Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

buqatar wadannan ma'adanai da ka 6oye su tun shekaru talatin da suka wuce. Kai kadai ka san inda suke duk fadin duniyar nan, muna so ka taimakemu ka fadi mana inda suke baba."
.
Nalamma ya ce da sadi.
.
"kuna #atawa kanku lkc ne yaro, tun daxun ai na fada maku. Ba zan fada maku ba." iyaka dai ku ce zaku kashe ni, to ni bana tsoron mutuwa, ko ynx idan kun so, kuna iya kashe ni, amma ba zan fada maku ba!"
.
Shago yayi sauri ya fita waje ya je ya tsaya a kusa da qofar falon, bashi da qarfin hali da juriyar da zai iya tsayawa a gaban wannan tsohon, yana fadar irin wadannan maganganun, ba tare da yayi masa wani aiki ba, don ya ganar dasu ba a fada masu irin wadannan maganganun a kwana lfy.
.
A can cikin falon sadi ya ci gaba da cewa Tsohon cikin gargadi.
.
"ai yawanci dama ba mutuwa mutane suke tsoro ba baba. Wahala ce abar tsoro, ita kowa yake gudu. Zamu iya zama da kai kayi ta shan wahala, ba tare da ka mutu ba,ya zamu riqa matsarka ne daga lkc xuwa lkc, kafin ka mutu mu da kanmu zamu nemo maka magani ka sake murmurewa, sai ka samu lfy sannan mu ci gaba da aiki. Kana jin zaka iya jurewa da irin wannan zama da zamuyi tare da kai baba?"
.
Tsohon ya ce da sadi qare-garke
.
"a haka na zauna a hannun 'yandoka har nayi shekaru talatin da biyar, don haka yara ne, ba zaku iya tursasani in fadi maku abin da ban yi niyya ba."
.
Da Nalamma ya fadi haka ne, sai sadi ya juya inda shago yake tsaye.
.
.
Lp=31}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 31
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Da ya fadi haka ne sai sadi ya juya inda Shago yake a tsaye, da yaga bai ganshi a cikin falon ba, sai ya tashi ya je ya dafa bakin qofar falon ya leqa waje yaga Shago a tsaye yana kumbura yana sacewa kamar kwado. Sadi ya ce dashi.
.
"Shago baba dai yayi tauri da yawa, ya qi yayi magana mai dadi, dolene sai ka zo kuna yi aiki tare.".
.
Shago wanda dama tuntuni umarnin da yake jira kenan daga wajen ubangidansa, ya ce cikin qosawa.
.
"abin da ya kamata tun farko mu fara yi kenan oga."
.
Ya shigo falon da sauri ya wuce sadi, da xuwanshi ya sa hannu daya ya cakumi dan tsoho Nalamma ya daga shi tsam! Kamar yadda shaho yake tsame dan tsako daga cikin 'yan uwansa yayi sama dashi. Shago ya garzaya da Nalamma daya daga cikin dakunan barcin, da shigarsu ya turo qofar ya kulle da qarfi.
.
Ya kulle qofar kenan sai sadi ya ji Tsohon ya fara wani irin ihu mai cike da azaba. Sadi qare-garke ya matsa kusa da qofar, ya daga murya ya dakawwa Shago tsawa.
.
"kada kayi hauka Shago. Sama-sama zaka yi, bana son rashin hankali kai Shago."
.
To amma sadi qare-garke bai gargadi yaronsa a lkcn da ya dace ba." don kuwa da shigarsu ya karyawa Tsohon qashin qwaurinsa, kamar yadda qaramin yaro yake daukar sillan kara ya karya daga hannu idan zai qera motar wasa.
.
.
.
.
*** *** ***
.
.
Babi na tara.
.
.
Hauwa ta dade tana sheqa gudu a cikin dajin ba tare da ta san inda ta dosa ba." Bayan ta shafe lkc tana faduwa tana tashi, a wata faduwar da tayi ne, sai ta saurara ta kasa tashi, sbd qarfinta ya qare. Bugu da qari kuma qafafuwanta sun galabaita, duk ta ji rauni a dalilin abubuwaan da take takawa masu tsinin dangin duwatsu da itattuwa akan hanyar da take bi....
.
Wannan faduwar da tayi, ta sakankance cewar koda nura ya qariso ba zata iya ta6uka komai ba,ya tsayawa kawai zata yi yazo ya kasheta, ta huta da azabar da take ji. A can cikin qirjinta ji take yi kamar anan hura mata wuta, daqyar take iya shaqar numfashi sbd tsabar gajiyar da tayi.
.
.
Nima haquri zan baku, don kuwa zan tsaya a nan ne, ba don naso ba, zan tsaya ne kawai sbd tsabar uzurin da ya taso mani.
.
.Lp=32
}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 32
.
Daga alqalamiN
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Daqyar take iya shaqar numfashi sbd tsabar gajiyar da tayi.
.
Sai da ta huta ne ta saurara, sannan ta tashi ta zauna a cikin wasu dogayen ciyayi da ta fada koraye shar dasu a cikin hasken farin watan da yayi wa daren kwalliya. Iskar da take dan busawa lkc-lkc ta taimaka mata wajen dawo mata da qarfin jikinta. Hauwa tayi ajiyar xuciya, sai a lkcn ne hankalinta ya fara dawowa jikinta, ta fara tunanin abin da yake faruwa da ita.
.
Shin da gaske nura masoyinta ne yake bin ta zai kasheta?
.
Hauwa ta fara tunanin anya kuwa wannan abin ba mafarki bane? Ta lumshe idanunta tana fatan idan ta bude idanun zata ganta a kwance akan katifarta a cikin dakinta. Sbd ba zai ta6a yiwuwa ba ace nura ne zai yi mata irin wannan butulcin. Bayan duk halaccin da tayi masa a rayuwa. Ta san nura ba wani son ta yake yi ba, to amma dai ta san duk rashin kirkin shi zai yi wahala ace shi ne ya dauki makami yake bin ta zai kasheta? nura ba zai iya yi mata haka ba."
.
To amma inda komai ya razanata ya sake daburta mata tunani shine, da ta bude idanunta a halin ynx bata samu kanta a kwance a kan katifarta tana barci ba." a cikin dajin dai ta sake samun kanta, ita kadai a cikin daren bata san ko a ina take ba." hakan shi yasa ta yarda da abin da xuciyarta bata son ta yarda dashi...
.
Babu shakka da gaske nura ita ya biyo zai kashe.
.
Hauwa ta ji hawaye ya fara taruwa a idanunta. Bata buqatar ta hana kanta kuka a halin ynx, kuma bata buqatar ta sa hannu ta share hawayen da suka fara xubo mata akan fuskarta, dolene tayi kuka mai yawa, sbd ta ci karo da hadarin soyayya da Kuma cin amana da butulci muraran.
.
Nura shine wanda tafi amincewa fiye da kowa a rayuwarta, sbd tsabar son da take yi masa ne ma har ya sa ta qi 6oye labarin da tsoho Nalamma ya fada mata yace kada ta fadiwa kowa. Bata fadiwa ko mahaifiyarta ba, tana rawar jiki ta nemi nura ta fada masa. Sbd alqawarin da ta daukarwa kanta tuntuni, kome ta zama a duniya ba zata ta6a mancewa da nura ba." zata soshi, Kuma zata ci gaba da taimakonsa da duk wani abu da ta samu a tsawon rayuwar ta...."
.
Amma sbd cin amana irin na 'yan adam, yau ga abin da nura ya yi mata. Ynx wannan shine sakamakon duk wahalar da ta sha yi akan wannan saurayin? Wannan shine sakayyar da zai yi mata bisa tsawon lkcn da tayi tana yi masa halacci a kowacce rana?
.
Hauwa ta sunkuyar da kanta, ta ci gaba da rusa kuka cikin 6acin rai da qunan xuciya, to wai me yasa ma ta gudu? Me yasa bata tsaya nura ya kasheta ba,ya don ta huta da ganin wannan baqin cikin rayuwa? Ynx bata buqatar komai a rayuwarta. Ta san har abada ba zata sake yin wani qwaqqwaran farin ciki ba." nura ya tarwatsa mata duk wani jin dadin duniya. Ta san har ta mutu ba zata sake yin soyayya ba."
.
Ba zata qara kula wani namiji ba...koma wane ne, kuma kome zai fada mata. Sbd duka maza basu iya komai ba sai zalunci da cin amanar soyayy. Wannan shine abin da Hauwa ta tabbatarwa da kanta, a daidai wannan lkcn da take zaune a cikin daji cikin daren, daga ita sai tsuntsaye da qwari, wadanda suke gudanar da sha'anin rayuwarsu cike da annashuwa, ba tare da sun san me yake damunta ba."
.
Hauwa ta dade a zaune bata san tsawon lkcn da ta shafe a wajen ba,ya sai daga baya kuma ta fara tunanin tashi ta koma gida. Duk da haka akwai tunanin nura a xuciyarta, ta fara tambayar kanta, me ya faru da nura, wanda ya biyota zai kashe ta? Shin komawa yayi da yaga tayi masa nisa, ba zai iya kamata ba?" ko kuwa dai yayi 6atan hanya ne ya nufi wani wajen a tsammanin san can ta nufa?
.
Tayi mamaki da ta ji duk da halin da ta tsinci kanta na xullumi da razana, amma ta damu da ta san halin da nura yake ciki. Haka kawai Kuma sai ta ji ta fara tunanin wataqila kuma nura ba a cikin hayyacinsa yake ba lkcn da ya biyota zai kasheta. Ta san yana shaye-shaye, babu mamaki a sanda suka zo dajin, yana cikin qwaya ne, don haka komai zai iya yi mata. Amma idan ya dawo hayyacinsa ai dolene yayi nadama ya zo ya roqeta, ta yi haquri ta yafe masa.
.
Wannan tunanin ne ya dan fara kwantar mata da hankali, sbd in har maganar gsky za'ayi, kome nura zai yi mata ba zata daina sonshi ba." ta riga tun farko tayi sakaci, son shi ya shiga xuciyarta yayi nisa sosai, har yayi mata illa ba tare da ita kanta ta sani ba." in ba domin haka ba,ya ta yaya zata ci gaba da son mutumin da yake qoqarin kasheta sbd kawai ya mallaki wani abin duniya?
.
Ynx ita hauwa ba ma ta wadannan gwala-gwalai take yi ba." bata sonsu, ta tsanesu, sbd akansu ne har masoyinta ya biyota zai kasheta. Ta yaya zata ci gaba da son abubuwan da suka rabata da masoyinta. In banda wadannan gwala-gwalai, da ynx tana can gida tare da masoyinta nura, suna gudanar da hirarsu ta soyayya.m. Wannan dukiyar bata da wani amfani a gareta ynx, wataqila Kuma nura ya koma ya kwashe ya gudu. Ta san ita da nura Kuma har abada, wannan shi ne qarshen zamanta da wanda take so fiye da kowa a duniya.
.
Bayan ta gaji zama da tunane-tunane barkatai wadanda ita kanta ta san a halin ynx basu da wani amfani, sai ta yunqura ta tashi daga korayen ciyayin, xuciyarta cike da tsoro da fargaba, don kuwa bata ta6a tsintar kanta da daddare a cikin daji itakadai ba,ya sai a wannan lkc, da wannan tsautsayi ya fadowa rayuwarta.
.
Hauwa ta rasa hanyar da zata bi ta koma gida. Ta san ba zai yiwa ta iya komawa gida a qasa ba, sbd tafiyar kusan kilomita arba'in suka yi a babur da zasu zo ita da nura...? Ynx abin da yafi mata shine, ta nemi wanni gari mafi kusa, ko wani qauye ta samu ta kwana a can, ta fadiwa mutane 6arayi ne suka biyota da gudu ta fado cikin dajin. Ta san duk wanda ya ganta a cikin wannan halin zai taimaketa, ya mayar da ita gida.
.
Hauwa ta fara daqyar, qafafuwanta suna zogi da radadi, kamar an yayyanka mata su da reza. Ta san ta ji raunika da yawa a qafarta, amma ynx ba tasu take yi ba." ta dai samu ta tsira da rayuwarta, ta koma gida shi ne burinta.
.
Ita kadai akan siririyar hanyar da ta keta ta cikin dajin, tayi ta tafiya sanya da fararen kayanta na aiki, a cikin farin watan kamar fatalwa daga nesa. Tana dingisa qafa, ta cije baki sbd zafin da take ji har tayi nisa. Hauwa ta kai inda wasu manyan fadamu suke, wadanda aka shuka kayayyakin lambu dangin su yalo da albasa, xuwa tumatir da tattasai. Sanyin da ta ji yana ketowa yana ratsa jikinta, shi ya tabbatar mata akwai rafi ko tafki a kusa. Ba ta san koina take ba, duk da haka bata saurara ba,ya ta ci gaba da tafiya tana fatan samun gari ko wani qaramin gari qauye a gaba inda zata yada zango ta roqi mutane su taimaketa, su mayar da ita gida.
.
Sa'ar da Hauwa ta kai inda wasu bishiyun turare suke ne, da Kuma jefi-jefin gwaibobi sai ta hangi wani gida shwal a gefen wata fadama wacce ga alama idan aka wuceta, ba da nisa ba, za'ayi samu rafin da take jin sanyinshi yana busowa.
.
Hauwa ta ji farin ciki ya lulli6e xuciyarta, ta tunkari gidan kai tsaye ba tare da wani tsoro ko fargaba ba, a yadda ta sha wahalar tafiya tana buqatar ta huta, ga kuma yunwa da qishi da suke damunta a lkc guda.
.
Da ta je qofar gidan ne ta iske wata farar mota .yar madaidaicciya ta matasa an ajiyeta ba a shiga da ita cikin gidan ba." Hauwa tayi mamakin kasancewar wannan tsararren gidan da mota a cikin fadamu babu gida gaba babu a baya. Kuma akwai alamar da mutane a ciki, don kuwa ta so ta ji maganar wani namiji.
.
Qofar gidan a rufe take, amma ba a sa kwado ko sakata ba, don haka sai Hauwa ta tura qofar a hankali ta bude ta leqa kanta cikin gidan. Bashi da girma daga ciki, da shigar mutum zai shiga cikin falon dake hade da duk wasu dakuna na cikin gidan.
.
Hauwa ta sa qafa ta shiga cikin gidan, sbd ita a tsammanin ta koma me zai faru da ita, ya fi da ace tana waje cikin daji tare da miyagun dabbobi, bata san me zai sameta ba." sai da ta shiga sannan tayi sallama muryarta na karkarwa.
.
"salamu alaikum!"
.
Ta ji an yi shiru ba a amsa ba." ga kuma hasken fitila a cikin falon, kamar rana fari sol. A wannan karon ma ba taji an amsa ba. Hauwa ta ji tsoro ya cafi xuciyarta, anya kuwa mutanen da suke da wannan gida suma ba mutane bane dake cutar bil'adama?"
.
Kafin ta sake yin wata sallamar ne, a sannan ne ta ga wani mutum ya fito da sauri tun kafin ya qariso tata fahimci hannunsa daya riqe yake da bindiga, Kuma ya saita ta ne a daidai goshinta. Hauwa yayi sumar tsaye xucirta na bugawa da sauri kamar ta fado waje. Tayi gudun gara ta fada gidan zago! Ta kawo kanta inda za a halakata.
.
"wacece ke, Kuma me kike nema?"
.
.
Lp=33}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 33
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"wacece ke, kuma me kike nema?"
.
Mutumin ya daka mata tsawa kuma bai cire bindigar daga saitinta ba." Hauwa ta fara inda-indar magana sbd kaduwar da tayi. Ta ce dashi tana shassheqar kuka.
.
"don allah kayi haquri ban san gidanku bane, wani ne ya biyoni zai kashe ni, shine na gudu ban san inda nake ba' ba zan iya komawa gida ni kadai ba."
.
Hauwa ta fashe da kuka. Mutumin ya sake razana ta da muryarsa dake kama da sautin gangar aikin gayya.
.
"a ina kike, kuma ke wacece?"
.
Ta ce dashi jikin ta yana kyarma.
.
"ni suna na Hauwa, kuma ni likita ce a asibiti nake aiki..."
.
Tun kafin ta kai qarshe sai ta ga mutumin ya saki ranshi ya sauke bindigar da ya nuna mata. Ya tambayeta.
.
"kina nufin kin iya lura da marasa lfy.... Kin iya yin allura da duk wani aikin jinya da likitoci suke yi?"
.
Hauwa ta gyada kai ta ce dashi.
.
"eh, haka ne....! Aikina kenan."
.
Mutumin ya yi dariya ya ce da ita.
.
"sannunki da xuwa Hauwa. Mun yi farin ciki da xuwanki wajenmu. Dama muna da mara lfy, wanda muke xullumin kada ya mutu, yi sauri ki shigo ki duba mana shi, wani tsoho ne, yana da muhimmanci a wajen mu."
.
Mutumin ya matso daf da ita yana yi mata murmushin qarfafa guiwa, don ta kwantar da hankalinta.
.
"kada ki ji tsoro Hauwa."
.
Ya ce da ita.
.
"shigo ki ganshi, sunanshi Nalamma. ni Kuma suna na sadi qare-garke."
.
Hauwa ta ji kamar an jefo mata dutse a saman kanta.
.
.
.
*** ***
.
.
Idan gari ya waye haske ya fara bayyana. duk wata halitta dake rayuwa a yankin dajin tudun kudi sukan fito su nuna jin dadinsu da gamsuwarsu, kamar dai yadda bil'adama suke yi a kowacce safiya a duniyar mutane.
.
A wannan ranar da yake an tashi da yanayi mai dadi, ba a yi ruwan sama ba, kuma babu iska mai qarfi, sai dai daddadan sanyi, wannan shi ya ba duk wani qwaro, da tsuntsaye damar fitowa waje, wasu a sararin samaniya, wadansu kuma a doron qasa. Suma halittun dake a cikin ramuka ba a barsu a baya ba, da yawa sun furfito domein su amfana da wannan yanayi mai gamsarwa, kafin mutane su fara shigowa dajin, su zaluncesu da harbe-harben da suka saba yi na farauta.
.
A can qololuwar samaniyar balbelu ne suke ta sintiri, a qungiyance, kansu a hade kamar masu zanga-zanga, jemagu ne suke a warwatse sun rasa a inda zasu yada zango, kamar masu cinye kasuwar sama.
.
Idan aka koma 6angaren bishiyoyin dake a saman tsaunin, abin sai wanda ya gani. Wata yarinyar kashar-kama ta keto a guje ta miqa wuyanta kamar jirgin sama a yayin da ya diro a filinsa. Wani tukku da tsigi ya rufa mata baya kamar tafiyarsu daya, sa6anin haka sai ta fada cikin wani qaramin iccen talauniya. Shi kuma yayi sama abinsa ya saje da sauran tsuntsaye, ba tare da xullumin wani fin qarfi daga wani jinsi ba."
.
Daga qasa-qasa inda ganyen tafasa ya lulli6e fatar qasar dake a wajen, wani jan barde ne shi kadai ya ware kanshi yana ta rera wani daddadan kuka, wanda da ace za'ayi iya fahimtar kome yake cewa, wataqila yana nuna gdyr san ne da yabawa ga Sarkin sarakuna, kuma buwayi gagara misali, wanda Ya halicci duniya, Kuma ya sanya ta ta zama lkc-lkc daidai da buqatar kowacce halittun mai rai, wadanda suke da qarfi, da kuma wadanda basu da qarfi.
.
Duka dajin a cike yake da koke-koken halittun barkatai, wadanda mutum yake gani, da kuma wadanda suke 6oye a cikin itatuwa da koguna, Suna ganin komai duk da dai su ba a iya ganin su."
.
A daidai wannan lkc ne da duk wadannan halittu suka furfito Suna guddanar da rayuwarsu ta sanyin safiya, wata bafillatana 'yar kimanin shekara ashirin mai Suna rabi ta hawo saman tsaunin riqe da wani bokitin roba qarami mai murfi a hannunta, tana tafe tana rera waqar lawali dan qaura wanda take sonshi fiye da duk wani mawaqin fulani na da da na ynx.
.
Rabi kyakkyawace wacce aka yi wa aure tun shekaru hudu da suka wuce, a sanda ta kai shekaru goma sha-shida mijinta mai suna iro wani matashin ne....! Wanda ya fado daga saman mangoro ya karye, wata takwas kawai da yin aurensu. Tun lkcn, sheksru hudu kenan a haka suke zaune, iro bai warke ba har ynxn, kullum yana a kwance komai sai dai a yi masa, sannan kuma allah bai qaddara kwanakinsa sun zo qarshe ba."
.
A da auren soyayya rabi da iro suka yi. To amma tunda wannan larura ta sameshi, sai Kuma ta fara gajiya da zaman jinyarsa. Tayi iya bakin qoqarinta don ganin an raba auren nasu, ta barshi don ta samu wani mutum mai lfy ta aura, amma iyayenta sun qi yarda, sbd akwai alaqa mai kyau a tsakanin iyayenta da iyayen iro.
.
Duk da ba a barta ta kashe auren nata ba, wannan bai san ta zama mace mai tawakalli ta bi mijinta sau da qafa ba. Tun sanda ta nuna gajiyarta da zama tare dashi, ta qaurace masa, bata yi masa aikin komai, ko dawainiya, sai dai wasu qannensa maza suke yi masa komai, su suke miqar dashi daga kwance su gyara masa zama, su bashi abinci, da kuma magungunan gargajiya da ake amso masa a wurare daban-daban. Su suke yi masa wanka da wanki, amma rabi babu abin da yake hadata da mijinta iro, sai dai ido kawai, ko kuma idan 'yan arziqi suna kusa, ta ce dashi 'sannu' idan ta zo wucewa ta ji yana qugi da matagugun ciwo.
.
Farko tun lkcn da iro ya fado daga sama, an kai shi asibiti, aka buqaci kudi masu yawa. Mahaifin iro kuma bashi da kudi, ko shanu basu dasu a rugarsu, watt nonon da suke amfani dashi, sai dai su sayo a wata rugar dake maqwabtaka dasu.
.
Rabi tana taller nono ita da mahaifiyar iro. Amma sayowa suke yi su kai birni su sayar, su samo 'yar ribarsu wacce suke amfani da ita wajen sayen sabulun wanka da kuma kudin niqa... Da dai sauran qananun matsalolin gida na yau da kullum, wanda mata suke yi tare da 'ya'yansu, ba tare da maza sun tallafa masu ba."
.
Don haka aka tattaro iro aka dawo dashi gida, aka mayar da hankali wajen maganin gargajiya. Rabies bata riqe amana ba,ya sbd idan ta tafi tallar nono gari babu irin shallin da bata yi. Akwai maza fiye da goma da suke nemanta, kuma suna kashe mata kudi, rabi tana da bahauwar waya mai layi biyu, wacce take take kusan kwana tana jin waqoqi idan ta dawo gida. Sutturu masu tsada basu yanke mata, bata dogara da tallar nono ba, tana dai yin garkuwa ne dashi tana xuwa gari ta sheqe ayarta, don kada ace bata yin sana'ar komai, amma tana samun kudi, amma kudin da take samu a wajen sharholiyarta ko rabin-rabinsu bata samu a wajen tallar nono.
.
Kudin da ake buqata a asibiti don yiwa iro aiki, basu wuce dubu dari da talatin ba." da ace rabi ta ga dama, ko ita zata iya hada kudin yau da kullum ta biya a yiwa mijin nata aikin. To amma tun sanda wannan matsalar ta sameshi ba tashi take yi ba, ko iro ya mutu ko yayi rai, wannan kuma matsalarshi ce. Ta dai yi biyayya ta zauna a dakinta, ba ta kashe auren ta gudu ba, amma kuma maganar ace ta tsaya tana wahala akan mijinta iro, safe da rana da yamm, to a nan fada ba zata sa6u ba, wai bindiga a ruwa.
.
Idan ta tashi kullum tunda sassafe zata dauki qaramin bokitinta na roba ta tafi wata ruga dake a bayan tsaunin tudun kudi, wacce suke cewa 'rugar alhaji baffa' a nan ne suke sayo nono sari, da kuma manshanu, su dawo dashi gida su yi 'yan dabarun su na kado wawa, don ya qara auki, sai su shirya su tafi gari talla, rabi bata dawowa gida sai misalin qarfe shida na yamma, wani lkcn kuma ta kan kai dare a can. Ya danganta ga abubuwan da suka tsayar da ita, amma wasu lokutan mutanen da suke nemanta, ko kuma qarancin masu baburan da suke haya a hanyar qauyukan nasu, musamman idan an yi ruwa, hanya ta jagwale da ta6o.
.
A wannan safiyar ma da ta taho tana 'yan waqe-waqenta, rigar alhaji baffa ta nufa. Rabi kyakkyawace doguwa, wacce take da dogayen ga6o6i da surorin halittun. Yatsunta da hannuwa da na qafafuwa duk dogaye ne....! Gashin kanta dogo ne musamman idan ta hadeshi waje guda ta fito da kakkauran gora daya wanda yake fadowa gadon bayanta, sai kace budurwa a birnin hindu. Rabi 'yar fulani kyakkyawace, duk da yake ma a cewar wani attajirin saurayi a birni dake sayar da kayan wuta a shago da take tallar nono a birnin zaria.
.
Ya ce.
.
"da ace rabi a birni ta girma, da ba haka ba." ba ta san ko ita wacece ba, shi yasa take kula kowanne banza da wofi a kasuwa. Amma da rabi zata bayyana kanta kowa ya santa a duniya, da tuni masu shirya fina-finai da kuma masu kudin auren farar mace sun fara raba rana akanta."
.
Rabi tana cikin tafiya ne tazo inda qololuwar tsaunin tudun kudi yake, sai ta ci tuntu6e da wadannsu abubuwa wandanda suke ta qyalqyali kamar gilasai, a yashe a bakin wani rami.
.
.
Lp=34}~~~~~~{ gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 34
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Sai ta ci tuntu6e da wadansu abubuwa wadanda suke ta qyalqyali kamar gilasai, a yashe a bakin wani rami da aka gina, ta Ja ta tsaya cikin sauri tana kallon abubuwan da bata ta6a ganin irin su ba a rayuwar ta...."
.
Rabi 'yar fulani ta sake matsowa daf da su, ta tsuguna ta ajiye qaramin bokitin ta a gefe guda ta qurawa wadannan abubuwa idanu, bata san ko mene ne su ba." to amma da ganin su ta san dolene suyi daraja, wa ya sani ma ko dasu Ake yin tsakiya da Kuma sarqar tatatuna, irin wacce take gani a wuyan kakanninta da suka rage a raye. Wadanda suke bada labarin a qasa ake gino irin wadannan duwatsun a hadasu a zira zare a rinqa daurasu a wuya.
.
Wata kakar rabi wacce ta makance tayi murabus da

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment