Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bindiga. Da shigar sadi ya sanmi Tsohon a kwance, bai tsaya jiran komai ba sai ya cakumeshi ya watsashi a kafadarshi, sai a lkcn ya lura da igiyar qarin ruwa a hannun Tsohon, sadi ya kama robar ruwan ya tsinketa, ya jiya zai fice waje.
.
Nalamma bai motsa ba, duk da yake kuwa ya tabbatar Babu lfy, bai yi yunqurin yin wata turjiya ba." daga jin irin hannuwan da suka cafkeshi, ya san idan ma ya ce zai yi jayayya zai jawowa kansa karaya ne a banza.
.
Kafin sadi ya fito daga cikin dakin ne, wasu Jami'an tsaro uku, 'yansanda biyu da gandiroba daya suka juya, suka ga abin da yake faruwa. Gandiroban ya daka tsawa ya nuna mai ankwa dake a bakin qofar. Cikin sauri suka fitar da bindugu suka yi shirin sakarwa mai ankwa wuta.
.
To amma kafin suyi hakan, tuni mai ankwa ya riga ganin yunqurin nasu. Ya sakarwa Jami'an tsaron uku wuta wadanda suka kwanta a qasa, suka ba harsashin waje ya wuce ya tarwatsa wani qaramin tankin ruwa na roba dake a jikin wani daki.
.
Sadi ya na a cikin dakin bai fito ba, ya na dauke da Nalamma. Da ya ji mai ankwa yana musayar wuta da 'yansanda a waje, sai shima ya ciro tashi bindigar, ya dafe Tsohon da hannu daya, ya fito waje ya sami mai ankwa suka fara harbe-harbe tare.
.
Bayan sadi ya tabbatar sun tsorata 'yansandan duk sun xube a qasa sun 6oye. Sai ya tura mai ankwa ya ce su tafi, sadi ya shiga gaba ya fara gudu dauke da Nalamma kamar wanda ya dauki buhun totuwa. Mai ankwa ya tsare masara hanya yana binsa da baya da baya. Yana duba wanda zai biyosu, ya sakar masara wuta.
.
Sauran Jami'an tsaron da suka je taimakon kashe gobarar, jin harbe-harbe sai hankalinsu ya dawo 6angaren Nalamma. Da yake hayaqi ya turniqe asibitin, da Kuma hayaniyar mutane, wannan ya sakar basu samu damar hango su sadi ba, wadanda suka yi nisa, suka kusa ficewa daga asibitin.
.
Jami'an tsaron dake a akwance sun 6oye, suka sake dagowa suka fara harbi a lkc guda. Da yake mutane sun fara tsorata suna ta guje-guje a ko ina, sai suka tsayar da harbin don gudun kada su sami wani a cikin mutanen dake a asibitin.
.
Babban Jami'in 'yansandan wanda shima yana daga cikin wadanda suka je wajen gobarar, ya fara dakawa 'yansandan tsawa, don kuwa ya fahimci abin dake faruwa. Duk da haka bai yarda ba, sai da ya fada cikin dakin da Tsohon yake, ya iske Babu komai sai tsurar gadon, dansandan yayi kururuwa ya san in har suka barin Nalamma ya 6ace, su dukkansu Suna cikin Hadari.
.
Ya fito waje ya fara ba 'yansandan barni cikin qaraji su bi sawun 6arayin da suka sace Tsohon. Jami'an tsaron suka bi su mai ankwa, Suna cin karo da mutanen da suke shigowa cikin asibitin don su kawo daukin gobarar da suke hange daga nesa.
.
Wutar ta kama dogon dakin sosai, ta fara toroqo xuwa sama tana miqae harshenta tana taso abubuwan da take iya samu. Aka fitar da marasa lfyn, aka nesanta su daga inda wutar take ci. Tuni har an yiwa Jami'an kashe gobarar waya sun kamo hanya Suna take.
.
.
'yansandan da suke gaba wajen bin sawun 6arayin, suka fara hangssu a lkcn da suka fita daga asibitin. nan da nan suka qara qaimi don ganin sun cimmusu sun kama su kafin su yi nisa.
.
Tun kafin su sadi su qariso, tuni har Shago ya bude masu qofofin motar, yana a zaune yana ba motar wuta yana jiran xuwansu. Sadi da yake a gaba shi ya fara xuwa wajen motar, ya jeff Nalamma a 6angaren baya ya fada ciki kusa dashi...?wannan mai ankwa ya nufi 6angaren gaba inda Shago yake. Kafin ya shiga motar ne Jami'an tsaron da suke bin su aguje suma suka fito daga asibitin.
.
Dansanda daya ya budewa motar wuta a lkcn da suka ci taya suka cilla aguje. To sai dai kuma harbin bai tashi a banza ba, don kuwa ya....
.
.
Lp=15}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 15
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Dansanda daya ya budewa motar wuta a lkcn da suka ci taya suka cilla aguje. to sai sai Kuma harbin bai tashi a banza ba, don kuwa ya sami mai ankwa a cinya. Sautin tashin motar da Kuma qarajin da mai ankwa ya yi a lkcn da harsashin ya sokeshi, ya gauraye ya bayar da yanayin da mutum zai ji a sansanin yaqi.
.
Kafin 'yansandan su sake yin wani yunquri, tuni motar 6arayin tayi nisa. Duk da haka basu yi nisa a guiwa ba, a cikin minti daya har sun fito da nasu motocin uku dake a harabar asibitin. motocin 'yansandan suka Hau titi suna 6urari a yayin da Jami'an tsaron suka riqa leqowa da bindigoginsu waje.
.
Mutanen dake akan titi suka riqa darewa, ababen hawa Suna sauka qasa. To amma har suka yi nisa basu hango ko inuwar motar 6arayin ba."
.
Babu shakka a wannan karon an sace Nalamma dan Tsohon da kowa yake buqatar ya mallake shi don ya bashi wani labari da ya 6oye tun shekaru talatin da suka gabata.
.
.
.
***
.
.
.
Tafiyar minti arba'in a babur din ya kai nura da Hauwa dajin tudun kudi, daga inda tsaunin yake tsakaninsa da titi, akwai tafiyar kilo-mita daya wacce wata siririyar hanya ta keta ta cikin gonaki, ta doshi yamma har xuwa kan tsaunin.
.
Yawancin manoma suke bin hanyar da kekunansu da kuma leburorin da suke xuwa su sari icce da rana a saman tsaunin. lkc-lkc motocin sukan bi hanyar, to amma yawancinsu motocin kaya ne manya wadanda suke shigowa dajin su dauki itace da kuma amfanin gona idan kaka ta yi.
.
Manyan tayoyin motocin da suke shigowa yau da Kullum sun tsaga hanyar gida biyu. A tsakiya Kuma inda tayoyin basu takawa, dogayen ciyayi ne suka fito suka yi tsawo irinsu tsintsiya, wuta-wuta da kuma tuji.
.
Nura ya saki titin da suke kai ya hau siririyar hanyar ya shiga dajin, fitilar babur din ta taimaka masa wajen ganin nesa, tun kafin su kai inda tsaunin yake yana iya hango itatuwa da bishiyoyi, wadansu an sare su suna yin sabon toho, wasu kuma Suna nan a yadda suke, Suna ta kada reshikansu a cikin saurayin daren.
.
Giza-gizan dake a sararin samaniyar ynx sun sake dawowa sun lulli6e faffadan farin watan wanda ya cika fal. Idan wani gutsiren gajimaren ya zame jikinsa hasken ya baiyana, ba dadewa sai kuma wani ya sake xuwa ya rufe watan. Don haka hasken bai zauna daram ba, har zuwa ynx.
.
Hauwa dake zaune dafa'an a Bayan babur din, ba sanyi yafi damunta ba a halin ynxn, don sanyi anan sanyi, musamman ma bayan shigowarsu dajin. To amma tsoro da fargaban xuwansu dajin ya kawar mata da sanyin, iska ta ture gyalenta da ta yafa a jikinta, ynx tana riqe da gyalen ne a hannunta.
.
Kukan qwari ya cika ko ina a cikin gonakin da suke wucewa, dangin su tsanya da maqyesu. Akwai Kuma wadanda suke tashi suna yawo a iska Suna barazanar fadawa Hauwa a cikin idanu, kamar su barbaje da barkonun tsohuwa. Sau biyu kunamar gero tana fado mata a fuska, Hauwa ta na kai hannu tana bugewa cikin damuwar kasancewa a wannan hali, a irin wannan lkcn da ya kamata ace tana can a dakinta a kwance tana hutawa, ko Kuma tana hira da mahaifiyarta.
.
Nura aljan bai damu da duk wadannan abubuwan ba." hankalinsa yana akan wadannan gwala-gwalai da Hauwa ta bashi labarin Nalamma ya fada mata suna a saman tsaunin inda ya binne su, ba wanda ya sani. Ya riqa qugawa babur din wuta babu saurarawa, yana hawa kan ciyayi da kwazazzabai, da kuma kui6in bazawara.
.
Kasancewar dare yayi, halittu da yawa sun fito shan iska, nura ya riqa taka jerin gwanon cinnaku da suke ratsa hanyar, da kuma dodunan kwadi wadanda basu fito daga cikin kwansa ba." tayoyin babur din sun kashe rayukan tana da rozozo babu adadi, to balle kuma su qadandoniya mai qafa dari, da su hajiyar makka, wadannan duk ba tasu ma ya ke yi ba."
.
Da hanyar ta zo qarshe Babu yadda za ayi babur din ya hau saman tsaunin, sai nura aljan ya saurara da gudun ya rage wuta. Ya tsayar da babur din a kusa da wani qaramin iccen faru da aka sare.
.
Hauwa ta suko da taga ya kashe babur din, ta duba kowanne 6angare ba gida gaba ba gida baya, babu alamar wani bil'adam sai su kadai a tsakiyar dajin. Ta ji tsoro ya sake kamata, ko ya suka motsa sai tsuntsaye su furgita su fara kuka a cikin ma6oyarsu dake a ko ina a cikin daruruwan bishiyoyin dake a wajen.
.
Nura ya kafe babur din ya kalli Hauwa wacce in banda fararen idanunta dake yawo Suna motsawa a cikin duhun, babu abin da mutum zai gani a tattare da fuskarta ya fahimci halin da take ciki.
.
"gamu mun zo Hauwa."
.
Ya ce da ita.
.
"zaki iya gane kwatancen da ya yi maki daga nan kuwa?"
.
Hauwa ta girgiza kai a sanyaye,
.
"ya ce da ni a saman tsaunin wurin yake, kusa da wani shuri."
.
Nura ya ce da ita cikin sauri.
.
"zo mu hau saman tsaunin, indai shurin yana nan har ynx, ai wajen da ya rufe gwala-gwalai ba zai yi wahalar ganewa ba, tunda ya ce a kusa da shurin ramin yake."
.
Hauwa ta yi shiru bata ce komai ba." nura ya sake hannu ya fizgo qatuwar digar haqa ramin da ya sako a bayan babur din, ya ciro cocila a aljihunsa, ya haska don kuwa lullumin da ake yi a sararin samaniyar qara haduwa yake yi, ya zama qaramin hadari wanda indai ba wani ikon allah ba da wuya a yi ruwa a daidai wannan lkc.
.
Nura ya shige gaba yana haska inda zasu taka. Hauwa ta bishi a baya tana dora qafarta inda ya cire. Suka fara hawaye kan tsaunin suna wuce kututturen itatuwa, da Kuma kargo wanda ko ba a tona ba da wuya a rasa miyagun macizai a cikinsa, irin su tsadaraki da su gajera uwar azaba, har xuwa su jannashuri da danbida. To amma tunda dai ba tsokanarsa saurayi da budurwar suka zo yi ba, suna a cikin ganyaye a kwakkwaance basu damu da motsin tafiyarsu ba, musamman idan sun taka busassun ganyaye.
.
Tsaunin yana da bisa sosai, don kuwa tun kafin su kai qololuwa, da hauwa ta waiga baya sai ta ga gonakin duk sun yi qasa, tana iya ganinsu fulilu kamar an shimfida tabarmu. Daga nesa can kuma danjojin motoci ne da fitilunsu akan titi Suna kiliya, wasu suna dawowa. Motocin sun koma kamar kwaduna, titin Kuma kamar an shimfida baqin zare.
.
Hangen motocin da tayi ya san ta ji tsoron dake damunta ya ragu. Don haka ko ba komai tana iya ganin wani abu da take gani a gari, daga saman tsaunin maimakon tsuntsaye da qwari da kuma qananun dabbobin da suke gilmawa ta gabansu aguje, wadanda suke xullumin wataqila mafarauta ne da suke yawan takura musu.
.
Hankalin zomaye da kurege yafi na kowa tashi, don kuwa sun san sun fi komai farin jini a wajen mafarauta. To amma ba su kadai suke guduwa ba a dalilin motsin tafiyar saurayi da budurwar, hatta bushiya ma ba a barta a baya ba, wajen neman mafaka. Wani dam, da wata gafiya suka fara rige-rigen fadawa wani babban rami da nura ya matso kusa dashi...?wannan sai dai kuma sun yi kasada don kuwa tsautsayi yana iya hada su da kasa ko yanyawa a cikin ramin basu sani ba."
.
Nura da Hauwa suka ci gaba da tafiya har xuwa lkcn da suka kai qololuwar tsaunin, da xuwansu nura ya fara haska cocilarsa, kowanne h6angare, suna bin inda hasken ya nufa tare, Suna qoqarin ganin daya daga cikin abubuwan da Nalamma yake za a gani a saman tsaunin. Nura ya ce.
.
"to gashi dai ba wani shuri a nan."
.
Hauwa ta ce dashi cikin sauri.
.
"dama na fada maka ya ce da ni, me yiwuwa ynx babu shurin tunda an dade, mu duba ko zamu ci sa'ar ganin ragowar qasar shurin..."
.
Nura ya ci gaba da haska cocilar, ya fara kaiwa da komowa, yana duba wurare daba-daban akan tsaunin, Hauwa ta tsaya waje guda a wannan karon bata bi shi sun duba tare ba, don kuwa qafafuwanta sun gaji. Ta jingina da wani gajeren iccen wanda aka qonashi da ranshi.
.
.
Lp=16
Lp=11

}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 16
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ta jingina da wani gajeren icce da aka qonashi da ranshi, ya bushe yayi baqi. Tunanin da ya fara darsuwa a xuciyarta shi ne, ya zata yi da ranta idan basu samu nasarar samo inda wannan dukiya take ba, a saman tsaunin? Ita bata damu ba, nura take ji kada yayi fushi ya ce ta basu wahala a banza, sun zo dajin basu samu komai ba."
.
Hauwa ta ci gaba da tsayuwa cikin xullumi tana kallon nura, wanda ya juya mata baya daga nesa kadan, yana duba wani waje, wanda yake da duhun qananun itatuwa. Da Hauwa ta ga nura ya dade a wajen bai qara gaba ba, ya tsaya yana nazarin wani sashin da ya haska da cocilarsa.
.
Sai ta taso daga jikin iccen da ta jingina. ta matsa xuwa inda nura yake tsaye, tun kafin ta qarisa wajen ta tambayeshi.
.
"ka gano wajen ne nura?"
.
Ya ce da ita ba tare da ya juyo ya dubeta ba."
.
"ina jin haka, akwai alamar qasar shurin a nan...amma ya dade da rugujewa."
.
Ya haska wani qaramin fili da cocilarsa wanda babu ciyayi ko itatuwa a wajen, sai dai farar qasa da kuma ramin gara inda ya huhhuje, amma Babu gara a halin ynx, ko kuma tana a ciki tana huce gajiyar zirga-zirgar da take yi a kowacce rana.
.
Nura ya dauke hasken cocilar daga inda gidan garar yake, ya fara haska Sauran abubuwa dake kusa da wajen. Akwai wani icen ararra6i, daga 6angaren dama, sai kuma itatuwan kanya da ta watsa daga 6angaren hagu. A can gaba kadan ne nura ya haska sai ya hasko wata qatuwar marmara wacce ke 6oye cikin ganyen wani qaramin iccen dargaza wanda ya sakii yado ya rufe abubuwan dake kusa dashi..
.
Nura yayi murmushi ya ce da Hauwa
.
"nan ne wajen da ya 6oye gwala-gwalan. ga marmarar da ya fada makin can a cikin ganye, har ynx ba a dauketa ba."
.
Hauwa ta ji gabanta ya fadi, tayi ajiyar xuciya, wannan abu da ya faru ya girgiza tunaninta. Babu shakka wannan tsoho bai yi mata qarya ba." tun kafin ta motsa daga inda take nura ya nufi inda marmarar take. Da xuwanshi ya ajiye digar dake hannunsa a qasa, ya sakii cocilarsa a baki ya riqe da haqoransa, ya haskawa kanshi, a lkcn da ya sa hannayensa biyu ya kama marmarar ya fara qoqarin tun6uketa daga inda take kafe shekara da shekaru.
.
Marmarar ta kafe sosai a qasa, nura ya runtse idanunsa ya sake jajircewa ya sa qarfinsa yana girgiza qatuwar marmarar, wacce ta fara rawa tana yin sakwa-sakwa. A qarshe sai nura yayi nasarar tun6ukota, ya rabata da wajen zaman nata ya tureta gefe guda, suka tafi tare, sauran qiris ya fadi.
.
"ka bi a hankali kada ka ji ciwo nura."
.
Hauwa ta ce dashi cikin xullumi. Wacce take tsaye tana kallonshi tun sanda ya fara kokawa da marmarar. Ga alama nura baya buqatar taimakonta ynx, ko cocilar bai bata ta riqe masa ba." ya mayar da hankalinsa baki daya akan gwala-gwalan shi kadai tun lkcn da ya gano wajen.
.
Nura bai huta ba,ya dauko digar da ya ajiyeta a gefe guda, cocilar tana a bakinsa har ynx, ya ci gaba da haska inda ya qwaqulo marmarar, qananun qwari barkatai dangin kiyashi da damina wadanda suke rayuwarsu a qarqashin marmarar suka fara guduwa, Suna darewa. Lkcn da hasken cocilar ya tona asirin muhallinsu wanda Babu wani mahaluqi da zai ce ga iya adadin shekarunsu a wajen, sai Buwayi gagara misali, Masanin sirrin duk wata halitta dake a 6oye ko bayyane.
.
Nura bai tsaya sauraren watsewar kiyasan ba,ya ya dauki digar da hannu biyu ya fara sara gurbin da ya zaro marmarar, duk lkcn da ya saro qasar sai ya janyota waje da tsinin digar a cikin dan lkc qanqani yana ta ginin ramin bai gama ba,ya gina babban rami mai fadi. Hauwa wacce tayi tagumi a gefe guda tana kallonshhi ta ce dashi a karo na farko, tun fara aikin ginin ramin.
.
"katsaya ka huta nura."
.
Nura ya ci gaba da haka ramin ba ji ba gani. Kamar bai ji maganar da tayi ba." yana cikin haqan ramin ne a wani sara da yayi, sai tsinin digar ya funciko wata ru6a66iyar leda. Nura ya rude ya ajiye digar a gefen ramin, don kuwa ya fara ganin alamar abin da suka xo nema. Ya durqusa bakin ramin, hasken cocilar dake kafe a bakinshi ya sake fito da ledar fili. Wacce ta ratattake ta fara ru6ewa.
.
Nura ya sake hannu biyu ya fara tono ledar, kamar wanda yake qwaqulo dankali, yana tono ledar tana ffitowa sarari. Hauwa ta matso kusa dashi tana rungume da hannuwanta, ga alama ita bata xumudin abin da ya fara tonowa, don kuwa ji take yi kamar a maqabarta suke.
.
A daidai lkcn da nura ya janye wasu 6aragusan qasa biyu, sai wasu abubuwa dake kama da duwatsun gilashi suka fara bayyana. Hannayensa suka fara kyarma, ya fara ciro duwatsun dake qyalqyali waje, ya ajiye guda uku a bakin ramin. Hauwa dake a bayansa ta riqe numfashinta a kidime da ta ga nura ya fara ciro gwala-gwalan daya bayan daya a cikin ramin.
.
"su ne...nura, ashe Suna nan a cikin ramin babu wanda ya kwashesu.
.
Nura bai juyo ya dubeta ba,ya ya ci gaba da zaqulo gwala-gwalan wadanda suke kama da duwatsu qanana. Sai da ya tono guda goma sannan ya daina ganinsu. bayan nura ya gama tarasu a bakin ramin ne ya sake mayar da hankalinsa wajen namin da hannuwansa, da fatan samun wasu. A lkcn ne Hauwa ta ce dashi...?wannan
.
"su kenan nura, dama ya ce da ni guda goma ne, ka qirgasu ka gani sun kai. Babu saura."
.
Sai a wannan karon nura ya waiwaya 6angaren da take, ya dubeta, da yake cocilar tana a bakinsa haskenta ya sa an razananniyar fuskarta. Nura ya cire cocilar daga bakin sa ya riqeta a hannu, ya sake haska gwala-gwalan wadanda suke dube a qasa, fararen tas! Nura ya shafasu da hannuwansa. Ga mamakinsa akwai zafi a jikinsu kamar ba daga jiqaqqiyar qasa aka tonosu ba." hauwa wacce to qosa su bar dajin ta ce dashi...?wannan
.
"ba tsayawa zamu yi ba nura. Kwashe su zamu yi mu koma gida, idan muka koma duk wata magana sai muyi a can, sai mu tattauna yadda zamu yi dasu a 6oye."
.
Shiru nura yana a durqushe, ga alama wani abu yake tunani a xuciyarsa. Bai cire hannunsa daga kan gwala-gwalan ba." hauwa ta sake daga muryarta don ta dao dashi hayyacinsa,
.
"nura ka taso mu tafi gida, na gaji da dajin nan, na fada maka tsoro nake ji. Kwaso mana gwala-gwalan nan in xubassu a a cikin gyalena mu 6oyesu mu tafi gida."
.
Nura ya ci gaba da tunani, bai cewa Hauwa komai ba,ya yana a durqushe a bakin ramin. Wani faffadan gajimare ya kauce daga inda yake a sararin samaniya, ya ba farin watan damar warwatso tataccen haskensa a ko ina a duniya. A lkcn ne nura ya sake juyowa ya dubi Hauwa suka hada idanu, ynx tana iya ganin abin dake tattare a fuskarshi, sbd hasken farin watan da ya bayyanar da komai a wajen.
.
Tsoro ya sake kama Hauwa da taga fuskar nura ta canza, Akwai wani irin kallo dake tattare da idanunsa mai ban tsoro, wanda Hauwa bata ta6a ganin yayi mata irin sa ba,ya a duk zaman da suka yi na shekara da shekaru. Hauwa ta bude baki cikin razana, kafin ta sake yin magana ne ta ga nura ya jawo qatuwar digar da ya haqa ramin ya miqe ya nufi inda take.
.
Da Hauwa ta ga kallon da yake yi mata bai sauya ba,ya sai ta Jami'an baya a tsorace, ta fara alamar fashewa da kuka.
.
"nura me yake faruwa? Me ye haka naga ka dauko diga kana kallona, don allah me ye haka?"
.
Nura ya sake matsowa yana kallonta, ya ce da ita.
.
"kada ki ba kanki wahala Hauwa, kin san abin da nake nufi. Kashe ki zan yi in mayar dake cikin ramin nan, in rufeki a ciki, don kuwa ni kadai nake so in mallaki wadannan gwala-gwalan, kuma bana son kowa ya sani. Dole ne in kashe ko in binneki ba tare da kowa ya sani ba." ki tsaya in kashe ki a hankali Hauwa kada ki ba kanki wahala!"
.
Hauwa ta dora hannayenta akanta, ta fara rusa kuka kamar ranta zai fita. Ta Jami'an baya a furgice, nura ya sake biyota riqe da qatuwar digar yana kallonta......
.
.

<>karshe<>
Mu hadu a littafi na biyu animal kadan bayan sallan la'asar. Idan mai duka ya kaimu.
.
Godiya ta tabbatar ga Aallah (swa) wanda ya bani ikon kawo maku qarshen littafin gobe jar kasa na 1.
.
Kuma biyo ni a "TASKAR GIDAN LITTAFI" don jinjinawa ci gaban labarin a yammaCi.
.}~~~~~~{ Gobe jar kasa 2}~~~~~~{
Page 017
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Labarin sace Nalamma da wasu 6arayi suka zo asibiti suka yi, ya sami shugaban gidan yarin ne a mintoci goma bayan da aka tabbatar 6arayin sun 6acewa Jami'an tsaro, Kuma babu wanda ya san inda suke a halin ynxn.
.
Kwantirola janar musa sabo, wanda yake zaune a falonsa, yana riqe da wayarsa a kunne, ya fara yiwa gandiroban da ya sanar dashi labarin 6urari yana cewa.
.
"duk inda suka shiga Ku je ku nemo su, nan da awa daya. Me kuke yi da har zaku bari a sace shi, kuna tsaye kuna kallo? Don kada a sami matsala ne fa, na aikawa Dpo ya bani yaran takwas na hada su da ku, don su taimake ku ku tsare mana shi har ya sami lfy."
.
Gandiroban dake sanar da shugaban nasu labarin a can 6angaren ya ce dashi cikin nadama.
.
"wuta suka hada a cikin asibitin don su dauki hankalinmu.
.
Kwantirolan ya katse shi ta hanyar daka masa tsawa.
.
"ba ruwana da yadda suka yi wajen sace shi, abin da kawai nake nufi shi ne, da ku da police din da kuka yi sakaci har 6arayin suka saceshi. Ku je ku nemo su ko a ina suke. Idan kuka kuskura kuka barsu suka yi nisa baku gano su ba, bayan rasa aik ku da zaku yi, sai kun fuskanci fushi mai tsanani."
.
Ya kashe wayar a fusace yana zare idanu. Kakkauran ma'aikaci ne mai kimanin shekaru hamsin da biyar a duniya, Kuma ya kai kimanin shekaru hudu riqe da wannan muqami na shugaban gidan yarin. Tun lkcn da ya samu labarin Nalamma bashi da lfy, hankalinsa bai kwanta ba, don kuwa duk wani abu da zai shafi rayuwar wannan tsohon, Suna kaffa-kaffa da wannan al"amarin, sbd sun san muhimmancin sa da kuma abubuwan dake tattare dashi.
.
Musa sabo ya tashi cikin sauri ya shiga dakinsa ya canza kayan jikin sa. Ya dawo falon ya dauki wayarsa ya kira lambar jami'in 'yansanda na shiyyarsu, wato eriya kwamanda tanko dan asabe. Da lambar ta shiga ne, aka dauki wayar, sai jami'in tsaron ya ce da Kwantirola cikin raha kamar yadda suka saba wasa.
.
"mai 6arayi ya aka yi ne?"
.
Musa sabo ya ce cikin sauri.
.
"ba lfy! Kana ina ne?"
.
Eriya kwamanda tanko dan asabe ya kausasa muryarsa ya cire wasan da ya fara yi, ya dawo kan aiki."
.
"me yake faruwa kuma?"
.
Musa sabo ya ce dashi...
.
Nalamma aka sace a asibiti. Tsohon 6arawon nan da yake furzin tun shekaru talatin, wanda ya qi fadar inda ya 6oye ma'adanan nan...shi ne 6arayi suka sace shi."
.
Jami'in tsaron ya tambayeshi.
.
"ya aka yi kuka bari haka ta faru musa sabo? Bayan kun san muhimmancin sa? Ya kuka yi sakaci dashi?"
.
Kwantirola musa ya hadiye qululun da ya tsaya masa a maqoshinsa kafin ya ce.
.
"ba sakaci muka yi ba tanko, 6arayin sun shammaci yaranmu ne da kuma naku yaran da muka nemi taimakonsu a lkcn da zamu kaishi asibiti. Kana dai ina ne ynx in zo muyi maganar a tsanake, don mu san ya zamu yi mu gano 6arayin tun kafin su yi nisa?"
.
Eriya kwamanda ya ce.
.
"ynx haka ina ofis, ka zo zan yiwa kwamishina waya in sanar dashi

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment