Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take son xuwa ba, ya tabbatar ta tsorata dasu, bata da qarfin guiwar da zata iya guduwa daga wajensu a halin ynxn.
.
Hauwa ta shiga daya dakin wanda yake jere da dakin da sadi yake ciki yana ta sharar barcinsa. Ta turo qofar dakin ta rufe, don tayi sallah. Minti goma bayan haka tana a zaune a kan darduma dake a malale da tsakar dakin, lulli6e da wani mayafi da ta dauka wanda ta sameshi a cikin kayan matar dake da dakin. Wacce Hauwa ta tabbatar ita ce su sadi suka turasu su kwana bandaki tare da mijinta
.
Zaman da Hauwa tayi ne a halin ynxn bayan da ta idar da sallar ta daga hannu tayi addu'a, ta roqi allah ya fitar da ita daga cikin wannan qangin. Hawaye ya xubowa Hauwa don kuwa ita kanta ta san cewar tayi kuskure a rayuwarta. Ta dade tana bin son xuciyarta, bata jin nasihar mutane, da ace tuntuni ta gyara tsarin rayuwarta a baya, da duk wadannan masifun basu fado mata ba." nura! Babu shakka shine sanadin koma me ya faru da ita.
.
Hauwa tana cikin tunanin ne ta ji sadi qare-garke ya fito daga cikin dakin da ya kwana, ta ji ya tambayi Shago.
.
"ina Hauwa likita take?"
.
Shago ya ce dashi.
.
"oga tana daki tana sallah."
.
Sadi ya yi shiru xuwa can sai ta ji yana cewa.
.
"suma wadancan na cikin bandakin a kwancesu mana su fito su Sha iska Shago."
.
Shago ya ce.
.
"oga a rabu dasu kawai wadann bamu da buqatar su sai xuwa jimawa."
.
Sadi yayi farat ya ce da Shago
.
"baba ya fara motsawa, ina jin ynxn nan zai farfado. Ga hannunsa nan yana motsi."
.
Hauw ta taso cikin sauri ta tsaya a bakin qofar ta leqa ta ramin qofar tagar sadi ya tsugunna yana ta6a Nalamma. Shago ya taso yana riqe da taba a hannunsa, ya matso kusa da Tsohon shima.
.
Nalamma ya sake motsawa, ya yi tari sannan ya fara qoqarin bude idanunsa. Hauwa ta ji gabanta ya fadi. Babu shakka Nalamma ya farfado. Ta ga sadi ya kamashi ya miqar dashi zaune yana tarairayarsa ya ce
.
"hannu baba. Daure ka zauna, bari a kawo maka ruwa ka sha."
.
Nalamma ya bude idanunsa a rude yayi magana bakinsa yana rawa ya tambayesu
.
"a ina nake..?"
.
Sadi yayi masa murmushi ya ce.
.
"har ynxn kana nan a duniya baba baka mutu ba." har ynx muna nan tare da kai, mune dai jikokin nan naka dake tambayarka abin nan da ka 6oye. Dama kai muke ta jira tun jiya ka farfado ka fada mana. A ina suke baba? Ka daure ka yi magana."
.
Hauwa ta ji wani sabon tsoro ya sake kamata da taga Nalamma ya 6ata fuskarsa, kamanninsa kamar na Tsohon aljani. Ya sake taqarqarewa daqyar ya ce dasu.
.
"me yasa baku kashe ni ba?" me kuke jira? Ku kashe ni in huta ba zan fada maku ba."
.
Shago ya sake matsowa daf da shi, sadi ya ci gaba da yiwa Tsohon murmushi ya ce.
.
"ba zaka mutu ba baba. Tun jiya na fada maka wahala zaka yi ta sha a banza, amma ba zaka mutu ba. Ynx haka mun samu wata likita tana nan a cikin daki, ynxn nan zata fito, mun dauketa aiki ne kawai don ta riqa kula mana da lfy ka. Duk wahalar da zaka sha zata yi qoqari ta baka allura da magunguna qarfinka ya sake dawowa. Ka fada mana abin da muke so ka huta da wahalar nan baba."
.
Nalamma wanda yake a hannun sadi baya iya ko zaunawa da kansa sbd jikinsa babu qarfi, ya kausasa muryarsa ya ce da sadi.
.
"sai dai ku gaji ku kasheni 'yan banzan yara, amma ba zan fada ba..."
.
Tun kafin ya gama fadar abin da yake so, Shago ya daga tabar da yake sha tana hayaqi, kanta jawur da wuta ya dosanawa Nalamma a fuska, ya danna da qarfi, wutar ta shigeshi sosai. Tsohon ya rintse ido ya cije baki yana qara. Hauwa ta runtse idanunta cikin kaduwa, bata ta6a ganin rashin imani irin wannan ba."
.
Sadi ya janye hannun Shago wanda hakan ya bayyana ta'adin da tabar tayi a fuskar Tsohon....
.
Kuncinsa ya qone har fatar wajen ta dauke cikin lkc qanQani.
.
Sadi ya ce da Nalamma
.
"laifinka ne baba, ka cika taurin kai....
.
.
Page 39 is comming soon inshaa allah.}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 39
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Laifinka ne baba, ka cika taurin kai, ba a son raina nake yarda kana aiki tare da Shago ba." ka qi bani hadin kaine kayi magana mai dadi, wacce zan gamsu da ita."
.
Nalamma ya ja numfashi daqyar idanunsa suka firfito kamar zasu fado qasa. In aka dauke idanun da kuma ranqwamemen kansa babu wani abu dake da alamar rai a jikinsa. Ya sake jajircewa ya ce da sadi.
.
"qarya kuke yi shegun yara, baku isa ku ji inda na 6oye wannan dukiyar ba,ya kome zaku yi mani."
.
Shago ya sake matsowa da hannunsa kenan zai dosanawa Tsohon tabar a idonsa na dama, sai Hauwa ta yi qarfin halin fitowa daga dakin tana kuka.
.
"ku dakata. Ku rabu dashi."
.
Ta ce a lkcn da ta matso wajensu, sadi da Shago suka mayar da hankalinsu akanta. Hauwa ta tsayar da kukan da take yi, ta ce dasu kai tsaye.
.
"ni na san inda gwala-gwalan suke, zan kaiku ku ga wajen da kanku. Don allah ku rabu dashi, kada ku sake ta6ashi."
.
Sadi wanda ya kadu da jin kalaman Hauwa likita ya miqe tsaye ya fara yi mata magana.
.
"ke ba a yaudarata a kwana lfy. Kada ki 6ata mana aikinmu, idan kin san qarya kike yi, ki rufawa kanki asiri ki koma daki ki jiramu mu caji baba, idan mun gama sai in kira ki ki ci gaba da naki aikin."
.
Hauwa ta ce da sadi cikin magiya.
.
"ba qarya nake yi maku ba." ya fadi mani inda gwala-gwalan suke. Kuma mun je wajen ni da saurayina mun haqosu jiya da daddare. Da saurayina ya haqosu ne ya biyoni zai kashe ni na gudu, shi ne na fado nan wajenku da daddare."
.
Hauwa ta share hawayenta, ta durqusa gaban Nalamma ta ce dashi cikin ladabi.
.
"kayi haquri baba, na san nayi kuskure, ka gargadeni kada in fadiwa kowa, to amma ina son nura, da na fada masa ne ya ci amanata, ya yi yunqurin ya kasheni don ya riqe gwala-gwalan shi kadai."
.
Nalamma wanda ya bi Hauwa da kallo cikin takaici yayi shiru bai ce komai ba." sadi ya sa hannu ya fusgo Hauwa ta baya, ta juyo ta dubeshi a kidime, ya zaro mata idanu ya tambayeta.
.
"ina saurayin naki yake a halin ynxn?"
.
Hauwa ta ce tana kuka.
.
"ni dai tunda ya biyoni ban san yadda akayi na gudu masa ba." na waiga ne naga ban ganshi ba, ban sani ba ko ya koma ne..."
.
Sadi ya dakatar da ita ya sake daka mata tsawa.
.
"lkcn da ya biyoki zai kasheki ya kwashe dukiyar tana wajensa? Ko kuwa a can ya barta?"
.
Hauwa ta ce a tsorace
.
"a can ya barsu a qasa, ya biyoni har muka yi nisa bai koma ba..."
.
Sadi ya cire hannu ya wanke Hauwa da mari, iya qarfinsa har sai da taga wuta. Hauwa ta kwarara ihu iya qarfinta, ta fadi qasa. Sadi ya riqeta da hannu daya ta bayan rigarta ya ce da ita.
.
"munafukar yarinya. Tun jiya kina jin muna zancen nan, kin san abin da muke nema, amma kika barmu muka yi ta 6ata lkc baki yi mana bayani ba."
.
Sadi ya juya inda yaronsa Shago yake yana durqushe yana kallon abin dake faruwa tsakanin sa da Hauwa ya ce dashi...
.
"Shago daga Hauwa likita ta mununceni ko?"
.
Shago ya ce da sadi qare-garke
.
"to oga laifin waye? Ba kai ka ke cewa a yi komai a hankali ba?" tun jiya da mun cajeta sosai tunda dai ta san inda gwala-gwalan suke da tuni tayi mana bayani mun je mun kwashesu. Ynx Wataqila shi saurayin nata ya kwashesu ya gudu."
.
Sadi ya ce a fusace.
.
"a'a, qarya ne, ko ina wadannan gwala-gwalan suke, sai mun je mun daukosu. Ynx ba zama zamuyi ba, tafiya zamu xo muyi, Hauwa ta rakamu inda wajen yake mu gani da idonmu. Hada mana kayanmu ka kai cikin mota mu tafi. Mun gama yada zangonmu a nan, aiki ya koma kan Hauwa likita ynx."
.
Sadi ya saketa ta fadi qasa ta kifa kanta akan guiwarta tana rusa kuka kamar ranta zai fita. Cikin gaggawa suka fara hada kayayyakin da suke so, da nasu da wadanda suka tarar a gidan ba nasu ba." shago ya kaisu cikin mota. Da ya dawo ne ya tambayi sadi.
.
"oga ya zamu yi da baba? Ina ganin ynx amfaninshi ya qare a wajenmu tunda dai mun gano abin da muke so ya fada mana."
.
Sadi ya ce dashi cikin fada.
.
"wa ya ce maka amfanin baba ya qare sakaran banza? Ai ynx ne baba yake da amfani. idan mun gano inda gwala-gwalan suke, wa zai tabbatar mana da sune gwala-gwalan ainahi wadanda baba ya tona rami ya rufe? Ai dolene mu ci gaba da aiki tare da baba da kuma Hauwa likita, sune zasu tabbatar mana da gwala-gwalan na gaske ne idan sun sake ganinsu? Dauki baba ka kai shi cikin mota, zamu taho ni da Hauwa ynxn nan."
.
Shago ya sa hannu daya ya dauki Nalamma kamar ya dauki buhun 6awon kara, ya fita dashi ya kaishi cikin mota, kafin ya dawo ne sadi ya je ya yiwa masu gidan magana suka bude qofar bandakin ya ce dasu, su fito haka nan.
.
Mijin da matar suka fito hankalinsu a tashe, sun galabaita da yunwa da rashin barci, ga kuma uwa-uba rashin mazauni mai kyau, a tsaye suka kwana. Matar wacce ta fi mijinta shan wahala daqyar take iya tafiya da fitowarsu suka zauna a qasa gaban sadi cikin girmamawwa kamar malami da dalibansa. Sadi ya ce dasu.
.
"lkcn tafiyarmu ya yi, dama na fada maku zai yiwu mu tafi a kowanne lkc, idan mun gama aikinmu. Ina son in gargadeku kada kuyi yunqurin tona mana asiri bayan mun tafi. Zamu dauki motarku mu tafi da ita sbd zata yi mana amfani. na san a shirye kuke da zaran mun bada baya ku je wajen 'yansanda kuyi masu bayani akanmu, su bi su kamamu."
.
Sadi qare-garke yayi dariya kadan sannan ya girgiza kansa ya dubi mijin da matar tasa wadanda suka yi masa quri da idanu ko qyaftawa basu yi ya ce dasu.
.
"idan kuka kuskura kuka yi hakan, ina tabbatar maku cewar zamu sake dawowa nan gidan wata rana. Ba sai na fada maku abin da zai biyo bayan sake dawowarmu ba wajenku, kuma kun san abin da zai faru."
.
Mijin yayi saurin cewa da sadi.
.
"Wlh babu wanda zamu fadawa, ba zamu ce komai ba."
.
Sadi ya juya ya basu wuri ya ce da hauwa, wacce ta dawo tana shassheqar kuka ynx, tun sanda ta ji yana gargadin masu gidan. Sadi ya ce da ita.
.
"ke kika jawowa kanki na mareki Hauwa likita. Bana son munafunci idan ina aiki. ki kiyaye a lkc na gaba, taso mu je dajin da kuka haqo gwala-gwalan zamu yi bincike tare dake, ko waye ya dauki dukiyar nan zamu bi sawunsa mu kamashi, kuma dolene ya fito mana dasu, ko'ina aka kaisu sai sun dawo hannunmu."
.
Hauwa ta tashi tana share hawaye ta bi sadi suka fice daga gidan suka samu Shago ya zaunar da Nalamma a kujerun baya na motar, ya fito yana jiran su suzo su shiga. Da sadi ya qariso wajen motar ne shi da hauwa, kafin su shiga sai Shago ya tuna wani abu ya ce da sadi.
.
"nayi mantuwa a cikin gidan nan ogga. Ina xuwa."
.
Sadi ya ce dashi cikin damuwa.
.
Kayi sauri ka fito mu tafi ba 6ata lkc zamuyi ba."
.
Shago ya koma cikin gidan da gudu, ba wani abu ya mance ba." tun jiya da baqin cikin wani abu ya kwana a ranshi. Tun xuwansu gidan yake ta bincike yana neman karta suyi caca shi da oganshi sadi bai samu ba." duk inda ya duba sai dai yaga litattafan karatu da tarin jaridu. Abinda ya baqanta masa rai kenan, ya ke son ya shiga ya koyawa masu gidan ladabi su riqa ajiye karta a lkc na gaba.
.
Shago ya shiga gidan ya samu mijin da matarsa sun yi jugum a zaune, da ganin fadowarsa cikin falon, suka miqe a tsorace. Shago ya dubesu ya fara yi masu hargaginsa.
.
"tsakanin kai da matarka waye yake ajiye wadann takardurdun banzan a nan gidan?"
.
Mutumin ya ba Shago amsa a tsorace.
.
"ba takardun banza bane ranka ya dade. (Documents) dina ne da kuma (Newspapers) din da nake ajiyewa.
.
Tun kafin ya kai qarshe Shago yayi sufa ya dirar masa. Mai gidan ya xulle ya nufi dakinsu a guje yana ihu, Shago ya bi shi a karce kamar mage da 6era suka fada cikin dakin tare. Matarsa ta jingina da bango tana kuka cikin xullumi. Da ta ji Shago ya ritsa mijinta a daki suna ta hargitsa kayayyaki mijin yana ihu. Bayan wani lkc sai shago ya fito a fusace ya samu matar a falo ya nunata da yatsa ya ce da ita.
.
"ki fadawa mijinki nan gaba ku riqa ajiye karta a nan gidan. Ba tarin takardun banza ba."
.
Shago ya fita cikin sauri ya koma wajen su sadi dake jiran ya fito su tafi. Da fitar Shago matar ta ruga cikin dakin ta samu mijinta a zaune rashe-rashe kamar dan shayi ya jingina da bango. Fuskarshi tana ta xubar da jini, kamar wanda yayi hadarin mota, Shago ne ya bar masa wannan alamar don ya riqa tunawa dashi. Matar ta fashe da kuka ta tambayi mijin nata.
.
"me yayi maka? Ya aka yi fuskarka ta koma haka? Mun bani mun lalace, da wadannan zzaluman mutane."
.
Mijin nata yace da ia a tsorace.
.
"hada manakayanmu mu bar gidan nan, daga yau mun gama zamaa wannan gida....
.
.
Lp=40}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 40
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Hada mana kayanmu mu bar gidan nan, daga yau mun gama zama a wannan gidan, zamu koma cikin mutane muyi rayuwarmu kamar kowa."
.
Matar bata yiwa mijin nata musu ba, sbd jiki magayi ne....! Ta fara hada kaya, cikin minti ashirin suka fito daga gidan dauke da akwatinan kayansu kamar 'yan gudun hijirah. suka nufi wani qauye inda mutane suke. A ynx kam sun tabbatar jama'a, rahama ne....!
.
A lkcn su kuma su sadi sun yi nisa sun doshi dajin tudun kudi tare da Hauwa likita da dan tsoho Nalamma. sun yi alqawarin ko a mutu ko a yi rai, sai sun cimma burinsu na mallakar wadannan ma'adanai masu daraja.
.
Lokaci ne kawai zai nuna wa zai kai labari a gobe? Sannan kuma jar kasa a kabarin wa za a gani gobe bayan gari' idan rigimar ta dauki zafi?
.
.
Ku biyomu a littafin "gobe jar kasa 3"
.
.
Nan muka kawo qarshen littafi na 2
.
Ga kuma ci gaban shi daga
.
}~~~~~~{ gobe jar kasa 3 }~~~~~~{
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
Tare da ni
Abu ihsan bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Mu'azzam ya dubi agogon dake a hannunsa yaga qarfe sha biyu da rabi na rana har da minti uku. Ya sake fitowa daga ccikin shagonsa a karo na kusan biyar ya waiga 6angaren dama da shagon nasa inda rabi 'yar fulani take ajiye qwaryar nononta idan tazo kasuwar, a kusa da wata bishiyar tsamiya. Mu'azzam ya yi tsaki da yaga bata zo ba, babu kowa a wajen.
.
Ya tsaya a bakinn shagon ya sa hannunshi a cikin aljihun qaton wandonsa wanda duk da fadinsa da tsawonsa Mu'azzam daqyar yake quga wandon a jikinsa sbd girman jikinsa da qibarsa. Wani wanda bai san Mu'azzam ba idan ya gashi a haka sai yayi zaton babban mutum ne dan shekara arba'in, wanda hakan ya sa mutane da yawa baqi suke girmamashi.
.
To amma har ynx Mu'azzam bai gama cika shekararsa ta ashirin da daya ba." qaramin yaro ne wanda ya taso da ruwa-ruwan jiki, tun yana dan shekara sha-uku ya zama jibgegen qaton da duk fadin unguwarsu babu qato kamarshi.
.
Mu'azzam fari ne mai qananun idanuwa, da faffadan hanci wanda ya kusa 6acewa a cikin faskekiyar fuskarsa dake kama da danyen naman da ya kwana. Akan dade Mu'azzam bai yi dariya ba, idan ya zauna akan kujera indai ba kwastone ya zo ba, to a duk fadin kasuwar babu wanda ya ishe shima magana. Tun farkon bude masa shagon da yazo ya fara zama, maqwabtansa dake da shaguna a kusa da shagonsa da suka fahimci halinsa na qyashi sai suka riqa yin taka-tsan-tsan dashi.
.
Mu'azzam mugu ne wanda bai mayar da cin kayan haram a bakin komai ba. Ko ynx fushin da yake yi na rashin xuwan rabi mai fura da nono, yana son shan furar ne sbd tun safe bai karya ba." idan rabi ta hada masa fura ko ya sha baya biyanta, sai dai suyi ta lissafi na wata da watanni. Idan kudin sun yi masa yawa sai yayi mata rinto ya rage yawansu, yayi ta rantsuwa ya ce mata iyakarsu kenan.
.
Wani lkcn rabi ta kan yi fushi ta ce ba zata qara damo wa Mu'azzam fura ba, tunda dai taurin bashi gareshi. Idan yaga haka sai ya ce a cikin kudin da take bin sa nawa zata taimaka ta rage masa, zai biyata. Dole sai rabi 'yar fulani ta raba kudin da take bin sa kashi biyu ta ce ta yafe masa rabi, sannan Mu'azzam zai dan ciro wani abu ba duka ba ya rage mata don dai ta ci gaba da damo masa furar Kullum yana sha a banza baya biya.
.
Kayan dake a shagon Mu'azzam sun kai na milyan biyu. Babu komai a ciki sai 'yan kunne da sarqoqin mata masu tsada da sauran kayan qarau na kwalliyar daki. Shekara daya kenan da budewa Mu'azzam wannan shagon, kuma daga wannan lkcn xuwa ynx a wani lissafi na fushi da alh. Madugu ya yi, ya ce an yi asara ta kai ta milyan hudu sbd ko Mu'azzam yayi ciniki baya kaiwa, sai dai ya bisu ya cinye duka. Da yake ba a son shagon ya muttu, ba a son Mu'azzam ya dawo gida ya zauna haka nan, da zarar alh. Madugu mijin yayarsa ya gama yin qorafi haka nan zai sake xuba masa wasu kayan, kafin a kai lkcn da Mu'azzam zai sake muurqushe su."
.
Mu'azzam maraya ne gaba da baya, shi ne dan auta a dakinsu. Tun shekaru goma sha-tara da suka wuce sanda yayarsa haj. Maimuna zata auri alh. Madugu ta zo dashi gidan, don basu da wanda zai riqeshi tunda iyayensu duka biyun sun rasu. Alh. Madugu hamshaqin attajiri ne, ma'aikacin gwamnati ne wanda a ynx ya rikide ya zama babban dan siyasa, yake kuma kokuwar neman kujerar sanata bakinn rai bakin fama.
.
Idan har akwai abin da alh. Madufu yafi tsana a rayuwarsa, bai wuce ya zauna da wanda zai riqa xubar masa da mutunci a idon mutane ba. Shi yasa baya son zama da Mu'azzam ko misqala zarratan. Ya sha yunqurin korarsa daga gidansa, haj. Maimana take rarrashhinsa tana roqonshi yayi haquri da halin qaninta Mu'azzam tunda maraya ne. Tun yana yaro yake riqe dashi ynx shi ne ubansa, idan ya kori Mu'azzam ina yake son ya je ya zauna?
.
Da irin wannan magiyar Alh. Madugu yake huccewa, amma ba don yana son zama da Mu'azzam ba. Tun yana yaro yake fama dashi, tun tasowar Mu'azzam yake da wannan halin na mugunta da zalunci. Idan ya toge a qofar gida baya shiga cikin yara suyi wasa. Sai dai idan tsautsayi ya sa wani yaxo kusa dashi sai ya sa qafa ya tokareshi ya ruga cikin gida ya bar yaron yana 6urari a waje. Iyayen yara da yawa a layin sun sha su xo su kawo kashedi a wajen alh. Madugu kan ya tsawatawa Mu'azzam ya daina zaluntar 'ya'yansu don yaga yafi su qarfi.
.
Da Mu'azzam ya fara girma ya daina cutar yara, sai ya dawo kan abokansa. Ba wanda yake so ya ci abinci dashi sbd hadamarsa, kafin mutum ya kai hannu sau daya Mu'azzam ya wawushe abincin shi kadai ya cinye. Idan yazo dakin mutum ya ari kayansa, to sai dai mutum ya bar masa. Mu'azzam bai ta6a yin aro ya dawowa da mai shi ba." duk abin da yazo hannunsa yazo kenan, ya kuma cinyeshi har abada.
.
Maganar karatu kuwa a wajen sa, wannan dama tuni an daina zancen, don kuwa Mu'azzam baya iya gane karatu, da ya zauna a aji zai fara barci, Kuma in za'a wuni ana bashi horo ba zai daina ba." abin da yafi qwarewa a makaranta fiye da komai shi ne sanya yara kuka.
.
Kafin a tashi kullum daga safiya xuwa rana, Mu'azzam bai yi zalunci sosai ba idan ya raunata yara goma.
.
Da aka koreshi a sakandire ne wani malami da yake mutunci da alh. Madugu ya same shi har gida ya bashi shawarar ya nwmawa Mu'azzam sana'a. Don kuwa ba zai iya tsayawa yayi karatu ba sai dai yayi ta jawo mashi fitina kullum.
.
A sannan ne alh. Madugu ya nemar masa sana'ar takalma ya bude masa shago a bakin titin dake a kusa da gidansa. A wata biyu kacal Mu'azzam ya cinye kudin shagon ya rufeshi ya dawo ggida ya kwanta babu aikin yi. Alh Madugu ya ssha alwashin ko kwabo ba zai sake bashi ba tunda shi mutumin banza ne....!
.
Ganin haka sai Mu'azzam ya ci gaba da rayuwarsa ta nemo rigima a unguwar, kullum sai yayi fada ya raunata wani ko da makami ko kuma da zafin duka. Idan duk wannan bai samu ba Mu'azzam ya kan tsaya a zaure duk yaron da aka aiko gidansu sai ya mintsileshi a duwawu.
.
Dole mutane suka daina aiko 'ya'yansu gidan, ko kuma idan za'a aikosu sai ace kada su bi ta gidan alh. Madugu sbd tsoron muggun nan Mu'azzam. da alh. Madugu ya ji maganar mutane ta iskeshi a layin, gashi babban mutum dan siyasa yana tsoron wani abu da zai sa mutane su tsaneshi, sai ya kira Mu'azzam ya ce ynx me yake so a yi masa don ya daina wannan dabi'a ta banza da wofi?
.
Mu'azzam ya ce yana so ne a bude masa shagon sayar da sarqoqin gwal a kasuwa.
.
.
Lp=41}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 41
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Mu'azzam yace yana son a bude masa shagon sayar da sarqoqin gwal a kasuwa, alh. Madugu ya kira matarsa had. Maimuna ya kira Mu'azzam ya ce ta zama shaida, zai bude masa shago zai xuba masa kayan milyan biyu' amma a wannan karon idan bai yi a hankali ya ririta kudin shagon ba, idan ya rushe kudin to shi da Mu'azzam haihata-haihata. Sai ya sa 'yansanda sun kamashi sun kulle.
.
Haj. Maimuna ta ce ta amince zata ja masa kunne ya kula, aka budewa Mu'azzam shagon, ko wata daya ba a yi ba ya ragargazashi. Don kada alh. Madugu ya gane abin dake faruwa, Haj. Maimuna ce ta sa kudinta aka qara kayan shagon suka dawo yadda suke. Ta yiwa Mu'azzam zagin fitar hankali, to amma mai hali baya barin halinsa, da anyi wata daya, biyu ko uku shagon yake qara durqushewa dole sai alh. Madugu ya qarawa shagon qarfi sannan komai yake dawowa daidai. yana yin haka ne kawai don dai Mu'azzam ya riqa yin wani abu, kada ace ya lalace yana yawon banza a gari, ya riqa jawo masa abin magana a wajen mutane.
.
Ba wata hanya Mu'azzam yake bi wajen 6annatar da kudinsa ba sai a kulob-kulob din holewa na dare. Da ya je mashaya karuwai zasu yo masa can! Don kuwa ba wani abu bane don Mu'azzam ya sayi giya kires goma ya ce kowa yayi ta sha. Mutanen kirki basu cin kudinsa, tsakaninshi dasu sai dai tsabar mugunta, amma idan ya yi golewa a wajen taqadaran bariki to anan don ya yi gwaninta zai iya kashe ko milyan ne a tashi daya bai damu ba."
.
Haj. Maimuna bata haifi 'ya'ya da yawa ba tare da alh. Madugu, 'yar ta daya kawai ta rage a gidan wacce ta fara haihuwa shekararta sha-takwas. Sunanta larai. Ta kasance kyakkyawa, tamkar mahaifiyarta. Kuma ynx haka tana zaune ne a gida tana jiran fitowar sakamakon jarrabawar da ta zauna ta qarshen karatunta na sakandire.
.
Mu'azzam ya koma cikin shagonsa ya sake

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

4 months ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment