Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dauki daya ya ji akwai danshi-danshin lemar sabunta wanda hakan ke nuni da ba a dade da yin simintin ba."
.
Ya daga kansa sama ya dubi hoton da aka maqala aka rufe ramin dake jikin bangon. Kafin ya miqe ya sa hannu ya ciro hoton ne, Sa'adu ganganci ya shiga cikin dakin Mu'azzam, da ya yi ido biyu da abin dake a jikin bangon. Baya buqatar tsayawa 6ata lkcn duba ramin. A karo na farko ya lura da tsiya aka gina ramin, kuma akwai abin da aka 6oye a ciki.
.
Duk da haka sai yasa hannu ya laluba ciki, bai ji komai ba, ya san dama da wahala ya samu wani abu a ciki. Don kuwa alamu sun nuna an cire abin da ake so. Shi yasa ba a mayar da simintin an rufe ramin ba." Tabbas akwai wani abu mai muhimmanci da aka ajiye a ciki, sannan aka cire shi daga baya.
.
Lkcn da D.P.O Rabe yake yin wannan tunanin ne, ya ji Sa'adu ganganci dake a ciki dakin barcin Mu'azzam yana cewa.
"Wani yaro ne aka kashe shi Sir, ga gawar a cikin loka."
.
D.P.O ya bar wajen da ramin yake, ya shiga dakin barcin , ya samu Sa'adu ya bude lokar zuba kayan, gawar Ashiru ta fado waje kamar dama abin da take jira kenan. Kallo daya Jami'an tsaron suka yiwa gawar suka tabbatar gawar yaron da ake nema ce, ana cewa baqon ya zo ya sace shi. Ba sace shi ya yi ba, kashe shi ya yi, kashe shi ya yi ya 6oye gawar don kada asirinshi ya tonu da wuri. In har ba Najib ne ya kashe wannan yaron ba, dalilin me zai sa yazo ya 6oye shi a cikin loka ya dauki jakarsa ya gudu ba tare da yayi wa ko da masoyiyarsa bankwana ba?"
.
Ya yi shiru yana wasa qwaqwalwarsa, yana harhada abubuwan dake a warwatse na binciken da suke yi.
"......masoyiya tazo da baqonta har cikin gidansu, wanda yazo zai yi karatu a garinsu.....masoyin ya gudu ba a san inda ya shiga ba.....kwatsam saika tsinci gawar wani yaro a dakin da aka ske shi,....kuma an ganshi tare da yaron da yamma.....akwai wannan daaka fasa a jikin bango aka ciro wani abu aka tafi dashi........"
.
D.P.O Rabe ya yi ajiyar xuciya, ba inda wannan al'amarin ya fuskanta sai abu daya kawai, baqon ya kashe yaron ne sakamakon tsoron kada ya tona masa asiri a game da wani abu wanda yaron n I ya sani......ba zai ayin da ya zo gari da qudurin yin karatu, kuma ya aikata wani laifi mai girma kwatankwacin kisan kai ba.....dolene a samu wani babban dalili....... Gidan hshaqin mutum mai kudi kamar Alh. Madugu, me ai sa baqo ya aikata laifin kisan kai in har ba dukiya ya sata ba.? Har kullum biyu sau biyu hudu take bayarwa.
.
D.P.O ya dan yi yaqe a makare wanda ya so ya yi kama da murmushi. Ya sosa ggirar idonshi wacce ta kode babu sauran alamun gashi, hakan da kuma ayin jajayen idanunsa wadanda ke 6oye a cikin kwarmi, su suka mayar dashi kamar tunku a cikin mutane. Shekarunshi ashirin da bakwai a wannan aikin, tun daga kurtu ya fara aikin dansanda. A tsawon shekarin ba abin da bai gani ba a nau'ukan laifi. Da ya ga laifi zai ji warinsa ko daga nesa ne, duk wani bita da qulli, da almundahana da mai laifi zai yi, in har D.P.O Rabe ai zo ya gani to a tashi daya zai ka6o jirgin mai laifi, ya fahimci abin da ya faru.
.
Ynx kam ya gano akwai cutar da Najib cikin gidan, kuma koma me ya dauka to a ramin nan ya cire shi. In har mutum zai yi kasan kai akan wata dukiya to ba qarama ba ce kuwa. Sbd haka ya zama dolene su gano inda Najib ya shiga, ko ba don kisan kan da ya yi ba, ko don satar da ya yi dolene su kamoshi su qwace dukiyar, bai isa ya gudu da ita ba."
.
Abin da ya daurewa D.P.O Rabe kanshi shi ne,ta yaya Alh. Madugu zai ajiye wata dukiya a dakin wani yaro qanin matarsa? Akwai yiwuwar shi kanshi Alh. Madugu bai san da dukiyar ba." kuma shi Mu'azzam da yake kwana a dakin in har yana da gsky me zai kaishi 6ula rami a jikin bango ya 6oye wata dukiya? Shima ba kayansa ba ne....!
.
.
.
Lp=76}~~~~~~{ Gobe Jar kasa }~~~~~~{
Page 76
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Abin da ya daurewa D.P.O Rabe kai shi ne, ta yaya Alh. Madugu zai ajiye wata dukiya a dakin wani yaro qanin matarsa? Shi kansa Alh. Madugu bai san da dukiyar ba." kuma shi Mu'azzam da yake kwana a dakin in har yana da gsky, me zai kai shi 6ula rami a jikin bango ya 6oye wata dukiya? shima ba kayanasa ba ne, don haka su zasu nemo Najib zai yi masu bayani mai kyau akan abin da ya sata. Wa ya sani ko lkcn da D.P.O yake jira ne ya zo?"
.
Saura shekaru biyu ya yi ritaya, har ynx in banda motarsa guda daya qirar (Carina 2) ba wani qwaqqwaran abu da ya mallaka, wanda zai nuna ya ta6a mallakar gida nasa na kansa, tsautsayi yasa ya auri wata 'yar qabilar Ibira, wata tsohuwar 'yar duniya. Sai da ta tabbatar ta side shi daga shi sai dan albashin sa na wata-wata bashi da komai, sai ta tsallake ta rabu dashi...tun wannan karyewar da ya yi har ynx bai murmure ba." ynx haka yana tare da wata matar da ya aura daga baya, wata bayerabiya ce....' ita bata da wata matsala game da 6annar kudi, sai dai ta haifi 'ya'ya biyu tare dashi, a kansu ne kawai yake samun matsala da ita, kome ya yi wa yaran bata yabawa, da ta ji labarin wata sabuwar makaranta mai tsada, zata hura masa wuta dolene sai an cire 'ya'yanta daga inda suke an kaisu can. D.P.O yana burin ya samu wani abu mai qwari ya adana kafin ya yi ritaya, a ynxn kam komai ya shigo hannunsa to Ba sauqi. D.P.O yana buqatar ya samu wani abu mai qwari ya adana kafin ya yi ritaya,
.
Bayan ya gama nazzaarin dan abinda ya fahimta akan wannan matsalar da ta faru, sai ya juyo ya fuskanci yaronshi Sa'adu ganganci, wanda shi ko kusa bai fahimci inda komai ya dosa ba." D.P.O Rabe ya fita da sauri ya bar dakin, ya koma 6angaren babban falon Alh. Madugu dake a sama, ya same shi a zaune tare da matarsa da 'yarsa kamar yadda ya barsu daxu, yana ta aikin balbala masu masifa. Haj. Maimuna tana a kusa da shi kamar abin bai dameta ba, Larai ta sunkuyar da kanta tana kuka, tana sauraren mahaifinta
.
Shigowar D.P.O Rabe ya sa su dukansu suka mayar da hankalinsu akan sa. Da shigowarsa tun kafin ya zauna ya ce da Alh. Madugu.
.
"mun samu yaron da ake tsammanin baqonku ya sace shi, ba sace shi ya yi ba." kashe shi ya yi. Yana nan a cikin dakin da kuka sauki baqon. Ku nemo mana iyayen yaron, ina so in zauna dasu muyi magana mai kyau."
.
Haj. Maimuna da 'yarta Larai suka kalli dan sandan a tsorace, kamar sun ga aljani. Larai ta kasa jurewa ta fasa kuka da ihu, ta tashi ta ruga ta nufi dakinta sbd xuciyarta ba zata iya daukar wadannan razanannun al'amura dake faruwa ba." Haj. Maimuna tayi salati, a lkcn da zata dafe qirjinta kamar wacce take ciwon tarin tibi.
.
A can dakin Larai da shigarta sai ta fada kan gadonta ta kifa cikinta tana kuka, xuciyarta cike da razana. Najib? Ta yaya Najib zai yi kisan kai a gidansu? Wannan wani abu ne da ba zata ta6a yarda dashi ba." Najib masoyinta ne, duk wadann abubuwan dake faruwa an shirya su ne, domin a yi masa sharri. Tun suna yara ta san Najib. ba shi ya aikata wannan laifin ba." ina zata ga masoyinta Najib a halin ynxn don su zauna suyi magana. Ta tabbatar idan har ta ganshi zai yi mata bayanin duk abin da ya sani......ba bashi da laifi, ba shi yayi wannan kisan ba."
.
Kamar yana karantar xuciyarta a can inda yake, tunaninta ya zo daidai inda take matuqar burin ko'ina ya ke zata hadu da shi. Sai ta ji wayarta ta dauki sarewar kira. Tayi sauri ta tashi daga kwanciyar da ta yi, ta kaiwa wayarta kamu, wacce ta dawo da ita daki tun daxu ta jefar da ita akan kujerar da take zaunawa.
,.
Larai tana dauka ta ga sunan Najib a fuskar wayar. Najib ne ya kira ta! Ta yi sauri hannunta yana rawa ta amsa kiran ta dora a kunnenta, ta fara yi masa magana muryarta na rawa.
.
Najib! Najib kana ina ne ynx? Kayi mani magana masoyina. Kana ina?"
,.
Ta fashe da kuka kafin ya bata amsar tambayarta.
.
.
***
.
.
Tun sanda Najib ya kuccewa Nama'u daga tambayar da ya yi masa inda ya kai yaron shiru-shiru bai jawo ba." bayan Najib ya tsayar da mai babur ya hau sun tafi ne, sai ya ce da mai babur din cikin tsoro.
.
"ka kaini wani otal mafi kusa da ka sani.....ni baqo ne ban san ko'ina ba a nan garin."
.
Mai Babur din ya keta cikin gari, bai tsayar da Najib a ko'ina ba sai a wani otal mai suna (Al'umma Guest House).
.
.
.
Lp=77}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 77
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
.
Najib kana ina ne ynx? Kayi magana mana masoyina, kana ina?"
.
Najib ya ji larai ta fashe da kuka a can 6angaren. Tunanin sa ya zama gsky, tabbas ta fahimci duk abin da ya aikata a gidansu ya gudu. Kuma daga jin muryarta tana cikin babbar matsala. Najib ya fara rarrashinta cikin tausasa murya.
.
"ki daina kuka Larai."
.
Ya ce da ita.
.
"ki daina kuka ina nan a garin nan ban yi nisa ba." har ynx ban gujeki ba Larai, ki daina kuka."
.
Larai ta dan saurara da kukan da take yi, ta ce da Najib
.
"Ina son ganin ka ynx-ynxn nan Najib, don Allah ka fada mani inda kake zan zo in same ka. Ka fada mani inda kake ba zan fadiwa kowa ba, ni kadai zan zo."
.
Wannan maganar da ta fada ne yasa Najib ya fara kuka shima, sbd ya fahimci duk irin qaton laifin da ya aikata a gidansu Larai, har ynx tana son shi. Ya ce da ita.
.
"na yarda da ke Larai. na san ke mai rufa mani asiri ce a duk halin da na tsinci kaina. Shi yasa na kira ki don in fada maki inda nake, ynx haka ina a wani Otal mai suna (Al'umma) ki zo Larai ina son ganinki, ki zo mu yi magana."
.
Larai ta share hawayen da yake xubo mata, ta yi qasa-qasa da muryarta ta ce .
.
"gani nan xuwa ynxn nan Najib. zan xo in same ka."
.
Larai ta cire wayar tayi saurin lalubo inda ta jefa makullin motarta, ta dauki gyalenta ta yafa, ta fito daga cikin dakinta da sauri, ta dawo falo ta samu mahaifiyarta ne kadai zaune ta yi tagumi. Mahaifinta da D.P.O Rabe sun sauka qasa suna qarishe sauran maganar da zasu yi akan abin da ya faru. Haj. Maimuna ta dago kai ta kalli Larai.
.
"Ina kuma zaki je ynxn naga kin dauko gyale?"
.
Larai ta yi ajiyar xuciya ta ce da mahaifiyarta
.
"zan sayo katin waya ne a nan waje ina so ne zan yi magana."
.
Da yake ta san Hajiya ba zata hanata xuwa sayo kati ba, tun kafin ta sake yi mata magana, sai Larai ta gangara qasa da sauri, ta fita waje cikin gudu-gudu. Larai ta gangara qasa da sauri, ta fita waje ta shiga motarta ta tayar ta fito daga cikin gidan ta fara gudu ta nufi otal din da Najib yake. Har xuwa lkcn da ta hau titi bata daina kuka va. Najib shima 6angaren sa tun sanda suka gama waya da Larai ya ci gaba da kuka shi kadai a cikin dakin. Yana nadamar laifin da ya aikata a gidan su Larai masoyiyarsa, wacce duk duniya bashi da tamkarta.
.
.
.
*** *** **
.
.
.
BABI NA 21
D.P.O Rabe yasa Jami'an tsaro suka dauke gawar Ashiru suka tafi da ita ofishin sa. Ya aika a kira masa hakimin yankin, da kuma manyan mutanen dake a unguwar masu fada a ji. Yasa aka nemo masa iyayen Ashiru, Tabawa da Nama'u suka zo suka ce sune iyayen sa, dukansu suna ta faman shar6e, domin kuwa tun kafin D.P.O yasa a kira su sun samu labarin an ga gawar Ashiru a gidan Alh. Madugu, ashe kashe shi aka yi ba sace shi aka yi ba."
.
Bayan kowa ya hallara ne a ofishin D.P.O Rabe, sai ya sanar dasu cewa ya sa a kira su ne don ya fada masu abin da yake faruwa aka zargin da ake yiwa Alh. Madugu na 6acewar wani yaro a gidansa. Ya ce dasu Ashiru ya mutu, kuma wani baqo da akayi a gidansa Alh. Madugu shi ake zargin ya kashe shi ya gudu. Ynx haka an baza Jami'an tsaro su nemo shi a duk inda yake. Za a kama shi kuma duk abin da hukunci ya tanadar a yi masa' za'ayi. Ya qara da cewa.
.
"Ku fadawa matasa su daina daukar doka a hannayensu. Alh. Madugu babu sa hannun sa akan wannan kisan gillar da aka yiwa wannan yaron. Bashi a gida ma sanda abin ya faru. 'Yarsa ce ta zo da baqon da ya yi wannan aika-aikar, wani saurayinta ne....! Shi kansa Alh. Madugu ya bamu hadin kai cewar zai yi duk qoqarin da ya kamata wajen ganin an kamo wannan saurayin 'yar tasa an hukunta shi, horn mai tsanani. Ya ce a baku haquri, kuma zai zo har gida ya yi maku ta'aziyya, bai ji dadin wannan abu da ya faru ba." don haka ina so ku bar wannan al'amarin a hannunmu, zamu yi binciken gaggawa mu kamo wanda ake zargi."
.
Hakimi ya yi magana ya ce....'
.
Shima an zo an same shi da zancen, abin da yasa bai zoo ya samu hukum akan maganar ba." ya ji labarin tuni 'yan sanda sun shiga maganar. Amma zai jawo hankalin talakawansa da su zamo masu ladabi da da'a, su riqa girmama doka, su daina daukar mataki a hannnunsu."
.
Bayan kowa ya gama fadar albarkacin bakin sa ne, sai D.P.O Rabe ya sa aka fito da gawar Ashiru. Ubangidansa Nama'u ya kar6a yana kuka, suka dunguma shi da Tabawa da sauran mutanen da suka zo ofishin 'yan sandann, suka tafi da gawar gida.
.
Bayan nura ta lafa ne, D.P.O Rabe ya sallami duk mutanen da ya gana dasu a daren, sai ya kira babban yaronsa na hannun damar wato Sa'adu ganganci ya ce dashi ya shiga mota su tafi. Duk sanda shugaban ya bawa yaronsa irin wannan umarnin, ba ya tambayarsa inda zasu je. Sa'adu ya san cewar akwai wani qwaqqwaran al'amari da yake buqatar sirri. A qofar wani matsakaicin gida suka tsayar da motar. Suka nufi cikin gidan Sa'adu na biye da shugaban nasa a baya cikin ladabi kamar yadda ya saba binsa in suna tafiya.
.
Minti biyu bayan haka suna a cikin falon D.P.O dake a waje, Sa'adu ya qame a tsaye kamar falwaya yana jiran umarnin ssshugaban nasa. Bayan D.P.O ya shiga gida ne ya cire rigarsa ta aiki. Ya saka mara nauyi, sai ya dawo falon a zauna akan kujera, ya kalli Sa'adu ganganci ya ce dashi kai tsaye.
.
"ba zai yiwu ba haka kawai daga mutum yazo gida baqunta ya yi kisan kai ya gudu ba, dole akwai wani qwaqqwaran dalili a 6oye. Abin da na tabbatar zai zama gsky shi ne, akwai wani abu da wannan baqon mai suna Najib ya yi, wanda yaron ya gani. Shi yasa ya kashe shi don kada ya tona masa asiri.
.
"ina zaton kuma shi wannan baqon wato Najib , wani abu ya sata a gidan, sbd na lura da wani rami da aka fasa a jikin bangon dakin sanda muka shiga muka yi bincike daxu. Ynx dolene mu kamo Najib duk inda ya shiga a qasar nan...ka kuma wannan binciken zamu yi shi ne a 6oye daga ni sai kai, ba aiki ba ne na ofis. Bana son kowa ya san wannan al'amarin' ko mataimakina ban yarda dashi ba." kai kadai zaka yi mani wannan aikin Sa'adu . Shi yasa nayi saurin ka maganar don kada Eriya kwamanda ya samu labarin......
.
.
Lp=78}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 78
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
,
"Ranka ya dade an gama, zan nemoshi, duk inda ya ke zan kawo shi."
.
D.P.O Rabe ya gyara zama akan kujera cikin jin dadin albishir din da Sa'adu ganganci ya yi masa. Tunda yake aiki tare da hatsabibin yaron bai ta6a yi masa alqawarin zai yi masa wani aiki daga baya ya kasa ba." ya yi imanin ko tsauni Sa'adu ya ce a nada masa gammo zai dauka, to fa ko zai mutu sai ya daukeshi. Shi yasa D.P.O Rabe yake sonshi. Bayan ya gyara zama ne yace dashi...
.
"Ynx wuraren saukar baqi dake a garin nan zaka fara dubawa. Tunda ance dalibi ne bai samu wurin kwana ba a makarantar da ya zo. Kuma bai san ko'ina ba a garin sai gidan Alh. Madugu, dolene a sameshi a daya daga cikin otel-otel din dake garin nan. Ka fara xuwa ka duba shi a wadannan wuraren ina saurarenka Sa'adu kayi sauri ka je. Bana so wannan yaron ya kucce daga hannu na. Yana da matuqar amfani a gareni da kai kanka. Idan ka gano mani shi."
.
Sa'adu ganganci ya ce da shugaban nasa
.
"An gama ranka ya dade, zan nemo shi duk inda ya shiga."
.
Kafin Sa'adu ya sarawa D.P.O Rabe ya tafi ne da yake wani lkcn suna dan ta6a wasa, sai Sa'adu ya ce dashi.
.
"Idan na kamo Najib din ko ban ganka ba ina iya kaiwa mataimakinka (D.C.O), ya yi masa bayanin inda ya kai dukiyar da ya sata sbd...."
.
Tun kafin ya kai qarshe D.P.O Rabe ya tashi a rude ya tsaya a gaban Sa'adu kamar zai hadiyeshi ya fara daka masa tsawa cikin fushi
.
"wa yace ka kaiwa mataimakina? baqauye ne Sa'adu. ni zaka kawo mawa. Idan ka kamo Najib nan gidana zaka zo dashi. Ina jiranka. Na fada maka wannan ba aikin ofis bane aikina ne....! Idan ka kuskura kayI mani qauyanci har wannan yaron ya gudu ya bar garin nan, baka kamoshi ba sai nasa an kore ka a wannan aikin. Shashasha mara hankali."
.
Sa'adu ganganci ya nemi afuwa ya sarawa shugaban nasa, sannan ya juya cikin sauri ya 6ace daga falon kamar walqiya. Ya bar D.P.O Rabe a rude yana mayar da numfashi
.
.
.
*** ***
.
.,
Oga Sadi da tawagarsa suna a zaune a cikin gidan kowa yana tunanin da ya damu xuciyarsa. Sautin motar da suka ji a waje ne ya dawo dasu hayyacinsu. Sadi qare-garke ya saki ransshi ya ce....'
.
"Ga Shago nan ya dawo daga sayo abincin."
.
Hauwa likita ta ji gabanta ya fadi. Tun daxu da Oga Sadi ya ce dasu zai yi fada da yaronsa Shago idan ya dawo, ta ji tsoro ya kamata. Domin kuwa bata saba ganin tashe-tashen hakula ba irin wadannan. Rabi 'yar fulani maganar ita ma ta dan tsorata ta, amma ba kamar Hauwa ba." Rabi ta sha ganin fada, idan suna wani sha'ani na fulani, anan yawan karawa da sanduna a tsakanin samarin dake neman budurwa daya.
.
Kwatsami da Sadi suna zaune tare a kusa da juna, a matsayin su na manya a tawagar. Shago ya shigo cikin sauri ya samesu a haka, yana rumgume da ledar abinci, wacce ta cika fal da ledojin tafi-da-gidanka. da xuwansa ya ajiye abincin a tsakiyarsu, fushin da ya tafi dashi, yana nan akan fuskarsa kamar duhun hadari. Sadi ya ce dashi.
.
"Ba dai wata matsala a hanya ko Shago? na fada maka 'yan sanda suna nemaanmu riwa a jallo."
.
Shago ya ce dashi cikin fushi da zafin rai.
.
"Ba matsala Oga. Ban hadu da 'yan sanda ba akan titi, har na je na dawo."
.
Sadi ya kalli su Hauwa ya ce da su
.
"to ga abinci nan an kawo Hauwa. aikin ku ne wannan, koda yake ke likita ce....' bari a baiwa Rabi 'yar fulani wannan aikin na 6angaren abinci." rabi ga abinci nan ki ba kowa nasa."
.
Rabi 'yar fulani ta yi saurin matsowa kusa da faffadar ledar ta sa hannu ta budeta. Ta fara ciro robobin tana ajiyewa. Sadi ya ce da ita.
.
"ki bude robobin kowa zai gane nasa. Sad qare-garke da abokinsa Kwatsami suka kai hannu tare suka dauko nasu abincin. Hauwa ta dauki nata, ta jira Rabi ta gano nata bayan ita ma ta dauka ne sai matan biyu suka kalli juna. Oga sadi ya ce dasu.
.
"idan kuna jin kunyar cinye abinci a gabanmu ku koma can ku juyo mana baya. Mu muna nan bamu jin kunyar yin loma ko a ina ta kama yinta muke."
.
Kwatsami ya fashe da dariyar jin maganar da Sadi ya fada, dalili na biyu kuma yana cikin murna da samun abincci. In banda wannan xuwan da Sadi yayi da jama'arsa, yau da yunwa zai kwana a gidan tunda dai bai samu baqi sun zo gidan ba." ya sa hannu ya motsa shinkafa da miyar dake turiri a cikin robar. Ya ce a cikin farin ciki
.
"baka rabuwa da abin dariya Oga Sadi."
.Hauwa da rabi ''yar fulani suka koma gefe daya, suka juyawa sauran mutanen baya. Shago ya dauki nasa abincin, ya koma gefe daya shima ya juyaawa su sadi baya. Amma shi ba kunyarsu yake ji ba, in banda yana cikin fushi, tare da Oga Sadi suke cin abinci kullum. Sai da Oga sadi ya juya yaga an ajiye ragowar ledar fura daya ba a dauka ba, sannan ya tuna da Nalamma dake a kwance a gefe daya. Sadi ya daga murya ya ce da Hauwa
.
"An mance da Baba, idan kun gama cin abinci ki zo ki taimakawa Baba ki bashi fura ya sha Hauwa."
.
Cikin biyayyar dole Hauwa ta ce da Oga Sadi, zata ba Nalamma fura ya sha. Bayan minti goma da suka gama cin abincin, bayan kowa ya natsa ne, sai Sadi ya ce da yaronsa shaGo
.
"An ci abinci an gama Shago, saura dambe. Daura zare kazo mu gani, sauri nake yi mu gama in je in kwanta, barci nake ji."
.
Shago wanda dama umarnin da yake jira kenan daga wajen sadi yayi saurin miqewa yana 6ata rai ya ce....'
.
"Oga ba sai na daura zare ba." a hannu dafi yake ba a zare ba."
.
Sadi ya miqe tsaaye shima ya ce....'
.
"nima bana buqatar daura zare. Dama na tuntu6eka ne don kada ka ce na zalunceka. In baka shiya ba ka sake shiri sosai zan jiraka Shago."
.
Shago ya sake hade rai yana cin magani ya ce....'
.
"ba wani shiri da zan sake yi Oga. In zamu buda kawai mu buda ni na shirya."
.
.
Tomorrow is our El-classico. Choose ur star due to ur opinion.
.
Shago
Or
Sadi?
.
.
Lp"79}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 79
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"ba wani shiri da zan sake yi Oga. In zamu buda kawai mu buda."
.
Sadi ya dubi Kwatsami dake a zaune yana qarishe xuqar guntuwar tabar da ya kunna bayan ya gama cin abinci. Wacce tayi jawur a hannunsa tana hayaqi yana tashi sama yana 6acewa a cikin duhu.
.
"Gyara mana fili Kwatsami, zamu fito filin daga."
.
Hauwa wacce take a gefe daya tare da dan tsoho Nalamma wanda aka jingine shi a jikin bango, tana bashi fura yana kur6a da qyar, ta sake ja baya cikin tsoron abin da mutanen ke shirin yi a gidan. Rabi 'yar fulani tana a kusa da Hauwa, sai dai ita babu tsoro maimakon haka sai alamar dariya dake a fuskarta a halin ynxn. Kwatsami ya tashi yana murmushin mugunta sbd ya tabbatar Sadi ba zai ta6a yarda wannan yaron yayi nasara akanshiba." ya sa hannu ya nannade tabarmar da suka fito da ita waje, sannan ya dan dingisa ya je inda wani qaramin benci yake a kusa da wurin ya kawar dashi, farin watan da ya kunno kai, tare da bila'adadin taurarin dake a sararin samaniya, su suka taimaka wajen rage duhun dake a gidan.
.
Shago da sadi suka matso suka tsaya a tsakiyar gidan, kowa ya ja baya ya basu wuri.

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment