Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shago ya fara raba rana ya ta6e hannu yana hasashen inda zai buga ya 6arar da ubangidansa Sadi. Bayan sin yi gaisuwa, sai Sadi shima ya ja daga, suka fara kallon-kallo. Kafin su fara 6ata lkc sai Shago ya kawowa sadi duka a fuska, Sadi ya kauce gefe guda hannun Shago ya wuce ta kusa da fuskarsa yana huci.
.
Shago bai haqura ba, ya sake kaiwa Sadi wani dukan daidai haqarqarinsa. Sadi ya sa hannu ya tare hannun Shago suka hadu a hanya. Kowanne sai da qashin hannunsa ya motsa. Da Shago ya ga bai samu nasara da hannu bane. Sai ya kaiwa Sadi ham6ari da qafa. Wannan karon yayi nasarar samun Sadi a qaffarsa. Amma ko girgiza bai yi ba ya ci gaba da kallon yaron nasa yana murmushi, yana jiranshi ya gama gwada tashi sa'ar, kafin shi kuma ya fara aiko masa da nasa saqon.
.
Sai da Shago ya daki sadi sau kusan ashirin, wani lkcn ya kare, wani lkcn kuma ya shanye, bayan ya tabbatar yaron ya gama duk wani hanqoron da yake son yi, sai Sadi ya shammaceshi ya yi masa fitar sauri ya kai masa duka a gefen wuyansa ya sameshi. Shago ya kife qasa, amma sbd zafin rai bai yarda ya huta ba da faduwarsa ya sake yunqurawa ya tashi ya kuma fadawa Oga sadi suka cure suna kokuwa.
.
Kowanne ya riqa kaiwa dan uwansa duka. Sun kai kusan minti biyu suna musayar hannu, da Oga sadi ya tuna lkcn da suka dauka ya fara yawa, sai ya qarawa hannunsa kuzari ya daki Shago a haqarqarinsa. Dole Shago ya sake shi ya Ja baya yana tangadi kamar ai fadi, sai kuma ya jure ya kai jikin bango, ya jingina ya tsaya yana kallon Oga sadi a fusace yana mayar da numfashinsa, sbd ya san ya yiwa yaronsa illa, ya ci qarfinsa ynx abin da ya rage kawai ya qarasashi ya je ya kwanta.
.
Kwatsami yana a baya ya sake kunna wata sabuwar tabar yana wangale gi6i yana dariyar mugunta. Hauwa ta tsaya da ba Nalamma furar, ita dashi sun xubo idanu suna kallon karawar dake gudana tsakanin Shago da ubangidansa Oga sadi. Rabi tana zaune dirshan tana kallon yadda mazan suke karawa. Ta san hannun namiji akwai zafi idan ya yi naushi, to amma idan har ba ita za a nausa ba tana maraba da kallo tun tana qarama. Indai zata tsaya a bayan fage ya kasance ba za a sameta ba, to kare ya kashe kare.
.
Shago ya sake yunqurowa a guje ya fadowa Sadi suka yi karo. Da yake Sadi bai riga ya shiryawa fadowar tasa ba, shima a wannan karon sai da a ja baya kamar zai fadi. Kwatsami ya fasa kai tabar da yake sha xuwa bakinsa da yaga kamar yaron ya ta6a Oga a wannan haduwar. Shi kanshi sha da yaga ya kusa 6arar da Sadi, sai ya sake binshi da wani naushin ya sameshi a kafada, sadi ya sake ja da baya amma ya jure ya qi faduwa. Shago ya ci gaba da binsa yana dukansa da kowanne hannunsa ta ko'ina. Oga Sadi ya ci gaba da ja baya har sai da ya hadu da bangon dakin dake a bayansa.
.
Hauwa likita ita ma wannan sa'ar da Shago ya samu ta dan girgiza ta...." ba wai tana tausayin Oga sadi ba ne....! Ta san cewar muddin wannan azzalumin yaron mara imani Shago ya yi nasara ya 6arar da Sadi ya kai shi qasa, to shi zai zama jagoran tawagar tasu. Dolene shi zai riqa basu umarni tunda Sadi ya fadi. A yadda Hauwa ta fahimci baqar xuciyar Shago in har ya zama jagoran tafiyar zai iya sa bindiga ya harbesu su dukansu, sbd bashi da hankali. Don haka sai Hauwa ta miqe tsaye cikin karaya tana fatan ganin Oga Sadi ya murmure ya kashe azzzalumi Shago.
.
Kamar sadi ya san abin da 'yan kallo suke fada a xuqatansu. Lkcn da Shago ya kai shi bango ya kawo masa wani mahaukacin duka kenan, sai ya goce da sauri. Hannun Shago ya naushi tsohuwar katangar gidan daga sama' ta yi motsi, wadansu bulullukan qasa guda biyu suka fado qasa. Kwatsami ya hade fuskarsa cikin damuwa da yaga ta'adin da hannun Shago ya yiwa katangarsa. Ya matso kusa yana qoqarin xuwa ya raba fadan. Tunda dai yaga alamar Oga Sadi ya xo da wasa, har an yi minti goma suna fada da yaronsa amma ya kasa bugeshi, gashi zasu yi masa 6arna su rusa masa dan gidan da yake cin abinci dashi.
.
Kafin Kwatsami ya zo inda suke ne, hannun Sadi ya yi wani irin fitowa kamar tsinin mashi. Shi kanshi Shago bai ga sanda hannun ya fito ba." ya dai ci karo dashi a hanya, lkcn da .zai kai nasa dukan. Hannun Sadi ya riga nasa xuwa, ya samu Shago a fuska. A lkcn ne Shago ya ji kamar wuta ce ta tarwatse a fuskarsa, ya yi tsammanin bombing Sadi ya jefo masa a fuskar. Sai da Shago ya tashi sama kamar balo-balo sannan ya fado qasa a watse ya yi daidai bai qara motsi ba." Kwatsami wanda ya riga ya fusata ya matso yana dingishi.
.
""Aikin banza kawai, tun daxu ka kashe yaro, amma ka zauna sai wasa kake yi masa.......
.
.
Lp=80}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 80
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"Bai kamata in kashe shi da wuri ba Kwatsami, gara da na barshi ya wasa jininsa. Fada yake so muyi, vai kamata in cuceshi ba."
.
Sadi ya daga muryarsa ya ce da Hauwa
.
"Yi sauri ki zo ga aikinki ya taso Hauwa likita. Ba sai an riqa fadawa mutum aikinsa ba a wannan tafiyar. Ya kamata kowa ya saba da abin da yake yi. Da kinga wani ya samu lahani ko rauni ba sai an ce ki zo ba." dauko kayan aiki ki tayar da Shago ya farfado, suma ya yi ba bugun mutuwa nayi masa ba." har ynx yana da amfani a wajena tunda bamu samu gwala-gwalan da muka fito nema ba." tayar dashi mu fita aiki."
.
Kwatsami ya je inda katangar sa ta samu nata raunin, inda Shago ya daketa ya tsaya cikin takaici yana jimamin yadda wannan mugun yaro ya kusa kayar masa da katanga. Hauwa ta dauko ledar da take xuba magunguna da allurai ta matso inda Shago yake a kwance a sume, ta durqusa ta fara tunanin abin da ya dace ta fara yi masa. Nalamma wanda yake jinggine da bango, yana kallon duk abin da yake faruwa, ya ji takaici ya kamshi a lkcn da Sadi ya kashe yaron sa Shago. baya son yaron ya mutu ynx, ya fi son yaron ya rayu har xuwa lkcn da zai samu lfy. Shi da kanshi yake son ya kashe wannan azzalimin yaron. Ynx burin da ya ragewa Nalamma daya ne kawai a duniya. Ya dai samu sa'a ya kashe Shago. wannan ne kadai tunanin dake a xuciyar wannan Tsoho Nalamma.
.
Sai da Hauwa ta kai fiye da minti talatin tana aiki akan Shago kafin ya farfado. Numfashinsa yana dawowa yayi xumbur ya tashi ya zauna yana zare idanu. Hauwa ta matsa baya ta bashi wuri, kada yayi zaton Sadi ne a kusa dashi ya kawo masa duka yayi mata lahani a banza.
.
Sadi wanda yake zaune a baya yana kallon abin da yake faruwa ya yiwa Hauwa dariya ya ce da ita.
.
"Ki kwantar da hankalinki ba abin da zai yi maki Hauwa. Ynx ladabinsa ya dawo, sai nan da wata uku zan sake sabunta masa wani ladabin. Dama duk bayan wata uku nake yi masa wannan aikin. Ynx ba zai qara fada da kowa ba a cikin mu, sai nan da wata uku kuma."
.
Bayan ya gama dariyar da yake yi ne, sai ya koma kan Shago ya ce dashi.
.
"An ta da jini an gama Shago ya maganar aiki? Ya kamata mu fara tunanin yadda zamu 6ullowa wannan Mu'azzam din gobe nake so gwala-gwalan nan su zo hannuna. Bana so mu wuce gobe muna wannan aikin. Ko mu rayu ko mu mutu gobe nake so mu gama wannan aikin." ....
Shago ya ce da Sadi cikin ladabi.
.
"Duk abin da ka ce haka za'ayi Oga. Zamu nemo wadannan gwala-gwalan ko'ina suka shiga a duniya su dawo wajenmu. Sbd namu ne ba ba kowa bane."
.
Sadi wanda ya ji dadin maganar yaronsa. Ya miqe tsaye ya kalli sauran abokan aikinsu ya ce....'
.
"Kowa ya kwana cikin shiri. Gobe ce ranar qarshe. Gobe wannan yaqin zai qare. Ban yi maku alqawarin mu duka zamu kai qarshe a raye ba." amma nayi maku alqawarin duk bala'in da ya taso ni zan fara shiga gaba in tunkare shi.da fatan zaku biyo ni komai wuya komai rintsi?"
.
.
Mu hadu a littafi na biyar don jin qarshen wannan labarin.
.
Na gode.
.
.
.
Dangane da yadda mutane da yawa suka riqa qorafi game da yadda rubutun littafin GOBE JAR KASA ya riqa tafiyar hawainiya. Yau ranar wanka ce babu 6oyon cibi. A cikin lokutan nayi ta fafutika ne wajen neman Ja-gaba kuma jigon adabi don tuna masa wani TSOHON ALQAWARI da ya yiwa ahalin "TASKAR GIDAN LITTAFI" cewar da kanshi zai zo don bamu ke6antacciyar kyauta. Ta yadda zamu karanta littafin GOBE JAR KASA 5 wanda har xuwa ynx babu shi a kasuwa. Sai dai har ynxn da na kammala wannan rubutun ban samu ganawa da mai gidan littafi kan al'amarin ba."
.
Ina mai baku haquri bisa hakan.
.
Godiya ta tabbata ga Allah (SWA) da Ya bani ikon kawo qarshen wannan labarin da yake a hannuna.
.
Ni Iliyas nake cewa ku ci gaba da kasancewa da "TASKAR GIDAN LITTAFI" domin nishadinku a kodayaushe.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment