Join Our WhatsApp Group

SARAN BOYE Complete Hausa Novel Document by SARAN BOYE


SARAN BOYE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 239681



SARAN BOYE

Reading Time: 19 Hours

Added On: 18, Sep 2023

Author: Billyn Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 09033181070, 0903 234 5899

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.36 mb

File Type: txt

Views: 2898+

Download: 3089+

Last download: 23 hours ago

Description/Story: *_Typing📲_*



*_SARAN ƁOYE!!_*


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_ƊANƊANO DAGA ZAFAFA BIYAR 2021_*


No. 1

...........Tun a farkon shigowa anguwar zaka shaida lallai ana biki, musamman da gidan da ake taron ya kasance shine na biyar a farkon shigowa layin.
      Cike titin layin yake da yara da ƴammata harma da manya maza da mata. Musamman a cikin babban haraban massalacin dake manne da katafaran gidan da tun daga kallon gate ɗinsa zaka san ya wuce raini a gine da yalwar girma.
      Rumfunane guda uku a tsaye, waɗanda gaba ɗayansu an cikasune da fararen kujeru bisa tsari. Rumfar farko cike take da manyan malamai masu faɗa aji a ƙasar dama wasu ƙasashen ƙetare musamman na musulmai. Rumfa ta biyu kuwa matane zalla a cikinta tundaga ƙanan har zuwa manya. Rumfa ta uku mazane suma manya da yara.
      Babban abin birgewar da ƙayatarwar shine shigar kamala da mutunci dake tattare da jama'ar wajan. Duk da taron bikine kowa ya suturta jikinsa, babu wani mai shigar ALLAH wadai ta nuna tsiraicin da ake laɓewa da sunan biki.

       Duk da cikar da wajen take da shi hakan bai hana yawaitar mutane a cikin gidanba shima. Lallai da gaske gidan babban gidane, dan a kallo ɗaya zaka fahimci gidan family house ne, dan kuwa yafi ƙarfin mallakar mutun guda kai tsaye. Daga jikin gate ɗin gidan zaka iya ganin dukkanin yawan ɓangarorin gidan da aƙalla zasu iya kai sashe biyar zuwa shidda, ginin iri ɗaya ne babu wani banbanci game kallo da ga nesa, saika shiga daga cikine ka fahimci kowa da kalar tsarin da yafi buƙata a nasa sashen.
          Lokacine bana banbance minene a cikiba, ko mi aka tsara. dan haka nabi ayarin mutane masu kai kawo zuwa sashe na biyu da yafi ɗaukar jama'a. Kasancewar duk mutane na a harabar masallaci wajen da za'a gudanar da walima ya bani damar kutsa kai har cikin ɗakin da naji ana masa ishara da amarya na ciki.
         Ƴammata ne da a ƙalla zasu kai goma zuwa sha a ciki, kowacce nata ƙoƙarin ƙimtsa jikinta dai-dai buƙatarta cikin doguwar riga milk color mai adon golden ɗin furanni da aka ƙawata da stones a gabanta da ƙarshen hannun. Hirarsu suke da dariya har baka iya jin mi wani yake faɗa.
          “Oh ALLAH, Aure mai saka kowa hankali. Su o'e tunkan Yah Ab.. Yaci ƙaniyar bakin harya mutu haka?”. Ɗaya daga cikin ƴammatan dake naɗa ƙaramin golden veil a kanta ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya. Kusan a tare duk suka juya suna kallon wadda ke kwance saman gado ita kaɗai ta juya musu baya, kwance take rubda ciki da ɗaurin ƙirji sai ƙaramin hijjab a jikinta. “Hhhhh! Wlhy kuwa Iman, kinga dai bakin tsiwa tun jiya ya mutu”. Wata tabama mai maganar amsa tana dariya itama da ƙarasawa jikin gadon, yayinda suma sauran suke dariya suna nufar gadon. Sai da suka zagayeta sannan suka haɗa baki wajen faɗin “Gobe zata fashe!!!” tare da ƙyalƙyalewa da dariya suna tafawa.
             Ƙaramin tsaki wadda ke zaune can gefen mirror tana kwalliya taja tare da taɓe baki, taɗan hararesu idanunta cike da ƙwalla, cike da fushi ta ajiye hodar da take shafawa ta fice daga ɗakin.
Bama susan tanayiba, dan sukam hankalinsu nakan amarya suna cigaba da mata ihun “Gobe zata fashe!! Gobe zata fashe!!!”. Faɗi suke da ihu sosai suna dariyar tsokana irinta ƙawen da ƙuruciya ke ɗawainiya da su, dan gaba ɗaya yarane ƙanana da bazasu wuce 16-17 ba.
Hawayen da tun ɗazun take haɗiyewa ne suka silalo saman kumatunta a hankali. Bata motsaba, kamar yanda bata buɗe ido ta kalli ƙawayen nata dake mata shaƙiyancin ba. Ita kaɗai tasan mi takeji a ranta tun daren jiya. Tabbas wannan ranace data daɗe tana fatan zuwanta itada masoyinta Yah Abdallah tun bata gama sanin ciwon kanta ba. Sai dai batasan miyasa tunda aka shiga satin bikin jikinta yay sanyi ba kuma. Tasan hakan bazai wuce nasaba da sabuwar rayuwar da zata wayi gari a cikinta gobe idan ALLAH ya kaimu ba. Ta sake matso hawayen masu zafi tana jan ajiyar zuciyar da har jijiyoyin wuyanta saida suka miƙe...........
           “Ya salam! Yaran nan lafiyarku kuwa!!?”. Akafa faɗa a bayansu da ƴar kakkausar murya. Tsitt ɗakin yayi, duk suka juya suna kallon mai maganar. Ta sake tafa hannayenta tana riƙe haɓa. “Oh ku ɗin nan, yanzu nan bama ku sakata ta shiryaba kuka zauna shiriritar da kukafi ƙwarewa akai?”.
         “Afuwan Addah”. Ɗaya ta faɗa tana ɗan sosa bayan wuya na alamun jin kunya. Girgiza kai Addah tayi tana ƙarasowa gaban gadon, “To naji, ku fita ku bani waje na kimtsata”. Ɗai-ɗai suka ringa fita suna ƙananun ƙunƙunai na alamar ba haka sukaso ba, amma sanin yau Addah babu fuskar wasa tattare da ita yasa babu wanda ya iya cewa komai. Ita dai bata kulasuba, dan yau babu ƴan wasan a kanta. Kamo ƙyaƙyƙyawar budurwar tayi ta zaunar tana faɗin, “Tashi kinji dear, kukan ya isa haka, kefa amaryace, amaryarma mai tsada ga ƙyaƙyƙyawan miji irin Abdallah. Ko bakison auren a fasa ne?”.
       Baki budurwar ta tura gaba tana sake matso hawayenta, sai kuma ta faɗa jikin Addah ta sake fashewa da kuka. Karan farko Addah tai dariya tana shafa bayanta. Tace, “Oh Rabbi, yau ga Nu'aymah shugabar tsiwar gidanmu tayi laushi darajar aure”. Ita dai sakema ƙarfin kukanta tai tana narkewa jikin Addah. Sunja kusan mintuna huɗu a haka kafin Addah ta ɗagota tana sake faɗaɗa fuskarta da murmushi, zaunar da ita tai sosai ta kama bakin mayafinta ta share mata hawayen fuskarta tas duk da wasu na silalowa kaɗan-kaɗan.
         “Haba Nu'aymah'n Abbah kukan ya isa haka mana, ko an miki wani abune?”. Kanta ta girgiza tana sauke ajiyar zuciya a jajajjere. “To wani waje ke miki ciwo ne?”. Nanma ta girgiza mata kai. “Ikon ALLAH, to minene ya sakaki kuka irin haka? Keda zakiyi auren soyayya Nu'aymah?. Ki duba kowa a family ɗin nan cikin tsantsar farin ciki yake da auren nan naku, dangi ta ko ina sun iso gobe idan ALLAH ya kaimu kawai ake jira. Umm. Hajjo, su Abbanki damu baki ɗaya kowa yana cike da farin cikin wannan alkairi. Ɗazun nan mukai waya da Angon shima jirgin ƙarfe uku zasu biyo daga Abuja, yanzu hakama sun taso inaga shi da abokansa. Ai nazata yau ranar farin cikice a gareki mara misaltuwama Nu'aymah. Uhhmm?”.
      Hannu tasa ta share hawayenta, cikin rawar murya tace, “Addah wlhy inajin tsoro ne?”. Da mamaki Addah tace, “Tsoro kuma Nu'aymah? To tsoro akan mi Uhhmm?. Ko wani abune ya faru dake bamu saniba?”. Nanma kanta ta girgiza mata tana haɗiyar zuciya dajan numfashi.
       Addah ta sauke nishi tana girgiza kai, hannu ta ɗaura kan haɓarta ta ɗago fuskarta. “Kalleni Nu'aymah”. A hankali ta ɗago manyan idanunta da launinsu ya koma Jaa, gashi sun kumburo saboda kukan data sha ta saukesu akan Addah”. “Kukan ya isa haka kinji daughter, kicire komai a ranki babu abinda zai faru sai alkairi, duk wani tsoro da kikeji ki ciresa a zuciyarki, kiyi farinciki dan gobe ranarki ce idan ALLAH ya kaimu, fatanmu ALLAH ya sanya albarka a al'amarin ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, ALLAH yasa wannan haɗi ya zamewa family ɗinmu alkairi duniya da lahira”.
         A zuciyarta ta amsa da amin, a zahiri kuwa sai tai ƙasa da idanunta alamar jin nauyin ta. Lura da hakan yasa Addah yin murmushi da lakace dogon hacinta. Tace, “Yauwa tagaban goshin Hajjo tashi ki shirya gashi can har an fara walima babu amarya”.
     Ɗan murmushin yaƙe kawai tayi da miƙewa bisa umarnin Addah. Dama tayi wanka tuni, dan haka ta sake wanko fuskarta yanzu kawai ta dawo inda Addah ke jiranta. Ƴar kwalliya taimata da bazata takurataba, kafin ta sata ta shirya cikin atanfa zani da riga pitch da ratsin Maroon. Ɗinkin yay mata ɗagwas ajiki kasancewarta mai murzajjen jiki, dan sam Nu'aymah ba siririya bace, badai za'a kirata mai ƙiba ba, amma jikinta a mulmule yake babu alamar rama sam duk da kasancewarta yarinya ƙarama sosai. Baƙar riga mai zubin alƙyabba da tasha ado da pitch zare aka bisa da stones ta saka mata, da ɗan turare kaɗan, ta bata flat takalmi baƙi ta saka wanda yayma farar ƙafarta data sha ƙunshi jaa da baƙi ɗas. “Masha ALLAH amaryan ɗana Abdallah” Addah ta faɗa tana mata alamar tayi ƙyau👌🏼 da hannu. Ɗan murmushi tayi da maida kanta ƙasa na alamar jin kunya.
Yarinyar ɗazun dake jikin Window a laɓe tana kallonsu ta share hawayen da take faman yi tun ɗazun, duka maganar Addah da Nu'aymah akan kunnenta da idonta suka faru, ta taune leɓenta da ƙarfi tamkar zata hudashi tana ƙoƙarin danne kukan dake neman kufce mata da ƙarfi...
      Babu ɓata lokaci Addah ta taimaka ma Nu'aymah suka fito harabar gidan, inda sukaci karo da wasu tsoffin mata su kusan biyar. Da ɗan faɗa farar ciki ta watsa musu harara tana faɗin, “Wai mi kuke da amaryar a cikin gida da har yanzun an gaza kaita wajen walima Fauza?”. Cike da girmamawa Addah tace, “Ayi haƙuri Hajjo, mun tsaya shirine shiyyasa”.
         “To wane shiri kuma nikam kamar wadda za'a kai ɗakin miji yau, kinga taho Zainabu”. Tai maganar da kama hannun amarya Nu'aymah. Babu musu Addah ta sakar mata ita tana murmushi da binsu da kallo har sai da suka isa gab da gate sannan ta sauke ajiyar zuciya. Yunƙurawa tai zata bi bayansu itama.........
Caraf aka riƙe hannunta. Juyawa tai da sauri, sai dai ganin wadda ta riƙotan yasa taƙi cewa uffan. Kallon gefe da gefe tai, ganin mutane nata ɗan kai kawo yasa ta sake tsuke fuska tana kallonta.......
“A'ah! Adawiya lafiya kuwa? Fauza mi akai mata haka?”. Firgigit Addah tai da ture hannun Adawiya daga kan nata tana harararta, sai kuma ta kalli mai maganar fuska a narke. “Umm bar wannan ƴar taki kinji, bansan mike damun kansuba daga ita har Nu'aymah, canfa na iskesu sun haɗe kai a ɗaki sunata dirzar kuka ko shiryawa basuyi ba, ni wannan shaƙuwa tasu har tsoro take bani wlhy, gashi kuma mai rabawa yazo....” ta ƙare maganar da sharce hawaye tana kallon Adawiya dake jikin Umm tana kuka tamkar ranta zai fita.
Murmushi ƙyaƙyƙyawar matar mai tsananin kamanni da Amarya Nu'aymah tayi, ta sake rungume Adawiya a jikinta tana ƙoƙarin haɗiye nata hawayen da suka ciko mata idanu. “Ya isa kukan haka Daughter, kiyi haƙuri, namiki alƙawarin insha ALLAH duk yanda zanyi sai nayi dan kibi ƴar uwarki sai kuje can kuyi karatunku tare kamar yanda kuka fara a tare kafin ALLAH ya baki naki mijin kema musha biki”.
Maimakon Adawiya tai murna sai ta sake fashewa da kuka tana ƙanƙame Umm.
“Oh ALLAH, ya isa haka mana daughter, ko sokike muma ki sakamu kukan ne uhhhmm?”. Ɗagowa Adawiya tai zatai magana Addah tai saurin tarar numfashinta tana harararta ta ƙasan ido, “Faɗa mata dai Umm, tundama ance mata ga mafita an samu ba sai tai haƙuriba, nifa banason shashanci kuma, a haka zaki bama Nu'aymah ƙarfin gwiwar yin farin ciki? Haba mana, k........”
“A'a Addah ya isa haka mana, a barta taji da abinda ya dameta dan ALLAH, ɗiyata muje ki shirya kinji, tarema zamu fita wajen walimar da anyi sallar la'asar”. Ɗan satar kallon Addah Adawiya tayi, ganin harar data watso mata ƙasa-ƙasa ya sakata saurin ɗagama Umm kai alamar to. Kamata Umm tai suka bar Addah a wajen, tabisu da kallo ƙasa-ƙasa tana ɗan murmushin jin daɗi......
“Uhhm Fauza! Dama ke naketa nema ashe kina anan”. Wata mata dake tunkarita ta faɗa. Juyawa tai da sauri ta kalli matar, sai kuma ta saki murmushi da faɗin, “Oh! Ya salam Yaya, wlhy namafa manta na barki kina jirana a kitchen, rigimar ƴaƴanki ta ɗaukemin hankali”. Ƴar dariya sukai a tare, tare da barin wajen suna cigaba da maganarsu.

A waje kam dai har yanzu ba'a kai ga fara gudanar da komaiba, sai dai wata ɗaliba a cikin ƴammatan da zatai sa'anni da amaryace ke karatu cikin zazzaƙar muryarta, wanda hakan yasaka wajen yin tsitt ana saurarenta.
Wasu zafafan motocine guda biyar suka shigo cikin layin, duk da mutane hakan bai hanasu kutso kaiba kansu tsaye jikin ƙofar babban gate ɗin harabar massallaci. a take mafi yawan mutanen dake a wajen walimar hankalinsu ya koma ga kallon motocin da sukai parking a jere abin birgewa. Kowa ya zuba ido yaga su wanene zasu fito a ciki?....
Ni kaina sai da na sauke numfashi da faɗin Masha ALLAH, saboda fitowar wasu samari masu ji da lokaci da gayu daga motar, da gani babu tambaya waɗanan abokan angone dama angon kansa, bankai ga cankar angonba wani mafi ƙyawun haiba da tsarin kwalliya a cikinsu ya fito a motar tsakkiya waya manne da kunnensa yana murmushi. Sanye yake cikin ɗanyar shadda Maroon color sai maiƙo take da ɗaukar idanu. Ya saki lallausan murmushi yana gyaɗa kansa alamar amsa mai maganar daga can, sai kuma ya sauke wayar ya tura aljihu dabin abokansa dake tsaitsaye suna kallon ƴan taron walimar da suma mafi yawansu su suke kallosu da kallo. Kafin yace wani abu ɗaya daga cikinsu ya juyo yana faɗin, “Woow Ab harfa na canko amaryarka”. Ɗan hararsa yayi da ɗauke kai kamar bazaice komaiba, sai kuma ya sake kallonsa yana wani furzar da numfashi. “Malamai dalla kallon ya isa haka, ku bakwa ganin su Baba Malam duk mu suke kallo suma”. A tare duk suka juyo da kallonsu garesa suna dariya, wanda yay magana ɗazunne ya sake faɗin, “Hahh! Go gefe malam, kai dai faɗa mana kishi kakeyi dan ance anga Angel ɗinka”. “Shashasha, to idan nayi kishin laifine?”. Abdallah ya faɗa yana ratsa tsakkiyarsu yay gaba.
Cike da shaƙiyanci sukabi bayansa suna dariya ƙasa-ƙasa da faɗin, “Shege uban zumuɗi, anya kuwa zaka cika alƙawarin da kaima su Baba Malam na barin ƙwailarnan taka tai karatu? Karfa muji nanda wata tara ana nemanmu a labour room”. Duk da yana jinsu sarai bai...


Read / Download SARAN BOYE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On SARAN BOYE
avatar
maryam-8-1

5 months ago

Reply

Amazing book

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album