Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lfy? Daga yau ka riqe wannan darasin, idan mutum hancinsa ya fashe ya yi ha6o, fura mai sanyi yafi buqata. Ko kai ka san haka ne, da ka ke fushi don an ce ka tsaya a taimake ka?"
.
Sadi ya amshi takardar a hannun Hauwa, ya miqawa Shago a fusace.
.
"Amshi ka yi sauri ka dawo, kuma ka yi a hankali wajen tuqi, ka san Jami'an tsaro suna nemanmu ruwa a jallo, kada ka yi abin da zasu biyoka suga inda ka zo."
.
Shago ya juya ya amshi takardar, yana girgiza kai kamar mai shirin hawa bori. Da amsar takardar ya fice daga dakin, sai da ya tabbatar ya yiwa Sadi nisa, yadda ko biyoshi ya yi ba zai kamashi ba sannan ya daga murya ya ce.
.
"Ba Tsoronka nake ji ba oga, Wallahi bana tsoronka. Ba abin da zaka iya yi mani
.
Sadi ya yi dariya kamar maganar bata 6ata masa rai ba, shima ya daga murya ya ce da Shago.
.
"Je ka sayo abincin ka dawo Shago, yau zamu tantance mu gani, dama tun daxu nake tunanin abin da ya kamata muyi a wannan daren tunda ba aiki. Ka dawo mu buda ga 'yan kallo nan su Hauwa likita ko banza zasu rage dare, su samu abin da zasu kalla, ka yi sauri ka dawo."
.
Kwatsami ya sa baki da sauri.
.
"ba girmanka ba ne Oga sadi, ka rabu dashi kawai."
.
Sadi ya hade fuska ya ce da Kwatsami
.
.
"dolene in nuna masa da fifiko har ynxn, dama a qa'ida duk bayan wata uku yake ja na da rigima, yana so ne ya gani, na fara lafawa ne ko kuwa har ynxn a gabansa nake? Haka yake yi mani, ynx da zaran ya dawo idan yaga na ci ubansa zaka ga ya dawo ya bini, amma idan na qyaleshi bamu yi fadan ba, to ya shiga yi mani rashin mutunci kenan. Dole sai mun yi fada yau Kwatsami."
.
Sadi ya kalli Hauwa ya yi mata murmushi
.
"Kin ta6a kallon dambe Hauwa?"
.
Hauwa ta girgiza kai, tun kafin ta ce A'a, Sadi ya ce da ita.
.
"Yau zaku kalli yadda ake yin dambe a fili ba a hoto ba, idan 'yan dambe suka raba rana ba a raba su, sai daya ya kashe daya. Yau ni da yarona Shago dolene sai daya ya kashe daya a cikinmu."
.
Hauwa ta dafe qirrji a tsorace da ta ji Oga Sadi ya ambaci kisa. Suka kalli juna ita da Rabi 'yar fulani. Ga mamakinsu Sadi bai ji tsoron maganar da ya fada ba. Ya ci gaba da yi masu dariya, kamar an yi masa albishir din wata gagarumar kyauta, kamar ba albishir din hannun yaronsa Shago yake sanar da su ba. Wanda a cewarsa Shago ya kai mutane sama da dari qiyama da hannunsa.
.
.
.
***
.
.
Mu'azzam yana cikin motarsa ya yi nisa a hanyar legas, sau biyu kawai ya yada zango a hanya. A karo na farko ya tsaya ya ci abinci a wani gari, tsayuwar da ya yi kuma a karo na biyu tayar motarsaa ya tsaya ya duba wacce ya ji kamar babu iska, idan ya fada rami. Da yaga lfy lau tayar take sai ya ci gaba da tafiyarsa, baya xullumin komai, yana ta tsere da manyan motocin jigilar kayayyaki. Doguwar tafiya ba sabon abu ba ne a wajen Mu'azzam , idan da sabo ya isa ya saba.
.
Ba a dade ba sai Mu'azzam ya tuno da ajiyar da ya yi a cikin dakinsa. Da ya tuno sai ya yi murmushi, sbd ya tabbatar ynx shi ba qaramin attajiri bane a duniya.
.
.
Lp=72}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 72
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Sbd ya tabbatar ynx shi ba qaramin attajiri ba ne a duniya, lkc kawai zai jira, sai komai ya lafa idan ya tabbatar ba wata matsala sannan zai koma gida ya fasa bangon dakinsa ya ciro gwala-gwalansa, ya fara neman manyan dillalan da suka san darajarsu a duniya.
.
A cikin tafiyar da Mu'azzam ya yi ta kusan awa uku bai zauna haka nan a cikin motar ba, kade-kade yake ta tashi a cikin motar kamar zai fasa ta, duk da haka hankalin yana kan lissafin da yake ta yi, na yadda zai gudanar da harkokin dukiyarsa. Da ya saqa wannan sai ya kwance ya canza wata daban.
.
Yana a cikin tafiyar ne ya ji wayarsa ta dauki kuwwa, ya sa hannu ya rage sautin kidan da ya cika motar, sannan ya dauko wayar a gurbin malejin motar, yaga abokinsa ne Dumba ya kira shi. Ya yi murmushi ya dora wayar a kunnensa bayan ya amsa kiran.
.
"Dumba ya aka yi ne?"
.
Dumba wanda shi ne babban aminin Mu'azzam a layinsu ya ce da shi cikin rashin jin dadi.
.
"Wai kai ina ka shiga ne tun daxun?"
.
Mu'azzam ya ce
.
"ba ni a gari Dumba, ina kan hanyar Lagos, nayi nisa a can nake son in kwana."
.
Dumba ya ce da shi.
.
"ka tafi ka bar baya da qura banza, ana ta rigima a gidanku har 'yan sanda sun zo, suna nan ynx haka a wajee."
.
Saura kadan motar ta qwace daga hannun Mu'azzam' ya samu ya tarairayeta ya yi saurin rage gudu ya koma gefe.
.
"Lfy Dumba, me yake faruwa?"
.
Dumba ya ce da shi.
.
"Na tambayi Jingul yadda abin ya faru, don nima dawowa nayi naga ana hayaniyar, wai wani gaye ne ya zo wajen Larai shi ne ta bashi masauki, ance dakinka ta kai shi. Bayan ya huta ne ya je wajen su Nama'u kafinta ya nemi a bashi yaro ya yi masa gyara a dakin, to tunda aka hada shi da yaron nan Ashiru mai ciwon sikilan nan dake aiki tare da su Nama'u, har ynx ba a san inda ya kai yaron ba." kuma shi gayen ya gudu, shi ne su Nama'u suka yo zuga suka jawo mutane suna zage-zage. Ana cikin haka ne sai ga 'yan sanda tare da Alhaji."
.
Mu'azzam ya ji cikinsa ya duri ruwa, ya yi saurin daga qafarsa ya sa sigina, ba ai iya ci gaba da tuqi ba, dole sai ya huta sbd wannan mugun labari da Dumba ya fada masa. Idan har Larai zata yi wani baqo ta kai shi dakinsa, kuma gayen ya gudu, to dole babu lfy. Banza bata kai zomo kasuwa.
.
Dumba wanda yake saurare ya ji Mu'azzam ya yi magana ya ce.
.
"Na ji kayi shiru ma'adanai, kada ka damu an sasanta rigimar, 'yan sanda sun kori Nama'u tare da tawagarsa, kuma suna nan suna gadin gidan ba matsala komai ya wuce."
.
Mu'azzam bai saurareshi ba." sbd ya san Dumba bai san wainar da ake toyawa ba." Dumba ba wanda zai 6oyewa duk wani sirrinsa ba ne, shi ne abokin ta6ararsa a layin, inda suka raba jaha kawai shi ne, Duba bashi da komai, gashi da sabar zalamar tsiya, idan ya zauna kullum bashi da wani abokin gaba sai mai kudi. Duk wani mai tsaleliyar motar da ya wuce ta gaban Dumba dole sai ya sha zagi, amma idan ya ga mutum a cikin tsumma to yaga masoyinsa. Ynxn nan zai ja mutum su fara hira suna gulmar masu arziqi.
.
"Duk ka rabu dasu, muna nan zamu cimmasu, azzaluman banza macuta. Ai lkc ne kawai ba damuwa, duk su gama hawa motocin mu ma zamu hau namu."
.
Farin cikin Dumba a duniya daya ne, bai wuce yaga shahararren mai kudi ya talauce ba." idan yana bayar da labari anan zzaka ga har buga qafa yake yi yana dariya. kuma duk irin alaqar da zaku yi dashi, ko shekara naea zaku yi, indai aka hau tsanin arziqi, shi kenan kuma an samu matsala.
.
Duk cikin masu kudin dake a layinsu da Mu'azzam kawai yake abota, shi dinma ba sonshi yake yi ba har a cikin xuciyarsa. Dalili biyu kawai yasa yake abota da mu'azzam. Dalili na farko duk layin babu wani qato irin shi sai Mu'azzam, babu inda yake samun aron wandon da yake yi masa dai-dai sai a wurin Mu'azzam, sannan kuma duk da tsabar rowar Mu'azzam indai zasu hadu sai ya kawo na kashewa ya ba Dumba. Inbanda wadann dalilan biyu to da ba abin da zai hada Dumba da mu'azzam a layin. Amma ynx abokai ne, dukansu biyun tiqa-tiqan qatti ne kamar a fasa su su sace, wadanda suke da xuciyar hadama da mugunta.
.
Mu'azzam ya numfasa bayan ya tabbatar cewa matsala ta afku, in har baqon larai zai gudu to me ya aikata? Kawai sata ya yi, kuma gwala-gwalansa ya sata ya gudu wadanda ya 6oyesu a cikin bangon dakinsa, Larai? Babu shakka Larai ta cuce shi, to amma bata nemi zaman lfy ba, dolene ya nemo saurayinta indai yana a cikin wannan duniyar. Bai isa ya mallaki wadann gwala-gwalan ba, ya saci kayan 6arawo, dolene ya dawo dasu duk inda ya kai su."
.
Mu'azzam ya ce da abokinsa kai tsaye.
.
"Dumba gani nan zan yo kwana in dawo gida, na fasa xuwa Legas din. Ku jira ni komin dare zan dawo akwai taron da zamu yi, ka fadawa Jangul shi da Sisi kwandem, akwai zama gani nan xuwa."
.
Dumba wanda bai fahimci abin da Mu'azzam yake nufi ba ya ce dashi.
.
"Na fada maka indai don wannan rigimar ne, 'yan sanda sun zo sun kori mutane, ba wanda zai sake xuwa gidanku Mu'azzam' ka je kawai ba matsala."
.
Mu'azzam ya ce da Dumba cikin kwaratsi.
.
"Ni ba ruwana da rigimar da ake yi, su qona gidanma idan sun ga zasu iya ba ruwana. Akwai abin da yake faruwa ne, wannan saurayin da ka bani labarin ya zo wajen larai ban yarda dashi ba, akwai abin da ya sata a dakina. Ina so ku taimakeni mu bishi duk inda ya shiga mu kamo shi, 6arawo ne kada kowa ya je ko'ina, ka fadawa su Jangul da Sisi kwandem an ta6a ni, an yi mani illa sosai dole sai an sa mani hannu, akwai yaqi ba dan qarami ba, kowa ya shirya kafin in zo."
.
Dumba ya ce dashi.
.
"Mu a shirye muke kodayaushe Mu'azzam, kazo muna jiranka, ko me ka ce za a yi indai zaka saki cadas."
.
Mu'azzam ya juyo da sauri ya kama hanyar dawowa, ya riqa tsugawa motar wuta ba ji ba gani. Ya sa hannu ya share zufar da ta taru a goshinsa.
.
.
Lp=73}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 73
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Mu'azzam ya juyo da sauri ya kama hanyar dawowa, ya riqa tsugawa motar wuta ba ji ba gani. Ya sa hannu ya share zufar da ta taru a goshinsa. "Larai da masoyinta dolene su fito mani da dukiyata koma ina suka kai ta...."
.
Mu'azzam ya tabbatarwa kansa.
.
.
.
*** *** ***
Babi na Ashirin
.
.
Ba wanda ya yi magana a cikinsu, tun kammala bayanin da Haj. Maimuna tayi. Tana a zaune a 6angaren da mai gidanta Alh. Madugu yake, Larai ita kadai a 6angare daya, sai D.P.O Rabe daga 6angaren da qofar falon take. Sun kai minti Ashirin a cikin falon suna magana akan matsalar da ta faru. Bayan D.P.O ya saurari jawabin Haj. Maimuna, xuwa can sai ya dubi Larai wacce har ynx bata daina kuka ba, ya tambayeta
.
"Lkcn da ki ka kai shi dakin Kawunki, ya fada maki dama yau zai tafi, ko kuwa me ya fada maki?"
.
Larai ta sunkuyar da kanta ta ce.
.
"Ni bai ce mani yau .zai tafi ba, mun yi dashi sai ya gama Rijista a makaranta ya samu daki sannan zai koma."
.
Alh. Madugu ya daka mata tsawa a fusace.
.
"To wai in banda shashanci da rashin hankali irin naki larai, yaushe zaki yarda da mutumin da ba tare kike da shi ba?" don kin sanshi tun kuna yara? Lallai ne ki san duk wasu dabi'unsa da yake yi ynx? Wa ya sani ma ko sace yaron yayi ya tafi da shi, gashi ynx ya barmu a cikin matsala."
.
D.P.O ya ce.
.
"zamu yi bincike sosai, indai yana a cikin garin nan zamu kamashi nan ba da jimawa ba' ai tunda an sanshi, an san daga inda ya fito komai zai zo da sauqi, zamu je har can Abuja, mu nemi inda gidansu yake, kwantar da hankalinka Alhaji."
.
Haj. Maimuna ta sake cewa.
.
"Ni dama tun xuwan yaron nan bai yi mani ba." tun sanda Larai ta shigo da shi gidan nan naji a raina sai ya jawo mana matsala. Yarinya ce ka ganta nan bata jin magana yalla6ai, ta kafe akan yaron nan, nayi mata fadan, nayi nasihan, amma ta qi ta gane abin da nake nuna mata."
.
Alh. Madugu ya juya kan Haj. Maimuna
.
"Me yasa tuntuni da kika fahimci haka baki sanar da ni ba?" da na san tana yin wannan iya shegen a nan gidan ai da tuni nayi maganinta, shedaniya! Ana magana tana sunkuyar da kai, Yalla6ai ku tafi da ita Ofis ku bata kashin tsiya, gobe ma idan ta je ta sake jawo wani dan iskan har cikin gidana."
.
D.P.O ya ce da su."
.
"Duk yaran nan haka suke ynx Alhaji, muyi haquri tunda wannan shine karo na farko da tayi wannan kuskuren. Na san da ace ta san yaron mai laifi ne ba zata yarda dashhi ba." ynx ina so in shiga dakin da aka sauki yaron da ya zo, ya kamata muyi bincike a ciki, Wataqila ya bar wani abu da zai taimaka mana wajen gano inda yake,"
.
Alh. Madugu ya kalli Larai cikin fushi.
.
"ki je ki bude masa dakin ya gani."
.
Ku jirani bayan magribh inshaa Allah.
Ynx wani uxuri ya taso mani.}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa }~~~~~~{
Page 74
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Alh. Madugu ya kalli Larai cikin fushi.
.
"ki je ki bude masa dakin ya gani."
.
Larai ta share hawayen da ya xubo mata kan fuskarta, ta ce da mahaifinta
.
"Da mabudin dakin ya tafi, bayan ya kulle qofar, kuma ba sauran wani mabudin, dama guda biyu ne, kuma dayan yana wajen Kawu Mu'azzam, shima kuma baya nan ya yi tafiya."
.
D.P.O Rabu ya ce da su."
.
"Dole ko 6alle qofar ne a yi, sbd muna buqatar muyi bincike a dakin."
.
Alh. Madugu ya ce.
.
"in zaku iya 6alle qofar, ku 6alle ta kuyi duk binciken da zaku yi ba matsala. Ni dai fatana ku taimakeni a gano wa wadannan mutanen dansu, don in fita daga zargi."
.
D.P.O ya tashi cikin sauri, ya koma waje ya sami Jami'an tsaron da suka yi dafifi a wajen, da xuwanshi ya san wanda zai kira ya yi masa irin wannan aikin. D.P.O Rabe ya kira Sa'adu ganganci wanda bashi da igiya ko daya, har ynx kurtu ne....! Amma a sakamakon jarumtakarshi da tsabar wauta da qarfi kamar dan doki, duk wani aikin gaggawa na musamman da ya taso, indai D.P.O zai tura Jami'an tsaro su je, to dole akwai Sa'adu ganganci a cikinsu.
.
Dan sandan ya baro inda 'yan uwansa suke, ya samu shugaban su ya sara masa. D.P.O ya ce ya biyo shi a baya suka hau saman benen. Yanayinsa idan aka kwatantashi da shugaban nasu, kamar raqumi ne yake bin dan maraqi a baya. Sa'adu ganganci mirdeden qato ne, zabgege baqi wanda ya taso a qauye.
.
A shekarun baya kafin ya sami aikin Dansanda mahaukaci ne....! Bai ta6a shan inuwar sili ba, ko sunansa a da baya iya rubutawa. Har sanda ya samu wani Hedimasta a qauyen su suka sa labule a bayan aji, Hedimastan ya sayar masa da takardun firamare. Ko "zo in kashe ka." ba zai iya rubutawa ko karantawa ba."
.
Da yake a lkcn shiga aikin dan sanda ba wuya. Da aka je tantancewa duk tambayar da ake yi masa bai san me ake cewa ba." hatta sunansa da aka ce ya rubuta kasawa ya yi, jami'in tantancewa ya fara zzaginsa ya ce ya tashi ya ba mutane wuri.
.
Sa'adu ya tashi jiki ba qwari yana hade fuska, har ya kusa fita daga babban ofishin tantancewa, sai Jami'an dake aikin suka sake kallonshi. Sun tabbatar idan ya tafi an yi asarar namiji, matsalarshi kawai ba ilimi. Kafin ya fita daga ofishin ne suka yi saurin hada baki suka kira shi.
.
Don kada ya ga kamar abin aikin banza ne, sai da daya ya ja masa kunne ya gargadeshi cewar, lallai ya matsa ya iya rubutu da karatu in ba haka ba ko ya fara aikin sai sun sa an kore shi, aikin dan sanda ba na marar ilimi bane. Sa'adu ganganci ya bayar da takardunsa wadanda ya sako su a cikin leda. Ba a jima ba ya wucce kwalejin horo ta 'yan sanda. Duk atisayen da sketching yi bai ta6a faduwa ba." dalilin ce masa ganganci kuwa wannan baya rasa nasaba da halinsa. Duk wani abu mai hadari wanda kowa yake tsoron yi, Sa'adu yana lale marhabin da xuwan sa.
.
A qauyen nasu a da can ya ta6a zama yaron motar daukar kaya' wata doguwar a kori kura ce da Kawunsa ya dorashi akanta, ya ce ya zama kiyateka sbd direbansa yana cutarsa. Sun je wani gari sun yi lodi mutane fiye da hamsin sun haye saman motar sun yi rimi. Sai fada ya kaure tsakanin direban da Sa'adu ganganci. Direban ya jefowa Sa'addu mabudin motar, ya ce ya tuqa motar idan ya isa. Sa'adu a lkcn ko sitiyarin motar bai ta6a dafawa ba, amma sbd ganganci ya shiga motar ya tayar da ita ya ja buhuna arba'in da uku da mutane hamsin a saman kayan.
.
Da ya hau titi dole sai da motoci suka riqa sauka qasa suna bashi hanya, mutanen dake a saman motar suka rude, wadansu suna salati wadansu suna kuka suna roqqonshi ya tsaya su sauka don girman Allah kada ya kashe su."
.
A haka Sa'a ganganci ya kai su har qauyen da zasu sauka, yana tsayawa mutanen suka fara dirowa, bai kashe kowa ba a cikin fasinjojin, kowa ya sauka da rai, amma da aka dduba an samu fiye da mutum ashirin sun yi fitsari a wando. Tun daga ranar motar ta dawo hannunsa. Watansa daya yana aiki da ita ya kayar da ita a cikin wani rami, da yake lkcn bai dauko kowa ba, shi kadai ya sha wuya motar bata qara amfani ba, shi kuma bayan ya gama jinya sai ya koma sana'arsa ta gasa nama a qauyen su."
.
Wani mai kudin noma dake a qauyen ya ta6a sayen sabon janareto, ya zo dashi wajen da Sa'adu Kwatsami sana'ar nama ya ce a tayar masa dashi a gwada masa ya gani. An tayar da janareton kenan, mai kudin ya tafi gida zai yi wanka ya dawo, sai ga wani mai gurmi ya zo ya fara yiwa Sa'adu kirari, yana wasa shhi. Sa'adu ganganci ya kashe janareton ya ce ya dauka ya bashi.
.
Mai janaretln yana a bandaki yana wanka ya shafe kansa da fuskarsa da sabulu fari fat da kumfa, ya ji mai gurmi yana gdy yana cewa.
.
"Sa'adu ya ba mu janareto."
.
A haka bai ko wanke kanshi ba ya sako babbar rigarsa ya fito waje da gudu ya shawo kwana a rude don ya ji ko wane jannareto Sa'adu ya bayar ake yi masa gdy?"
.
Tun kafin ya fito dama Sa'adu ya gudu ya kama gabansa, Alajin qauye ya samu mai gurmi har ya nada gammo za a dora masa janareton a kansa.... Ya tsayar da shi ya qwacw janaretonsa, ya ce nasa ne ba na Sa'adu ba ne, ajiyar kawai ya bar masa kaffara ya je gida ya dawo..." fan dari ya ba mai gurmin ya ce yayi haquri.
.
Don haka Koda Sa'adu ya zama dan sanda wautarsa tana nan...ka idan aka zo da masu laifi aka sa su a sel. Da yazo ai ce a sa shi a ciki a kulle a ciki yana so zai wasa jininsa. Sa'adu ganganci ya ya bugi in buga da manyan 'yan ta'addan da ake kowowa folisiteshan, idan aka bude qofar ana zaton za a ga sun yi masa lahani, maimakon haka sai dai a samu 'yan cikin sell din a kwance, Suna juye-juye kamar tsutsotsin da aka daddatsa, wani ya karye, wani kuma ya kasa zama.
.
Sa'adu har so yake lkcn za6e yazo, yafi son a turashi maza6ar da tsagerun matasa suke, wadanda suke satar akwatu su ruga. Idan aka fara rigima za a sace akwati. Da zaran Sa'adu ya daukeshi ya rungume a jikinsa, to in duk mutanen dake a wajen zasu tarar masa, dole sai an kai akwatin lfy.
.
Ba a son Sa'adu yana kamo mai laifi, sbd wani laifinsa bai kai ya kawo ba." idan ya kamo hannun mai laifi suka tafi ofis, da an je kafin a fara yin komai dolene sai an nemo mai dori, ya dora karayar dake a hannun mai laifin. Don kuwa duk wanda Sa'adu ganganci ya riqa to dolene ya karyashi ba tare da ya sani ba." idan ya yi wani halin wauta, baya son ana fada a gabansa' domin kuwa shi a tsammanin sa daidai ya yi, kawai an rainashi ne ake damunsa da surutu.
.
Jarumtakar Sa'adu ganganci tana burge D.P.O Rabe, yana so duk inda zashi ace Sa'adu yana a bayanshi.
.
.
Lp=75}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 75
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Jarumtakar Sa'adu tana burge D.P.O Rabe, yana so duk inda za shi yasa Sa'adu a bayansa. Ba shi da wani matsayi a sashin aiki, sbd bashi da ilimi, bai san doka ba." amma ya qware a wajen aikin qarfi, indai za a kama mai laifi komin hatsabibancinsa da an hada mutum da Sa'adu ganganci dolene ya yi saranda.
.
Shi yasa a ynx da D.P.O ya samu umarnin a 6alle qofar dakin Mu'azzam a duba a gani ko Najib ya mance da wani abu wanda za a yi amfani dashi a gano inda ya shiga, sai ya tabbatar Sa'adu ganganci kawai zai sa ya yi masa wannan aikin hankali kwance da qarfi ba sai an sha wahalar nemo kayan aiki ba."
.
Da xuwansu qofar dakin Mu'azzam wanda yake a kulle, faffadan qwan wutar dake a gosshin qofar dakin ya haske ko'ina a wajen. D.P.O ya kauce gefe daya ya ce da Sa'adu ganganci
.
"ina so a bude mani qofar wannan dakin Sa'adu, ya za'ayi ne?" bamu zo da kayan aiki ba.
.
Sa'adu ganganci ya ce da shugaban sa.
.
"Akwai kayan aiki ranka shi dade. Ynxn nan za'a bude ta."
.
Sa'adu yana gama fada ya Ja da baya kamar ragon da zai yi karo, ya rugo aguje ya gwara kanshi da hannuwansa a jikin qofar, kwadon dake a jikin qofar ya fashe qofar ta karye, suka rufta ciki tare da Sa'adu ganganci, Sa'adu ya tashi ya bar qofar a karye da nata raunin, bai damu da nasa raunin ba wanda ya ji a hannuwansa. D.P.O ya sa kai ya shiga cikin dakin, wanda ya ke da haske tarwai kamar rana. Bai jinjinawa Sa'adu akan qoqarin da ya yi ba, don kuwa tuni ya saba da ganin wautarsa sau daya ko sau biyu ba." shi ne fa wanda ake fashi a wani gida kusa da folisiteshan, ya ce a barshi ya je shi kadai, baya son kowa ya taimake shi.
.
Sbd a yi maganinsa aka bar Sa'adu ya tafi a qasa, ba a san yadda ya yi gwagwarmaya da 'yan fashin ba, ya dai harbi mutum uku a cikin su." 'yan uwansu suka sa su a mota suka gudu, shi kadai din ya fasa su kamar yadda ya sha awash. Don haka Sa'adu yana da fada a wajen D.P.O, shi kadai yake yi wa D.P.O Rabe abu ya kwana lfy, sai dai a zage shi, don kada ya ga kamar ana wasa dashi ya riqa kawo raini. Amma ba wanda D.P.O yake so sama dashi a duk cikin 'yan sandan.
.
D.P.O Rabe yana shiga dakin Mu'azzam sbd tsabar dadewarsa yana aiki ya ce da Sa'adu ganganci
.
"Na ji warin gawa a dakin nan Sa'adu' zo ka shiga ka duba ko'ina ka fito min da ita a duk inda aka 6oye ta."
.
Sa'adu ganganci ya shiga cikin dakin, ya wuce D.P.O Rabe, ya fara janye dirka-dirkan kujerun dake zagaye da falon, yana dubawa kamar yana neman mushen 6era. A sannan ne shi kuma D.P.O ya kai ganinsa wajen simintin dake a tarwatse a dai-dai inda Mu'azzam ya fasa ramin da ya yi a bangon. Wannan shi ya yi saurin jan hankalin D.P.O Rabe ya matsa wajen ya duqa ya yi nazarin 6aragusan simintin da ya xubo daga jikin bangon, yasa hannu ya

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment