Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai janye daga takara, amma kuma bari dai a bashi kwamishinan kowa zai gani a qwaryarsa don kuwa ilimi dolene ya ta6ar6are, duk abin da ya shigo hannunsa na sayen kayayyakin aikin da za a wadata makarantu, shi zai yi ruf da ciki akansu. 'yayansa goma duk makarantun kudi suke yi, idan abin ya tabbata to nan kusa zai kai guda uku qasar Malesiya su fara karatun digiri. Don haka inma harkar ilimi ta palace wannan matsalar talakawa ce. Ya ce da shugaban jam'iyya.
.
"Na janye daga takara, kuma zan bayar da goyon baya dari bisa dari a wannan tafiyar tamu, Allah Ya bamu sa'a."
.
Aka sake kaurewa da tafi a dakin tattaunawar. Saura 'yan takara biyu. Alh. Madugu Bala, da kuma Sanata Dan Iya. Wanda dama shi ne mai ci akan kujera.
.
.
Lp=64}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 64
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni.
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Saura 'yan takara biyu, Alh. Madugu Bala, da kuma Sanata Dan iya, wanda dama shi ne mai ci a kan kujera, yana neman zarcewa. Shugaban jam'iyyar ya nuna Alh. Madugu wanda ya cure a fusace, sanye da farar shadda, da farar hula mu hadu a banki, wacce ta zauna daraf akan qaton kanshi. Ya ce da shi.
.
"Na dawo kanka Alh. Madugu Bala, kaima jam'iyya ta roqi ka janye daga wannan takara, ka barwa Sanata Dan iya Tasi'u ya sake komawa kan kujerarsa a zagaye na biyu. Idan muka sake kama gwamnati Gwamna ya yi maka alqawarin zai baka Kwamishinan gona."
.
Duk sauran mahalarta taron suka juya suka kalli Alh. Madugu. wanda ya ja dogon numfashi sannan ya miqe tsaye ya daga faskeken hannunsa mai kama da faranti ya bugi teburin dake a gabansu, fas! Sannan ya ce a fusace.
.
"Ba zai yiwu ba (Chairman), na gaji da irin wadannan abubuwan da ake yi mana a jam'iyyar nan. A waccan tenuwar ni na fara fitowa neman takara kafin Sanata Dan iya. Amma aka yi sasanci aka ce in bar masa, in yaso a wannan tenuwar ni jam'iyya zata tsayar takara, shi kuma Sanata Dan iya zai yi takarar Gwamna, kowa ya san da wannan maganar, sai ynx bayan mun yi kamfen mun nemi mutane, a zo a ce kuma in janye? To ba zan janye ba, sai dai kome za'ayi a yi."
.
Shugaban jam'iyyar ya hade fuskarsa a cikin damuwa da jin kalaman Alh. Madugu, ya ce dashi.
.
"Amma kai sanin kanka ne Alh. Madugu Bala, Gwamna yana so zai sake komawa kujerarsa shima, shi yasa ya roqeku shi Sanata Dan iya ya koma majalisa ya bar masa takarar gwamna, a taru a hada kai a tafi tare, kai kuma kayi haquri da Kwamishinan gona. Kaga kenan tenuwa ta gaba, shi Sanata Dan iya shi zai yi takarar gwamna, kai kuma kayi takarar Sanata. Ni ina ga ba wani son kai a wannan tsarin, ko kuwa me kuka gani?"
.
Sauran mahalarta taron suka fara magana da junansu. Yawancinsu suna nuna goyon bayan Shugaban jam'iyyar ne na jiha, tunda suma an dakatar dasu daga takara kuma sun yi biyayya, sun barwa mutum daya. Alh. Madugu yayi nazarin alqawarin da aka yi masa na Kwamishinan gona. Ma'aikatar aikin gona ta jihar, tana tallafawa talakawa ne mutanen qauye da kayan aikin gona, da takin zamani a bisa farashi mai rangwame. Babu tallafi ko tausayin talaka a xuciyar Alh. Madugu. A wajensa shi da ire-iren 'yan siyasa masu ra'ayin tara abin duniya, suna neman shugabanci ne don amfanin kansu ba don su gina al'umma su kawowa rayuwar talakawa ci gaba ba, ba domin kowa ya samu sauqin rayuwa a cikin qasa ba."
.
Su in dai zasu ji dadi tare da 'ya'yansu a duniya to buqatar su ta biya. Talaka kuwa ya dade ma bai mutu da wahala ba, wannan matsalarsa ce. Alh. Madugu ya ce da Shugaban jam'iyyar.
.
"Wannan hukuncin ba zai zo qarshe ba a halin ynxn, ina son a bani kwana biyu zan je in yi shawara, idan zan janye xuwa lkcn zan fada, idan kuma na zauna tare da mutanena basu yarda in janye ba, to sai dai mu bar jam'iyyar mu koma wata tunda a nan ba za'ayi mana adalchi ba."
.
Alh. Madugu yana gama fadar haka, sai ya zare kansa daga cikin da'irar kujerun hamshaqan 'yan siyasar suke zaune. Ya fita a fusace ba tare da ya yi wa kowa bankwana ba, ya bar sauran 'ya'yan jam'iyya suna tofa albarkacin bakinsu akan rashin hadin kan da Alh. Madugu ya qi bayarwa da kuma azababbiyar hadamarsa.
.
Alh. Madugu Bala ya shiga motarsa ya nufi gida a fusace kansa yana sarawa kamar zai tsage gida biyu. A yadds 'yan majalisun tarayya suke ca6awarsu da dukiyar al'umma, a wannan zamani na mulkin farar hula, idan jam'iyya bata tsayar dashhi ba, kamar an kashe shi ne da sauran ranshi. To amma duk wannan mai sauqi ne akan masifar dake jiran Alh. Madugu a gidansa.
.
.
.
*** *** **
.
.
Babi Na Sha takwas.
.
"Yarona Ashiru da kazo ka tafi dashi daxu nake tambayarka. Yana ina ne?"
.
Kafintan wanda ake cewa Nama'u ya sake tambayar Najib a karo na biyu, muryarsa cike da qosawa.
.
.
Lp=65}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 65
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
.
"Yaro na Ashiru da kazo kuka tafi tare daxu nake tambayarka yana ina ne?"
.
Kafintan wanda ake cewa Nama'u ya sake tambayar Najib a karo na biyu' muryarsa cike da qosawa. Najib ya yi saurin cire kaduwar da ke tattare dashi ya ce da kafintan
.
"Tun daxu na sallame shi ya tafi. Bai koma wajen aikin ba ne?"
.
Nama'u kafinta ya hade fuska.
.
"Da ya koma nazo in tambayeka inda yake kuma? Kakarsa ce take son ganin sa tun daxu sai aike take yi mana, gashi har mun tashi aiki tun tafiyarku bai dawo ba."
.
Najib ya ji wani abu dake kama da kiyashi yana yi masa yawo a kayan cikinsa, da ya tuno da gawar Ashiru kafinta da ya 6oye a cikin dakin Mu'azzam' inda yake xuba sutturunsa.
.
"Ban san inda ya tafi ba bayan na sallame shi, sai ku je ku neme shi ni sauri nake yi malam zan je wani wuri ne."
.
Najib yana gama fadawa Nama'u haka sai yasa kai ya wuce ya bashi wuri yayi tafiyarsa. Mutumin ya bishi da kallo cikin rashin yadda, har xuwa lkcn da Najib ya tsayar da wani mai babur ya yi masa bayanin inda zai kai shi. Ya hau suka tafi.
.
Nama'u kafinta yayi ajiyar xuciya' ya ci gaba da tsayuwa a qofar gidan Alh. Madugu. ya tabbatar ba halin Ashiru bane wucewa yawo wani wuri daban, duk lkcn da aka aikeshi wani wuri to da zarar ya kammala abin da aka sa shi zai dawo wajen ubangidansa, ya bashi abin da ya samo.
.
Ashiru yaro ne mai ladabi, Nama'u ya daukeshi kamar dansa na cikinsa sbd halin da yaron yake ciki. Ashiru bai cika lfy ba tun yana yaro ya taso da ciwon sikila, gashi kuma maraya ne a hannun wata kakarsa yake zaune, sunanta Tabawa, maqwabciyar su Nama'u ce. Ganin irin zaman da suke yi na babu, suyi ta fadi tashin magani bashi a wajen masu kyamis idan ciwon Ashiru ya taso, sai Nama'u kafinta ya same ta ya ce idan babu matsala ta bashi Ashiru ya koya masa aiki, sbd su riqa samun abin da zasu rage matsalolin rayuwa na yau da kullum.
.
Ba matsalar komaI Nama'u, mun gode da wannan abin arziqi da ka yi mana, dama Kullum haka yake zaune, karatun ma ya gagara tunda aka yi korar kudin makaranta bara Ashiru bai qara xuwa ba."
.
.
Kuna ji ni shiru matsawar kwanaki. Hakan ya faru ne sakamakon rashin karantawarku. Domin kuwa bananas gane adadin mutanen da suka karanta sai in naga comment da like sun kai munzalin da nake tsammanin an karanta din.
.
Tun shekaru biyu da yin wannan maganar Ashiru ya dawo hannun Nama'u kafinta. bayan koya masa aikin da yake yi sai ya mayar da yaron tamkar dan cikinsa. A wajen sa yake ci ya sha kullum, idan ma rashin lfyr tasa ce ta taso Nama'u yake sayo masa magunguna. Tabawa babu abin da take cewa sai dai gdy, idan ana labarin masu taimako a layin ta sha cewa babu sama da Nama'u
.
"tunda dai wanda ya yi maka ai shi ne zaka fada...l"
.
.duk sanda Ashiru ya fito gida da safe ya je wajen aikinsu na kafinta. Kakarsa bata damuwa don taga ya kai yamma bai dawo ba, sbd ta san kama wanne lkcn zai kai bai dawo ba baya wuce wajen ubangidansa Nama'u.
.
.
Lp=66}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 66
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Baya wuce wajen ubangidansa Nama'u' ko dai yana can suna aiki tare, ko kuma an aikeshi wani wuri. Idan ya dawo da daddare kuma sai ya wuce makarantar da wani malami ya bude a wata tsohuwar firamare ta karatun addini. Duk daliban makarantar yawancinsu samari ne 'yan sha-shida xuwa ashirin da biyar' wadanda suke qoqarin su samu ilimin tun ynx kafin shekaru masu xuwa su kasa yi. Don haka Tabawa bata damun kanta, in har Ashiru bashi a gida to ta san inda ya ke.
.
Ba wani dalili ya sa yau tunda yamma ta zo wajen su Nama'u ta same shi ta tambayeshi inda jikanta Ashiru yake ba. Sai don wata 'yar uwarta da ta zo, kuma ba kwana zata yi ba, tana a kan hanya ne, so take yi ta kwana a cikin gari, washe gari tunda safe Gombe zata wuce. Baquwar ta dade rabonta da garin, tun Ashiru bai fi shekaru takwas ba a duniya. Tana so ta ganshi to amma abin takaici tun daxu shiru-shiru Nama'u yana jiranshi ya dawo, bai dawo ba har sai da ya gaji ya zo gidan Alh. Madugu don yaga ko me ya tsare Ashiru. daga kawai gyara katakon, aikin da bai wuce minti biyar ba, amma ya kai kusan awa daya.
.
Ynx da Nama'u ya xo ya yi kaci6us da Najib, saurayin da yazo ya tafi da Ashiru, ya ji ya ce ya sallami yaron Nama'u ya ji duk abin ya 6ata masa rai. Me zai koma ya fadawa Tabawa kakar Ashiru? wacce take faman aiko yara wajen aikinsu, su gani ko Ashiru ya dawo..."
.
Nama'u ya numfasa ya juyo ya dawo jikinsa a sanyaye. A halin ynx an fara kiran sallar magriba a duk masallatan dake a garin, sbd lkc ya yi.
.
Nama'u bai koma gida ba, ya tsaya wani masallaci dake kusa da wajen aikinsu, ya yi alwala ya bi mamu aka yi sallah tare dashi. Ana sallamewa ya fito ya tafi gidan Tabawa don ya gani, Wataqila Ashiru ya koma, wa ya sani ko wani wajen ya shiga bayan ya baro gidan Alh. Madugu? Da kamar wuya tunda dai bai saba yin hakan ba."
.
Lkcn da Nama'u kafinta ya je qofar gidan Tabawa ne ya same ta a waje tare da wata tsohuwa dauke da qaramar jakar gana mas go, Tabawa ranta a 6ace kamar zata fashe da kuka tana cewa Baquwar tata.
.
"Ya za'ayi tunda ya je ya yi zamansa? Ba rabon zaku gana Lantana, wata rana in Allah Ya dawo da ke kya ganshi, ya za'ayi?"
.
Nama'u ya yi turus a tsaye ya tambayi Tabawa.
.
"Wai har ynx bai dawo ba?"
.
Tabawa kakkaurar tsohuwa 'yar kimanin shekaru sittin a duniya ta dago kai ta kalli maqwabcinsu Nama'u kafinta bata san lkcn da yazo qofar gidan ba."
.
"Wallahi bai dawo ba har ynx Nama'u."
.
Ta ce da shi muryarta a karaye da damuwa irin ta kakar dake matuqar son jikanta qwara daya jal da ta mallaka a duniya.
.
"Na je duk inda nake sa ran zan ganshi a unguwar nan, amma kowa sai ya ce bai ganshi ba."
.
Baquwar Tabawa wacce take sauri ta tafi, ta ce da .su.
.
"Ku rabu dashi mana, ko'ina ya je ai zai dawo, abin da ba qaramin yaro ba balle a ce zai 6ace?"
.
Ta rungume jakarta ta ce.
.
"Ni na tafi Tabawa saduwar alheri."
.
Tabawa ta katse wani gajeren tunani da ta fara yi ta ce da baquwarta.
.
"To Lantana ki sauka lfy' Allah Ya kiyaye hanya."
.
Baquwar ta tafi ta barsu, ta nufi bakin titi inda zata hau mota. Ta bar Nama'u kafinta da Tabawa a tsaye. Duhun almurun da ya fara lulli6e garin, bai hana kowannensu ganin alamun damuwar da suke ciki ba. Nama'u kafinta wanda ransa ya fara 6aci ya ce.
.
"Ba zai yiwu ba, gaskiya al'amarin nan akwai ayar tambaya a cikinsa. Ta yaya Ashiru zai je ya yi zamansa har ynx bai dawo ba?" ina yake xuwa a garin nan? Ko bai dawo don wani abu ba, ai ya dawo don ya ci abinci. Gsky ina zargin mutumin nan da yazo ya tafi da Ashiru xuwa gidan Alh. Madugu. Bari kawai muje gidan a san abin da ake ciki Tabawa, ba zama zamuyi mu sa ido ba."
.
"To nima dai shi na gani Nama'u."
.
Ta ce dashi cikin xullumi, muryarta ta fara karkarwar kuka. Ta fara da cewa.
.
"Gashi ynx zamani na siyasar nan, satar mutane ta zama ruwan dare, wa ya san dalilin da ya sa mutumin yazo ya tafi dashi? Alh. Madugu waye bai san mugun halin shi ba a garin nan? Idan ma shi ya aiko a sace mani jikana ai ba abin mamaki ba ne. Tun yaushe ake cewa shima ya shiga qungiyar yankan kai? Ba mu san halin da Ashiru yake ciki ba."
.
Tabawa ta fara kuka. Wannan maganar da ta fada ita ce ta sake tunxura Nama'u kafinta ya ce a fusace.
.
"Zo mu je gidan Alh. Madugun, bari in kira su Auta su zo mu tafi tare, mu tayar da balli don a fito mana da yaronmu. Don an ga mu talakawa ne bamu da komai, sai ace za'a cucemu? Satar mutum da rana qiri-qiri ba wani . 6oye-66oYe?. To wallahi sam' ba zata sa6u ba. Yau akwai bala'i a layin nan..... Daina kuka Tabawa jirani in nemo mutane, kowa ya san halin da ake ciki."
.
Nama'u ya garzaya ya nufi qofar gidan su jikinsa yana tsima. Akwai qaninsa da yake sana'ar shayi da Indomi a wajen, kodayaushe ba a rasa matasa a wajen. Da xuwan Nama'u ya fara hargowa a gabansu ya na cewa.
.
"An sace Ashiru, kuma yana gidan wannan mugun mutumin Alh. Madugu. Daxu-daxun nan da yamma wani gaye ya xo ya same mu muna aiki, ya ce yana so mu bashi mutum daya zai yi masa aiki a gidan Alh. Madugu, shi ne na hadashi da Ashiru. naje na samu gayen ya ce waiga tun daxu ya sallameshi. Kuma in gsky ne da tuni Ashiru ya dawo. Yana can a cikin gidan."
.
Da jin haka matasan dake a wajen suka miqe cikin hargitsi suna zage-zage. Dama zani ne tarar da muje. Matasan unguwar basu son Alh. Madugu, a siyasance bai fito a jam'iyyar da suke yi ba, a zamantakewa kuma baya taimakawa matasa, wadanda suke neman ci gaba, sai 'yan jagaliya da sauran 'yan shaye-shaye. dama kuma koaa yake yi wani abu kyas! Ya hadashi da mutumin a yi masa wulaqanci a layin.
.
Don haka Nama'u yana rufe baki su Auta mai shayi qaninsa suka fara zagin Alh. Madugu. Kowa ya dakatar da abin da yake yi. Matasa suka ce a je gidan a yi fitina dolene a fito da Ashiru kafinta. Nama'u ya ja xugar matasa a qalla su takwas, suka tafi yana gaba suna biye da shi, suna zage-zage da banbami. A hanya mutane suka fara tambayar abin dake faruwa. Wani matashi yana akan babur da ya ji halin da ake ciki, sai ya kafe babur din, ya ruga ya bi tawagar su Nama'u yana cewa.
.
"Ta6! Ai qarya ne wallahi, ku mu je sai an fito dashi ko'ina aka kai shi, satar mutanen da suke yi shi ne har ya fara xuwa kan qannenmu?"
.
Kafin su kai gidan Alh. Madugu an samu mutane sama da talatinn yawancinsu a hanya aka tsincesu, duk mayaqan sa kai ne, masu adawa da Alh. Madugu a unguwar. Da xuwan mutanen suka yi dafifi a qofar gidan suna cewa.
.
"A fito mana da danmu da aka sace, mun bayar da mintuna biyu a fito mana dashi ko mu sa wa gidan nan wuta."
.
.
Lp=67}~~~~~~{ Gobe jar kasa }~~~~~~{
Page 67
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda GiwA
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"A fito mana da danmu da aka sace, mun bada minti biyu, a fito mana dashi ko mu sawa gidan nan wuta."
.
Tabawa wacce ta biyo xugar masu zanga-zangar a baya, ta tsaya gefe guda tana shar6ar kuka' a lkcn ne wani matashi ya daga murya yadda za a ji a cikin gidan ya ce.
.
"Zan qirga goma, Wallahi in ba a fito mana da Ashiru ba, zan sa wuta. Daya..biyu...."
.
Fara kiran sallar da Haj. Maimuna ta ji ne yasa ta shiga dakin Larai wanda yake kusa da nata, ta same ta tayi sheqeqe akan gadonta tana ta sharar barci hada munshari kamar ta kwana tafiya bata huta ba." Haj. Maimuna tayi qwafa sannan ta ce a bayyanane....!
.
"Ai dama na san za a rina. A ce tun safe yarinyar nan ki fita ki bar gidan nan kina can kin liqewa wannan yaron kuna yawo a gari, ko gajiya baki yi. To sai ki tashi ki yi sallah, ba qyale ki zan yi ba, tunda ba ni na aike ki nace ki je ki wuni kina yawo ba."
.
Haj Maimuna mahaifiyar Larai ta sharwa 'yar tata tafi a cinya fau! Haka ta saba tashin Larai daga barci tun tana qarama. Sbd ta san halinta da nauyin barci, in don ta magana ne ko girgiza qafa sai tayi awa daya tana tashin Larai, sai dai ta motsa amma ba zata farka ba, sbd tsabar nauyin barci. Tana gama kwadawa mata hannun Larai tayi firgigit ta farka, ta bude idanunta a lkc guda, ta samu mahaifiyarta a tsaye a bakin gadon, suka hada ido.
.
"Ki tashi an kira sallah, in kin yi sai ki dawo ki sake shantakewa, tunda ke baki san ki yi barci na hankali ki tashi bam idan aka sa maki ido' sai ki kai ggobe baki gaji kin tashi ba."
.
Larai ta tashi ta zauna, tayi hamma, cikin sauri ta tuno da baqonta kuma masoyinta Najib, wanda ke a qasa dakinn kawunta Mu'azzam. Ta tambayi mahaifiyarta
.
"Mama Najib ya shigo ne da ina barci' ko kuwa tunda...."
.
Mahaifiyarta wacce bata son jin maganar Najib a kunnenta ta katse ta da cewa.
.
"Ban ganshi ba, ki tashi ki je inda kika kai shi mana ki duba shi ko baki da qafa ne?"
.
Ta yi tsaki ta juya ta fice daga dakin. Larai tayi ajiyar xuciya, ta tashi ta dauki kallabinta da ya warware tana barci bata sani ba, ta dauka jikinta a sanyaye ta daura, ta san ba wani dalili ya sa mahaifiyarta take yin wannan fushin ba, kawai sai don rashin goyon bayanta akan soyayyarsu da Najib.
.
Larai ta fito daga dakinta, ta fita daga falon ta gangara qasa dakin Mu'azzam don ta gani ko Najib ya tashi. Lkcn da ta je dakin ne ta samu qofar a rufe, a tsammaninta Najib ya tafi masallaci ne....! Don haka sai bata damu ba, ta dawo cikin gida ta shiga bandakinta tayi alwala, ta dawo daki ta sa hijabi tayi sallah, a lkcn an gama sallar a duk masallatan dake a layin. Ta san indai masallaci Najib ya tafi ynx ya isa ace ya dawo, indai ba wani wuri kuma ya tsaya ba." to amma ina zai tsaya, tunda shi baqo ne a garin, kuma wa ya sani a layin da zai je wajensa?
.
Larai ta tashi ta sake komawa dakin kawunta Mu'azzam, ta sake samun dakin a rufe Najib bai dawo ba." abin ya bata mamaki a halin ynxn. Ta yi sauri ta koma ciki ta dauko wayarta dake caji, ta kira lambar Najib. Ta ji wayar ta shiga, ta tsaya tana jiran ya dauka don ta tambayeshi inda ya shiga tun daxu sai nemansa take yi? Wayar ta gama qararrawa ba a dauka ba." da Larai ta sake kiran wayar ne a karo na biyu, ta ji an kashe wayar, wanda hakan ne ke nuna kai tsaye Najib ne ya kashe wayar baya buqatar ya yi magana da ita a halin ynx.
.
Ta ji tsoro da fargaba sun mamaye xuciyarta. Me zai sa kuwa Najib ya kashe mata waya? To amma kada ta yi saurin ganin laifinsa, me yiwuwa Sallah yake yi ta kira shi, shi yasa ya kashe wayar, Wataqila har ynx yana a cikin masallaci ne....!
.
Larai ta zauna tayi tagumi, ta riqe wayar tana kallon agogo a fuskar wayar, ta yi tagumi, ta riqe wayar tana kallon agogo don ta bata Najib lkc koda minti biyar ne, tana sa ran xuwa lkcn idan ma yana sallah ne to ya kammala ya fito.
.
Tana nan zaune har a akayi minti shida bai kira ta ba, don haka sai ita ta sake kiransa. Wayar tana nan a rufe. Larai ta tabbatarwa kanta ko dai da gangan Najib ya kashe wayar, ko kuma cajinsa ne ya qare. Tafi yarda da kashe wayar ya yi, sbd taga wayarsa daxu akwai sauran caji wanda zai iya kaishi har gobe. Wannan tsammanin da ta yi yasa ta ji ranta ya 6aci, ba zata iya gano wani sahihin dalili, da zai sa Najib ya qi daukar wayar ta ba."
.
Larai ta kasa zaunawa, ta sake komawa dakin Mu'azzam ta sameshi a rufe. Ina Najib ya sani a garin shi da yake baqo? Ina zai je bayan sallar magriba? Larai tayi ajiyar xuciya, ta kama hanyar komawa dakinta xuciyarta a karaye. Kafin ta isa ne ta ji ana hayaniya a waje, mutane suna zage-zage a qofar gidansu kamar ana rigimar siyasa a ranar za6e.
.
Kafin Larai ta fahimci abin da yake faruwa ne, ta ga mahaifiyarta ta fito daga cikin falon a kidime. Suka hadu a hanya ita da 'yarta Larai.
.
LaraI ta ce da mahaifiyarta
.
"Me yake faruwa ne?"
Haj. Maimuna ta ce.
.
"Nima ban sani ba."
.
A lkcn ne suka kasa kunne, suka ji wani matashi mai doguwar murya yana cewa.
.
"Zan qirga goma, wallahi in ba a fito mana Ashiru ba zan sa wuta. Daya.biyu...uku..."
.
Haj. Maimuna ta kama hannun 'yarta Larai a tsorace, ta ce.
.
"Mun shiga uku, me kuma muka yiwa mutanen unguwar nan, kin ji suna cewa zasu sa wuta, zo mu fita mu gani Larai
.
Mahaifiyarta ta ja hannunta a guje, suka sauka daga saman benen, suka sake saukowa xuwa qasa su dukansu a rude ko lulli6i babu wacce ta yafa. Sun fito harabar gidan ne inda suke ajiye motocinsu, suka samu dandazon mutane maqil a wajen, wadansu sun kutso cikin gidan wasu suna a waje sun dafa babbar qofar dake a bude. Wanda yake qirgar yana a gaba-gaba, wani marar kunyar saurayi ne, ya sa jar hular sanyi, a lkcn har ya kai takwas, kafin ya ce tara ne, Haj. Maimuna ta fara yi masu magana da qarfin murya a kidime.
.
"Ku tsaya don Allah ku saurara, me yake faruwa? Me muka yi maku?"
.
Fara maganar da Haj. Maimuna ta yi ne, ya sa wasu a cikin mutanen suka rage hayaniyar da suke yi, Haj. Maimuna ta sake basu haquri tana tambayarsu abin da ya kawosu suka yi cincirindo a qofar gidan suna zage-zage. Ta san mijin ta dan siyasa ne babba, kuma ta san yana da abokan hamayya, wataqila sharrin 'yan adawa ne suka turo masu 'yan jagaliya har gida su xo su yi masu rashin mutunci.
.
Da mutane suka lafa da zage-zagen ne sai Nama'u wanda shima yake a gaba, ya dubi matar gidan ya ce da ita.
.
"Hajiya danmu yana a cikin gidan nan, ku fito mana dashi kawai idan kuna son zaman lfy. Ba zamu yarda ba!"
.
Haj. Maimuna ta tambayeshi.
.
"wanne yaro ne yake a cikin gidanmu? Ban fahimceku ba Malam' don Allah kayi mani magana ta hankali yadda zan gane."
.
Nama'u ya ce da ita.
.
"Daxu muna a cikin aiki a wajen da muke sana'''armu ta kafinta, sai wani gaye ya zo ya same mu yace daga nan gidan yake shi baqo ne, yana son a bashi mai gyara, zai mayar masa da wani katako da ya fado a dakinsa. Shi ne na hada shi da Ashiru, tun bayan La'asar har ynx bamu ga

1 Comments On GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4
avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Thanks fatan zaku karo littafan marubuta Maza na baya

Please Login or Register in order to submit comment