Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi mata dariya da gabza-gabzan haqoransa masu kama da madannan fiyano. Ta miqa masa qwaryar nonon ya amsar mata, ya ce.
.
"A ha, rabi zo mu tafi."
.
Ya tayar da babur din ya yi murji, rabi ta taka ta hau bayan ta tattare zaninta, ya miqo mata qwaryarta ta baya msa. Ta gyara zama ya ja suka kama hanya.
.
.
Lp=51
}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 51
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ta gyara zama ya ja ta suka dauki hanya. Ba wanda bai san rugar su rabi ba a cikin 'yan aca6an dake kai kawo a hanyoyin qauyukan, shi yasa dan aca6an bai tambayeta inda zata sauka ba."
.
Matsalar kawai da take fuskanta wajen xuwa gari daya ce, babur baya shigowa har cikin rugarsu ynx, sakamakon ruwan da yake yawan taruwa a wani qaton kwatami dake a hanyar wanda aka sa itatuwa mutane suna lalla6awa a hankali suna hawa kai suna wucewa.
.
Idan masu baburan suka zo wajen a nan suke tsayawa su sauke wanda suka dauko, dole sai dai mutum ya qarasa a qafa ko'ina ne qauyen su." amma idan rami ya yi ruwa ya qare har mota tana wucewa ta wajen, musamman idan mazauna yankin suka yi aikin gayya na shekara suka fitar da hanyar sbd zirga-zirga.
.
Har dan aca6an ya kawo rabi gefen kwatamin ya tsayar da babur din basu yi wata qwaqqwarar magana ba." ya yi gudu sosai, sbd yana so ya yi sauri ya koma gari. Da tsayawarsa rabi ta sauka, dama ta ciro naira saba'in dinta ta riqe a hannu. Ta miqawa dan aca6an ya amsa yana dariya, ya san ta rage naira talatin kudinta naira dari ne, to amma rabi ba wacce za a tsaya ana sa'insa da ita ba ne, don ta rage masa kudi. Ko kyauta ta ce a kawota ba matsala. Tunda dai ana tare yau da kullum, kuma an zama daya.
.
Dan aca6an yayi kwana ya koma bayan ya ce da rabi ta sauka lfy. Rabi bata daina murmushi ba, ta daga masa hannu. Bata tsaya 6ata lkc ba, ta fara taka itatuwan tana kallon ruwan dake kwance a qasa. Da yake ruwan a kwance yake a qasa baya tafiya, ta6o ya sa yayi jawur, yawanci nan makiyaya na kusa suke xuwa su ba shanu ruwa, idan sun dawo kiwo.
.
Rabi ta tsallake kwatamin ta dauki hanya ta fara tafiya a qasa tana ta sauri don ta je ta dora abinci. Ba ta dade da fara tafiya ba ta hango rugarsu dake nesa. Ta zo daidai wani qaramin kwazazzabo da yake tara ruwa rani da damina a gefen hanya ne, ta hadu da wasu mutane uku a gefen hanya, biyu maza dayarsu kuma wata budurwa ce tana maqure a jikin dogayen ciyayin da suka yiwa hanyar katanga kamar baiwar da suka kamo.
.
Mutanen biyu basu da kyan gani. Ba kayan dake a jikinsu da yayi baqin datti yaffi damun rabi ba, da ta kalle su. Akwai wani yanayi dake tattare dasu wanda ke sa da zarar mutum ya dubesu zai ga sun fi kama da masu wasa da maciji.
.
Rabi ta waiga ko'ina a kusa dasu ta ga ba kowa daga ita sai wadann mutanen da ta iske akan hanyarta. Ta ce dasu a tsorace.
.
"sunnun ku."
.
Ta sa kai zata wuce kenan, sai ta ji daya daga cikin mutanen ya kira sunanta.
.
"rabi kin dawo?"
.
Rabi ta amsa cikin tsoro, ta sake juyowa ta kalli mutanen, tana mamakin yadda akayi suka santa. Ga alama basu da tabbacin ita ce, sun yi kintace ne sun kira sunan, da suka tabbatar ita ce rabi tunda har ta juyo da taji sun kira sunanta, sai suka matso kusa da ita suka biyota. Ita kuma budurwar da suke tare da ita, tana nan a maqure tana kallonsu, akwai xullumin faruwar wani abu a fuskarta. To amma ba kanta take yiwa wannan xullumin ba, ga alama rabi 'yar fulani take tausayawa.
.
Daya daga cikin mutanen biyu da suka biyota da sauri ya ce da ita.
.
"hannu da xuwa rabi, dama tun daxu ke muke ta zaman jira a nan, an ce mana kin tafi kasuwa."
.
Rabi ta tsaya turus! Tana kallon mutanen a tsorace. Abin da ta fara darsawa a xuciyarta shi ne, 'yan fillan kai ne....! Ta ji jikinta ya dauki kyarma, tana so ta yi ihu, amma ta kasa ko motsawa daga inda ta tsaya. Wanda ya yi mata magana tunda farko ya hade fuskarshi, ya ce da ita cikin kakkausar murya.
.
"ke ba mun tsayar dake bane don muyi hira dake rabi. Muna so ne ki dauko mana abin nan da kika tsinta daxu da safe a saman tsaunin can. Kin san ko me muke nufi, mu je ki bamu, kayanmu ne....!"
.
Rabi ta ja baya a kidime, da ta ji abin da mai maganar ya ce. To amma a halin ynx ba maganar tafi tsorata ba, abin da ta gani a hannun mutanen shi ya sa ta kaduwa fiye da komai. Su duka biyun bindigogi ne a hannuwansu. Suna fuskantarta a fusace.
.
.
.
*** *u* ***
.
.
Larai tana zaune ita kadai a cikin motarta fara sol! Qirar (honda civic), a gefen faffadan titin jami'ar Ahmadu Bello dake zaria. Ta kai minti goma a wajen tana jiran fitowar Najib masoyinta wanda ya shiga wani banki dake kusa da inda ta tsaya a bakin titin zai fitar da kudi a (A.t m) kamar yadda ya fada mata.
.
Layin muttanen da ya samu a harabar bankin, a gaban (atm) din ya sa ya 6ata lkc bai dawo inda larai take ba a inda ta tsayar da motar. Sauri biyu tana kiransa yana bata haquri, layi ya kusan xuwa kansa, mutane sun fara raguwa a wajen. Don haka sai larai ta ci gaba da zama tana kallon motocin dake kaiwa da komowa akan titin.
.
Larai matsakaiciyar budurwa ce 'yar kimanin shekaru goma-sha-tara a duniya. Gajera ce mai kaicin jiki, wacce Kodayaushe mutane suke mamakin kasancewar ta 'yar gidan alh. Madugu. Don kuwa babu ta inda ta biyo kamannin mahaifinta ko mahaifiyarta.
.
Larai baqa ce wacce take da kyakkyawar fuska. Idanunta wadanda suke haduwa da launin fuskarta, su bayar da wani sinadari mai raunana xuciyar samari, a zahiri a iya cewa sune jigo cikin abubuwan dake tattare da surorin halittarta, masu ban sha'awa.
.
Samari da yawa a qasar hausa suna matuqar son farar mace, kamar yadda mayen qarfe yake lale da qarfe. To amma ga duk wanda ya san me ake nufi da kyau, idan ya ga larai dolene ya yarda akwai baqaqe kyawawa a duniya.
.
Qaramin jikin larai da kuma doguwar fuskarta, da murmushinta, sune suka fi rikita wani saurayi dake sayar da katin waya a layin gidan alh. Madugu. Kullum aka zauna maganar 'yanmata kyawawa a duniya, larai yake fara kawowa matsayin misalin farko, tare da ra'ayin da yayi imani dashi cewar baqaqen mata sun fi farare kyau, indai hukuncin gsky za'ayi.
.
To ko da dai ace saurayin ya zuzuta larai da yawa, abinda kowanne saurayi zai yarda dashi a lamarinta shine, budurwar tana da wani irin nasibi a halittarta wanda ke sa duk wani namibia idan ya kalleta zai ji ta yi masa a rai, a lkc guda.
.
Tana da murya mai dadi, tana da saurin fara'a, da kuma saurin canja irin kallon da take yiwa mutum idan ya yi mata wata magana wacce bata gane ba." duka wadann abubuwan idan aka hadasu da cikakken qirjinta mai daukar hankali, da kuma daskararren kwankwasonta dake a cure kamar dutse, abin ba a magana.
.
Wasu a ganinsu alh. Madugu yana da sakaci wajen lura da halayen 'yarsa larai. Wadanda suke da wannan tunanin suna la'akari ne da yadda larai take rayuwarta, yadda take so, da kuma yadda take facaka da kudi. Bata dade da kammala karatunta na sikandire ba, ynx haka ma tana jiran sakamakon jarrabawar da auka yi ne ta (S.s.c.e), wacce har ynx bata fito ba."
.
Larai tana shiga sutturu masu tsada, sannan kuma duk wani bikin qawayenta da take xuwa ita ce take zama babbar tauraruwa, duk da yake kuwa yawancin qawayenta suma 'ya'yan manyan mutane ne.
.
A 6angaren soyayya larai tana wahalar da samari fiye da duk yadda za'a fada. Babbar matsalarta shi ne, da wahala mutum ya san ko mene ne matsayin a xuciyar larai. Tana da samari bala'adadin wadanda suke matuqar wahala akanta, amma duk a cikinsu idan za a tona xuciyarta babu wanda take so, kuma idan larai bata son saurayi bai isa ya gane ba, bata da wulaqanci Kodayaushe tana lalle marhabun da duk wani mai sonta. Za'a zauna a sha hira a yi dariya kamar da gaske, amma ita ta san matsayin kowa a xuciyarta.
.
.
Lp=52}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 52
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."

.
Za a zauna a sha hira ayi dariya kamar gaske, amma ita ta san yadda take daukar kowa a xuciyarta.
.
Duk duniya ba wanda larai take so da gaske kamar najib. Ba a zariya yake ba, a cikin birnin tarayya abuja yake, babansa ma'aikaci ne a wani kamfanin yin hanyoyi da gine-gine. Najib kuma dalibi ne sabon shiga a jami'a wanda tuntuni yake burin ya zo zariya yayi karatu don kawai ya matso kusa da larai masoyiyarsa.
.
Soyayyar najib da larai bata yau ba ce, sun kai shekara bakwai da fara haduwa. Hakan ya samo asali ne tun sanda larai ta zauna a abuja, wajen wata qanwar mahaifiyarta wacce ta ta6a yin aure a can. Gida daya suka zauna tare da najib da yake a gidan haya ne....! Tun lkcn suka shaqu da juna, ko'ina zasu je suna nan tare. Ko aiken su za'ayi dolene tare zasu, don kuwa idan daya bai ga daya ba ba zai je aiken ba."
.
Suna nan a haka kwatsam, sai qanwar mahaifiyar larai ta rabu da mijinta. mutuwar auren shi ya jawo sanadiyyar tarwatsewar zamantakewar larai da najib, a ranar da zasu rabu qanwar mahaifiyar larai ta nemo mota zata kwashe kayanta su tafi da kuka riris aka rabu tsakanin larai da najib, da qyar iyayensu suka lallashesu.
.
A sannan ne alh. Madugu ya ce da haj. Maimuna ta amso masa 'yarsa, tunda dai ta dawo gida bata da aure. Dama ba da yawunsa haj. Maimuna ta bada 'yarsa ba, don dai kawai ta ce ba dadewa zata yi ba, da ta gama firamare zata amso ta ta dawo. Don haka sai faduwa ta zo daidai da zama, tana gama firamaren sai auren qanwar mahaifiyarta hassana ya mutu suka baro garin. Larai ta dawo gidan ubanta alh. Madugu dake zariya, ita kuma hassana ta koma gidansu dake kawo kaduna ta fara zaman zawarci.
.
Duk wadannan shekarun soyayyar larai da najib tana nan daram! Lkcn farkon rabuwarsu da basu da waya, sai dai su riqa yiwa junansu wasiqu. Duk wanda larai ta ji zashi abuja ko ba unguwar su najib zai je ba, sai ta rroqeshi ta bashi wasiqa ya kaiwa najib. Haka shima indai ya samu wanda zai zo zariya to qa'idane ya dora masa dawainiyar kawowa larai wasiqa.
.
To amma tun sanda suka fara girma kowa ya mallaki waya a cikinsu, sai komai ya zo masu cikin sauqi. Haka suke wuni suna qona kudi a waya ba dare ba rana. Duk kudin da larai take samu a wajen mahaifinta yawancinsu a sayen kati suke qarewa. Idan kuma wani saurayi ya yi karambanin tura mata katin waya, to ya bayar da gudunmawarsa ne wajen yada soyayyarta ga najib, don kuwa shi kadai ne saurayin da zata iya kira a waya, ba tare da taga asara ba."
.
Duk wani saurayi da larai take kulawa yaudararsa kawai take yi, abin da yasa yawancin samari basu san haka ba shine, najib ba a garin yake ba, ba wanda ya san shi balle a san matsayin sa a wajen larai. Ko xuwa zariya ba ya yi, sai dai in wani abu ya hadasu a wani waje su hadu shi da ita.
.
Mahaifiyarta haj. Maimuna dake ta san sirrin 'yarta fiye da kowa a duniya, tana sane da yadda larai take ba samari wahala, da yawa wadansu da aure suke sonta, amma ita hankalinta yana can a wani waje, a wani gari. Haj maimuna bata ta6a baiwa larai goyon baya game da soyayyarta da najib ba, da yake mijin hassana qanwarta ya yi mata wulaqanci sanda ya saketa. Da zagi ta uwa ta uba suka rabu, tsanar da haj. Maimuna tayi wa mutumin ya shafi hatta soyayyar larai da najib, musamman da haj. Maimuna ta ji ashe gida daya suka zauna tare da yaron a zaman da tayi a abuja shekarun baya.
.
Wata rana larai ta sayo kati ta zauna a falo tana xubawa a wayarta, mahaifiyarta ta zo ta sameta, da yake ta san wanda zata kira idan ta sa kudin, sai ta ce da ita.
.
"har ynx baki rabu da yaron nan ba ko larai? Na fadi maki kina wahalar da kanki ne a banza, in zaki samu saurayi tsayayye a gida ki samu tun wuri, amma ba wanda zai daukeki ya ba wannan wannan yaron, wadanda ba mutunci suka sani ba." in banda ke sakarya ce har kin mance irin rashin mutuncin da mijin hassana ya yi mata? Shi ne kema zaki koma can a wulaqantaki ko?"
.
Larai wacce take takaicin yadda mahaifiyarta ta kasa gane wane ne najib ta ce da ita kamar zata yi kuka.
.
"mama wai don allah sauri nawa zan fada maki najib bai hada komai da mijin da anti ta rabu dashi ba?" zaman gidan haya kawai ya hada su, kuma ynx najib sun tashi ma a wannan gidan sun yi nasu. Ba abin da suka hada dasu, najib yana da mutunci ki bari wata rana ya zo ki ganshi da idonki."
.
Irin wannan magiyar bata ta6a sanyawa haj. Maimuna ta canza ra'ayinta ta ji tana son soyayyar larai da najib ba." halinta daya da kowa ya sani shine, in tana son abu kawai tana so, in kuma bata so, to kawai bata so.
.
Kwana biyun da suka wuce ne najib ya kIra larai muryarsa cike da farin ciki a waya, ya shaida mata cewar yayi nasarar samun shiga cikin sabbin daliban da jami'ar ahmadu bello ta dauka, kuma zai zo ya yi rijista kai tsaye.
.
Larai ta fi najib xumudin xuwansa. Da ranar ta zo yau tunda safe ta dauki motarta ta je tarbarsa da yace ya taso, ta je tashar motar da za a saukeshi ta tsaya zaman jiransa. Ta kai fiye da awa daya sannan motar da ya shigo ta zo tashar cike da fasinjoji.
.
Najib yana fito yayi kaci6us da larai tsohuwar masoyiyarsa. Suka yi kamar su rungume juna sbd jin dadi da murna. Yaushe rabon da su hadu? Shekara kusan bi kenan, tun wani xuwa Kaduna da larai tayi wajen kakanninta shima najib ya zo wajen wasu 'yan uwan mahaifinsa suka hadu a can.
.
To amma wannan haduwar tasu tafi kowacce armashi, sbd kowa ya qara girma a cikinsu. Sun fahimci soyayya da alqari fiye da lokutan baya. Najib fari ne, wanda yake da qaqqarfan jiki. Yana da tsawo da kauri sannan kuma idan aka dawo wajen halayensa yana da fadin rai.
.
Larai ce kawai bata san yana da wannan halin ba, sbd tun sanda suna yara da suka zauna gida daya, babu wani lkc da najib yake cikin farin ciki irin in suna tare.
.
Larai ta dauki najib a motarta ta kai shi jami'a, ya fara hada-hadar yin rijistar. Abubuwan da zai yi ba zasu kammalu ba a kwana daya, don haka larai da ta ga yamma ta yi, sai ta ce dashi, ya zo ta kai shi gidansu ya kwana in yaso bayan kwana biyu idan ya gama rijistar ya samu daki a cikin makarantar sai ya koma can.
.
Najib bashi da wani za6i da ya wuce ya amince da abin da ta ce. Tunda dai bai san kowa ba a garin sai larai masoyiyarsa. Ya yi mata gdy suka shiga motarta, ta tuqa suka kama hanyar xuwa gidansu. akan hanyar ne da ya lalubi aljihunsa ya ji kudinsa sun yi qasa sai ya ce, ta tsaya a wani banki da ya gani a bakin titi, zai shiga ya ciro kudi a (Atm).
.
Zaman da larai tayi a halin ynx ita kadai a cikin farar motar tata, najib take zaman jira ya fito daga cikin bankin. Bayan ta qara 6ata wasu mintocin kimanin biyar tana zaman jiranshi, sai gashi ya fito cikin sauri yana yiwa larai murmushi tun daga nesa, sanye da matsattsiyar farar (T-shirt) da kuma shudin wando.
.
Da xuwansa tun kafin ya shiga cikin motar, larai ta ce dashi cikin shagwa6a.
.
"ka je kayi zamanka najib, sau biyu mama tana kirana in koma gida."
.
Najib ya bude motar ya shiga cikin sauri, ya zauna kusa da ita kafin ya ce.
.
"afuwan! Larai. Na fada maki akwai mutane ne da yawa a wajen, kin san daxu ba (network) sai yanzu ya dawo..."
.
.
Lp=53}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 53
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.

"afuwan! Larai. na fada maki akwai mutane ne da yawa a wajen, kin san daxu ba (network) sai ynx ya dawo."
.
Larai ta tuqa motar aguje suka tafi. Ta saki ranta tayi murmushi itama ta ce dashi...
.
"ban ta6a jin farin ciki irin na wannan ranar ba tunda nake a duniya najib. Wai yau nice tare da kai a garin mu. Sannan kuma zaka zauna a nan har sai ka gama karatunka, Kullum muna tare. Wannan shine abin da na dade ina fatan gani a rayuwata najib, Kodayaushe ace muna tare, ina ganinka."
.
Najib ya dubi wasu jerin gwanon dalibai dake tafiya a gefen titin, sun taso karatun yamma ya juyo ya dubi larai wacce hankalinta ke akan tuqin da take yi ya ce da ita.
.
"ni ya kamata in fadi haka larai ba ke ba." ina so ki san cewar a dalilin ki na zo wannan makarantar zan yi karatu, don kawai in matso kusa dake in ga muna zaune a gari daya, babu wani abu da zai sake rabat mu har abada in allah ya yarda."
.
Larai tayi dariyar farin ciki. Ta rage gudun da take yi, wani mai babur yazo ya wuceta a tsiyace, babur din yana bulbular da hayaqi, to amma ba tashi larai take yi ba." ta rabu dashi har ya yi nisa ba ta qarawa motar gudu ba." ko a waya suke magana ita da najib haka yake kashe mata jiki idan ya sanar da ita irin tsagwaron soyayyar da yake yi mata a xuciyarsa.
.
Suna tafiya a motar suna hira, suna murmushi da dariya, suna iske gosilo suna tsayawa, har suka isa gida. Najib bai ta6a xuwa gidan su larai ba sai yau, ya sha jin labarin cewar mahaifinta mai kudi ne, babban dan siyasa ne, amma bai ta6a zaton gidan su larai ya kai haka qeruwa ba." ba ma kamar sanda ta sa sigina ta shiga wagegiyar qofar, ya ga kwalliyar da aka yiwa harabar gidan da kayan qarau, da manyan qwayayen lantarki a ko'ina masu ban sha'awa.
.
Larai ta kai motarta inda take ajiyeta kullum. Bata samu sauran motocin mahaifinta da motar Mu'azzam ba." motar mahaifiyarta kawai ta gani. Ta ce da najib a lkcn da suka fito daga cikin motar.
.
"baba bai dawo ba, sai anjima zaku gaisa."
.
Najib ya yi mata murmushi kawai, bai ce da ita komai ba, ya mayar da hankali akan abubuwan dake gida su." gidaje masu kyau ba baqin idanun najib bane. To amma shi yadda yake tsammanin mahaifin larai bai tsammci dukiyarshi ta kai ba." kuma ko a hira larai bata ta6a fadi masa cewar sun kai haka matsayi ba." ta dai ta6a ce masa suna da rufin asiri daidai gwargwado, to amma wannan makadeden gidan da najib ya gani, ai ya wuce ace rufin asiri, dukiyace a fanfare a cikinsa tsagwagwa.
.
Larai ta jagoranci najib suka hau benen suna ta wuce sassan gidan, har suka isa gidan sama inda falon su yake na iyali. Da shigarsu syndrome yi sallama kenan, sai ga haj. Maimuna ta fito daga cikin daki kamar wacce aka jeho. Har zata rufe larai da fadan dadewar da ta yi tun safe ta yi zamanta, sai ynx da yamma ta ga damar dawowa, sauri ta ga najib bata san tare suka shigo ba." haj? Maimuna ta sauke wuta, larai ta ci arzin baqon saurayinta. Ta saki ranta ta ce da su."
.
"sannunku da dawowa."
.
Larai wacce take cikin murna ta ce da mahaifiyarta
.
"mama yau ga najib yazo."
.
Haj. Maimuna ta kalli ganjejen saurayin, dan kimanin shekaru ashirin da hudu a duniya. Haka kawai ta ji bai yi mata ba a ranta, dama can tun kafin ta fara ganinshi, bai yi mata ba, ynx kuma da ta ganshi ido-da-ido sai ta ji ta qara tsanarshi. Ta ce da shi.
.
"zauna mana, nan gidanku ne ka saki jikinka."
.
Najib wanda yake dan jin kunyar haj. Maimuna, ya zauna akan daya daga cikin shirga-shirgan kujerun falon. Ya gaishe da hajiya ta ce dashi ya hanya? Ya ce ya zo lfy. Suna gama gaisawa ta dubi larai wacce take ta murmushin ganin najib a gidansu ta ce da ita.
.
"larai zo nan."
.
Larai ta bi mahaifiyarta suka shiga ciki, suka turo qofa, suka bar najib a zaune yana kallon katafaren falon, yana girgiza kai. Bai ta6a tsammanin a shekaru bakwai da suka wuce, da 'yar gidan masu kudi yake soyayya ba, sai ynx da ya zo gidansu.
.
Da shigarsu daki, haj. Maimuna ta hade fuskarta, ta fuskanci 'yarta larai ta soma yi mata ruwan fada.
.
"ke ynx larai abinda kika daukarwa rayuwarki kina ganin ya kamata? Ace tun safe kisa qafa ki tsallake ki bar gidan nan, kina can tare da wannan yaron baki tashi dawowa ba sai ynx ko?"
.
Larai ta ce da mahaifiyarta cikin damuwa.
.
"mama na raka shi yin (registration) ne....! Kuma bai gama ba muka dawo don kada mu kai dare. Dole sai gobe zamu koma ya kammala."
.
Haj. Maimuna tayi tsaye kawai tana kallon 'yarta larai wacce take shirin fashewa da kuka idan har mahaifiyarta bata fitar da ita kunyar wannan baqon nata ba, ta ce da ita muryarta a narke.
.
"bai san kowa ba a garin nan sai ni mama. In ban taimakeshi ba, wa zai taimaka masa?"
.
Haj. Maimuna ta dan rage fushin da take yi kadan ta ce.
.
"to ynx da kika jawo shi kuka ruguntsumo nan, meye manufarki in kin ce bai san kowa ba sai ke a nan garin? Kina nufin a nan gidan zaki ajiyeshi ya zauna?"
.
Larai ta ce da mahaifiyarta
.
"a nan zai zauna mana mama, ba zai wuce kwana biyu ba. Na fada masa ba matsala ya zo nan. Kuma ya amince
.
Haj. Maimuna wacce ita dai inda za'ayi bi son xuciyarta ba zata amince najib ya zauna masu a gida ba. To amma kuma da ta tuno yadda 'yarta larai ta mace wajen son yaron, da kuma yadda ta tabbatar larai zata shiga damuwa idan bata samu goyon baya ba, sai ta numfasa ta ce da ita.
.
"tunda kin riga kin xo dashi yaya za'ayi? Sai ki kai shi can dakin baqi qasa ya zauna a can, in babanki ya dawo sai ki yi masa bayani da kanki, na gaji da xuwa in fadi masa irin jaye-jayen da kuke yi a nan gidan ke da kawunki Mu'azzam. ba zaku riqa jefani a cikin matsala ba, kullum yana yi mani fada akan ku."
.
Larai ta sake marairaicewa, saura kadan ta fara kuka, ta ce da mahaifiyarta
.
"dakin baqin nan bashi da kyau mama, kwanaki da baba ya yi wasu baqi 'yan qauye anan suka kwana suka yi baza-baza da abinci a (carpet), har ynx ba a share ba, ya za'ayi in kai najib can ya kwana?"
.
Haj. Maimuna bata son taga kukan 'yarta larai. Duk fushin da ta yi, indai larai zata yi kuka to ya zama dole ta dawo ta yi mata abin da take so. Tana da qoqari wajen kula da tarbiyya, amma bala'in son 'ya'yan dake damunta tun larai tana a ciki har ynx bai ragu ba." ta ce da larai cikin rarrashi.
.
"to ina kike son ki ajiyeshi tunda dakin baqi yayi maki qazamar riba?"
.
Larai ta ce da mahaifiyarta
.
"mama bari

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment