Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan asabe wanda yake a shiyyar da aka sace Nalamma ya dauki qwararrun yaransa hudu dake a sashin kula da laifuka da ta'addanci, suka dunguma xuwa asibitin da Hauwa take aiki inda aka sace Nalamma' don ganawa da masu lura da asibitin, da kuma likitocin da suke akan aiki lkcn da al'amarin ya faru a daren da ya gabata.
.
Da xuwansu asibitin suka samu babu mutane, basu yi mamaki ba domin kuwa a dalilin gobarar da ta tashi jiya da daddare a asibitin, an sallami marasa lafiyan dake jinya, sun koma wadansu asibitocin har xuwa lkcn da za a yi gyaran gagarumar 6arnar da aka yi.
.
Kowa yana sane da labarin da ake ta yi cewar wasu mutane ne suka zo suka sace mara lfy a asibitin. Da kuma dalilin sace shi da akayi. Shi kansa Dakta saminu wanda shine babban likitan asibitinn, yana kan aiki abin ya faru a daren jiya. Bai san dalilin da yasa wadann 6arayin suka zo suka tayar da gobara suka sace wannan tsoho ba, kuma bai san dalilin da yasa Jami'an tsaro suka kawo shi suna kaffa-kaffa dashi ba."
.
Tun faruwar al"amarin dakta saminu bai samu sukuni a xuciyarsa ba." inda ya godewa allah babu wanda ya qone acikin mutanen da gobarar ta ritsa. Sai da gari ya waye da safe bayan hankali ya dan kwanta, sannan ya tara sauran ma'aikatan dake a asibitin suka yi taron gaggawa suka yanke hukuncin sallamar duk wani mara lfy, don su mayar da hankalinsu wajen gyaran asibitin, kada aiki yayi masu yawa ba isasshen wurin da zasu kwantar da mutane.
.
Duk da sun sallami marasa lfyn, dakta saminu bai iya barin asibitin ba, ya zauna a ofishinsu yayi jugum yana jimamin faruwar wannan al'amarin, bai ta6a fuskantar wata masifa kwatankwacin wannan ba a tarihin aikinsa na tsawon shekara goma sha-bakwai a duniya.
.
A nan Jami'an tsaron suka zo suka same shi, bayan sun ajiye motarsu mai duhun gilasai a wajw. A.c. Tanko wanda shine jigon binciken wanda kuma bai yarda ya nada kowa ba, da kanshi ya fito wannan aikin, shi ya fara yiwa dakta saminu magana bayan gabatar da kansu a wajensa. Sauran Jami'an tsaron suka tsaya a waje a bakin ofishin suka bar shugabansu tare da likitan suna magana a hankali.
.
Dakta saminu bai yi mamakin ganin Eriya kwamanda da kanshi a asibitin baya san akwai wani babban al"amari wanda ya shafi sace Tsohon da aka kawo masu asibitin. ya san ba haka kawai za a zo a qona masu asibiti a dauki wani mara lfy a gudu dashi ba." dolene a samu wani abu a qarqashin wannan ta'addancin.
.
A.c. Tanko ya tattara hankalinsa wuri guda ya kalli siririn likitan dan kimanin shekaru arba'in da bakwai ya ce dashi.
.
"a sakamakon abin da ya faru jiya da daddare, wanda ya jawo raunata yaranmu biyar da kuma qona asibitin nan da akayi aka sace wani Tsohon fursina, me ka sani game da wannan al'amari?"
.
Dakta saminu yayi ajiyar xuciya ya ce da shi.
.
"ban san komai ba yalla6ai, ni dai na shigo ba da dadewa ba sai muka ga wuta ta tashi. A sannan ne su (police) dake tare da Tsohon suka fara harbi, mu kuma muka 6oye, sai da abin ya lafa sannan muka firfito, muka taimakwa marasa lfyn dake a dakin da gobarar ta tashi, muka kaisu wadansu (ward) din."
.
A.c. Tanko ya gyada kai cikin gamsuwa da bayanin likitan ya sake tambayarsa.
.
"sanda (police) suka kawo mara lfyn, kana asibitin, kai ka yi masa aiki?"
.
Dakta saminu ya yi saurin girgiza kai.
.
"a'a....bani nan, bai nayi masa (treatment) ba." Hauwa ta amshesu ta basu daki. Ta sa masa (Drip). na dawo ne na same su."
.
A.c. Tanko ya tambaya.
.
"wace ce Hauwa?"
.
"wata (nurse) ce a nan da muke aiki tare da ita."
.
Dansandan ya mayar da hankalinsa akan Hauwa ya sake buqata.
.
"tana nan abin ya faru ita Hauwa din, ko kuwa?"
.
likitan ya ce
.
L"a'a, a lkcn ta tafi gida. Amma dai ita tayi wa mara lfyn (treatment)."
.
A.c. Tanko ya sake gyada kai cikin gamsuwa ya ce.
.
"bayan faruwar al'amarin Hauwa ta sake xuwa asibitin ko kuma ta bugo maka waya da ta samu labarin abin da ya faru?"
.
Dakta saminu ya ce.
.
"tunda ta tafi jiya ban sameta ko a waya ba, duk ma'aikatanmu wadanda basu nan abin ya faru sun zo da suka ji labarin abin da ya faru, wadansu kuma sun kirani a waya sun tambayeni yadda akayi gobarar ta tashi, amma Hauwa bata zo ba, kuma bata kira waya ba har ynx."
.
Dansandan ya sake gyada kai ya ce da likitan.
.
"zan so mu je ka kai ni gidansu ita Hauwa din, akwai tambayoyin da nake so yi mata."
.
Dakta samunu ya ce.
.
"ba matsala yalla6ai gidansu ba nisa, ko ynx in ka shirya muna iya xuwa ka ganta."
.
Da yake motar da Jami'an tsaron suka hawo qirar (Jeep) ce ba tsarar kwararra6a66un tasi-tasi din da Hauwa ta saba hawowa bane idan zata je aiki. A cikin minti bakwai motar ta kai su har qofar gidansu Hauwa daga asibitin karama.
.
A.c. Tanko tare da yaransa hudu, da kuma dakta samunu, suka fito daga cikin motar, tsirarun mutanen da suka rage a layin, suka dawo da hankulansu kan 'yansandan. Kowa yana so yaga abin da yake faruwa a gidan su Hauwa. dama daxu da safe an ji mahaifiyarta ta fito a rude tana tambayar mutane wai Hauwa 'yarta bata kwana a gida ba. Don allah a taimaketa a cigita mata, bata san me ya faru da ita ba." tunda dai ita basu yi zata kwana a wani waje ba."
.
Babu wanda ya mayar da hankali ga maganar mama delu, tunda dama mutanen unguwar suna zarrgin cewar ita take sakarwa 'yarta fuskar duk wani tambadewa da take yi, sbd taga tana aiki tana daukar albashi tana bata, shi yasa bata iya tsawata mata.
.
Ganin 'yansanda ynx a qofar gidan ya sa wadanda tsohuwar ta samu da maganar 6acewar Hauwa, suka fara matsowa kusa suna cewa ai dama sun san za'a rina. Wai an saci zanin mahaukaciya.
.
Dakta saminu ya saba, yana shiga gidan su Hauwa kai tsaye. Da fitowarsu ya ce da A .c tanko.
.
"bari in shiga in kirata kuyi magana yalla6ai."
.
Dansandan ya bashi dama, dakta saminu ya shiga gidan ya yi sallama. Mama delu wacce ta zauna a qofar dakinta tayi tagumi, ta amsa sannan ta dago kanta. Bata gane mutane don suna xuwa gidan, da ganin likitan ta san a cikin abokan aikin Hauwa ne, amma bata iya cewa ga sunanshi tunda sun sha xuwa gaisheta idan bata da lfy, su kawo wani abu su bata, amma bata san sunan kowa ba a cikinsu. Suna dai da kara, in wani abu ya faru suna xuwa a gaisa.
.
Dakta saminu ya samu tsohuwar wacce ta gyara murya ta ce dashi.
.
"sannu da xuwa."
.
Ta sauka daga kan qaramar kujerarta ta kitso ta miqawa likitan.
.
"ga kujera ka zauna."
.
Dakta saminu ya ce.
.
"a'a mama na gode ba zama nazo yi ba."
.
Ya gaisheta a tsaye ko ran rage tsawo bai yi ba, mama delu ta amsa tana a durqushe bata sake jawo kujerar ta zauna ba."
.
"dama nazo wajen Hauwa ne....! In tana cikinn daki ayi mani magana da ita mama."
.
Delu ta sae gyaran murya, ta dago da busassun idanunta.
.
.
Lp=49}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 49
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Delu ta sake gyara murya, ta dago busassun idanunta wadanda ko ba a fada ba da ganin su, basu yi wani isasshen barci ba a daren da ya gabata. Ta kalli Dakta saminu ta ce dashi...?wannan
.

"Hauwa bata kwana gida ba, tun jiya da daddare da ta fita ta ce zata je wani waje amma shiru har ynx. Dama ynx nake cewa zan je asibitin in gani ko can ta kwana wajen aikin naku."
.
Dakta saminu ya ce da tsohuwar
.
"lallai mu ma bamu ganta ba mama. Wataqila dai wani waje taje, amma bata zo asibitin ba tun barowarta jiya."
.
Delu ta fara tafa hannu cikin taraddadi ta ce.
.
"to ko me yasa Hauwa ta je tayi zamanta haka oho? A ce yarinya tasa kai ta tafi kamar dabba, in kwanan zata yi ai ta ce mama ba zan samu dawowa ba, to ta ce zata je ta dawo ba nisa zata yi ba, gashi har an kwana tun daxu garin allah ya waye, har rana tayi bata ba dalilin ta."
.
Dakta saminu ya ce da mahaifiyar Hauwa
.
"mama ba ni kadai ke son ganinta ba, akwai wasu mutane a waje, ki dan leqo ki fada masu da kanki su ji."
.
Delu ta ce dashi cikin girmamawa.
.
"to mu je ai ba damuwa, in ta dawo sai in fada mata kun zo nemanta bata nan."
.
Ta tashi ta bi Dakta saminu a baya kamar jika da kakarsa, duk kuwa da yake a zahiri ba wasu qididdin shekaru ta bashi na azo a gani ba, banbancinsu kawai shi ne, shi tun haihuwarsa bai sha wahalar komai ba na matsalolin rayuwa, ita kuwa in labari zata bayar in har akwai mai saurin kuka a kusa da ita to dolene ya zubar da hawaye sbd tausayi. Delu taga ta duniya, kamar yadda take fada."
.
Suka fito qofar gidan tare suka samu Jami'an tsaron. delu ta dubi fuskokin mutanen biyar, taga kamar gumakan da 'yan koyo suka sassaqa. Tayi sauri ta rusuna ta ce dasu muryarta na rawa.
.
"sanunku dai."
.
A.c. Tanko ya ce da ita.
.
"sannu mama, tashi tsaye."
.
Ya yi mata wani murmushi da ya nemo shi daqyar akan daskararriyar fuskarshi. To amma ita mama delu da ta dubi fuskar Jami'in tsaron sanda ya yi murmushin nan take ta tuno da yanayin da ta gani a fuskar wani dodo dake cin mutane a wani fim da Hauwa ta ta6a kunna masu, sanda tana da kayan kallo kafin gari ya ga gari ta amshi kudinsu.
.
Dakta saminu ya ce da A.c. Tanko
.
"yalla6ai wannan ita ce mahaifiyar Hauwa. ta ce Hauwa bata kwana a gida ba, tun fitarta jiya da dare har ynx bata dawo ba, shine na ce ta zo ta yi maka bayani da kanta."
.
A.c. Tanko ya kawar da murmushin da yake yi masa qaiqayi a fuskarsa, sbd ba muhallinsa bane. Ya dubi ramammiyar tsohuwar ya ce da ita.
.
"da Hauwa zata fita bata fada maki inda zata je ba?"
.
Delu ta girgiza kai da sauri.
.
"A 'a, wallahi bata ce ga inda zata ba. Ta dai ce wata takarda zata je amsowa wajen aikin gwamnati amm...."
.
A.c. Tanko ya dakatar da tsohuwar da wata tambayar.
.
"da qarfe nawa ta tafi?"
.
Delu ta daga kai ta ce.
.
"to ina jin dai almuru ta dawo, amm sai bayan sallar isha'i ta bar gidan nan."
.
A.c. Ya ce da ita.
.
"ita kadai ce, ko kuwa tare da wani ta fita?"
.
Delu ta ce.
.
"A'a ita kadai ta fita, sai dai ban sani ba ko bayan fitarta ta samu wani sun tafi tare."
.
Jami'in tsaron ya numfasa, da ya ji amsar da tsohuwar take basu, ba inda zata kaisu a binciken da suke yi. Har zai ce ta koma cikin gida, sai kuma ya sake tambayarta a qarshe.
.
"mama su waye manyan qawayenta a wannan unguwar taku?"
.
Delu ta ce dasu cikin fushi.
.
"bata da wasu tsayayyun qawaye a wannan layin. Haka take rayuwarta kamar mujiya, barta dai kullum tana tare da wannan shedanin yaron na can gidan mai barin suma akai kamar arne. Na rabata da yaron nan amm ta liqe masa. Da za a ganshi Wataqila shi in aka tambayeshi ya san inda ta nufa."
.
A.c. Tanko yayi saurin tambayarta.
.
"anne yaro ne mama?"
.
Delu ta ce.
.
"wani yaro ne anan maqwabtanmu, sunansa nura aljani, shedanin yaro ne na innanaha. Duk inda Hauwa take ya sani."
.
Delu ta nuna masu gidan su nura daga inda suke tsaye. Nan take A.c Tanko ya tura daya daga cikin yaransa ya ce ya je ya binciko masa nura idan yana nan ya zo dashi. Dansandan ya tafi cikin sauri, ya tunkari mutanen dake tsaye a nesa suna kallon abin dake faruwa a qofar gidan su Hauwa
.
A.c. Tanko ya mayar da hankalinsa akan bayanin da delu take bashi na alaqar nura aljan da 'yarta Hauwa, ya sake tambayarta.
.
"mama shi nura sana'ar me yake yi? Kuma me ya hada shi da Hauwa?"
.
Delu ta ajiye fushinta ta ce da dansandan.
.
"ita a haukanta sonshi take yi. Ba irin nasihar da bamu yiwa yarinyar nan ba ta canza saurayi amma ta qi. Ba shi da sana'ar komai dan shaye-shaye ne, ance har kudi Hauwa take bashi, idan ta dauki albashi. To ina za a qulla wani abin arziqi da shashashan yaro irin nura? Tsakanina da wannan yaro sai dai allah ya isa ban yafe ba, tunda shi ya hana Hauwa ta za6inmu sahihin miji na gari."
.
Delu ta murtsike hawayen da ya sullo daga idonta, suna nan a tsaye sai ga Dansandan da ya je neman nura ya dawo. Da xuwanshi ya ce da A.c tanko.
.
"sir, na tambaya ance shima nura bai kwana gida ba tun jiya ba a ga dawowarsa ba." wani a cikin wadancan mutanen ya ce ya gansu jiya da dadaddare akan babur sun hau titi nura ya goya hau suna gudu misalin qarfe takwas na dare."
.
Ac Tanko ya nuna gamsuwarshi da duk bayanan da ya samu ya ce da delu.
.
"shi kwnan ki koma cikin gida mama, mun gode. Idan mun ga hau zamu ce mata ta dawo gida kina son ganinta."
.
Delu ta juya ta koma gida tana banbamin fada tana cewa.
.
"indai tana tare da wannan shaidanin yaron ai sai an ganta, tunda shine ubanta, sai sanda ya ga damar dawowa da ita..."
.
Ta shige cikin gidan. A.c Tanko ya dubi Dakta saminu ya ce dashhi.
.
"mun gode likita, ynx abin da muke so a wajen ka shine, ka bamu hoton Hauwa koda (passport) ne....! Muna so zamu yi bincike na musamman akanta."
.
Dakta saminu ya ce da shi.
.
"ba matsala yalla6ai, mu koma ofis za a samu hotonta a cikin fayil."
.
Jami'an tsaron suka shiga motarsu tare da likitan suka juya inda suka fito, baqar motar tana qyalqyali a cikin hasken ranar. Mutanen dake tsaitsaye a kusa da gidan su Hauwa suka yi ta mayar da martani, akan wannan xuwa na bazata da 'yansanda suka yi suna bincike a gidansu. Da yawa basu fadi alheri ba, sbd a zahirin gsky kowa ya san a yadda Hauwa take gudanar da rayuwarta, bata nemi ta gama da duniya lfy ba."
.
.
.
*** ***
.
.
Mutanen dake a yankin hayin na bayi da suka yi sammakon xuwa gona, su suka fara cin karo da gawar nura a yashe a gefen hanya kace-kace cikin jini. Nan da nan suka juya a tsorace suka koma gida, suka shaidawa mai unguwansu malam abashe, abin da suka gani akan hanyarsu.
.
Kafin wani lkc mai unguwa da sauran mutanen qauyen, suka dubguma qwansu da kwarkwata suka biyo mutanen don su ganewa idanunsu gskyr abin da suka fada. Da xuwansu suka samu gawar nura, wadanda suka qware wajen gane hadarin daji, da xuwansu suka ce kare ya kashe wannan mutumi wanda basu san ko daga ina yake ba." dama akwai wani mahaukacin karen fulani dake a yankin, wanda ake ta gargaddin mutane suyi hankali dashi yana fakar mutane da daddare. Mai unguwa abashe da mutanensa suka yanke hukunci lallai wannan karen shi ne wanda ya yi wannan ta'addancin.
.
Basu tsaya 6ata lkc ba, sai suka yanke shawarar xuwa su shaidawa mai garin kuringa, wanda shine yake jagoranttar qauyuka da dama na yankin a ciki har da hayin na bayi. Kafin su je kuringa ne, sai wani tsoho ya zo da sauri wanda shima a nan kusa da hayin na bayi gidansu yake, ya fadawa mai unguwa malam abashe cewar ya je tsaunin tudun kudi zai yi icce yaga wani babur an jefar dashi akan hanya, shi ne ya zo ya fada a yi cigiya.
.
Mai unguwa ya sa aka dauko babur din aka kawo shi gidansa. Ya je kuringa ya samu mai gari malam badamasi ya fada masa abind ake ciki. Sun tsinci gawar wai saurayikare ya kashe shi, kuma sun tsinci babur da sassaf a kusa da tsaunin tudun kudi.
.
Da mai gari malam badamasi ya halin daake ciki bai tsayawata-wata ba, sai ya jagoranci mai unguwa malam abashe suka ofishin 'yans na qaramar huk. Suka iske dpo bashi nan, suka fadiwa sajanin dake kankanta abin da ya kawosu.
.
Sajan murtala ya kirawo dpo a waya ya shaidamasa abin da mutanen qauyen suka zo suka fada. Dpo wanda ya yi dowar tafiya ya ce, ya ce zai shaidawa Eriya kwama halin da ake ci
.
Eriya kwamanda to ya dawoaga wajenbinciken d suka je biti, yana zaune afishinsa a nazarinqaramin hot Hauwa (passport) wanda dakta saminu ya bashi kafin y zartas da wani abu na gaba da zasu yi ne, sai dpo din dake a yankin hayin a bayi da kuringa ya kirashi ya fada masa ain da mutanen qauyen suka zo suka sanar.
.
A.c tanko wanda yake jiran ya ji wani
}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 50
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
.
A.c. Tanko wanda yake jiran ya ji wani qaramin abu ko ya yake ya faru, wanda yayi kama da wani abu da suke nema da ya ji dpo ya ce gawar wani saurayi da babur aka tsinta, sai ya tuno bayanin da suka samu a wajen mahaifiyar Hauwa da mutanen layinsu nura, inda aka ce ya dauki Hauwa a babur, tun jiya da daddare ba a san inda suke ba." ynx kuma ga rahoto ya zo cewar wasu mutanen qauye sun tsinci babu, kuma wani saurayi ya mutu a gefen hanya ba a san ko wane ne ba."
.
Bai tsaya 6ata lkc ba, A.c. Tanko da kanshi ya tura Jami'an tsaro, ya ce suyi bincike mai kyau su zo da gawar saurayin don a ga ko wane ne....! A cikin abin da bai wuce awa daya da rabi ba, jami'm tsaro suka dauki mota suka garzaya qauyen hayin na bayi suka dauko hoton gawar nura, sannan suka dauko shi suka zo dashi...
.
A.c. Tanko da kanshi ya zo inda aka shimfide gawar nura a qasa yayi masa kallo daya ya fahimci shine yaron nan saurayin Hauwa da aka ce an ganshi ya dauketa a babur a daren da ya gabata suna ta sheqa gudu a titi ba a san inda zasu je ba."
.
Don kada a samu matsala, sai Jami'an tsaron suka wanke hoton gawar nura cikin sauri suka je layin su, suka nuna hotonsa, mutane da yawa suka tabbatar shine nura aljan saurayin Hauwa.
.
Sun dawo da wannan bayanin kenan, A.c Tanko ya tara Jami'an tsaronsa baki daya yayi masu bayanin wani sabon aikin gaggawa da ya taso. Ya ce dasu.
.
"duk inda muke tsammanin wannan kes din ba a nan yake ba." daga jiya xuwa yau, har kawo ynx mun duqufa ne wajen neman 6arayin da suka sace Nalamma. to amma wani abu ynx ya faru, wanda zai sa dolene mu karkata akalar bincikenmu wajen neman Hauwa."
.
A.c. Tanko ya sa hannu a cikin aljihun rigarsa ya dubi fuskokin Jami'an tsaron dake tsaye suna saurarenshi cikin girmamawa, kansu a duqe. Ya ci gaba da cewa.
.
"na san baku san ko wace ce wannan hauwar ba da nake fada maku ita ya kamata mu nemo. Hauwa ita ce qaramar likitar dake kan aiki lkcn da yaranmu suka kai Nalamma asibiti. Akwai yiwuwar (police) din da muka tura suyi tsaro a asibitin sun yi sakaci wannan likitar tayi magana da Tsohon nan Nalamma. sbd in har bata san wani abu a game da dukiyar da Tsohon ya 6oye ba." me zai sa ita da saurayinta su hau babur a cikin dare suje daji su biyu? Kuma a binciken da akayi ynx, an tsinci digar haqa rami a cikin ciyawa kusa da gawar nura. wannan ya nuna mana kai tsaye hau da nura sun je daji ne zasu gino dukiyar da Tsohon ya 6oye, wacce mu kuma muke nema ruwa a jallo, shekara da shekaru."
.
A.c. Tanko ya qara kausasa muryarsa ya ce.
.
"Hauwa ta samu cikakken bayanin inda Nalamma ya 6oye dukiyar nan da ya sata. Bamusan inda take ba a halin ynxn, amma ina da tabbacin koma a ina take bata yi nisa ba." ya zama dolene mu fadada bincike a lardin nan da muka tsinci gawar nura...na tabbatar a wannan dajin Nalamma ya 6oye dukiyar nan tuntuni. Bamu san me yasa nura ya mutu ba, bincike ya nuna karen ya kashe shi. Tambayar a nan ita ce. ina ita Hauwa take a lkcn da karen ya kashe nura a dajin? Me yasa kuma inda aka tsinci gawar nura daban inda aka tsinci babur dinsa daban? Duk amsoshin wadannan tambayoyin, zamu same su ne kawai idan muka yi sa'ar gano inda Hauwa take. Bana tsammanin 6arayin da suka sace Nalamma sun yi nasara, koda sun tursasa Tsohon ya fada masu inda ya 6oye dukiyar, Wataqila Hauwa ta rigasu xuwa, don haka a ynx nafi son a duqufa a nemo mani Hauwa duk inda take, ita nafi so in gani fiye da wadann 6arayin, sbd su ynx suke qoqarin su tursasa Nalamma ya fada masu inda dukiyar take, amma ita Hauwa tuni ta sani, Nalamma ya fada mata. Hauwa nake so ku nemo mani. Ga hotonta mun samu, zamu sa a buga a jaridu, a nunata a gidajen tibi, duk wanda ya ganta ya yi gaggawar sanarwa Jami'an tsaro zamu sa lada mai tsoka ga duk wanda ya gano mana Hauwa, koda kuwa a cikin ku ne yaranmu."
.
Jami'an tsaron suka hada baki suka ce. Zasu gano ta...." A. Tanko ya yi murmushi kadan sannan ya ci gaba da cewa.
.
"zamu rarrabaku qungiya-qungiya. Zaku warwatsu a cikin qauyukan dake a yankin da muka tsinci gawar nura. Zan bada umarni ynxn nan Jami'an tsaron da suke aikin bincike da jirage su sauko haka nan, su rabu da wadann 6arayin da suka sace Nalamma bamu buqatarsu. Kowa ya shirya ku zo ku taffi wannan dajin ku binciko mana Hauwa, da kuma inda Nalamma ya 6oye dukiyar, duk suna nan a wannan dajin."
.
Jami'an tsaron suka sarawa A.c. Tanko dan asabe, sannan suka juya suka fara hada-hada helkwatarsu. Suna shirin tafiya dajin. Kafin minti goma tuni har an tayar da motocin sun shiga sun fara tafiya. Motocin 'yansanda goma cike fal. Suka doshi dajin tudun kudi. Sun tafi ba da jimawa ba A.c Tanko ya kira kwamishinan 'yansanda ya ce dashi...?wannan
.
"muna samun nasara sosai a bincikenmu. Akwai wata likita da muke zargin ta san inda Tsohon nan ya 6oye dukiyar, mun gano gawar saurayinta a dajin da muke tsammanin Tsohon ya kai dukiyar ya 6oye. Amma ita yarinyar bamu ganta ba, mun tura yara suyi binciken ko'ina a qauyukan dake zagaye da dajin su nemo mana ita."
.
Kwamishinan 'yansanda ba zumudi a muryarsa ya ce.
.
"kuna yi qoqari Tanko. ku tabbatar kun nemo ta a duk inda take. Ya sunan ta?"
.
A.c Tanko ya ce.
.
"sunanta Hauwa, qaramar likita ce a (karama hospital)."
.
Kwamishinan ya ce.
.
"ina son Hauwa ta zo hannunmu nan da awa biyu."
.
.
.
*** *** ***
.
.
.
Rabi bata kai yamma a kasuwar ba, bayan rabi tayi 'yan saye-sayen da zata yi, da kudinta suka qare sai ta yi haramar komawa qauyensu, ba haka ta so ba. Ta so ne ta sayi abubuwa da yawa, to amma ya zata yi da Mu'azzam mai shago tunda ya cuceta ya riqe mata kudi? Dole sai dai ta bari ta dawo gobe ta sa shi a gaba ta sake fusgar ko dubu daya ne ta sayi ragowar abubuwan da take so a kasuwar.
.
Rabi 'yar fulani ta je qaramar tashar 'yan aca6a dake kan hanruyensu, da yake ta saba da duk wani dan aca6a dake zirga-zirga daga cikin garinsu xuwa qauyensu, da xuwanta suka fara kiranta kowa yana qoqarin ya jawota ta zo ta hau nashi.
.
Rabi tayi murmushin jinjinawa dadi, ta sauke qwaryarta ta riqe da hannuwanta biyu tana kallon baburab dake a wajen, ta san tana da kwarjini ba kowacce 'yar fulani a tsararrakinta mutane suke yiwa irin wannan tarairayar ba." wani lkcn ma kyauta 'yan aca6a suke kaita, ba don komai ba kawai sbd tsabar kyanfuskarta da xubin mulmulallen jikinta dake sheqi kamar kwalba.
.
Rabi ta dubi wani gajeren qato dake

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment