Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can a asibitin?"
.
A qarshe Bayan ya sake saurarawa yana murmushi ya ce.
.
"ba matsala, na gode mugu, kada ka damu zan tuna da kai ba ha'inci a tsakanina da kai."
.
Ya katse wayar cikin sauri ya dubi yaranshi biyu dake lale karta a nesa yayi masu fito. Nan da nan mai ankwa ya hade karta waje suka taso cikin sauri suka taho inda oga sadi yake tsaye. Sun san indai yayi fito to yana son gani su ne, alamar aiki ya samu kenan.
.
Sadi yana tsaye yana kallon su kafin su qariso, dukkansu baqaqe ne wuluk majiya qarfi, suna sanye da singileti, mai ankwa fara, shagon sadi baqa, mai ankwa yafi shagon sadi tsawo kadan, Kuma zai girmeshi ko ba yawa.
.
Suna da banbanci a fuska, shago ko da yaushe fuskarta a murtuke take baya fara'a, Wanda ko shakka Babu idan aka hada rashin fara'arsa hade da jajayen qananun idanunsa dake kama da barkono ya isa ya kada hantar cikin duk wanda ya kalle shi.
.
Mai ankwa murmushi yake yi a Kowanne lkc, to amma ga Wanda ya ke da sirrinshi ya san ba murmushi yake yi ba." tun wani fada da ya ta6a yi ne da wani gagararre irin shi, ya lanta6a mashi yanka a le6e ya kusa yanke masa ha6a. Bayan wani qwararren mai kyamis a layinsu yayi iya qoqarinsa wajen dinke ha6ar, sai mai ankwa ya koma haka da ya warke. Zata a ganshi yana murmushi kamar mutumin kirki, sai dai Kuma ko da yana shirin yin kisan kai a haka zaka ganshi, mutum zai iya miqae masa hannu su gaisa cikin rashin sani, idan ya hada ido dashi...to amma miqawa mai ankwa hannu kamar saka hannu ne a bakin kura ko Kuma riqaqqen mesa a cikin rami.
.
Da xuwansa gaban ogansu sadi qare-garke Wanda shi ya dan fisu kyan gani da yake bafillatani ne, sai ya ce dasu.
.
"aikine ya taso Wanda na dade ina zaman jiran sa shekara da shekaru. yafi Kowanne aiki da muka ta6a yi hadari, amma ina tabbatar maku idan muka yi nasara a wannan aikin, to zai zame mana sanadiyyar barin komai mu zauna mu huta har qarshen rayuwar."
.
Shago da mai ankwa suka matso sosai kusa da shugabansu don su fahimceshi da kyau. dama sun fi so idan za a yi aiki muyi babba na azo a gani. Basu son qananun ayyuka wadanda zasu kashe abin da suka samo a rana daya. Sadi ya ci gaba da yi masu Bayani a snake.
.
"ina da wani aboki da na shaqu dashi a cikin ma'aikatan dake a gidan yarin da muka zauna. Ya ta6a bani labarin wani tsoho da suke tare dashi a gidan shekara da shekaru, ya ce Tsohon ya kai shekara talatin da biyar, anan tsaronshi ne sbd tuhumarsa da ake don ya bayyana inda ya kai wasu gwala-gwalai da ya satarwa gwamnatin tarayya. Ya bayyana mani qididdigar masana game da adadin dukiyar. Dukiya ce mai yawa daidai da yadda qasa guda zata yi alfahari da kanta tsakanin takwarori. Yaya suke ganin irin wannan dukiyar a hannu tsirarun mutane kamar mu ukun nan? Don haka na ce da gandiroban duk sanda dama ta samu aka fito da fursinan waje ya sanar da ni, zamu je mu mu sace shi yayi mana bayanin inda ya 6oye dukiyar, idan muka daukota zan rabat uku in baiwa gandiroban kashe daya."
.
Sadi yayi wa iblisan yaran nasa biyu dariya sannan ya ce.
.
"yau dama ta samu yara. Ynxn nan ya bugo min waya ya ce, an kai Tsohon asibiti, don haka ina so Ku shirya anjima da daddare zamu je mu sato tsohon."
.
Shago da mai suka ce a lkc daya.
.
"ba matsala oga, kome ka ce haka za ayi."
.
Sadi kare-garke ya ce dasu.
.
"ban yi maku alqawarin zamu tsira da rayuwarmu mu duka a wajen wannan gagarumin aiki ba." don kuwa wannan dukiya da Tsohon ya 6oye dukiyar gwamnatin tarayya ce. Don haka a hannun gwamnati muke shirin qwatar dukiya. Idan mun qwace tsohon a wannan karon BA ya nufin mu qwace dukiyar, don kuwa fada zamu yi da duk wani mai kaki na qasar nan, su za a sa su nemo mu don kada tsohon ya samu damar yi mana bayanin inda ya 6oye gwala-gawalan. To amma wannan ba zai sa mu fasa zuwa ba." kuna jinjinawa zamu iya muje anjima da daddare har asibitin mu sato shi?"
.
Suka sake cewa a lkc guda.
.
"oga kome ka ce fa haka za a yi."
.
Sadi qare-garke ya girgiza kai cikin gamsuwa. Ya ce dasu.
.
"ku shirya kafin anjima, nima zan sake shiryawa. An ce waigo shekara talatin wai 'yansanda suka yi Suna matsa tsohon amma wai ya qi yayi masu bayani, baring mu sato shi mu gani, akwai matsar da zamu yi masa mu samu duk bayanin da muke nema. na tabbatar idan ya jure azabar 'yansanda mu ba zai iya jure dafinmu ba....
.
.
Lp=8}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa}~~~~~~{
Page 8
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Na tabbatar idan ya jure wahalarr 'yansanda mu ba zai iya jure dafinmu ba, ko me kuka ce yara?"
.
Shago da mai ankwa da yake sun koyi zama da sadi, sai suka sake hada bakin suka ce.
.
"wane shi ya iya shanye dafinmu oga? Ai duk Wanda ya fado hannunmu ya hadu da bala'i."
.
sadi qare-garke ya fashe da dariyar mugunta wacce ta 6ace a cikin rugugin daf din da ta hau kan gadar zata wuce tana ta bulbular da hayaqi kamar jirgin qasa.
.

.
***
.
.
Duk bayan minti ashirin sai Hauwa ta je dakin da aka kwantar da tsoho ta dubai, don ganin halin da yake ciki. Duk xuwan da take yi tana samunshi ne a yadda ta barshi, ya dai yi barci na dan gajeren lkc kafin ya farka. Ga alama jikinsa ya fara qarfi, don kuwa ynx yana iya bude idanunsa ya kalli duk Wanda ya shigo cikin dakin.
.
Ledar ruwan da ta sa mashi ta qare, Hauwa ta koma dakin magani pharmacy ta qaro leda daya ta zo ta sake sa mashi, har xuwa wannan lkcn likita bai dawo ba."
Al"amarin Tsohon ya girgiza ta sosai, ta ji ta qosa lkcn tashinta aiki yayi, wani ya kar6eta, ba Tsohon yake bata tsoro ba, wadannan 'yansanda da suka zo suka cika asibitin sune suke damunta.
.
Daga baya sun fita daga dakin lkcn da suka ga Tsohon yayi barci, sai suka fita waje suka yi sansani. Wadansu sun koma gefe daya Suna shan taba, wadansu Kuma Suna shira Suna shafa bindigoginsu. Sun saki jikinsu da Hauwa . Sun san dai bata san komaI ba a game da tsohon, ballantana ta tambayeshi kan labarin gwala-gwalai
.
Ita Hauwa ta aikinta kawai take yi, idan ta shigo dakin ta duba ruwan da yake ta kwarara a jikin Tsohon, ta tabbatar bai tsaya ba, sai ta fice abinta, ko kallon shi ma ba zata yi ba."
.
A wani dawowa da tayi ne bayan ta dubashi, har zata sake ficewa kenan ta bar dakin, sai taga Tsohon ya bude idanunsa ya kalleta. Yayi mata xuru da ramammun idanunsa ya kalleta. Ta Jami'an baya cikin sauri. Ga mamakinta sai ta ga Tsohon yayi mata murmushi.
.
"na baki tsoro ko 'yaTa?"
.
Ya tambayeta muryarsa na kyarma. Hauwa ta rasa abin da zata ce dashi, bata ta6a zaton Tsohon zai iya magana da wuri haka ba, lallai jikin ya fara kyau.
.
"ki yi haquri yarinya."
.
Ya ce da ita.
.
"Kuma ki daina jin tsorona, halin rayuwa ya sani fadawa cikin wannan matsayin da kika same ni."
.
Hauwa ta ci gaba da kallon shi cike da mamaki, a haka idan mutum ya ganshi sai ya rantse ya kusa mutuwa, amma Kuma gashi yana magana radau har da murmushi . Lallai al"amarin wannan Tsohon akwai ayar tambaya a ciki. Hauwa ta ce dashi...?wannan
.
"sannu baba, ya jikin,"
.
Tsohon ya ce da ita.
.
"jiki yayi kyau 'yata, ke ce likitar da kika dubai?"
.
"ni ce baba."
.
Ta ce dashi ba tare da ta mayar masa da murmushin da yake yi mata ba, Wanda yafi zama abin tsoro fiye da abin sha'awa.
.
"na gode."
.
Ya ce da ita.
.
"ya sunanki yarinya?"
.
Ta ce dashi...?wannan
.
"Suna na hauwa."
.
Tsohon ya sake xura mata idanu a wannan karon cikin damuwa.
.
"sunan matata kenan, ko ina Hauwa take a halin ynx a duniya? Oho! Na san dai ni da in sake ganin Hauwa sai a darulsalam!"
.
Tsohon yayi shiru yana tunani, Hauwa ta ji tausayinshi ya kamata cikin sauri, da yake ta san tana da saurin kuka, sai ta ce dashi...?wannan
.
"rayuwa kena, sai haquri baba. Komai muqaddari ne."
.
Tsohon ya ce.
.
"wannan haka yake yarinya."
.
Har zata juya ta fice ta bar dakin. Sai ta ji Tsohon ya ce da ita cikin sauri.
.
"kakata Hauwa, Akwai maganar da nake son zamu yi ni da ke, amma sai kin mats kusa da ni. Bana so in daga muryata wadannan azzaluman ma'aikatan su ji abin da zan fada maki. Wannan sirri ne mai girma a tsakanina da ke."
.
Hauwa ta sake kallon idanun Tsohon, Akwai wani yanayi dake a tattare dashi, Wanda ya sa duk da yayi mata magana cikin natsuwa, tana shakkar matsawa kusa dashi...?wannan da yake Tsohon ya fahimci haka, sai ya sake cewa da ita.
.
"Kada ki ji tsorona Hauwa, na san abin da kika tunani a xuciyarki, kina tsammanin ko ni mahaukaci ne....! Ina da hankalin. wahalar da na sha ba ta sake na haukace ba, har ynx da hankalina. Ki matso kusa da ni in fadi maki abin dana ke so ki sani, Kada ki 6ata lkc har 'yansanda dake a waje su sake shigowa. Ke kadai ce nake son ki san wannan al"amarin
.
Hauwa ta dan matso kadan kusa dashi...?wannan
.
"yauwa to ko ke fa?k
"
.
Ya ce da ita yana murmushi.
.
"na san cewar baki sanni ba, kuma baki da tarihina. Shi yasa kike jin tsorona. To amma kina 'yansanda da suka kawo ni nan su basu jin tsorona. Lalla6ani suke yi kamar jariri. Don kuwa ina da muhimmanci a wajensu. Basu son in yi ko ciwon kai, shi yasa duk lkcn da nace bani da lfy zasu daukoni a mota jikinsu yana rawa su kawoni asibiti a yi mani magani in warke. Suna kulawa da ni kamar wani shugaban qasa."
.
Tsohon ya dan yi gajeriyar dariya, wacce bata fito sosai ba a dalilin gajiyar da yayi. Hauwa ta tambayeshi cikin mamaki.
.
"me yasa to suke yi maka haka baba, me yasa suke so ka warke, ban fahimci abin da yake faruwa ba."
.
.
Lp=9}~~~~~~{ Gobe jar Kasa }~~~~~~{
Page 9
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"me yasa suke yi maka haka baba, me yasa suke so ka warke, ban fahimci abin da ke faruwa ba."
.
Tsohon ya gyara kwanciyar sa, bayan ya cije baki da qyar, ya dubi Hauwa dake tsaye tana kallon shi.
.
"shi ne abin da nake so in fadi maki dama."
.
Ya ce da ita, sannan ya sake numfasawa.
.
"suna na Nalamma. tun ina yaro matashi na samo wannan sunan, kakata ita ce Lamma da yake a hannunta na girma sai ake ce min Nalamma
.
Tsohon ya ci gaba da murmushi ga alama ya na matuqar jin dadin wannan dama da ya samu na yin hira da wannan ma'aikaciyar asibiti. Ya ci gaba da sanar da ita.
.
"ba wani laifi nayi ba aka tsareni a gidan yari tsawon wannan lkcn Hauwa. Wataqila ki ji wasu suna cewa da ni 6arawo a waje, to amma ni na san ba sata nayi ba."
.
Wata rana ne an dauke mu aikin leburanci a wani aikin gina dam da ake yi, tun shekaru talatin da suka wuce. Ana cikin aikin sai wata mota ta gino wadansu duwatsu masu qyalqyali kamar madubi. Kafin Sauran mutane su farga na kwashe su na zuba su a ha6ar rigata na gudu.
.
Bayan na 6oyesu ne sai 'yan doka suka kamani. Tun lkcn suke tsare da ni ana tuhumata in fadi inda na kaisu, ni Kuma nayi alqawarin ko dafani zasu yi ba zan fada ba." sbd idan ma na fada wani zai je ya kwashe su, ba zasu amfani talakawa 'yan uwana ba." na sha fada musu da in fadi inda na kaisu na 6oye gara kowa ya rasa. Har in mutu ba zan fada ba! Ba irin azabar da basu yi mani ba, har sun gaji ma sun qyale ni, ynx sai dai tarairaya da lallshina in daure in fada masu inda na 6oye wadannan duwatsu masu daraja."
.
Nalamma yayi murmushi ya ce da Hauwa .
.
"ba zan ta6a fada masu ba har in mutu hauwa. Na dade ina son in samu wani mutum a cikin talakawa 'yan uwa na in fadi masa inda na 6oye duwatsun nan, to amma sun hana kowa kusantar inda nake. Su kadai suke magana da ni tsawon shekara talatin, ko ynx da sun san zan yi magana dake, ke kanki ba zasu bari ki matso kusa da ni ba." sun dauka har ynx barci nake yi shi yasa suka saki jikinsu suka barni tare da ke."
.
Nalamma ya sake qoqartawa yayi dariya da qyar, duk da zogin da yake ji a qirjinshi kamar zai rabe biyu. Hauwa dake tsaye sororo a bakinn gadon kamar gunki, ta qura masa idan ko qiftawa bata yi tana al'ajabin wannan magana da Tsohon yake sanar da ita mai kama da almara.
.
Shin da gaske ne wannan labarin da yake bata, ko kuwa dai zafin ciwon ya sanyashi sambatun hauka? To amma ai biri yayi kama da mutum, ba banza zata san haka kawai Jami'an tsaron su kawo shi asibiti da motoci uku ba, Suna gaggawar ganin an bashi magani cikin sauri don Kada ya mutu. Dole akwai wani abu da suke buqata a wajen Tsohon don haka maganarsa zata iya zama gsky.
.
Hauwa ta ji cikin ta ya duri ruwa. Ta ji tsoro ya kamata, da ta fahimci muhimmancin wannan tsoho a duniya.
.
Haduwarki da ni ya zame maki babban alheri a rayuwarki Hauwa."
.
Na lamma ya ce da ita ba tare da ya daina kallonta ba."
.
"kin samu arziqi, daga yau babu ke ba talauci a duniya, zan fada maki inda na 6oye wadannan ma'adanai ki je ki dauka sun zama naki hauwa, dama rabonki ne, shi yasa ban ta6a fadiwa kowa ba." a shekarar da aka kamani na tabbatar ba a haifeki ba." tun kafin kizo duniya suke tsare da ni.to amma rabonki ne Hauwa ba rabonsu ba ce, wannan dukiyar taki ce."
.
Hauwa ta dafe qirjinta a tsorace kamar zata fadi qasa, sbd jimamin abin da Tsohon ya sanar da ita. Dukiyarta ce?...shin yaya zata yi da irin wannan gagarumar dukiya a duniya, wacce gwamnati take son ta mallaka? Gsky sun yi mata yawa, da dai ace wani abin ne daban sai tayi farin cikin mallakarsa. Amma idan har gwamnatti zata yi shekaru talatin da doriya tana fafutikar neman wasu ma'adanai ita kanta ta san sun fi qarfinta. Ba zata iya riqesu ba,to amma duk da haka a wani 6angare na xuciyarta tana farin ciki da alqawarin da Tsohon ya yi mata. Tajikistan ta qosa ya ci gaba da magana, koda dai ba zata amfana da wannan dukiyar ba, a qalla maganar tasa Akwai dadin saurare, musamman ma da yace zata zama miloniya, zata samu arziqi mai tarin yawa.
.
Hauwa tayi qarfin halin tambayarsa.
.
"A ina ka 6oye wadannan ma'adanai baba? Zaka iya tunawa kuwa ynx.....shekarun fa Suna da yawa..."
.
Nalamma ya dan rufe idanu cikin gajiya, da alama zai iya komawa barci a kowanne lkc bayan ynx.....shekarun
.
"zan iya tuna komai Hauwa."
.
Ya ce da ita bayan yayi qoqarin sake bude idanunsa.
.
"wajen da na 6oye dukiyar ba 6oyayye bane, Kuma ynx haka na san yana nan Babu wanda hankalinsa ya kai wajen, ko shekara dari za a yi."
.
Na lamma yayi ajiyar xuciya, Hauwa ta dube shi cikin qosawa. Tana jin a tsoron kada ya mutu suna cikin yin maganar ba tare da ya fadi mata inda ya 6oye gwala-gwalai ba."
.
"to a ina ne baba? Ka ce ba 6oyayyen waje bane. Ina ne?"
.
Nalamma ya sake yin murmushi da qyar.
.
"Kada ki damu."
.
Ya ce da ita.
.
L"ba mutuwa zan yi ba, ina da sauran shan ruwa."
.
Hauwa ta ji kunyar Tsohon ta kamata, tayi shiru don kuwa ya fahimci tunanin da take yi, kamar yana duban xuciyarta. Nalamma ya bude ido sosai ya gyara murya ya ce da ita.
.
"kin san wani daji dake a nan arewacin zariya da ake cewa Tudun kudi?"
.
Hauwa ta gyada kai.
.
"eh, na sani baba, ina hangenshi a mota idan zan je unguwa, amma ban ta6a shiga ba."
.
.
.
Kun ji ni shiru kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon zazza6in da ya sarqafeni. Ynxn kamar alhamdulillah! Sauqi ya samu, na Kuma dawo gareku.
Wadanda suka san hakan sun bibiyi al"amarin har sun dubani. Na gode qwarai bisa kulawarku.
.
.
Tsohon ya ce da ita.
.
"to shiga dajin Tudun
Ku kudi ya kamaki Hauwa."
.
"idan kika je dajin kudi ki Hauwa saman tudun shi kadai ne a dajin, wani qaramin tsauni mai bisa. Na san har ynx yana nan"
.
Hauwa ta ce a dabirce.
.
"eh...yana nan har ynx..."
.
Nalamma ya ci gaba da cewa.
.
.
Lp=10}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa } ~
Page 10
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Hauwa ta dabirce.
.
"eh...yana nan har ynxn..."
.
Nalamma ya ci gaba da cewa
.
"da kin hau saman tsaunin zaki ga wani shuri a 6angaren yamma, ko an fasa shhurin zaki ga ragowar 6ur6ushinsa a qasa, sbd akwai babban rami a ciknsa. Daga gefen shurin kadan a hannun hagu, zaki ga wata qatuwar marmara, to ki daga wannan marmarar na gina rami a qasanta da kin gina ramin zaki ga jakar leda, na san ynx ta lalace, amma a cikinta na xuba gwala-gwalan, ki je ki kwashesu guda goma ne zaki samesu a ciki, sun zama naki Hauwa."
.
Nalamma ya sake yin murmushi cikin farin ciki. Hauwa tayi ajiyar xuciya ta ce dashi
.
"na gode baba, zan je."
.
Duk da yake ta yi farin ciki da labarin da ya bata, tana jin abin kamar tatsuniya ce. Ba lallai bane ta je ta samesu. Wa ya sani ma ko tuni wani ya je ya ga ramin ya tona ya kwashesu? Shekara talatin ba nan ba ce. To amma duk da haka zata je ta gani, inda rabo sai ka ga ta dace ta ga gwala-gwalan a inda Nalamma ya 6oye su."
.
"ina so in gargadeki 'yata"
.
Tsohon ya sake cewa da ita.
.
"kada ki je da kowa, ki je ke kadai, koda wani ya raka ki to ya tsaya daga nesa ya jira. Kada ki bar kowa yaga abin da kika dauko. Wannan dukiya ce mai dumbin yawa, kada ki yarda da kowa akanta!!
Mutanen duniya sun 6aci da son dukiya ki kiyaye Hauwa!!"
.
Ta ce dashi cikin ladabi.
.
"to baba na gode."
.
Tun kafin Hauwa ta gama yiwa Tsohon godiya, wasu Jami'an tsaro uku suka fado cikin dakin a kidime kamar an jefosu daga sama. Hauwa ta Ja baya a razane ta kauce daga kusa da gadon da Tsohon yake kwance. Nalamma yayi saurin rufe idanunsa kamar yana barci.
.
Dansanda daya a cikin su ya harari Hauwa ya daka mata tsawa a fusace.
.
"tun daxun me kike yi a cikin dakin baki fito ba?"
.
Hauwa ta ce dash a tsorace.
.
"ina gyara masa allurar ne, na shigo ne naga ruwan baya tafiya shi ne sai na..."
.
Tun kafin ta kai qarshe wani ya sake daka mata tsawa kamar faduwar aradu.
.
"fita ki bamu wuri, bamu yarda dake ba, kada ki sake shigowa dakin nan."
.
Kafin Hauwa ta fice ne ta ji Wanda ya fara yi mata magana ya ce da sauran.
.
"mu jira likita ya dawo ya amshi aikin. Mun sallami wannan matar daga ynx."
.
Hauwa ta fito waje jikinta yana tsima kamar zata fadi. Ta samu Sauran Jami'an tsaron suna ta kaiwa da komowa, kamar suna fareti a harabar asibitin. Daga nesa mutane ne suka firfito 'yan kallo sun yi sansani guda suna ganin abin mamakin da basu ta6a ganin ya faru ba a wata asibitin.
.
.
.
*** *** ***
.
.
.
Babi na hudu
Hauwa bata sake yin walwala ba, har xuwa lkcn da ta tashi aikin ta da yamma. Tun lkcn da Nalamma ya shaida mata wannan 6oyayyen al"amarin wanda duk duniya babu wanda ya sani sai ita, ta dawo ofishinsu tayi tagumi tana ta juya maganar a xuciyarta. Abin kamar gaske kamar kuma almara, to amma ta tabbatar maganar da wannan Tsohon ya fada mata ba almara ba ce, akwai hujjojin da dole zasu san ta yarda da maganar tsohon. Barazanar da Jami'an tsaron suka yi mata a lkcn da suka ritsa ta dakin tsohon. Ya isa ta amince duk abin da ya fadi mata gsky ne....!
.
Idan haka ne babu shakka wannan wani babban rabo ne ya fado mata, wai tsuntsu daga sama gasasshe. Babu abin da zata tsaya tana yin wasi-wasi da ya wuce ta je ta tona wannan tsohuwar ajiyar da Nalamma ya adana da dadewa.
.
To amma anya kuwa duk da dai Tsohon ya gargadeta, wannan sirrine da zata iya 6oyewa masoyinta nura? Ba zai ta6a yiwuwa ba ta 6oyewa nura wannan magana. Duk duniya bata da wani sirri da take 6oyewa nura. Ya san samunta ya san rashinta, ya san farin cikinta, haka nan kuma ya san matsalolinta. Ba zai yiwu ba don ta samu wannan dukiya, ta guji nura. Ta dade da yiwa kanta alqawarin kome ta mallaka a duniya, kowanne matsayi ta kai, ba zata guji nura ba." shi ne fada take so ta aura, ya zama mijinta har abada. To me zata samu kuwa ta qi fadi masa?
.
Lkcn da abokiyar aikinta amina ta zo misalin qarfe bakwai na yamma ta amsheta. Hauwa bata tsaya jiran komai ba, sai ta dauki jakarta cikin sauri ko hirar da suka saba yi kafin su rabu bata tsaya sun yi ba a wannan rana, don ma Kada ta gudu ne tayi laifi, amma in banda haka da tun lkcn da Nalamma ya gama bata wannan labarin. A lkc zata tafi gida tayi tunanin ta a dakinta hankalinta kwance.
.
Amina ta tambayeta saurin me take yi haka, ko gaisawa basu yi ba, zata tafi gida? Hauwa ta ce da ita.
.
"yau bana jin dadin jikina ne Amina, tun daxun dama ke nake ta jira, lkc ya yi ki zo ki amsheni in tafi gida."
.
Amina ta so Hauwa ta tsaya tayi mata bayanin wadannan 'yansanda da suka zo suka cika masu asibiti a wannan rana. Hauwa ta ce da ita.
.
"wani mai laifi suka kawo, kin san sha'anin tsaro, Suna tsoro kada ya gudu ne."
.
Duk da haka abin da mamaki, ace sbd mai laifi daya kawai a kawo wannan bataliyar Jami'an tsaro. To amma da Amina ta ga Hauwa tana sauri bata tsayar da ita ba." qawayen aikin biyu suka rabu cikin fara'a, Hauwa qarfin halin kawai take yi tana magana. Tunanin wadannan gwala-gwalai sune a xuciyarta.
.
Da ta fice daga asibitin ta ji wani abu yana raya mata, anya kuwa zata sake dawowa, ba wannan ne ranarta ta qarshe a asibitin ba?" idan ma aikin take sha'awa sai dai ta gina nata katafaren asibitin mai zaman kansa. amma ba dai ta riqa xuwa amatsayin qaramar ma'aikaciya ba." ynx kamar likkafa ga alama ta ci gaba.
.
Har Hauwa ta hau tasi a bakin titi ta nufi gida bata daina tunanin Tsohon Nalamma ba." ta so ace kafin ta tafi ta sake ganinsa ko sau daya ne daga nesa. To amma Jami'an tsaro sun yi mata iyaka dashi, basu yarda da ita ba. Aikin da ta fara yi masa sai dai likita yazo ya qarisa. Ta san shi din ma Jami'an tsaro ba zasu barshi ko da na qiftawar ido ba tare da Tsohon. Kome zai yi suna tsaye suna kallo, don kada yayi magana shi da Tsohon. A haka ake tun shekara talatin da baiyar da suka wuce.
.
Da hau ta isa gida, bata nufi dakin mahaifiyarta ba kamar yadda ta saba, Kullum idan ta dawo daga wajen aiki. Ta hango hasken qwai a dakin mahaifiyarta , in banda wannan al"amarin da ta dawo dashi a xuciyarta, da idan ta shiga dakin mahaifiyarta sai ta kai qarfe goma na dare. Koda kuwa ba zasu yi wata magana ba." ta fi son ta ci abincinta a cikin dakin, wani lkcn har ma barci ya kan kwasheta, sai mahaifiyarta ta tasheta idan zata rufe qofa.
.
Da shigar Hauwa dakinta ta jefar da jakarta akan katifarta, bayan ta ciro wayarta, hasken wayar wanda ya dan rage kaifin duhun dakin, shi ya bata damar ganin kayayyakin dake a cikin dakin, bata ci karo da komai ba, duk da yake kuwa an dauke wuta babu haske.
.
Hauwa ta nemo yar nura a cikin sauri

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment