Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kira shi. Ta kasa kunne tana sauraren wayar tana bugawa amma ba a dauka ba, har wayar ta katse. Hauwa tayi tsaki ta sake kiransa cikin damuwa.
.
.
}~~~~~~{ Gobe jar Kasa }~~~~~~{
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar wannan shafin ba."
.
Hauwa tayi tsaki ta sake kiransa cikin damuwa. Ta san dalilin da yasa ya qi daukar wayar, yayi zaton tana a can asibitin ne tana so ya je ya daukota. Sau da yawa idan baya son xuwa sai ta ci kiransa har ta gaji ba zai dauki wayar ba, sai dai ta hau tasi ta dawo gida.
.
Wayar ta sake shiga, Hauwa ta tsaya cikin damuwa a dakin nata tana riqe da wayar tana saurare cikin qosawa nura ya dauka, don kuwa ba zancen zuwa ya daukota ake yi ba yau, ana zancen dukiya ne da ta samu. Idan har da rabo, dukiyar tazo hannu mai kuma zasu yi da wani babur? Sai dai xuqa-zuqan motoci kuma na alfarma.
.
Karo na biyu kenan wayar na shiga nura bai dauka ba." zai yiwu kuma yana cikin hayaniyar gosilo ne a titi, shi yasa bai ji ba." da Hauwa tayi wannan tunanin sai ta yanke shawarar rubuta masa gajeren saqo, idan ma ya qi daukar wayar ne da gangan, ta san idan ya ga saqon zai dauki wayar in ta sake kiranshi.
.
Hauwa ta rubuta masa (text) a gurguje ta ce dashi...
"na dawo gida, ka zo ynx ina son ganinka. Magana ce ta qaruwa nura, inda rabonmu zamu samu wata gagarumar dukiya."
.
Hauwa ta tura masa saqon ya tafi, ya fada can cikin wayarsa a inda yake. Da ta tabbatar saqon ya shiga sai ta koma can inda lambarsa take, ta sake kiranshi bugawar farko nura ya dauki wayar cikin sauri.
.
"hello Hauwa ya aka yi ne?"
.
Hauwa ta ce dashi...?wannan
.
"ashe dama kana ji na, ka qi daukar wayar? Dama na san kana ji, ynx nura ya dace abin da kake yi min? Wayata ma ba zaka dauka ba idan baka son magana da ni...?"
.
Nura ya katse ta cikin fushin da ya saba yi mata.
.
"a ina naji kin kira ni? Ba ynx na tsaya ba da naji shigowar (message) dinki ba." na ji kin ce dukiya ta samu, wace iriyar dukiya ban gane ba?"
.
Hauwa tayi ajiyar xuciya, ba yadda zata yi dole ta amince duk da yake ta san qarya yake yi. Ta ce dashi a sanyaye.
.
"ka zo muyi maganar a ggida, ba maganar da zamu yi a waya ba ce nura, ina jiranka a gida."
..
Nura ya ce da ita.
.
"to gani nan xuwa."
.
Ya kashe wayar tun kafin ta sake cewa wani abu.
Hauwa ta girgiza kai cikin jimamin irin wannan wulaqanci da wannan saurayi yake yi mata. Ta zauna a sanyaye a gefen katifar da ta tsare filin dakin tayi tagumi, hasken fuskar wayarta da ta riqe ya dauko hotonta a cikin dakin a zaune ta yi jugum, da hasken wayar ya dauke sai duhun ya gauraye dakin, ita kanta bata iya ganin ko tafin hannunta.
.
Hauwa bata damu ba, ta ci gaba da zama a cikin duhun kamar Babu kowa a cikin dakin. Ta fara tunanin yadda rayuwarta zata kasance tare da nura. Ita kanta ta san kudinta nura yake so ba ita yake so ba." idan har tana so yazo gidansu, to sai dai tayi masa maganar kudi, wani lkcn idan yayi kwana biyu bai zo ba, kuma tana son ganinsa ruwa a jallo sai ta ce dashi ya zo ya amshi kudin gyara a duba babur dinnan, don kuwa qarfe sai da kulawa,
.
Ynxn nan kuwa zata ganshi a guje ya murxo babur ya zo cikin fara'a, idan suka sha hira sai ta kawo kudin ta bashi. Ko asibiti ya je zai daukota, idan ta tashi aiki wani lkcn sai sun biya ta gidan mai ta cika masa tanki fal! Idan tana so yaxo gobe kenan ya dauketa ko bata kirashi ba." amma idan aka ti kwana biyu bata xuba masa mai ba." to 6ata lkc ne tsayawa kiran nura ya xo ya dauketa, don kuwa ta san ba xuwa zai yi ba."
.
Zaman da Hauwa tayi a cikin duhu ynx ita kadai, tana tunanin anya kuwa idan wannan dukiya ta samu nura zai iya riqe amanarta idan suka yi aure suka zauna tare? To ko daI Babu komai ta san don kudi nura zai aureta, kuma inda kudin Suna nan zai iya zama da ita har tsufa, har mutuwa, indai zata dauko ta riqa bashi. amma da zarar kudi sun qare to zama ya qare a tsakaninsu da nura. Wannan abu ne da ita kanta ta sani, sai dai kawai tunda dai ta ji ta gani ta na sonshi. Haka nan zata rufe komai a ci gaba da soyayya a zauna Babu tone-tone. Amma ko shakka Babu nura baya sonta.
.
Hauwa tayi tsaki ita kadai a cikin dakinta ta girgiza kai. Da ace zata iya daina son nura da komai ya zo da sauqi. To amma tayi nisa bata jin kira, wannan saurayi shi kadai ne matsalar rayuwarta. Indai zata yi tsaki ko tayi kuka, ko ta zauna tana tunani, ko kuma tayi tagumi. To kada ma a zauna wahalar tambayarta kai tsaye nura ne!!"
.
To amma Babu mamaki idan suka yi aure komai ya canza, wannan tunanin shi yake dan qarfafa mata guiwa. Ta sha ganin irin wannan, ko da ana samun matsalar soyayya idan aka yi aure sai komai ya daidaita. Hauwa tana sa ran nura zai canza Indai ta samu ya amince ya aureta.
.
Ko ynx wannan tunanin shi ya fado mata a rai. Kamar an dauke mata wani kaya kanta, sai ta saki ranta ta kunna wayarta hasken ya gauraye dakin. Hauwa bata da fitila a dakinta, idan ba wuta tafi zama a dakin mahaifiyarta ko karatu zata yi sai dai ta kwashi litattafanta ta je can ta zauna ta yi. Don haka wannan duhun bai dameta ba, in da sabo ya isabella ace ta saba da duhu, da kuma kadaici a rayuwarta.
.
Tana nan zaune sai ta ji qarar babur din Nura a waje, ta ji yayi murji Sau biyu. Da yake ya san ta san sautin babur din, idan yaxo baya aikawa a kirata. Kuma baya kiranta a waya. Babur din kawai zai murza yayi hon sai ta taso ta fito ta same shi.
.
Hauwa ta tashi ko kayan aikin asibitin bata cire ba, ta dauki gyalenta ta yana ta fita cikin sauri. Ta wuce dakin mahaifiyarta yana nan da hasken fitila. Ba ynx take so ta shiga ba, tana jira ne sai komai ya gama kwaranyewa tsakaninta da nura. Sai ta shiga ta zauna ta ci abincinta.
.
Hauwa ta fita waje ta sami nura a zaune akan babur din da ta bashi (Nanfang), yana sanye da jar riga ta qwallo, mai lamba ashirin da uku a bayanta.
.
Kamar kullum yana nan da tarin suma akanshi, wacce ta riqe tsaitsaye kamar ana bata abinci. wata rana da yake jin nishadi, ya ta6a cewa Hauwa duk sati wanna sumar tana lashe masa kudi fiye da naira dubu biyu.
.
Don haka idan har Hauwa tana kashe kudinta akan nura, to shi Kuma akan suma yake yin tashi asarar. nura qaqqarfane dogo, wanda baya sassauta murya idan zai yi magana. Da wahala yayi magana biyu baiwa yanko ashar ba. Abbokansa sun ta6a sanya mashi gasar babur idan har yayi minti biyar baiwa yi ashar ba, ya zama nasa.
.
Nura ya so ya jure ya yi shiru har lkcn yayi, ya ci gasar babur din, anyi minti hudu kafin minti biyar din ne, sai wata kaza ta zo gabansu tana kyarkyara. Nura ya kai mata hauri ya mirgina mata ashariya. Kazar ta ruga aguje tana faffaka a daidai lkcn da abokan nura suka cika majalisar tasu da sowa da dararraku. Basu yi mamaki ba, don kuwa sun san indai nura zai yi magana, to ko milyan za a sanya masa, dole ne sai yayi ashar sbd tsabar zafin rai da rashin haqurinsa.
.
Tun kafin Hauwa tayi masa sallama ya ce da da ita.
.
"wai ke abidfada gsky ne, ko kuwa kin yi haka ne don in zo?"
.
Hauwa ba ta ce dashi komai ba sai da ta matsa kusa dashi ta dafa kan babur din, sannan tayi masa magana a sanyaye don ta kwantar da xuciyarsa ya dan lafa, su ti hirar a tsanake.
.
"ka san ba zan yi maka qarya ba nura."
.
Ta ce dashi kamar tana rera masa waqa.
.
"amma kafin muyi magana, ai ya kamata ko gaisaw muyi, kada fada ka mance rabon da in ganka tun shekaranjiya nura, na fahimci ynx guduna ma kake yi."
.

.
Hauwa ta qura wa fuskarsa idanu, duk da babu wadatuwar haske a layin nasu, ta samu damar ganin fuskarsa da taimakon qyallin wutar da wata yarinya ta hada a kusa dasu tana tuyar awara da doya. Da yake nura ya ji tabbas zancen kudin da tayi masa daxu a waya gsky ne, ba wasa take yi ba, sai ya dan saki ranshi ya ce da ita.
.
"ya za a yi in guje ki Hauwa? Ke Kullum haka kike cewa, wai ina gudunki. Ba haka bane, kin san bana zama a gida, ke kuma kin fi so kullum in zo gida ayi hira."
.
Hauwa ta ci gaba da kallonshi ta ce.
.
"to amma dai nura ko ina zaka je ai ya kamata dai a qalla ko sau daya ace ina ganinka a rana. Idan ba ni na kira nace kazo ka daukeni a asibiti ba ba zaka zo ba."
.
Nura ya ce da ita.
.
"duk lkcn da kike kirana bani a kusa ne, idan ina nesa kafin in zo asibitin ya isa ace kin hau tasi kin zo gida, maimakon ki tsaya jiran."
.
.
L=12}~~~~~~{ Gobe jar Kasa }~~~~~~{
Page 12
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Duk lkcn da kika kira bani a kusa da gida ne, idan ina nesa kafin in zo asibitin ya isa ki hau tasi ki dawo gida ki huta maimakon ki tsaya jiran."
.
Hauwa tayi murmushin jin dadi, yau wacce rana nura yana bata amsar maganarta cikin girma da arziqi? Da yake ta fahimci idan ta ci gaba da tuhumarsa, malejin haqurinsa zai iya qarewa ya bata amsar a fusace, sai ta canza akalar hirar, tayi ajiyar xuciya ta ce dashi...
.
"nura wani abu ya faru da ni a asibiti, wanda ya daure mani kai. Abin kamar almara ko mafarki, kai kanka idan na fada maka ba lallai bane ka yarda, to amma idan na fadi maka hujjojin dake tattare da abin dole ne ka yarda."
.
Nura ya yi shiru yana saurarenta. Hauwa bata cire hannunta daga kan babur din ba." ta waiga Kowanne 6angare ta tabbatar babu wani mutum a kusa da qofar gidan nasu. Ba mutane a layin. Yarinyar dake zaune ta tasa kaskon awara da doyar ne kadai, sai wasu tsirarun qannenta guda uku da suka zagayeta. Hauwa ta dawo da hankalinta kan nura wanda yake zaune akan babur yana saurarenta.
.
"wani tsoho aka kawo mana asibiti Bashi da lfy daga gidan yari."
.
Hauwa ta fara baiwa masoyinta nura labarin tsoho Nalamma da irin tsauraran matakan da Jami'an tsaron suka dauka akanshi. Hauwa ta fadiwa nura labarin da Tsohon ya bata, ta ce dashi a qarshe.
.
"ya kwatanta mani inda ya 6oye ma'adanan a dajin tudun kudi. Idan har Suna nan wani bai je ya kwashe ba." mun samu dukiya mai yawa. Don kuwa zamu iya daukesu mu kaisu qasashen waje, mu sayar dasu a can."
.
Tun kafin ta kai qarshe nura ya dakatar da ita.
.
"Hauwa kin tabbatar labarin da wannan Tsohon ya baki gsky ne?"l
.
Hauwa ta ce dashi..
.
"to idan qarya ne me zai san Jami'an tsaron su cika asibitin Suna gadinsa? Basu barin kowanne mutum ya ra6i dakin da aka kwantar dashi...su kansu basu yarda da junansu ba, basu barin kowa ya je inda Tsohon yake, sai dai su shiga su dduka a lkc daya.
.
Nura ya gyara zama akan babur din kamar Wanda ake cizonsa ya ce da Hauwa.
.
"to idan haka ne, me zamu jira? Kawai mu tafi dajin ynxn nan mu tono gwala-gwalan, ba 6ata lkc zamu tsaya yi ba."
.
Hauwa ta riqe numfashinta.
.
"ynx fa ka ce nura? Ya za'yi mu shiga dajin a wannan daren? Mu bari dai sai gobe da rana ido na ganin ido zai fi."
.
Nura ya qara daga murya cikin jayayya.
.
"dajin ne zamu je sai gobe da rana, kowa yana ganinmu? Ai irin wannan al"amarin a irin ynx ake xuwa a 6oye ba wanda ya sani, kada fa ki mance, dukiya ce mai zaman kanta ba a san inda take ba, ynx a cikin daren nan zamu tafi Hauwa, ba tsayawa zamu yi 6ata lkc ba har wasu su riga mu xuwa su tono dukiyar."
.
Hau tayi nazarin lkcn da suke ciki, kusan qarfe takwas kenan na dare. Idan ba larura ba adaidai wannan lkcn ko layinsu bata iya bari. Don haka zai yi wahala ta iya xuwa daji a wannan daren. To amma ta san halin nura idan ya kafe akan abu baya haqura. Hauwa ta ce dashi...?wannan
.
"gsky ina jin tsoro nura. Ba zan iya xuwa daji a cikin wannan daren ba." mu bari sai gobe."
.
Nura ya fara yi mata tsawar da ya saba idan yana fushi.
.
"ba zamu bari sai goben ba, ynxn zamu je. Tunda ke ya ya kwatantawa inda ya 6oye dukiyar dole ne ki zo mu je a daren nan mu gani in da gaskene!"
.
Hauwa ta san ko rami nura ya ce ta fada in dai zai nuna mata fushinsa zata iya fadawa. Don haka ba tare da ta tsaya sake yin tunani ba, sai ta ce dashi...?wannan
.
"to nura Tunda ka matsa sai mun je ynx, ai shi kenan. Amma gsky ni dai ina jin tsoro."
.
Nura ya ce da ita.
.
"ki shiga gida ki shirya ynxn nan, baring nima in shiga in dauko cocilata da kuma diga wacce zan haqa ramin da ita."
.
Yana gama fadin haka, ya sauko daga kan babur din ya kafeshi, ya garzaaya cikin gudu-gudu ya nufi gidansu dake a can gaba a daya 6angaren ba a jere da gidan su hauwa ba."
.
Hauwa bata motsa ba, har nura ya shiga gida, don gudun kada ya fito ya sameta tana nan ko gida bata shiga ba, sai tayi sauri ta shiga. Ta koma dakinta jikinta a sanyaye.
.
Hauwa ta rasa abin da zata dauka a dakin. Ta dauki rigar sanyinta, wacce 6ata qawarta ta saqa mata tun a shekaru uku da suka wuce, ta kakka6e rigar ta dora ta akan rigae dake jikinta ta aiki. Ba abin da zata dauka, don haka sai ta fito daga dakin riqe da gyalenta ta jawo qofar dakinta a wannan karon ta kulle.
.
Da yake ta san zasu dade wataqila basu dawo ba, sai ta shiga dakin mahaifiyarta ta sameta a zaune a gaban fitila tana dandaqa kwalli da danbida. Hauwa tayi mata sallama, sannan ta gaisheta. Mahaifiyarta ta ce da ita.
.
"tun daxu naji motsin shigowarki, sannan na kuma jin kin sake ficewa waje.
.
Hauw da yake ta san mahaifiyarta bata son nura sai ta ce da ita.
.
"eh, na je sayo ambulan ne a shago."
.
Har mahaifiyarta zata miqo mata abincinta, sai Hauwa ta ce da ita.
.
"mama zan je wani wuri ne ynx, sai dai na dawo...
.
.
Lp=13}~~~~~~{ Gobe jar kasa}~~~~~~{
Page 13
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Eh, naje sayo ambulan ne a shago."
.
Har mahaifiyarta zata miqo mata abincinta sai Hauwa ta ce da ita.
.
"mama zan je wani wuri ne ynx, sai dai na dawo.... Zan amsa wata takarda ne a wajen daraktan asibiti, kin san ina neman canjin wajen aiki, zan sake asibiti. To kujiba-kujibar da nake ta yi kenan a 'yan kwankin nan."
.
Sau da yawa irin wadannan qarerayin Hauwa take yiwa mahaifiyarta idan tana so ta je wani waje, wanda bata so ta yiwa mahaifiyarta bayanin ko ina ne....! Da yake Hauwa ta san tsohuwar wayayyiyace a zamanin da tayi nata tashen, kawai karatu ne aka rata dashi bata yi ba, shi yasa duk qarerayin da take yi mata, sun fi qarfin a wajen aiki ko karatu, ta san a nan ne kawai mahaifiyarta bata da ido.
.
Tsohuwar ta fasa dauko mata abincin ta ce da ita.
.
"to a dawo lfy, allah ya sa a dace Hauwa."
.
Budurwar ta fice ta bar dakin cikin sauri don gudun kada ta 6atawa nura raina yayi ta jiranta a waje. Da fitarta qofar gidan ta same shi har ya dawo, yana dauke da wata qatuwar diga mai tsini.
.
Hauwa ta warware gyalenta ta lullu6ashi akanta, ta tsaya jiran nura wanda yake ta qoqarin cusa doguwar digar a kariyar babur din. Bayan ya shigar da digar ne sai ya dago kai ya dubi Hauwa. Akwai wani yanayi na rashin natsuwa da ke tattare da nura wanda ya sa Hauwa ta ji ya fara bata tsoro, kamar ba nuranta da ta sani ba."
.
"ina fatan dai baki fadiwa kowa inda zamu je ba?"
.
Hauwa ta girgiza kai.
.
"ko mama ban fadawa ba." na ce da ita kawai zan je wani waje in dawo."
.
Nura ya cire matakarin babur din ya hau ya tashe shi cikin sauri, bugawa daya ya tashi, ya kalli Hauwa cikin qosawa wacce ta tsaya kamar ta na jin tsoron hawa babur din. Tayi qarfin hali ta hau a sanyaye, tun kafin ta gama gyarawa nura ya fizgi babur din suka cilla aguje.
.

Duk da Hauwa ta sa rigar sanyi baiwa magance mata qaqqarfan sanyyin dake ratsa har cikin qashinta ba." ta qanqame gyalenta da hannu biyu ta take a bayan babur din.
.
Nura ya riqa cilla gudu Babu saurarawa, Hauwa tana a baya, tana kokuwa da iska wacce ke ta yunqurin qwace mata gyalenta ta tashi dashi sama. Har suka bar gari suka doshi hanyar dajin tudun kudi, tsoro ne da xullumi a cikin xuciyarta.
.
.
.
*** *** ***
.
.
Babi na biyar
.
.
Farin watan da ya kutso daga cikin giza-gizan da suka toshe gabashin sararin samaniya, shi ya fara rage duhun da ya mamaye ilahirin duniyar. Kafin wani lkc tuni giza-gizan sun tarwatse, Suna sake matsugunni a wani yankin, farin watan yana sake fitowa, hasken yana ta qaruwa.
.
Wannan shi ya ba yawancin mutanen dake zaman jinyar 'yan uwansu a asibitin (karama hospital) damar firfitowa, don kuwa a yadda faffadan farin watan dan daren Sha biyar ya tsaya ddodar a sararin samaniya, abin gwanin ban sha'awa. ba kowanne bil'adama zai zauna a cikin daki ba tare da ya fito ya sha iska ba."
.
A cikin awoyi biyar xuwa shida da xuwan Jami'an tsaron asibitin, har mutane sun fara sabawa da ganinsu. Sun saki jikinsu. Da yake likita ya shiga kowanne daki ya kwantarwa da mutane hankali cewar, kada su damu kansu don ganin Jami'an tsaron, ba wanda zasu ta6a, suma sun kawo masu mara lafiyar ne....! Don haka sai mutane suka ci gaba da ficensu, Suna wuce Jami'an tsaron wadanda suka yi sansani guda a bakin qofar dakin da Tsohon yake kwance, Kowanne riqe da xungureriyar bindigarsa a hannu.
.
Da yake komin dare qofar a bude take, ana barin mutane Suna shiga duba marasa lafiya, akwai mutane a hanyar shigowa asibitin wadanda suka kama hanyar shiga babban dakin jinyar.
.
A cikin irin wadannan mutane da suke shigowa ne kai tsaye wadansu mutane uku suka iso bakin qofar asibitin, suka yi fakin da motarsu a waje ba tare da sun shiga cikin asibitin ba da motarsu. Da tsayawar motar mutum biyu suka bude qofofin baya suka fito, suka bar direban a zaune, ba tare da ya kashe motar ba." direban ba wani bane, shagon sadi ne....! Su Kuma mutum biyun da suka fito mai ankwa ne da ogansu sadi qare-garke
.
Duk da yake qananan kaya suka sanya ba wanda zai gansu a haka yayi zaton masu laifi ne....! Musamman da yake sadi yana riqe da baqar leda wacce ke cike da wani abu kamar tsaraba. To amma da ce mai gadin asibitin zai duba abin dake a cikin ledar zai sha mamakin abin da zai gani. Ba ayaba ko lemon sadi ya xubo a cikin ledar ba." wata qaramar jarka ce cike da fetur.
.
Bayan sun fito ne sai sadi qare-garke ya tsaya a dai-dai jikin qofar da Shago yake zaune a cikin motar ya ce dashi...?wannan
.
"ka zauna a cik shiri Shago , da mun fito dashi mun shigowa ka take mu tafi."
.
Shago ya girgiza kai cikin gamsuwa da gargadin mai gidan nasu. Wannan ba wani sabon aiki bane a wajenshi, yawanci dama idan suka je sata, indai da mota suka je Shago shi ne direba. Ya qware a wajen wauta da gudu a mota. A da can da talle yana nan shine yake riqe da wannan kambun, to amma da yake Babu talle ynx dole ne sadi ya nemi wanda zai riqe masara wannan layin. Lkc yayi da zai kaoyi zama cikin nasara ko da kuwa babu talle.
.
Shi kuwa mai ankwa tare dashi sadi yake so ya shiga duk inda zasu shiga, don kuwa idan tsanani ya yi tsanani, mai ankwa yana nuna ranarsa da bajintarsa a wajen aiki. Indai zasu shiga wani rintsi wanda za a yi batakashi, a yi kare-jini-biri-jini, to dole ne sadi ya shiga da mai ankwa. Ruwan wuta ko harsashin baya tsorata mai ankwa, indai ya san gaba sai yashiga, kuma indai ya dauko sai ya fito.
.
Sadi ya jiya wajen mai ankwa suka kama hanya, suka shiga asibitin kamar wadanda suka zo duba mara lfy, babu wanda zai ga mai ankwa ya gane Akwai bindiga sake a jikinshi.
.
.
Kwanaki biyu da suka gabata na samu matsala wajen typing. Nayi shi complete amma Bayan nayi post sai naga less than half. Ban san yadda kayi ba, ban san me yayi cutting nashi ba."
.
Afuwan ply...
.
.
.
Suka wuce kallamu mai gadi a bakin qofar, ya hada wuta a kasko yana shan dumi. Lkcn da suka kai inda dakunan jinyan suke ne, suka ga Jami'an tsaron sun zagaye wani daki, kai tsaye suka fahimci a nan dakin aka kwantar da Tsohon
.
Mai ankwa da san suka wuce Jami'an tsaron suka shiga babban dakin kwantar da marasa lfy maza, suka riqa wuce marasa lfy da masu jinyarsu. Babu wanda ya damu dasu, don kuwa basu banbanta da Sauran mutane ba dake xuwa asibitin yau da kullum.
.
Shu'uman mutanen biyu suka fakaici mutane suka shige can quryar dogon dakin.
.
.
Lp=14}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 14
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Shu'uman mutanen biyu suka fakaici mutane suka shige can quryar dogon dakin inda bandaki yake. Sadi wanda yake a gaba ya dakatar da mai ankwa ta hanyar daga masa hannu. Nan da nan ya Jami'an birki ya tsaya, ya bar shugabansa don ganin abin da zai fara yi.
.
Sadi qare-garke ya shiga cikin bandakin da xuwansa ya ciro jarkar fetur din ya bude ya watsashi a ko ina a cikin bandakin, kama tun daga silin, har xuwa jikin qofar da tagar wadanda dukansu na katako ne....!
.
Bayan ya gama watsa fetur din ne, sai ya ja da baya ya ciro makunnin taba ya qyasta wuta, ya cinnata a jikin tagar wacce ta dauki wutar nan take. Sadi ya fito cikin sauri, tun kafin yayi wa mai ankwa magana tuni ya fahimci abin da yake nufi.
.
Mai ankwa ya ciro guntuwar bindigarsa ya riqe a hannu, sadi ya shige gaba, shi Kuma ya take masa baya, suka dawo dakin da marasa lfyn suke.
.
Kafin kowa ya mayar da hankali akansu, tuni wutar ta kama dakin rigi-rigi, hayaqi ya taso ya fara turniqe asibitin. mutane suka fara thu a lkc guda Suna kururuwa.
.
"wuta jama'a! Wuta, Ku kawo mana taimaka!!"
.
Mutane suka fara rige-rigen kwashe marasa lfynsu Suna fita dasu waje a guji. Asibitin ya cika da ife-ife da kukan mutanen dake a wasu sassan. Suka fara gudu Suna qoqarin xuwa inda wutar take.
.
Sadi da mai ankwa suka saje a cikin mutane Babu wanda ya gansu. Jami'an tsoran da suke gadin Nalamma suka fara garzayowa babban dakin, don taimakawa wajen fitowa da marasa lfy waje kada wutar tayi qarfi rayuka su salwanta.
.
Jami'an tsaron suka mayar da hankulansu wajen gobarar, suka mance da Nalamma, don kuwa basu yi tsammanin an hada wutar ba ne don a janye hankalinsu. Lkcn da sadi da mai ankwa suka tabbatar duk Jami'an tsaron sun bar wajen sun tafi tallafawa mutane, sai suka garzaya xuwa dakin da Tsohon ya ke.
.
Sadi ya fada cikin dakin, mai ankwa ya tsare qofar riqe da

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment