
ta zo masa da Ita a yau bai bari
Imran ya kula da dan tsuntsun.
Bishiyar da suke zaune a
karkashinta ita ta fi kowacce
bishiyar inuwa da kyawawan
furanni a duk fadin farfajiyar
gidan su Rabi'atu. Imran ya
muskuta daga kan kujerar
sannan ya zaro wani farin kyalle
daga aljihunsa ya goge gumin da
ke kwararowa tun daga
goshinsa har zuwa gadon bayansa.
Imran ya dawo da hankalisa kan
Rabi'atu wace ke zaune a kan
kujerar dake gabansa kanta a
sunkuye tana wasa da ganye a
hannunta.
"Me ke damun ki ne yau Rabi'atu,
ni na ga duk hankalinki baya
gurin nan." Rabi'atu ta dube shi
ta tabe bakinta ta dauke kanta
gefe guda. "Ni babu abinda ke
damuna."
"Babu abinda ke damunki, amma
kike irin wannan tunane-tunane
haka?". "Ba komai wallahi, don
kaga na yi shiru, kawai dai na...".
Ta karasa abinda take son fadi a
ciki. Imran ya dubeta cikin
damuwa ya ce.
"To ai gani na yi tun da muka
fara hirar nan baki fadi jimla ta
kai goma ba, sai dai kawai in na
tambaye ki ki bani amsa. "Ni
kawai babu abinda zan ce ne,
idan akwai abinda zance ai da na
fada." Ta tabe baki ta sake
sunkuyar da kanta kasa ba tare
da ta dube shi ba.
"Abin ne yau ya ke bani mamaki
Rabi'atu, kin ga da idan na zo, ki
kan yi kokarin fadin duk kalmar
da za ta faranta min rai. Wasu
lokutan ma ko magana ba kya
bari na na yi sai dai na yi ta
sauraron muryarki abar kaunata.
Amma yau na rasa abinda ke
damunki."
"Idan ka san haka ne kuma mene
ne na damun kanka, ni nace da
kai babu abinda ke damuna,
amma kai sai mita kamar
maroki." Imran ya dafe kirji cikin
kaduwa, ba abinda ta fadi ba ne
ya sa shi kaduwa, irin muryar da
tayi amfani da ita tafi sashi
kaduwa. "Ra.. Rabi'atu me ki ke yi
min irin wannan maganganu,
don kawai na tambayi abin da ke
damunki." Ya dan yi shiru yana
sauraron ko za ta ce wani abu, to
amma bata ce uffan ba.
"ko kin fara gajiya ne da ni
Rabi'at." Wannan ya sa ta daga
kai ta dube shi sannan ta yi far-
fari da fararen idanunta ta tsuke
baki ta ce.
"kai ka sani ni dai ba a bakina ka
ji ba. Bai kuma dace ka fadi haka
ba, domin sanin kanka ne duk
cikin samarina babu wanda nake
kauna sama da kai ko karya ne
Imran?". Imran ya rasa abinda zai
ce saboda kaduwa tunda suke
da ita ba ta taba fadin sunansa
haka ba kai tsaye. Sai dai ko idan
ba ya gurin.
"To shike nan Rabi'atu...ni daman
abin da nake gudu shi ne yin
soyayya bisa takurawa."
"ASSALAMU ALAIKUM." Aka yi
sallama Gabadayansu suka dago
kawunansu Suna masu duba
izuwa inda aka yi...


Read / Download ACI BULUS

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album