Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shiga daya daga cikin dakunan barci biyun ne yaga hoton wani miji da matarshi a jikin bango. Mijin ya matse wuya da nakatayil, matar Kuma ta dafa shi tana dariya sanye da jaket ruwan qasa. Baqaqe ne, ko a cikin hoton basu haska ba,ya amma da ganin yanayinsu a hoton masu ra'ayin zamani ne da wayewar kai. Shago ya murtuke fuska da ya sake kallon hoton, tun ba ynx ba ya tsani duk wani mutum da zai fito ya riqa nunawa jama'a shi dan boko ne....! Baya son yaga wani abu mai kama da karatun zamani a kusa dashi, yafi so kome za'ayi a yi shi a yadda rayuwarshi take, tunda dai shi ko sunansa baya iya rubutawa.

.
Sai da ya qara shiga wani dakin ne ya tarar da kayan abinci da Kuma wani qaramin ma'adanar girki, wanda yake amfani da wutar lantarki. Shago ya bude ya iske soyayyar kaza a ciki, da kuma dafaffiyar shinkafa tana naso da mai, qamshi ya fara tasowa tun kafin ya ciro wadannan kayan qwalama da aka adana. Sai da ya ga abincin ya tuna da azabbiyar yunwanr da shi kanshi yake ji. Ya ciro dafaffiyar shinkafar cike fal a wani qaton mazubin abinci, sun barta a bude don kada zafi ya 6ata ta kafin su dawo.
.
Ya janyo soyayyar kazar, ya dorata akan shinkafar kafin ya fito daga dakin ne, ya duba inda aka jera farantan cinye abinci da cokula, ya dauko guda uku, ya hado da robobin ruwa dogaye da ya same su a cikin wani firji.
.
Ya tattaro kayayyakin ya fito, ya dawo falon, ya sami sadi yayi rashe-rashe a gaban Tsohon yana cewa dashi cikin sanyin murya.
.
"mu kanmu muna da iyaye da kakanni, suna nan a raye, kuma muna darajasu. Sbd idan ka daraja Tsohon wani, kaima kana gani za'ayi daraja naka, amma idan ka wulaqanta Tsohon wani, to kaima fada kana gani za a wulaqanta naka. Shi yasa muke baka girmanka baba, duk wanda yake ganin mutuncin tsofaffi wlh ba zai ta6e ba."
.
Shago ya ajiye kayayyakin da ya debo a gaban sadi, tare da fitilar, wacce ya dan matsa da ita gefe guda, sadi ya kalli abin da Shago ya samo a cikin gidan ya ce.
.
"lallai masu gidan nan sun iya yiwa baqi tanadi, wannan ragaja haka...."
.
.
Lp=28}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 28
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"lallai masu gidan nan sun iya yiwa baqi tanadi, wannan ragaja haka? Shago zuba mana abinci, yunwa nake ji. Ka zubawa baba da yawa, ka gyara kazar ka za6o masa wajen tsoka sosai, kada ka hada masa da qashi, wajen taushi zaka za6owa baba."
.
Shago ya dan yi qunquni a ciki, sbd baya son yadda sadi yake wahalar tarairayar wannan tsoho, yafi so in za'a, yi aiki kawai a tsaya a yi shi, tunda wuri kafin lkc ya qure. Ya xuba abincin a farantai uku, ya 6are kazar ya rarrabata ya bi umarnin oga sadi, ya za6owa Tsohon wajen taushi, ya dora masa akan abincin sa ya miqa masu. Shi kuma ya dauki nasa ya koma kan kujera ya zauna ya fara ci.
.
Sadi ya dauki abincin Nalamma ya miqa masa, ya dauki robar ruwan ya bude masa ya bashi. Nalamma ya dauki ruwan ya fara kwankwada kamar ya shekara bai ga ruwa ba." sadi ya dauki nasa abincin shima ya koma kan kujera da ya fahimci Tsohon ba zai tsaya ya saki jiki ya ci abincin sosai ba, idan yana kusa dashi.
.
Su dukansu suka saki jikinsu, suka yi baza-baza da gara kamar sun samu gidansu.
.
Basu san wannan gidan ko na su wane ne ba." kuma basu damu dasu sani ba." a yadda suke ji da kansu suna jin koda gidan kanal din soja ne, ko bataliyar mayaqa ya debo masu, suna da tabbcin zasu fita da ransu, sai dai a sha wahala. to me kuwa zai tayar da hankalin sadi qare-garke tare da yaronsa shagon sadi?
.
.
.
*** *** **
.
.
Babi na takwas
.
Dawan malam wani qaramin qauye ne wanda yake kusa da makeken kogin, fiye da Sauran qauyukan dake a lardin. Duk kusan fadamun dake a zagaye da kogin na mazauna Dawan malam ne, wanda ko ba a fada ba, da ganin irin gine-ginen dake a qauyen, da kuma yawan motocin dake karakaina, manya da qanana za a fahimci suna samun rufin asiri a sakamakon wannan kogin mai tarin albarka.
.
Duk wani mutum dake kwana yana tashi a Dawan mallam ya san da zaman wani mutum mai Suna baqin bature. asalinsa ba a qauyen yake ba." ya dai zo ne ya sayi wata fadama ya gina qayataccen gidan hutawa, wanda yake fuskantar kogin, sannan Kuma a zagaye da gidan bbishiyoyi ne na 'ya'yan itatuwa, irin su lemu da mangoro, da kashu, da kuma qananun filawoyi masu ban sha'awa.
.
Ba wanda ya san daga inda wannan mutum ya fito, don kuwa a hali irin nasa mutanen qauyen basu isheshi magana ba." har yaxo ya sayi fadamar, ya gina gidan hutawar basu san ko sunan shi ba,ya shi ya sa suke kiransa da Baqin bature.
.
To amma inda mutumin ya wanke kanshi basu fiye zaginshi ba shi ne, tun tarewarsa a gidan shekaru biyu da suka wuce, tare yake da wata matarsa itama 'yar boko,' wacce ke da hali irin nasa, wacce it kuma suke kiranta da 'Baqar baturiya'.
.
Wadannan mutanen biyu miji da mata, basu son wata rayuwa irin ta baqaqen fata, duk da yake kuwa su biyun baqaqe ne kamar zunubai. Basu son hulda da mutane kwata-kwata. Basu kowa ya matso kusa da su." jita-jita na yaduwa a qauyen cewar asalinsu 'yan jihar kogi ne, suka baro 'yan uwansu, suka zo wannan qauyen a cikin daji suka gina gida, suke zaune su kadai a ciki, don kada kowa ya damesu.
.
Baqin bature Tsohon ma'aikacin bankine, wanda ya riqe bahauwan muqami kuma ya tara kudi na azo a gani. Amma kuma har ya kai tsawon shekara arba'in da biyu bai ta6a yin aure ba." abin da yafi so fiye da komai a duniya shi ne, ya dauki jarida ya karanta, 'yar qaramar kyanwarsa ta riqa kaiwa da komowa a kusa dashi, tana hawa jikinsa.
.
Abin da yafi tsana kuwa bai wuce yara qanana ba." baya son hayaniyar yara, wanda wannan shine sa6anin farko da ya fara shiga tsakaninsa da matar yayansa a shekaru ashirin da suka wuce, sanda yana saurayi kafin ya fara aiki a gidan yayansa yake zaune, amma kuma qananun 'ya'yan yayansa basu da ikon suyi ko tari idan yana karatu, sai ya taso masu ya hau su da bugu, yana takaicin yadda har yayansa yayi sakaci ya bar matarsa ta tara masa wadannan yaran, har guda hudu, a cewarsa sai ka ce 6eraye!"
.
Sai da baqin bature ya sami aiki, da ya bar gidan yayan nasa sannan kowa ya sami kwanciyar hankali. Duk da haka maqwabtansa sun sha faman rigima dashi, don kuwa babu damar su dora girki hayaqi ya tashi sama ya riqa shigo masa gida, da yaga haka zai fita yana zage-zage yana rufe hancinsa don kada ya shaqi cuta.
.
To sai dai ta wani 6angaren maqwabtansa na can garinsu da ya baro sun dan ji dadin zama dashi, sbd shi yake bayar da kudi akai-akai, ake bin duk wata kwata da ta cika ana kwashe a layin, sbd baya son je wucewa ya ga kwata koda kuwa a mota yake.
.
Baqin bature ba a yi masa gwaninta, don kuwa ra'ayinsa ya sha banban da na kowa. Lkcn da yake a garinsu ya ta6a ajiye motarsa a waje, wasu mataa dake a layin, wadanda basu da aikin yi suka debo ruwa, suka sa qyalle mai taushi suka wanke masa motarsa ta fito fes,,don idan ya fito ya dan yaga masu wani abu ko na abinci ne su samu. Da baqin bature ya fito yaga suna goge motar, sai ya dora hannu akai ya fara kwaratsi, yana cewa, sun yi masa 6arna. A ranar yasa motar a kasuwa, wai sun goge masa fentin motar ta tsufa, ba qaramin asara baqin bature yayi ba da ya syar da motar, ya cika ya sayi wata irinta.
.
Duk shekarun da baqin bature yayi yana gudanar da wannan rayuwa tasa, bai ga matar da zai aura ba,ya wacce rayuwarsu ta zo iri daya. Sai a shekaru biyu da suka wuce, da yaje cin abinci a wani katafaren wajen shaqatawa ya hadu da wannan matar tasa, wacce suke tare a halin ynxn.
.
Hirar da suka yi bata fi ta awa daya ba,ya baqin bature ya fahimci irin ra'ayinsa daya da matar. Ita ma ba yarinya bace, ta kai shekaru kusan arba'in, amma a cewarta bata ta6a yin aure ba." da ya tambayeta ko me yasa haka a wancan lkcn, sai ta ce dashi, bata samu wa dace da ita bane. Sbd ita gsky duka wanda zai aureta, sai sun yi yarjejeniya ba zata haihu ba,ya magani zata riqa sha duk wata, don kuwa ba zata iya jura dawainiyar yara suna damunta da surutu ba."
.
Sannan kuma idan ta auri mutum ba zai yi mata kishiya ba har abada.... Ta ce dasi kuma duk wanda zai aureta , sai dai ya nemi wani waje mai sanyi da ruwa ya gina mata gida a can, inda babu hayaniyar mutane. Sharadi na gaba kuma shine bata yarda idan mutum ya aureta 'yan uwansa su riqa xuwa gidansa ba,, sai dai 'yan uwanta kawai. Hujjarta kuwa ita a cewarta wai duk duk dangin miji munafukai ne, sannan kuma a cewarta ba zai yiwu ba mijinta ya riqa kwasar dukiya yana rrabawa 'yan uwansa da iyayensa ba,ya tsoron da take ji shi ne idan ya mutu da me zata dogara, idan bai bar mata komai ba?"
.
Da baqin bature ya ji wannan ra'ayi na wannan baqar mata, sai ya fara murna don kuwa ya tabbatar ya samu matar da zai aura. Sun yi wannan hirar da wata uku aka daura aurensu, kuma kaffa-kaffa a yi haka ne baqin bature a binciken da yayi na gaggawa ya gano wannan kogin dake a qauyen Dawan malam, ya zo ya gina masu gidan, wanda ke da dakunan barci biyu da falo, sai kuma dakin cin abinci da dakin karatu, a qarshe sai dakin kare da dakin jannareto.
.
Basu tsara gidan da dakin baqi ba,ya sbd basu da buqatar baqo a rayuwarsu. Baqin bature ya guji danginsa da kuma , wadanda baya aimaka masu, ya dauki matarsa suka yiwo nisan kiwotun daga jr kogi, suka zo wannan qauye dake a lardinan birnin zariya. Inda babu wani dan uaji labarin sa. Balle ya zoa a wajensa.
.
Kudin da ya tara na aikinsa kafin ritaya, su ya tasa a gaba suke ta ragargaza shi da matarsa, wani lkcn ya kan dauketa a mota su tafi yawon shaqatawa, sbd zaman gidan ya kan ishesu, idan kuma suna a gida, basu da wani aiki sai kallon tauraron dan adam a tashoshin dake a duniya.
.
A wannan daren, sun fita xuwa cikin gari a motarsu, sun sayo kayan abinci, suna cikin tafiya ne sai motarsu ta lalace. Baqin bature baya so yayi duk wani abu mai wahala a rayuwarsa. Duka-duka wata waya ce ta tsinke wacce ke hada wuta, amma da ya fito shi da matarsa suka duba sai yayi tsaki ya ce.
.
"matsalar afirka kenan, ynx da ace a qasashen turawa ne irin haka ya samu mutum, da motarsa waya kawai zai yi (agency) su turo masu gyara.
.
.
Lp=29}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 29
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
....
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"matsalar afirka kenan, ynx da a qasashen turawa ne irin haka ta samu mutum, da motarsa waya kawai zai yi (agency) su turo masu gyara. amma mu nan masu gyaran ma sai ka bisu da motarka, ko Kuma ka je da kanka ka kirasu. Ya za'ayi mutane suyi (surviving) a haka ana irin wannan matsalar? ba dole ne ma a riqa mutuwa da wuri ba a afirka?"
.
Matar dake a baya-baya tana kallon injin motar da tarkacen wayoyin dake ciki, sanda mijin nata ya bude ya haska da fitilar wayarsa, sai tayi gaggawar ciro hankici ta rufe hancinta, sbd kada ta shaqi warin mai da Kuma tiririn da taga yana tasowa daga cikin injin. Ta ce dashi da sauri.
.
"ka rufe injin mana ka jira sai ya huce. Baka ganin tiriri yana tasowa? Irin wannan yana kawo cutar (cancer), ka dawo baya sai injin ya sarara."
.
Baqin bature yayi tsaki, shi kanshi ya san haka, sai dai kuma a halin ynx dole ne ya duba wayar da ta katse ya hada da kanshi, indai ba so yake yi su tafi a qasa su bar motar tasu a dajin ba."
.
Bayan ya gama duk qorafin da zai yi, da Kuma tsirfarsa da fushi, a qarshe sai ya nemi wayar da ta katse ya hadata, ya rufe murfin injin motar, ya shiga ya tayar da ita ta tashi, matar wacce duk abin da mijinta yake yi tana tsaye gefe guda tana duba agogo cikin damuwa. Ita ma ta bude motar ta shiga ta zauna kusa dashi.
.
Ba wani abu take dubawa agogo ba, daxun da yamma kafin su fito ta shirya lafiyayyen abinci da kaza ta ajiye sai sun dawo daga shaqatawa zasu ci ita da mijinta. Gashi lkcn cin abincin su har yayi, saura minti hudu, kuma a qa'idarsu indai har lkcn cin abincin ya zo ya wuce koda da minti daya ne, sai dai su xubar dashi, lkcn sa ya wuce, sai dai suyi haquri da yunwa su jira na gaba.
.
Tun da qarfe bakwai na dare ta gama abincin, to amma a qa'idarsu sai qarfe sha daya da minti ashirin da biyar dai-dai. A kowacce rana da qarfe takwas suke fita bakinn kogi yin fatsa. Idan suka je sai su ajiye motarsu a gefe guda, su sa qananun kaya, su zauna a bakinn kogin, kowa ya jefa fatsa cikin ruwa, suna jiran kifaye su kama fatsar, a lkc guda kuma Suna tattaunawa kan matsalar qasashen baqar fata, da ci gaban da turawa suka samu a duniya.
.
Baqin bature ya tuqa motar ya doshi hadadden gidansu dake maqwabtaka da kogin Dawan malam. Da suka isa gidan ne kamar kullum sai fitulun motar suka haske ko'ina a harabar gidan, da kuma farfajiyar qofar da suke shiga da motarsu. Da farko basu lura da kwadon dake a kakkarye ba, wanda aka bugeshi da tsiya ya 6alle. Sai da baqin bature ya tsayar da motar a kusa da qofar ya fito zai bude gidan, sannan ya ga yadda kwadon ya waskace ya koma gefe guda.
.
Ya tsaya turus! Cikin kaduwa, matarsa da taga haka, sai ta bude motar ta fito cikin sauri ta tambayeshi.
.
"ya akayi ne naga ka tsaya baka bude qofar ba?"
.
Baqin bature ya ce da ita.
.
"ina ga an yi mana 6arna a gidan nan. An 6alle mana kwado an shiga an yi mana sata, mu shiga mu gani, me suka daukar mana?"
.
Ya tura qaramar qofar, wacce take a bude, ya shiga gaba matar tasa ta biyoshi a cikin sauri tana cewa.
.
"ynx haka tsagerun matasan dake a qauyen nan ne, ya kamata muyi (report) dinsu a (poliice station) zasu tona koma su wanene suka shigo mana gida da bamu nan."
.
Tana cikin qorafin ne kuma sai suka ga akwai haske a falon nasu, sun dauka fitilar tasu aka kunna, aka haska aka yi masu satar da za'ayi, bayan an gama Kuma aka barta ba a kasheta ba." basu dauka sun yi baqi suna nan suna jiransu ba a falon. Don haka sai suka shiga falon kai tsaye duk su biyun, ba wani xullumi.
.
Da shigarsu suka yi karo da mutanen dake a falon nasu. A hakimce su. Sai wani dan tsoho dake a maqure a bangon, kamar a hureshi ya tashi sama. Sai Kuma qarti biyun dake a zaune daya qato ne ainun, dayan kuma matsakaici. Bahauwan yana kishingide da tsinken sakace a bakinsa, yana sakacce, sbd naman kazar da yaci duk ya maqale masa a haqori.
.
Shi kuma wanda bai kai bahauwan ba yana a kishingide kan daya daga cikin luntsima-luntsiman kujerun falon. Ganin mutanen basu tsorata da ganin shigowarsu ba,ya ya san baqaqen turawan suka fusata.
.
Baqin bature ya rasa me ma zai ce da wadannan baqi wadanda suka 6alle masu gida suka shigo babu izini, ga kuma abinci nan sun dauko sun ci sun barshi baza-baza a farantai, ko kawar da ragowar basu yi ba." matar wacce tafi mijin nata rashin haquri ta dakawa baqin tsawa cikin fushi
.
"su waye ku da zaku shigo mana gida babu izini, ba mu san da xuwanku ba?"
.
Tun kafin ta kai qarshe, ba ta san lkcn da sadi qare-garke ya zo ya sameta a inda suke tsaye ita da mijin ta, da xuwansa ya cire hannunsa dake kama da itace, ya tsinke ta da mari fas! Har sai da falon ya amsa kuwwa. Mijin nata ya bude baki yana kallon abin al'ajabi kamar a cikin mafarki. Su da gidansu amma daga matarsa tayi magana, wani qato ya zo ya kama marinta. Matar ta dafe kuncinta da hannu biyu, sannan ta fara tsandara kuka, don kuwa ji take yi kamar an kware mata fatar fuska.
.
Wanda ya yi marin yayi murmushi ya ce da ita.
.
"ki iya bakinki a lkc na gaba, bana son tsageranci da raini, kuma ina so in sanar da ke, daga ynx ni ne maigidan ki, duk abin da nake so ynx shi za'ayi a gidan nan, ina fatan dai kin fahimci ko mu su wane ne?"
.
Baqar baturiya ta kalli mijinta wanda ya kasa ta6uka komai,, yana tsaye kawai yana kallon wadannan miyagun baqi. Shirun da mijinta yayi shi ya fi komai 6ata mata rai, ta daga murya ta ce dashi tana kukan.
.
"ya ya kana kallon abin da dake faruwa zaka tsaya kana kallonsu, ba zaka yi wani abu ba?" su waye su wadannan mutanen da zasu shigo mana gida haka nan ka tsaya kana kallonsu?"
.
.
Lp=30}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 30
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"yaya kana kallon abin dake faruwa zaka tsaya kana kallon su, ba zaka yi wani abu ba?" su waye wadannan mutanen da zasu shigo mana gida haka nan kana kallon su?"
.
Mutumin ya ci gaba da tsayuwa ko motsawa baya son yi, don kuwa ita marinta kawai suka yi, bata ga abin da ya gani ba, shi yasa har take yi masa wannan banbamin, tsayuwar da yayi waje guda kallo-kallo suke yi shi da Shago, wanda yake zaune dafa'an akan kujera riqe da wata guntuwar bindiga 'yar madaidaiciya, kamar cinyar kaza. Baqin bature ya tabbatar idan yayi wani yunqurin a shirye wadannan mutanen dasu harbesu, su jefasu a cikin wannan makeken kogin. Idanunsu kawai ya kalla ya tabbatar da hakan.
.
Da yaga matar tasa zata qara hayayyaqewa, sai yayi gyaran murya, ya ce da ita cikin sanyin jiki.
.
"ki yi shiru bebi, kada ki sake magana, ki rabu dasu su yi abin da suke so."
.
Matar ta dan lafa, ta saurara ita ma, ganin yadda mijinta yayi saranda, ta san idan ma bata saraya ba, zasu ci gaba da marinta ne, har sai ta dawo ta bi ita ma. Don haka tun kafin sadi qare-garke mai hannu kamar itace ya sake samun gurbi a kumatunta, sai ta rufawa kanta asiri ta tsaya a kusa da mijinta, suka bushe suna kallon mutanen, Suna jiran abin da zai faru.
.
Sadi qare-garke ya ce dasu.
.
"tunda naga kun gane ko mu su wane' Kuma kun yi biyayya, bari mu zo kan abin da ya kawo mu gidanku. Da farko ina so in tabbatar maku cewa, in har kuka bamu hadin kai, kuka zauna tare damu lfy, to ba zamu cutar da ku ba." amma idan kuka bijire mana, ko kuma kuka yi yunqurin tona mana asiri, to ina tabbatar maku lkcn mutuwarku ya yi."
.
Mijin da matar tasa suka Jami'an numfashi a tsorace, da suka ji batun mutuwa. Duk duniya babu kalmar da basu so su ji irin mutuwa. Suna jin dadin rayuwarsu, suna holewa, ga kudi, ga gidan shaqatawa, basu da da ko daya. Su dukansu basu kawo mutuwa a kusa. Kuma basu so su ji an yi masu zancenta. Don haka suka sake yin saranda, suka yi shiru suna sauraren sadi qare-garke wanda ya ci gaba da cewa.
.
"bamu san ko kwana nawa zamu yi a nan ba,ya wataqila gobe mu tafi, wataqila kuma mu zauna har xuwa nan da shekara daya. Ya danganta da aikin da zamu yi, mu kanmu bamu san ranar da zamu gamashi ba." to amma koma dai yaushe zamu kai ya zame maku dole ku zauna tare da mu, ko kuna so, ko baku so."
.
Ya dubesu cikin hade fuska, don su dauki wannan umarnin da yake basu. Mijin wanda a bayyane yafi rudewa da ganin mutanen, yayi qarfin halin cewa da sadi.
.
"mun yarda ku zauna ko nan da yaushe ne, kuma mun yi alqawarin ba zamu fadiwa kowa ba."
.
Sadi qare-garke ya yi murmushin jin dadi da yaga mai gidan ya tsorata a dan lkc qanqani, ya matsa gaba kadan ya dafa shi, ya ce dashi..
.
"na ji dadi da naga ka zama wayayyen mutum mai ganewa. Ina fatan zaka ba matarka shawara itama ta zama wayayya kamar ka. Sbd ni a ganina mutumin da ba zai so harsashi ya ratsa jikinsa ba, shi ne wayayye mai gane al'amura a wannan zamanin."
.
Sadi ya koma baya ya dubi yaronsa Shago dake zaune ya ce dashi.
.
"zo ka fafi masu dokokin zama da mu, na gaji da magana barci nake ji."
.
Shago ya taso yana takawa da qarfi, sadi ya koma ya zauna akan kujera yana kallonsu. Sai da Shago ya kusa ture mijin da matar tasa, wadanda suka bi shi da kallo cikin karaya, sannan ya ce dasu cikin tsawa da fada.
.
"duka ta farko ita ce, daga ynx mune masu gida. Mu zamu riqa kwana akan gado, ku kuma zaku koma bandakine ku kulle kanku, a ciki zaku zauna. Doka ta biyu kuma ita ce, ku zaku riqa bamu abinci, duk inda zaku samo mana abin da muke buqata dolene ku je ku samo ku bamu. Kada kuyi zaton zaku gudu, koda yaushe zamu riqe daya mu tura daya inda muke so ya je, idan wanda muka aika ya kuskura ya fadiwa 'yansanda muna nan, zamu kashe wanda muka tsare a nan, kuma zamu gudu a qarshe ba tare da 'yansanda sun kama mu ba, domin kuwa mun dade muna artabu dasu, basu ta6a yin nasara akanmu ba."
.
Sadi wanda yake zaune a baya yana sauraren bayanin yaronsa Shago. Yayi dariyar farin ciki, don kuwa yana son kirari fiye da komai a rayuwarsa. Da a yi masa kyautar kudi komai yawansu ya gwammace a yi masa kirari a ce dashi ya gagari 'yansanda, kuma yafi qarfin doka.
.
Sadi ya ce dasu a qarshe.
.
"kuna iya xuwa makwancinku tun ynx.....kada ku mance bandakin wanka zaku shhiga, ynx nan ne makwancinku."
.
Baqin bature ya kama hannun matarsa bebi cikin sauri ya ce da ita.
.
"zo mu je can din, ki ji abin da suka ce ai."
.
Matar ta bishi babu gardama, Shago da sadi suka bi su da kallo, har xuwa lkcn da suka je kusurwar falon, suka bude qofar bandakin su na wanka. Matar ta dan so tsayawa baya, sbd a qa'ida bata iya wuce minti goma a bandakin su na wanka, duk kuwa da cewa sun qawata shi a tsaftace yake. Gashi ynx waigo nan ne makwancinta, tana gani wasu qarti sun zo zasu haye masu lafiyayyen gadonsu. Wannan ba qaramin wulaqanci bane da zalunci. Mijinnata ya ja ta da sauri suka shige bandakin suka turo qofar ta kulle. Ya qosa su 6oye su daina kallon-kallo shi da wadannan muggan mutane, wadanda da jin yadda suke magana zaka fahimci basu dauki rayuwar mutum a bakin komai ba."
.
Duk abin dake faruwa Nalamma yana a zaune ya jingina da bangon falon, yana kallon su bai cewa kowa komai ba,ya sannan kuma duk da barazanar da yaga su sadi sun yiwa wadannan masu gida, shi babu alamar razana a fuskarshi.
.
Bayan mijin da matar sun gama yiwa kansu qiyamullaini sun 6oye kansu a cikin bandakin sai sadi ya matso kusa da Nalamma ya durqusa kusa dashi ya ce.
.
"to baba mun dawo kana. Lkcn da zamu fara aiki yayi. Kamar yadda ka sani ne, ba sai na sake tuna maka ba." muna

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment