Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan abin da muke tambayarki. Ya kamata ki yi la'akari da yadda kai tsaye muka gane ke kika kwashe mana gwala-gwalanmu a saman tsaunin can. Kin san tunda har muka gane ki muka biyo ki ba zaki iya tsere mana ba, ko ina kika shiga a duniyar nan zamu bi ki mu kamo ki, ki dawo hannunmu."
.
Rabi ta sake rikicewa tana sauraren mutumin, tsoron gwangwamemiyar muryarsa da kuma bindigar da yake yi mata barazana da su, su suke sa hanjin cikinta yamutsewa waje guda. Sadi ya ci gaba da yi mata nasiha. Ya na cewa.
.
"idan baki fito mana da wadann gwala-gwalan ba zaki jawo wa mutane da yawa masifa Rabi. Mun san inda iyayenki suke, mun yi bincike a kanki, zamu bi su har rugarsu mu yanke masu hannuwa da qafafuwa mu barsu a haka ki riqa kallonsu. Sannan kuma suma qannenki da yayyenki ba zama barsu haka nan ba, su duka zamu farfasa masu idanuwa su zama makafi su riqa xuwa Bara kasuwanni. Ya kike ganin wannan mugun al'amari akanki Rabi? Kin amince a dalilinki a mayar da danginki su dukansu su zama guragu musakai, wadansu makafi' ke kadai zaki riqa kulawa dasu?"
.
Rabi ta furgice da jin wannan baqin labari. bata san lkcn da ta fara kuka ba tana yiwa Sadi magiya tana cewa.
.
"Don Allah ka yi haquri kada ka ta6a mani 'yan uwana da iyayena, me suka yi maka? Na ji ni na daukar maku kayanku ban san naku bane. Ku yi haquri..."
.
.
Zan tsaya a nan sbd lkcn Sallah
.
.
Lp=58}~~~~~~{ gobe jar kasa (4) }~~~~~~{
Page 57
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"Na ji ni na daukar maku kayanku ban san naku ba ne ku yi haquri..."
.
Sadi ya saki ranshi cikin sauri ya sake matsowa dab da Rabi 'yar fulani kamar zai share mata hawaye, ya ce da ita.
.
"Ba komai ki daina kuka, ki dauke mu amatsayin 'yan uwanki Rabi. Wannan magana babu wanda ya san da ita daga mu sai ke, sirri ne a tsakanin mu da ke. Ki daina daga murya kina yin kuka kada wani ya ji muryarki a rugarku ya zo abin ya shafe shi. Ynx tunda kin ce ke kika kwashe mana ajiyarmu, ina kika kai su mu je ki dauko mana ki bamu mu tafi, babu abin da zamu yi maki."
.
Tsoron dake rikita Rabi ya fara raguwa da taga yadda Sadi yake tarairayarta, kamar qanwarsa. Ta rage shassheqar kukan da take yi ta ce da shi
.
"Basu a wajena, suna can gari na kaiwa wani mai sayar da 'yan kunne, shi ya yi mani wayau ya ce zai saye su."
.
Sadi ya sake murtuke fuskarsa ya ji kamar ya sa hannu ya kifar da Rabi 'yar fulani, to amma sbd ya san idan ya yi haka ya karya qa'idar aiki, sai ya nuna mata kamar maganar bata dame shi ba." ya tambayeta.
.
"wa ki ka sayar ma wa Rabi? Kuma milyan nawa ya baki?"
.
Rabi ta sunkuyar da kanta qasa ta ce da Sadi.
.
"Dubu daya kawai ya bani, suna can a wajensa, ni ban san amfaninsu ba, ce min yayi wai ba a yayin su ynx. Taimakona ya yi ya saya."
.
Sadi ya yi murmushin qeta, ya sake hadiye fushinsa ya ce da Rabi.
.
"Ba komai, mu ma zamu taimakeshi mu saya a wajensa tunda an daina yayin gwal a duniya. Ynx bin ki zamu yi qafarki qafarmu Rabi, ki kaimu inda yake ki hada mu dashi, yin hakan shi zai sa ki wanke kanki da 'yan uwanki daga cikin wannan rigimar. Kin ga yamma ta yi gari ya fara yin duhu, ki yi sauri ga motarmu can a bakin hanya mu daukeki mu koma gari, muna so mu ga ko wane ne kin mance baki fada mana sunanshi ba?"
.
Rabi ta share hawayen da ya xubo mata, sannan ta ce da Sadi.
.
"Sunansa Mu'azzam, shagonsa yana nan a kasuwa yana sayar da 'yan kunne da sarqoqi, ynx ko mun je ba zamu same shi ba, lkcn tashinsa ya yi."
.
Sadi ya ce da 'yar fulanin.
.
"Ba sai lallai a kasuwa zamu gana dashi ba Rabi. Ko a gidansa ne zamu bi shi har uwar daka, mu da kayanmu kuma tsoron me zamu ji? Ke dai ba ruwanki mu tafi ki kaimu inda yake, ba ruwanki da abin da zai faru tsakaninmu da shi.
.
Rabi ta daga kai ta hada ido da Shago wanda ya koma baya yana tare idanu shi kadai, ta yi saurin dauke ganinta daga kanshi sbd kallon Shago idan yana irin wannan fushin kamar kallon mugun zakin da yunwa ta ciyo ne a daji. A karo na farko Rabi ta hada idanunta da Hauwa ita ma tana gefe a raku6e kamar an tsamota a cikin kogi, ko qwaqqwaran motsi bata yi tana jiran a bata nata umarnin.
.
"ku yi haquri in je rugarmu in dawo, ku jira ni a nan zan dawo ynxn nan mu tafi kada a ga shiru ban dawo ba ba a san inda na tsaya ba a tafi nema na."
.
Sadi ya sake fito da bindigarsa fili ya nunawa Rabi sbd yaga alamar ta fara mancewa da bindigar a hannunsa, shi ya sa ta fara rage ladabi, tana magana da 'yanci ba wani tsoro. Da taga bindigar ne ladabinta yayi saurin dawowa tare da tsoron da ta ji tun farko. Sadi ya ce da ita.
.
"wuce mu tafi idan kin dawo gidan anjima kya yi masu bayanin inda kika je."
.
Canjin da Rabi ta gani murya da fuskar Sadi, yasa ta yi gum da bakinta bata sake neman afuwa ba." tayi saurin wucewa ta kama hanyar komawa inda ta fito. Da Sadi yaga ta bi umarnin cikin sauri ne, sai ya yi murmushi ya ce da ita.
.
"Ban gabatar maki da mu ba gashi zamu yi aiki tare, Ni suna na Oga Sadi, amma wasu suna ce mani qare-garke." .
.
Sadi ya yi dariya sannan ya ce da 'yar fulani.
.
"Kada ki yi mamakin jin ana kirana da wannan sunan, akwai dalili, a da sanada nayi tashe a wajen sata, nasha in kore garke komin yawansa a cikin dare in tafi da shanu, kuma har abada ba wanda ya isa ya gano inda muka dosa ni da shanun."
.
Rabi ta dago kai a tsorace ta sake kallon Sadi da ta ji ashe ma har shanu yake sata, ba a riqe bindiga kawai ya tsaya ba." sadi ya rage fara'ar da yake yi ya nuna yaronsa ya ce.
.
"wannan sunansa Shagon sadi. Tsohon dan dambe ne, bai ta6a kai duka da hannu ya tashi a banza ba, ya kai mutum sun fi dari lahira, don haka ki yi hankali dashi, kada ki yadda ya matso da hannunsa kusa da ke."
.
Da Shago ya ji yau an yi sa'a Sadi ya yi abin arziqi ya yabeshi a gaban mace, sai ya sake murtuke fuska yana muzurai. Sadi ya nuna Hauwa ya ce da Rabi.
.
"Earn ita kuma likitarmu ce sunanta Hauwa, itama jiya muka dauketa aiki baquwa ce, ina fatan zaku zama qawaye ke da ita muyi aiki cikin jin dadi tare."
.
Hauwa da Rabi suka sake kallon juna, kowacce fuskarta cike da xullumi kamar wadanda aka kamo a wajen yaqi. Rabi tayi saurin matsawa kusa da mace 'yar uwarta Hauwa. Da farko da ta ganta tare dasu tayi zaton itama Hauwa muguwa ce, to amma a wannan gabatarwar da Sadi ya yi ya fadi mata sunan kowa da aikin da kowa ya qware akanshi sai Rabi ta fahimci babu shakka itama Hauwa kan dole take tare da wadann azzaluman mutanen.
.
Da Sadi yaga Rabi ta je inda Hauwa take ne sun hada kansu sai shima ya ware yaronsa Shago gefe guda suka juya baya, sadi ya ce da Shago yana fara'a.
.
"Me na ce maka? Dama na ce fada da baki yafi fadan hannu riba. Idan ka bugi mutum da zafin dukan ya wuce zai manta da kai. Amma idan magana ta shiga xuciya ta zauna, har mutum ya mutu ba zai daina jin zafin ta ba." da magana ake sarrafa mutum yayi abin da ake so Shago. Ba da duka ba, in kaga an sa hannu to tsanani ya kai tsanani ne, ina fatan zaka riqa gane hanyar aiki daga ynx."
.
Shago ya gyada kai babu alamar girmamawa a fuskarshi. Ra'ayinsa ya sha banban da na Oga Sadi a halin ynx. Shago ya yi amann da duka da horo wajen samun nasara a aiki, a yayin da Oga Sadi yayi amanna da yaudara da makirci. Duk wanda ya samu nasarar aiki a cikinsu qa'ida ne yayi wa daya burga a matsayinsa na wanda ya san yadd ake yin aiki.
.
Bayan Sadi da Shago sun gama qus-qus din su ne, kafin su juyo inda matan biyu suke, sai Shago ya tambayi shugaban nasa.
.
"ynx ina muka nufa daga nan Oga?"
.
Sadi ya 6ata rai cikin dan lkc qanqani, yadda tambayeshi.
.
"Me ka ce ne Shago? Ashe duk maganar da Rabi take fada ba ka ji ba? Zamu tafi tare da ita cikin gari ne ta kaimu wajen wannan 6arawon da ya yi mata wayau ya qwace gwala-gwalan, idan muka ganshi ya dauko ya bamu shi kenan aiki ya qare sai mu sallame su su dukansu, kowa ya tafi inda yake so."
.
Shago ya tambayi Sadi cikin kamata.
.
"to amma Oga idan bamu yi katarin ganin shi wanda muke nema ba ynx, ina zamu 6oye kanmu har xuwa lkcn da zai fado hannunmu ba tare da asirinmu ya tonu ba?"
.
Sadi ya dafa kafadar Shago ya yi murmushi.
.
"naga alamar ka fara gajiya da aikin nan Shago. Kada ka damu, wajen da zamu 6oye kanmu da ma'aikatanmu ba wani abu bane mai wahala, bari dai mu shiga garin mu gani."
.
Shago ya tattare mummunar fuskarsa a sakamakon iskar da ta buso mai dauke da sanyin fadamu, ko kuma albishir din samun ruwan sama a daren da yake tunkarowa. Sadi wanda shima iskar ta shige shi ya ce da Shago.
.
"Je ka ka dauko mana motarmu ka zo da ita bakin kadarkon can ynx zamu taho ni da su Hauwa likita....
.
.
Lp=58'}~~~~~~{ gobe jar kasa (4) }~~~~~~{
Page 59
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"Je ka dauko mana motarmu ka zo da ita bakin kadarkon can ynxn nan zamu taho ni da su Hauwa likita. Ka duba mana Baba ka gani yana nan a raye ko kuwa ya gaji ya wuce."
.
Shago ya juya ya tafi ya bar Sadi yana dariya shi kadai, ya ci gaba da magana kamar mahaukaci babu wanda yake saurarensa ya na cewa.
.
"Baba akwai taurin rai, yana nan har ynx a raye. Sa'a, kawai yake nema ya karta rashin mutunci, wannan tsohon bala'i ne shima, dole ne muyi a hankali dashi."
.
Ya taho yana dariya yana magana ya zo inda Hauwa da rabi suke tsaye suna magana cikin tsoro da fargaba, a lkcn Shago yayi nisa, ya kusa xuwa inda suka ajiye motar a cikin wasu dogayen keraren bagyazama da suka bushe. Da Sadi ya zo wajen su Hauwa da Rabi 'yar fulani ne ya ga sun tsaya da maganar da suke yi, kowacce ta quro masa idanu kamar suna shawarar taruwa su dokeshi su gudu. Sadi ya hade fuskarsa ya daina fara'a ya ce dasu.
.
"Tun ynx har kun fara hada kai kenan, me kuke shawartawa ke da sabuwar qawarki Hauwa?"
.
Matan biyu suka yi shiru babu wacce ta tanka masa. Sadi ya ciro bindigarsa ya nuna masu ita a fusace ya ce dasu.
.
"Bana son munafunci a aikina. Zan iya jure komai amma bana tausayawa munafuki. Idan wata a cikinku ta sake ta munafunceni, ko ta tona mani asiri ina mai tabbatar maku da cewa ba zata kai labari ba." ko'ina kuka shiga sai na biku na halaka ku."
.
A lkcn ne Hauwa ta tsorata sbd da ita yakE. Ta ce da shi.
.
"ba wani abu fa muka ce ba. Ta tambayeni inda nake ne ni kuma na fada mata, nima na tambayeta rugarsu ta fada min, shine kazo ka same mu muna maganar.
.
Sadi ya dan saki ranshi ya ce da Hauwa
.
"kawai ku dauka cewar aikine ya hadaku da an gama kowa zai ware, ba cewa nayi ku zama qawaye har abada ba." mu a rayuwa irin tamu bamu son sabo da juna. Aikin da ya hadamu kawai muke ba muhimmanci. na san ku duka baku sona a halin ynxn, to wannan ba ,atsala ba ce a gare ni, in dai zaku yi min aikin da nake so in samu nasara. Ba kya sona Hauwa likita, nima bana sonki. Shago baya sona nima bana sonshi. Wani lkcn sai in ji kamar in harbeshi in huta. Sannan mu dukanmu Baba Nalamma baya sonmu. To amma ya zamu yi tunda aiki ya hadamu? Mu dukanmu mu kawar da qiyayya ko soyayyar dake tsakanin mu Hauwa. Da zarar mun gama aikin nan kowa zai kama gabansa, ba ruwan kowa da kowa, ina fatan kuna gane?"
.
Hauwa ta gyada kanta, kafin Sadi ya sake yin wata maganar ne, suka ji an yi masu hon sauri biyu daga nesa.
.
"Ga Shago can ya dauko motar ya zagayo, ku zo mu tafi mu same shi."
.
Hauwa da Rabi 'yar fulani suka jera kamar ya da qanwa, Sadi ya tasa su suka tafi inda Shago yake jiransu a cikin motar. Bayan sun tsallake kadarkon ne, sai suka same shi a cikin farar motar ya dafa sitiyari da hannu daya, yana shafa idonsa da daya hannun yana dubawa ko zai ga rauni. Nalamma yana a kujerar baya a yanqwane kamar jiqaqqen mayafi, ya jingina da kujera yana kallon saman motar ko qyaftawa ba ya yi. Sadi ya tambayi Shago
.
"me ya samu idon naka Shago, ko qwarin nan ne suka fada maka? Nima ynx wani ya fada mani a cikin ido."
.
Shago ya yi shiru a fusace, xuwa can ya ce da Sadi.
.
"Baba ne ya kusa makanta ni, na ciro shi daga cikin but zan saka shi a cikin mota shine ya sa hannu ya dokeni a idona."
.
Shago ya juyo suka kalli juna shi da Sadi, idonsa ya kumbura daga sama, ya mayar da kamannin fuskar irin ta dorinar ruwa. Sadi ya qyalqyace da dariya ya koma 6angaren da Nalamma yake a bayan motar ya ce dashi...?wannan
.
"kai baba, ashe har ynxn kana nan da wannan zafin ran naka tun na jiya? Ai na zaci ynx mun zama 'yan uwanka tunda muna tare."
.
Nalamma ya ci gaba da kallon rufin motar ko motsawa bai yi ba, balle ya juyo inda Sadi yake.
.
Sadi ya lura da wani siririn jini da yake gangarowa daga hancin Tsohon yana diga akan rigarsa. Bai tambayi Tsohon ko jinin mene ba, sbd ya san duk duniya ba wanda zai doki Shago a ido, ba tare da shima yasa hannu ya mayar da martani ba." sa'a Nalamma ya samu Shago yana xullumin kada ya yi masa lahani da yawa, kada Sadi ya hau shi da zagi in banda haka da tuni Nalamma ya zamu taRihi.
.
Sadi ya miqe daga duqawar da ya yi ya ce.
.
"Ya kamata mu zauna lfy da junanmu. Bai kamata muna fada ba. Ynx na gama yiwa hau likita nasiha sbd na fahimci itama tana yunqurin kawo mana hari. Idan kowa ya yi haquri gobe a irin wannan lkcn duk mun rabu, kowa ya kama gabansa."
.
Da yake wannan maganar da kowa Sadi yake. Ba wanda ya ce dashi uffan. Ya ce da su Hauwa su shiga mota su zauna a baya tare da Nalamma. Hauwa da Rabbi 'yar fulani suka shiga, Nalamma ya matsa gefe guda ya manne da bangon motar ba tare da ya kalli matan biyu ba." sadi ya zagaya ya shiga gaba ya kalli Shago ya ga fuskarsa tayi duhu, idan fuskar azzalumin yaron ta koma haka zai iya kai mai qarar kwana qiyama a kowanne lkc. Sadi ya ce dashi cikin muryar umarni.
.
"Ja mu je yamma tana qara yi Shago, kada ka mance kasuwa zamu je shagon Mu'azzam mai sayar da sarqoqi."
.
Shago ya fusgi motar ransa a 6ace ya dauki hanyar da ta keta ta cikin dajin. Ya fara sheqa gudu kamar zasu bar qasar. Wani bafullatani wanda ya 6oye a nesa a bayan wata bishiya bayan motar ta tafi ya fito cikin mamakin ganin Rabi ta shiga mota ta bi mutanen. Abin da kawai ya raya a xuciyarsa shine taqadaran mutanen da Rabi take mu'amula dasu a gari ne suka biyota har dajin suka dauketa zasu tafi da ita gari suyi holewarsu. Wannan ba abin mamaki ba ne domin kuwa duk fadin lardin daga yara har manya kowa ya san Rabi 'yar shar holiya ce.
.
.
.
*** *** **
.
.
Najib da Ashiru kafinta suka yi shiru a tsaye suna kallon-kallo. Siririn yaron ya sake cewa.
.
"Sata ba abu ne mai kyau ba malam, idan ka yi haquri wata rana zaka samu naka ka ci halal dinka, amma idan ka dauki dukiyar wani ba abin da ka qulla a rayuwarka, sai dai ka yi ta gamuwa da asara da tashin hankali kullum."
.
Najib ya ja dogon numfashi ya kawar da kansa daga inda Ashiru yake, a lkc guda ya fara tunanin hanyar da zai bi ya sasanta da wannan yaron. Ya san zai iya korarsa da qarfi ya fita ya bar masa dakin, to amma idan ya fita ba zai rufa masa asiri ba. Da ya fita zai nemi mutane ya fada masu abin da yake faruwa, idan maganar ta dawo gida xuwa kunnen Larai ko mahaifinta Alh. Madugu, tabbas asirinsa ya gama tonuwa. Don haka ya zama dole ya yi wani abu akan wannan shashashan yaron Ashiru kafinta.
.
Najib ya ce da shi.
.
"Ynx abin da nake so da kai yaro, tunda kaga wannan al'amarin zan baka kudi kayi shiru da bakin ka, ina da kudi ynx haka, idan basu yi maka ba, zan daukeka muje banki in ciro ko nawa kake so in baka kayi shiru da bakinka kada ka fadiwa kowa. Nawa kake so in baka, fadi ko nawa ne....!
.
Tun kafin ya kai qarshe Ashiru ya girgiza kai ya ce.
.
"Ni ba zan amshi kudi a hada baki da ni a cuci wani ba." an sha fada mana a makaranta sata haramunce, kuma alamomin munafuki guda uku ne, hadisi sahihi ya zo dasu, akwai wanda za'a yarda dashi ya yi ha'inci. Kaga kai baqo ne a nan gidan malam, mutanen gidan nan sun yarda da kai ne, har suka baka wannan dakin don ka zauna a ciki, bai kamata ace kai kuma ka ha'incesu ba, wannan alama ce ta munafuki. Abin da yafi kawai shine, ka tattara wadann gwala-gwalan ka shiga ka kai masu ka ce fadowa suka yi a cikin bango."
.
Najib ya ji wani abu yana tokarinsa a cikin xuciyarsa, kamar ana yi masa lugude da ta6arya, nan take ya fara jinjinawa ciwon kai da zazza6i suna kawo masa farmaki.
.
.
Lp=60}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 60
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Take ya fara jin ciwon kai da zazza6i suna kawo masa farmaki. Ta sake juyawa inda gwala-gwalan suke, ya dubesu suna nan a qasa inda ya zubesu a jere irin su daya, kamar yara 'yan makaranta a filin asambile. A yadda ya tabbatar wadanan muhimman ma'adanai suna da daraja a idon duniya, tabbas guda daya kawai ya ishi mutum ya haye tsanin arziqi. To balle ga wadannan sun kai har guda goma. Kuma gasu da girma, an ce gwal ko kamar tsakuwa yake, indai na ainahi ne ba jabu ba, to kadara ce ba 'yar qarama ba, amma wadannan sun kai girman duwatsun ginin kankare, in kuma a qauyene sun kai girman fura.
.
Najib ya canza wani tunani, tunda yaron ya ce baya son kudi to bari kawai ya dauki daya daga cikin gwala-gwalan ya bashi, ya zai yi? Sai yayi haquri da guda tara. Ya duba ya dauko daya a cikinsu ya juyo inda Ashiru kafinta yake ya ce da shi cikin damuwa da hadama.
.
"Ga guda daya kaima ka je ka sayar, wannan kawai ya isheka ka zama attajiri tsawon rayuwarka. Amma kayi hankali kada ka bari wani ya gani, don bana son asirinmu ya tonu."
.
Maimakon yaron ya amsa cikin murna, sai Najib ya ga ya sake xuqewa ya maqe kafadarsa.
.
"Na fada maka ba zan amshi komai ba, bana son komai a cikin wannan dukiyar' ni dai kawai fatana shi ne inga an dauka an kaiwa masu gidan nan kayansu, amma ni bana so."
.
Najib ya ji xuciyarsa ta turniqe shi, ya ji kamar ya shaqo yaron ya maqare shi, a tunanin sa Ashiru ya raina duk abin da ya bashi ne....! Sai ya koma inda gwala-gwalan suke ya qaro guda biyu, ya hadasu da na farko suka yi tozo akan tafukan hannunsa biyu. Ya miqa wa yaron.
.
"Ga su guda uku ne duk naka ne....! Haka dai kake so in baka da yawa, to ga su." ni da na tsinta zan dauki guda bakwai, kai kuma ka dauki guda uku, kowa ya je ya nemi arziqi a cikinmu. Amshi ka yi tafiyarka."
.
Ashiru ya sake girgiza kansa yana kallon Najib da ramammiyar fuskarsa, kamar qashi a cikin leda.
.
"Bana so."
.
Ya sake maimaitawa.
.
"na fada maka nifa bana son ko daya a ciki. Ban ta6a yin sata ba kuma ba zan fara yi ba a wannan duniyar. Idan masu gidan suka dauka suka bani kyauta to wannan zan amsa, na san idan naci halas ne....! Amma ba zan sa hannu in dauki kayan da ba nawa ba."
.
Najib ya ji bayan ciwon kan da yake damunsa, har kuma wata xuwa take qoqarin hudo masa ta baya duk da sanyin da ake yi a garin. Yana ji yana gani ga tsuntuwa ya yi, amma wannan shashashan yaron ya 6ata masa ruwa ba don ya sha ba." me yasa ma wai har ya yi wannan shirmen ya je ya nemo kafinta don ya gyara masa katakon da ya fado? Da ace ya tsaya da kansa ya gyara shi kadai, da babu wanda zai ga wadannan gwala-gwalan, da ynx ya kwashe su ya gudu dasu.
.
To amma kuma anya zai iya yin haquri ya kaiwa iyayen larai masoyiyarsa wannan dukiyar' bayan basu san cewar ya gani ya kwashesu ba?" bai san tun wane lkc wadannan gwala-gwalan suke a 6oye cikin bangon ba." zai iya kwashe su ya gyara simintin bangon, ba tare da kowa ya sani ba sai wani lkcn idan ann zo dubasu za a gane babu su a wajen.
.
Wa zai yi zarginsa ya ce shi ne tunda ba kullum zai riqa xuwa gidan ba?" Wataqila ma lkcn an manta ya ta6a xuwa gidan. Sai dai su zargi wani. Ga ga komai nan cikin sauqi da ace wannan sakaran yaron bai yi masa dungu ba." To mm dolene ya yi iya qoqarinsa, ya sasanta da Ashiru kafinta, tunda dai xuciyarsa ta bushe da hadama da zalamar son ya zama attajiri a dare daya, da kayan da ba nasa ba."
.
Najib ya fahimci hanya mafi sauqi kawai shi ne, ya dauki rabin gwala-gwalan ya ba Ashiru rabi. Idan suka raba daidai biyar-biyar, dolene yaron ya amsa in dai ba qashin 6eran masallaci gareshi ba." Najib ya mayar da gwala-gwalai ukun da ya dauko a cikin 'yan uwansu, ya yi ajiyar xuciya ya ce da Ashiru.
.
"To na yarda mu rabasu biyu daidai wa daida. Ka dauki biyar, ka bar mani biyar, ko ka fara za6ar wadanda ka ke so, sauri nake yi in tafi kada wani ya zo ya ganmu a nan tare da wannan ganimar muga samu muga rashi. Yi sauri ka matso ka kwashi naka, rabonka ne shi yasa na je na kira ka, dama ance rabon kwado baya hawa sama, zo ka dauka ka tafi."
.
Ashiru kafinta ya sake turjewa gefe guda ya ce.
.
"Kana 6atawa kanka lkc ne kawai, na fadi maka ni bana cinye kayan haram, sbd na san cewar idan na zalunci wani mutum naci kayansa, idan bai kamani ba, to Allah yana nan yana jirana, akwai ranar hisabi tana nan xuwa, a ranar bani da qafar guduwa dole ina ji ina gani sai Allah Ya sakawa duk wanda na zalinta a duniya. A lkcn kuma babu dukiyar da na sata, ta qare tun a duniya dolene a aikina na alherin da nayi na samu lada, shi za

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment