Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miqa, sannan ya mayar da hankalinsa akan makeken kogin, wanda yake daukar idanu a cikin hasken ruwan inda wasu dogayen bishiyoyi suka yi masa katanga.
.
Shago ya dubi mutanen biyu da suke a kwance. Bai san wa yafi jinjinawa jiki ba a tsakanin mai ankwa wanda baya ko iya magana, da kuma Nalamma wanda ko idanu baya iya budewa. Shago ya mayar da hankalinsa akan sadi, ya tashi ya isa inda yake tsaye, suka hadu dashi suka ci gaba da kallon makeken ruwan tare.
.
"ya kamata mu zagaya mu gani, ko zamu samu kwale-kwalen da zamu haura, Akwai masunta da suke amfani da kwale-kwale a wannan kogin da rana. Mu duba ko zamu samu wanda zamu yi amfani dashi."
.
Shago ya amsa cikin kadai.
.
"to mu je mu duba oga, amma baka jin ya dace daya a cikinmu ya tsaya a wajwnsu, daya Kuma ya je ya duba kwale-kwalen? kada mu tafi mu barsu a halin da suke Babu kowa, wani abu ya faru."
.
A karo na farko sadi ya dauki shawarar yaron nasa, ya ce dashi...?wannan
.
"kai ka tsaya a wajen, ni bari in je in duba in gani."
.
Sadi ya tafi cikin sauri, ba tare da ya tsaya sake jin ra'ayin Shago ba." a rayuwarsa bai yadda ya dauki shawarar yaransa ba,ya koda kuwa abin da suka fada gsky ne....! Wannan ya Shago hada shi rigima da Tsohon yaronshhi talle, ba ya son yana amfani da tunanin yara, to amma dake ynx shi kanshi ya san Shago ya zo da tunani mai kyau, dole ya amince, amma Kuma wannan ba zai hanashi fushi ba,ya domin Shago ya fahimci baya son a bashi shawara. Don ya kiyaye a lkc na gaba.
.
Sadi ya bi ta cikin ciyayin ysna bin bakin rafin yana dubawa, da fatan samun kwale-kwalen da masunta suke ajiyewa a kogin, wadanda ake amfani dasu a wajen. Shago ya zauna a qasa bai damu da kimar ra6ar da ke kan ciyayin ba,ya don kuwa ya sha wahala ba 'yar qarma ba." ya tasa mutanen biyu dake a kwance magashiyan yana kallonsu. A zahiri mai ankwa shi ne zai fi zame musu matsala, fiye da wannan tsoho. Don kuwa daga ynx har xuwa wani lkc, idan ba asibiti suka kaishi aka cire masa harsashin ba,ya zai ci gaba da zama a haka, har qafarshi Ta lalace.
.
Shago yana nan a zaune, yana tunani, yana jiran sadi ya dawo. Sai yaga Tsohon ya yi motsi sauri biyu, sannan yayi atishawa, alamar ya farfado kenan daga doguwar sumar da yayi. Shago yayi saurin matsawa kusa da tsohon, ya kai hannu zai ta6a shi, sai yaga ya bude idanunsa.
.
Shago ya tsaya Suna kallon-kakklo shi da Nalamma. Akwai wani yanayi mai ban tsoro dake tattare da idanun Tsohon, zuru-zuru busassu, wadanda suke motsawa kamar an ajiye qasusuwa a cikin faranti. Tsohon ya bude bakinn daqyar yana kyarma ya ce da Shago.
.
"wane ne kai?"
.
Shago ya ce dashi cikin farin ciki.
.
"mu 'yan uwanka ne baba, tun daxun muke tare da kai, muna jira ka farfado. Yaya jikin haka?"
.
Nalamma ya sake kausasa murya ce da Shago.
.
"kai yaro ni bani da wasu Sauran 'yan uwa da suka rage a duniyar nan, qarya kake yi, kai ba dan uwana bane."
.
Shago ya sake kwantar da murya ycikin ladabi ya ce da Nalamma.
.
"tuntuni muke so mu fito da kai daga gidan yari da iyayenmu suka bamu labarinka, shi ne da muka ji labarin irin zaluncin da akayi maka muka yi alwashin sai mun qwatoka. Gashi yau mun cimma burinmu baba, mu 'yan uwanka ne na mini."
.
Nalamma ya dan yi murmushi kadan.
.
.
Lp=24}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 24
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Sai yau muka cika burinmu baba, mu 'yan uwanka ne na jini."
.
Nalamma ya dan yi murmushi daqyar ya fara qoqarin tashi ya zauna, Shago ya dafeshi cikin sauri.
.
"jikinka Babu qarfi baba, kada ka damu ka ci gaba da kwanciya, babu abin da zai sameka a ynx, indai kana tare da mu."
.
Duk da kalaman Shago dake cike da ladabi, bai hana Nalamma tashi ya zauna ba." ya kalli inda suke, ya dubi makeken kogin da kuma ciyayin dake a wajen, farin wata ya haska ko ina. Ya juya 6angaren sa na dama ya dubi mai ankwa dake magashiyan a kwance.
.
"wannan kuma wanene ke a kwance?"
.
Shago ya bashi amsa cikin ladabi
.
"dan uwanmu ne 'yansanda suka harbeshi a cinya, lkcn da muke qoqarin fitowa da kai."
.
Nalamma ya kawar da kanshi ya sake duban makeken kogin. yayi shiru yana wasi-wasin yin tsalle ya qunduma ciki ya huta. Ya yi ajiyar xuciya ya dubi Shago ya tambayeshi.
.
"me yasa kuke son ku fito da ni daga gidan yari?"
.
Shago ya sake yin qasa-qasa da murya, ya ce da Tsohon
.
"sbd muna jin zafin wahalar da aka bamu labarin kana Sha a wajen Jami'an tsaro. Tuntuni muke son mu fito da kai, domin ka dawo ka zauna tare damu. Ka kwantar da hankalinka baba, mu 'yan uwanka ne, ba zamu cuceka ba."
.
Nalamma ya hade ranshi cikin damuwa, ya kalli Shago har cikin idanunsa, ya ce dashi.
.
"kai yaro! Ka dubeni da kyau ina da Sauran hankalina. Na san duk maganar da kake qarya ne, na san dalilin da ya sa kuka satoni a wajen 'yansanda. kuna so ne in fada maku inda na 6oye dukiyar da na tsinta tun shekaru talatin da biyar da suka wuce, shi yasa kuka je asibitin da aka kaini kuka satoni."
.
Nalamma ya saurara yana numfarfashi, sannan ya sake cewa da Shago cikin shaqaqqiyar murya.
.
"kada ku ta6a tsammanin zan fada maku inda wannan dukiyar take. Na san duk mugun nufinku bai wuce kuyi min azaba har in sha wahala in karaya in fada maku inda na 6oye dukiyar ba,ya ku je ku daukota. Ina son ku san cewar, Babu wata wahala da zaku bani in fada maku. Ba zan ta6a fada maku ba." na san azabar da zaku gana mani, ba zata kai ko rabin wacce na sha a hannun 'yan doka ba. Kuma na jure ban fada masu ba." don haka Kuma ba zan fada maku ba. Kada ku ba kanku wahala, gara kuyi tafiyarku ku barni, ku daina wahala akaina, don kuwa ko shekaru nawa zakuyi tare da ni, ba zan ta6a fada maku ba."
.
Shago ya bi Tsohon da kallo cikin mamakin maganganun da yake fada masa, yana zaro masa busassun idanunsa. Bai sake tunanin yiwa Tsohon magana ba, sai ya sa yatsa a bakinsa yayi usir da qarfi, wanda ya tafi nesa ya karade ko'ina a harabar kogin. Wannan shine hanyar da suke bi wajen isar da saqo a tsakaninsu, idan daya yana a nesa. Kuma alama ce dake nuna cewar Babu lfy.
.
Shago ya gama yin usir din kenan ba da jimawa ba, sai ga sadi kare-garke ya yanko aguje ya dawo wajen, da xuwansa tun kafin ya dubi Nalamma, da ya farfado yana a zaune, sai ya tambayi Shago.
.
"me yake faruwa?"
.
Kafin Shago ya bashi amsa ne sai ya dubi Tsohon wanda yake a zaune dan tsurut dashi kamar bakwaini.
.
"hannu baba."
.
Sadi ya ce dashi...?wannan
.
"ka farfado ne?"
.
Nalamma ya ce dashi a fusace.
.
"eh na farfado, Kuma lkcn rabuwata daku yayi. Ina so ku yi tafiyarku ku rabu da ni, ko Kuma ku mayar da ni wajen 'yan doka, su ci gaba da tsare ni."
.
Sadi ya durqusa a gaban Tsohon cikin murnar farfadowarsa. Ya ce da shi.
.
"me yayi zafin haka baba? Na dauka kayi hira da Shago ne ya fada maka dalilin da yasa muka daukoka daga wajen 'yansanda?"
.
Nalamma ya ce dashi
.
"ko bai fada mani ba, nima zan iya gane dalilin da ya san kuka je wajensu kuka sato ni yaro. Kuna so ne in fada maku inda na 6oye gwala-gwalan da suka jawo aka tsare ni tun shekaru talatin da suka gabata, wannan shine abin da kuke so ku ji daga wajena, Kuma ba zan ta6a fada maku ba."
.
Sadi ya dubi Tsohon cikin mamaki. Ya ce dashi...?wannan
.
"baba me yasa ka ce haka? Baka ganin ka tsufa ka kusa mutuwa? Idan baka taimaka mana ba, babu wanda zai amfana da wannan dukiya, maimakon ayi asararta babu wanda ya sameta, me zai hana ka fada mana baba?"
.
Nalamma ya ce da sadi kare-garke
.
"ni mutum ne mai ra'ayin kaina yarO. Tun lkcn da Jami'an tsaro suka kamani, tambayar da suke yi mani kenan, ban yi niyyar in fada masu ba." don haka kuma ba zan fada maku ba. Wannan dukiyar tayi nisa a halin ynx, babu wanda zai sameta sai mai rabo. Kada ku ba kanku wahala, Babu a cikin mutanen da ya cancanta su mallaiann dukiyar, ba zan fada maku ba."
.
Shago ya matso a fusace ya ce da sadi.
.
"oga Tsohon nan fa yana kawo raini, a fara aiki mana akanshi. Don ya dawo cikin hankalinsa ya canza maganar da yake fada."
.
Sadi ya juya ya dubi Shago wanda hannunsa yake rawa yana hararar Nalamma. Ya yiwa yaron nasa murmushi ya ce dashi...?wannan
.
"ba ynx ba Shago, da Sauran lkc. Ba a nan zamu yi aiki ba,ya har ynx baba yana da damar da zai canza ra'ayin sa, ya dawo ya bamu hadi kai."
.
Nalamma ya ce da sadi.
.
"kai yaro, ina da zafin kai, Kuma a zamanin da nayi tawa rayuwar sa'ar da ina matashi kamarka, na tabbatar ba zaka iya maimaita irin abubuwan da nayi ba."
.
.
Lp"25}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 25
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Kai yaro nima ina da zafin kai, Kuma a zamanin da nayi tawa rayuwar sa'ar da ina matashi kamarka, na tabbatar ba zaka iya maimaita abubuwan da nayi ba." ku tafi ku rabu da ni, ko kuma ku mayar da ni wajen 'yan dokan da kuka sato ni."
.
Sadi ya yiwa Nalamma murmushi, ga alama bai karaya ba da maganganun da Tsohon yake fada.
.
"ba komai baba."
.
Sadi ya ce dashi.
.
"zamu ci gaba da tafiya tare da kai, har xuwa inda zamu samu ma6oya. kayi tunani mai kyau kafin lkcn. muna buqatar hadin kanka. Kuma muna fafan zaka fada mana abin da muke so a qarshe."
.
Nalamma yayi shiru yana kallon mutanen biyu, Akwai alamomin tsana qarara akan motsattiyar fuskarsa. Sadi ya ce da Shago.
.
"na samu kwale-kwalen da zamu hau mu qetare kogin nan. Ina ganin ynx tunda baba ya farfado bama buqatar daukarsa, amma dolene mu daure masa hannaye da qafafuwa, don kada baba ya zo da wasa a cikin kwale-kwalen idan muna tafiya."
.
Shago ya tashi cikin damuwa ya tafi nemo igiya, bai ji dadi ba, da sadi ya hana shi yin aiki akan Tsohon, bai kamata ba ace Tsohon ya riqa gaigaya masu maganganu irin haka ba." yaso ya bashi dama yayi aiki ko na minti biyu ne a jikin Tsohon. a qalla ko qafarshi ya karya ya dan matseta na wani lkc, ya tabbatar Tsohon zai canza irin maganar da yake fada masu.
.
Shago ya samo igiyar kaba a nesa kadan daga bakin rafin, a cikin fadamun dake maqwabtaka da wajen. Tun kafin sadi ya bashi umarrnin daure Nalamma, Shago ya cakumi ramammen Tsohon ya hada hannuwansa ya fara daurewa.
.
"kayi masa a hankali Shago. Ka san baba bai cika lfy ba, yana buqatar hutawa. Kada ciwon sa ya qara tashi."
.
Shago bai dauki umarnin ba a wannan karon, ya tsamkewa Tsohon hannuwansa, ya koma wajen qafafuwa wadanda suke kama da maburgin miya, ya hadasu ya daure su tamau, sai da Nalamma ya runtse idanunsa sbd zafin daurin. Sadi ya ce da Shago
.
"ka taimakwa baba ku taho muje inda kwale-kwalen yake."
.
Da Shago ya ga sadi ya tashi zai shige gaba, Su tafi, sai yayi saurin tambayarsa.
.
"oga baka ce komai ba a game da mai ankwa, naga Kuma zamu tafi."
.
Sadi ya dubi mai ankwa wanda ke sharkaf a kwance, ya ce.
.
"bamu da buqatar mai ankwa a halin ynx Shago, dama tun farko sai da na fada maku, wannan aikin yafi kowanne aiki da muka ta6a yi hadari. Ba lallai bane mu kai labari mu duka, ni kaina bani da tabbacin zan qetare, idan na fadi dole kai zaka dauki aikin ka ci gaba da gudanar dashi yadda ya kamata. Haka zan yi nima idan ka fadi, ba zan yi wahalar tsayawa yin dawainiya da kai ba Shago. A wannan aikin namu, muna da amfani ne kawai idan muna a tsaye, duk wanda ya fadi dole ne a tafi a barshi ko wane ne....! Koda kuwa nine, ina fatan ynx ka gane yadda aikin namu yake?"
.
Shago ya ce cikin ladabi.
.
"na gane oga."
.
Sadi ya shige gaba ba tare da ya qarawa yaron koda kalma daya ba a wannan darasin da ya koyar dashi. To amma Kuma duk da haka lkcn da Shago ya tattaro Nalamma da hannu daya, kafin ya bi sadi su bar wurin , sai da ya sake juyawa ya dubi abokinshi mai ankwa. Da yake ya tabbatar ba zasu sake haduwa ba, har abada, sai ya daga masa hannu cikin girmamawa, duk da kuwa ya san mai ankwa baya ganinsa. Ya zama dole ya jinjina masa a bisa namijin qoqarin da yayi a zaman da suka yi tare.
.
Shago yana rungume da tsoho Nalamma har suka je inda sadi yace yaga kwale-kwalen dake kafe a jikin wani turke. Sadi ya fara gangarwa ya kwance kwale-kwalen ya daidaitashi xuwa inda zasu fuskanta.
.
A cikin minti daya suka shiga cikin kwale-kwalen su duka ukun. Shago shine a gaba wanda ya dauki kwarashin janye ruwa, shi Kuma sadi yana a baya tare da Nalamma dake a daure yana kallon su daya bayan daya, ba tare da ya san inda zasu nufa dashi ba."
.
Shago ya fara janye ruwan, kwale-kwalen ya fara tafiya' sannu a hankali har suka yi nisa kadan-kadan ake iya hangosu.
.
Ba a jima ba da tafiyarsu wata ungulu wacce ke shawagi a sararin samaniya, tana neman mushe don kada ta kwana da yunwa. Kwatsam! Sai idanunta masu hangen nesa suka hango mata mai ankwa, kamar walqiya ta sulmiyo daga sama ta dira akan shi. Da tabbatar abinci ya samu, sai ta tashi sama, ta koma inda wasu bishiyoyin turare suke a wata fadama, ta jawo abokan zamanta suka dungumo baki dayansu tare, 'ya'yansu da jikoki suka fara sauka a bakin kogin inda mutumin yake a kwance, rai qwaqwai- mutuwa-qwaqwai.
.
A qa'idan ungulu bata gaggawar ta6a duk wani abu dake numfashi, ta gwammace dai ta hau saman bishiya ta jira a mutu ko kwana nawa zata yi a wajen. To amma sakamakon kwanakin da aka shafe ba a samu mushen komai ba a dajin, a wannan karon wadannan rukunin ungulai basu zauna jiran mai ankwa ya gama mutuwa ba." da sauran ranshi suka fada shi da tsattsaga. Awa daya bayan haka, mutum ba zai so yaga dan abin da yayi saura ba cikin abin da ungulayen suka ci suka rage, daga gawar mai ankwa.
.
.
.
***
.
.
A haka sannu a hankali cikin abin da bai wuce minti ashirin suka kai gabar kogin da suka dosa, 6angaren arewa. Da isarsu ko daure kwale-kwalen basu yi ba, suka fito. Sadi ya dauki Nalamma da hannu daya kamar zakara, shago ya bi bayansa suka fito daga cikin kwale-kwalen suka Hauwa yashi. Sadi ya fara yin magana, wanda Kuma tarsu waccan ga6ar Babu wanda ya cewa kowa komai, har xuwa fitar su ynx daga kwale-kwalen.
.
"indai ban mance ba akwai wani gida nan gaba kadan dake kusa da kogin nan...ka na ta6a wuceshi sanda muka zo wani aiki a wani qauye nan dake a kusa. ina jin gidan gona ne."
.
Shago ya ce cikin ladabi.
.
"mu je mu gani oga, ni ban ta6a xuwa nan ba."
.
.
Lp=26}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 26
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"mu je mu gani oga, ni ban ta6a xuwa nan ba."
.
Suka tafi, bayan sun fita daga harabar da ruwan kogin yake malalowa ne, yana taruwa a cikin fadamun manoman dake noman rani a yankin, sai suka hau wata qaramar hanya wacce ke da ta6o, da kuma alamun manyan sawun tayar mota, hakan alama ce dake nuna lkc-lkc motocin daukar rake sukan shigo wajen, duk da rashin kyan hanyar. wani lkcn Kuma suna kafewa sai mutane sun taru sun tura motocin.
.
Basu yi nisa ba a hanyar sai suka hango wani qayataccen gida a 6angaren su na hagu. Sadi dake a gaba rungume da Tsohon ya ce.
.
"kaga gidan nan, mu je mu saurara ko zamu ji maganar mutane a ciki. Ko su wanene ke zaune dolene su bamu wuri. Sbd bamu da wata sahihiyar ma6oya da ta wuce nan gidan."
.
Shago ya ce.
.
"wannan ai dole ne oga, duk inda muka shiga ai mune masu gidan."
.
Sadi ya dan yi murmushin jin dadi, yana son wannan kirarin da yaransa suke yi masa, ko suma sun fahimci haka, sbd zaman yau da kullum yasa suka gane haka. Idan mutum yana son ya zauna lfy da sadi qare-garke' to dolene ya riqa girmamashi koda kuwa mutum baya sonshi, kada ya nuna masa a fuska ya gane.
.
Duk surutun da suke yi dan Tsohon yana sauraren su, sadi yana ta kayansa, kamar ya rungumo kayan wanki. Bai sa masu baki ba a maganarsu, su kuma basu sa da shi ba."
.
Suka isa inda qofar gidan yake, suka tsaya. Yanayin da aka yiwa gidan ba fasalin ginin karkara bane. Dan madaidaici ne, amma an fitar da filin shaqatawa daga ciki, ko ina a zagaye yake da dakuna. Qofar shiga gidan a kulle take, akwai faffadar qofar shiga da mota, da kuma 'yar qarama a jone. Sadi ya dubi faskeken kwadon dake a jikin bahauwar qofar ya ce.
.
"ga alama masu gidan basu nan Shago. Mu shiga mu jirasu kafin su shigo su tarbemu, daga yau mun zama baqinsu."
.
Hakan da ya fada ya sa Shago ya fahimci umarnin karya qofar aka bashi. Shago ya ciro wata kakkaurar adda mai nauyi daga bayansa, wacce in ba irin wannan aikin ne ya taso ba,ya ba kowanne lkc yake cirota ba." da cirota ya dagata ya kaftawa kwadon sara, qarar dukan kwadon da addar ya tsorata halittu da yawa dake a kurkusa da wajen. Sannan Kuma ya dan gigita tsoho Nalamma wanda ya dan firgita a hannun sadi.
.
Faruwar hakan ya sa sadi murmushin jin dadi, don kuwa yafi so yaga Tsohon yana nuna alamar karaya da jin tsoro. Ta haka ne zai basu hadin kai idan sun zo yin aiki akanshi.
.
"ya tsorata ka ko baba? Kada ka damu, mun zo inda zamu huta da mu da kai, bari ya bude qofar mu shiga ciki."
.
Ya sake tallabe Nalamma kamar yana kula da yaro dan shekara biyu. Tsohon yayi dogon numfashi bai cewa sadi komai ba." Shago ya bude qofar bai shiga ba, da ya bude qofar sai ya baiwa sadi waje domin ya fara shiga, sannan ya bi shi a baya.
.
Da shigar su suka sami qofar da ake shiga falon wanda ta cikinsa ne kawai ake iya bi a shiga duk wani daki dake a gidan, idan aka dauke dakin kare da na inji, wadanda suka kasance a waje a hade da bahauwar qofar shigowa da motar.
.
A wannan karon shago bai jira sadi ya sake bashi umarni ba, ya sake datse qaramin kwadon dake a jikin qofar falon. Ya bude qofar ya turata. Sadi ya ciro cocilarsa a cikin aljihunsa ya haska falon daga waje. Tun kafin su shiga cocilar ta hasko masu hadaddun kujeru manya-manya na hutawa. Da kuma Sauran kayayyakin morw rayuwar dake a cikin falon. Sadi ya ce da da Shago.
.
"wannan gidan shaqatawar 'yan boko ne, wadanda suke buqatar yanayi mai sanyi, akwai kayan hutu a gidan nan."
.
Shago ya ce da dashi..
.
"oga ynx ai kaine mai gidan, kai zaka shaqata a ciki, idan sun zo bandaki zasu koma su riqa kwana. Sun zama bayinka."
.
Sadi qare-garke ya fashe da dariyar jin dadi. Ya ce.
.
"baka da dama shagona. Mu shiga mu huta kafin su zo su same mu."
.
Suka shiga cikin qawataccen falon. Da shigarsu sadi ya ajiye Nalamma a qasan falon, wanda yake malale da dadduma kalar ciyayin bakin kogi, da ya ajiyeshi ne ya ci gaba da haska ko ina a cikin falon, a tsanake ya fahimci akwai dakunan barci biyu da bandaki a ciki. Sai wani qaramin wanda bai san kp na menene ba."
.
.
Lp=27
}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 27
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
Tare da
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Sadi ya ajiye Nalamma a qasan falon, wanda yake malale da dadduma kalar ciyayin bakinn kogi, da ya ajiye shi ne ya ci gaba da haska ko'ina ya fahimci Akwai dakunan barci guda biyu da bandaki a ciki. Sai wani qaramin daki, wanda bai san ko na mene ba." yana cikin haske-hasken ne ya hango wata bahauwar fitila mai batir, wacce ke a kusurwar falon. Ya ce da Shago
.
"dauko fitila gata can ka kunnata mu ga haske Shago."
.
Tun kafin ya gama sanar da Shago, ya je ya dauko fitilar ya kunnata, hasken ya cika falon kamar rana. Sadi ya kashe cocilar sa tunda dai an samu wata. A lkcn ne ya dubi tsoho Nalamma wanda yake a takure a daure, ga alama igiyar ta ci jikin sa, kuma yana shan wuya. Sadi ya ce da yaronsa.
.
"Shago ya kamata a kwance baba haka nan, shima ya dan samu sauqi. Kafin mu zo kan aiki anjima."
.
Shago ya harari Tsohon, baya son ya kwanceshi, to amma dolene ya bi umarnin ubangidansa. Ya kama igiyar ya fara tsinkata da hannu, duk da haka sai da yayi qorafi, ya ce cikin damuwa.
.
"oga muna fada yiwa Tsohon nan sakwa-sakwa. Shi yasa yake ganin kamar abin wasa ne."
.
Sadi yayi dariya ya ce da Shago.
.
"ynx wasa muke yi mana Shago. Ai sai dare yayi nisa ake aiki. Na san kafin lkcn baba ya canza ra'ayinshi, zai bamu hadin kai Shago kada ka damu. Mu dai samu abinci mu ci tukuna, har ynx bamu gama hutawa ba."
.
Nalamma yayi tari muryarsa na kyarma yaCe.
.
"yara kuna 6atawa kanku lkc ne a banza. Dama kun rabu da ni, kun samu wani aikin kun je kun yi, amma ba zaku ta6a jin sirrin da kuke nema a wajena ba."
.
Shago wanda ya durqusa a gabansa yana kwance masa igiyar qafa, ya tsaya ya harari Tsohon, da yake sadi ya san in bai yi saurin shiga tsakanin su ba, Shago zai iya ba kanshi umarni ya mangare tsohon, sai yayi saurin matsowa ya ture Shago gefe guda ya ce dashi.
.
"kauce ka bani wuri, na lura baku jituwa kai da baba. Ban san me yayi zafi a tsakanin ku ba tun daxu."
.
Ya qarishe kunce masa igiyar a hankali, Shago wanda ya tsaya a baya xuciya ta gama suqe shi, yayi sauri ya ciro kwalin taba, ya zaro kara daya ya cinna mata wuta. Sbd in har bai Sha wani abu ba a dai wannan lkc. Xuciyarsa ba zata haqura ya qyale wannan Tsohon yana fada masu maganar da yaga dama ba."
.
Bayan ya kwance masa igiyar ne ya ce da Tsohon
.
"ka daukemu a matsayin 'yan uwanka baba, bai kamata ka riqa yin fada damu ba." kaga mu jikokinka ne, wannan maganganun da kake fada ba girmanka bane, abin yana bani kunya idan naji kuna fada kai da shagona, bai dace ba ace kana haka baba. Ka bamu hadin kai, ba abin da zamu yi maka. Ka kwantar da hankalinka. Kada ka ce zaka gudu don kaga mun kwanceka, bamu son mu fito maka a yadda muke, shi yasa kaga muna girmamaka."
.
Tsohon yayi ajiyar xuciya duk da yake dai bashi da niyyar bayar da hadin kai, akwai alamar maganar da sadi ya fada ta dan yi masa dadi a ranshi. Ya gyara murya ya ce dashi.
.
"ina so zan sha ruwa, qishi nake ji."
.
Sadi ya juya ya duni Shago, wanda ya koma gefe yana shan taba yana kallon Tsohon a fusace. Ya ce.
.
"duba mana ka gani ko za a samu ruwa a gidan nan, idan akwai abinci ka dauko mana ka kawo."
.
Ya juya 6angaren Nalamma cikin fara'a, ya tambayeshi.
.
"na san kana jin yunwa ma ko baba? Bari ya duba, in ba a samu ba a nan, sai ya shiga gari ya nemo maka, ko a ina yake. Ni dai burina in ga hankalinka ya kwanta."
.
Shago ya dauki fitilar ya fara dube-duben inda masu gidan suke ajiye abinci. Ya bar sadi tare da Nalamma wadanda suke zaune a qasa, sadi yana rarrashin Tsohon kamar dan yaye a hannun kakarsa.
.
Shago ya fara bincika dakunan gidan, da

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

4 months ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment