Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ashiru ba kuma nazo daxu na samu gayen a qofar gidan nan ya fito dauke da jakarsa zai tafi.... Na tambayeshi Ashiru ya ce wai tun daxu ya sallameshi, kuma qarya yake yi, inda ace lfy ba wani abu ya yiwa Ashiru ba da tuni Ashiru ya dawo, sbd haka mu yaronmu kawai muka sani a fito mana dashi. Ehe!"
.
Wani matashi da rigarsa ta 6arke a hammata hannun rigar yana lilo ya ce.
.
"Qwarai a fito mana dashi koma ina aka kai shi. Kuna ganinmu cikin wahala baku taimaka mana, shi ne zaku sace mana yaro, to wallahi yau sai dai a mutum a nan."
.
Haj. Maimuna ta fahimci baqon da suke magana, ba wani bane Naj ne saurayin da Larai ta zo da shi.
.
Ta ce da mutanen muryarta na rana.
.
"ku saurara indai shi ne yazo ya tafi da danku ba abin da zai same shi. Don Allah ku bamu lkcc ina xuwa.
.
Ta juya 6angaren da Larai take a tsaye, tayi sumar tsaye.
.
.
.
Lp=68}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 68
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Haj. Maimuna ta juya 6angaren da Larai take a tsaye. Ta yi sumar tsaye, tun sanda ta ji an ambaci Najib shi ne ya je ya taho da yaronn, yazo dashi gidan su za'ayi masa gyara a dakinn da ta saukeshi. Haj. Maimuna ta janye larai wanda hakan shi ne ya zama dalilin yankewar tunanin da ta fara yi. Suka koma cikin gidan da sauri. Wani matashi a cikin tsagerun layin ya ce.
.
"Muna nan a nan, ba inda zamu je, ku gama borin kunyarku ku fito mana da danmu. Azzalumai masu satar 'ya'yan mutane."
.
Lkcn da suka kai zauren gidan ne inda matattakalar hawa benen yake, wanda yake tarwai da haske kamar rana, sai Haj. Maimuna ta tsayar da Larai, ta dubeta cikin fushi da xullumi a fuskarta, ta ce da ita.
.
"Kin ga fitinar da kika jawo mana muna zaune ko larai? Wannan yaron da kika zo dashi daxu shi ne ya je ya dauko masu dansu, gashi ya tafi ba musan inda yakai masu dansu ba." ya kike son mu yi da ranmu ynx a nan gidan? Me zamu fadiwa Alhaji idan ya dawo ya ya iske wannan tashin hankalin Larai?"
.
Larai ta dabirce, abin duk ya rikita ko'ina a xuciya da qwaqwalwarta, ta kasa samun natsuwa. Ta rasa abin da zata cewa mahaifiyarta, Qwaqwalwarta ta dabirce ta ma rasa wanne irin tunani zata yi. Ba ta san dalilin da zai sa Najib ya yi wani laifi a gidan su ya gudu ba." bata ta6a zaton a yadda take sonshi kamar ta hadiyeshi, zai iya jefa rayuwarta a cikin tashin hankali ya gudu ba. Larai ta fara kuka, ta dubi mahaifiyarta wacce ke tsaye tana jiran ta ji abin da zata ce.
.
"Mama Najib ba zai sace masu dansu ba, ba abin da ya hada shi da irin wannan halin. Karatu ya kawo shi nan garin, kuma tare da ni ya je ya yi (Ragistration) daxu a Jami'a, ba shi ya sace masu dansu ba."
.
Haj. Maimuna ta dakatar da ita a fusace.
.
"To wai idan bashi ba ne, yana ina ynx? Ai tun daxu ina ta kallon ki daga daki kina kaiwa kina komowa, kina xuwa kina dubawa ki gani ko ya dawo..." Idan har yana da gsky me yasa ya gudu?"
.

Larai ta yiwa kanta wannan tambayar cikin sauri a xuciyarta. Ta qara da wata tambayar wacce mahaifiyarta bata yi mata ba." kuma idan har Najib yana da gsky, me yasa da ta kira shi a waya har ta shiga ta katse ya kashe wayar? Tabbas 6acewar yaron na da alaqa da guduwar Najib.
.
Larai ta rufe bakinta tana qoqarin ta hana kanta fashewa da kuka, idan tashin hankali ya sameta komai qanqantarsa bata iya jurewa. Kuka take yi riris kamar 'yar yaye. Larai bata da dakakkiyar xuciya, da yake mahaifiyarta ta san haka, sai ta yi tsaki ta rabu da Larai ta fara tunanin hanyar da zasu warware wannan matsalar, wacce ta fado masu ba zato ba tsammani.
.
A can qofar gida saurayin da ya yi barazanar zai sa wa gidan wuta daxu, ya sake daga murya ya ce.
.
"ku fa muke jira Hajiya' kuna 6ata mana lkc kuna gane ko? Ku yi sauri ku fito da yaron nan. Tunda asirinku ya tonu kuyi haquri da sace shi mana, nan gaba za ku samu wani tunda sai kuna yi farfesu da yaran mutane sannan zaku ci za6e."
.
Mutanen dake a wajen suka fashe da dariya, Nama'u ne kawai bai yi dariyar ba." duk da ana cikin fushi akwai wadanda dama an san taqadarai ne a unguwar. A banza ma suna iya shege balle ynx da dalili ya samu.
.
Haj. Maimuna ta fusge wayar dake a hannun Larai wacce take ta kuka, ta kasa ta6uka komai. Da amsar wayar sai ta kira mijinta Alh. Madugu ta ce da shi.
.
"Ka yi sauri ka dawo gida Alhaji babu lfy."
.
"Me yake faruwa?"
.
Ya tambayeta a lkcn yana a cikin motarsa ya kamo hanyar dawowa gida.
.
"Ka dai yi sauri ka dawo, in ka zo mayi maganar."
.
Ya daka mata tsawa a wayar.
.
"Na ce me yake faruwa, baki iya fada mani dole sai na dawo? Ko an ce maki zan dawo gida ynxn ne?"
.
Bata ran sa a 6ace yake haka ba." daga wajen taron da suka yi na siyasa yake. An 6ata masa rai a can kuma gashi tana son ta qara masa wata damuwar.
.
"Ka yi haquri Alhaji."
.
Ta ce da shi.
.
"Wallahi daxu ne Larai ta yi wani baqo, wani saurayinta ne da yazo daga Abuja, wai zai yi rijista a nan jami'a, to shi ne tazo dashi nan gida, tunda bai san kowa ba a nan garin. To mu bamu san me ya faru ba tun lkcn yaron ya gudu, bayan tafiyarsa ynx haka mutane suna nan a qofar gida, hayaniyarsu ka ke ji ynx haka, wai a fito masu da yaronsu da aka sace masu, da muka tambayesu wanne yaro aka sace masu? Sai suka ce baqonmu ne ya tafi da yaron, wato saurayin da larai ta zo dashi. Mutane suna nan a waje suna hayaniya kazo ynx da sauri."

.
Alh. Madugu ya ce da ita.
.
"To ynx ni me kuke so in yi maku? Ku kuka jawo rigimarku don haka ku san yadda zaku yi da su. Zan yiwa D.P.O waya yazo ynx, kada in samu wani a qofar gidana kafin in zo. Idan ke zasu kama da 'yarki su tafi da ku kuyi rigimarku a can inda zaku yi, amma ba a gidana ba." ba zan yarda da irin wannan shirmen da kuke yi mani ba, ta yaya zaku sauke mani wani yaro a gidana ba tare da kun san halinsa ba, ku jawo mani matsala, ku bar ni mana da abin da yake damuna a halin ynxn?"
.
Haj. Maimuna ta san halin dan gogan nata, duk wannan maganar da yake fada ta san fushi ne kawai ya sa shi. Amma dolensa ya dauki mataki. Kafin ta sake cewa dashi wani abu ne ya kashe wayarsa. Ya yi saurin nemo lambar waya abokinsa D.P.O Rabe wanda shine shugaban jami'an tsaro na qaramar hukumar da grid Alh. Madugu ya ke, ya ce da shi.
.
"Ynxn nan matata ta kirani ta yi mani waya cewar wasu matasa sun je gidana suna yi mani rashin kunya da hayaniya akan wata matsala, ina son ka zo ynx nima bani a gidan ina mota can na nufa, ka zo da Jami'an tsaro mu hadu a gidan."
.
D.P.O ya ce da shi.
.
"Zan zo ynxn nan tare da yarana, kada ka damu Alhaji."
.
A cikin minti biyu D.P.O ya jawo tawagarsa suka shiga motoci biyu suka nufo gidan Alh madugu, da xuwansu suka samu dandazon mutane sun cika qofar gidan, suna ife-ife. Jami'an tsaron suka fara direwa tun kafin motocin su tsaya, da mutanen suka ga 'yan sandan sai suka fara watsewa, suna barin qofar gidan. Wani dan sanda ya fara yin harbi a sama, mutane suka fara yin nisa.
.
D.P.O ya ffito daga cikin motarsa sanye da kakinsa, wadanda suka sanshi, musamman wadanda suka ta6a fadawa komarsa, suka riqa guduwa, kadan ne wadanda suka tsaya daga can a baya suna cewa.
.
"qarya ne wallahi, qarya ne, muna nan babu inda zamu je."
.
'Yan sandan sun gama fasa dandazon mutanen ba da jimawa ba, sai ga motar Alh. Madugu ta silalo, ya tsar da mortar a kusa da motocin Jami'an tsaron. Ya fito cikin sauri. Suka hadu shi da D.P.O suka gaisa, ya tambayeshi.
.
"Alhaji me ya jawo wannan rigimar a tsakaninka da mutane?"
.
Alh. Madugu ya ce da shi.
.
"Zo mu shiga cikin gidan mu zauna tare da iyalina, ni kaina ban san abin da ya faru ba, tun safe na fita sai ynx na dawo, zo mu shiga cikin gidan."
.
Alh. Madugu ya hagoranci shugaban 'yan sandan suka shiga cikin gidansa da sauri. Da shigarsu mutanen dake tsattsaye ragowar wadanda basu gudu ba, suka fara daukar dutse suna yin jifa. 'Yan sandan dake a qofar gidan suka bazama suka bi mutanen a guje, basu samu sa'ar kama kowa ba, har xuwa sanda suka rakasu qarshen layin, suka dawo kowanne riqe da bindiga a hannu, kamar wadanda suka fito yaqin duniya, ba don komai ba sai don kawai mutanen suna shirin ta6a wani babban mutum a layin wanda yakw da qumbar susa.
.
.
.
*** *** **
.
.
Babi na goma sha-tara.
.
.
.
Tun suna a hanya cikin daji kafin su shiga gari, Sadi ya yi wa wani abokinsa waya mai suna Kwatsami, ya sanar da shi cewar yana nan tare da mutanensa ya jira su, kuma suna buqatar masauki, akwai wani babban aiki ne da yake yi.
.
Sai al'amura sun yi zafi Sadi yake neman Kwatsami. Shi kanshi Shago bai san Sadi yana da irin wadannan mutanen ba a 6oye, a kusan kowanne gari. Amma da ace za a samu wanda ya san lkcn da Sadi yake kan ganiyar sata dolene ya san Kwatsami, sbd tare suka yi zamani. Kwatsami ba yaro bane ya girmi Sadi nesa ba kusa ba." dogo ne baqi, wanda ya rasa haqoran gaba guda biyu a wajen wani fada da suka yi tun shekaru goma sha uku da suka wuce, shi da wasu yaransa biyu da yake fita aikin dare tare dasu. A wajwn rabon kudin da suka sato ne, rana ta 6aci yaran nasa suka sa shi a tsakiya sai da suka tabbatar sun yi galaba akansa, sannan su tattara duk waniabu da suka samu tare dashi, suka qasa gaba.
.
Tun daga lkcn Kwatsami ya daina ajiye yara, ya dawo yana yin laifukansa shi kadai.
.
.
.
Lp=79,}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 70
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Tun lkcn Kwatsami ya daina ajiye yara, ya dawo yana laifukansa shi kadai. A wajen satar shanu sadi ya hadu da Kwatsami, suka jone suke fita tare. Ba a jima ba rana ta 6aci, 'yan sanda suka cafke Kwatsami a kasuwar qauye, ya je zai sayar da wani bajimin sa da suka sato a wata rugar fulani. Kai tsaye aka wuce da Kwatsami cibiyar binciken manyan laifuka ta jiha, kwanansa goma a can Jami'an tsaro suna qera shi.
.
A can ne aka yi masa wani duka na musamman. wanda ya tabbatarwa kansa in har ana yi wa dan Adam irin wannan bugun to da wahala mutum ya yi tsawon rai. Tun kafin a sakeshi ya yi alqawarin ya gama fita sata, sai dai kuma 'yan dabaru da ba a rasa ba." abin da ya birge Sadi game da Kwatsami shi ne, duk da irin uban wahalan da ya sha a wajen tuhuma, bai tonawa kowa asiri ba a cikin abokan muguwar sana'ar tasu. Don haka Sadi ya riqeshi amana, komaI ya samu sai ya tuna da Kwatsami, duk da yake sun daina fita yawon sata tare.
.
Dan abin da Kwatsami ya samu bai gama 6al6ancewa ba ne, ya ririta shi ya sayi wani qaramin fili, ya gina gida wanda ya zame masa jari, yawanci a nan 6arayi suke xuwa su fake idan ana nemansu. Kwatsami ya kan caji duk wani wanda ya zo fakewa gidan kudi matsayin ladan 6uya, bashi da mata shi kadai yake zaune a gidan. Kuma da yake bayan wata sabuwar unguwa ya yi gidan, ba wanda ya san me ake yi a gidan, Kullum yana nan a rufe kamar gidan maye.
.
Idan 6arayi suka hadu a gidan Kwatsami, kwana suke yi da wuni aikin caca, kudin da suka samo a nan wani yake cinye su." Kwatsami shi ne kartagi, da yake Tsohon mugu ne, duk kudin da 6arayin suke xuwa dasu gidan a hankali yau da gobe sai sun dawo wajen sa. Sbd ko ruwa mutum ya sha a gidan sai ya biya, komai na kudi ne, ba sani ba sabo. Ba yadda 6arayin suka iya dolene su bi shhi, tunda dai basu da wata qwaqqwarar mafaka idan rana ta 6aci, fiye da gidan Kwatsami.
.
Shi ya sa da Sadi ya kira shi ya sanar da shi cewar zai zo da tawagarshi, sai Kwatsami ya fara dariya, ya tabbatar kudi sun samu. Shi dai ba zai fita sata ba, ya tabbatar akwai hadari, domin kuwa har ynx dingisa qafarsa daya yake yi ta dama, tun sanda Jami'an tsaron suka cafkeshi a zamanin da ya saci wannan bajimin sa, wani kurtu ya daga kulki ya makawa qwaurinsa ana sanyin safiya. Tun a wancan zamanin baya iya miqar da qafar, don haka sai dai wanda yaga zai iya ya je ya sato yazo gidansa ya 6oye, amma shi kam ya ji tsoro, sbd bai ji dadi ba.
.
Ba su fi minti ashirin da gama wayar ba, motar su Sadi ta yada zango a qofar gidan Kwatsami, wanda yake tsaye yana jiran qarisowarsu. A lkcn duhu ya yi, kuma da yake ba wuta a unguwar, ba wanda ya lura da mutanen dake cikin motar, har suka zo qofar gidan.
.
Fitilar motar ta haske Kwatsami, wanda ya dingisa ya kauce ya basu wuri da sauri yana dariya, wangamemen gi6insa yana yi masu lale marhabin. Sadi ya fara fitowa daga cikin motar, ya samu Kwatsami a inda ya dogare ya dafa bangon gidan, don kuwa baya iya tsayawa daram. Abokan biyu suka daga hannuwansu suka tafa fau!!
.
"mugu sai mai shi dan karen uba."
Sadi ya ce da Kwatsami yana dariya.
.
"Kai dai nemi sa'a ko dare ko rana, sa'a maganin 6acin rana yaro."
.
Kwatsami ya yiwa sadi irin kirarin da yake yi masa, tun a zamanin da suke tare. Ba wani gargadi ya sa yake yiwa SadiI gargadi da wannan kirarin ba, sai don la'akari da rashin sa'ar da shi ya samu a rayuwa. A cewar Kwatsami, ba qaramin hadari bane mai laifi ya fada hannun hukuma. Shi yasa yake nemawa yara tsari da 6acin rana, tunda dai shi ya riski nashi hadarin.
.
Sadi ya daina yin dariyar, fuskarsa ta dawo kan aiki. Ya ce da Kwatsami
.
"ina fatan dai ba wasu baqi a cikin gidan."
.
"Ba kowa sadi."
.
Ya ce da shi yana qoqarin hango sauran mutanen dake a cikin motar. Ya dai hango wani yaro wanda ya hade rai a gaban motar ya dafa sitiyari yana jiran a bashi umarni ya fito.
.
.
Lp=71}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 70
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ya ce da shi yana qoqarin gano sauran mutanen dake a cikin motar. Ya dai hango wani yaro, wanda ya hade rai a gaba ya dafa sitiyarin motar yana jiran a bashi umarni ya fito, sauran wadanda yake dan ganin qyallin kayansu a bayan motar' bai san ko su wane ne ba."
.
"ko da akwai mutane a ciki ai dolene in sallame su sbd kai nawa ne Sadi. Na san baka yin qaramar harka."
.
Sadi ya juya ya daga murya kadan ya ce.
.
"ku fito mu shiga ciki Shago, ka dauko Baba ka shiga da shi, mun zo sabon masaukinmu."
.
Shago ya bude qofar ya fito, bai san Kwatsami ba, basu ta6a haduwa ba, akwai wani dai mai irin sunansa da suka yi wasa tare sanda suna dambe, amma shi wancan kwatsamin yaro ne, ba irin wannan ba ne wanda yake da qafa daya, mai shekaru kusan hamsin a duniya. Da fitowar Shago kafin ya bude qofar 6angaren qofar baya, ya fito da Nalamma da su Hauwa likita, sai Sadi ya ce da shi.
.
"Na mance ban ce ka zo ku gaisa da Abokina ba, laifi na ne da ban ta6a baka labarin sa ba, shima gwarzo ne a harkarmu, matsalar dai kawai ya yi saurin tsufa da wuri ne."
.
Kwatsami ya fashe da dariya
.
"Sadi ai ba yau muke ba, shekaru sun tura dolene mu tsufa ko bama so."
.
Shago ya dauke kansa, bai je ya gaisa da Kwatsami ba, don kuwa tun xuwansu da ya kalli mutumin ya ji bai yl masa ba." irin wannan abin da sadi yake yi masa yana 6ata masa rai. Baya son ya hadu da wani tsohon abokin sa ya riqa turasasa shi sai ya yi masu biyayya, don kuwa a yadda yake jin kansa yawan shekaru kawai zasu fadi masa, amma ba xuciyar aiki da tsantsar taurin kai ba."
.
Ya bude motar ya ciro Nalamma, wanda jikinsa ya qara yin laushi tilis, idanunsa a rufe kamar yana a sume. Shago ya xubashi a kafadarsa, ya kalli su Hauwa da Rabi 'yar fulani wadanda suka manne a wuri guda ya ce da su cikin tsaWa.
.
"ku ba zku iya fitowa ba ne da kanku, da kuka tsaya kuna kallon mutane?"
.
Hauwa ta bude qofar ta fara fitowa da sauri, Rabi ta bi bayanta. Sadi wanda yake a tsaye tare da abokinsa Kwatsami a gefe daya ya yayi murmushi ya ce da shi.
.
"Dukansu mutane na ne Kwatsami, kowannensu yana da amfanin da zai yi mani a wajen aikin da nake yl."
.
Kwatsami ya ce da shi.
.
"mu shiga ciki, sadi bana son wani ya zo wucewa ya ganmu. Mutane sun fara sa mani ido a 'yan kwanakin nan."
.
Sadi wanda ba baqo bane a gidan, shi ya fara shiga' Kwatsami ya bishi a baya, Shago ya tasa Hauwa da Rabi, suka bi tawagar xuwa qaramin gidan, wanda yake da dakuna uku a ciki dai-dai, rufin kwano ne babu silin. Ko'ina a tsakar gidan guntayen taba ne da ake jefarwa yau da Kullum, sai kuma tsoffin karta wadanda suka kode aka xubar dasu.
.
Minti biyar bayan su duka sun hallara a daki, sai Sadi ya miqe ya kallesu ya ce.
.
"kamar yadda na sha fada a baya, ynx ma zan sake maimaitawa, ina son hadin kanku. Zamu zauna a nan ne na wani dan taqaitaccen lkc, kafin mu samu abin da muke nema. Bana jin zamu yi wani aiki a yau sbd lkc ya qure, mutum na gaba da muke nema ba zzamu same shi ba a inda muke zato. Don haka zamu bari sai gobe idan ya fito kasuwa, ni da kaina an je in same shi muyi magana, idan ya zama wayayye ya bani hadin kai, shi kenan aiki ya qare, idan kuma shima yazo da taurin kai dolene sai mun yi aiki tare da shi a nan...ka dole in kamoshi in dawo dashi ya zauna a qarqashina a lkcn na san zai yi mani ladabi ya bani abin da nake so, ina fatan kowa ya gane abin da ya rage mana?"
.
Shago kadai ya yi magana ya ce.
.
"Mun gane Oga."
.
Kwatsami wanda yake tsaye a gefe daya bai san komai ba akan wannan aiki da sadi yake magana. Amma sbd biyayya haka nan ya gyada kai, alamar shima ya amince. Nalamma yana a gabansu a kwance, kamar sun tasa gawa suna shirin yi mata suttura. Hauwa wacce tayi tagumi, ta sauya hannun taguminta. Rabi bata damu ba sosai a halin ynxn, har ynx maganarsu kawai take saurare, tun haduwarsu babu wanda ya mareta ko sau daya. Shi yasa bata ga wani tashin hankali a zamanta da su Sadi ba." amma da yake ita Hauwa da kakanta Nalamma sun yi aiki tare da azzaluman mutanen, dolene su fi Rabi damuwa.
.
Bayan Sadi ya gama jawabin ne, Rabi ta ce da shi.
.
"Ina jin yunwa tun daxu ban ci komai ba...."
.
.
Lp=71}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 71
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ina jin yunwa, tun daxu ban ci komai ba."
.
Da Sadi ya ji ta fadi maganar a tsorace ne, ya yi mata dariya ya ce.
.
"ki daina jin tsoron yin magana Rabi, mu ma muna jin yunwa, ynxn nan Shago zai je ya sayo mana abinci, kowa zai fadi abin da yake so a kawo masa. Na fada maku indai zaku zauna da ni lfy ba munafunci to kowa zai ji dadina. Komai mutum yake so ya yi magana zan nemo masa."
.
Sadi ya ciro kudi ya qirga wadanda yake so ya fitar ya miqawa Shago ya ce.
.
"dauki mota ka je ka sayo abinci Shago, bari a rubuta maka abin da kowa yake so a kawo masa, don na san ba zaka iya tunawa ba idan ka je.
.
Sadi ya ce da Hauwa
.
"rubuta masa Hauwa, mun zo kan naki aikin, kin san Shago bai yi karatu ba, sai kin riqa taimaka mana."
.
Shago ya tashi da sauri kamar wanda yake jin kashi, ya je bakinn qofar dakin ya tsaya yana cije le6e, kamar zai jure sai kuma ya fara fada yana cewa.
.
"Oga gsky bana so! Duk abin da ka ce ina yi, amma Oga Kullum sai ka disga ni a gaban mutane. Haka nake yi maka?"
.
Sadi ya fusata ya ce da shi.
.
"To don ubanka ka zo ka buge ni, naga kana jin zafin kai yau, idan fadan ka ke ji, me yasa baka yi mani bayani ba tun da wuri, tun sanda muna a daji? Na fada maka tuntuni, idan kana jin fada kada ka cuci kanka, kayi mani bayani mu buda, tunda hannunka ya fara qaiqayi."
.
Kwatsami ya shiga tsakaninsu da sauri.
.
"Yawa ne Oga sadi, ka daina biye masa yaro ne....!"
.
Sadi ya juya a fusace ya kalli Kwatsami
.
"in banda na san haka tuntuni me zai hana ni in harbe wannan dan iskan yaron in huta? Mu sanda muna koyon aiki wane irin bala'i ne bamu gani ba?" satar mu zamu je mu yo mu kawo kudin, amma ko na sigari ba za a bamu ba." in banda mun yi haquri zamu kawo ynx ne?"
.
Kwatsami ya yi murmushi
.
"To ai su yara ne basu san haka ba, tunda suna shigowa cikin manya ana yin komai tare dasu."
.
Takaicin wannan maganar da Kwatsami ya fada ne ya sa Shago ya fashe da kuka. Har sai da ya ba Hauwa tsoro. Sadi ya ce da ita.
.
"yi aikinki ki rabu dashi Hauwa, dauko biro da takarda."
.
Hauwa ta dauko biro da takarda da ta samu a gidan baqin bature da matarsa. Ta fara rubuta abincin da take so ta ci, ta juya ta tambayi Rabi, itama ta fada mata abincin da take so ta ci Hauwa ta rubuta. Sadi da Kwatsami suka fada mata masu irin abincin da suke so, bayan Hauwa ta gama tsara sunayen abincin ne, sai ta tsayar da kallonta ga Nalamma da ke a kwance fuskarta cike da tausayawa, tana wasi-wasin da wahala idan akwai wani abinci da zai iya ci a wannan halin da yake ciki domin dukan da Shago ya yi masa daxu a hanci ya gigita shi. Da sadi ya fahimci tunanin da Hauwa take yi ne sai ya ce da ita.
.
"Baba ya qi motsawa tun daxu ya yi magana, amma ki za6ar masa abincin da kika ga yafi dacewa da shi Hauwa. Ke likita ce, zaki fi mu sanin abin da mutum yafi son ya cci idan ba a dade da fasa masa hanci ba."
.
Hauwa ta rubuta masa sassanyar fura, a ganinta Nalamma yafi buqatar abu mai sanyi da ruwa. Sadi ya tambayeta.
.
"me kika rubuta Hauwa likita?"
.
Ta dago kai ta kalleshi kafin ta ce.
.
"fura na rubuta a nemo masa.l"
.
Sadi ya nunawa Shago hannu wanda ya juya masu baya yana kakarin kuka, kamar an maqare wuyan jaki, ya ce da shi.
.
"to ka ji aikin masu ilimi Shago, anyi maka magana kana fushi da mutane. In banda mun samu Hauwa likita ta yaya zamu san abincin da zamu baiwa Baba ya qara masa

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment