Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa }~~~~~~{
Page 1
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
................................
Babi Na Dya.
Tana zaune akan katifarta ita kadai a cikin dan qaramin dakinta. Ta dade a haka tun kusan kimanin awa daya tana kallon kundin adana hotunanta (album) Wanda ta riqe shi da hannu biyu kamar littafin karatu.
.
Duk da yake ta rufe qofar dakin nata, hakan bai hanata ganin hotunan ba, ta hanyar hasken qwan wutar dake a goshin dakin. wutar babu qarfi, wani lkcn sai ayi kamar za a dauke, xuwa can Kuma sai ta tsaya. Bata yi mamakin hakan ba, don kuwa ruwa ake ta sheqawa a lkcn kamar da bakin qwarya, ga kuma iska da walqiya. Don haka za a iya dauke wutar a Kowanne lkc bayan ynx.
.
Duk lkcn da aka ce ana ruwa, in dai wannan budurwa tana a gida, Sau da yawa babu abin da ta fi sha'awa irin ta dauko hotunan ta na da, da na ynx, ta riqa kallon su tana tuno abubuwan da suka gabata a rayuwarta.
.
A haka zata wuni a cikin dakin nata, har xuwa lkcn da za a dauke ruwan, idan ta gaji sai ta fito waje ta sha iska, ko Kuma ta je dakin mahaifiyarta su yi hira.
.
Sa6anin Sauran ranakun da irin haka ya sha faruwa da ita, yau ruwan ya sauko ne a daidai lkcn da take shirin xuwa asibiti inda take aiki. Ynx aikin rana take yi, da qarfe sha biyu saura kwata take fita ta isa asibitin da qarfe sha-biyu daidai. Daga nan ba zata dawo ba sai kuma qarfe bakwai na yamma.
.
Gashi yau ruwan ya tsareta, har ta ci kusan awa daya a gida tana jira a dauke, don haka tana dai kallon hotunan ne don kada ta rasa abin da zata yi a dakin nata, amma ba don tana so ba."
.
Sannu a hankali ta ci gaba da bude shafukan hotunan tana cin karo da hotunanta, wadanda ta dauka ita da qawayenta tun a shekarun baya da suka shude. Ta na da qoqarin adana hoto, da wahala ta dauki hoto ta bari ya salwanta. Da haka take tunawa da yawancin qawayenta wadanda suka yi karatu tare, tun a sikandire... Tun Suna aji daya wadanda wasu da yawa a cikin su ynx ita kanta bata san a inda suke ba a duniya. Ko a raye, ko a mace, allah kadai ya sani.
.
Yawancin hotunan ta na da sun fi dadin gani, don kuwa ta daukesu ne cike da farin ciki, Suna dafe da juna ita da qawayenta sun sanya kayan makaranta iri daya, sun dafa juna Suna dariya. Kowacce sanye da hijabi gwanin ban sha'awa.
.
A shekarun baya sa'ar da tana qarama a zahiri ta fi jin dadin rayuwa, sbd a wancan lkcn babu wani abu da yake damunta. Tana rayuwarta cikin kwanciyar hankali da farin ciki. Amma yawancin hotunan ta wadanda basu wuce shekaru uku ba, ta daukesu ne cikin damuwa Wanda kai tsaye za a iya gane hakan ta hanyar ramewar da tayi a a cikin hotunan, ynx kam ta fi zama mace sosai, amma in har za a dauko hotunan nata a hada su waje daya, da an gansu za a fahimci rayuwa ta canza, da ba ynx ba."
.
Duk da yake hotunan nata Suna debe mata kewa, a 6oye Suna tayar mata da hankali, wani lkcn ma har kuka suke sa ta a cikin dakin nata, ba tare da kowa ya sani ba." shi yasa ba kowanne hoto take so ta riqa kallo ba a kowanne lkc.
.
Hotunan da ta dauka ita da qawayenta sun fi komai debe mata kewa, don kuwa da yawa a cikin su sun yi aure, wadansu ma ynx sun haihu ya kai sau uku, ita kadai ce har ynx tana gida, har ta fara aiki, amma kama-kama auren bai kankama ba tukuna.
.
Ko ynx da ta ke zaune a dakinta tana jiran daukewar ruwan bata yarda tayi nisa a cikin album din ba, shafi uku kawai ta bude, na farko shine shafin da hotunanta suke can zamanin da take a sikandire.
.
Xuwa can kuma sai ta qara bude na gaba, a can ne tayi karo da wani hoton ta guda daya da ta ware shi shi kadai, sbd tsabar son shi da take yi. Tunda take daukar hoto a duniya bata ta6a daukar hoton da ya fito da ita ba, ya bayyana kyawawan siffofinta irin wannan ba." yawanci shi ta fi baiwa duk wani saurayi da ya dameta ta bashi hotonta, don kuwa ta sa an wanke mata wannan hoton yafi kala talatin daga bara xuwa bana, Kuma duk ta rabar dasu, saura wannan guda dayan kuma shi ne dai wanda ya rage a cikin album dinta. Kuma ta yi alqawarin babu wanda zata baiwa, indai ba wani ta sa aka wanko ba."
.
Sanye take da tsukakkiyar jar riga wacce ta kama jikinta, tun daga tsukakkiyar mararta har xuwa bisan qirjinta. Ta lanqwasa dogon wuyanta a cikin hoton tayi tagumi da hannunta daya, sannan tana sanye da baqar hular sanyi, wacce bata yi nasarar suturce yalwataccen dogon gashin kanta ba, da ya xubo har xuwa dokin wuyanta.
.
Tana sanye da farin siket wanda ya dan leqo kadan a cikin hoton, ta hanyar durqusawar da tayi ta dafa guiwarta da daya hannun tana kallon kyamara da kyawawan idanunta dake kama da qanqara. Ba murmushi take yi ba, ta tsayar da hankalinta ne waje guda, duk da haka idan ba lura mutum yayi ba, sai ya rantse murmushi take yi a cikin hoton, wannan ya samo asali ne sbd qyalqyali da le66anta suke yi, a dalilin wani rantsattsen man le6en da tayi amfani dashi sa'ar da ta dauki hoton, shekara daya da rabi kenan da ta wuce.
.
Duk lkcn da wannan kyakkyawar budurwa tazo kan wannan hoto nata, Sau da yawa ta kan 6ata lkc akan shi, tana kallo kafin ta wuce xuwa hoto na gaba. Ko a wannan karon ma ta dan dade tana kallon hoton xuwa can Kuma sai ta yi ajiyar xuciya.
.
Babu shakka ita kanta ta san cewar Allah ya yi mata baiwar kyau da cikar halitta!
.
Hoton yayi kyau, to amma ita ma fa kyakkyawa ce a zahiri, wa zai ganta ynx a haka ya ce ta kai shekara talatin a duniya? Komai yana nan bai canza ba a tattare da ita, jikinta ba rukuta bane, marke ne....! Wanda ya santa a shekaru goma da suka wuce, idan ya ganta ynx zai ga tana nan a yadda ya santa, bata canza ba."
.
A bayyane a iya cewa, wannan ya taimaka mata wajen rage surutun mutane, wadanda suke yi mata maganar aure shekara da shekaru. Jikinta baya bayyana yawan shekarunta, wadanda suka santa ne kawai, suke gane ba yarinya ba ce, amma ga baqin idanu ba Wanda zai ganta ya ce ta wuce shekara ashirin da haduwa.
.
Idan aka ce wannan budurwa bata son aure gskyr magana ba a yi mata adalci ba." tana son aure kamar yadda take son ranta. Matsalar kawai ita ce, tayi rashin sa'ar fadawa tarkon son wani saurayi dake a layinsu, wadanda shi a 6arinsa ko kusa ba ta ita yake yi ba."
.
Abin da ya daurewa mutane kai shi ne, ganin yadda saurayin yake wulaqanta kyakkyawar mace ma'aikaciya, mai aji. Koda yake ba abin mamaki bane idan aka yi la'akari da mugayen halayen saurayin. Sauran da yawa ma idan aka zo layinsu idan ba cewa kayi, Nura aljan ba, ba kasafai ake gane shi ka zo neman ba." akwai dalilan da suka sa ake kiran sa da aljan duk da yake kuwa mutum ne sak! Kamar kowa.
.
Tun yana yaro ya taso da rashin hankali, da hatsabibanci, Wanda hakan ya sa ya yiwa kratu tawaye, ko ynx a sana'arsa ta aca6a yayi qaurin suna a wajen jama'an tsaron kan titi, zai yi wahala nura aljan ya zo wucewa a dakatar dashi ya tsaya. Kuma indai zai fito aiki da safe xuwa dare, qa'ida ne yayi fada da direbobi aqalla goma akan tituna Daba-daban
.
Nura farin saurayi ne wanda yayi sa'a tabar da yake shafi'u babu qaqqautawa bata canza mashi kala ba." don farin jini kam wannan bashi da matsala, maza da mata Suna sonshi duk da mugun halinshi da zafin ransa, yana da kyau, sai dai Kuma halinsa ne baiwa zamo kyakkyawa ba."
.
Wannan kyakkyawar budurwar ta dade tana son Nura aljan, koda yake ita bata yarda aljani bane, ta sha yi masa nasiha kan ya daina yadda anan ce masa aljani, Tunda dai shi mutum ne kamar kowa. Abin da ba ta sanin ba shi ne, Nura yana son wannan Suna fiye da yadda yake sonta...idan ma yana sonta din kenan, don kuwa ita ce take bin shi a Kowanne lkc, ba shi ne yake xuwa inda take ba."
.
Wadanda abin ya dame su, sukan yi mata fada su tambayeta. Me ta gani a wajen wannan saurayi marar tarbiyya da take so shekara da shekaru? Kyakkyawar tana fadar maganganu daban-daban don ta kare kanta a wajen mutane. Idan tana jinjinawa kunyar mutum ta kan ce cikin sunkuyar da kai.
.
"ka san yana da kyau idan daga mutum cikin mawuyacin haii kayi qoqari ka jawoshi ya zama mutum sosai, ni ina sonsa ne tsakanina da Allah, Kuma ina fatan adalilina ya daina duk wadannan halayen na sa ya zama mutumin kirk, ya shiryu."
.
Idan Kuma a cikin qawayenta ne wadanda su bata jin kunyar ta fading komai a gabansu ta kan ta kan yi dariya ta ce.
.
"kai ina son Nura, Kuma ba zan ta6a daina sonsa ba." ni kawai fara'arsa da Kuma qarfinsa ne suke burgeni. Nura ya shiga raina, kawai halayensa ne suke damuna, amma Kada Kuma damu zai bar komai ya dawo (normal) in dai muna tare zan gyara shi."
.
Ita kanta da ta ke fadar haka, a can cikin xuciyata ta fi kowa sanin dalilin da yasa Nura yake saurarenta, Kuma har yake dan ganin mutuncinta, babur din da yake aca6a dashi nata ne wanda ta amshi bashin ma'aikata anan cire kudin a cikin albashinta. Duk duniya babu Wanda ya san wannan zancen, ko mahaifiyarta da suke kwana tare bata ya
.
.
Lp=2}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa }~~~~~~{
Page 2
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Babu wanda ya san wannan zancen, ko mahaifiyarta da suke kwana tare bata yarda ta sani ba, don gudun kada ta sha zagi, ta gargadi nura tun a lkcn idan an tambayeshi ya ce, wani abokinsa ya sai masa ya bashi ya riqa kai masa balas, kada ya ce nata ne don gudun surutun mutane.
.
Nura bai ta6a kawo mata balas ba, wani lkcn ma idan mashin din ya lalace bashi da kudin gyara, ita take bashi kudin ya je a gyara, ya ci gaba da aikin, kada dai ya riqa zaman banza kamar yadda take yawan gargadinsa idan ta ciro kudi zata bashi.
.
abin da yafi komai faranta mata rai shi ne, duk lkcn da zata je wajen aiki, nura yake xuwa ya dauke ta ya kaita har asibiti idan kuma ta gama aikinta, sai ta yi masa waya ta ce ya zo ya dauke ta ya mayar da ita gida. Don haka ya sa kawai ta mallaka masa babur din kyauta, domin kuwa in banda haka, ita kanta ta san bata da martabar da nura zai zo ya dauketa ya kaita wajen aiki, ya Kuma je ya daukota ya dawo da ita Kullum
.
To kowa dai da abin da yake fada a game da halin wannan kyakkyawar mace da Kuma wannan dan tawayen masoyi nata da suke a layi daya. Wasu Suna ganin ai ba wani abu bane don ta nace shi take so, tunda dai tare aka taso ga gida ga gida, wa ya sani ma ko irin shaquwar nan ce tun Suna yara? Shi dama so ai haka yake.
.
Wasu kuma suna ganin duk wannan ba hujja bace.
.
Kawai dai yarinya bata da masu fada ma ta gsky shi yasa take abin da ta ga dama. Shi kadai ne saurayi? Kawai idan aka ce mace 'yar mace ce, sai dai haquri."
.
Mahaifinta ya rasu tun tana qarama, kuma mahaifiyarta bata yarda ta rabu da 'yarta ba, ita kadai ta rage mata a raye, da mahaifiyarta ta dan yi aure-aurenta ta gaji, sai ta dawo ta rungumi 'yarta suka gyara gidan su na gado da mahaifin yarinyar ya rasu ya bar masu. Gidan qasa ne, Kuma bai samu wani gyara na azo a gani ba." a qalla dai yafi ace Suna tsugunne a wajen 'yan uwa.
.
Ta wani 6angaren yarinyar tana qoqari, don kuwa ba nura kadai yake qarar mata da albashinta ba, rashin lfyr mahaifiyarta Wanda ke tasowa akai-akai na ciwon suga da kuma sukurkutaccen gidan nasu dake buqatar gyara duka Suna taka rawar gani wajen lashe dan albashin nata. Shi yasa har ynx ta kasa ajiye komai, Suna dai ci su sha kullum, Kuma duk wata sai ta dinka sabbin kaya, Suna cikin rufin asiri daidai gwargwado, matsalolinta dai biyu ne xuwa uku, gskyr mutane ne, tabbas bata da masu yi mata fada ta ji, mahaifiyarta ta kanta take yi, bata cika damuwa da sha'anin 'yar tata ba."
.
babbar matsala ta biyu kuma, soyayyar nura Wanda ko kusa shi ba zancen aure ne a gabansa ba." idan ma tayi masa maganar auren, ko fara'a, yake yi sai ya 6ata ransa.
.
"kin san fa bana son kina yi mani wannan maganar, kawai dai idan zamu yi soyayya muyi, amma bana son zancen aure, don ba shi nasa a gabana
.
Sau da yawa ta kan lallashe shi ta ce.
.
"haka nura, an ta6a yin mutum ya zauna haka ya ce ba zai yi aure ba? Na san baka da kudi, amma kada ka damu, ni zan dauki nauyin komai, ni zan kama mana gidan da zamu zauna."
.
Nura ya ta6a cewa da ita.
.
"ko mota da kaya zaki riqa bani, in dai aure ne ba na so, ni kawai burina in samu kudi na bala'i in take in bar qasar nan in huta...kawai mutum ya ware inda ba za a riqa ganin san ba."
.
Tun daga ranar ta tabbatar tana soyayya da riqaqqen matar hankali a duniya. Son xuciya da Kuma rashin mafadi ne yasa ba zata iya cire nura daga cikin xuciyata ba." ta za6i wani mutumiin kirkin ta aura a cikin mutanen da suke sonta ba tsawon lkc, wadanda da yawansu abokan aikinta ne da suke aiki tare, da Kuma jefi-jefi mutanen da suke biyo ta har gida su san a kirata ta ce ace dasu ba zata zo ba."
.
Tana nan a zaune tana riqe da album din hotunan, sai ta ji an dan tsagaita da ruwan. Tayi sauri ta rufe album din, ta ajiye hotunan akan katifartta. Ta yunqura ta tashi a cikin gajiya don kuwa ta dade a zaune.
.
Da tashinta t kai hannu ta bude qofar cikin sauri, ta qosa ta tafi asibitin, ta san ana can ana jiranta, duk da yake dai an san abin da ya tsayar da ita. Bude qofar ke da wuya, feshin ruwan da iska ke watangariri dashi ya feso cikin dakin, ya sauka akan fuskarta. Ta lumshe idanunta dade da yin ajiyar xuciya, sbd tsananinn sanyin da ya daki fuskarta ba zato ba tsammanin
.
Babu damuwa don ruwan ya jiqa mata idanu, ta dade tana kallon hotuna har idanunta sun fara yi mata zafi, Kuma kimanin mintI hamsin da suka wuce Akwai wani tunani da tayi Wanda ya 6ata mata rai har hawaye ya xubo mata, ko ba komai dai ynx feshin ruwan zai dauraye mata kyakkawar fuskar tata, da Kuma jurwayen hawayen da ya bushe, ita kanta bata san dashi ba."
.
Bayan ta bude idanunta ne ta ga garin har ya fara washewa. Akwai alamar ruwan ya wuce, giza-gizan da suka cunkushe a sararin samaniya ynxn duk sun warwatsu a ko ina, Kowanne ya kama gabansa. Shudin samaniyar ya fara bayyana a kowanne 6angare a yayin da jefi-jefi tsuntsaye ke shawagi a qololuwar samaniyar, Kuma sun taimaka wajen qawata yanayin
.
Ta dawo da hankalinta tsakar gidansu. Inda ruwan ya cika yayi maqil a dalilin kwatarsu dake toshewa lkc-lkc. Duk lkcn da aka yi ruwan idan bai samu hanyar fita ba, ta kan dade a gida tana bude hanyoyin da yake bi yana fita, kafin tayi hakan ranta ya kan 6aci, don kuwa ko ba komai ruwan da yake taruwa a qofar dakinta yana qirqirar mata qaramin kogi, yana bata wahala a kodayaushe.
.
A wannan karon bata da lkcn tsayawa bude wata kwata ko hanyar ruwa, sauri take yi ta je wajen aikinta. Ta san idan mahaifiyarta Delu ta fito zata bude hanyoyin ruwan ya fita. Duk wannan kafin qarshen wata ne, don kuwa tayi wa wani burkila magana zai zo ya san masu babban kwaroron ruwa a kwatarsu. Jira kawai take yi su samu albashin wannan watan idan ta ci sa'a, ciwon sugan mahaifiyarta bai taso ba, sannan kuma idan nura nura aljan bai jawo mata wata sabuwar rigimar ba, Babu shakka a wannan watan tana da 'yan kudi.
.
.
Lp=3}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa. }~~~~~~{
Page 3
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ta saki qofar dakin da ta dafa. Ta koma ciki, da shigarta ta dauko jakarta ta duba ciki taga komai yana nan bata fito da komai waje ba, hodarta da Sauran tarkacen kwaskwarima, sai Kuma 'yan kudinta dari takwas.
.
Dama tun daxun ta sanya fararen kayanta na aiki, tayi kwalliyarta, jira kawai take yi a dauke ruwan ta sanya takalminta ta fita. Ta dauko farin hijabinta ta sa, ta dauki wayarta dake akan katifa tayi sauri ta bar dakin, ko madubi bata tsaya ta sake dubawa ba."
.
Lkcn da ta fito waje an dauke ruwan qaf! Akwai hayaniyar mutane a waje, da Kuma 6urarin ababen hawa da suka fara yawo a titi. Ta san a ynx da wahala idan nura yana nan a kusa, don haka ba zata tsaya wahalar kiransa ba, zai fi sauqi ta hau tasi, in yaso anjima ko ina yake zai je ya dauko ta su dawo gida, idan ta tashi aiki da almuru.
.
Ta tattare farin siket dinnta don ta ji dadin tsallake ruwan daya cika gidan nasu. Ta dade tana zagay-zageye kafin tazo daidai qofar dakin mahaifiyarta wacce ita ma a daidai lkcn ta bude qofar dakin ta ta leqo waje tana yake, ga alama ita barci take yi ma ynx ta farka ta leqo ta ga halin da garin yake ciki.
.
Busasshiyar tsohuwar 'yar kimanin shekaru hamsin da biyar, ta fesar da dusar goro, tun kafin tayi magana 'yar tata ta ce da ita cikin sauri.
.
"mama na makara zan tafi asibiti, sai na dawo."
.
Tsohuwar ta ce cikin shaqaqqiyar murya.
.
"to Hauwa, a dawo lfy."
.
.
.
*** ***
.
.
BABi NA BIYu
.
.
Hauwa ta sauko daga motar, Bayan da direban yayi fakin a daidai qofar asibitn, a yayin da wadansu mutanen suke fitowa, wadanda yawancinsu masu jinya ne, wadanda suke fitowa sayen abinci da kuma diban ruwa.
.
Da xuwanta ta shige sashin marasa lfy maza, inda take da aiki a wannan rana, ta isa sashen da marasa lfyr ke a kwana a gadajensu. A daidai lkcn ne wani gajeren ma'aikata a cikin qananan ma'aikata 'yan share-share sanye da kayan aiki ya tarbeta cikin girmamawa.
.
"sannu da xuwa hajiya."
.
Ta ce dashi cikin fara'a.
.
"sannu baba mati, ka ganni a makare ko?"
.
Tun kafin yayi mata magana ta duba agogo cikin damuwa
.
"zan fito kenan aka goce da ruwan nan, dole na tsaya sai da aka dauke. Dakta yana tambayar ina nake ko?"
.
Gajeren ma'aikacin ya ce da ita.
.
"A'a, shima tun daxun ya fita kafin a dauke ruwan. Shi Kuma Labaran da ya ga lkcn tashinsa yayi, tun kafin a dauke ruwan ya yi tafiyarsa, shi ne yace da ni in tsaya in lura da (patents) kafin ki zo ."
.
Hauwa ta nufi dan qaramin ofishinsu dake jone da babban dakin kwantar da marar san lfy, ta tambayi mai shaa.
.
"Dakta yayi sallama da yawa ne yau?"
.
Gajeren mutumin ya ce.
.
"mutum uku kawai ya sallama. Kuma ba a samu qariin wasu ba."
.
Hauwa ta shiga ofishinsu ta zauna akan kujerra daya dake fuskantar teburin dake dauke da fayil-fayil da wani qaton littafi. Mati mai shara ya tsaya a waje don ya bata sararin yin rubuce-rubucen da ya shafi'u ganin ma'aikatan Suna yi kullum idan suka zo aiki.
.
Bayan Hauwa ta gama rubuta abin da take so a jikin littafin ne sai ta rufeshi ta tashi ta shiga dogon dakin marasalfy dake kwance akan gadajensu.
.
Hauwa ta bi gado-gado tana duba marasa lfy da magungunansu, wadanda ke yiwa qarin ruwa kuma ta gyara allurar ruwan ya ci gaba da tafiya yadda ake so. Bata dade ba tana kaiwa da komowa, sai ta ji sautin shigowar wasu motoci a waje kimanin guda uku a lkc guda, wadanda suka ja birki hade da cinye taya kamar sun zo kama mai laifi.
.
Fahimtar hakan bai zama al'adar shigowa asibitin ba, sai ta kama hanyar fita daga babban dakin jinyar don ta fita ta ga ko me yake farruwa a waje. Ta kusa fita kenan ta ci karo da jami'an tsaro riqe da bindiga sun fado ciki da sauri. Hauwa tayi turus! A tsaye cikin mamaki, tana kallon abin da ke shirin faruwa.
.
Jami'an tsaron sun kasu kashi biyu, 'yansanda ne hade da ma'aikatan gidan yari. Ta ganesh haka ne ta hanyar launin kayan jikinsu, wadansu baqaqe kamar zunubi, wadansu Kuma kalar fatar jaki.
.
.
(muna farin cikin sanar da ahalin "TASKAR GIDAN LITTAFI" cewar a yau za a fara gabatar da wani sabon shiri don nishadi da qara danqon zumunchi ga al"ummar gidan nan...shirin mai Suna "FILIN rAHA" zai zo maku ne da misalin qarfe takwas na lahadin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment