Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau qarqashin gabatarwar 'yar uwa rahmert khaleel zazzau. Ku kasance tare da "TASKAR GIDAN LITTAFI" a kodayaushe domin nishadinku a kowacce rana.
.
Sai da kusan ma'aikata goma suka shigo dakin jinyar, sannan kuma sai 'yansanda uku suka tako masu baya dauke da wani motsattsen Tsoho fari qwal dashi.
.
.
Anjima kadan zaku sake tsinkayar shafi na gaba inshaa allah.
.
Lp=4}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa }~~~~~~{
Page 4
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Sannan sai ga wasu 'yansanda uku dauke da wani motsattsen tsoho fari qwal dashi, kamar gawa. In banda idanun tsohon dake harbawa lkc xuwa lkc kamar idanun 'yar tsana, babu wani abu dake iya motsawa a jikinsa. Kanshi ya qoqe babu gashi sai guntayen furfura, kayan jikinsa na fursuna sun yi datti, maimakon farare sun koma kalar kunun kanwa.
.
Tsohon zai iya zama komai tsakanin shekara saba'in xuwa saba'in da biyar. A bushe yake kamar qwarangwal, duk qasusuwanshi sun fito ranbatsau, Wanda ko mutum bai yi tambaya ba, ya san wannan Tsohon ya dade yana fama da yunwa da kuma azaba iri-iri a rayuwar da yayi a gidan yari.
.
Hauwa tana tsaye tana kallon su, Sauran mutanen dake a dakin 'yan jinya duk suka miqe tsaye cikin furgici domin kuwa idan mutum ya shigo yaga yadda dakin ya cika da Jami'an tsaro sai ya rantse da allah yaqi ne ya taso a cikin asibitin.
.
Tun kafin Hauwa ta samu damar tambayar abin dake faruwa, wani babban jami'in gandiroba mai qirar 'yan kokuwa ya ce da ita.
.
"mun kawo marar lfy ne, ina likita yake?"
.
Hauwa ta ce dashi.
.
"likita ya fita."
.
Ta ci gaba da kallon su daya bayan daya kamar aljanu sun kawo mata ziyarar bazata.
.
Wani sajan din 'yansanda ya ce cikin fushi.
.
"ba sai likita yana nan ba, ita aikin me take yi? Ta duba mana shi mana kafin likita ya zo."
.
Ya waiwaya 6angaren da Hauwa take tsaye ko motsi bata yi, ya ce da ita cikin barazana.
.
"muna buqatar daki na musamman guda daya, ba zamu iya ajiyeshhi a nan ba, sbd sha'anin tsaro, ina zamu kai shi? Ki yi sauri ki duba mana shi, ya kusa mutuwa ne....! muna buqatar ya ci gaba da rayuwa ba ynx muke so ya mutu ba."
.
Ga alama dan sandan yayi maganar ne cikin barazana. Sai da yayi murmushi da ya kai qarshe. ganin duk Jami'an tsaron su kusan goma sha bakwai sun xuba mata idanu, kamar zasu cinye ta, sai Hauwa tayi saurin tattara tunanin ta waje guda tace dasu
.
"Akwai dakin da muka ware na musamman yana a waje kusa da (maternity ward) ku xo muje ku kwantar dashi a can."
.
'yansandan da suka tare hanya suka bata wuri ta shige gaba cikin sauri, suka bi ta a baya, Suna kaffa-kaffa da motsattsen Tsohon da Jami'an tsaron uku suke dauke dashi, kamar Suna tsammanin wani abu zai xo ya ffuxgeshi ya tashi dashi sama.
.
Bayan sun fita waje ne sun kama hanyar xuwa dakin da Hauwa zata kaisu, Suna biye da ita buu! Kamar qudaje sun biyo tiren alewa, sai mutanen dake cike a dakin jinyar suka riqa leqowa ta tagogin asibitin Suna kallon abin mamaki. Don kuwa ko Gwamna aka kawo asibitin iya kulawar da Jami'an tsaron zasu bashi kenan, amma kuma bisa mamakin duk wadanda abin ke faruwa akan idonsu, wani tsoho ne tukuf daga gidan yari, ko me yasa Jami'an tsaron suke kaffa-kaffa dashi...?wannan Kuma wani sirri ne da ya shafi aikinsu.
.
Hauwa ta kai su dakin da zasu kwantar dashi, wanda duk da yake qarami ne, yana dauke da gado da kujeru biyu, da kuma teburi mai bisa na ajiyar magunguna. Jami'an tsaron da suka kinkimo tsohon suka shimfidar dashi a hankali kamar qwai, kamar suna tsoron Kada qasusuwanshi su kareraye.
.
Sajan din 'yansandan da yayi magana daxu, ya matso kusa da gadon cikin xullumi ya tambayi Hauwa.
.
"kina jin zai rayu kuwa likita? Duba shi ki gani, yana numfashi...?"
.
Ganin yadda Jami'an tsaron suka qosa da farfadowar Tsohon sai Hauwa tayi gaggawar komawa babban dakin jinyar ta dauko kayan aiki, da xuwanta ba tare da ta cewa Jami'an tsaron komai ba, da suka yi cirko-cirko, wadansu waje wadansu Kuma a cikin dakin, sai ta fara 'yan gwaje-gwajen numfashin tsohon, da kuma bugun xuciyarsa.
.
Tsohon yana a kwance magashiyan ya bude baki. Idanunsa rabi a bude, rabi a rufe, cikin sauri Hauwa ta ciro ledar ruwa ta za6ii wata faskekiyar jijiya dake a bayan hannun Tsohon ta kafa masa allura ta jona da ledar ruwan, wacce ta sagaleta a jikin tagar dake a dakin.
.
Bayan ta jawo allurai ne ta kwararawa ledar ruwan, sai Kuma ta sake fasa wasu kwalaben alluran ta kwararawa Tsohon a duwawu Sau biyu a jere. Duk abin da take yi 'yansanda da gandirbobin dake kan aiki suna tsaye suna kallonta.
.
Hauwa ta kammala aikin da zata ta iya yiwa mara lafiyan. Ta juyo ta dubi Jami'an tsaron ta ce dasu.
.
"ba matsala zai rayu in allah ya yarda. Damar rashin ruwa ne yake damun sa, shi ya haifar masa da zazza6i mai zafi, amma zai samu sauqi ya farfado nan ba da jimawa ba." yana buqatar Ku bashi wuri ya dan sami wadatacciyar iska."
.
Jami'an tsaron suka dan saki ransu. Wani gandiroba yayi murmushi ya ce da ita.
.
"kin yi qoqari, a dalilinki idan wannan tsoho ya farfado wataqila a yi maki qarin girma ki zama babbar likita. Don kuwa rayuwar wannan tsohon da kike gani daidai take da wani 6angare na arziqin qasar nan."
.
'yansandan dake tare da da gandiroban da ya yi maganar suka qyalqyale da dariya. Hauwa ta dubesu cikin rashin Fahimtar yadda za a ce rayuwar wannan mokadadden Tsohon dake kama da lemun tsami, wai daidai take da wani arziqin qasa.?
.
A tsammanin Hauwa iya shege Jami'an tsaron suke so su yi ma ta...." ta yatsina fuska cikin ko in kula, ta kwashe kayan aikinta ta fice daga dakin, ta bar Jami'an tsaron tare da qwarangwal din Tsohon da suke gadi.
.
.
.
** **
.
.
Duk wannan al"amarin da yake faruwa mati mai shara yana a tsaye daga can nesa yana baiwa idanuwansa abinci. Tun xuwan Jami'an tsaron asibitin dauke da Tsohon ya samu wuri a doguwar barandar dake lulli6e da hanyar shiga sashin jinyar, ya dafa qarfen barandar cikin al'ajabi yana kallon yadda 'yansandan suke ta kaiwa da komowa. A cikin barazana, Wanda a tarihin wannan aasibiti tun daukarsa aiki kusan shekara goma-sha uku kenan, shi dai ko sau daya bai ta6a ganin an kawo wani mara lfy tare da Jami'an tsaro haka ba, Kowanne.
.
.
Lp=5}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa }~~~~~~{
page 5
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Shi dai ko sau daya bai ta6a ganin an kawo wani mara lfy da Jami'an tsaro haka ba, ko wane ne....!
.
Bayan komai ya lafa da mati yaga Hauwa ta fito daga dakin da ta kwantar da tsohon ta kwaso kayan aikinta na gwaje-gwaje ta koma ofishinsu na ma'aikatan jinya, sai yayi ajiyar xuciya ya fara tunanin xuwa ya same ta don suyi magana. Yana son ya ji dalilin da zai sa Jami'an tsaro su cika masu asibiti daga kawai sun kawo wani ramammen tsoho fursina.
.
To amma Kuma da mati yaga 'yansanda sun tare ko ina babu hanyar wucewa, ko kusa da inda harabar dakin da tsohon yake basu yadda wani ya matso ba, sai ya haqura ya bar tambayar da zai yi a cikin sa, don kuwa a rayuwarsa babu abin da yafi tsoron gani tun yana yaro irin bindiga. 'ba ta da kyan gani' haka ya sha fada idan yana cikin dattawa 'yan uwansa Suna hira.
.
Da yake abin yana cizonsa, yana buqatar ya samu wanda zasu tattauna akan wannan al"amarin da yake faruwa. Sai mati ya zagaya ta baya, ya kaucewa dandazon 'yansanda da gandirobobin, ya bi ta bayan dakunan jinyar, inda ke surqume da ciyayi, da ledojin da majinyata ke jefowa ta taga daga cikin dakunan. A haka har ya samu ya 6ulla ta can qarshen asibitin, ya zagayo ta jikin katanga ya zo inda wani tsoho ya saba zama a gindin wani qaramin iccen mangoro dake fuskantar qofar shigowa asibitin.
.
Mati ya saba zama da dan Tsohon wato Kallamu mai gadi. Da yake shine sa'ansa a cikin ma'aikatan asibitin, kuma da yake duk matsayin su daya, mai gadi ne da mai shara. Tare suke wuni Suna hirar duniya, da kuma 'yan tsegunguni na yau da Kullum da suke faruwa a asibitin.
.
Tun kafin mati ya qariso inda kallamu mai gadi yake zaune akan bulon siminti yana gyara cocilarsa don kada ta sake yi masa gardamar da ta saba yi idan dare yayi, Tsohon ya dago ya kalle shi da yaji alamun tafiyarsa.
.
"kai! Daga ina kuma naga ka biyo ta baya haka mati?"
.
Mati ya qariso inda kallamu mai gadi yake ya tsugunna a gabanshi cikin qosawa.
.
"ba dole in yi zagaye ba Baba kallamu, kawai muna zaune lfy an cika mana asibiti da kwalawa sai ka ce bataliyar yaqi, ni na rasa ganesh kan wannan al"amarin fa."
.
Kallamu mai gadi ya bushe da dariya.
.
"to kai 'yansanda kake jin tsoro mati? Ba aikinsu suka zo yi ba? Ina ruwansu da kai tunda kaima aikin ka kake yi?"
.
Mati yaga hirar tasu ta dan yi tsawo, sai ya zauna a qasa inda babu tsakuwa da yawa. Da kallamu mai gadi yaga haka sai shima ya tattara cocilarsa da karikitanta ya ajiyesu a gefe guda, don ya ba.da hankalin san kan amininsa mati mai shara.
.
"ni fa abin nan ya daure mani kai baba kallamu."
.
Mati ya ce da Tsohon Wanda duka-duka bai fi ya bashi shekara takwas ba a duniya.
.
"duk wannan tawagar fa da kake gani, ba wani hanmshaqin mutum suka kawo ba, wani motsattsen tsoho ne sanye da kayan fursina, ina jin daga gidan yari suke. Amma zo kaga yadda suke taran-taran dashi, Suna lalla6a shi kamar wani muhimmin mutum, ba dan fursina ba." damar a qasar nan ana kulawa da fursina haka? Ni ban ta6a gani ba sai yau."
.
Kallamu dake sauraren mmati ya kai ganin sa nesa dasu, inda mutane suke kaiwa da komowa a hanyar shigowa asibitin. Duk da ya tabbatar babu Wanda yake sauraren hirar tasu, sai da ya rage murya sannan ya ce da mati.
.
"ka iya bakinka mati, don kuwa wannan Tsohon da kaga 'yansanda sun kawo bashi da lfy, Akwai qatuwar rigima a tattare dashi...wannan ni ina da labarin komai, don kuwa Akwai wani yaronmu dake a cikin gandirobobin da suka zo dashi, na tambayeshi Kuma ya bani labarin komai, dama Kuma ina da masaniyar wannan Tsohon da dadewa, ban dai ta6a ganinsa bane ido-da-ido sai yau."
.
Mati ya girgiza kai cikin qosawa, da yaji kallamu mai gadi ya saurara. Ya bishi da kallo kamar Wanda yake sa ran zai fada masa inda zai je ya samo maganin fatara.
.
"wannan maganar sirri ce mati. Ba kowa ya san da ita ba, sai Jami'an tsaro. Don haka idan ka sake kayi su6ul da baka a wani waje aka tsareka babu ruwana."
.
Mati da yaga kamar kallamu mai gadi ba zai fada masa maganar ba, sai ya marairaice ya ce dashi cikin girmamawa.
.
"haka baba kallamu, ai ka sanni dai wajen riqe sirri, ba yau nake tare da kai ba." me ka ta6a fada min ka ji shi a bakin wani? Maganar nan ni da kai ne a nan, anan muka yi anan zamu rufeta.. Babu wanda zan je in fada mawa."
.
Kallamu mai gadi ya gyara zama da ya ji mati ya kai qarshen aya, ya sake tsareshi da idanu sun shafi'u tozali kamar kwarto. Kallamu ya gyara tsohuwar babbar rigarsa wacce ta tattare kamar sufirin, sannan ya sake waigawa ko ina don ya tabbatar babu wanda yake sauraren hirar tasu.
.
"wannan al"amarin ya dade da faruwa mati."
.
Kallamu ya ce dashi cikin kuntar da murya.
.
"shekaru zasu kai talatin da biyar da suka wuce, wataqila su fi haka, Tunda ina jin tun zamanin firimiya Aallah ya jiqan rai. wannan al"amarin ya faru ne a lkcn an zo ana yasa a wani dam Wanda turawa ke yin aikinsa. Su Kuma mutanenmu baqaqen Fata an daukesu ne aikin leburanci Suna yin aikin qarfi.
.
To anan aikin ne fa, sai wata mota a cikin motocin da turawan suke haqa ramin dasu, ta tono wadansu manyan gwala-gwalai masu daraja. Wadanda yadda muka ji anan labari a lkcn, ance irin wadannan gwala-gwalai ba a kowacce qasa ake katarin samun su ba." ma'adanai ne na musamman, wadanda zasu kawowa qasa kudin shiga idan aka ajiyesu a gidan tarihi. Mutane a ko ina a duniya zasu riqa xuwa Suna kallo, don kuwa na fadi maka Suna da matuqar daraja, ba irin sauran qananan gwala-gwalai bane da kake ji ana labari ba."
.
Mati ya dake kumatunshi da hannu biyu yayi kasaqe yana sauraro kamar mai ciwon haqori. Kallamu ya ci gaba da sanar dashi...?wannan
.
"ana cikin haka kafin kowa ya farga a cikin turawan da suke aikin, sai wani lebura ya tattara wadannan ma'adanai da aka tsinta ya xubasu a rigarshi ya sheqa da gudu. Aka bi shi ana ihun 6arawo-harawo, amma kafin a kama shi yayi tsiyar. Ya arce!
.
Lp=6}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa }~~~~~~{
Page 6
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Aka bi shi ana ihun 6arawo 6arawo, amma kafin a taroshi, ina! Ya yi tsiyar. Ya arce! Aka nemo 'yansanda suka bi sawunshi, don kuwa idan aka sake yayi bisa ya gudu ya bar qasar da wadannan ma'adanai, to ya salwantar da dukiya mai yawa. Kuma maimakon ace qasarmu ce ta amfana dasu, kaga zai je ya sayar dasu a wata qasar su zama nasu."
.
Kallamu mai gadi ya saurara kafin ya ci gaba.
.
"ba a jima ba sai 'yansanda suka kamashi, amma matsalar Kuma ita ce, a lkcn har ya 6oye gwala-gwalai a wani waje.
.
Tun daga lkcn aka kaishi gidan yarin ana gana mashi azaba ya fadi inda ya kai gwala-gwalan amma ya qi ya fada. An yi mashi siyasa, an lallashe shi ya taimaka ya zama dan qasa na gari ya fito dasu daga inda ya 6oyesu. Amma ya qi. An yi binciken dukiya nan sama ko qasa, amma tun lkcn babu wanda zai ce maka ya san a inda wannan lebura ko Kuma in ce maka 6arawo ya kai wadannan gwala-gwalai. Bari in takaice maka labari mati . Wannan 6arawo ba wani ba ne, shi ne Wanda ka ga 'yansanda sun kawoshi asibitin nan ynx Suna lalla6ashi don kada ya mutu."
...
Kallamu mai gadi yayi dariya a lkcn da mati ya tambayeshi a kidime.
.
"wannan Tsohon shi ne 6arawon da ka bani labari mai taurin kai?"
.
Kallamu ya ce.
.
"qwarai kuwa, shi ne, ban ta6a jin labarin 6arawo mai taurin kai irin wannan Tsohon ba." shekaru talatin da biyar kenan yana shan azaba a gidan yari, amma ya qi ya fadiwa Jami'an tsaron inda ya 6oye ma'adanai. gashi har tsufa ya cimma shi. Kullum lalla6ashi suke yi kamar qwai, ko a can gidan yarin na samu labarin dakin Tsohon na musamman ne....! Shi kadai ake gadinsa, dare da rana, ba a yarda yayi magana da kowa ba, don kada ya ba wani labarin inda ya 6oye wadannan gwala-gwalai. su kansu Jami'an tsaron da suke gadin sa ba a yarda suyi magana dashi ba." yawanci wadanda ake ba gadinsa ba hausawa bane, sbd ba a son yana magana da kowa."
.
Babu irin hikimar da ba a yi masa ba, na samu labarin har cewa aka yi Idan ya fito dasu, za a yafe masa, za a gina masa gida, za a bashi maqudan kudi da motoci, za a bashi komai da yake so na jin dadin duniya. Amma da yake yana da taurin kai, yayi shiru ya qi magana, shekaru talatin da biyar. Wannan al"amarin ya 6atawa Jami'an tsaro da manyan qasar nan rai. 6arawon ya zama qadangaren bakin tulu, a barshi ya 6ata ruwa, a kashe shi Kuma a fasa tulu
.
Kallamu mai gadi ya sake bushewa da dariya, har sai da tari ya sarqeshe.
.
"tafdijan!"
.
Mati ya ce cikin al'ajabi yana gyada qaton kanshi dake kama da murhun wankan jego.
.
"lallai wannan tsoho ya cika namijin duniya. To idan ya mutu kuma ya za a yi kenan baba Kallamu?"
.
Tsohon yayi gyaran murya ya ce.
.
"Shi kenan qurunqus, ta faru ta qare kowa yayi asara. Shi ya rasa, Gwamnti ma ta rasa. Shi yasa kaga ana yin kaffa-kaffa dashi idan bashi da lfy. Ba wanda yake son wannan tsoho ya mutu, don kuwa har ynx ana san ran wata rana idan yaga babu dama ya canza ra'ayi ya fadiwa Jami'an tsaro inda ya 6oye ma'adanai aje a debo su."
.
Mati mai shara ya ci gaba da tagumi, xuciyarsa tuni har ya fara rayawa da ace shi ne wannan tsohon 6arawo da ynx ya fadi inda suke. Don kuwa ance har gida za a gida masa . A yadda mati ya shekara ashirin a gidan haya, yana fada da kiyateka, shi a gani sa indai za a gida masa gida, to an gama masa komai a duniya. Duk da haka baiwa fito fili ya fadiwa Kallamu manufarsa ba." tambayarsa kawai ya sake yi cikin jimamin rashin kasancewar sa wanda ya tsinci ma'adanan.
.
"to yaya kuma naga 'yansanda suna dama-dama dashi, basu son mutane Suna matsowa ko da kusa da harabar inda yake, na dauka magana kawai suke tsoro Kada yayi shi da wani?"
.
"ba magana kawai suke tsoro ba mati."
.
Kallamu ya ce dashi. Akwai alamar ya fara gajiya da hirar.
.
"dole ne su tsaurara matakan tsaro akan shi, don kuwa akw 6arayin da suka sha zuwa Suna kawo mashi farmaki a gidan yarin suna so su sace shi. Ka kuwa san idan 6arayi suka sace shi, me yiwuwa su ya fadi masu inda ya 6oye, su je su daukota. Wannan Tsohon ya wahalar da hukuma mati, akan shi shi Kadai ake ta wannan wahala shekaru talatin da biyar."
.
Dattawan biyu suka katse hirrarsu a cikin sauri a lkcn da suka ji shigowar wata motar aguje ta fado cikin asibitin cike da wasu Jami'an tsaron, Suna a tsaye cikin motar, dama da hauni sun turo bakin bindigunsu waje. Tabbas an qaro wasu Jami'an tsaron ne sbd an raina adadin na farko.
.
.
.
*** *** ***
.
.
.
Babi na uku.
.
Daga inda sadi yake zaune a qarqashin gadar. Yana iya hango yaranshi biyu Shago da Mai ankwa dake a zaune akan yashi Suna wasan karta. kusan kodayaushe nan ne wurin shaqatawar wadannan riqaqqun 6arayi. In dai ba su fita sata ba, to a qarqashin gadar suke xuwa su baje kolinsu, yawancin lokuta sun fi yin karta, ko kuma wasan kariya Wanda ya sha zame masu fadan gaske. To amma kuma da yake tare suke rayuwarsu, ko fadan suka yi dole ne su dawo su shirya.
.
Sadi qare-garke sanannen 6arawo ne tun da dadewa, wanda ya sha yin aawon gaba da garken shanu su 6ace komin yawwan su." ya ta6a fadawa hannu 'yansanda Sau daya, ya je gidan yari ya yi wata tara, tun daga lkcn da fito ya sake shiri, ko sau daya bai sake yarda an kamashi ba."
.
A shekarun baya sadi ya sha yin yara wadanda ke fita yawon sata tare dasu, to amma su da yake basu kai shi hatsabibanci ba, tuni duk zamaninsu ya qare, sun dade da mazauni a gidan yari, waddansu kuma an dade da harbeesu.
.
Sadi qare-garke ya sha zama ya tuno manyan yaranshi irin su talle, irin su bello, irin su kwandagi. Duk zamani ya tafi da 'yan maza, da yake mai halin ba ya iya barin halin sa, har ynx sadi bai haqura ya tuba ba, da wasu yaran sun qare zai sake nemo wasu ya kafa wata sabuwar dabar, ta 6arna.
.
Da a ce sadi ba ya 6acewa, da bai riqa ba Jami'an tsaro wahala ba." da wahala sadi ya je 6arna a ganshi ido da ido. Ko da an ga xuwanshi, to da wahala a ga tafiyarsa, sai dai a duba a ga ba kaya sadi yayi tsayar! za a iya ganin sawun sadi qare-garke amma matsalar kawai ita ce,idan kaga sawun qare-garke yayi gabas, to amma ya nufa. Idan aka bi shi arewa, to qare-garke kudu ya nufa, inda ya tafi daban inda sawunsa ya nufa daban, don haka sadi qare-garke iblishi ne na gaske a cikin 6arayi.
.
Bayan yaransa talle sun qare, ya dade bai dawo sana'ar sata ba, don kuwa duk da wannan baqin halin nasa baya son ya fita aiki shi kadai, daga baya ne ya koma tsohuwar sana'arsa ta dambe sai ya hadu da yaronsa shagon sadi. Sun yi wasannin dambe a garuruwa dabn-daban, da sa'arsu ta fadi aka fara kashe su. Sai sadi ya ce da yaron nasa shago zai ajiye aiki ya koma inda yafi wayo. kai tsaye shagon nashi ya biyoshi suka ci gaba da tafiya tare.
.
Shi kuwa mai ankwa tun a zaman da sadi yayi wata tara a gidan yari suka hadu, sadi ya riga shi fitowa, to amma dama tun a gidan yarin sadi ya daidai ankwa cewar idan lkcn fitowarsa yayi ya neme shi suuyi aiki tare, don kuwa a yadda sadi ya fahimci yanayin mai ankwa zai iya mayest masara gurbin talle indai ya dore a haka baiwa lafa ba."
.
Mai ankwa ya samo sunansa ne a gidan yarin, ba don komai ba sai don wuni yake yi yana kwana da ankwa a hannaye da qafafuwa. hadari ne sosai a bar mai ankwa ba a daure hannuwansa ba a cikin mutane. Don kuwa yana da wani muggun hali na son ya kai naushi ko duka a toe lkc, ko da kuwa babu Wanda yayi masara laifin komai.
.
Farkon xuwansa gidan yarin kafin ma'aikatan su fahimci halinsa ba a fara san mashi ankwa ba, a ranarsa ta uku ya samar da mutum biyu a cikin abokan kwanansa da suke daki daya. Da yake ya san idan ma'aikatan suka zo suka ga ta'annatin da yayi, jikinsa zai gaya masa shim, sai ya dauki kwanon da ake xuba masa abinci ya kwada a a goshinsa,sai da goshihe jini ya xuba.
.
Da gandirobobi suka xo suka ga abin da ya faru sai ya nuna masu goshinsa, ya ce kare kansa yayi, sun tarar masa ne zasu kashe shi. Dole suka qyaleshi da yake wannan al"amarin akan idon sadi ya faru yana daga cikin dakinsu nesa kadan da dakin su mai ankwa sai yayi murmushin jinjinawa dadi, ya san tabbas ya samu abokin tafiya idan suka gama zaman gidan yarin suka fita.
.
.
Lp=}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa }~~~~~~{
Page 7
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Sai yayi murmushin jin dadi, ya san tabbas ya samu abokin tafiya idan suka gama zaman gidan yari suka fita.
.
Ba a jima ba mai ankwa ya sake yin halin nasa da aka tura su aiki a wani daji, suna saran ice. Duk da tsattsauran tsaron gandirobobin sai da mai ankwa ya xubar da qarti hudu a wani fada da suka yi akan abinci, tun daga ranar suka fahimci baqin ranshi, Kuma tun daga ranar suka sa mashi ankwa sai da ya shekara biyu ba a cire masa ita ba, da ita yake komai don kuwa idan yana nannade da ankwa za a sami sauqi kafin ya sake kwantar da wani.
.
Da ya gama iya lknsa ya fito, 'yan gidan yarin da yawa sun dade Suna kida da murna, don kuwa tafiyar mai ankwa tamkar dauke masu mafadaciyar damisa ne, ko maciji a gidan yarin.
.
Ynx suna tare da sadi qare-garke ne, da Kuma shagon sadi. Ba kasafai sadi yake shiga cikin su su zauna tare ba, sbd ba ya son raini ya shiga tsakanin shi da yaran, shi yasa yake komawa gefe ya kame yana busa sigari cikin izza, yaran Kuma Suna yin harkokinsu. Kamar yadda yake faruwa a halin ynx da suke wasan karta a qarqashin gadar, a sama Kuma motoci na wucewa lkc xuwa lkc babu Wanda ya damu da sha'aninsu.
.
Sadi dake zaune a can gefe xuciyarsa cike take da tunanin yadda zasu samo kudin gaggawa shi da wadannan yaran nasa biyu, sai ya ji wayarsa ta fara 6urari tana busa qaho da kirarin adahama, shi ne sautin da ya saka idan an kira shi a kodayaushe. Bayan mai kirarin ya mangaro wata ashariya kafin ya kai qarshe sai sadi ya katse 6urarin ya dauki wayarsa ya sa a kunne.
.
Cikin sauri ya miqae kamar an soke shi da mashi a kunne ya ce da mai maganar.
.
"ka tabbatar ynx haka yana

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment