Join Our WhatsApp Group

SILAR SOYAYYA Complete Hausa Novel Document by SILAR SOYAYYA


SILAR SOYAYYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14303



SILAR SOYAYYA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 29, Dec 2023

Author: Rabe'ah Shuaib Na baba ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09037093702

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 85.76 kb

File Type: txt

Views: 592+

Download: 169+

Last download: 1 day ago

Description/Story: [6:08pm, 6/14/2017] Bebe'arth(yar gatan hudah: 💦💧💦💧SILAR
SOYAYYA💦💧💦💧
(Labarine Wanda yakunshi SOYAYYA ,tausayi,fadakarwa ,nishadantarwa )

®Adabiancy
💬©O.H.W

Dedicated to RSN novels


Ina,mika godiyata ga ubangiji ,domin babu abin godiya saishi ,Shi yanufeni da fara littafinnan ,Allah kma yasa na kammalashi lafiya ,

Allah karabamu da sharrin masu sharri aduk inda suke,


Dimbin gaisuwa ga masoyana ,ina kaunarku aduk inda kuke,da masu karanta novels Dina dama wayanda basa karantawa Adabiancy na Kaunarku😘


1-2


*GIDAN FARARE*
shine asalin sunan da ake kiran wannan gida,
Kafatanin yan gidan ba baki ko daya,dukkaninsu fararene tas ,

Alhaji bukar shine asalin mai gidan ,bafulatinin mutum ,kyakkkyawan gaske ,Allah yaimai tarin dukiya mai yawa,matarshi daya hajiya bilkisu ,balarabiyace itakuma ,kyawunta ma baxai faduba ,
suna da Ya"Ya biyar duka maxa ,
Hassan Hussain. Nura ,shamsu Abdallah ,
sun taso kawunansu a hade ,suna matukar Kaunar juna ,dukkaninsu kyawawane babu baya cikinsu ,fararene kar ,
Yayin dasuka isa aure ,iyayansu suka turasu danginsu suxabo mataye acan,dama al'adarsu knn auren xumunci ,
Alhaji bukar yagina gida katoton gaske ,akashatarwa kowa akaimasa gini mai kyawun gaske ,
gidaje shida akayi acikin wannan gida ,gidan yatsaru matuka gaya,

duk Wanda yai aure cikin wannan gida yake tarewa ,tafi2 har dukkaninsu sukai aure , da binta
Hassan Aisha
Nura hafsa
Shamsu Hauwa
Abdallah Rabi'ah
Matayen dasuka aura kenan ,dukkaninsu yan dangine ba bare ,kma dukkaninsu fararene tas,
Alhaji bukar ma yatare acikin wannan gida ,gida ya hadu yaxama family guda


Tafi 2dukkaninsu suka tara iyali ,
Hussain yana da Ya"Ya 4
Hasanma 4
Nura 3
Shukurah,safiyya sai autanshi MIQDAD yaro mai farin jini takensa kenan, agida ko a makaranta ,
Tun yana yaro yake da farin jini har kawo samar takarsa
Kyakkyawane ajin karshe ,dan gayune ,yahadun mutuminnan ,hatta tafiyarshi abar kalloce ,
shamsu shikuma yayanshi uku duk Mata ,
nabila ,Fatima ,MUJIBAH,
kyakkyawace ta karshe ,kyawunta irin mai fisgar hankaline ,yarinyar tanaji da gayu ,

Abdallah ,yayanshi biyu shikuma ,
Ahamad Aysha ,

sai matar shamsu ta biyu da yayi mai suna khadija itama bafilatanace ,Amma ansha gwagwarmaya kan ya aureta ,sbda ksancewarta ba yar dangiba ,
Yayanta biyu
Mubina, MUWADDAH,

dukkanin wannan family fararene kar ,shiyasa akewa gidan take da
*gidan farare*
Amma MUWADDAH ta kasance .....





sakon gaisuwa ga kawata xaharatee luv u😘





Adabiancy😘
[6:08pm, 6/14/2017] Bebe'arth(yar gatan hudah: 💦💧💦💧SILAR💦💧💦💧SOYAYYA



(2017)

®Adabiancy
©O.H.W


Dedicated to Rsn novels


3-4

MUWADDAH takasance bakace ita ,Amma bakinta mai kyaune ,
irinsu ake kira chaculate colour ,kyakkyawace dai2 gwargwado ,

duk cikin jikokin alhaji bukar ,yafi qaunar MUWADDAH ,akodayaushe tana gurinsa ,musamman in amminsu nagun Aiki ,dayake barrister ce ,
Wannan Kauna da alhaji bukar ke nunawa MUWADDAH Shi yakara janyo tsanarta a family ,

suna ganin duk cikinsu itace bakar fata ,Amma duk dahaka alhj bukar yafi nuna Mata so ,
Yadda yake nuna Mata so ,kamar Shi yahaifeta ,
Makaranta dakanshi yakaita ,komai nata alhj bukarne ke biyanshi ,dahaka har saida MUWADDAH tadawo gurinshi da xama ,
Ada ahalin gidan farare naxiga hjy bilkisu ,har tafara tsangwamar MUWADDAH bashiri alhj bukar yaimata Jan Ido ,nan da nan taxub da mukaman yakinta tarungumi MUWADDAH ,ta taya alhj bukar kaunarta ,

MUWADDAH tunda ta taso akwaita da san shigar yan filani ,
Kuma intai shigar ba karamin kyau take mataba ,sai tafito a bakar bafilatanarta sak ,

Tare suka taso da MUJIBAH kansu daya ,dama sa'annine,
MUJIBAH na kaunar MUWADDAH ,Yayin da mahaifiyar MUJIBAH bata kaunar MUWADDAH da mahaifiyarta ,tana matukar kishi da ita ,itakwa ammin su mu MUWADDAH xuciya daya take xaune daita ,ita bata ma gabanta aikinta kawai tasa gaba ,duk da tasan irin kisan mimmiken datake Mata gurin abbansu MUWADDAH ,duk sai tahadasu ta watsar tamai da hankalinta kan aikinta ,


Takwana da sanin duk matan gidan haushinta sukeji ,saboda anfi kaunar yarta ,sunbi duk sun hade Mata kai ,barema kishiyarta mamin su MUJIBAH da momyn su MIQDAD,suna matukar yimata hassada ,Amma gabadaya sai taja lamarinsu ta ajiye gefe ,


Wannan Abu da ake baishawa MUJIBAH da MUWADDAH kaiba ,
suna matukar kaunar junansu kai kace ciki daya suka fito ,ganin haka yasa alhj bukar Maida MUJIBAH makarantar da MUWADDAH takeyi ,duk makarantunsu daya kuma ajujuwansu daya ,ahaka suka tashi har sukai candy ,
sukai sauka duk tare ,yanxu suna xaune agida sai islamiya dasuke xuwa ,alhj bukar yace duk mesan cigaba tabari sai tai aure in mijinta naso tayi ,haka yaiwa yayyansuma kafin su ,
Mubina ma yayar MUWADDAH nanan ya hanata cigaba ,
Anwar ne dan gidan auncl Hussain kesanta ,yace
"yabarta tafara Amma fur yaki yace in anyi auran tayi karatun ,

Wannan kenan
Kudai kuci gaba da bina cikin nishadi



*****

MIQDAD yana matukar shiri da MUJIBAH Amma basa shiri da MUWADDAH ko kadan ,yarasa sbda me Shi kawai haushin yarinyar yakeji ,
itakuma MUWADDAH tana so suyi shiri dashi kmar Yadda suke da MUJIBAH ,Amma baya sakar Mata fuska ko kadan ,asalima inyagansu tare baiwa MUJIBAH magana ,

gashi ita akodayaushe tanaso sukasance tare ,xuciyarta na kwadaita Mata kyawunshi ,
Kyawunshi yana fusgarta ,burinta akodayaushe tadinga ganin kyakkyawar fuskarshi ,
in suna tare da MUJIBAH saidai ta buya tadinga lekenshi
Tun batasan me hakan ke nufiba ,har tagano takamu da masifar son MIQDAD ,Wanda ko muryarshi taji ,sai taji kirjinta yabuga ,
ba karamin tsurewa taiba ,data gano ,inda xuciyarta kesan kaita ,tafara lallashin kanta ,domin tasan ko da kudi MIQDAD baxai auretaba , yake da hadaddun yan mata ,domin har gida suke biyoshi ,dan haka mai xaici daita yana ganin jajayan fata kalarsa ,
ga MUJIBAH ma hakan take ,domin tajita tsundum cikin kaunar MIQDAD ,Wanda hartakasa barinshi cikin xuciyarta tagayawa MUWADDAH ,
Aranar MUWADDAH tashiga tashin hankali sosai ,kuka tadinga yi wiwi ,tasan tarasa MIQDAD har abada ,yana ganin MUJIBAH mai xaiyi daita ,

To ga MIQDAD ma hakanne ,xuciyarshi tayi male2 cikin kaunar MUJIBAH ,
Kyahunta na rudarshi ,domin kyawunta yana fisgar Shi ,duk da yana da yan matan dasuka takata akyawu ,Amma baiji san ko daya cikinsuba sai MUJIBAH ,itakadai yakeso ,
Amma har yanxu bai sanar mataba ,

Akwai wata MUBARAKA cikin yan matanshi da ta nace masa ,
Tana matukar kaunarshi ,Amma Shi burinshi ya yakiceta ,Amma taki yakicuwa ,ta like mai kamar cingum,





*****

Wannan satin aka Shiga hada hadar bikin Mubina da Anwar ,
MUJIBAH da MUWADDAH ba xama ,kullum yinan yican suke ,
Suna ta shiri ,sosai ,
hakama Ammi shiri take ba na wasaba ,domin wannan karan ne farko fara aurar da yarta da xatai ,

Gidan farare yacika taf da yan uwa ,aka fara bidirin biki.





Adabiancy😘
[6:08pm, 6/14/2017] Bebe'arth(yar gatan hudah: 💦💧💦💧SILAR 💦💧💦💧SOYAYYA


(2017)


®O.H.W
©R.S.N


5-6

*fulani day*

yau ranar ta yan filloce ,
ka'fatanin Wanda ke gurin duk yan fillone ,kma dukkaninsu sunyi shigar filani ,

Amarya da ango ma shigar filani sukai ,sunyi matukar kyahu ,

can nahango MUJIBAH da MUWADDAH sunyi kyau suma sosai ,
suna ta xuba hotuna ,
MUWADDAH ta tatsaya jikin mota ,da korya a hannunta ,aka kyasa Mata ,
ba karamin kyau taiba ,haka dai sukaita daukar juna ,
Kamshin turaransane yafa'ra xiyartar hancinta ,
ta'riga da ta haddace kamshinsa ,domin tana matukar san ta shaki kamshinshi ,akodayushe burin hancinta yashaki kamshin MIQDAD ,

Kanta tadaga tana bin gun dayake tahowa da kallo ,
ba dan karamin kyau MIQDAD yaxubaba,
Sakin ba'ki kawai tai tana binshi da kallo ,

Murmushi yake saki mai tsima xuciya ,
A tunaninta ita yakewa ,
itama sai tasakar mai murmushi tana kallanshi ,har yakaraso daf daita ,kawai sai taga yashigeta ,baki bude tabishi da kallo ,

Ya'isa ga MUJIBAH da ke tsaye tana sakar mai murmushi ,
Ya danyi murmushi mai sauti ya ka'ma Han.unta yadan murxa ka'na yafurta I love u

. Kalmar da tadade tana jira yafurta Mata ,sai gashi ba xato ba tsammani yau yafirta Mata ita ,
Aikwa batai wata2 ba tace masa me too ,
yasa hannu ya la'kace Mata hanci ,suka saki dariya atare ,


MUWADDAH datai suman tsaye a gurin ,ji take kafafuwanta sunyi nauyi ,sun kasa daukarta ,
ga wani Abu da yataho ya tokare Mata kirji ,
gashi kanta sai juwa yake ,
Idanuwanta yacika taf da hawaye yana kokarin xubowa ,


MIQDAD yacewa MUJIBAH mukarasa ciki mana ,tajuya gurin da MUWADDAH take ,tace :
" MUWADDAH Kixo mushiga ciki" ,

Murmushin yake tai ,tadaga Mata kai ,
tana daga kafarta xa'ta motsa ta fa'Di sai ji kake tim ,

A hargitse MUJIBAH tayo gurin da take tana jijjiga'ta , Amma ina ta sume
Kuka MUJIBAH take tana girgixa'ta

Shi kwa MIQDAD ya rasa ma me xaiyi
dai2 nan Amminsu ta fito kenan ,da hanxari taka'rasa gun dasuke ,
ganin MUWADDAH a kwance , nan ta'ke hankalinta yatashi ,
tana tambayar me ya sameta ,
nima wlh Ammi ban saniba kawai ganinai ta fa'di ,MUJIBAH ta ba'ta Amsa ,

Ammi tace tashiga ciki ta daukko Mata ruwa,
da gudu taje tadaukko ta ka'wo aka yayyafa mata ,

Tana far fadowa ta fashe da kuka ,
Ammi ta rungumo ta jikinta tana tambayarta mai ya'faru ,
bata ba'ta amsa'ba taci gaba da kukanta ,har sai da taga ran Ammi ya fa'ra ba'ci sannnan ta tsaigaita kukanta ,
tace :
"Ammi kawai jinai kaina yana juya'wa ,jiri na diba'na ,shine nafadi ,

sannu Ammi taimata ,sannan ta ka'Mata ta mike ,
MUJIBAH nai Mata sannu Amma ko tajuya ta kalleta ,saima ciki2. da ta amsa ,jitai kwata2 ba'ta'san kallanta wani irin haushinta takeji ,



Ammi ni gida xan koma kaina ciwo yake ,
to xa'ki iya karasa'wa ke kadai ko MUJIBAH ta rakaki?
Ammi ta tambayeta ,

ta turo ba'ki a'a xan iya ka'tasawa Ammi ,kuje kawai ,Ammi tace to shikenan ,in Kunje kisha magani kan nada'wo Allah ya sawake ,
tace Ameen ,tajuya ta tafi ,


tana xuwa daki gado ta fa'da taci gaba da risgar kuka kan kice meye wannan xaxxabi ya rufeta ruf ,
tana ta karkarwa hakoranta suna haduwa da juna ,
Ahaka suka dawo suka tadda ita ,

MIQDAD ne ya duba'ta ,(likitane a shekar karshe yake da xai xama cikakken doctor)

ya kalleta ,yace : ke me ke da'mun ki ?
can kasan makoshi ta furta *SOYAYYA*
Yace :
"me kikace?" tace "ba komai nace "

karya kike bayan binciken danai ya nunan harda damuwa ke damunki ,me ya jaho hakan ,?
cikin ranta ta furta *SILAR SOYAYYA*
Kmar tai kuka tace:" ba komai ni ba abinda ke damuna "ta turo baki ,
tsaki yai
Ya rubuta Mata ma'gun guna ,


A haka aka karashe wannan biki MUWADDAH ba lafiya cikakkiya ,sai da tai sati ,sannan tai garau daita kamar bataiba
Soyayyar MUJIBAH da MIQDAD sai bunkasa take ,tun a family ba'a saniba har taxo da kowa ya sani ,an tsai da ranar bikima ,yana kammala karatunshi ,kannan MUWADDAH ma ta tsayar ,



MUWADDAH kwa kullum tamkar ka'ra Mata kaunar MIQDAD ake
Xaxxafar kauna take masa ,
soyyyyace xallah wacce babu digon algus aciki ko kadan ,
Idanuwanta sun Riga da sun Saba da kuka *SILAR SOYAYYAR* MIQDAD ,

ga wani xa'fi da kirjinta ke Mata ,
samun saidarta tai idanuwa hudu da MIQDAD shine kwanciyar hankalinta ,

duk ranar da kaga MUWADDAH cikin farin ciki da nishadi ,to sunyi Ido hudu da MIQDAD,
Abinci MUWADDAH bata iya xama taci miki sai ta'ga MIQDAD,
soyayyar MIQDAD na neman xautar da MUWADDAH ,

duk bidirin da take ,ba Wanda ya rafko jirginta ,sbda ta iya takunta ,
bata fatan kowa yasani ,domin idan xancan yaje kunnan alhj bukar ,MIQDAD ko yana so ko ba'ya so dole ya aureta ,

itakuma bata fatan haka yakasance ,shiyasa tabarwa kanta sirri ,daga ita sai xuciyarta ,

Lokacin da aka sanya lokacin bikin MUJIBAH da MIQDAD kwanciyarta asibiti biyu ,dakyar aka shawo kanta ,tun lokacin take fa'ma da matsanancin ciwon kirji ,duk dan *SILAR SOYAYYA*




Ko da la'bari yajewa muba'raka nasa ranar MIQDAD hankalinta inyai dubu ya tashi matuka ,

da tasamu MIQDAD da xancan sai cewa yai aishi da'ma bai amsa mata soyaytarta ba ,itace dai take haukanta ,








Adabiancy😘
[6:08pm, 6/14/2017] Bebe'arth(yar gatan hudah: 💦💧💦💧SILAR💦💧💦💧SOYAYYA


(2017)

®Adabiancy
©O.H.W


Dedicated to R.S.N. novels😘


7 -10

_À kace Ra'n'a ba'ta karya saidai uwar diya taji kunya ,_

_to dai a wannan satin aka shiga hidimar bikin MUJIBAH da MIQDAD , har lokacin soyayyar MIQDAD n'a nan cikin xuciyar MUWADDAH ,duk da ta'riga da ta fudda ran sa'mun MIQDAD ,Amma kullum ka'mar ka'ra Mata kaunarshi ake ,_

dauriya take kawai ,ake hidimar daita ,sbda itace aminiyar MUJIBAH kuma yar uwarta ,MUJIBAH ta wuce komai à gurinta ,sbda tana kaunarta ,ba'ta daka ta maminsu da sauran yan uwanta ,ba'ta yan ubanci dasu ,shiyasa itama take kaunar MUJIBAH ,

À Ranar da akai dinner ,byan Sun da'wo gida xaxxabi mai xa'fi ya rufe MUWADDAH ,MUJIBAH n'a gefenta tana tai mata sannu ,
çan dai kirjinta ya faraimata ciwo ,kamar ansa blo an tokare mata shi ,numfashi take sama2
MUJIBAH da ta Ankara da ita ,hankalinta ya tashi ,ta danna numb MIQDAD tana kuka ta sanar dashi ,

yana xuwa daukarta yai kawai ya nufi asibiti da ita ,
À gidan ba wanda ya sani ,har saida aka gama du'bata ,aka ba'ta kwanciya ,sbda tunda ta sume har lokacin bata farfadoba ,

Wa'ya yai gida ya sanar dasu ,
Aikwa à daren Ammi da hajiya bilkisu suka taho ,
Alhj bukarma ya biyo ba'yansu hankali ta'she ,
haka sukai jigum 2 har misalin 12:00pm MUWADDAH bata far fado ba ,MIQDAD ne ya lallami alhj bukar da kyar ya tafi gida ,Amma yace hajiya bilkisu ta xauna ,

sai misalin 01:00pm MUWADDAH ta farka lokacin MIQDAD ya shigo dubata ,
ido hudu...


Read / Download SILAR SOYAYYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album