Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in kaishi dakin kawu Mu'azzam su kwana tare, bani daya cikin makullan da ya baki na dakinsa, in bude in kaishi can ya kwanta ya huta, agajiye yake tun safe yake zirga-zirga a makaranta."
.
Haj. Maimuna ta ce
.
"Mu'azzam ya yi tafiya daxun nan, kin yi sa'a tunda bashi nan, amma da yana nan ba zan iya baki mabudin dakinsa ki kai masa baqo ba, kin san halinshi da baqin ran tsiya. Yana iya xuwa a gaban baqonki ya ce zai yi qwallo da ke. Amma tunda bashi nan bari in dauko maki makullin dakin ki tabbatar kuma kin share masa dakinsa yadda kika same shi. Don in ya dawo ya ga 6ann to ni 'yar kallo ce."
.
Haj. Maimuna ta bude murfin daya daga cikin kwanonin (rose) din dake jere akan teburin gilashin da take kwalliya dasu a cikin dakin. Ta dauko wani farin mabudi ta miqa wa larai. A lkcn ne larai ta saki ranta da taga ta fita kunyar najib masoyinta.
.
Larai ta fito daga cikin dakin mahaifiyarta fuskarta cike da farin ciki. Ta ce da shi.
.
Ka yi haquri najib na barka anan kai kadai ko?"
.
Najib wanda yayi tagumi ya yi saurin dawowa hayyacinsa ya yi wa larai murmushi
.
"ba komai."
.
Larai ta ce dashi...?wannan
.
"zo mu je in kaika daki ka huta, yau ka sha wahala."
.
Najib ya yi dariya.
.
"mun sha wahala tare zaki ce."
.
Suka fito daga dakin tare, larai ta jagoranceshi suka nufi 6angaren tsakiya inda sashin Mu'azzam ya ke. Larai ta sa mabudin ta bude qofar dakin Mu'azzamnajib wanda ke tsaye a bayanta ya ce.
.
"ba dai dakin baba kika kawoni ba ko larai?"
.
Ta juyo suka hada ido ta harareshi cikin wasa.
.
"baba ne zai zo nan ya zauna? Dakin wani qanin mahaifiyata ne da yake zaune a nan gidan. Ka saki jikka najib, ya yi tafiya ba yau zai dawo ba."
.
.
Lp=54}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 54
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"Baba ne zai zo nan ya zauna? Dakin wani qanin mahaifiyata ne da yake zaune a gidan mu. Ka saki jikinka Najib' ya yi tafiya ba yau zai dawo ba."
.
Suka shiga cikin dakin, Najib wanda a zahiri agajiye yake ti6us, ya fada kan daya cikin kujerun dake a falon Mu'azzam ya kishingida. Larai tayi dariya ta ce.
.
"Dama na san agajiye kake, na san kawaici kawai kake yi tun daxu, bari in je in dauko maka jakarka a cikin mota, ka kwanta kayi barci xuwa nan da a kira sallar magriba. Nima barcin nake ji, xuwa zanyi in kwanta, anjima da daddare idan mun huta sai in zo muyi hirar da zamu yi, kaga lkcn shima Baba ya dawo sai ku gaisa.
.
Najib wanda ya gitta qafafuwansa a kan doguwar kujerar ya ce da ita.
.
"shi kenan ki je Larai, idan na huta zan kira ki anjiman."
.
Larai ta fita ta barshi a dakin ta gangara qasa ta fita waje, ta je inda motarta take ta bude but ta dauko doguwar jakar Najib ta matafiya. Ta riqo jakar da hannu daya, ta shiga gidan, ta koma dakin Mu'azzam inda ta sauki najib baqonta. Da xuwanta ta same shi har ya rufe idanunshi yana gyangyadi, don kada ta takura masa da doggon surutu, sai ta ajiye jakar a qasa kusa dashi tayi saurin ficewa ta dan jawo masa qofa.
.
Najib wanda ya ji shigowarta da ficewarta ya bude idonsa ya tashi zaune ya jawo jakar tashi kusa dashi ya zage zif ya budeta. Kayan dake jikinsa sun yi masa nauyi ba zai iya yin barci dasu ba." Najib ya ciro wani qaramin wandonsa na farin yadi, da kuma singiletinsa, ya cire kayan jikinsa ya saka kayan barcin, kafin ya koma ya kwanta ne, ya dubi dakin sosai a karo na farko, hotunan da ya gani na 'yanmatan duniya a liqe a kowanne bango a falon, ya sa shi saurin fahimtar kowanene ke da dakin matashi ne dan zamani.
.
Najib ya rufe jakarsa ya fara nazarin inda zai ajiyeta a cikin dakin. Baya son ya ajiyeta a qasa, sbd tsautsayin 6arewar ruwa, kada ya jiqa masa kaya, duk da yake dai akwai dardumar a tsakar dakin, yafi son ya sagale jakarsa a jikin qusa.
.
Najib ya duba ko'ina a falon bai ga inda wata qusa mai girma take a jikin bango ba, wacce zata iya dauke nauyin jakarsa. Ya dauki jakarsa ya tashi daga inda yake zaune, ya je bakin qofar dakin barcin dake a cikin falon, inda aka gitta katako a saman qofar, wajen dora takalma ko wasu qananun abubuwa.
.
Najib ya fito da mariqin jakar ya daga ta ya sagale ta a jikin katakon ta zauna daram. To amma kuma tun kafin ya juyo ya sake kwantawwa akan doguwar kujerar, kamar jira take yi ya sagaleta a kan katakon, jakar ta wazgo tare da katakon suka fado qasa ricaaa!
.
Najib yayi turus a tsaye a cikin takaici, yana kallon 6annar da yayi a dakin daga xuwanshi, ya dubi inda katakon ya su6uto a jikin bangon, yaga wani gizo-gizo wanda sai yau asirinsa ya tonu a zaman da ya yi na tsawon lkc a dakin. Inda katakon yake kafin ya fado babu fenti, Najib ya fahimci Wataqila tunda aka gina gidan katakon yake anan, bai ta6a fadowa ba sai yau a dalilinsa, daga xuwansa.
.
Najib ya ji ya damu sosai, an san tsautsayin a ko'ina, kuma an san dai mutum mai hankali ba zai yi 6arna da gangan ba." to amma duk da haka shi ba zai so Larai masoyiyarsa ta dawo dakin anjima ta iske wannan ta'adin da yayi masu ba."
.
Gashi ta ce dakin qanin mahaifiyarta ne, Wataqila ko ta nuna abin bai dameta ba, shi idan ya dawo zai iya nuna 6acin ransa. Don haka ya zama wajibi ya gyara masa katakon ya mayar dashi inda yake a goshin qofar.
.
Najib ya yanke shawarar ya fita waje ya nemo kafinta ya zo da kayan aiki ya gyara katakon. A kusa da gidan Alh. Madugu dab da kan kwanar da suka shigo daxu da suka zo, najib yaga wasu kafintoci dake aiki a cikin wata baranda, su ya kamata ya je ya samu su bashi mutum daya ya zo ya gyara katakon kada larai ta zo ta gani.
.
.
Najib ya haqura da yin barcin, ya cire kayan da ya saka, ya dauko baqar rigarsa (T-shirt) da shudin wandon da ya cire daxu ya sake mayar dasu jikinsa. Ya dauke jakarsa wacce ta fadi gefe kusa da katakon ya kaita kusurwar dakin inda babu komai, ya ajiyeta. Ya fita daga cikin dakin ya jawo qofar ba tare da ya kulleta da makulli ba, tunda dai ba dadewa zai yi ba. Ya gangaro daga saman benen ya sauko qasa, ya fito daga cikin tanqasheshen gidan, ya kama hanya xuwa wajen kafintoci. Wadanda suke maqwabtaka da gidan Alh. Madugu.
.
.
.
*** *** **
.
.
Babi na sha-biyar
.
Najib ya yiwa kafitocin hudu sallama, wadanda suka mayar da hankulansu akan aikin wadansu manyan kujeru baji ba gani. Mutum biyu suna shirya soso a cikin lallausan yadin tintin, daya yana buga qusa, a yayin da wani dan siririn a cikinsu yake goge katako.
.
Mutanen suka amsa sallamar, suka dago kansu a lkc guda suka kalli Najib, mutum daya kawai ya tsaya da aikin ya taso ya matso inda najib yake tsaye. Sauran kafintocin suka ci gaba da aikin da suke yi, hakan ya ganar da Najib cewar sune yaran mutumin da ya taso ya tarbeshi a halin ynxn.
.
Najib shima ya matsa gaba, suka hadu da gajeren mutumin wanda yayi busu-busu da dusar katako a ko'ina a jikinsa. Najib ya miqa masa hannu ba wani tsantsani, mutumin ganin yadda jikinsa yake. Ya ji nauyin miqawa Najib hannu su gaisa, to amma da yaga saurayin ya bashi girma bai nuna wata qyama ba, sai ya bashi hannun suka gaisa. Najib ya ce.
.
"Ya aiki?"
.
Gajeren kafintan fuskarsa cike da fara'a wacce ta tona asirin manya-manyan haqoransa guda biyu na roba dake sama ya ce da Najib
.
"Aiki mun godewa Allah."
.
Bayan sun gama gaisawa na Najib ya ce da shi.
.
"Dama ina da wani dan aiki ne, shi ne nake so a yi mani ynx a gida. Wani katako dake saman qofa ya fado, shine nake so mayar mani dashi...?wannan aikin ba wani mai yawa bane."
.
Gajeren kafintan ya rage fara'ar dake a fuskarsa ya ce.
.
"Gashi kuma kazo ka same mu muna aiki Malam....ka yi haquri sai xuwa gobe da safe kafin mu fara aiki sai a samu wani ya je ya gyara maka."
.
Najib ya ce da mutumin.
.
"Indai da sarari a taimaka ynx muje a gyara mani, ba nesa bane, nan ne gidan Alh. Madugu."
.
Fadar sunan hamshaqin mutumin da ya yi ne, ya sa sauran kafintocin uku suka dago kawunansu a lkc guda suka dubi saurayin.
.
Ubangidansu wanda yake magana da Najib, da ya ji ya ambaci Alh. Madugu sai ya dawo da fara'arsa ya ce.
.
"Ba matsala bari in hada ka da yaro daya ku je ya gyara maka tunda ba nisa, ashe nan ne gidan Honarabil?"
.
Najib bai yi mamaki ba da saurin amincewar kafintan, sbd a yadda ya fahimci unguwar, duk fadin yankin ba wani mutum kamar Alh. Madugu mahaifin Larai. Kafintan ya yi wa daya daga cikin yaransa dake aikin kujera magana.
.
"Ashiru zo ku je tare dashi ka gyara masa katakon, ka dauki qusa inci biyar da maqwarqwasa, ka yi sauri don Allah ka gama ka dawo, kaga muna da sauran aiki ga yamma ta yi."
.
A lkc ne siririn yaron dan kimanin shekara sha-shida ya taso a cikin mutanen uku dake aikin, ya amsa cikin girmamawa. Ya ce.
.
"An gama Oga."
.
Najib ya dubi saurayin da aka hada su dashi, duk da yake shi baqo ne ba a layin yake ba, amma yana da tabbacin wannan yaron mai suna Ashiru yana fama da ciwon sikila ko kuma nimoniya. Yaron a bushe yake kamar mutumin kara. Gashi da rafkeken kai kamar tulu, qafafuwanshi sirara sun tamuqe gasu a bushe sun yi fari qwal. A kallo daya da Najib ya yiwa saurayin, nan take ya tuno da cutar tamowa.
.
Ashiru ya za6o wasu qusoshi a qaramin kwano. Ya dauki maqwarqwasar ya kalli Najib cikin girmamawa. Ya ce.
.
"mu je mai gida."
.
Najib ya yiwa ubangidansu gdy, suka yi sallama ya shiga gaba Ashiru yana biye dashi a baya. Suka tafi kamar bajumin sa da ramammen dan akuya.
.
.
Lp=55.}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 55
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ashiru ya bi shi a baya suka tafi kamar bajimin sa da ramammen dan akuya. Da yake kuma Ashiru wani kodadden farin yadi yasa, rigar tayi masa yawa, wandon kuma ya fashe a guiwa. Idan iska tana kada kayan sai mutum ya rantse tashi zai yi sama.
.
Najib bai juyo ya dubi Ashiru ba, har suka kai gidan Alh. Madugu. A kallon farko da Najib ya yiwa yaron ya ji sam bai yi masa ba a rai. Musamman da ya dubi wandon Ashiru kafinta ya ganshi a dake irin na matasan Ustazai. Najib baya ga maciji da duk wani mutum wanda baya son cashewa. Ya sha fada da wani abokinsa a gida wanda yake koyarwa a makarantar islamiyya, don kawai abokin nasa yana yi masa nasiha yana fada masa qabli da ba'adi.
.
Najib ya jagoranci Ashiru suka hau benen, har xuwa dakin da Larai ta saukeshi. Da xuwansu ya bude qofar ta bude, ya ce da saurayin dake dan yin baya-baya.
.
"shigo mana, ga katakon nan da ya fado qasa."
.
Suka shiga dakin, Najib ya kauce ya ba Ashiru wuri, wanda da shigarsa ya dauki katakon da hannu biyu yana duba ta inda ya ciro. Ganin yadda hannuwansa ke rawa, alamar katakon yayi masa nauyin riqewa, sai Najib ya matso don ya taimaka masa. Ya ce.
.
"Bari in kama maka mu mayar dashi sai ka buga qusar."
.
Najib ya sa hannu daya ya amshi katakon daga hannun Ashiru, ya saita shi a goshin qofar daidai inda ya ciro. Ya ce dashi...
.
"Buga qusar kawai na dafe maka."
.
Ashiru ya ciro qusa daya a cikin aljihun rigarsa, ya daidaita inda zai kafata a jikin katakon, ya daga mabugin ya doka shi a kan qusar kau! Sautin buga qusar ya amsa kuwwa a cikin dakin, sannan a lkc guda bangwayen dakin suka amsa kuwwa.
.
A sanadiyyar haka ne wani sabon siminti da ba a dade da shafa shi ba a jikin bangon ya yanko ya fado qasa curi guda. Akwai alamar laima a cikinshi. Najib da Ashiru kafinta suka dawo da hankalinsu inda lakar simintin ya fado. A nan take suka fahimci daga qarqashin faskeken hoton zuqeqiyar matar dake manne a jikin bangon ya fado.
.
Najib ya sake jinjinawa wani sabon takaicin ya kamashi. Ana wata ga wata. Suna kan gyara wata 6annar gashi kuma an sake yin wata. Ya saki katakon da yake dafe dashi, ya barshi a hannun Ashiru kafinta, wanda ya ya dafeshi da qarfi. Najib ya xo inda hotton yake, yasa hannu ya ciro shi a jikin qaramar qusar dake riqe dashi.
.
Da ciro hoton ya ga qaramin ramin da ya bayyana a jikin bangon dakin. Najib ya tsaya cikin mamaki yana kallon ta'adin da suka yiwa bangon, qaramin ramin wanda yake cushe da lakar simintin, bai yi kama da abin da Najib ya ke tsammani ba." domin kuwa wannan simintin da ya fado ba na ainahin ginin gidan bane, wannan sabon rami ne da aka gina shi ba da jimawa ba a jikin bangon. Don kuwa akwai laima da danshi-danshin ruwa a zagaye da qaramar qofar ramin dake a jikin bangon.
.
Najib ya mance da al'amarin katakon da zasu gyara shi da Ashiru kafinta. ya ajiye hoton da ya ciro wanda ya lulli6e qofar ramin. Ya sa hannunsa ya ta6a sabon simintin da aka shafa wanda du-du-du, ba zai wuce awa uku xuwa hudu ba.
.
Ashiru wanda shima da yaga abin da ya faru, sai ya sauko da katakon daga goshin qofar ya ajiye shi a qasa, ya matso kusa da bangon. Yana mamakin yadda daga kawai an buga qusa a jikinshi sai fadowa kamar bangon gilashi. Ashiru ya ce.
.
"mai gida amma wannan ina tsammanin sabon ginine aka yi shi ba da jimawa ba." naga akwai laima a jikinshi."
.
Najib ya numfasa ya ce.
.
"to nima abin da nake gani kenan, tunda gashi babu fenti a wajen. Ina ganin yau akayi wannan aikin, nima baqo ne a gidan ba dakina bane."
.
Ashiru ya numfasa bai sake cewa komai ba, ya yi gum da bakinsa yana kallon qofar ramin a jikin bangon, sai ka ce gyambo a lafiyayyar qafar da aka shafe ta da mai. Najib ya rasa inda zai sa kanshi a sakamakon wannan sabon ta'adi da ya faru. Da ace ya san haka tsautsayi zai ratsa da bai nemi kafinta ya gyara katakon da ya fado qasa ba." a qalla dai gara a zo a samu fadowar katakon a dakin fiye da wannan gagarumar 6arnar ta fashewar bango."
.
Najib ya sake tura hannunsa cikin ramin, ragowar sabon simintin da aka rufe ramin dashi wanda ya dan fara bushewa, ya sake yankowa ya fado qasa, ramin ya qara fadi ya zama wagege, najib ya ji tsoro ya fara kamashi. Bai ga dalilin da zai sa a gina wannan ramin a jikin bango a cikin tsararren daki irin wannan ba, indai ba wani muhimmin abu aka ajiye a ciki ba."
.
Wannan zargin da Najib yayi a xuciyarsa ne, yasa ya cire duk wani tsoro da kokwanto, ya sake sa hannu ya 6an6are sauran simintin da aka zagaye bakin ramin wanda yayi saura bai fado ba. Ramin ya fito sosai, bulon da aka fasa ya bayyana a fili. Najib ya sa hannu a ciki ya laluba can qasa, a lkcn ne ya ji ya shafo wata leda da wadansu abubuwa kamar duwatsu-duwatsu.
.
Bai tsaya canza tunani ba, ya kamo ledar da yatsun hannunsa ya fara jawo ta waje, Najib ya fito da ledar daga cikin ramin, ya ji ta da nauyi jigum' da kuma qulalan wadansu abubuwa a cikin ledar, kamar zasu fasa ta su fado qasa.
.
Najib ya mance kwata-kwata yana tare da saurayin kafintan a cikin dakin, idanunsa sun rufe da qosawa yaga ko mene ne a cikin ledar, wanda ya tabbatar sbd muhimmancinsa aka fasa bangon dakin aka 6oyeshi a ciki, aka shafe shi da siminti.
.
Najib ya ajiye qunshin ledar a tsakar dakin, ya durqusa ya kunce ledar cikin sauri, ya budeta ya ci karo da abubuwan da suke ciki. Ba Najib ba hatta shi kanshi Ashiru kafinta dake tsaye a baya yana kallon abin mamakin, sai da ya dauke numfashinsa da ya qyalla ido akan abin dake qyalqyali a cikin ledar. Najib ya farke ledar, abubuwan suka watse akan daddumar dake malale a tsakar falon, suka yi daidai suna sheqi kamar gilasai masu rai.
.
Najib ya ji jinin jikinsa yayi tsayuwar wucin gadi sbd kaduwar da ya yi. Ya dade yana jin labarin ma'adanai masu daraja a duniya irin su gwal, azurfa dasu tagulla wadanda kullum ake yayata darajarsu a duniya. Ko yaya mutum ya samu daya daga cikin su to ya zama attajiri. Najib ya tabbtar wadann ma'adanai da aka 6hoye a cikin ledar, suna da matuqar daraja, kuma gagarumar dukiya ce mai zaman kanta, wadanda indai mutum ya mallakesu to yayi adabo da talauci indai na duniya ne.
.
A zaman da Najib ya yi tun haihuwarsa a birnin tarayya Abuja, yaga abubuwa bala-adadin wadanda suka sa shi ya dage karatu don kawai ya ggirma shima ya zama mai kudi. Kullum yana ganin motoci na tashin hankali da qerarrun gidaje na alfarma. Don haka yake da burin ya zama miloniya don shima ya shigo gari a fantama dashi.
.
Najib ya sake kallon wannan ajiyar da ya qwaqulo a bangon dakin. Ya tabbatar I'dan har ya mallakesu, shi kenan ya huta, ba ma sai yayi wahalar tsayawa yin wani karatun jami'a ba." ga dukiya ta samu, wane karatu kuma zai tsaya ya yi ynx? Babu shakka wannan tsintuwar da yayi sun zama nasa.
.
To amma kuma tun kafin Najib ya gama wannan tunanin sai Ashiru kafinta dake tsaye a bayansa shima yana kallon abin da yake sheqi a gaban Najib, ya ce da shi.
.
"ina ganin wannan ajiyar ta Alhaji ce ya yi a nan dakin. Ya kamata ka gaggauta mayar dasu ramin ka gyara kada ya gani ya yi fada."
.
Najib ya waiga baya a fusace ya dubi siririn saurayin. Ya mance dashi gabaki daya. Tabbas ya kamata ya sallami wanna yaron, in yaso bayan tafiyarshi sai ya yi tunanin da ya dace.
.
.
Lp=56
}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 56
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ya mance dashi gabakidaya. Kamata ya yi ya sallami Ashiru idan ya tafi sai ya yi tunanin sa a tsanake, don ya gano hanyar da zai bi ya kwashe wannan dukiyar ba tare da kowa ya ganshi ba."
.
Najib ya miqe tsaye, ya sa hannunsa a aljihu cikin sauri ya ciro dari biyu ya miqawa siririn kafintan ya ce da shi.
.
"ga wannan ka tafi kawai abinka, zan gyara katakon da kaina... Na gode."
.
Saurayin ya amshi kudin cikin zargi da rashin yarda qarara a fuskarsa. Najib ya yi zaton yaron zai dauki kayan aikinsa ya yi tafiyarsa. Maimakon haka sai yaga ya ja ya tsaya yana kallon sa. Najib ya kausasa muryarsa cikin barazana ya ce da siririn saurayin.
.
"me kuma ka tsaya jira a nan? Ba na sallameka ba?" ko ba ka gaji da kallon dakin ba ne.?"
.
Ashiru kafinta ya duqa ya dauki maqwarqwasarsa jikinsa a sanyaye babu kuzari, ya sake kai ganin sa inda Najib ya xube wadann gwala-gwalai masu ban sha'awa akan dadduma. Najib ya juya masa baya don kada ya kalli fuskarsa ya fahimci abin da yake shirin yi. Gashi yayi su6ul da baka ya fadiwa Ashiru cewar shi baqo ne a gidan, dolene yaron ya nuna bai yarda dashi ba a game da wannan tsintuwa da yayi a dakin.
.
A lkcn da Najib yake sauraron ya ji saurayin ya fice daga dakin ne, sai ya ji motsin shi a kusa dashi. Najib ya juya cikin fushi da kaduwa suka hada ido shi da Ashiru, yaron ya ce dashi kai tsaye.
.
"Mai gida wannan abin fa da ka ciro a bango ba kayanka ba ne, bai kamata ka dauki kayan da ba naka ba, haramun ne yin sata. Ka ji tsoron Allah ka kaiwa Alhaji, wata qila shi ya ajiye su."
.
Najib ya ji gaban sa ya fadi. Ya dubi dan tsigiggin yaron da ke tsaye a gabansa yana fada masa wannan maganar. Babu shakka akwai matsala a tattare da niyyarsa ta mallakar wannan tsintuwa da ya yi. A lkcn Najib ya tabbatarwa kansa indai yana so ya mallaki wadannan ma'adanai laqadan, ya zama dole ya yi wani abu akan Ashiru kafinta.
.
Me zai yi masa don kada ya tona masa asiri?
.
Ku nemi GOBE JAR KASA (4)
.
Shafi'u Dauda Giwa
.
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki.
Jinjina ga mai gidan littafi wanda ya wallafa ya kuma sadaukar ga masoyanshi, madallah da jumurinku na saurarena ahalin "TASKAR GIDAN LITTAFI"
Na so ace labarin soyayya ne tabbas da na sadaukar dashi ga Aminina kuma abokin aikina wato Abu Basmerh tare da sahibarsa Nafeesert.
.
Iliyas ke busharantarku da samun ci gaban labarin Gobe JAR kasa (4) a wannan yammacin bisa yardar mai duka.}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 57
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Babi na sha-shida.
.
"Mu je ki fito mana da ajiyarmu da kika sace a saman tsauni, sauri muke yi tun daxu muke jiranki a nan Rabi."
.
Sadi qare-garke wanda yake fadiwa Rabi 'yar fulani wannan maganar cikin barazana ya sake matsowa kusa da ita yana gyara zaman bindigar dake a hannunsa, wacce take kallon kyakkyawar matar kamar yadda maciji yake ritsa mai qarar kwana a cikin daki.
.
Rabi ta dabirce ta rasa inda zata sa kanta, ba ta san lkcn da ta saki qwaryar nonon dake a hannunta ba, qwaryar ta fadi qasa ta tsage biyu kowanne 6angaren ya nufi inda yake so. To amma duk da tsabar sanin darajar qwarya irin na 'yar fulani' wannan matashiyar mace ba ta ko waiwaya ta kalli qwaryar ba." in ana ta rai wa yake ta kaya? Rabi ta bude baki tana kyarma ta ce da su."
.
"me na daukar maku? Ba ni ba ce..ban daukar maku komai ba, ba ni ba ce..."
.
Har Shago ya taso ya wuce Sadi zai kifar da Rabi don ta fara suma ta san abin bana wasa ba ne da gske ake yi. Sai Sadi ya sa hannu ya jawo shi baya ya ce da shi.
.
"Da sauran lkc Shago. Ka rabu da ita muyi magana sosai ta fahimce mu tukuna, kullum ina fada maka fadan magana yafi fadan hannu muhimmanci. Da magana ake samun nasarar yaqi ba da hannu ba."
.
Shago ya koma baya yana mayar da numfashinsa, Kullum yana jin dadin darasin da Oga Sadi yake koya masa akan dabarun aiki, sbd ya san wata rana dole ne ya yayeshi ya fara cin gashin kansa. Amma a wannan karon bai yi murna da wannan darasin na yau ba, sbd a yadda suka wuni a daji basu ci komai ba tsawon wannan ranar suna jiran Rabi 'yar fulani ta dawo daga talla ta basu gwala-gwalansu da ta kwashe, wannan gardamar da ta yi ta ce ba ita ce ba, ta zo wa Shago ne a matsayin yadda mutum zai jinjinawa idan aka watsa masa tafasasshen ruwa a tsakiyar kansa.
.
Sadi shi kan shi wannan maganar da Rabi ta fada ta tayar masa da hankali sosai, don kuwa rabi ita ce tsaninsa a halin ynxn, babu inda yake da tabbacin zai cimma burinsa ya samo wannan dukiya sai a wajenta, tunda ya tabbatar ita ce ta kwashe su, sawun takalminta ya riga ya bayyanar da ita. Ya yi ajiyar xuciya sannan ya sake kallon Rabi 'yar fulani wacce take neman hanyar sheqawa aguje zata nufi rugarsu. Ya ce da ita a sanyaye kamar yadda Malamin kwaleji yake ba malalacin dalibi shawara.
.
"Rabi ina so ki natsu ki fahimcemu da kyau. Na san baki sanmu ba, kuma baki ta6a ganinmu ba, shi yasa kike son ki yi mana jayayya

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment