Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a dauka a ba wanda na zalunta. Kenan idan ka saci kayan mutum kanka ka zalunta, kayi masa guxuri ne....! Da ace ka bar masa dukiyarsa, da a duniya shima zai barta ta qare. Sbd haka ni ba zan zalunci kaina ba, in dauki kayan wani in cinye su zame mani bala'i a ranar sakamako. Duk wani abu da zan ci indai ba halas dina bane. To ina roqon Allah Ya kareni da shi. Don haka kaima ina dada baka shawara, ka haqura da wadannan gwala-gwaln mu je mu kaiwa masu gidan nan shi yafi alheri a garemu."
.
Najib ya sa hannu ya share fuskarsa cikin tashin hankali, ynx ba a gadon bayansa kawai yake jinjinawa xufar ba." har a fuskarrsa yana jin gumi. Ya ce da yaron dake tsaye a gabansa.
.
"Ni kaina nasan duk wannan abin da kake fada, nayi karatun nan nima ba jahili ba ne. Abin da yasa kaga na dage akan mu dauki wannan dukiyar, ina lura ne da yanayin qasar nan tamu. Ynx idan baka da kudi kai ba komai bane a wannaan qasar, kamar gawa ka ke baka da amfani. Idan baka da kudi baka isa ka je asibiti ba, sai dai ka kwanta a gida ciwo ya kasheka. Baka isa ka je makaranta ba, sai dai kaga 'ya'yan masu kudi suna karatu."
.
Idan baka da kudi a qasar nan abin da zaka ci ma sai ya gagareka, shi yasa kaga ana neman kudi bakin rai bakin fama, ynx nema ya koma ya ki halal ya ki haram. Haka kowa ya ke yi kaine da baka sani ba yaro, ka amshi dukiyar nan kada ka cuci kanka a banza, arziqi yana kiranka tsiya tana hanaka xuwa."
.
Ashiru ya ce da Najib.
.
"A'a, ni bana so. A makaranta ance mu daina kafa hujja da laifukan da wadansunmu suke yi. Don wadansu sun zama azzalumai suna babakere da handamar dukiyar talakawa, to mu bai kamata mu riqa koyi da su ba. An ce mu daina hangen girman laifukan wasu. Kullum mu riqa ganin girman namu laifin komin qanqantarsa, mu kiyaye mu daina aikatawa sbd idan muka raina laifi ba mu san da wanne Allah zai kama mu ba."
.
.
Lp=61
}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 61
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"An ce mu daina hangen girman laifn da wani yake yi, Kullum mu riqa ganin namu laifin komai qanqantarsa, mu kiyaye mu daina aikatawa sbd idan muna raina laifi ba mu san da wanne Allah zai yi fushi damu yayi mana azaba kansa ba."
.
Gaskiya ni dai in duk duniyar nan kowa zai zama 6arawo , ni ba zan ta6a daukar kayan da ba nawa ba Malam, kayi haquri kawai mu kwashe wannan dukiya mu kaiwa masu ita."
.
Najib ya ji juwa tana daukarsa kamar zai fadi qasa. Idanunsa sun rufe dukansu wajen hadamar ya mallaki wannan gagarumar dukiya. Ya fara yiwa Ashiru kafinta magiya yana roqonsa arziqi ya taimaka masa ya yi masa rai.
.
"ka rufa mani asiri yaro. Idan kai baka so ni ina so, don Allah ka taimake ni kayi shiru, ni zan dauki ko guda uku ne, sai mu kai masu sauran mu ce abin da muka tsinta kenan, tunda a gabanka abin ya faru kai ne shaida, idan ka ce abin da muka tsinta kenan zasu amince, zan dauki guda uku a cikim gwala-gwalan nan, sai mu kai masu saura ka rufa mani asiri."
.
Najib ya bi Ashiru da kallo cikin karaya, yana fargabar sake rashin amincewar yaron.
.
"Idan nayi haka kuma ai nayi qarya kenan."
.
Ashiru kafinta ya ce dashi kai tsaye.
.
"qarya ma haramunce, tana daga cikin munananan ayyukan da Allah ba Ya so mu aikata, sbd haka ni ba zan bayar da shaidar zir ba. Ga gsky ina gani qiri-qiri in 6oye in fadi qarya don in faranta maka rai, kuma in sa6awa Ubangijina, ba zan iya ba." idan ka dauki gwal daya, sai na fadi gsky, guda goma ne gasu nan na gansu da idona, dukansu za a dauka a kai wa wanda yake dasu."
.
Najib ya fita hayyacinsa sbd tsabar takaici. Ya nuna Ashiru da yatsa ya ce da shi a fusace.
.
"Amma kai dai matsiyaci ne....! Shege wanda zai mutu a talauce. Dama da ganinka baka gaji arziqi ba, irin ku ne ko a tandun mai aka tsoma ku, haka za a tsamo ku qamas sbd tsabar rashin rabo. Ga dukiyar mun samu a banza, amma zaka yi mana baqin ciki. Dan ubanka in wani ya tsinta zai kai masu ne?"

.
Yaron ya fara jin tsoron Najib, ya dan ja baya kadan duk da haka bai daina magana ba, ya ce da Najib
.
"Dukiya ba wata abin alheri ba ce indai ba akan tafarki mai kyau zamu sameta ba." duk wata dukiya komin yawanta a duniya, indai har zata zamewa mutum sanadin da zai hallaka ya hadu da fushin Ubangiji, to wannan dukiyar ta zama masifa, bata da amfani ko qanqani."
.
Najib ya sake tasowa Ashiru kafinta da zagi.
.
"to ni sai naci wannan dukiyar, baka isa ka yi mani baqin ciki da wannan dan guntun ilmin naka na zamani wanda bai fi cikin cokali ba." shegun yara kawai qauyawa, malamanku suna ta cutarku suna barinku da talauci suna shiga manyan motoci."
.
Ashiru kafinta ya ce.
.
"Subhanallahi, baka san illar wannan maganar da ka fada ba." kai kana baqin ciki ne don Malamai sun hau manyan motoci, a wulaqance kake so kaga wadanda suke yiwa addini hidima? In har wannan ce hujjarka shi yasa ka duqufa cin haram, to kayi kuskure. Ta yaya kai da kake jahili zaka hada kanka da wanda yake da ilmi, bayan kuma Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya fadi cewar, "Babu talauci ga wanda ya yi ilimi." to kaima ka je ka yi ilimin mana ka zama Malamin, kaima ka riqa hawa manyan motocin. Me yasa zaka dauki dukiyar wani ka ce da ita zaka zama attajiri? Idan kayi haka kayi gsky kenan?"
.
Najib ya tabbatar yana 6atawa kansa lkc ne kawai, wannan yaron ba zai ta6a bashi goyon baya ba ya dauki ko gwal daya, gashi kuma shi ba zai iya haquri ya dangana ba." ya ce da Ashiru a fusace.
.
"To dan iyayenka na riqe wadannan gwala-gwalan, ba zan kai wa masu gidan ba, me zaka yi a kai?...kana da abin da zaka yi ne?"
.
Yaron ya sosa kai ya ce.
.
"Ni ina ruwa na? Ni dai in anzo an tambayeni gsky ba zan 6oye ba, zan ce kai ka dauka.... Illah iyaka kenan."
.
Najib bai san lkcn da ya tashi kamar yadda mahaukaci yake dira akan yaran da suka tsokane shi ya fada kan Ashiru kafinta. Kafin yaron ya iya motsa siririn jikinsa tuni har hannuwan Najib sun damqi wuyansa. Najib ya dauki Ashiru kamar yadda mage take cafar 6era ta raba shi da qasa, yayi jifa dashi ya hadu da bangon dakin.
.
Ashiru ya yi kuwwa a makare, a sakamakon tsoron da ya ji, sautin muryarsa bai je ko'ina ba, bayan ya hadu da bangone ya watse a qasa qafafuwansa suka yi dai-dai, kowacce ta dubi inda take so, kamar an jefar da 'yar tsanar qyanqyale shi.
.
Najib ya bi yaron a fusace ya sake kama siririn wuyansa dake kama da laima, ya shaqare yana daka masa tsawa.
.
"Ni zaka tonawa asiri? Ka ce ba zaka fadawa kowa na tsinci gwal a dakin nan ba." ka fada in ji ko in kashe ka."
.
Idanun Ashiru sun qafe tuni ya daina kallon komai, sai da Najib yaga jini ya taru a bakin yaron ya fara xubowa ne kamar jaririn da aka durawa maganin kwalba, sannan ya fara jin tsoro. Ya yi saurin dawowa hayyacinsa, kada fada xuciya da hadama su ja ya yi kasassa6a ya yi kisan kai, daga kawai yaxo baqunta gidan su masoyiyarsa.
.
Najib ya saki wuyan Ashiru kafinta a tsorace, ya girgizashi jikinsa na rawa.
.
"Kai...lai tashi wasa nake yi maka." ....
Ashiru yana nan ya yi lagwaf a qasa, babu inda yake motsawa a jikinsa. Najib ya sake jin tsoro da fargaba sun mamaye xuciyarsa. Ya ta6a qirjin yaron da sauri ya ji shiru, xuciyarsa bata bugawa. Ya sake kallon fuskarsa wacce ta yanqwane a dan lkc qanqani. Jinin da yake xubowa daga bakin yaron ya fara taruwa a qasan daddumar dake malale a tsakar dakin.
.
Najib ya ja baya a tsorace ya fara tsima yana kallon Ashiru kafinta.
.
.
.
Lp=62}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 62
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI"
Bata amince da daukar shafin ba."
.
Najib ya ja baya a tsorace ya fara tsima yana kallon Ashiru kafinta.
"me nayi maka?"
.
Ya tambayi yaron a kidime kamar zai fashe da kuka.
.
"me nayi maka? Wasa nake yi na haqura da gwal din bana so. Don Allah ka tashi."
.
Ashiru yana nan a tarwatse a inda yake, idanunsa a kafe. Najib ya sake ta6a shi jikinsa a kidime kamar yaga fatalwa. Bai san lkcn da ya fara kuka ba, sbd shi kansa ya san Ashiru kafinta ya mutu, kuma tabbas shi ya kashe shi!!
.
.
*** *** ***
.
.
.
Babi Na Sha-Bakwai
.
Ya kai fiye da minti biyar yana taran-taran a tsakar dakin, ya rasa inda zai sa kanshi ya samu sauqi. Sai daga baya Najib ya fara tattara tunaninsa waje daya, qwaqwalwarsa ta dawo ta fara aiki. Ya tsaya gefe daya ya yi tagumi yana kallon gawar Ashiru, ya san cewar fushin da yayi na rashin samun hadin kan yaron game da sace gwala-gwalan shi ya tunxurashi har ya aikata wannan mugun aiki. Amma shi kanshi ba a son ranshi ya kashe wannan yaron ba." bai yi masa dukan da zai mutu ba,, tsautsayi ne kawai ya gifta, abin kuma ya zo da qarar kwana.
.
Najib ya yi ajiyar xuciya, ya fara tunanin abin da ya kamata ya yi a halin ynxn. Ya tabbatar idan har aka ritsa shi bashi da mafita, ba abin da zai fada ya kare kanshi cewar bashi ya kashe Ashiru ba." a wajen binciken da Jami'an tsaro zasu yi dolene su sashi tsakiya da kulki a lkc qanqani zai rera masu waqar dalilin da yasa ya kashe wannan yaron. A qarshe idan ya fadi gsky, zai tashi bai tsira da komai ba, bashi ga tsuntsu bashi kuma ga tarko. Ba zai mallaki gwala-gwalan ba, ga kuma hukuncin kisan kai ya hau kanshi.
.
Don haka dolene ya nemi mafita, Najib ya tabbatar wa kanshi ba zai ta6a tsayawa a kama shi da wannan laifin ba." to amma kuma a daya 6angaren idan ya gudu ya abin zai kasance ga masoyiyarsa Larai? Ita ce ta kawo shi gidansu, komai zai faru a kanta abin zai qare ita da iyayenta. Shin ya yiwa Larai halacci kenan, idan ya barta a cikin wannan tsomomuwar? Babu shakka yayi mata butulci, to sai dai da a kamashi da wannan laifin gara ya gudu ko me zai faru zai zo da sauqi, a qalla dai ba shi za a kama ba."
.
Ya san mahaifin Larai babban mutum ne, kome zai je ya dawo zai iya kashe maganar ba tare da Larai ta shiga matsala ba." Najib ya sake yin wani tagumin ya sauya hannu. Ya sake qurawa gawar Ashiru kafinta idanu. Wataqila dama can yaron bashi da isasshiyar lfy ne....! Najib yayi tsammanin haka, tunda idan ba haka ba ta yaya daga kawai ya mangare shi yayi jifa dashi, sai mutuwa ba ko shurawa'. Ina ma laifi ya dan yi gajeruwar suma ya farfado.?
.
Najib ya yi ajiyar xuciya . Babu lkcn da zai tsaya yana yin duk wadannan tunane-tunanen, yana a cikin wannan qatuwar matsalar, idan ya yi sakaci wani ya zo ya ritsa shi da gawar Ashiru
Kashinsa ya bushe. Ga kuma uwa uba wadann gwala-gwalan wadanda a dalilinsu ne har ya yi wannan muguwar aika-aikar. Idan har yana so ya mallakesu, dolene ya yi hanzarin guduwa ya bar gidan.
.
Najib yayi sauri ya nufi inda jakarsa take, ya dakota ya ajiye ta a qasa a kusa da inda gwala-gwalan suke a xube a qasan daddumar. Ya zage zif din ya bude jakar, ya fara daukar gwala-gwalan daya bayan daya yana sakawa a ciki. Bayan ya gama xubasu ne, sai ya zuge zif din ya rufe Jakar ya duba agogon hannunsa yaga qarfe shiga saura minti goma.
.
Magriba ta kusa, Larai zata iya xuwa a kowanne lkc daga ynx don ganin ya farka daga barcin. Ya san dolene Larai taga abin da ya faru, kuma shima ba zai iya 6oye mata ba." amma ba zai yarda ta ritsa shi a gidansu a wannan yanayin ba." in yaso idan ya gudu ko'ina ya je zai nemeta a waya ya fada mata duk abin da ya faru tun daga farko har qarshe.
.
Larai tana sonshi, ya tabbatar ba zata gujeshi ba." duk wani halin da zai shiga zata taimakeshi a garin. Ba zata yarda ya fada hannun 'yansanda ba."
.
Najib ya dauki jakarsa zarar zai fita sai kuma xuciyarsa ta raya masa, bai kamata ya tafi ya bar gawar Ashiru a tsakar dakin ba, kuma bai kamata ya bar dakin a hautsine ba, idan Larai ko wani ya shigo dakin, da shigowa za a ci karo da gawar, za a fahimci abin da ya faru. Kafin ya yi nisa za a bi sawunsa a kamo shi a dawo dashi. Amma idan ya 6oye gawar ko a cikin dakin ne, ya gyara kadan daga 6annar da yayi, kafin a gano abin da ya faru za a dan dauki lkc, wannan zai bashi damar da zai gudu ba tare da an gano abin da ke faruwa ba."
.
Najib ya ajiye jakarsa, ya matso inda gawar Ashiru ke kwance. Ba ya son ya ta6a gawar yaron, to amma babu yadda zai yi. Aikin gama ya riga ya gama, shi ya kashe shi sbd zafin xuciyarshi, don haka dolene yasa hannu yayi wani abu in har yana so ya ku6uta daga kamun Jami'an tsaro, kafin su bazama nemansa.
.
Najib ya runtse idanunsa ya kama qafar yaron daya, ya tallafo kanshi wanda ha langa6e ya koma gefe daya, ya daukeshi tsam kamar ramammen zakaran da ya kasa, ya bude idanunsa kadan ya fara hasashen inda zai 6oye shi a cikin dakin.
.
Najib ya duba ko'ina a cikin falon, babu inda zai 66oye koda takalmi ne ba tare da an ganshi ba, don haka sai ya nufi uwar dakin dashi, inda Mu'azzam yake da qatuwar katifarsa mai dauke da kakkauran bargo da matasan kai guda hudu.
.
Bai tsaya yin wani sabon tunani ba, Najib ya dora gawar yaron akan qatuwar katifar, ya je inda lokar take a daya 6angaren, ya kama mariqin qofar ya jawota. Ya ci sa'a a bude take, da qofar ta bude ne, Najib ya samu kayan dake shirye a ciki, yawancinsu qananun kaya ne (Jeans) kala-kala da (T-shirt) an wankesu an ninke su tari guda, sai kuma takalma daga sama.
.
Najib ya sa hannu ya kwashe kayan ya fara fitowa dasu waje yana ajiyesu a qasa. Bay ya gama kwashesu ne fili ya samu tun daga qasa har sama, sai ya koma kan katifar ya cicci6o gawar Ashiru kafinta yaxo da ita wajen lokar, bai tsaya jiran komai ba sai yafa tura gawar a ciki. Da yake lokar na da fadi Najib bai sha wahalar saka gawar a ciki ba." kafa daya ta bashi matsala bata shiga ba, ita dinma da ya lanqwasata ya turata da hannu, sai ya ja qofar lokar ya danneta ta.
.
Bayan ya 6oye gawar Ashiru, sai ya dawo falon, ya duba kayayyakin dake a warwatse, ya dauki hoton kyakkyawar yarinyar da ya rufe fasasshen bangon, ya mayar dashi ya sake rufe ramin, ya kai ganinsa inda Ashiru ya jefar da qaramar maqwanqwasar buga qusa, ya dauketa ya daga kujera daya dake a cikin falon ya 6oyeta a ciki.
.
Najib ya sake tsayawa ya kalli dakin, a qalla dai ynx ba kowa zai zargi wani abu ba a shigowar farko, to amma ya san dolene asiri ya tonu. Ya yi sauri ya dauki jakarsa ya fice waje. Gari yayi duhu, sauran 'yan mintoci kadan a fara kiran sallar magriba a masallatai. Ya yi sauri ya jawo qofar dakin ya rufe, ya juya dan makullin dake a cikin kwadon qofar ya rufeta. Ya saka saka makullin a aljihunsa. Ko ba komai kafin a bude qofar za a dauki lkc, wannan zai bashi damar yin nisa, ko a ina yake zai 6oye kanshi kafin bincike ya tsananta.
.
Najib ya gangaro cikin sauri daga saman benen, a can cikin xuciyarsa wani abu yana gargadinsa cewar abin da yake shirin yi ba shi ne abin da ya cancanta ya yi ba." bai kamata ya yiwa Larai haka ba." to amma ba komai, ya ce a xuciyarsa. Zai samu inda zai 6oye kansa ko a Otal ne zai kama, ba zai bar garin ba sai ya sake ganinta. Ba zai fada mata gskyr dalilin da yasa ya kashe Ashiru ba, zai ce da ita ya kira yaron ne don ya yi masa gyaran katakon da ya fado, sai tsautsayi ya gitta katakon ya fadowa yaron a kai.... Ba wanda zai yarda da wannan labarin, to amma a irin soyayyar da Larai take yi masa ya tabbatar ita zata amince da shi.
.
Najib ya fito daga cikin gidan dauke da jakarsa ta gajerar tafiya. A daidai lkcn da yazo farfajiyar gidan ne inda faffadar qofar motar gidan take ya ci karo da wani mutum wanda a kallo daya Najib ya gane ko wanene. Gabansa ya fadi, saura kadan jakar dake a hannunsa ta su6uce ta fadi qasa. Mutumin ba wani bane, ubangidan su Ashiru kafinta ne....! Wanda Najib ya gaisa dashi daxu da je neman wanda zai gyara masa katakon da ya fado.
.
.
.
Lp=63}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 63
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince daukar shafin ba."
.
Ubangidan su Ashiru kafinta ne wanda Najib ya gaisa dashi daxu sanda yaje neman wanda zai gyara masa katakon da ya fado.
.
Mutumin ya gane Najib tun a ganin farfo, da haduwar tasu tun kafin Najib ya gama wartsakewa daga kaduwar ganinsa sai mutumin ya ce da shi cikin damuwa.
.
"Kai nazo nema dama. Tun daxu Ashiru bai dawo ba, daga kawai ya zo mayar maka da katakon, yana ina ne?" kira mani shi sauri nake yi."
.
Najib ya ji kansa ya yi nauyi kamar an dora masa buhun alkaki.
.
.
*** ***
.
.
.
Mutane bakwai ke zaune a cikin tsararren dakin taron, dukaninsu sanye cikin manyan kaya na alfarma, sun saka tanqasheshen teburi a gabansu, wanda yake bayyana hotunan su a jikinsa kamar sun zauna a gaban qorama.
.
A cikin mutanen daya ya ware gefe daya akan kujerarsa wacce tafi tsaruwa da girma fiye da sauran. Da yake kuma sauran mutanen shi suke fuskanta, hakan alama ce dake nuna shi ne mai magana kuma uban taron da suke gudanarwa na sirri. Sunansa Alh. Baballe Dan Abu, shi ne shugaban jam'iyyar su Alh. Madugu na jiha.
.
Sauran mutane shidan dake fuskantar shugaban jam'iyyar duk 'yan takara ne wadanda kuma duk kusan muqami daya suke nema. Wasu har sun fara manna fastocinsu, wadansu kuma sun sayi fom amma sun lafar suna jira suga ina al'amuran suka dosa kafin su yunquro.
.
Wannan dan qaramin taron da suka kira na sirri na 'ya'yan jam'iyyar ne, don a zauna a yi sulhu a tsakani kada a samu rarrabuwar kawuna. Alh. Madugu yana a cikin mahalartan taron na 'yan takara shida, tun zamansa bayan an gaggaisa bai sake yiwa kowa magana ba, sbd yana zargin akwai manufunci da zagon qasa a wannan zaman da zasu yi.
.
Shugaban jam'iyya Alh. Baballe ya gyara murya ya miqe tsaye ya kalli 'yan takarar cikin fara'a da annashuwa, yayi masu gdy bisa amsa kiran da suka yi, duk da yake sanarwar anyi ta ne a qurarren lkc. Ya sake gyara muryarsa sannan ya ce.
.
"Na kira kune sakamakon zaman da muka yi da 'yan jam'iyya. Ganin yadda abubuwa suke tafiya a tsakaninmu ya sa muka yi wani hasashe domin mu nemowa jam'iyyar mu mafita. Sanin kanku ne cewar gwamnati a hannunmu take ba zamu ta6a yin sakaci, abokan hamayya su qwace mana gwamnati a hannunmu ba. Kome za'ayi ko yaya za'ayi, zamu tsaya da qafafuwanmu don ganin dorewar wannan jam'iyyar tamu."
.
'Yan takarar suka dauki tafi raf! Raf!! Amma shi Alh. Madugu sauri daya kawai ya tafa hannu ya gyara zama ya sake murtuke fuska. Alh. Baballe ya ci gaba da cewa.
.
"Ku dukanku kun fito takara' kuma ku dukanku mutanenmu babu wanda zamu ware muce wane muke so. Amma dolene mu sasanta ku, mu rarraba maku takarar domin mu hada kanmu. Ku hudu a cikinku kun fito takarar sanata, biyu kuma suna neman kujerar majalisar wakilai ta tarayya duk daga shiyya daya. Don haka ba zamu bar mutum biyu ko uku suyi (Primary election) ba, sbd bamu son mu rasa wanda bai samu nasara ba. Zamu yi sasanci ne mu ba kowa muqamin da zai nema, in yaso sai mu tunkari abokan hamayya mu ji da babban za6e mai xuwa. Kun san wannan za6en da za'ayi na wannan lkcn yafi kowanne da muka yi a baya zafi. Kun san cewar jam'iyyun hamayyarmu sun fi mu mutane. Kuma a wannan lkcn mutane sun qara wayewa da siyasa. Hanyoyin da muka bi a baya muka ci za6e ynx ba zasu yi aiki ba. Dolene mu hada kanmu mu warware matsalarmu ta cikin gida, mu hada qarfinmu waje daya mu fuskanci abokan hamayyarmu. Amma idan ba mu sasanta matsalar tsakanmu ba, da wanne zamu ji? Da fafatawarmu da abokan hamayya, ko kuwa da rikice-rikicenmu na (Party)?"
.
Shugaban jam'iyyar ya saurara yana kallon 'yan takarar daya bayan daya. A wannan karon basu tafa masa ba, sun yi shiru ne a zaune suna jiran su ji inda maganarsa ta nufa. Ya dubi daya daga cikinsu ya nuna shi ya ce.
.
"Alh. Mamuda Iro, zaka yi haquri ka janye takarar da ka ke nema ta majalisar wakilan tarayya, zaka barwa Alh. Sale Barau. Idan gwamnatinmu ta dore Gwamna yayi maka alqawarin zai baka Kwamishinan kudi."
.
Alh. Mamuda Iro ya cure a waje daya kamar an dorawa kwado dutse, xuwa can sai ya numfasa ya ce.
.
"Ba komai ranka ya dade, na janye na bar masa, Allah Ya bamu nasara, Ya kaimu gaci."
.
Yana gama fadin haka sai dakin ya sake kaurewa da tafi, shugaban jam'iyyar wanda aka yi tafin tare da shi ya ce cikin jin dadi.
.
"To madallah nayi farin ciki da biyayyar da Alh. Mamuda ya yi. Ina fatan sauran 'yan jam'iyyar zasu yi koyi da shi."
.
Alh. Mamuda ya 6ata fuska, kamar wanda yayi karo da kyankyaso a cikin qoqon furarsa. Alh. Baballe ya dube su ya ce.
.
"Na dawo kanku masu neman kujerar sanata a shiyyarmu ta farko. Duk sauran shiyyoyinmu bamu da matsala mun fitar da 'yan takararmu guda dai-dai, a wannan shiyyar ne kawai muke da 'ya'yan takara ga ku nan ku hudu. Zamu yi sasanci a barwa mutum daya, amma kafin in fadi kowa za a barwa takara, sai na fara sanar da kowa albishir din da Gwamna ya yi masa, idan kuka bada hadin kai a wannan tafiyar."
.
Alh. Ayuba Mai atamfa zaka yi haquri ka janye daga takara. Gwamna ya yi maka albishir zai baka kwangilar yasar dam din garin Da6akere."
.
Alh. Ayuba ya washe baki, don kuwa tuni har qwaqwalwarsa wacce bata tunanin komai sai babakere akan dukiyar talakawa ta lissafo masa biliyoyin kudin da zai yi sama da fadi dasu a wannan kwangila mai tsoka da zai samu. Baidai an hana shi takara an yi masa alqawarin kwangila ba?" to ko aikin milyan daya ba zai yi ba, talakawa sun dade qishin ruwa bai kashe su ba." Shugaban jam'iyyar ya sake nuna Kwamared Abashe Qasimu ya ce dashi...?wannan
.
"Abashe kaima jam'iyya ta nemi ka janye daga wannan takara a tafi tare da kai, gwamna ya yi maka alqawarin zai baka Kwamishinan ilimi, idan mun kai gaci a wannan tafiya."
.
Kwamared Abashe shima wata tsohuwar qaya ce a gwamnati, ya ta6a yin sama da fadi da albashin ma'aikata na jiha, wani wata sanda yake riqe da muqamin akanta na shekaru biyar da suka wuce. Da ya ji wannan albishir ne ya tuna da kudin da ake warewa fannin ilmi a jihar, sai yayi murmushi. Ba komai

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

4 months ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment