Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

xuwa gari talla, tana da wata sarqar tsakiya, wacce ta ta6a cewa rabi kwabo biyar aka sai mata wannan sarqa. A zamanin da ta yi aurenta na farko shekaru hamsin da suka wuce.
.
Rabi tayi tagumi da ta kalli wadannan abubuwa dake kama da duwatsun gilashi, ta tuno in har a shekaru hamsin da suka wuce za a sayi wani abu kwabo biyar. To ynx kuwa babu shakka zasu kai naira dubu biyar. Duk da kudin da rabi take samu, ta san dubu biyar zasu yi mata amfani, tunda waye zai ce baya son qaruwa indai ba na duka bane? Indai har ta kwashe wadannan abubuwa dake daukar idanu tunda sanyin safiya, indai zata kaisu gari yau din nan a sami wanda zai sayesu dubu biyar to tabbas ita kakarta ta yanke saqa. Bama sai ta sayi nono ba." tana iya cin kwalliyarta ta dauki qwaryarta kawai babu komai a ciki, tayi kamar zata je tallar nonon, to amma 'yan tsillar duwatsu masu qyalqyali zata je gari ta yi, ba nono zata je talla ba."
.
Rabi ta yanke shawarar kwashe wadannan dunqulallun abubuwa. Ta matso da bokitinta na roba kusa dasu, ta fara daukarsu daya bayan daya tana saka su a cikin bokitinta, har sai da ta kwashe su baki daya, sannan ta tashi ta dauki bokitin da hannu daya ta juya ta kama hanyar komawa gida can rugarsu dake a bayan tsaunin.
.
Rabi ta gangara ta sauka daga saman tsaunin tudun kudi ta juya baya riqe da bokitinta na roba, tana dauke da abinda bata san darajarsu ba, kuma bata da tarihin komene. Abin da rabi bata sani ba shi ne, wadannan abubuwa da ta tsinta ba duwatsun wasa bane, ma'adanai ne da gwamnatin tarayya da na jiha suke neman inda suke ruwa a jallo. Sannan Kuma mutane da yawa dake a wurare daba-daban suke ta shan wahala, wasu kuma suka rasa rayukansu a dalilin wadannan abubuwa da ta xubasu a bokitinta ta tafi dasu gida, ba tare da wani tsoro ko fargaba ba."
.
.
.
*** *** ***
.
.
.
Babi na goma
.
Kwamishinan 'yansanda na jiha c.p Jibo yana tsaye a faffadan falon dake hade da tsararren ofishinsa, tare da sauran Jami'an tsaro hudu dake riqe da shiyyoyi hudu na jiha, dake a qarqashinsa, su duka ofisoshin hudu suna a tsaye suma cikin ladabi da girmamawa, suna sauraren maganar da Kwamishinan yake fada masu, bayan ya kirasu a lkc guda sun hallara a ofishin nasa, minti goma da suka gabata.
.
A.c. Tanko Dan asabe yana daya daga cikinsu, wanda a shiyyarsa ne aka samu ta'adin da 6arayi suka yi, wadanda suka sace Nalamma, a hannun Jami'an tsaro, suka gudu dashi har ynx bko sama ko qasa ba a san inda suka nufa dashi ba." sauran jam tsaro uku dake a sauran shiyyoyin sun hada da A.c Alamisiya Damina, A.c Ibrahim Sani, da kuma A.c Bako waziri.
.
Kwamishina jibo ya sake kaiwa ya komo ranshi a 6ace, ya tsaya a gabansu ya ce dasu cikin muryar da yake yiwa masu laifi barazana shekara da shekaru ya ce dasu.
.
"dolene ku gano mana wadannan masu laifi a cikin gaggawa. Ina so ku tabbatar kun hanasu dora hannu akan wadannan ma'adanai, wadanda suke neman bayanin inda Nalamma ya kaisu ya 6oye. Ba lallai bane mu sake samun Nalamma a raye ba a halin ynx. Me yiwuwa su kashe shi bayan sun gama jin sirrin da suke nema a wajen sa. Don haka ynx ba Nalamma muke nema ba, wadannan 6arayi muke nema. Ku shiga duk inda suke ku nemo su kafin su je inda wadannan gwala-gwalai suke. Ina so ku kamo mani su a raye in gansu."
.
Duka manyan Jami'an tsaron hudu dake sauraren sa suka amsa cikin girmamawa. Ac tanko dan asabe ya ce da shugabansu.
.
"zamu tabbatar mun gano inda suke, duk inda suka shiga a jihar nan..ll amma muna buqatar tallafin jiragen sama na bincike masu saukar ungulu, sbd ta nan ne kawai zamu samu damar tura yaranmu kowanne lungu ta sama su gano mana mafakar wadannan 6arayin da suka sace NalammA suka 6oyeshi."
.
Kwamishina jibo ya ce.
.
"za a samar da jiragen a yau din nan. Ku je ku shirya yadd zaku rarraba yaran su shiga ko'ina. Ina son lallai ku kamo mana wadannan masu laifin. Bana son su rigamu dora hannu akan wadannan ma'adanai. Ku je ku yi shiri, ni zan je inga gwamna da safiyar nan domin mu tattauna akan wannan matsalar. nnayi masa alqawarin zamu kamo 6arayin da suka sace Nalamma mu cajesu su bayyana mana abin da Nalamma ya fada masu don a je inda dukiyar take a ginota."
.
Jami'an tsaron hudu suka sake amsawa cikin girmamawa, kwamishina jibo ya sallamesu suka nufi motocinsu, xuwa dakin taron da zasu tsara aikin bincikensu na gaggawa don nemo 6arayin da suka sace Nalamma. Don su hana su xuwa inda gwala-gwalan suke.
.
Anyi haka da awa biyar Kwamishinan ya nemo qarin kayan aiki daga sufeto janar din 'yansanda na qasa. Jiragen sama...
.
.
Lp=35}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 35
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Anyi haka da awa biyar Kwamishinan ya nemo qarin kayan aiki daga sufeto janar din 'yansanda na qasa. Jirage uku masu saukar ungulu suka diro a jihar ba tare da wani 6ata lkc ba, Jami'an tsaron da suka qware wajen binciken sama suka fara shawagi a sararin samaniya suna bin qauyuku da lardina da Kuma cikin daji suna nazarin duk wani wuri ko wata ma6oya wacce basu yarda da ita ba."
.
A lkcn da Jami'an tsaron suke ta wannan rangadi a jirage masu saukar ungulu, rabi 'yar fulani ta shirya xuwa kasuwa, ta fito daga dakinta ta ci kwalliya da leshi mai ruwan ganye, ta raba gashin kanta uku, ta daureshi a kowanne 6angare. Ta dauki qwaryar nononta wacce ta sha zane radau, kwatankwacin zanen dake a fuskarta wanda yake dara-dara.
.
Rabi ta dubi farfajiyar rigarsu ta fara hango mijinta iro a kwance a gindin wata bahauwar bbishiyar labadiyar da yake jinya a qarqashin inuwar da take barbazarwa a rigar tasu Kullum kafin rana ta koma yamma, inuwar ta goce a zo a daukeshi a canza masa wata inuwar.
.
Rabi 'yar fulani ta dauke kanta daga kallon yanqwanannen mutumin da take baqin cikin dangantashi a matsayin mijinta. Yana ta barci fuskarshi biyu-biyu da qasumba, jikinsa a dabaibaye da tsummokara babu kowa a wajjensa, qanensa masu zama Suna taimaka masa a halin ynx sun tafi kiwo. Mahaifiyarsa Kuma ta tafi debo ruwa, mahaifin iro kuwa dama ba zaune yake ba, sai yayi wata da watanni a kudu bai dawo gida ba."
.
Rabi 'yar fulani ta wuce mijinta iro a kwance bata sake waiwayar inda yake ba, dama ba ta shi take yi ba." ta fice daga rigar ta dauki hanyar da ta doshi wani qarramin rafi da suke hayewa su sami babur ya kaisu gari.
.
A dai-dai lkcn da rabi take tafiyane a cikin dajin, jiragen dake bincike suna neman Nalamma da 6arayin da suka saceshi, suka wuce daya bayan daya a sararin samaniya.
.
Rabi ta daga kai ta kalleesu, suka wuce a guje basu kula da ita ba." kamar yadda itama bata san wadannan jiragen na mene ne ba, da kuma dalilin shigowarsu cikin dajin kamar tsuntsaye Suna kaiwa da komowa ba.
.
To amma abin da Jami'an tsaron dake a cikin jiragen basu sani ba shi ne, wannan kyakkyawar 'yar fulani wacce take ta tafiya tana sauri zata gari tallar nono, babu komai a cikin qwaryar da ta dorawa kanta, sai gwala-gwalan da kowa yake neman inda suke ruwa a jallo. Basu san cewar rabi 'yar fulani dubu biyar kawai take so ta je gari wani ya bata ta bashi wadann ma'adanai ba."
.
Da ace wadannan Jami'an tsaro sun san abin da wannan 'yar fulani ta xubo a cikin qwaryar nononta, da sun rage gudu sun juyo baya, sun sauka sun taryeta.
.
Jiragen suka tafi suna ta shawaginsu su kadai a qololuwar saman dajin. A yayin da rabi 'yar fulani ta tafi tana ta sauri xuwa gari, don ta samu wanda zai taimaketa ya bata koda dubu biyar ne, ta sayar masa da wadannan abubuwa masu qyalqyali wadanda bata san komene ba."
.
.
.
*** ***
.
"shigo cikin gida Hauwa. Ba abin da zai sameki nan gidanmu ne, kada ki ji tsoro, zo mu je in kai ki falo."
.
Sadi qare-garke ya shaidawa Hauwa cikin xumudi, da yaga tana shakkar bin sa su shiga cikin gidan. To amma a xuciyarta bashi take jin tsoro ba, tunda dai ya daina nunata da bindigar dake a hannunsa. Maganar da ya fada mata cewar suna da wani Tsohon mara lfy sunansa Nalamma shi ne abin da ya kada mata hantar cikinta, fiye da komai.
.
A ina ta san wannan sunan? Ba shi bane Tsohon nan da ya bata labarin dukiyar da ya sata ya 6oye ta je tare da nura aljan zasu gino ta ba daxun? Babu shakka ya ce da ita sunansa Nalamma. to in haka ne ynx me ya hadashi da wannan mutumin da yazo wajenta da bindiga? Ba daxun nan ta barshi tare da Jami'an tsaro ba asibiti? Hauwa ta ji tsoro ya kamata. Sadi ya ce da ita. Tsohon bashi da lfy. Me sukayi masa? Wanne hali Nalamma ya ke ciki?
.
Sadi ya sake katsewa Hauwa tunani ya jagoranceta ya na cewa da ita.
.
"babu abin da zai sameki a nan gidan Hauwa. Ki taimakemu ki shigo ki kula mana da wannan mara lfy namu. Tun daxu yake ta suma yana farfadowa, mu bamu san abin da zamu yi masa ba, ku ne likitoci, wannan aikinku ne, shigo ki taimaka mana."
.
Da Hauwa ta ji haka ne ta yi sauri ta bi sadi qare-garke xuwa cikin falon. Nalamma yana ta suma? me suka yi masa yake ta suma? Anya kuwa wadann mutanen ba 6arayi bane, suka je suka satoshi don yayi masu bayanin inda ya 6oye dukiyar da ya bata labari daxu a asibiti?
.
Da shigarsu ta ganshi kwance a qasa kusa da fitila, dan firit dashi sanye da kodadfun kayansa na gidan yari, idanunsa a rufe ko qwaqqwaran numfashi baya iya yi. Babu shakka Nalamma ne, Tsohon da har abada ba zata ta6a mancewa dashi ba a rayuwarta.
.
Hauwa ta ji tausayin Tsohon ya kamata, sbd da ganinsa zaka fahimci yana cikin wahala sosai, sai da Hauwa ta ji motsi a gefenta, sannan ta mayar da hankalinta akan sauran abubuwan dake a cikin falon. Sai a lkcn ne tayi ido biyu da shago, wanda yake zaune akan kujerra yana ta zaro idanu shi kadai, kamar sabon mahaukaci, jajayen idanun Shago da suka harareta ya san ta ja baya tana niyyar komawa waje. Sadi wanda ya tsaya a bayanta tun sanda suka shigo ya ce da ita.
.
"kada ki ji tsoronsa tare muke aiki, yarona ne sunansa Shago. Babu abin da zai yi maki, ke dai ki yi aikinki kawai' duba mana Tsohon nan ki gani zai rayu kuwa?
.
Hauwa ta durqusa jikinta a sanyaye ta sake duban Nalamma yana a kwance sharkaf bai san a inda kanshi yake ba." akwai alamar kumbburin duka a wani sashi na jikinshi da kuma fuskarshi, ba haka ta ga Nalamma ba daxu. Babu shakka rayuwar Tsohon tana cikin uquba. Da hauwa ta tuna cewar, idan har wadann mutane suka san itama ta na da masaniya akan wannan 6oyayyiyar dukiya, itama abin da zai faru da ita kenan, sai ta ji cikinta ya duri ruwa. To amma indai akan wadann gwala-gwalain ne ake ta azabtar da wannan Tsohon, me zai hana ba zata fada masu gsky inda suke ba, su je su dauka su rabu dashi? Babu shakka abin da zata yi kenan, zata fada masu su je su dauka, don su rabu da Nalamma itama ta huta da wannan masifa haka nan."
.
Da sadi ya ga Hauwa tana ta kallon na Nalamma tana tunani sai ya matso kusa da ita, shima ya rage tsawo ya tambayeta.
.
"baki ce komai ba, me kike ganin ya dace a yi masa? Za a yi masa allura ne ko kuwa magani za a nemo masa?"
.
Hauwa ta yi ajiyar xuciya kafin ta ce wani abu ne, Shago dake a zaune yana zaro idanuwa ya dako mata tsawa.
.
"ba ke oga yake yiwa magana bane, ko baki jin hausa ne?"
.
Hauwa ta dabirce saura kadan ta fadi, don kuwa muryar Shago ta fado dodon kunnenta ne a yayin da mutum zai jiidan qatuwar bishiya ta fadi qasa. Sadi ya waiga inda Shago yake ya ce dashi a fusace.
.
"wa yace ka tsorata ta' an ce ne kayi mata magana? Tashi ka shiga daki kada ka fito sai na nemeka, sakarai, wawa, wanda baya jin magana."
.
Shago ya tashi yana qunqunai hannunshi riqe da guntuwar bindiga tsirara, ya shiga dakin farko a cikin dakuna biyu dake a falon. Duk abin da yake faruwa Hauwa shi ta qurawa idanu tana tsammanin zai iya aukowa kanta a kowanne lkc, idan tsautsayin hakan ya xo. Sadi yayi mata murmushi don ya kwantar mata da hankali da yaga ta tsorata sosai da Shago. Ya ce da ita.
.
"ki yi haquri Hauwa haka yake, yaro ne ba hankali ya cika ba." mu dawo kan maganar baba ya kike ganin za a yi masa ynxn?"
.
Hauwa ta numfashi ta ce da sadi, muryarta a tsorace.
.
"kamata ya yi a kaishi asibiti a can ne za a ganesh duk abin da yake damunsa, a san irin taimakon da za a yi masa."
.
Sadi ya dan 6ata ranshi ya ce da Hauwa.
.
"a'A bamu son asibiti a nan muke son muyi komai, mu gama. Ina so tun ynx ki san cewar zamanmu a nan sirri ne, ke kanki muna buqatar ki iya bakinki bamu son ki yi magana da kowa. Zamu biyaki ki tsaya a nan ki riqa jinyar baba har sai ya warke. Duk abin da kike buqata na kayan aiki da magunguna da allurai ki rubuta mana zan aiki Shago ya je gari ya sayo maki ya kawo. A nan muke so muyi jinyar baba har ya warke ba tare da kowa ya sani ba." ina fatan kin fahimcci abin da muke so?"
.
Hauwa ta gyda kanta cikin xullumi. Babu shakk wadann mutane biyu 6arayi ne, kuma xuwa asibiti suka yi suka sace Nalamma suka xo dashi wannan gidan suna yi masa azaba don ya fadi masu a inda ya 6oye gwala-gwalai
.
Sadi ya sake cewa da ita.
.
"ynx kin ga dare yana qara yi ba 6ata lkc zamuyi ba, rubuta mana magungunan da kike so a nemowa baba.
.
.
Lp=36}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 37
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"ynx kin ga dare yana qara yi, ba 6ata lkc zamu yi ba, rubuta mana magungunan da kike so a nemowa baba. Da kayan aikin da kike buqata a je a kawo maki su ki fara yi masa aiki."
.
Hauwa ta ce dashi cikin biyayya.
.
"to a samu biro da takarda in rubuta magungunan."
.
A lkcn ne sadi ya tashi ya nufi inda qofar bandaki take a kusurwar falon, da xuwanshi ya daki qofar da hannu daya ya ce.
.
"nazo wajen ku mutanen bandaki, ku bude ina son ganin ku."
.
Hauwa ta qura masa idanu kamar wanda yake magana da aljanu. Yana gama magana ta ji an bude qofar an janyeta ciki. Wani baqin mutum ya fara leqowa yana wurga idanuwa a tsorace. Duk da sanyi-sanyin da ake yi akwai qyallin zufa a fuskarsa. Xuwa can sai wata mata ita ma ta leqo tana toshe hancinta da hannu daya, fuskarta tayi sharkaf da xufa da hawayen kuka. Sun yi tsammanin afuwa 6arayin zasu yi masu su tafi su bar masu gidansu, har zasu fito daga cikin bandakin, sai sadi ya dakatar dasu ya ce.
.
"takarda muke so da biro, a ina kuke ajiye su?"
.
Mai gidan ya ce dashi cikin kwantar da murya.
.
"bari in zo in dauko maka ranka ya dade, akwai su."
.
Sadi ya daka masa tsawa wacce ta fi ta Shago ban tsoro.
.
"wa ya ce ka ffito? Na ce ka fada mani inda suke in je in dauko."
.
Mai gidan ya ce.
.
"ka yi haquri, suna nan akan teburi a dakin da muke kwana kusa da litattafan karatunmu."
.
Sadi ya ce dasu.
.
"to ku koma ciki ku rufe kanku. Daxu naji anyi tari ban san waye yayi ba a cikinku. Idan na sake jin tari ku duka zaku dandana kudarku. Ba a yi min rashin da'a, idan ina gida, abin da nasa mutum yayi shi kadai nake so in ga yayi."
.
Mai gidan ya ce.
.
"kayi haquri ranka ya dade, ba zamu qara ba."
.
Suka koma cikin bandakin matar tana ta kuka, ta toshe hanccinta da qarfi tana jin tsoron shaqar iska. Suka tura qofar suka sake rufewa, sadi ya dawo ba tare da ya yiwa Hauwa magana ba, ya shiga dakin da Shago ya shiga. Hauwa ta ji kamar ta tashi ta fita da gudu. To amma kuma ta san yin hakan ba qaramin hadari bane a gareta, tunda kafin tayi nisa wadann azzaluman mutanen zasu bi ta su kamota. Kuma ko ma ba don haka ba a halin ynx ba zata iya guduwa ta bar Nalamma a cikin wannan halin ba. Tsohon yayi mata halacci ya taimaketa ya so ta da arziqi. Ya fada mata abin da bai ta6a fadawa kowa ba a duniya tsawon shekaru talatin, abin da kawai zata yi ita ma ta saka masa shi ne, ta tserar dashi daga hannun wadann miyaggun mutane.
.
Hauwa tana cikin wannan tunanin ne sadi ya fito daga dakin da sauri, riqe da fararen takarda da biro yana fara'a. Da xuwanshi ya miqa mata su ya ce.
.
"ga abin rubutun an samu hauwa, rubuta ynxn nan yarona Shago zai je ya siyo maki magungunan dukansu."
.
Hauwa ta amshi biro da takardar ta dora akan dardumar dake malale a falon, ta fara rubutawa hannunta yana rawa sbd tsoron dake tattare da ita.
.
Ta sake duban Nalamma ta kama hannunsa ta ji babu qarfi kamar gawa. Ta sake rubuta wani abu a jikin takardar sadi yana a tsaye yana kallonta. Hauwa ta dubi qafar Nalamma ta ga kamar a karye take ta tambayeshi
.
"me ya sameshi a wannan qafar naga kamar a karye take?"
.
Sadi ya ce da ita.
.
"daxu qafar ta karye da suka yi aiki shi da yarona Shago. LaIfin Shago ne, sai da sace ya bishi a hankali kada yayi wauta. To amma shima baba yana da laifi ya cika taurin kai ne da yawa, ki dubashi sosai Hauwa' ko me kike buqata na magani ki rubuta, za a nemo maki."
.
Hauwa tayi ajiyar xuciya ta rubuta magunguna kimanin guda goma da allurai, a lkcn ne tayi mamakin kowanne irin aiki sadi yake nufi sun yi shi da Nalamma,
Wanda har qafarsa ta karye. Duk da bata san ko aikin mene ba, bata tambayeshi yayi mata qarin bayani ba."
.
Ta gama rubuta abubuwan da take so, ta miqa masa takardar ya amsa, a lkcn ne ya kwadawa Shago kira ya fito daga cikin dakin, riqe da guntuwar taba a hannunsa tana hayaqi. Sadi ya miqawa Shago takardar ya ce dashi...?wannan
.
"wannan takardar magani ce, Hauwa ta rubuta, ka je gari ka samu kyamis su hada maka su ka kawo mana, kada ka 6ata mana lkc Shago, magungunan da za a ba babba ne."
.
Shago ya amshi takardar ya linketa da sauri ya sa a aljihunsa, baya buqatar yaga rubutun dake a jiki, don kuwa ba layinsa bane. Sadi ya juya 6angaren da Hauwa take durqushe kusa da Nalamma ya tambayeta.
.
"nawa kudin zasu kama duka Hauwa?"
.
Ta ce a sanyaye.
.
"ba zasu wuce dubu uku ba."
.
Sadi ya ciro kudi tari guda daga nasa aljihun ya qirgo dubu uku ya baiwa Shago ya qara da cewa.
.
"ka je da motarsu tana nan a waje, ka tambayesu makullin motar su baka, kada kayi wasan Shago, kayi sauri daga bamu da isasshen lkc."
.
Shago ya amshi kudin cikin damuwa, sbd har ynx bai gama hucewa ba da fadan da oga sadi ya yi masa ba daxu. Shago ya je qofar bandakin inda masu gidan suke kulle, ya hauri qofar ya ce dasu a fusace.
.
"ku bude."
.
Mai gidan ya bude, shi kadai ya leqo a wannan lkcn fuskarshi cike da tsoro. Shago ya daka masa tsawa.
.
"ina mabudin motarku yake, muna buqata."
.
Mutumin yayi saurin laluba aljihunsa hannunsa na rawa. Ya ciro mabudin ya miqawa Shago, shi Kuma Shago ya warta ya juya inda sadi da Hauwa suke. Kafin ya fice ne sadi ya ce dashi...?wannan
.
"idan an samu canji kada ka manta da tsarabata shago. Bani da sauran abar nan, kazo min da ita."
.
Shago ya daga murya cikin damuwa ya ce.
.
"na ji oga."
.
Ya fice ba tare da ya juyo ya kalleshi ba." sai da Shago ya tayar da mota a can waje ya bata wuta sannan sadi qare-garke ya juyo ya ce da Hauwa.
.
"fushi yake yi da ni, don na hanshi ya yi maki aiki."
.
Hauwa ta kalli sadi cikin fargaba ta tambayeshi.
.
"wane irin aiki yake so ya yi min?"
.
Sadi yayi dariya mugunta, Hauwa ta qura masa ido a kidime, ya ce da ita.
.
"tun ynx ya kamata ki san qa'idar zama damu Hauwa. Idan muka aqunci mutum, ko kuma idan tsautsayi ya jawo mutum ya zo inda muke ya baquncemu, dolene mu yi masa barka da xuwa. Hanyar yin hakan kuwa shi ne, qafafuwan mutum muke karyawa don kada ya gudu ya tona mana asiri. Ke kanki qa'ida abin da ya kamata muyi maki kenan, tun sanda kika fado hannunmu. Da Shago yaga kin zo ban bashi wannan umarnin ba,ya shine yake ta wannan fushin da ni. Amma kada ki damu zai haqura Hauwa.
.
Hauwa ta dafe qirjinta a tsorace da ta ji xuciyarta tana bugawa da sauri kamar zata fado waje. Ynxn kamar ta gano irin aikin da Nalamma yayi da wadann shu'uman mutanen biyu. A lkcn ne Hauwa ta fara addu'ar a xuciyarta tana neman tsari da mugun aikin da sadi yake bata labarin suna yi tare da mutane.
.
.
.
*** *** **u
.
.
Babi na sha daya
.
Bayan Shago ya zo da magungunan da Hauwa ta rubuta tana buqata, sai suka bata wuri suka koma gefe guda. A daren Hauwa ta nannade duk wani rauni dake a jikin Nalamma da bandeji. Ta yi masa allurar kashe zafi da na zazza6i.
.
Shago ya tsaya tare da ita a falo yana gadinta, a lkc guda kuma yana lura da bandaki inda baqin bature yake kulle tare da matarsa. Kafin ya zauna sai da ya je yayi masu gargadin mu kwana lfy, ya tabbatar masu da cewar zasu iya yunqurin fitowa su ce zasu gudu idan dare yayi nisa. Shago ya ce ba zai hanasu fitowa ba, idan sun buqaci hakan, amma kada su zargi harsashin bindigarsa idan suka ji ya ratsa qasusuwan qafufunsu.
.
A haka suka kwana su da gidansu, amma a cikin bandaki a maqure. Sadi a matsayinsa na oga shi kadai ya shiga daki ya kwanta a lafiyayyen gado. Hauwa tana tare da Nalamma a qasa, bayan ta gama yi masa taimakon da zata iya. Sai ta zauna tayi tagumi tana tunanin Kuma abin da zai faru idan garinsu ya waye. Tana so ta dan rintsa barci ko ba yawa, sbd tsabar gajiyar dake tattare da ko'ina a jikinta, to amma ba zata iya yin barci ba,ya matuqar tana kallon Shago zaune a kusa da ita yana wasa da bindigarsa.
.
.
Ta san shago mugune, bata yarda dashi ba tana jin tsoron kada ta saki jiki aiki ya taso akanta. A xuciya irin ta Shago yana iya gwada harbinta a qafa ko a goshi ya ce wasa yake yi mata. Ta san kuma ko kasheta suka yi bai wuce su dauki gawarta su jefa a cikin kogin dake a kusa dasu ba."
.
.
Lp=38 ﹑
}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 38
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ta san kuma ko kashe ta suka yi bai wuce su dauki gawarta su jefata a cikin makeken kogin dake a kusa dasu ba." shi yasa ta qeqashe ta qi rintsawa. A haka suka yi kwanan zaune shi zuru ita zuru. Sai dai ya kashe taba ya sake kunna wata, ita kuma tana sake duba jikin tsoho Nalamma tana sauraren lkcn da zai farfado ya qara bude idonsa.
.
Da safe bayan gari ya dan fara washewa ne Hauwa ta roqi Shago, ta ce tana so zata yi sallah. Ya barta ta dauki ruwa a cikin firji wanda masu gidan suke sha, ta kewaya waje ta yi alwala ta dawo cikin falon, Shago bai yi yunqurin rakata duk inda

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment